Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan takalmi mai tsawon
gaske ne koda zamu kwana bakwai a nan ba zan iya gama
jawabi ba ina sanar dakai cewa makiyanka ne suka ciyar
da wannan doki naka wata ciyawar sihiri don ya haukace
yaje ya hallakar da kai lokacin da ya afka dakai cikin
tekunne na biyoku cini na aza dokin a kaina naci gaba da

tafiya daku kuma na dinga zuko iskar numfashi daga can
saman tekun ina feso muku kuna shaka.
Hm kaji Aikin sihiri .
Wannan shine iyakar bayanin da zan iya yi maka a yanzu
sai kuma idan ka sake ganina a karo na biyu koda gama
fadin haka sai aljanin ya bace bat bacewarsa keda wuya
sai na tashi dokina tsaye na haye kansa na taho nan fada.
Nima yanzu da wannan kalami nake muku sallama don
haka na sallami kowa ya tafi izuwa gida a sanar da sauran
jama a wadanda basu san hallarataba cewa ina nan a
raye ban mutu ba
nan take fada ta watse jama a suka tafi izuwa gidajensu
suna masu farin ciki
Al amarinsu waziri Akiyanu kuwa batun bakin ciki a cikin
zuciyoyinsu ba sai an fada ba domin yadda sukaga rana
haka suka ga dare a wannan rana
kashe gari da sassafe sukayi shiri su takwas suka tafi
izuwa wani kauye da ake kira BAHUS a sirrance don
ziyarar wani maketacin boka wanda ake kira da
SHUBURUL UZAB
.
boka shuburul uzab ya shahara a cikin yankin kasar misra
harma ana ganin cewa in banda boka HADIMUL ASUR
babu wand aya fishi ilimin tsafi
da rana tsaka su waziri suka isa gidan boka shuburul uzab
inda suka iske shi tsaye a kofar gidansa ya kura musu
idanu yana mamaki koda suka matso daf dashi sai ya
dubesu ya tuntsure da dariya yace..
Lale marhaban da manyan baki wadanda na dade ina
jiran zuwansu a irin wannan rana........
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama su waziri
Akiyanu suka sauko daga kan dawakansu cikin sanyin jiki
gaba dayansu suka risina suka kwashi gaisuwa sannan
waziri ya dubi boka shuburul uzab cikin nutsuwa yace.
Yakai wannan boka mai daraja kai kuwa menene dalilin
da yasa kace ka dade kana jiran zuwanmu gareka?
Idan har kana son mu ziyarceka me yasa tuntuni baka
aika mana muzo ba?
Koda jin wannan tambaya sai boka shuburul uzab ya
bushe da dariya sannan yace yakai babban waziri ka sani
cewa amsar wannan tambaya tana bukatar a saurareta a
cikin nutsuwa ku kuwa yanzu gashi babu nutsuwa a tare
daku domin kun gaji ainun kuma kuna bukatar abinci da
abin sha don haka zaifi kyau mushiga daga cikin gidana
ku zauna ku sami nutsuwa tukunna.
.
Ba tare da wata gardama ba sai su waziri Akiyanu suka bi
boka shuburul uzab a baya har izuwa cikin turakarsa da
zuwa suka iske an tanadar musu shimfidu da abinci da
abin sha irin nasu na sarakai.
Kawai sai boka shuburul uzab ya umarcesu da su zauna
su kintsa cikinsu shi kuwa sai ya wuce zuwa wani dakin

daban bai fito ba sai bayan sun gama kimtsa cikinsu boka
shuburul uzab ya zauna a gefe daya yana mai fuskantarsu
boka shuburul uzab yace yaku wadannan manyan baki
na sani cewa kuna cikin matsanancin bakin ciki bisa
rashin samun nasarar hallaka sarki Aminul has?
.
.
Tabbas ba zaku taba samun nasara ba face kun rabashi
da wannan sandar tsafi da takalmin sihiri duk duniya
babu wanda zai iya taimaka muku ku sami nasarar
rabashi da wadannan abubuwa face mutum biyu.
Na farko shine boka hadimul Asur sai kuma ni din nan ni
kuwa ba zan taimaka muku ba face kunyi mini wani abu
guda daya.
Cikin matukar mamaki waziri Akiyanu ya dubi boka
shuburul uzab yace kai kuwa menene abin da kake son
muyi maka.
Boka shuburul uzab yayi murmushi sannan yace ina son
ku sato mini dokin nan na sarki Aminul has wanda yai
tafiya dashi a can karkashin teku,
domin na ciri wani sinadarin tsafi a jikinsa wanda shi ne
zan cika burina na duniya.
Cikin mamaki Akiyanu ya dubi boka shuburul uzab yace
to ai wannan doki bashi da wani sihiri a jikinsa,
boka shuburul uzab ya kyalkyale da dariya yace kaine dai
baka sani ba ai sakamakon daukan da wannan guntun
Aljanin yayi masa yanzu ya sami sirrikan tsafi guda dari
ba daya irin na sadauki awaisu.
Akiyanu ya sake tambaya wane ne kuma sadauki Awaise?
Boka shuburul uzab yace sanin wannan bashi da wani
mahimmanci a gareku yanzu saiku amsa mini muradina
kafin na gaya muku hanyar da zakubi ku raba aminul has
da ababan dogaronsa.
Shin kum amince zaku sato mini dokin.
Waziri akiyanu yace kwarai kuwa ai sato wannan doki a
garemu abu ne mai sauki tamkar wanke hannu da ruwa,
boka shuburul uzab yayi dariya sannan yace to shi kenan
sai ku tashi ku tafi izuwa birni na baku kwana biyu rak ku
sato wannan doki ku kawo mini kuna kawo mini shi nayi
Alkawarin zan gaya muku yadda zakuyi ku raba aminul
has da sandarsa da kuma talakawansa na tsafi don ku
sami damar hallakashi.
Koda gama wannan jawabi sai boka shuburul uzab ya
lumshe idanunsa ya bace bat daga cikin turakar koda
ganin haka sai suma suka hau dawakansa suka nufi birnin
misra.
Basu isa cikin gari ba sai da dare ya soma maimakon su
rarrabu kowa ya tafi gidansa sai suka sake dunguma gaba
daya suka tafi izuwa gidan waziri Akiyanu suka sake sabon
zama na musamman don tunanin hanyar da zasu bi su
sami nasarar sato wannan doki na sarki Aminul has,
abinda su waziri akiyanu basu sani ba shine boka

shuburul uzab yaudararsu zaiyi kawai amma a zahirin
gaskiya ba zai iya raba sarki Aminul has da abubuwan nan
biyu ba.
Sihirin da yake so ya cire a cikin jikin dokin Aminul has
kuwa shine irin sihirin dake jikin yarinya Alfila yar sadauki
Awaisu kuma irinsune a jikin wannan sanda da takalmi na
aminul has.
Duk abinda wannan guntun Aljanin ya taba da
hannayansa sai ya sami wannan sihiri dalilin haka ne
dokin Aminul has ya sami wannan sihiri.
++ ++ ++
Acan birnin Askandariyya kuwa lokacin da sarki sahibul
hairi yaci gaba da labewa a cikin fadar sarki barusa yana
hangen abubuwan dake faruwa kawai sai ya gga wata
kyakkyawar mace ta gaban kwatance ta baiyana a
gabansa tana mai yi masa murmushi.
Har ya yunkura zai bar wajan ta dakatar dashi tace tsaya
na nuna maka hanyar da zaka bi kaje inda gatarin sihiri
yake in kuwa kabi wata hanya daban halaka zakayi cikin
matukar mamaki da rashin yarda sarki sahibul hairi ya
dubeta yace ke kuma wacece kuma saboda me zaki nuna
mini inda gatarin sihiri yake alhalin kuna son wannan
gatari fiye da komai a cikin birnin nan?
Kyakkyawar tace babu isashshen lokaci da zan iya maka
bayani yanzu amma bayan ka sami nasarar dauko gatarin
sihirin zanyi maka bayanin komai.
Koda gama fadin haka sai ta jashi izuwa wani sako daban
sukaci gaba da tafiya suna ratsa wadansu manyan dakuna
har saida suka shige cikin dakuna dari koda suka isa
gaban kofa ta dari da daya sai kyakkyawar ta tsaya tace
gatarin sihiri na cikin wannan daki a rataye a jikin bango
kuma akwai dakaru mutum dubu uku a ciki masu tsaron
gatarin wadanda suka kasance karfafa kuma sadaukan
gaske yanzu saika shiga cikin dakin ka yaki sadaukan
dubu ka karkashesu sannan ka fito na saka a hanyar da
zaka fita daga cikin gidan sarautar nan sannan kuma nayi
maka jagora izuwa gidan boka shamzubul azwas don
dauko yarinya Alfila yar sadaukin duniya Awaisu''. An ya
kuwa nima ba zan bisu ba kuwa ganin yadda mace take
son raka sarki sahibul hairi?.
Koda jin wannan batu sai sarki sahibul hairi ya cika da
tsananin mamakin yadda akayi wannan kyakkyawar
budurwa ta san dukkan shirinsa har ya budi baki da nufin
ya sake yi mata tambaya sai tace dashi.
Na gaya maka cewa bamu da isashshen lokaci a yanzu
wanda zan yi maka bayanin komai don haka kayi sauri
kaje ka dauko gatarin sihirin nan.
Koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya bude wannan kofa
ya kunna kai ciki ba tare da fargabar komai ba yana shiga
kuwa ya hango gatarin sihiri a rataye a jikin bango sai
sheki da walwali yake tsaitsaye a gaban bangon da aka
rataye gatarin wadansu murza murzan kartine majiya

karfi su dubu uku kowannansu a tube daga shi sai kamfai.
Kuma duk suna rike da manyan makamai ababan
tsoratarwa wani makamin ma tunda sarki sahibul hairi
yazo duniya bai taba ganin irinsa ba su dai wadannan
karti sun ninka sarki sahibul hairi sau uku a girma da cika
ido gaba dayansu kansu daya tamkar tagwaye kai kace
mace daya ce ta haifesu rana daya.
Koda kartin sukaga sarki sahibul hairi ya shigo cikin dakin
sai suka yi masa kawanya su duka kowannansu ya kama
gyara makaminsa shima sarki sahibul hairi sai ya gyara
tsayuwarsa a cikin farin kayan karfe yana jiran yaga
wanda zai fara afko masa..
Kamar hadin baki sai suka tasammasa gaba daya a lokaci
guda ya zamana kowa na kai masa sara da suka shi kuwa
sai ya zama tamkar shaidani a tsakiyarsu yayi ta kare
kansa yana mayar musu da martani nan fa aka yi ta
gumurzu dauki ba dadi da fafatawa tsakanin sarki sahibul
hairi da dakaru masu tsaron gatarin sihiri.
Sai da aka shafe sa a biyu a haka subasu barshi ya sami
damar isa inda gatarin yake ba shi kuma ya kasa hallaka
koda daya daga cikinsu domin idan ya samu sa ar sarar
jikinsu ma sai yaga kaamar dutse ya sara babu abinda
yake samun su wani abu daya kara firgita sarki sahibul
hairi shine ko kadan dakarun basa gajiya kuma basa
alamar cewa zasu gaji sarki sahibul hairiya tabbatar da
cewa idan akaci gaba da wannan fada a haka zata kai
cewa ya gaji sun samu lagonsa
.
Don haka ya zama wajibi a gareshi yayi tunanin mafita ba
zato ba tsammani sai dakarun sukaga ya sauya salon fada
dabarar da yayi kuwa itace ya fara tsalle tsalle yana taka
kawunansu yana karawa gaba a haka suka rinka kaiwa
kafafunsa sara amma saboda zafin namansa sai suka kasa
cimmasa bare samunsa
.
Kafin su ankara ya daka tsalle ya dira akan gangon da aka
rataye gatarin sihiri nan take ya yarda takobin hannunsa
ya suri gatarin
duk da cewa gatarin nada matukar nauyi amma sai gashi
da hannu daya ma sarki sahibul hairi ke jujjuyashi.
sa adda dakarun sukaga sarki sahibul hairi ya suri gatarin
sihiri sai suka sake yin caaa a kansa da nufin su
ragargazashi shi kuwa sai yayi amfani da gatarin yaci gaba
da saransu wohoho
a wannan lokacine labari ya sha bambam domin duk
wanda ya sara da gatarin sai dai kaga ya faskarashi gida
biyu.
..
Sarki sahibul hairi yaci gaba da ragargazarsu tamkar mai
yanke kabewa kafin a jima yai fata fata da su babu sauran
mutum daya a tsaye gabansa koda yaga ya sami wannan
nasara sai ya cika da tsananin murna kawai sai ya saba

gatarin a kafadarsa ya bude kofar dakin ya fito.
.
A wannan lokaci duk jikinsa yayi kaca kaca da jini hatta
fuskarsa kuwa sai da ya cire hular karfen dake kansa
sannan ya goge jinin akan idanunsa fitarsa ke da wuya sai
yaga wannan kyakkyawar budurwa a tsaye tana jiransa
koda ta gasnhi rike da gatarin sihiri sai ta tareshi da farin
ciki ta kama hannunsa
.
Faruwar hakan keda wuya sai suka face bat a tare suka
bayyana cikin wata babbar turaka wadda akayi matukar
kawata da kayan kawa iri iri daga can kuryar kudu an
ajiye wani shimfidadden gado na alfarma irin na sarakai
kwance akan gadon kuma a lullube cikin mayafi ba wani
bane face bawa HALUF yana ta sharar barci tamkar
wanda ke dakin matarsa.
.
Nan fa sarki sahibul hairi ya cika da tsananin mamaki
domin shi a saninsa ya baro bawa haluf a can bayan gari
toyaya akayi ya shigo har ma ya sami jiki yana barci mai
nauyi haka.
Koda kyakkyawar budurwar ta fahimci cewa sarki sahibul
hairi na mamakin ganin bawansa haluf a cikin wannan
turaka sai tayi murmushi sannan ta zauna a gefen gadon
tana mai fuskantar sarki sahibul hairi tace dashi.
.
Yakai wannan jarumi uban jarumai ai saika zauna don ka
huta sannan na baka amsoshin tambayoyin da kayi mini
dazu sarki sahibul hairi ya dubeta cikin kaduwa yace
yanzu ni ina na ga lokacin zama alhalin nayi sata a cikin
wannan gidan sarautar kuma na tabbatar da cewa da
zarar an ankara cewa an dauke wannan gatari dole ne a
bazama nemana''
.
Koda jin wannan batu sai kyakkyawar ta dubi sarki
sahibul hairi da wani irin kallo mai tattare da alamomin
tambaya tace ka kwantar da hankalinka yakai mai birnin
Misra ka sani cewa kana tare da wadda tafi kowa sanin
sirrin gidan nan.
Gama fadin haka keda wuya sai ta mike tsaye taje kan
wani tebul ta dauko tambulan na ruwan inibi tazo Gaban
sarki sahibul hairi ta ajiye kofunan ta tsiyaya ruwan inibin
a ciki sannan ta dauki kofi guda ta mika masa guda take
ta kai kofin bakinta ta fara shan ruwan inibin
,
ya yinda sarki sahibul hairi yaga ta sha ruwan inibin sai
shima ya sha nasa kyakkyawar tayi dariya tace ai nasan
cewa in ban shaba kaima ba zaka sha ba domin akwai
alamar cewa kana zargi zan iya ha intarka''
.
Sarki sahibul hairi yayi murmushi ya ce ai a duniya idan
akwai abinda nake tsoro bai wuce kaidin ya mace ba

domin zata iya sawa mutum ya rasa mulkinsa dukiyarsa
da rayuwarsa gaba daya.
.
Kyakkyawar tai murmushi tace hakika zancenka dutse ne
to amma ina sonka saki jikinka dani domin nai maka
alkawarin ba zan cutar dakaiba.sarki sahibul hairi yace to
shikenan na gode.
Yanzu kafin ki bani labarin komai ina son ki gaya min
yadda akayi bawana haluf ya shigo cikin wannan turaka
taki har ya kama barci haka tamkar yana cikin dakinsa
kyakkyawar na jin wannan tambaya sai tayi murmushi
tace na yarda zan baka wannan labari amma dole sai na
fara da gabatar da kaina a gareka da farko dai ni sunana
gimbiya shukura kuma nice matar sarki barusa mai
mulkin wannan birni na Askandariyya.
.
Koda jin wannan batu sai tsoro ya kama sarki sahibul
hairi ya mike tsaye daga inda yake zaune ya danja da
baya yace ke kuwa menene dalilin da ya sa kika ci amanar
mijinki har kika taimaka mini na dauko wannan gatarin
nasa na sihiri??
.
Sa adda gimbiya shukura taji wannan tambaya sai ta
bushe da mahaukaciyar dariya tace ai cin amanar maci
amana ibadane yakai wannan jarumi kayi sani cewa
asalin sarautar birnin nan ta mahaifinace amma tun ina
cikin mahaifiyata uban sarki barusa ya kashe mahaifina
alhalin ya kasance babban amininsa kuma wazirinsa don
wai ya gaji dukiyarsa da karagar mulkinsa
A wannan lokaci sarki barusa baifi shekara bakwai ba ni
kuwa kamar yadda na gaya maka ko haihuwata ba ayi ba
amma mahaifiyata na dauke da cikina wata shida bayan
shekara bakwai sai uban sarki barusa ya mutu
sakamakon cutar ajali don haka sai barusa ya gajeshi
yana da shekara goma sha bakwai a duniya ni kuma a
lokacin ina da shekaru goma kacal.
.
Tun kafin sarki barusa ya hau kan karagar mulki ya shaku
dani ainun kuma yake nuna min tsananin kauna A zahiri
ina nuna masa kauna amma cikin zuciyata na kanji na
tsaneshi kamar yadda na tsani mutuwata mahaifiyata ta
bani labarin cewar a gaban idanunta mahaifin barusa ya
kashe mahaifina ya haye kan karagar mulkinsa amma bai
san cewa tana labe tana gani ba
.
Dama mahaifiyar tawa ta lura da cewa baruwa na sona
don haka saita rokeni da na yarda na aureshi ko don na
samu damar daukar fansar ran mahaifina akansa da
wannan manufa a zuciyata na girma na isa aure a lokacin
da aka daura mini aure da sarki barusa tsawon shekara
shida ina tare dashi bamu samu haihuwa ba kullum sai
nayi yunkurin hallakashi amma sai na kasa bisa wannan

dalili ne na fake da batun tafiyar neman maganin
haihuwa wajen bokaye amma a zahirin gaskiya ba
maganin haihuwar nake nema ba
..
Dama nake nema wacce zan iya hallaka sarki a cikin
yawona neh na hadu da wani shahararren boka wanda ya
sanar dani wai ba zan taba samun damar hallaka sarki
barusa ba face na mallaki wadansu sirrikan tsafi guda
dari ba daya su kuwa wadannan sirrika suna nan a jikin
wata karamar yarinya mai suna alfila
.
Yar wani mashahurin matsafi kuma jarumin gaske ana
kiransa da suna awaisu koda naji wannan batu sai na
tambayi bokan nace yanzu ya za ayi naje inda wannan
yarinya take har na sami sirrikan tsafi daga gareta?
.
Bokan ya kyalkyale da dariya sannan ya murtuke fuska
kamar an aiko masa da sakon mutuwa yace ke yarinya
baki isa kije inda wannan yarinya take ba domin tana can
cikin wani gida dake tsakiyar tekun bahar zallus mallakin
sarkin bokayan aljanu na duniya mai suna shamzubul
Azwas.
.
Yarinya ke dai baki isa kije wannan wuri ba har ki sami
ikon shiga cikin wannan gida amma idan kikayi hakuri
nan da wadansu yan shekaru kadan akwai wani jarumin
sarki da zaizo birninku neman gatarin sihirin da kuke
bautawa idan kika taimaka masa ya mallaki gatarin sihirin
za ki iya tafiya tare da shi izuwa tsuburin bahar zallus ku
shiga har cikin gidan boka shamzubuk Azwas ku dauko
yarinya alfila a sannan ne saiki biya bukatarki ta samun
surrikan jikinta''
.
Lokacin da bokan yazo nan a zancensa sai na tambayeshi
nace tayaya zan iya cire sirrikan tsafin daga jikin
yarinyar?
Koda jin wannan tambaya sai bokan ya bushe da dariya
yace ai wannan kuma aikinmu ne na bokaye ba naku ba
kedai da kinga kun dauko yarinyar saiki san dabarar da
zakiyi ki raaba abokin tafiyar taki da ita ki kawota gareni.
.
Tunda naji wannan batu sai naji hankalina ya dugunzuma
naji cewa ko kadan ban yarda da wannan boka ba da ga
wannan rana na dada jajircewa wajan neman ilimin tsafi
nayi yawo kasa kasa gari gari ina ziyartar bokaye ina yi
musu alheri mai yawa suna koya mini tsafi sannu a
hankali nima na zama gawurtacciyar bokanya a sirrance
ba tare da mijina ya sani ba.
.
Don haka a yanzu ina sanar dakai cewa hadimul asur so
yake kawai ka Kawo masa wannan yarinyar don cika
burin rayuwarsa amma ba dan ya biya maka bukata ba ni

a yanzu nayi maka alkawari indai ka taimaka mini muka
dauki alfila na ciri sirrikan tsafinta guda dari ba daya
zanyi tsafin da zaka zamo attajirin da babu kamarsa a
duniya zaka auri wadannan yan mata uku da babu
kamarsu a duniya kuma sunanka da mulkinka zasu
shahara ko ina cikin duniya.
Sa adda gimbiya shukura tazo nan a jawabinta sai sarki
sahibul hairi yayi shiru ya shiga tunani mai zurfi yana
juya al amarin a ransa daga can saiya dago kai ya dubeta
yace.
Na gamsu da duk jawabinki kuma na amince zan baki
hadin kai domin mu cika burin rayuwarmu yanzu saiki
amsa mini tambayar da nayi miki akan yadda akayi
bawana yazo cikin turakarki
.
Har ya kama barci mai nauyi akan gadonki na alfarma
nan take gimbiya shukura ta kwashe labarin duk abinda
ya faru tsakaninta da bawa haluf ta zayyana masa har
izuwa sa adda ta yaudareshi da batun zata ceci rayuwarsa
da ta maigidansa dalilin da yasa ya bata kansa kenan suka
kwanta tare shukura tace maganar gaskiya ban tara da
bawa haluf dan na samu haihuwa ba sai don kawai naci
mutuncin mijina
.
Kuma naci amanarsa saboda yadda nasan cewa yana
tsananin tsanar bakar fata a rayuwar to yau gashi
matarsa da yake matukar so fiye da komai a rayuwarsa ta
kwanta da bakin fata kuma bawa.
.
Lokacinda gimbiya shukura tazo nan a zancenta sai
takaici da mamaki suka kama sarki sahibul hairi ya jinjina
kai yace hakika ku mata ababan tsoro ne domin dafinku
da kaidinku yafi na maciji saurin tasiri a jikin dan adam
hakika sai yanzu na fuskanci cewa ba karamar ni ima
nake ciki ba da banyi aure ba
shukura na jin wannan batu saita bushe da dariya tace
haka kuma ba karamar ni ima kayi asara ba domin duk
mutumin da bai taba yin aure ba ya rasa kaso tamanin
cikin dari na dadin duniya.
.
Zama da su fitina rashinsu kuma asara sarki sahibul hairi
ya ce har yanzu dai ban fahimci wannan karatu naki ba
abinda nake so dake yanzu mu ajiye wannanzancen
komai a gefe daya kawai ki fitar damu daga cikin gidan
sarautar nan mu tafi izuwa tsibirin bahar zallus don shiga
gidan boka shamzubul azwas mu dauko yarinya alfila
gimbiya shukura tayi murmushi tace yanzun nan zan
aikata haka amma dai ina mai dada yi maka tuni da
cewar ka manta da batun bokanka hadimul asur cewar
zai taimakeka idan ka kai masa yarinya alfila tabbas
yaudararka zaiyi kawai ya biya tasa bukatar abinda nake
so dakai shine ka bani wuka da nama indai muka mallaki

alfila tamkar burinmu gaba daya ya cika ne sarki sahibul
hairi yayi murmushi yace ai shi kenan na amince da duk
abinda kika shirya na baki wuka da nama..
.
A zuciyar sarki sahibul hairi ko kadan bai baiwa gimbiya
shukura amana ba don haka duk yadda zaiyi ba zai yadda
ta rabashi da alfila ba bayan sun daukota daga gidan boka
shamzubul azwas acan karshen zuciyar sarki sahibul hairi
sai yaji yana wasu wasu dangane da al amarin boka
hadimul asur yaji cewa shima bai yarda da shiba kawai
akawai alamun cewa shima akwai wani abinda yake so ya
mallaka shiyasa yake son mallakar yarinya alfila
.
Abinda sarki sahibul hairi ya yankewa kansa hukunci
shine indai ya sami nasarar dauko yarinya alfila kai tsaye
zai tafi da ita zuwa ga mahaifinta sadauki awaisu sannan
ya nemi taimakonsa bisa nemo wadannan yan mata uku
.
Sahibul hairi yace a cikin ransa idan idan har sadauki
awaisu ya cika dan halak wanda yasan mutunci kuma har
idan kaunar da yake yiwa yarsa dari bisa dari ce to lallai
ba zaiki taimakonsa ba idan ya sada shi da alfila
.
Sahibul hairi na cikin yin wannan tunani gimbiya shukura
ta runtse idanunta ta fara karanto wadansu dalasimai na
tsafi fara hakan keda wuya saiga wata jibgegiyar halitta ta
ratso ta cikin saman rufin dakin kamar haske ta fado a
gaban shukura wannan halitta ba komai bace face
ALJANU DABARUS.
ALjani dabarus na da siffa irin ta bil adama wato yana da
hannaye kafafu kirji wuya da kai sai dai kansa rabkeke ne
yana da wangamemen baki cike da hakora hancinsa ma
wawakeke ne amma idanunsa yan kanana neh ko yaushe
jawur suke kamar gauta yana da dogayen kunnuwa
wadanda suka kara masa muni fuka fukansa manya ne
guda biyu
.
Koda saukar aljani dabaru a gaban gimbiya shukura sai
ya rusuna ya kwashi gaisuwa sannan yace ya shubata me
kike bukata daga gareni?
Ki sani cewa a shirye nake na sallama rayuwata don
faranta miki shukura ta dubi aljani dabarus tace bukatata
dakai kawai itace ka daukeni da wannan jarumin ka
kaimu can tsibirin bahar zallus inda gidan boka
shamzubul azwas yake koda jin wannan batu sai aljani
dabarus ya kwalla ihu ya fadi kasa.
Yana birgima da tuba yace kiyi min rai ya shugabata ki yi
sani cewa tsakanin mutum ko aljan duk wand aya
kusanci gidan boka shamzubul azwas take yake narkewa
ya dige ya zama ruwa don haka ina mai rokonki daki
sauya min aiki da wata bukatar amma ba wannan ba
.... Koda jin wannan batu sai gimbiya shukura ta dakawa

aljanu dabaru tsawa tace kai sha saha sha banza ai ba
cewa nayi dole saika kaini har kofar gidan ba zaka iya
ajiye mu nesa da gidan koda ya kai tafiyar rabin sa a ce
mu mun san yadda zamu karasa can kai kuwa saika
jiramu a baya inda zaka iya tsayawa Aljani dabarus ya
saki murmushin murna yace yauwa yanzu naji kan zance
wannan ai ba matsala bace saiku hau bayana mu dau
hanya
.
Koda jin haka sai shukura ta bude wata akwatu ta dauko
wata garkuwa ta zinare ta mikawa sarki sahibul hairi tace
ka ruke wannan domin zata maka amfani a gidan boka
shamzubul azwas ba tare da gardama da fargabar komai
ba yasa hannu ya karbi wannan garkuwar da hannun
hadu
A hannun dama kuwa ya damke gatarin sihiri nan take
shukura ta taba kafadar bawa haluf kawai sai ya farka
daga barci ya mike zaune zumbur a firgice,
amma da yaga sarki sahibul hairi tsaye a gabansa ruke da
gatarin sihiri da bakuwar garkuwa sai murna ya kamashi
gimbiya shukura ta dubi sarki sahibul hairi tace ai saika
hau kan aljani dabarus ka zauna daga gaba dani da haluf
mu zauna a bayanka.
Sarki sahibul hairi yace wannan ba laifi bane nan take
kuwa ya hau kan bayan dabarus ya zauna faruwar hakan
keda wuya sai haluf da shukura suka yunkura da nufin
suma su hau bayan dabarus:
bazato batsammani sai sukaga bangon dakin ya dare gida
biyu saiga sarki barbusa ya ratso ta ciki sanye da bakaken
kayan yakin nan wadanda sarki sahibul hairi ya gani a
gidan karkashin kasa a sakale a jikin bango tare da
fararen daya sa da kuma jajaye.
ni kaina bayyanar sarki barusa a wannan lokaci ya
razanani kamar ba zan iya ci gaba da typing din ba amma
nayi ta maza naci gaba...
Sarki barusa ya dubi gimbiya shukura cikin tsananin
bakin ciki idanunsa cike da hawaye yace yake bakar
annamimiya maci amana ki sani cewa karyarki tasha
karya domin baki isa ki ha inceni ba har ki hada kai da
makiyina don a nakastani a rabani da abin dogarona
wato gatarin sihiri.
.
Na dauki so da kauna na gaskiya na baki tun muna yara
kanana ashe ke ba kaunata kike ba asalima so kike ki
hallakani to kin makara domin na gaba yai gaba na baya
sai labari ki sani cewa duk hirar da kukayi yanzu tsakanin
ki da wannan sarki duk na gani a cikin madubin tsafina
don haka naji dalilin da ya sa kike son ki hallakani don ki
dauki fansar mutuwar mahaifinki.
.
Haba shukura ni idan kika ce dole a kaina zaki dau fansa
bakiyi mini adalci ba domin babu sa hannu na akan

mutuwar mahaifinki
asalima sa adda aka kasheshi ina yaro karami ban san
abinda yake faruwa ba ba wai ina fadin haka bane donki
janye ra ayinki sai donki sani cewa ke kin cika butulu
maci amana haka kuma naji da bakinki kina cewa kin
kwana da wannan bakin bawa don kawai kici amanata ki
tozarta mutuncina tabbas kin sami nasara bisa hakan
amma ki sani nima sai na tozartaki irin tozartawar da ba a
taba yiwa wata ya mace ba a duniya kuma saina
wulakantaki fiye da kima a cikin wannan birni namu na
askandariiya yadda duk mai kaunarki idan ya tuno da
abinda nai miki sai ya

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment