Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iska
mai karfi da sanyi ke kadawa koda haluf yaji sanyi yayi
masa yawa sai yahada wuta a bakin tantin ya zauna yana
jin dumi jim kadan da faruwar haka sai shima ya fara
gyan gyadi yana jin wannan hali ne wadannan gabza
gabzan mutane suka fara ketowa ta cikin duhun dare
daga cikin bishiyoyi suka durfafo wannan tanti nasu sarki
sahibul hairi sudai wadannan mutane sun kasance karti
majiya karfi adadinsu yakai dubu dukkaninsu sanye suke
da walkin fata kuma damatsansu cike suke da gurayen
tsafi kowannensu na dauke da muggan makaman yaki
kuma ya murtuke fuska dajan shuni kai wannan mutane
dai matukar kwarjini da ban tsoro suke dan ko a mafarki
mutun ya gansu sau daya har abada ba zai daina tunawa
dasuba
.
NIMA KAINA SAIDA NAYI MAFARKINSU
Cikin sanda mutanen suka iso daf da bawa haluf wanda
ke ta sharar barci bai san abindake faruwa ba da zuwansu
sai babbansu ya dubi mutum uku yayi musu inkiya dasu
duba cikin tantin nan take kuwa mutum ukun suka shiga
cikin tantin sai gashi sun fito dauke da sarki sahibul hairi
a kan shimfidarsa yanata shara barci shima baima san
cewa an fito dashi ba daga cikin tantin
Al amarin da ya baiwa shugaban mutanen dariya kenan
ya takarkare ya saki mahaukaciyar dariya mai kama da
kukan jaki karfin dariyar ne ya farkar da sarki sahibul
hairi da bawa haluf daga barci koda haluf yayi arba da
wadannan karti ababan tsoro saiya firgice ya yunkura da
nufin ya ruga da gudu shubana kartin ya dakawa bawa
haluf tsawa yace tsaya nan inda kake ko yanzun nan
takobina ta sha jininka Jin wannan batune yasa haluf ya
dada rudewa ya fadi kasa yana makyarkyata bai san sa
adda ya saki fitsari a wando ba
shi kuwa sarki sahibul hairi koda ya farka ya bude
idanunsa yaga wadannan zakwakuran karti saiya kare
musu kallo ya kwanta yana mai lumshe idanu da nufin
yaci gaba da barcinsa tamkar baisan da tsayuwar kartin
ba al amarin da ya bawa shugaban kartin mamaki kenan
kuma ya fusatashi kawai ya sake dokawa sarki sahibul
hairi tsawa kai waye har da zaka bude idanu ka ganmu
amma baka tsorata ba?
Na rantse da darajar wannan sana a tamu ta fashi yau
shekara ashirin kenan muna wannan aiki ama bamu taba
haduwa da wani mahaluki ba face ya razana da ganinmu
kai kuwa gashi harma kwanciya kake a gabanmu da nufin
yin barci, Sa adda sarki sahibul hairi yaji wannan batu sai
ya mike zaune ya fuskanci shugaban yan fashin yace yaku
wadannan kartin banza masu sana ar banza kuyi sani

cewa baza kusan komu suwaye ba face kunci gaba da
hanamu yin barcinmu koda gama fadinhaka sai sarki ya
koma ya kwanta ya sake lumshe idanu cikin tsananin
fushi da kuma zafin nama shugaban kartin ya zare wata
lafceciyar takobi ya kaiwa sarki sara a ciki da nufin ya
tsinkashi gida biyu
kafin takobin ta dira a jikin sarki sahubul hairi tuni ya
goce yai tsalle can gefe daya tamkar an janyeshi da
majaujawa gaba daya kartin saida sukayi mamakin
wannan zafin nama da jarumtaka tashi
hm kunji manyan sadaukan duniya sarki SAHIBUL HAIRI
.Shugaban yan fashin ya sake rugawa da gudu kan sarki
sahibul hairi da nufin ya sake kai masa sara shikuwa sai
ya daka tsalle sama ya doki kirjinsa da kafa guda karfin
dukanne yasa shugaban kartin yai sama ya fado kasa ya
baje kamar an shanya tsumma
koda ganin haka saigaba dayan dakarun nan suka zare
maka mansu sukayi kan sarki sahibul hairi babu wanda
ya kula da batun bawa Haluf wanda ya bude baki yana
kallon abinda ke faruwa cikin tsananin mamaki
nanfa karti da sarki sahibul hairi suka kacame da
azababben yaki suna kai masa sara da suka yana gocewa
amma duk wanda ya nausa saikaga ya zube kasa
sumamme
wani lokacin kuma in ya kama hannun mutum ko kafarsa
sai dai kaji ya karya basss! Tamkar ya karya silin kara
babu abinda zai baiwa mutum mamaki face tsananin
zafin naman sarki sahibul hairi da iya kauciya da zilliya sai
da aka shafe kusan rabin sa a yana turmutsa yan fashin
nan amma baiyi tunanin zare makami ba da makaman
nasu suka dinga sarar junansu saida yacewa gaba
dayansu su dubu sun zube kasa daga matattu sai
sumammu sai karyayyu shi kuwa shugaban yan fashin
nan kirjinsa ya karye bai iya motsawa ba bare ya samu
ikon tashi sa adda bawa haluf yaga irin wannan tsabar
sadaukantaka ta mai gidansa sarki saiya cika da mamaki
dukda cewa yasha jin labari a birnin misra cewa indai aka
fita filin yaki sarki bai taba kasa samun galaba ba akan
abokan gaba
Ance idan ya fusata ma yana shafe sa a bakwai yana yaki
bai gajiba kuma a duk rayuwarsa baitaba gudu ba ko
juyawa abokan gaba baya yayinda sarki sahibul hairi ya
gama da dukkanin yan fashin saiya dauki shimfidarsa ya
koma cikin tantinsa yayi kwanciyarsa nan da nan barci ya
sake kwasheshi harda minshari tamkar baiyi wahalar
komai ba
shikuwa bawa haluf sai idanunsa suka kekashe saboda
ganin wannan masifa har gari ya waye bai sake rintsawa
ba wannan shine abinda ya faru ga sarki sahibul hairi da
bawa haluf bayan sun baro birnin misra da nufin zuwa
birnin Askandariyya don dakko gatarin sihiri
++

A cAN birnin misra kuwa tun sa adda sarki sahibul hairi
ya sallami fadawansa akan cewa ya barwa Galadima
Aminul has rikon kasa sai gaba dayansu suka taru a gidan
waziri Akiyanu da tsakar dare suka shiga tattaunawa ta
sirri kan yadda zasu bullowa wannan lamari Waziri
akiyanu ne ya fara mikewa tsaye yace yaku yan majalisar
birnin misra kun sani cewa talauci ya zauta sarkinmu har
ya bazama cikin duniya neman arziki labari ya isar mana
cewa duk duniya babu matsafi kamar boka shamzul
azwas kuma babu wani mahaluki daya taba shiga cikin
wannan fada tasa wadda ke can tsuburin bahar zallas
amma haukan sarkinmu da tunaninsa na shirme ya
yanke hukuncin zuwa can don dauko yarinya Alfila
ko shakka babu Ajalin sarki yazo dole ne ya hallaka a
kokarin shiga gidan boka shamzubul azwas kaibama shiga
fadar boka shamzubul azwas ba ai zuwa fadar sarki
Barusa na birnin Askandariyya ma tafi karfinsa bare har
ya shiga ya dauko gatarin sihirinsu duk abinda sarki ke
takama dashi walau jarumta ko tsafi dakarun sarki
barusa sun ninkashi sau goma lallai idan ya shiga wannan
fada saiya zama gawa
wannan bayani da nayi muku yaisa ku tabbatar da cewa
sarki ya tafi kenan har abada ba zai dawo ba a raye saidai
gawarsa tazo yanzu gashi munaji muna gani ya bayar da
karagarsa ga Aminul has mutumin da gaba dayanmu
mun fishi cancanta da karagar mulkin yanzu wacce
shawara kuke da ita bisa wannan lamari?
Sa adda waziri akiyanu yazo nan a zancensa sai gaba daya
yan majalisar su bakwai sukayi shiru aka rasa wanda
zaice wani abu daga can sai wani dattijo waishi KILZAM ya
gyara murya yace juyin mulki na farat daya a cikin
wannan dare ! Ina nufin musa aje gidansa a kashe shi
kuma a hallaka iyalansa gaba daya inyaso gobe da safe
saimu nada ka sarki mu kuma ka raba mana mukamai
waziri Akiyanu ya jinjina kai yace kaima kazo da shawara
mai kyau amma kuma akwai matsala matsalar kuwa itace
gaba dayan jama ar gari sun san cewa sarki ya bawa
Aminul has rikon gari idan aka wayi gari akaga an kashe
shi kuma har na hau mulki nan da nan za ayi zargin cewa
ninaje nasa aka kashe shi lallai ba zamuyi gaggawar
hallaka shiba dolene mu tsaya muyi tunani da hangen
nesa don kada jama a suyi mana tawaye
yanzu mu bari ya fara mulkin muga iya gudun ruwansa
lallai nayi muku alkawarin cewa saina dawo mana da
mulkin kama karya irin wanda muka saba dashi Ada kafin
hawan sarki sahibul hairi' koda jin wannan batu sai farin
ciki ya kama gaba dayan yan majalisar suka aminta da
wannan shawara ta waziri Akiyanu sannan taro ya watse
kowa ya tafi izuwa gidansa a sirrance
++
Al amarin magajin karagar mulki kuwa wato Aminul has
tun sa adda sarki ya sallameshi a matsayin ya bashi rikon

kasa sai ya tafi izuwa gidansa yana mai matukar farin ciki
mara misaltuwa
koda dawowarsa gida sai ya iske matarsa SHULAIBA tsaye
a harabar gidan tana wasa da wadansu tsuntsaye dake
cikin keji
tsuntsayen sun kasance yan kanana ababan sha awa
masu launin ruwan Kwai
Tsuntsayen sun kasance yan kanana ababan sha awa
masu launin ruwan kwai sulaiba ta kasance kyakkyawar
mace mai karancin shekaru domin bata haura ashirin ba
tun tana da shekara tara ta auri Aminul has har yanzu
bata taba samun haihuwa ba
koda shigowar aminul has cikin harabar gidan ya hango
shulaiba a cikin nishadi saiyaji ya kara cika da farin ciki ka
tsaye suka nufi juna kowannensa na murmushi ta
tarbeshi cikin murna tana mai cewa yakai mijina yau
kuma wanne farin cikineya samemu naga ka shigo da
walwala ba kamar yadda ka saba ba kullum
sa adda aminul has yaji wannan tambaya sai yakama
hannayen shulaiba ya rike sannan yace ya abar kaunata
kiyi sani cewa daga yau na zama sarkin birnin misra''
koda jin wannan batu sai shulaiba ta dago idonta a firgice
ta soma ja da baya fuskarta cike da alamomin tsoro da
fargaba ba zato ba tsammani sai idonta suka ciko da
kwallah suka fara zubar da hawaye al amarin da yayi
matukar tayarda hankalin Aminul has ke nan ya matso
daf da ita ya sake rike hannayenta yace yake matata ina
dalilin zubar wannan hawaye naki
shulaiba tayi ajiyar zuciya tace yakai mijina hakika kayi
ganganci kuma kayi babban kuskure harda ka bari ka
karbi rikon kasar nan a hannun sarki domin kuwa yanzu
ne zaka tara makiya masu yawan gaske yanzu ne
rayuwanmu zata zamo a cikin mugun hadari domin
farautarta za a shiga yi ka san irin mulkin da sarki yake yi
a kasar nan mulkine wanda talakawa ke so amma kuma
su sarakai basa so, ina tabbatar maka da cewa wannan
tafiya da sarki yayi damace babba ga sarakunan kasar
nan wacce suka samu donsu dawo da mulkin zalunci da
murdiya
na sani cewa kai baka da irin ra ayinsu , ra ayinka irin na
sarki sahibul hairi ne lallai duk yadda zasuyi suga bayanka
sai sunyi ina mai shawartarka daka hakura da wannan
matsayi ka mika musu abinsu yayinda shulaiba tazo nan a
zancenta sai hankalin aminul has ya dugunzuma ya rasa
abindake masa dadi a duniya domin tabbas ya san cewa
duk abinda ta fada gaskiya ne
aminul has ya sunkuyar da kansa kas yana mai tunani
zuwa dan lokaci daga can kuma saiya dagao ya dubeta a
lokacin shima idanunsa suka ciko da kwalla yace yake
abar begena dare da rana ina sonki tuna cewa yau
shekara goma sha daya kenan dayin auranmu amma har

yanzu bamu sami magaji ba ki tuna cewa akan wannan
matsala muka je wajan boka Hadimul Asur yayi mana
bincike inda ya sanar damu akan cewa bazamu taba
samun haihuwa ba face mun kwanta akan gadon
sarautar kasar nan sau sittin yau ga dama ta samu donme
zakice mu barta? Nikam na yarda na hakura da wannan
mulkin amma bayan cikar kwanaki sittin akan gadon
sarautar
sa adsa aminul hass yazo nan a zancensa sai hankalin
shulaiba ya kara dugunzuma fiye da koyaushe ta fashe da
kuka tana me cewa hakika azzaluman kasar nan bazasu
bari muyi kwana sittin ba a cikin gidan sarautar kasar nan
face sun rabamu da rayuwarmu cikin tsananin tausayi
aminul has yasa hannu ya gogewa shulaiba hawayanta
yace ki kwantar da hankalinki abar kaunata ki tuna cewa
daga yau gaba dayan dakarun sarki sahibul hairi masu
tsaron lafiyarsa sun dawo karkashina ina nufin zasuci
gaba da tsaron lafiyata kamar yadda suke tsaron tasa
kinga kuwa ashe babu abinda ya isa ya taba lafiyata
kodajin wannan batu sai shulaiba tayi yake tace haba
mijina ashe ka manta da karin maganar da akace
'makashinka na jikinka' ina tabbatar maka da cewa da
dangari akanci gari su dakarun da kake takama dasu
aidasune za a hada kai aci amanarka
yayinda aminul has yaji haka sai yayi shiruyana tunani
domin ko shakka babu haka abin yake bayan dan gajeran
tunani sai ya sake duban shulaiba yace ki tuna cewa
mahaifinki shine mutuminda yafi kowa hikima da hangen
nesa a cikin birnin misra kafin rasuwar mahaifinki saida
ya zamana cewa babu abinda za a zartar face an nemi
shawararsa kuma bai taba bayar da gurguwar shawara ba
hatta yake yaken da ake fita ance shine yake sanar da
sarki hanyoyinda ake bi a samu nasara cikin gaggawa
A tarihin kasar nan babu wanda yafi mahaifinki sanin
sirrin mutanen kasar da sirrin gidan sarauta yake matata
nikam na sani cewa babu yadda za ayi barewa tayi gudu
danta yayi rarrafe yanzu wacce shawara zaki bani wacce
zata kaimu ga iya kare kanmu daga sharrin makiya har
izuwa lokacinda sarki zai dawo daga wannan tafiya na
damka masa amanarsa?
Lokacinda aminul has ya tuno mata da mahaifinta
mutuminda ake kira ABU HAKIM nan take tashiga tunani
mai zurfi abu hakin ya kasance shahararren mutum ko
ina a cikin birnin misra ya kasance mutum mai hangen
nesa kakkaifar kwakwalwa tarin ilimi da basira
saida abu hakim ya shekara sittin a duniya sannan ajali ya
riskeshi abu hakim nada tsatstsauran ra ayin rayuwa fiye
da sarki domin har ya rasu bai mallaki dukiyarda ta kai
darajar dinare goma ba suturarsa guda biyuce kacan sai
takalminsa na fada guda daya sai kuma wata sandarsa
wacce duk inda ka ganshi yana tare da ita yana dogara
duk da kasancewarsa ba tsoho baDuk da kasancewarsa ba tsohoba jama a sun dade suna

mamakin dalilin da yasa yake dogara sanda a duk sa adda
yake tafiya alhali bai tsufa ba har Abu hakim ya rasu babu
wanda yasan dalilin da yasa yake amfani da wannan
sandan Lokacinda cutar Ajali ta kama abu hakim a
wannan lokaci tuni matarsa ta dade da rasuwa kuma ta
bar masa ya guda daya wato shulaiba
saboda aminci da kaunar dake tsakanin sarki sahibul hairi
da abu hakim saiyasa aka kawo shi cikin gidan sarauta ya
zamana cewa shi da kansa yake jinyarsa sannan kuma
yasa aka dinga kula da shulaiba tamkar yar cikinsa bayan
kamar wata hudu da faruwar haka sai ciow ya kara
tsanani wani yammaci sarki sahibul hairi da shulaiba na
zaune a gaban abu hakim sun zuba masa ido suna kwalla
sbd ganin halinda yake ciki
sai abu hakim ya dubi sarki sahibul hairi yayi murmushi
sannan ya dubi shulaiba ya fashe da kuka koda ganin
haka sai hankalin sarki sahibul hairi ya dugunzuma yace
yakai aminin mahaifina shin zaka iya gaya min dalilin da
yasa ka dubeni kayi murmushi amma da ka dubi shulaiba
saika fashe da kuka sa adda abu hakim yaji wannan
tambaya saiya gyada kai yana mai alamun cewa zai iya
amsa tambayar cikin karfin hali ya bude baki yace
yakai wannan sarki mai adalci zanso ka tashi kafaduna ka
jingina bayana a wannan gado da nake kwance domin
naji dadin sanardakai abinda zai amfani rayuwarka data
yata nan gaba
koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya mike da sauri ya
kama kafadun abu hakim ya tashe shi zaune ya jingina
bayansa a jikin marikin gadon koda gama hakan sai abu
hakim ya kira sunan shulaiba yace taho gareni yake yata
shulaiba ta fada kan kirjinsa ya rungumeta a lokacinda
duk su biyun suka fashe da kuka al amarinda ya sa sarki
cikin tsananin tausayinsu kenan shima bai san sa adda ya
fara kuka ba
jim kadan sai abu hakim ya dubi shulaiba yace yake yata
kiyi hakuri domin ciwonnan nawa bana tashi bane amma
ki sani cewa ko a bayan raina baki da wani gata
koda jin wannan batu sai mamaki ya kama sarki sahibul
hairi yace haba yakai wannan aminin abbana saboda me
kake irin wannan furuci alhali ina raye a matsayin sarkin
misra
Abu hakim ya dago kai ya dubi sarki sahibul hairi a
lokacinda hawaye ya subuto masa yace yakai dan
aminina ina mai bakin cikin sanar dakai cewa nan gaba
awasu shekaru masu zuwa saikashiga cikin wani irin
mummunan hali na rashi harta kai cewa ba zaka iya
daukar nauyin kanka ba bare ka dauki nauyin wani dukda
cewa kana matsayin sarki
A wannan lokaci jama a zasu gujeka musamman
fadawanka abokanka sauran sarakai zasu kyamaceka su
dinga yi maka ba a da isgilanci ka kasance mai hakuri a
duk matsayin da ka tsinci kanka kuma ka jajirce wajen

neman mafita amanar da zan bar maka itace ga yata
shulaiba lallai ka aurar da ita ga mafi soyuwa a ranka
daga cikin fadawanka wanda ka tabbatar da cewa yana
kaunarka dari bisa dari kuma lallai kada ka aurar da ita a
lokacin da ta haura shekara tara a duniya ina nufin ka
aurar da ita nan da shekara biyu.
Sa adda abu hakim yazo nan a zancensa sai sarki ya cika
da tsananin mamaki yace haba ya aminin abbana saboda
me kace zanyi talauci alhalin ina da matsayin sarkin misra
kuma taya za ayi kace na aurar da yarka a lokacinda take
shekara tara alhalin ba a taba yin haka ba a garinnan?
Abu hakim ya dubi sarki sahibul hairi yace shin ka yarda
cewa kafin rasuwar mahaifinka bashi da abokin shawara
wanda ya fini sarki yace gaskiya ne
Abu hakim yace shin na taba baka shawara wacce ka bita
kaga ba dai dai ba sarki yace A'a to abind anake so ka
gane shine abinda na sani har abada ba zaka saniba face
na sanar dakai abinda zan hango har abada ba zaka iya
hangoshi ba
abinda nake so aidakai shine ka kiyaye da duk
abubuwanda na fada maka a baya kuma kayi aiki dasu
idan kana so ka cimma nasara a rayuwarka
lokacin da abu hakim yazo nan a zancensa sai ya janye
shulaiba daga kan kirjinsa ya dubeta yace yake yata ki
sani cewa nitalaka ne babu abinda zan bar miki na daga
dukiya amma zan bar miki wadansu abubuwa guda biyu
wadanda indai kina tare dasu har abada keda mijinki ba
zakuyi talauci ba kuma babu wani tsautsayi da zai hau
kanku
wadannan abubuwa biyu ba komai bane face sandata da
kuma takalmina nan take Abu hakim ya dauko takalminsa
a karkashin gadonda yake kwance gami da sandarsa ya
mikawa shulaiba ta karba sannan yace ki boye wadannan
abubuwa biyu da kyau har zuwa ranar da kikaga mijinki
ya sami babban matsayi a kasar nan to a sannan ne zaki
dauki wannan sanda da takalmin ki bashi kuma ki
umarceshi da yayi amfani dasu ko yaushe dare da rana
koda kuwa yana kwance ne a kan gadonsa
ina nufin kada ya kuskura yacire wannan takalmin daga
kafarsa face zai shiga kewaye ita kuwa wannan sanda ko
barci zaiyi ya ajiyeta a daf dashi lokacinda shulaiba tazo
dai dai nan a tunaninta Sai aminul has ya girgiza
kafadunta yace Wai shin wanne irin tunani kike yi ne
haka??
009. SARKIN SARAKAI BOOK1
<
.
Aminul has ya girgizata yace tunanin me kikeyine haka
kamar wacce ta farka daga bacci haka ta zabura koda
tadawo cikin hayyacinta saita dubi Aminul has tace ka
jirani Anan karka matsa ko ina zan shiga daki na fito
nan take shulaiba ta juya ta nufi cikin dakinta shi kuwa sai

yabita da kallo kawai jim kadan saiga shulaiba ta dawo
rike da shohuwar takalmi a hannunta koda ta iso gaban
Aminul has saita tsaya suka kurawa juna ido yana mai
mamakin ganin tada wadannan tsofaffin abubuwa biyu
shulaiba tayi murmushi mai taushi a gareshi tace yakai
mijina shin kayi imani da kaunar da nake maka cewa ta
cika dari bisa dari?
Aminul has yace babu kokwanto ga hakan shulaiba tace
idan har kayi imani da hakan toka rike wannan takalmi da
wannan sanda daga yau ka kasance a tare dasu dare da
rana ya zamana cewa babu abindake rabaka dasu hatta
kwanciya bacci face idan zaka shiga kewaye tabbas
idanka kiyaye da haka babu tsautsayin da zai sameka
kodajin wannan batu sai aminul has ya kurawa wannan
sanda da takalmi idanu kawai ya karbesu ya rungumesu a
kirjinsa yana mai cewa hakika na gamsu cewa wadannan
abubuwa biyu sun fito daga hannun wanda ba za a taba
mantawa dashiba lallai zaki sameni mai kiyayewa da
umarninki.
Nan take aminul has ya cire takalmin dake kafarsa ya
saka wannan tsofaffi sannan ya dogara wannan sanda ya
nufi cikin turakarsa yana mai waigen shulaiba suna yiwa
juna murmushi.
Wannan shine abinda ya faru tsakanin aminul has da
matarsa shulaiba bayan ya karbi rikon kasar misra daga
hannun sarki sahibul hairi
++
Al'amarin sarki sahibul hairi da bawa haluf kuwa tun da
sarki ya kama barci a cikin tantinsa bai farka ba saida gari
ya waye har rana ta iske koda budewar idanunsa sai yaji
rurin gagarumar wuta a wajen tantinsa cikin sauri ya
mike tsaye ya fita waje da hanzari yana mai zare
takobinsa don tsammanin ko wadansu yan fashi ne suka
kawo sumame da fitowarsa saiyaga ashe bawa haluf ne
ya tara gawarwakin yan fashin da ya kashe jiya a waje
daya ya kunna musu wuta, sarki sahibul hairi yayi
murmushi sannan ya yafito bawa haluf da hannu cikin
hanzari haluf ya rugo gareshi suka koma cikin tantin tare
da shigarsa sai haluf yaga ashe har sarki ya fiddo abincin
kalaci ya shirya shi bisa faranti.
Sarki ya dubi haluf yace ina son muyi sauri mu gama
kalaci domin muci gaba da tafiya ka san cewa a kalla nan
gaba sai mun kwana talatin da bakwai kafin mu isa birnin
Askandariyya ba tare da gardamar komai ba bawa haluf
yabi umarni suka zauna tare suna masu fuskantar juna
suna cikin cin abincin ne sarki sahibul hairi ya lura
idanun bawa haluf yaga sunyi jawur kawai sai yayi
murmushi yace yakai haluf kai kuwa menene ya hanaka
yin barci jiya da daddare?.
Koda jin wannan tambaya sai haluf yayi ajiyar zuciya
yace ya shugabana hakika jiya naga bala'in da bantaba
gani ba kuma naga jarumtaka a wajenka wacce inda

zanje na bayar da labarinta baza a gasgata ni ba hakika ka
cika sadauki uban sadaukai ka sani cewa ko a yanzu idan
na runtse idanuna sai nayi ta ganin yadda ka dinga karya
barayin jiya kana sawa suna sare kawunansu da soke
juna.
Yayinda sarki sahibul hairi yaji wannan batu saiya bushe
da dariya yace yakai haluf hakika inda kana nan a lokacin
da nayi wani yaki da mutanen birnin Rum da wata kila
kwakwalwarka ta birkice ka sami tabin hankali A
rayuwata ban taba yin yakin da na sha bakar wahala ba
kamarsa domin saida na kwana na yini ina yaki ba tare da
na sami damar hutawa ba daidai da dakika daya a
wannan yakine na shiga tsakiyar abokan gaba mutum
dubu dari uku ni kadai suka yanyameni suna kawo mini
sara da suka nima ina maida martani A tsawon kwana da
yinin ne nayi musu mummunar barna na kashe mutum
dubu dari da talatin
A wannan yaki gaba dayan dakaruna mutum dubu dari
biyu da hamsin saida aka kashe su ni kadaine na rage
Lokacinda abokan gaba sukaga inatayi musu barna
amma sun kasa cimmani sai suka kara kaimi suna
kokarin hallakani ta kowanne hali amma saina zame
musu alakakai kaini kaina a wannan yaki saida na
tausayawa abokan gaban saboda irin kisan gillar da nake
musu.
Wani lokacin idan na sari mutum saidai kaga gangar
jikinta tsage gida biyu bari da bari duk inda nasa gaba sai
daikaga sassan jikin bil'adama suna yawo a sararin sama
gaba dayan jikina saida ya rine da jini ba a ganin komai
sai idanuna tamkar anyi mini wanka a kogin jini babu
abinda zai baka tausayi face ganin yawan gawarwakin a
zube tuli a filin yakin tamkar yabanya a gona
lokacin da muka kwana muka yini muna wannan yakin ya
zamana cewa na kasa karar da abokan gaba sukuma sun
kasa cimmani sai gajiya ta fara riskata a sannanne fa
abokan gaba suka fara samun lagona har aka yi min sara
uku a gadon bayana
kuma aka sokeni a kwibin hagu na cikina nan fa jini ya
fara zuba a jikina koda naga zan hallaka saina kwarara
uban ihu wanda ya firgita gaba dayan abokan gabar suka
jada baya suka tarwatse koda naga hanya ta samu saina
ruga da gudu ina gudun ina saransu kafin abokan gaba su
ankara nayi nisa
.
Ai kuwa sai suka biyoni cikin matsanancin gudu amma na
gaba yai gaba na baya sai labari lokacin da nake wannan
gudu ina yinsane cikin takaici domin a rayuwata ban taba
guduwa ba daga filin yaki yau gashi bala'i yakai har gudu
ya zamadole a gareni inba haka ba kuwa na rasa
rayuwata
shidai wannan yaki muna yinsa ne a wani daji wanda ake
kira BAHARUL SHARUL dajin na dauke da manyan

tsaunuka da manyan koguna inda ruwa ke bulbulowa
daga cikin duwatsu yana kwaranya yana gudu sa adda
abokan gaba suka tasoni a gaba na ga babu matsera
kawai saina durfafi wani katon tsauni wanda nidai a
rayuwata ban taba ganin tsauni mai tsawonsa ba ina
kyautata zaton cewa duk duniya babu tsauni mai fadi da
tsawonsa nan fa naci gaba da gudu suna biye dani har
muka isa can saman tsaunin muka kureshi koda na leqo
kasan tsaunin na ga zurfinsa sai zuciyata ta bugu abokan
gaba kuwa sai suka ja dinga a bayana suka fara kyakyata
dariya don sun tabbatar da cewa duk wanda ya fada
daaga saman wannan tsauni sunansa gawa.
Nanfa na tsaya ina tunani a raina nace hakika idan ajalina
ya tabbata a hannun abokan gaba an rusa mini
tunkahona da darajata a idanun duniya kawai saina sake
lekawa kasan tsaunin naga yadda ruwa ke kwarara kasa
sanna na yanke hukuncin na daka tsalle na sallamo kasa
ko dai na rayu ko na mutu kafin nayi hakan saina juya na
dubi abokan gaba nayi murmushi nace idan akwai da
namijin da ya isa a cikinku ya biyoni inda zan tafi'
kafin abokan gaba suyi wani yunkuri na daka tsalle na
sallamo izuwa kasan tsauni lokaci guda abokan gaba suka
rugo izuwa karshen tsaunin suka yi cirko cirko suna masu
lekowa kasa don suga irin mutuwar da zanyi saboda
nisan dake tsakanin saman tsaunin da kasansa sai da
dakika dari uku ta shude sannan na iso kasa cikin kogi
saura kiris kuwa kaina ya fado kan wani dutse amma sai
kafata ta bugi wani wuri a jikin tsaunin saina sauya wuri
na nutse izuwa can karkashin kogi.
A wannan lokaci na suma bansan halinda nake cikiba
kawai sai farkawa nayi na ganni a gabar kogi a can wani
daji daban koda na tsinci kaina a raye sai murna ta
kamani nan take na mike tsaye na tafi neman itatuwan da
zan sarrafa na yiwa raunikan jikina magani saida na shafe
kwana sittin ina tafiya a

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment