Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin jarumtakarsa ya tabbatar da cewa Badakaren ya
sha gabansa. Sarki Sahibul Hairi ya dubi Badalaren ya ce,
"wai shin kai wana irin mutun ne mai karfi kanar na
zakuna? Na rantse da darajar burin da ke gabana ban
taba ganin sadauki kamarka ba. Kai kuwa ya ya akayi ka
sami nasara sadaukantaka?".
Koda jin wannan tambaya sai Badakaren ya yi murmushi
bai ce komai ba, kuma ya nuna da cewa kawai du ci gaba
da tafiya a cikin gidan.
Ya yin da sarki sahibul Hairu ya fuskanci nufin Badakaren
sai ya ce, "na yar da zamuci gaba da tafiya, amma ina mai
rokun alfarma guda daya. Na gamaka da girman
Ubangijin da kake bautawa da ka ya ye rawanin fuskarka.
Bana so murabu banga fuskarka ba, domin na samu
damar bayar da labarinka da cikkakkiyar kwatancen
suffarka".
Sa'adda Badakaren ya ji bukatar sarki Sahibul Hairi sai ya
yi masa nuni da hannu cewa ya yi hakuri sai nan gaba zai
ga fuskarsa.
Koda gama fadin hakan sai Badakaren ya juya ya ci gaba
da tafiya. Bisa dole sarki Sahibul Hairi ya bishi da sauri
yana mai dafa kafadarsa inda yaji rauni sabo da zugin da
yake masa.
A sannan ne tunanin Bawa Haluf ya fadowa sarki sahibul
Hairi ya ce a ransa, "tabbasa Haluf tsananin furgita ne ya
sashi suma. Amma babu komai, nasan zai farfado kuma
zai biyo bayanmu".
Badalaren da sarki Sahibul Hairi suka ci gaba da kurdawa
acikin gidan Boka Shamzabul Azwas, amma sai da suka
sake shafe wata rabin sa'a busu sake haduwa da wani
mugun abu ba. Ba zato ba tsammani sai sula ga wadansu
irin jibga-jibgan Dodanni munana sun yi musu kawanya
ba tare da ganin ta inda suka bello ba. Daga sama ne ko
daga kasa ne, Allahu ya alamu.
Sudai wadannan dodanni adadinsu ya kaidubu daya. Ko
wnnansu na dauke sa mulmulallan sugumi mai kaco-
kacon tsini. Fyskar dodannin a rube take har tsutsa na
zuba, sai dai kaga suna ciro tsutar suna jefawa a bakinsu
suna cinyewa. Idan daya daga cikinsu ya yi tafiya sai kaji
karar sawunsa tamkar ana goga karfe a makera da
katuwarguduma.
Lokacin da sarki Sahibul Hairi yaga wadannan dodanni
sunyi nusu kawanya babu ta inda zasu iya ratsewa su
wuce, sai hankalinsa ya dugunzuma ya sare, domin ya
tabbatar da cewa ajalinsa yazo.
Shi kuwa Badakaren sai ya zare takobinsa guda biyu ya
gyara tsayuwar cikin cikin yarda da kai yana jiran mai
tsautsayin da zai fara dirfafoshi.
Koda ya fuskanci cewa sarki Sahibul Hairi ya tsorata da
ganin wadannan dodanni, sai ya dafa kafadarsa ya yi
masa murmushi yana mai nuna masa alamun kara masa
kwarun gwewa.
Ai kuwa sai shima ya zare takobinsa suka hada baya da
bada suna waige-waige don kada dodannin su
shammacesu. Kamar hadin baki sai dodannin suka ruga
gaba dayansu a lokaci guda da nufin suyi musu rubdugu
Cikin zafin nama Badakaren ya daka tsalle sama yana mai
cafar sarki Sahibul Hairi da hannu daya ya tashi sama da
shi, sai gasu a saman Dodannin. Su kuwa Dodannin sai
suka yi gware da junansu. Sautin haduwar kawunan
Dodannin kamar ana rugurguzo duwatsu. Koda su
Badakaren suka wado kan Dodannin sai suka hausu da
sara da suka, amma sai hakan ya zamo a banza, domin
kaifi da tsini baya tasiri a jikinsu. Nanfa Dodannin suka
dinga kaimusu wafta da hannayansu da nufin su cafkesu,
amma sabo da tsananin zafin nama irin na Badakaren sai
yaki yarda Dodannin su sami nasarar cafke su din. Tabbas
in badan kokarin Badakaren ba da tuni Dodannin sun
cafke sarki Sahibul Hairi sun halakashi, domin zafin
namansu ya fi nashi, na Badakaren yafi nasu.
Koda aka dan jima kadan a cikin wannan hali, sai hanlalin
Badakaren ya dugunzuma, donin ya san cewa idan aka ci
gaba da gumurzu a haka ba tare da ya gani lagon
Dodannin ba, komai zai iya faruwa, wato Dodannin za su
iya hallakasu shi da sarki Sahibul Hairi. Nan take dabara
ta fado masa a rai, ya ce, "bari ya jarraba ya gani. Cikin
hanzari Badakaren ya takarlare ya naushi daya daga cikin
Dodannin da dukkan karfinsa a cikin kunne. Bisa mamaki
sai kawai hannun ya burma cikin kunnan na dama ya bull
ta cikin na hagu. Take Dodannan ya sulale kasa matacce.
Koda da ganin haka sai shima sarki Sahibula hairi ya
jarraba hakan, shima ya sami nasara.
Wohoho! Nan fa suka yi ta burma kunnuwan Dodannin
suna zubar da su kasa. A wannan lokaci Sarki Sahibul
Hairi ya taka muhimmiyar rawa, damin ya kashe
Dodannin sama da guda dari shida. Sauran kuma duka
Badakaren nan ya kashe su.
Bayan sun gama da dodannin sai suka ci gaba da tafiya
suna ta haduwa da mugwayan aljanu iri-iri da mugwayan
dabbobi suka yi ta fafatawa da su. Basu gushe ba a
wannan hali har sai da suka shafe kwana tara. Batun
abinci da ruwa basu sami matsala ba, domin guzurin bai
kare ba. Amma fa sun sha bakar wahala. Shi dai
Badakaren Sau daya wani aljani ya sami nasarar yankarsa
a kafada da farcen hannunsa. Amma shi sarki Sahibul
Hairi sai da ya kara samun raunuka bakwai a jikinsa. Akwi
lokacin da sarki Sahibul Hairi ya suma sau uku, sa'adda
suka fafata da wasu mugwayan bakaken aljanu masu
siffar jemagu masu yawan gaske masu karfin tsiya da
naci. In ba dan Badakaren ya bai wa sarki Sahibul Hairi
kariya ba da sai aljanun sun sami nasarar kashe shi. Sai
da aka kwana uku ana wannan gumurzu da bakaken
aljanun sannan Badakaren ya sami nasarar hallakar da su
gaba daya ta hanyar karanta wata addu'a wadda ta zamo
sanidiyar konewarsu da wuta kurmus.
A ranar kwana na tara ne suka iso wata katuwar fada
wadda babu komai a cikinta face tarkacen kayan tsafi iri-
iri, wadansu ma tun da sarki Sahibul Hairi yazo duniya bai
taba ganin su ba. Babban abinda yafi bawa sarki Sahibul
Hairi mamaki shi ne, kowacce irin dabba ta daji akwai
kwarangwal dinta a sakale a jikin bangwan fadar. Haka
kuma wace irin bishiya ta duniya akwaita a shuke a cikin
fadar. Baya da haka sai suka ga wasu manyan kwalabe
dirka-dirka guda dari. Kwalaban basu da kofa a jikinsu ta
inda za a zura a ciki, amma kuma da ruwa a cikinsu,
kuma ga yarinya Alfila a cikin kowacce kwalbar a kwance
kamar tana barci ko motsi bata yi.
Koda ganin wadannan kwalabe sai sarki Sahibul Hairi da
Badakaren suka shiga rudani na rashin fahimtar kowacce
ce Alfila ta gaskiya.
Sarki Sahibul Hairi ya tafi inda kwalaban suke. Da isarsa
sai ya daga takobinsa ya dinga saran kwalaban da nufin
ya farfasa su gaba daya ya fito da dukkanin Alfilolin.
Maimakon kwalaban su fashe sai takobin sarki Sahibul
Hairi ta dinga dakushewa kuma suk sa'adda ya sari
kwalben sai takobinsa ta dume da mugun zafi tamkar
zata narke, bisa dole ya hakuara ya daina saran kwalaban.
Ana cikin haka suka ji an bushe da irin mahaukaciyar
dariyar nan wacce aka yi musu tun a ranar farko da suka
iso kofar gidan. Ba zato ba tsammani sai suka ga wani
shirgegen aljani mai mutukar kwarjini da ban tsoro ya
bayyana a gabansu. Fuskar aljanin kamar ta dodannin
take, kuma ido daya gareshi manne a tsakiyar goshinsa, a
saman idon a kwai murtukeken gashin gira. Inda za a
yanko gashin girar a jiyeshi a kasa sai mutun yay kokari
zai iya daukarsa. Gangar jikin aljanin irin ta zaki ce cike da
zara-zaram gashi. Hannayansa irin na gwagwgwan buri
ne. Daga kugumsa zuwa kafafunsa kuwa irin na kada ne.
Jelarsa kuwa murtukekiya ce kuma doguwa mai tsananin
tsawo wadda takai kusan kamu ashirin. Gaba daya jikin
jelar cike yake da kahuhhuna masu tsini da kaifai. A
hannunsa na dama akwai dirkekiyar takobi, haka ma
fadinta. A hannunsa na hagu kuwa, wata katuwar
garkuwa ce wadda za a iya kife mutane hamsin da ita su ji
tamkar rumfa aka rufa musu. Aljanin ya dauri kugunsa
da wata irin damarar karfe ja.
Koda Badakaren ya kurawa jikin damarar idanu sai ya
cika da tsananin mamaki. Ba komai ne ya sashi mamaki
ba face ganin synayan ubangijin musulunci iri-iri a jiki da
kuma wadansu addu'oi kala-kala duk na ma'a bota
addinin musulinci.
Badakaren yace a cikin zuciyarsa.
"wannan fa shine kwaba. Tabbas wannan aljanin kafuri
ne, kuma mashiriki ma'abocin tsafi! Ta mene ne gaminsa
da wannan damara mai dauke da ayoyin Allah da
sunayansa tsarkaka?"
Kamar aljanin ya san abinda Badakaren yake ayyanawa a
zuciyarsa, sai ya dubeshi ya tuntsure da dariya ya ce.
"lale marhaba da jinin imam Sadik.
Koda jin wannan batua sai Badakaren ya sha jinin jikinsa.
Ya tabbatar da cewa aljanin ya san ko shi waye. Aljani ya
sakea bushewa da mahaukaciyar Dariya, sannan ya dubi
sarki Sahibul Hairai ya ce, "kaiconka ya kai wannan sarki!
Kasani cewa tun daga gida ake yaudararka har izuwa nan
fadata ni boka Shanzabul Azwas. Idan baka manta ba
bokanka ya gaya maka cewa idan harka mallaki gatarin
sihiri zaka iya balle kofar wannan gidan nawa ka shiga?
Amma sai gashi gatarin sihirin bai amfana maka komai
ba. Wannan Badakaren da kataho tarr da shi a matsayin
namiji, to ba namiji bane maca ce. Kuma ita ce babbar 'y
ga imam sadik, shugaban ma'abota addinin musulinci na
birnin Hairin Nur, sunanta jaruma Humairat. Idan har
abin da na fada ba gaskiya bane ta yaye rawaninta ka ga
fuskarta".
Koda jin wannan batu sai sarki Sahibul Hairi ya juya ya
dubi Badakaren. Nan take Badakaren ya cire rawanin
fuskarsa, yayi jifa dashi, sai ga dogon bakin ga shi wuluk
mai tsawo da sheki ya zubo kasa. Kyakkyawar fuska abar
kwatance ta baiyana. Sabo da tsananin mamaki da takaici
sarki Sahibul Hairi bai san sa'adda ya durkusa kasa ga
gwewoyinsa. Babban abin takaici shi ne, yanzu ashe duk
irin jarumtakarsa da juriyarsa ashe akwai macan da ta
fishi? Kuma akan wana dalili Imam Sadik zai yaudareshi
ya hadashi da 'yarsa mace a matsayin namiji, gashi tayi
abin al'ajabi da har abada ba zai iya ba.
Cikin fushi sarki Sahibul Hairi ya dubi jaruma Humairat
ya ce, "mai yasa ki ka yaudareni ke da mahaifinki kika
biyoni izuwa wannan gagarumin aiki a matsayin ke namiji
ce?"
Ya yin da Humairat taji wannan tambaya sai ta yi ajiyar
zuciya sannan ta ce da shi cikin wata zazzakar murya mai
dimautarwa, tamkar tana magana da sarewa.
"ya kai wannan sarki mai babban buri ka sani idan
banrakoka nan ba da babu yadda za ai ka shigo cikin gida
nan. Haka kuma idan kasan cewa ni 'ya maca ce ba zaka
yarda muyi wannan tafiya tare ba ka sani cewa na biyo ka
wannan tafiya ne domin na jaddada addinina a gareka ka
gamsu cewa shi ne addinin gaskiya, tun da gashi ka kasa
kare kanka daga cikin masifa da ke cikin gidan nan, sai ni
ce na kareka da taomakon Ubangijina, wannan abu da ya
faru ya isa yasa ka gamsu cewa babu wani abin baytawa
da gaskiya face Ubangijin musulinci"
.________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________ure guda daya wata
kyakykyawar budurwa wacca babu kamarta a duk fadin
junsin aljanu na duniya, ana kiranta da suna Harfiza.
Labarin Harfiza ya bazu a ko ina a duniya, kuma har yake-
yake anyi akanta, sarakunan aljanu da bokayansu babu
abin da basu yi ba akan su mallaketa amma sai gashi
boka shaharuz zaman ne ya zamo zakara a cikinsu, wato
shi ne kadai ya samu damar mallakarta. Yau shekara tara
ke nan da yin auran boka shaharuz zaman da Harfiza
amma har yanzu basu sami haihuwa ba. Shaharuz zaman
ya san cewa bazai taba samun haihuwa ba a duniya,
domin ya yi bincike a cikin tsafinsa, tsafin nasa ya
tabbatar masa da hakan, amma ya boyewa Harfiza
wannan sirri.
Wata rana Harfiza ta ziyarci wani mashahurin Boka a
sirrance ba tare da sanin sharuz zaman ba, sai ya sanar
da ita wannan sirri.
Koda taji hakan sai ta cika da tsananin bakin ciki ta fashe
da matsainai cin kuka ta tambayi wannan Boka ta ce,
"yanzu ya ya za ai na rabu da mijina Boka shaharuz
zaman, domin a halin yanzu na tsaneshi kamar yadda na
tsani mutuwata, sabo da bani da wani buri a duniya
wanda yafi na sami Haihuwa."
Ya yin sa Bokan ya ji wannan tambaya sai ya yi shiru ya
shiga bincike a hallarar tsafinsa. Jim kadan ya dago kai ya
kalleta ya ce, "kiyi hakuri akwai lokacin da zaku rabu,
amma idan kika bukaci rabuwa da shi a yanzu zai iya
hallakaki".
Daga wannan rana Harfiza ta rungumi kaddara, amma
kullum sai tayi kukan bakin ciki kuma bata taba bari
shaharuz zaman ya fahimci halin da take ciki ba.
Lokacin da jarumi Saif da aljani Hurbas suka iso sansanin
yaki suka dura a gaban dakarunsu sai suka iske ashe tuni
Boka shaharuz zaman ya hallara. Koda suka yi arba dashi
sai ya daka musu tsawa ya ce, "ya ku kananin halitta, kuyi
sani cewa yau kun hadu da zaki sarkin dawa, dan haka
daga yau an daina jin duriyarku a doraon kasa. Yanzu nan
zamu murkusheku yadda ko tokarku bazata moru ba"
.
KODA JIN HAKA SAI JARUMI SAIF YA MAIDA MASA DA
MARTANIN TSAWAR YA CE "kai tsohon annamimi, babban
makiyin Allah, ka sani cewa karyarka ta kare daga yau. A
yau ne zamu kawo karshan kafircinka da fasikancinka da
dukkan zaluncinka. Tabbas da kai da jama'arka dayansu
bazai koma gidansu ba, idan zamu shekara muna wannan
yaki duka babu gudu ba ja da baya har sai muga
karshanku".
Sa'adda jarumi Saif yazo nan a zancensa sai fuskar Boka
shaharuz zaman ta kama girgiza kamar za ta zazzago kasa
sabo da tsananin fishi, zuciyarsa kuwa ta kama tafarfasa
kamar zata kone. Nan take ya zare takobinsa ya yi nuni da
ita izuwa ga dandazon su jarumi Saif, wannan almace ta
umarni a afka musu. Ai kuwa nan take kowana 6angare
ya taso cikin matsainaicin gudu. Na kan dawakai na
sukuwa sukuwa aljanu na kada fuka-fukansu a sama suna
tsala gudu, domin a hade a tsakiya. Tun kan a hade ihun
mazaje ya cika dajin gaba daya, kura ta tshi ta turnuke a
sararin sama tamkar ana rairayar sahara. Kasa kuwa sai
ta kama girgiza saboda karfin sukuwar dawakai.
Ya yin da aka hade a tsakiya sai aka ruguntsume da
azababban yaki mai matukar tashin Hankali. Hakika bala'i
ba'asa masa rana, ita ko masifa idan ta tunkaro, to fa
babu abinda zai iya lafr da ita face ikon Allah.
Lokacin da aka fara wannan masifaffan yaki, sai ya
zamana cewa ido bai isa ya yanke hukunci ba, ya fadi
6angaren da yake samun nasara, duk da cewa 6angaran
su Boka Sharuz zaman sun nunka su jarumi Saif a yawa.
Duk 6angaren da mutun ya duba sai yaga ana yi musu
6arna domin mazaje ne suke zubewa kasa tamkar ana
karkadar busassun ganyayen bishiyoyi a daji. Sai da aka
kwana aka yini gumurzu sannan dukkanin maya kan suka
zama gawa, yarage saura mahaluki uku kawai kacal a filin
yakn, wato daga Boka Sharuz zaman sai Jarumi Saif da
Aljani Hurbas. A wannan lokaci duk su ukun sun gaji
ainun, sai haki suke kamarransu zai fita kuma sunyi
carko-carko suna kallon juna kamar zakaru.
Hurbas da Saif na tsaye daf da juna shi kuwa Boka
Shaharuz zaman na can gefe daya rike da manyan
makaman yaki. Tsawon 'yan dakiku suna kallon juna daga
can sai Boka Shaharuz zaman ya tuntsure da dariya
sannan ya nunasu da tsinin takobi ya ce, "karyarku ta sha
karya ya ku manyan abokan gaba. Tabbas yanzu zan zare
muku ruhin numfashinku, sannan na yanke kawunanku"
Koda jin haka sai jarumi Saif ya daka masa tsawa ya ce,
"kai tsohon jahili, kuma babban fasiki ka yi sani cewa
babu mai kashewa da rayawa face Ubangijin musulunci.
Tabbas kai baka isa ka kashemu ba. Ka sani cewa da izinin
Ubangijinmu karfin dantsanka da karfin sihirinka ba zai
sa ka sami nasara a kanmu ba, mune da nasara a kanka. A
yanzu kuma matarka ta zamo baiwarmu, sannan mu duk
kayan sihirinka yadda har abada baza a sake tunawa da
kai ba."
Boka Shahaz zaman ya bushe da dariyar mugunta ya ce,
"ai wannan furci naka da tatsuniy duk matsayinsu daya.
Ka sani cewa inda ba kasa nan ake gardamar yin kokawa.
Ga fili ga mai doki sai a kasa mu ga wanda zai ci riba ni da
ku".
Kafin Shaharuz zaman ya gama rufe bakinsa tuni jarumi
Saif da Hurbas sun afka masa da dukkan karfinsu shima
ya taresu aka fara fafatawa.
Koda fara wannan yaki sai Boka shaharuz zaman ya zame
musu alakakai suka kasa hallakashi ta farat daya. Domin
ne ma yake ya gagaresu duk da cewa suma syn kuntace
shi. Babu abinda ya dagawa shaharuz zaman hankali
kuma ya bashi mamaki face ganin yadda ko dan kadan ya
kasa yiwa jarumi Saif illa. Duk sa'adda ya sari jikinsa ko
kuma ya sare shi da makami sai yaji kamar dutsen wuta
ya kaiwa hari, domin makanin baya tasiri a jikinsa. Haka
kuma tsananin zafin nama Saif din ya hana ya hallaka
Hurbas amma duk da haka sai da ya shammaci Hurbas ya
dankara masa wawan naushi a wuya. Take Hurbas ya
sulale kasa sumamme ko motsin kirki bai kara yi ba. Ya
yin da jarumi Saif yaga abinda ya faru da abokinsa kuma
amininsa Hurbas, sai ya nutsu. Nan rake ya sake afkawa
shaharuz zaman kuma ya tattare dukkan karfinsa suka
rikice da sabon artabu. Sai da suka shafe sa'a tara suna
yaki amma ko sau daya babu wanda ya yiwa dan uwansa
lahani.
Al'amarin da ya fusata Boka Shaharuz zaman ke nan, ya
fara amfani da karfin sihiri. Duk masifar da ya watswa
Saif sai yaga taki kamashi. Bayan Shaharuz zaman ya
gama jarraba dukkanin sihirinsa na tsafi akan jarumi Saif
basuyi tasiri ba sai suka yarda makamansu suka fara 'yar
gwada kwanji. Ko shakka babu Boka shaharuz zaman ya fi
karfin Saif a zahiri, domin girmansu da kwarjinsu ma ba
daya bane. Za a iya kwatanta banbancinsu da dantsako da
muzuru. Amma bisa mamaki sai gashi jarumi Saif nata
ragargazar Boka Shaharuz zaman ya dinga jera masa
naushi da bugu hannu da kafa. Kafin ya kare wani dukan
ya karo masa wasu cikin matukar zafin nama. Nan da nan
ya hada masa jini da majina.
Kai! Tun Sharuz zaman na iya daga hannayansa har ya
kasa, kuma tun yana tsaye sai ya durkushe kasa bisa
gwiwoyinsa. Ba wani abu bane ya bawa jarumi Saif
wannan gagarumin karfi ba face taimakon wannan
damara da ke kugunsa.
Lokacin da jarumi Sai yaga ya yi laga-laga da Boka
Shaharuz zaman yadda ba zai iya ceton kansa ba sai yazo
kansa ya tsaya ya daga takobin sai ya dubeshi a lokacin da
jini ke ta zuba daga hancin Shaharuz zaman da bakinsa,
iadanunsa na gani dashi-dishi ya ce, "ya kai wannan
tsohon Boka, ka tuba ka kar6i addinin gaskiya, yanzu ni
kuwa sai na fasa hallaka ka
Koda jin wannan batu sai Boka Shaharuz zaman ya bushe
da dariyar kafirci. Cikin karfin hali ya bude baki ya ce,
"har abada kafiri na kwarai baya musulinta sabo da
tsoran mutuwa. Babban abin kunya ne a gareni ace a yau
kacini da yaki har na kar6i addininka. Ni kuwa da naji
kunyan duniya gara naji tacan lahira! Tur da kai! Tur da
addininka.....!!!
Kafin harshan Shaharuz zaman ya gama fadar wannan
furci tuna jarumi Saif ya yi kabbara ya cire masa kai. Nan
take kan ya yi tsalle sama ya fado kasa tum. Faruwar haka
ke da wuya sai Aljani Hurbas ya farfado. Koda yaga gawar
Boka Shaharuz zaman a gefe daya sai ya cika da tsananin
farin ciki, ya mike zumbur ya taho wajan Saif suka
rungume juna cikin tsananin farin ciki suna masu godiya
ga Allah".
Bayan sun nutsu sai suka dubi tulin gawarwakin 'yan uwa
musulmi da ke kwance a wajen wadanda suka yi
shahada. Saif ya ce, "kamata ya yi mu koma can cikin gari
nu debo jama'a domin su zo su tayamu binne
gawarwakin nan na shahidai".
Hurbas ya ce, "wannan gaskiya ne, to amma muna
guntun aiki wanda bamu karasa ba, kuma barinsa na iya
janyo mana babbar asara, domin tamkar mun kashe
maciji ne bamu sare kansa ba".
Koda jin wannan batu sao mamaki ya kama jarumi Saif
ya ce, "ya kai aminina me kake nufi da wannan batu? Ban
gane munufarka ba."
Hurbas ya ce, mun kashe Boka amma bamuje mun kama
matarsa ba, kuma bamu kone dukkanin kayan tsafinsa
ba, tabbas matarsa zata iya kawo mana harin sumame ".
Koda jin wannan batu sai Saif ya jinjina kai ya ce, "hakika
kayi gaskiya. Abinda za ai yamzu ni zan koma gari na taho
da jama'ar, kai kuma kaje ka kamo matar Shaharuz
zaman. Sannan ka bankawa gidan wuta ka tabbatar da
cewa komai ya kone ya zama toka". Sa'adda Husbas yaji
haka sai ya yi shiru kamar ya ce a'a amma sai ya dubo
Saif sai ya ce, "ya kai Abokina hakika nasan cewa zan iya
wannan aiki, amma masu iya magana sunce idan kana da
kyau ka kara da wanka, me zai hana kabani aran
damararka ta yaki a yau naje na wannan gagarumin aiki
domin kada nayi kuskure ko kuma na hadu da wani
tsautsayi".
Ya yin da Saif yaji haka sai ya yi murmushi ya dubi
Hurbsas cikin aminci ya ce, "ai ka san abinda zaka karanta
ka cire wannan damara daga jikina, don haka bisimillahi".
Nan take Hurbas ya biya wata addu'a a zuciyarsa, sannan
ya sa hannayansa biyu ya cire wannan damara ya san
yata a nasa kugun. Ko sallama bai yiwa Saif ba sai ya bude
fuka-fukansa yai sama ya nufi inda gidan Boka Sharuz
zaman yake.
Gidan Boka Shaharuz zaman an kawata shi ainun fiye da
tunanin mai tunani. Domin jama'a da yawa suna yiwa
gidan kirari da aljannar duniya. Sabo da babu abinda ba
bu a cikinsa na jin dadin duniya. Sai mai cikakken imani
ne zai shiga gidan ya kasa mancewa da Allah.
Lokacin da aljani Hurbas ya shiga cikin wannan gida yaga
irin daular da aka shirya a cikinsa sai ya dimauce ya shiga
zancen zuci a lokacin da yake ta shiga sako-sako na gidan
yana morewa idanunsa da kallo.
Ko ina a gidan fes-fes yake kamar kurra bata ta6a sauka
ba, kai ko a kasa mutun ya zuba ruwa a kasa ya sha,
domin duk inda kafa zata taka a shinfide yake da lu'u-
lu'u. Shuke-shule na kyawawan furanni masu kamshin
gaske gasunan burjik ba adadi. Tsuntsaye kuwa kyawawa
suma gasu nan har da irin wannan mutun bai ta6a gani
ba, kayan marmari kuwa da kayan abinci da abubuwan
shaye-shaye suma gasu nan barkatai na alfarma iri'iri,
duk bayan munti sittin sai su 6ace sai wasu su sabbi su
sake baiyana. Kai da gani kasan cewa aljanu ne ke ta
hidima a gidan.
Lokacin da Hurbas ya shiga 6angarab da turakar Boka
shaharuz zaman take, ya taka luntsumeman kilishin da
aka shinfida a ciki sai yaji tamkar ya lwanta ya kama
bacci. Haka dai ya daure ya wuce har izuwa cikin dakin
inda yayi arba da wani lafcecan gado na zinare mai
tsananin kyau da kawatuwa an kerashi da siffar tsuntsun
dawisu. Sai yaga wani kwnce akan gadon Harfiza ce tana
sanye da fararen tufafi mai shar-shara wanda ke bayyana
kyawawan surar jikinta da tsraicinta.
Koda aljani Hurbas ya yi arba da ita sai yakara
dimaucewa fiye da ko yaushe, ya manta da cewa zuwa ya
yi ya kama Harfiza kuma ya kone kyakkyawan gida.
Bisa mamaki sai yaga Harfiza ta mike zaune kuma ta kura
masa idanu tana yi masa murmushi mai dauke da
almomin tambaya. Cikin rawar jiki Hurbas ya karasa
gareta ya zauna daf da ita bisa gefab gado cikin Dari-dari.
Koda ganin haka Harfiza sai ta dubeshi ta ce, "haba
babban jarumi, tsoron me kake alhalin da ni da wannan
gida duk mun zama mallakinka? Kayi sani cewa duk abin
da ya furu tsakaninka da mijina a filin yaki na gani daga
nan a cikin madubin taafi, kuma nayi matukar farin ciki
da kuka kashe shi. Domin dama wannan ce ranar da na
dade ina jira.
Ka sani cewa a duniya babu abinda nake so sama da
haihuwa, sho kuwa Boka shaharuz zaman ba zai ta6a
Haihuwa ba, amma sai ya 6oye mini wannan sirri sai daga
baya na gano hakan bayan ya aureni. Bisa dole na ci gaba
da zama da shi domin in ya gane damuwata kasheni zai
yi. Yanzu bukatata dakai ita ce ka sadu dani domin in
zamo uwar danka".
Ya yin da Hurbas yajo wannan batu sai hankalinsa ya
dugunzuma, ya dubeta cikin tsananin damuwa ya bude
baki zai yi magana sai ta yi masa nuni da ya yi shiru,
sannan ta ce, ba sai kayi mini bayani ba, ai na san cewa
kayi alkawari ba zaka taba aurar jinsun aljanu ba. To ka
kwantar da hankalinka ni bana nufi ka aureni, sai dai ka
zamo abokin rayuwa na dan lokaci. Bayan ka biya mini
buakatata duk abinda ka ke so zan baka in dai akwai shi a
nan duniya. Amma ka sani cewa ba zamu sami nasara da
kwanciyar hankali ba face ka bijirewa abokinka Saif.
Yanzu sai ka ware wannan damara da ke kugunka ka
ajiyeta a gefe daya bayan mun gama shagalimmu sai ka
sanya damarar ka koma ga abokinka Saif ka hallakashi,
sannan ka dawo gareni mu ci gaba da more rayuwarmu.
Sa'adda Harfiza tazo nan a zancenta sai Hurbas yaji gaba
daya kaunarta ya mamaye zuciyarsa. Nan take ya cire
damarar nan daga kugunsa ya ajiyeta a kasan gadon ya
afka ma ta suka shiga lalata.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Al'amarin jarumi Saif kuwa, bayan sun rabu da Hurbas
sai ya hau dokinsa ya koma gida inda ya fara tattaro
jama'a domin aje sansanin yaki a yiwa mtune sutura.
Lokacin da matarsa ta dubeshi taga babu damararsa a
kugunsa sai da tsananin tsoro ta ce, "ya kai mijina, ina
kuma ka baro damararka a yau? Alhali tunda na aureka
ban ta6a gani ka cireta ba".
Koda jin wannan batu sai Saif ya bata labarin duk abinda
ya faru tsakaninsa da abokinsa Hurbas. Ya yin da taji haka
sai idanunta suka ciko da kwalla ta ce, "ya kai mijina
hakika kayi babban kuskure da ka da ka aiyana a ranka
cewa abokinka Hurbas ba zai ci amanarka ba. Ka san
cewa da yawan aljanu basu da amana kamar yadda shida
kansa ya ta6a baka labarin yadda mahaifiyarsa ta ci
amanar magaifinsa ta zamo sanadin ajalinsa. Iana
tabbatar maka da cewa ina ji ajikina sai Hurbas ya ci
amanarka. Ni kam abinda naso shi ne kada kowa ya ta6a
wannan damara bayan kai face danmu Sadik. Ko shakka
bana yi mun rabu da wannan damara kea nan har abada.
Koda fadin haka sai ta fashe da matsanaicin kuka. Shi
kuwa Saif ta shiga rarrashinta yana

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment