Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuri
sai hanyar daya biyo ta shafe ya zamana cewa babu
batun komawa da baya babu gaba sahibul hairi ya gyara
tsayuwarsa yana wulkila idanuwansa izuwa kowanne
bango yana jiran duk abinda zai baiyana gareshi bazato
ba tsammani sai ya ga wadansu irin gabza gabzan
dodanni suna ta fitowa ta cikin gango tamkar haske suna
yi masa kawanya Adadin dodannin yakai dari biyar kuma
kowannensu yana rike da zabgegiyar makami kai koda
guda daya daga cikinsu aka turo birnin Misra zai iya
tarwatsa birnin gaba daya wasu da majaujawa ce mai
kula kulan tsini wanda girman makaman kadai yafina bil
adama bare kuma su kansu don haka lokacin da
dodannin sukayi masa kawanya sai ya zamo dan mitsitsi a
tsakiyarsu don dayansu ma zai iya tatsileshi da kafa daya
babu abinda zai firgita mutum face irin munin fuskokin
dodannin don idan mutum ya cika kura musu idanu
zuciyarsa zata iya tashi kumallo bayan dodannin sun
gama yiwa sarki sahibul hairi kawanya sai suka kama
karkada makamansu suna jujjuyasu koda ganin haka sai
shima sarki sahibul hairi ya kama wasa takobin hannunsa
yana jujjuyata .
Lokaci guda dodannin suka kawo masa wawan duka da
sara da makamansu cikin zafin nama sarki sahibul hairi
ya daka tsalle sama har saida ya tabo rufin saman dakin
koda makaman dodannin suka bugi kasa sai suka haifar
da wawakeken rami tamkar rijiyar da karti hamsin suka
kwana suna hakwa A sama sarki sahibul hairi ya fara
saran dodannin amma sai yaji kamar karfe yake sara don
har tartsatsin wutane ke tashi nan fa dodannin sukayi ta
kai masa sara da suka yana zukewa kuma shima bai fasa
saran su ba tuni hankalin sarki sahibul hairi ya
dugunzuma domin ya san cewa idan aka jima ana
wannan artabu gajiya zaiyi in kuma ya gaji take dodannin
zasu gama dashi Lokacinda dodannin sukaga sarki
sahibul hairi na wahalar dasu ya zame musu alakakai sai
suka fara wani irin sabon gurnani mai tsananin kara
wanda ka iya sa kunnan mutum ya dode ba shiri sarki
sahibul hairi ya yagi rigar jikinsa ya nannadata a kansa
wato ya rufe kunnuwansa yaci gaba da artabu amma
dukda haka saida kunnuwansa sukayi dum ! Kamar an
zuba masa ruwa a ciki ana cikin wannan gumurzu ne
daya daga cikin dodannin ya yagi kirjin sarki sahibul hairi
da faratan hannunsa guda uku.. .
Take wajan ya dare tamkar an sareshi da takobi uku a

lokaci guda har saida jini yai tartsatsu sarki sahibul hairi
ya kwarar uban ihi saboda tsananin jin zafin da yayi ya
fado kasa magashiyan . Koda ganin haka sai dodannin
sukayi ca a kansa gaba daya da mugun nifi kowannansu
ya zaro faratan hannunsa da nufin su yi tsire da gangar
jikinsa cikin tsananin zafin nama sarki sahibul hairi yayi
katantanwa a tsakiyarsu yana filfila takobinsa ya fice fit ta
karkashin kafafuwansu .
Lokacinda suka kawo masa suka da faratanne bisa
tsaursayi wani daga cikinsu ya caki wani da farce a
tsakiyar kai take wanda aka caka aka kansa ya huje saiga
jini yai tsira sama take ya sulale kasa matacce . Wani
kuma da ya soki wani a hannu sai ya tsinke masa hannu
koda sarki sahibul hairi ya fahimci abinda ya faru sai yayi
wata irin yar dungure a kasa ya mirgina sau goma a cikin
dakika daya ya suri guntulallen hannun dodon da ya
guntule ya mai dashi makaminsa .
Ai kuwa sai fada ya sauya salo domin da farcen hannun
dodannin ya dinga yiwa dodannin barna wato yayi ta
saran jikinsu jini na zuba amma saboda naci da taurin kai
saikaga sunyi girgiza sun ci gaba da kokarin hallakashi
babu abinda zai burge mmutum kuma ya bashi mamaki
face yadda sarki sahibul hairi ke yin wannan yaki cikin
matukar karfin hali da juriya domin tuni jiri ya fara
dibarsa sakamakon jinin dake zuba a kirjinsa amma duk
da haka yaki yarda ya fadi kasa kuma bai fasa ci gaba da
ragargaza su ba abindake tayar masa da hankali shine
basa mutuwa .
Saida aka shafe sa a ana wannan artabu ya kasa kashe
dodannin su kuma sun kasa hallakashi amma kuma suma
sun fara nakasa shi domin sun yayyankeshi da kaifin
faratansu gaba daya jikinsa yai fata fata da jini kamar
yadda nasu yayi A wannan lokacin ne sarki sahibul hairi
da dodannin suka kamalayi kamar wadanda suka sha giya
suka bugu Wohoho hakika idan namiji ya cika namiji
baya faduwa kasa banza sai dai ayi ragas sai da ya rage
saura kiris ayi mutuwar kasko sai sarki sahibul hairi ya
sami nasarar sukar tsakiyar kan daya daga cikinsu nan
take kuwa dodon ya sulale kasa matacce .
Koda ganin haka sai sahibul hairi ya tabbatar da cewa
ruhin dodannin a tsakiyar kansu yake nan fa ya ringa
tsalle a kansu kamar dan biri cikin zafin nama tamkar
walkiya yana ta soka musu farcen a tsakiyar kawunansu
sai gashi dodannin suna sulalewa kasa matattu tamkar
ana sassabe a gona cikin abinda bai wuce dakika dari da
sittin ba gaba daya dodannin suka zama gawa . Koda ya
gama kashe dodannin sai shima ya sulale kasa sumamme
sarki sahibul hairi bai farfado ba sai bayan sa'a biyu
farkawarsa keda wuya sai yaji kirjinsa na yi masa
azababben zugi da radadi koda ya dubi kirjin yaga
wannan lafcecen yanka guda uku sai hankalinsa ya
dugunzuma domin ya tabbatar da cewa wannan rauni zai

iya zama sanadin ajalinsa don har yanzu jini na zuba a
jikin rauninnan fa ya fara tunanin hanyar da zaibi ya yiwa
kansa magani yana cikin hakan ne wata dabara ta fado
masa da jan ciki ya rarrafa yaje kan gawar dodo guda ya
cisgi gashin kansa sili uku sannan ya dauki guntulallen
hannun dodon ya sa a bakinsa ya fisgi farce guda sannan
yayi amfani da wani farcen ya yanke wannan farcen da ya
cisge har saida ya mayar dashi dan siriri kamar allura . Da
wannan allura da kuma silin gashin dodon ya dinke
raunin dake kirjinsa guda uku bayan ya kammala dinke
raunikan ne ya jingina bayansa a jikin bango yai shiru
yana hutawa da tunani tabbas yanzu dai ya san cewa ba
zai iya shiga cikin daki na biyar ba face ya zauna yayi
jinyar raninsa a kalla kwana bakwai .
Abin tambayar anan ya za ayi ya rayu har tsawon kwana
bakwai a cikin wannan daki baci basha? Kai idan ma
akwai abinci da sha ai gawan dodannin ma idan ta rube
warinta kadai ya isa ya kashe shi wai shin ma masifu
nawa ne suka rage a gabansa kafin ya samu ya fita daga
cikin wannan wuri na karkashin kasa?
Koda yazo nan a tunaninsa sai zuciyarsa ta karaya
nadama ta sake zo masa a karo na biyu ya fara sabon
tunani . Lokacin da sarki sahibul hairi yayi tunani har
tunanin ya ishe shi sai yace da kansa kai wannan banzan
ba zai fishsheni da komai ba abinda zai fishsheni kawai
shine na yi tunanin hanyar da zan iya rayuwa a cikin
wannan daki har tsawon kwana bakwai . Sarki sahibul
hairi ya shiga sabon tunani ai kuwa bai dade ba yana
wannan tunani sai dabara ta fado masa cikin karfin hali
ya mike tsaye yana kama gawarwakin dodannin yana
zuba su cikin ramin nan da suka yi sakamakon kawo
masa sara da makamansu sai bayan ya zuba fiye da rabin
gawar a ciki ya fuskanci cewar ramin ba zai cinye
dukkanin gawar ba bisa dole ya sake fito da gawarwakin
ya shiga aikin daddatsa gawarwakin gutsun gutsun sai dai
ya yi sa a biyar yana wannan aiki sannan ya gama
daddatsa su duka.
Daya gama sai ya kwashi kadan daga cikin sassan jikin
dodannin ya ajiye gefe guda kuma ya saro kofaton dodo
guda biyu ya ajiye da yai haka sai ya dure gangar jikin
dodannin duka a cikin ramin sannan ya kama bako kasa
yana watsawa cikin ramin har saida ya binne wannan
sassan jiki duka a cikin ramin . A sannan ne fa ya gaji likis
kuma ya jike sharkaf da gumi kamar an tsamoshi daga
kogi saida ya huta tsawon rabin sa a sannan ya sake
mikewa yaje gaban kofaton dodon da ya ajiye ya
tsugunna kawai sai ya maida kofaton kyastu ya dinga
goga daya akan daya har izuwa tsawon lokaci sannan yayi
sa a wuta ta kama a jikin naman dodon daya hada waje
daya . Kawai sai ya kurawa wutar da naman idanu har
saida naman ya babbake gaba daya kawai sai ya kama cin
naman dodon yana ci yana zubar da hawaye ba komai ne

ya haddasa wannan hawaye ba face tsananin rashin
dadin naman dodon da kuma tsananin takaicin da ya
tsinci kansa a ciki ya tuna cewa shifa sarki ne guda amma
yau gashi ya tsinci kansa a cikin wannan mugun hali har
ma yaci danyen naman zaki kuma yaci naman dodo haka
dai sarki sahibul hairi yaci gaba da cin wannan naman
cikin matukar juriya har saida yaji cikinsa ya cika yana
gamawa kuma sai yaji kishirwa ta addabeshi a sannan ne
fa ya gane kuskurensa domin ko kadan baiyi tunanin
hanyar da zai magance kishi ba . Bisa dole ya kama
kwankwadar jinin dodannin nan da ya malala a kasa cikin
dakin nan ma saida ya sha ya ishe shi sannan ya bingire
kasa cikin jini ya kama barcin dole Allah sarki ita masifa
ba a samata rana ita kuwa kazar wahala indai mutum ya
yankota to sai ya fige abarsa .
HAKa dai sarki sahibul hairi yaci gaba da rayuwa a cikin
wannan daki na hudu har izuwa tsawon kwana bakwai ya
zamana cewa bashi da abinci sai wannan babbakakken
naman dodon daya tanada ruwan shanshi kuwa wannan
jini ne nasu har saida jinin ya daskare amma bai daina
shansa ba ahaka duk da cewa jinin yana wari da karni
mai tayar da zuciya . A ranar kwana na bakwai ne sarki
sahibul hairi yaji kwarin jikinsa kuma wannan rauni na
kirjinsa ya kame nan take sarki sahibul hairi ya mike tsaye
ya sungumi gatari daya daga cikin na dodannin nan da ya
kashe shi kansa saida ya hada karfinsa waje guda sannan
ya iya daga gatarin sama . Nan fa ya shiga saran bango
domin ya samarwa da kansa hanya ta fita bai gushe ba
yana saran bangon har saida yayi sa a uku ta shude
sannan ya sami nasarar fasa garun kofa ta samu kawai sai
ya yarda gatarin ya kunna kai cikin daki na biyar . Shidai
wannan daki na biyar ya bambanta sosai da sauran
dakunan hudun da ya wuce a cikinsu domin ko kadan
babu duhu a cikinsa a haskake yake fayau kamar rana
babu komai a cikin dakin face wasu manyan akwatuna
guda bakwai wadanda aka rufesu ruf da wani irin
murjejen kwado mai kaurin gaske kafin mutum ya iya
sareshi sai ya jike sharkaf da gumi .
Koda sarki sahibul hairi yayi arba da wadannan
akwatunan sai yayi tsaki yace '' To meye gamina da
wadanna akwatuna Ai ni hanya kawai nake nema da zan
fita daga cikin karkashin kasar nan '' koda gama wannan
furuci sai ya koma da baya izuwa wannan daki na hudu
ya dauko gatarin nan ya dawo ya kama saran bangon
daki na biyar din don ya sami hanya koda ya fara saran
bangon sai yaji kamar karfe yake sara koda ya kara kaimi
sai bakin gatarin ya kama dakushewa al amarin da ya
dugunzuma hankalinsa kenan amma saboda naci bai fasa
sara ba har saida ya gaji likis yaga babu alamar nasara
sannan yayi jifa da gatarin ya tsugunna a kasa cikin
alamun bakin ciki da karayar zuciya . Ya kurawa
wadannan akwatunan bakwai idanu ya shiga tunani'' to

wai in banda abinka ai gatarin sihiri kazo nema babu
mamaki ma yana cikin daya daga cikin akwatunan nan
don haka me zai hana ka jarraba bubbude su ka gani '' .
Wata zuciyar kuma sai tace kai kada ka bude akwatin nan
domin wata kila wasu masifunne aka tanada a ciki haka
dai sahibul hairi yayi ta tunani iri iri ya kasa yanke
hukunci daga can sai ya mike tsaye yaje ya kwankwasa
akwatin farko baiji alamar akwai wani abu a ciki ba . Ya
kara kunnansa a jikin akwatin nanma yaji shiru babu
alamar wani motsi a ciki kawai sai ya mike tsaye yaje ya
dauko gatarin nan ya kama saran kwadon makullin
akwatin ta farko aikuwa bai dade ba yana saran ya
bincineshi . Sarki sahibul hairi ya sunkuya ya cire kubar
sannan ya daga murfin akwatin dagowar ke da wuya sai
yaji wasu abubuwa kaman kwari sun yi fitar burgu daga
cikin wannan akwatin sun doki fuskarsa saboda karfin
dukan saida yayi sama ya gwaru da rufin saman dakin ya
fado kasa a galabaice . Ba wasu abubuwa bane suka fito
daga cikin wannan akwatu face wasu yan kananan aljanu
wadanda girmansu bai wuce na fara ba Adadinsu yakai
miliyan daya su duka suna wata irin kara mara dadin ji .
Kafin sarki sahibul hairi yayi wani yunkuri tuni sun
sureshi sunyi sama dashi suka rinka gwarashi a jikin
bango basu saukeshi ba saida sukaga sun farfasa masa kai
da jiki ya suma .
Bayan sun sauke shi ya rikito kasa sai suka rinka curewa
waje guda da kadan kadan kafin su gama curewa sai sarki
sahibul hairi ya farfado koda ya gama kyallara idanunsa
ya hango wadannan kananan aljanu suna curewa a waje
guda ba tare da sanin abinda suke shirin yi masa ba sai
hankalinsa ya dugunzuma tabbas ya san cewa ba zai iya
yin fada da wadannan aljanun ba kawai sai ya yunkura
cikin zafin nama ya dauki . Akwatin da suka fito daga ciki
ya kifa a kansu ta rufe su fuf to amma ya rufe daki ya
kulle da barawo domin akwai ragowar kimanin guda
dubu da bai rufe dasu ba duk da cewa ya zauna akan
akwatin sai da suka ringa girgiza suna kokarin jefar dashi
daga kanta don su fito waje shikuwa sai ya yi amfani da
dukkan karfinsa wajen danne akwatin yayinda ragowar
aljanun suka ga an danne yan uwansu a cikin akwatin sai
suka tasamma sarki sahibul hairi suna kai masa cizo da
yakushi nan fa sarki sahibul hairi ya raba karfinsa da
hankalinsa gida biyu .
Ya zamana cewayana yaki da wadannan aljanu dubu
kuma yanaci gaba da kokarin danne wannan akwatin
wadda ya zauna a kanta. Sudai wadannan aljanu suna da
fuka fukai don haka shawagi sukeyi kawai akan sarki
sahibul hairi suna kai masa hari tako ina shi kuwa ya
wanzu yana kai musu sara cikin zafin nama da takobinsa
takobin bata iya yi musu komai amma karfin dukan da
yake shine yake kadar dasu su fadi kasa. Ana cikin
wannan dauki ba dadi ne daya daga cikin aljanun ya sami

nasarar kafa hakoransa akan kafar sarki sahibul hairi
aikuwa koda ya ciza sai ya finciko. Sai ga gudan tsokar
nama a bakinsa tsananin zafi da zugin da sarki sahibul
hairi yaji ne yasa ya kwala kara mai karfin tsiya. Wadda ta
firgita aljanun suka ja da baya a dai dai wannan lokaci ne
ya lura da cewa aljanun da ya danne a cikin akwatin da
yake kai sun daina motsi koda ya sunkuya kansa sai yaga
jini na malalowa waje. Cikin sauri ya daga akwatin sai
yaga ashe gaba daya aljanun sun mutu. Ba wani abu bane
ya kashe wadannan aljanun face rashin iskar da zasu
shaka numfashi A farko kafin sarki sahibul hairi ya bude
wannan akwati a saman murfinta akwai hudoji masu
yawa wadanda koda mutum ya leka ta cikinsu ba zai iya
hango abin dake ciki ba sirrin ruhin wadannan aljanu
shine ko yaya suka daina shakar iska a duniya sai jikinsu
ya kama daddarewa shi yasa da aka kullesu a cikin
wannan akwatin aka hurhuda samanta. . Sa adda sarki
sahibul hairi ya kifesu da akwatin a kasa ba sa shakar
numfashi shiyasa suka mutu lokacin da sauran aljanun
guda dubu sukaga gaba daya yan uwansu sun mutu sai
suka harzuka suka sake afakawa sark sahibul hairi da
nufin su hallakashi farat daya shi kuwa sai yaci gaba da
makesu da wannan takobi tasa.amma duk wanda ya fadi
kasa sai ya sake tasowa tamkar babu abinda ya sameshi
sai da aka shafe sa a hudu ana wannan gumurzu in banda
rauni na farko da aka yiwa sarki sahibul hairi a kafa babu
abinda ya sameshi amma kuma gajiya ta fara riskarsa . Su
kuwa wadannan aljanun kamar ma a sannane suka fara
fafatawa koda sarki sahibul hairi ya fuskanci cewa idan fa
akaci gaba da wannan fada izuwa wani lokaci zasu
hallakashi sai ya sauya shawara cikin zafin nama ya suri
wannan akwatin ya ruke a hannunsa duk aljanin da ya
make a sama suka fado kasa kafin su yunkura su sake
tasowa sai ya kifesu da wannan akwati ya take akwatin da
kafarsa guda yana mai ci gaba da saran sauran ba zai
daga akwatin ba har saiyaga jini na fitowa daga
karkashinta a haka a haka har sarki sahibul hairi ya samu
da kyar da sidin goshi ya karar da wadannan aljanun
duka . Nan fa ya tsugunna kasa yana numfashi sama
sama cikin karfin hali ya yagi rigarsa ya daure wannan
rauni dake kafadara don tsaida jinin sannan ya kurawa
ragowar akwatunan shida idanu yana shawara a cikin
zuciyarsa akan ya budesu ko kuwa kada ya bude. Wata
zuciyar tace dashi ''ya za ayi kaci gaba da bude wadannan
akwatuna alhali baka san masifar dake cikinsu ba''.
Wata zuciyar tace dashi kuma' ++ to idan baka bude
akwatunan ba me zakayi tunda baka da wani zabi wand
ayafi hakan''. Koda gama wannan tunani sai ya mike tsaye
yaje kan akwati ta biyu ya dauki gatarin nan ya kuma
saran kwadon sannu a hankali ya bincine kwadon yasa
hannu ya zareshi ya daga murgin akwatin sama faruwar
hakan keda wuya saiga wata katuwar kunama ta fito daga

ciki tunda sarki sahibul hairi yazo duniya bai taba gainin
kunama mai girma kamarta ba . Koda kunamar tayi arba
da shi sai ta tasammasa tana wurkila kafafuwanta guda
goma sha biyu masu fitar da dafi ga kuma kaifin farata.
Sarki sahibul hairi ya kama ja da baya ita kuma taci gaba
da binsa har sai da ya kure a jikin bango. Nan fa suka fara
mugun artabu ya zamana cewa tana kawo masa suka da
kafafuwanta ta ko ina shi kuma yana kare kansa gami da
kai mata suka amma duk inda ya soka a jikinta sai yaji
kamar dutse ya soka ko kwarzanewa bata yi Al amarin da
ya dugunzuma hankalinsa kenan. Ya tabbatar da cewa
bashi da wata sauran dabara face yayi iya yinsa inda
karfinsa ya kare shi kenan haka dai aka ci gaba da
fafatawa kunamar ta kasa hallaka sarki sahibul hairi
shima ya kasa cutar da ita har izuwa tsawon lokaci ana
cikin hakane kunamar tayi masa wata irin mahaukaciyar
sura tayi sama dashi ta makashi a jikin bango ya fado
kasa . Cikin tsananin galabaita harma yaji ba zai iya tashi
ba koda ganin haka sai kunamar ta taho gareshi cikin
tafiyar kasaita da nufin ta caka masa kafafunta shida ta
zuba masa dafi... ... .
Koda ta iso daf da shi ta daga kafafuwan nata sama zata
cakeshi sai ya yunkura cikin zafin nama ya daka tsalle ya
haye samanta kawai sai ya kama naushin idanunta da
hannunsa guda ita kuwa ta rinka kawo masa suka da
kafafunta yana kadasu da takobinsa nan fa suka yi ta
wutsil wutsil da mirgin mirgin ya zamana cewa ta kasa
cafkoshi shi kuma ya kasa burma idanunta . Koda ganin
wanki hula zai kaishi dare sai ya fusata ya dunkule
hannunsa ya tattaro karfinsa duka ya gabzawa kunamar
mahaukacin naushi a ido take kwayar idon ta fashe
hannunsa ya lume a cikin idon tamkar an zura guga a
rijiya saiga jini na bulbulowa nan fa kunamar ta kama
tamagungun. . Cikin hanzari sarki sahibul hairi yya daka
tsalle ya dira a kasa daga kanta kunamar taci gaba da
birgima a kasa tana wani irin gurnani da kakarin mutuwa
tun tana motsi sai data sandare komai na jikinta ya daina
aiki. .
A sannan ne hankalin sarki sahibul hairi ya dawo jikinsa
ya kawo gwauron numfashi ya ajiye ya kurawa gawar
kunamar idanu jim kadan sai kuma ya dubi akwati ta uku
ya fara tunanin budeta sarki sahibul hairi ya mike tsaye
yaje kan akwatin. . Har ya sunkuya zai dauki gatari ya sare
makullin sai ya fasa kawai sai ya dauki gatarin ya wuce
izuwa kan akwatin kashe ya kama saranta koda ya balle
makullin ya budeta sai yaga wani irin haske ya fito daga
cikinta ta bugi jikin bango take zanen kofar ya fitar da
kansa sai ga wata kofa ta bayyana kuma ta bude kanta
wanda ta cikinta ne za a iya shiga cikin daki na shida sarki
sahibul hairi ya kurawa kofar idanu cikin tsananin
mamaki yace '' Oh! Na yankewa kaina wahala yanzu inda
na bude sauran akwatunan can da yanzu ina cikin masifa.

. Gama fadin hakan keda wuya ya yarda gatarin dake
hannunsa ya dauki takobin ya kunna kai cikin wannan
kofa ta shiga da shigarsa kofar sai ya tsinci kansa a cikin
wata wangamemiyar fada wadda aka kawatata ainun da
abubuwan ban sha awa komai dake cikin fadar an
sassakashi ne da dutsen lu'u lu'u don haka fadar ta
haskake da sheki da walwali . Sarki sahibul hairi yaci gaba
da tafiya a cikin fadar yana wuce wadansu gumaka
wadanda aka yi su cikin siffofin dukkanin sarakunan da
suka mulki birnin Askandariyya sarki sahibul hairi yaci
gaba da tafiya a cikin fadar nan yana kallon abubuwan al
ajabi iri iri ba tare da ya taba komai ba . Kwatsam sai ya
hango wani karamin baho na zinare a tsakiyarsa an kera
wani kyakkyawan dawisu na karfe ruwa na diga daga
cikin bakin dawisun yana zuba a cikin bahon har ya dan
taru mamaki ya kama sarki sahibul hairi bisa yadda
makerin wannan dawisu da bahon yayi basira wajan
sassakasu . Abinda yafi bashi mamaki shine ta ina wannan
ruwa yake shiga cikin jikin dawisun har yake digowa kasa
ta cikin bakinsa sarki sahibul hairi ya zagaye bahon yaga
babu ta inda ake zuba ruwan sai ya dada cika da mamaki
kawai sai sha awar dawisun ta debeshi ya dafa kansa
faruwar hakan keda wuya sai wadansu kibiyoyi suka rinka
cillo kansu ta ko ina zasu soke sarki sahibul hairi. Cikin
zafin nama ya rinka karkade kibiyoyin amma sai yaga
kibiyoyin sunki karewa saboda haka sai ya zabura ya
kama gudu a cikin katon dakin yana gudu yana karkade
kibiyoyin ta gaba ta baya. Hakika in ba don sarki sahibul
hairi ya kasance mai tsananin zafin nama ba da tuni sama
da kibiyoyi dari sun cake a jikinsa duk da zafin namansa
sai da kibiyoyi uku suka cakeshi. Har ya fada bayan wani
gunki ya labe kibiyar farko a cinya ta cakeshi ta biyu a
bayansa wajan kuibin kafadar hagu ta uku kuwa a
hannunsa na dama. Cikin tsananin galabaita ya fadi
sharam!! A bayan gunkin a sannan ne kuma kibiyoyin
suka daina cillo kansu daga inda suke fitowa cikin
tsananin dauriya sarki sahibul hairi ya zare kibiyar dake
jikin hannunsa jini yai tsartuwa yana mai rusa ihu saboda
tsabar zafi da zugi A haka ya zare kibiya ta biyu da ta uku
sannan kuma ya daure inda kibiyoyin suka cakeshi da
tsumman rigarsa dan tsaida jini gama yin hakan ke da
wuya sai yaji jiri ya debeshi nan take ya sulale kasa
sumamme. .
Sarki sahibul hairi bai farfado ba sai bayan rabin sa a
yana bude idanu ya tsinci kansa anan inda yake. Wato a
bayan wannan gunki kawai sai ya mike tsaye da kyar yaci
gaba da tafiya a cikin katuwar fadar saida yayi doguwar
tafiya sannan ya kure karshenta ba tare da ya sake shiga
wani hadarin ba kawai saiyaga wadansu kayan yaki kala
uku na karfe a rataye a jikin bango. . Daya bakine daya
fari daya kuma ja kowannensu rigane da wando da hula
kuma da takalmi har da takobi sarki sahibul hairi ya

kurawa kayan yakin idanu yana shawarar wanda ya
kamata ya dauka ya sanya a jikinsa da ya dubi bakaken
kayan da farko sai yace.. Kai shifa bakin abu duk inda
yake ba abin sha awa bane kuma kalace mai nuna
mugunta don haka bazansa bakin ba. Ya dubi jajayen
yace. Shikuma jan abu ai kalace ta ban tsoro mai nuna
alamun tashin hankali don haka bazansa jaba. Ya dubi
farin yace. Yauwa fari kalace ta adalci da nuna alamun
tausayi don haka zu sansa.....
Sarki sahibul hairi ya ci gaba da cewa
yauwa fari kalace ta adalci da nuna alamun tausayi don
haka su zansa ba tare da fargabar komai ba sai ya dauki
fararen kayan ya sanya a jikinsa tsaf
wohoho duk wanda yaga sarki sahibul hairi a cikin
wannan shiga ta fafaren kayan yaki dole ne ya bashi sha
awa kuma ya bashi tsoro saboda sunyi masa kyau
matuka kuma sun kara bayyana kwarjininsa a fili
.
Gama sa tufafin ke da wuya sai yaga wata kofar ta
bayyana a jikin bango kai tsaye ya nufi kofar ya shiga
cikinta sai gashi yana ratsawa ta cikin wadansu kofofi
wannan na bin wannan tun yana irga kofofin har sai da
ya gaji ya daina nan fa sarki sahibul hairi yayi ta ganin
abubuwan tsoro iri iri da abubuwan mamaki kala kala
amma duk inda yazo sai yaga ya wuce lafiya ba tare da
wani abu ya same shi ba mamaki ya turnuke sarki sahibul
hairi
.
Abin da bai sani ba shine duk wanda yasa wadannan
fararen kaya na yaki babu wani mahaluki walau mutum
ko aljan da zai iya ganinsa kai hatta tsuntsaye da dabbobi
ma bazasu iya ganinsa ba face mutum daya kwal a duniya
ba wani bane face sarki barusa mai birnin Askandariyya
.
Sai da sarki sahibul hairi ya wuce kofofi dubu tara da dari
tara sannan ya iso gaban wata matattakalar kasa koda
ganin wannan matattakalar sai murna ta kama sahibul
hairi
kai tsaye ya khau kanta ya kama tafiya har ya iso
karshenta inda yaga wata kofar koda ya bude kofar saiya
hango cikin fadar sarki barusa ga jama a nan a cike an
kewaye sarki barusa ana fadanci
.
A lokacin wani mai baiwa sarki labari na zaune a gabansa
yana ta sharara labari mai ban dariya sarki barusa na ta
kyakyatawa saboda karfin dariyar tasa ma kiris ya rage
bai fado kasa ba daga kan karagar mulkinsa cikin sauri
sarki sahibul hairi ya fito daga cikin dakin ya kulle kofar
ba tare da kowa ya ganshi ba sannan

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment