Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kece da dariyar mugunta, kawai sai ya
mike tsaye daga kan karagar mulkin yana mai sauya
kamanninsa izuwa ainihin siffar gimbiya shukura matar
sarki barusa
koda ganin haka sai humaira dasu sarki sahibul hairu
suka cika da tsananin mamaki, sahibul hairi yai ajiyar
zuciya yace, haba ni fa naji ajikina
sa adda na gaisa dake na kama hannunki, tabbas ba
hannun namiji na kama ba
hannun mace ne, ashe kece kika yaudaremu yaya aka yi
kika
rigamu zuwa wannan
gari harkika yi mana wannan mugun tanadi, kuma yanzu
ina alfila da mahaifinta ?
Koda jin wannan tambaya sai shukura ta bushe da
dariyar mugunta sannan tace ai a halin yanzu tuni
yarinya
alfila anyi tafiyar kwana arba in da ita a sararin samaniya
an tafi da ita can inda baku isa ku
jeba har abada
naso na sami damar hallakaku cikin ruwan sanyi ba tare
da kun ankara ba, amma sai wannan hatsabibiyar
humaira
ta gano dukkan makircina
to idan kun san wata baku san wata ba, lallai idan hagu
taki sai a koma dama
a yau dai, kuma a yanzu, banga ta yadda zaku iya tsira
ba daga sharrina ban ga wanda daga cikinku ya isa ya
hanani na zama sarkin
sarakunan duniya ba
tap ! Babbar Magana Jin wannan kalami yasa Nima AA
Misau na dakata a wannan gaba
kuma nake cewa Sai allah Ya kaimu gobe zan cigabBANGA WANDA DAGA CIKINKU YA ISA
YA HANANI NA
ZAMA
SARKIN SARAKUNAN DUNIYA BA, Sai nafi dukkanin
sarakunan duniya matsayi, mulki
da arziki, mutane da aljanu duk sai sun zamo a karkashin
ikona ya zamana cewa ina sarrafa duniyar nan gabaki
dayanta
akan tafin hannuna, batun awaisu da sarkin wannan gari
kuwa duk suna cikin mugun hali na tsakanin RAI DA
MUTUWA, sai hukuncin da na yanke

musu
idan naso su rayu , idan naso kuma su hallaka a cikin yan
dakiku zan kashesu
kafin gimbiya shukura ta rufe bakinta sai humaira ta daka
masa tsawa tace ke tsohuwar munafukar Allah,
algunguma, maci amanar mijinta
kiyi sani cewa ba ayi duniyar nan domin ku kadai ba
batattu ma abota shirka da izinin ubangijina ba zaki cika
wannan
mugun buri naki ba
cikin tsananin fushi shukura ta tari numfashin humaira
tace
aishikenan ga mai fili gamai doki, sainaga wanda ya isa ya
hanani ida abin dana soma, nan take shukura ta dakawa
wadannan samudawan dakaru nata tsawa tana mai
umartarsu dasu afkawa su humaira
ai kuwa sai dakarun suka zare makamansu
sukayi caa a kansu aka ruguntsume da azababben yaki a
tsakiyar fadar
shukura ta koma kan karagar mulki ta zauna tana mai
harde kafa cikin nishadi ta zuba ido kawai taga yadda
karshen
wannan yaki zai kasance
haka dai wuri ya gama yamutsewa karar karafa da cika
dodon kunne gami da ihun
mazaje, dakarun suka lullube su humaira suka
yanyamesu tamkar an ajiye kwayar hatsi guda daya a
tsakiyar miliyoyin tururuwa
duk inda humaira da sarki sahibul hairi suka durfafa
saidai
kaga suna tarwatsa dakarun suna ragargazarsu suna
zubewa kasa, amma abin haushi shine dakarun basa
mutuwa duk wana ya fadi kasa koda kuwa an daddatsa
shi yayi filla fill saikaga komai na jikinsa ya koma ya hade
tamkar ba a taba gididdibashi ba, sannan ya mike
zumbur ya
cigaba da fafatawa
al amarin da ya matukar dugunzuma hankalin su sarki
sahibul hairi kenan domin sun fahimci cewa wadannan
dakaru basa gajiya, kuma muddin aka sami tsawon lokaci
ana wannan fafatawa a haka tabbas zasu iya gajiya har
dakarun
su sami lagonsu
Al amarin bawa haluf kuwa tuni a wannan lokaci ya fara
gajiya in ba don ma humaira da
sarki sahibul hairi na kareshi ba da tuni dakarun sun
hallakashi
ana cikin wannan artabu ne wani daga cikin dakarun ya
sababa ta bayan bawa haluf ya dankara masa sara a
gadon baya da takobi nan take bayan nasa ya dare, jini
yai
tsartuwa haluf ya kurma uban ihu ya sulale kasa

sumamme
koda ganin abinda ya faru ga bawa haluf sai sarki sahibul
hairi ya fusata ainun yayi kururuwa mai firgita maza
wacce tasa dakarun suka jajja da baya a tsorace
cikin zafin nama sarki sahibul hairi ya sunkuyo kasa ya
dauki takobin bawa haluf ya hada guda biyu kenan a
hannunsa
ya sake rugawa kan dakarun yaci gaba da saransu tako
ina
AA Misau Ke magana gabas da yamma kudu da arewa
suna zubewa kasa tamkar yana ta adi a gonar kabewa
amma duk a banza domin ba sa mutuwa sai dai kaga
suna mikewa kamar a sannan aka haliccesu
koda aka sake samun gushewar lokaci sai dakarun suka
shammaci sahibul hairi suka yankeshi har a waje biyu a
lokaci guda
yanka na farko a tsakiyar kafarsa ta hagu, daya yankan
kuma akan cinyarsa ta dama, duk da
juriya irin ta sarki sahibul hairi sai da ya kwala ihu ya
durkusa kasa bisa guiwoyinsa, a lokacinne yaji wani irin
jiri ya debeshim idanunsa suka kama lumshewa suna
gani dishi dishi kwai sai ya tafi kasa luuu ! Zai kife Ba zato
ba tsammani sai yaji an rukoshi da hannu
Daya anyi cilli dashi izuwa can saman tudu kusa
da karagar mulki inda gimbiya shukura ke zaune
Ba wani ne yayi wannan bajinta ba face humaira,
cikin zafin nama humaira ta sake daukar bawa
haluf wanda ke kwance a kas sumamme tamkar
gawa shima ta cillashi inda ta cilla sahibul hairi
ya zamana cewa saura ita kadai a tsakiyar
wadannan dakaru
Kawai sai ta fara jaranta wata addu a ta
musamman kuma ta kutsa cikin tsakiyar
dakarun taci gaba da gididdibasu
Wannan karon kuwa sai labara ya sha
banban domin duk wanda ta sara ya fadi
kasa baua tashi sai dai kaga ya kama da
wuta ya ruburbushe ta zama toka
Koda gimbiya shukura ta hango abinda
ke faruwa ga dakarunta sai ta fusata
ainun ta mike zumbur daga kan karagar
da take zaune ta zare takobinta ta daka
tsalle daga inta take tamkar an janyeta
da majajjawa ta dira a inda bawa haluf
yake takaimasa suka da takobinta a
cikinsa da nufin ta maidashi gawa
Cikin matukar zafin nama sahibul hairi
ya daka tsalleya kai masa dauki da nufin
ya kade takobin shukura
Maimakon takobin tata ta soki bawa haluf
sai ta soki sahibul hairi a gefen kirjinsa
tabullo ta gadon bayansa

Sahibul hairi ya kwala ihu a karo na biyu ihu
mai karfin gaske wanda yasa humaira ta juyo
a dimauce ta kalli abin da ke faruwa kawai
sai tag a sa adda shukura ta zare takobinta
dafa cikin kirjin sahibul hairi sannan ta sake
daga takobin tata sama zata fille kan
sahibul hairi tamkar an harbor kibiya daga
cikin baka humaira ra dako wawan tsalle
sama ta baro cikin wadannan dakaru
Kafin takobin shukura ta kai wuyan sarki
sahibuk hairi tuni humaira ta doki kirjin
shukura da kafafunta biyu saboda karfin
dukan said a shukura tayi tsalle sama ta
gwaru da bango ta fado kasa a galabaice
jinni na yoyo a hancinta
Koda shukura ta shafa hancinta taga jinni
sai ta kwarara wani irin uban ihu tankar
saukar aradu
Take wata irin tsawa ta sauka akan wadannan
ragowar dakaru yaki na ta kawai sai duk
suka fadi kasa matattu dayansu bai tsira ba
Shukura ta mike tsaye a fusace ta tnkari
inda humaira take tsaye koda ta kusa zuwa
kusa da ita sai ta tsaya suka fara kallon kallo
irin wanda ke nuna KAR TA SAN KAR
a wannan lokaci sarki sahibuk hairi na
kwance a kas magashiyan yana nu,fashi sama
sama kai da gani ka san cewa abu ne mawuyaci
ya rayu domin har a sannan jinni ne ke
bulbulowa ta cikin gefen kirjinsa inda shukura
ta sokeshi da takobi
Da kyar da makyarkyatar hannu ya cisgi suturar
jikinsa ya dora akan raunin kirjin nasa ya danne
raunin don tsaida jinni AA Misau Ke Magana
Bayan anyi kallon kallo na yan dakiku tsakanin
humaira da shukura sai shukura ta bushe da
dariya sannan tace yake wannan jaruma mai
taurin rai a hatsabibanci kiyi sani cewayau kin
gamu da dai dai dake domin niba sarki Barusa
bane kuma ni ba shamzubul azwas bane
Yadda duk kike tsammani na na wuce nan yau
shekarata goma sha uku kenan ina tanadin wannan
rana ta haduwa da ke domin tun-tuni nayi
bincike a cikin tsafina na gano cewa ke kadai
ce zaki iya kawo mini matsala a cikin kokarin
cika burina na son zama SARKIN SARAKAN
DUNIYA. Hm AA Misau Ke Magana,
Ina tabbatar miki da cewa duk abin da kike
takama da shi baki fini ba idan karifin damtse
ne da jarumtaka kike takama da shi ai yanzu
zamu fitar da raini, idan kuwa takamarki ki nemi
taimakon ubangijin musulunci to ki sani cewa

baki fini sanin ubangijin musulunci ba
Ki sani cewa ni asalina na fito ne daga
zuri’ar sheik abul nasir na birnin misra,
mahaifiyata ce babbar ‘yarsa, don haka
an haifeni a cikin musulunci, kuma na girma
a cikinsa na sami karatu da ilimi mai yawa
a wajen kakana
Tun a wannan lokaci bani da burin da ya fi na
sami matsayi da daukaka irin wanda babu
wani mahaluki daya sameshi a duniya
A lokacin da kakana Abdul nasir ya rasu
ina da shekara goma sha hudu a duniya
kawai sai aka wayi gari aka nemeni aka
rasa domin sulalewa nayi na gudu na bar
birnin misra a cikin dare
Daga wannan rana ba a sake jin duriyata
ba sai na bazama a duniya na rinka farautar
abubuwa uku
Abu na farko shine, ilimin addinin musulunci
, duk da cewa na sami mai yawa a wajan
kakana, amma sai na ci gaba da neman kari
Abu na biyu sai na dinga ziyartar bokaye ina
yi musu bauta suna bani iliminsu
Abu na uku na dinga koyon fada da yaki
a wajan sarkin yaki na kasashe daban daban
Sai da na shekara shida ina wannan yawo a
duniya ina koyon abubuwa ukun har said a na
tabbatar da cewa na sami kowanne isashshe
kamar yadda ya kamata sannan na fara bincike
a hallarar tsafina akan yadda zan sami nasarar
cika babban burina na duniya
A cikin binciken nawa ne aka nuna mini cewa
bazan taba samun nasara ba face na fara
auaran daya daga cikin manyan sarakunan
duniya
Bisa wannan daliline naje birnin sarki barusa
na zamo daya daga cikin dakarunsa na yaki
har jarumtakata da kyawuna suka burgeshi ya
aureni
A wajan sane na sami labarin boka shamzubul
azwas da batun yarinya alfila a sannan ne na
gano cewa ashe iyakar amfaninsa kenan a
wajena wato na san mataki na karshe da zan
cika burina
Koda na sake yin bincike a tsafi sai aka nuna
mini zuwan sarki sahibul hairi domin ya dauki
gatarin sihiri na mijina sarki barusa
Koda ganin hakan saina cika da farin ciki domin
nasan cewa lokaci yayi d azan rabu da sarki
barusa na bi sarki sahibul hairi domin na
mallaki yariny alafila wacce a jikinta ne zan
sami sirrin tsafin da babu kamarsa a duniya

Abinda dukkan matsafan duniya basu gano
ba shine, yarinya alfila ta taba shan wani
tsumin tsafi na sarkin aljanu wanda ya yi
zamaninsa kimanin shekaru dubu dari biyu
da arba’in baya
Shi dai tsumin tsafin a hannun wata jikarsa
yake wacce wara rana ta fita yawon shan
iska sai ta shiga gonar wani azzalumin bakin
aljani ta tsinka amfanin cikinta, ashe yasa
guba a jikin duk amfanin gonar saboda
maganin masu yi masa sata
Ai kuwa sai wannan aljana ta kama aman
jinni da kyar ma ta bude fukafukabta tayi
sama ta bar cikin gonar ta fada daji tna
shure-shure AA Misau Ke Magana
A wannan lokaci tsumin tsafin na cikin wata
batta dake rayaye a wuyanta, amma saboda
dafin day a shigeta yaci karfinta sai ta kasa
cire battar tsumin daga wuyanta tasa a bakinta
tasha
Tana nan kwance a kas tana shure shuren
mutuwa sai ga mahaifiyar alfila tazo giftawa
ta wajan ta dawo daga daji samo itace
A wannan lokaci alfila bata fi shekara biyu
bad a haihuwa mahaifiyar na goye da ita a
bayanta kuma a sannan rana ta take matuka
duk su biyun suna jin kishirwa
Mahaifiyar alfila sauri take ta isa cikin agri domin
ta nemi ruwa ra shayar da kanta da yarta koda
mahaifiyar alfila taga wannan aljana a kwance
tana kakarin mutuwa sai ta firgita ainun ta
yunkura zata gudu cikin karfin hali aljanar
tace kada ki gujeni yake wannan bil’adama a
wannan lokaci da nake neman ceto
Na rokeki daki zoki cire battar dake wuyana ki
budeta ki tsiyaya mini rowan cikinta a bakina
Idan kika yi min haka nima zanyi miki sakayya
da abinda duk duniyar nan babu mai irinsa
Koda jin wannan batu sai mahaifiyar yarinya
alfila ta tsaya cak a waje daya
Jikinta na karkarwa saboda tsananin tsoro
tana tunanin tabi umarnin wannan aljana
ko kuma ta gudu
Daga can sai ta yanke hukuncin ta taimaki
aljanar koda kuwa tarkone tayi mata domin
ta cutar da ita
Hunnunta na karkarwa taje ta durkusa akan
aljanar sannan ta cire nattar daga wuyanta
ta budeta tasa mata a baki tasha rowan
Faruwar hakan keda wuta sai aljanar tayi
kumallo na wannan dafi da taci a jikin amfanin
gonar

Nan take ta sami lafiya ta mike zaune daram
kamar wani abu bai taba samunta ba
Aljanar ta dubi mahaifiyar alfila tayi mata godiya
sannan sai ta karbi battar daga hannun mahaifiyar
alfila ta girgiza taji rowan dake ciki dan kadanne bai
wuce makarwa uku ba
Aljanar ta girgiza kai gami da ajiyar zuciya tace
kinga wannan ruwan dake cikin wannan battar
maganin kowacce irin cutace kuma sinadarine
na sihirin tsafi wanda babu kamarsa a duniya
Wanda duk ya sha wannan tsumi babu wani
makami da zaiyi tasiri a jikinsa kuma duk irin
matsayin da mutum ke son kaiwa a duniya sai
yah au
Na gaji da wannan tsumi ne a wajen kakana
kuma duk duniya babu mai irinsa sai ni kadai
bincike ya nuna cewa nan gaba bazan kara
shekara goma ba a duniya zan mutu kinga kenan
idan na mutu babu mai sauran wannan sihiri
face wanda na baiwa ragowar wannan tsumi yasha
saboda haka ni yanzu zan baki ragowar tsumin ki
sha albarkacin taimakon da kika yi mini kika ceci
rayuwata dama kuma gashi na fuskanci kina
fama da kishirwa lallai wannan tsumin zaiyi miki
maganin kishirwar
Sa adda a;jamar yazo nan a zancenta sai mahaifiyar
alfila tce ai duk yadda nake son kaina bai kai yadda
nake son wannan yar tawa ba wadda na goya a
bayana saboda haka indai kin bani wannan tsumin
ita zan baiwa tasha AA Misau Ke Magana
Aljanar ta jinjina kai tace ai zabi na gareki amma ki
sani cewa duk wanda ya sha wannan tsumin
tsakanin keda ita sai ya fuskanci wata matsala
guda daya idan kece kika sha tsumin ba zaki
yi nisan kwana ba a duniya idan kuwa itace
tasha zatayi nisan kwana a duniya amma zata
rabu da ke tun tana karama kuma idan ta fara
girma matsafan duniya zasu saceta daga wajan
ubanta saboda su cire sihirin tsafin dake
jikinta amma a karshe sai ta daukaka a duniya
Lokacin da aljanar tazo dai dai nan a zancenta
sai mahaifiyar alfila tace ai kuwa indai hakane
na zabi yata ta sha wannan rowan tsumin
Koda jin haka sai aljanar ta bude bakin alfila ta
dura mata wannan ragowar rowan tsumin ta
shanye, sannan aljanar ta gargadi mahaifiyar
alfila akan cewar kada ta kuskura ta gayawa
kowa wannan al amari day a faru a tsakaninsu
Koda gama fadin haka sai aljanar tab ace bat
Daga wannan rana mahaifiyar alfila tayi shiru
da bakinta bata taba gayawa kowa ba sai a
ranar da ta kwanta cutar ajali

Koda ta fahimci cewa ciwonta bana tashi
bane sai ta sanar da mijinta sadauki awaisu
duk abninda ya faru tsakaninta da wannan
aljana a daji
Aikuwa wannan shine babban kuskuren da
tayi domin inda bata fada masa ba babu yadda
za a yi sauran matsafan duniya su san da batun
tsumin tsafin dake jikinta har suyi kokarin cireshi
daga jikinta
Ina son ki sani cewa boka shamzubul azwas
shine matsafi na tara wanda yayi kokarin cire
sihirin tsafin dake jikin alfila amma sai kuka je
kuka tarwatsa masa shiri
Yanzu nice matsafiya ta goma wacce zata
cire wannan sihirin tsafi daga kikin wannan
yarinya kuma ba makawa saina sami nasara
domin ku baku isa ku hanani ba…………………..
.
YANZU NICE MATSAFIYA TA GOMA WACCE ZATA CIRE
WANNAN SIHIRIN TSAFI DAGA JIKIN ALFILA KUMA BA
MAKAWA
SAI NA SAMI NASARA DOMIN KU BAKU ISA KU HANANI
BA
yake humaira ki dubi abokan tafiyarki Sarki sahibul hairi
da bawansa haluf
ga su nan duk a kwance magashiyan sun kasance
ragowar mutuwa
ke kadaice kika rage
kuma kike nema ki zame mini matsala, tabbas ba zaki
zame mini matsalar ba domin
yanzun nan zan hallakaki sannan na tafi can fadata
in da aka kai alfila aka ajiye mini na cika burina a kanta
koda shikura ta zo nan a zancenta sai humaira ta tari
numfashinta
ta daka mata tsawa tace
yake wannan munafukar Allah hakika ire irenku
annobace a doron kasa domin kun san gaskiya kun
taketa, kyma irin azabar da Allah zai yi muku idan kuka
koma gareshi ta musamman ce
lallai ba zan bari ki je ki ida wannan nufi naki ba idan kika
ga kin fita daga cikin
fadar nan sai dai idan bana numfashi
koda jin haka sai shukura ta bushe da dariya tace ai ga fili
ga mai doki kuma inda babu kasa nan ake gardamar
kokawa
nima ba zan yarda na fita daga nan ba face na tabbatar
keda abokan tafiyarki
babu mai numfashi domin idan na tafi na barku a raye
tamkar na kashe maciji ne
ban sare kansa ba domin na san sai kun bini har can
fadata kun tarwatsa mini shirina kamar yadda kuka
tarwatsawa

boka shamzubul azwas nasa
Yanzu zaki san cewa shirina ba irin na shamzubul azwas
bane
takadarancina da hatsabibanci na ya ninka nasa sau
goma
koda gama fadin haka sai shukura ta daga takobinta
sama tayi kukan kura ta ruga kan humaira, da ganin
haka sai itama humaira ta daga tata takobin ta tareta
suka ruguntsume da azababben yaki
nan fa shukura ta rinka kaiwa humaira sara da suka
cikin tsananin zafin naman da bata taba haduwa da
sadaiki mai irinsa ba kuma
saboda karfin saran duk sa adda humaira ta kare
sai taji kamar katon dutse mai nauyi aka buga mata har
sai ta durkushe kasa
wani lokacin ma har faduwa kasa take, in ba don itama
tana da zafin nama ba da tuni shukura ta hallakata
al amarin da ya dugunzuma hankalin humaira kenan ta
tabbatar da cewa lallai yau dai kam ta gamu da gamonta
babu abinda ya sa humaira takaici face ganin yadda
shukura ke ta karanta addu o'i irin na addinin
musulunci a lokacin da take karanto nata addu o'in
domin samun nasara a tsakaninsu
sahibul hairi dake kwance a can gefe daya yana ganin
abindake faruwa sai hankalinsa
ya fi na humaira tashi domin zuciyarsa ta karaya bisa
ganin yadda wannan gumurzu ke wakana domin fadan ya
nuna cewa shukura ce zata sami nasara saboda juma ar
da zatai kyau tun daga laraba ake ganeta
kuma da zarar shukura ta gama hallaka humaira ya san
cewa kansu shukura zata
dawo wato shida bawa haluf tasu tazo kusa, haka dai
humaira da shukura suka ci gaba da fafatawa babu
sassauci
har tsawon sa a uku
shukura bata sami nasarar koda kwarzanar jikin
humaira ba
saboda tsananin naci da juriya irin na humaira, duk da
cewa an fita zafin nama da karfin damtse, a wannan
lokaci
ne shukura ta fahimci cewa indai fada da makami zasu ci
gaba
dayi ba zata taba samun nasara akan humaira ba domin
ga dukkan alamu ba karamin horo
humaira ta samu ba akan sarrafa makaman yaki
koda gama aiyana hakan sai shukura ta shammaci
humaira ta doki hannunta da kafarta
takobin ta subuce kasa
itama shukura sai ta yarda tata takobin ta dunkule
hannayanta biyu kuma ta gyara tsayuwa ta ce yauwa
yanzu ne zamu banbance tsakanin aya da tsakuwa
kuma yanzune zakisan cewa ruwa ba sa an kwando bane

koda jin haka sai itama humaira ta gyara tsayuwarta
kuma ta dunkule hannunta tayi kabbara ta ruga kan
shukura
ai kuwa itama shukura sai tayi kabbarar ta tareta
suka ruguntsume da sabon masifaffen fada ya zamana
cewa suna kaiwa juna naushi
da bugu hannu da kafa, fara hakan keda wuya sai
humaira ta gane cewa shayi ba ruwa bane
domin shukura tafita karfin damtse nesa ba kusa ba
nan fa shukura ta rinka gabzawa humaira naushi a fuska
da cikinta AA Misau Ke Magana
tun humaira na kokarin kare naushin har ta kasa ya
zamana cewa tana layi a tsaye tana yin baya
taga taga kamar zata fadi, amma sai kaga ta cije
ana cikin haka ne shukura ta gabzawa humaira wani
katon naushi a fuska har wani gudan jini yayi fitar
burgu daga cikin bakin humaira kawai sai ta sulale kasa
magashiyan ta kasa koda motsawa bare ta mike tsaye,
koda ganin haka sai shukura ta bushe da dariyar
farin ciki sannan ta hau kan gadon bayan humaira ta
zauna
ta kai hannayanta biyu izuwa kanta da nufin ta
murde mata wuya, ba zato ba tsammani sai shukura taji
an daki bayanta da kafa
saboda karfin dukan sai da taji kamar bayan nata ya
burme kuma sai tayi
tsalle can gefe daya ta fado kasa da fuska ta fasa hanci
da baki jini ya kama zuba, a fusace shukura ta waigo
don taga wanda yayi mata wannan dukan shammace, ai
kuwa sai ta ga ba wani bane face sarki sahibul hairi,
yana tsaye amma yana tangadi kamar wanda ya sha
giya ya bugu sakamakon jinin dake zuba a
Raunin kirjinsa
bisa mamaki sai shukura taga sahibul hairi ya durkusa a
gaban humaira yana duba lafiyarta
jar hawaye na zuba a idanunsa domin a zatonsa ta mutu
koda ganin haka sai shukura tayi murmushin mugunta
sannan ta mike tsaye zumbur ta dubi sahibul hairi
ta bushe da dariyar mugunta tace
yau fa ga masoya biyu
duk a cikin mugun hali babu wanda zai iya ceton rayuwar
wani, lallai daya bayan
daya zan kasheku domin ku dandana takaicin kisan gillar
da zanyi muku, koda gama
fadin haka sai shukura ta daka tsalle daga inda take ta
dira a gaban sahibul hairi
ta rinka tumurmusashi tamkar ta sami tamola harma
tana fyadashi a kasa
kaico yaufa ga maza a hannun mata sun kasa tabuka
komai
a dai dai wannan lokaci ne humaira ta farfado ta dawo
haiyacinta

koda ta bude idanunta taga yadda shukura ke
tumurmusa
sahibul hairi harma tana naushinsa akan raunin nan na
kirjinsa yana
jini yana ihu da kara sar hankalinta ya dugunzuma
nan take humaira ta fara kiran sunayen Allah tsarkaka
tana yi masa kirari tana cewa
ya ubangin da bashi da kishiya kaine kayi alkawari cewar
zaka
kare addininka da kanka ya allah kada ka bari wannan
batacciyar ta sami nasara
akanmu
domin addininka take son ta dakusar ya allah ka
karfafani da karfi irin naka na sami nasara akanta
ai kuwa humaira na cikin yin wannan addu a ne sai taji
wani irin gagarumin karfi ya shiga jikinta irin wanda bata
taba ji ba kawai sai ta mike zumbur itama ta daka tsalle
daga daya ta dira a kan shukura
ta cakumo gashin kanta ta baya ta rukeshi tamau tayi
hajijiya da ita sannan ta fydata a kasa
shukura ta baje a kasa cikin wani irin hali mai kama da
rabi suma rabi mutuwa
domin kanta ma ya fashe jini na zuba
a tsammanin humaira shukura ta mutu don haka sai ta
ruga kan sahibul hairi a dimauce ta dora kansa akan
cinyarta
yayinda yake numfashi sama sama kamar zai mutu
cikin hanzari humaira ta dauko jakar guzurinta ta foddo
wani garin magani
ta zuba akan raunin da sarki sahibul hairi ke dashi ya
kwalla ihu sakamakon zogi da radadin da yaji
humaira ta yagi rigar jikinta ta daure raunin sahibul hairi
tamau sannan ta shiga
karanta addu o'i tana tofawa akan raunin nasa a lokacin
da hawaye ke zuba daga idanunta yana diga bisa fuskarsa
cikin matukar karfin hali sahibul hairi ya bude idanunsa
suka dubi juna sai yace yake ma abociyar kyau da
jarumta
kiyi sani cewa tsananin
ciwon da nake ji a jikina yayi yawa don haka ba zan rayu
ba
mutuwa zanyi
koda jin haka sai humaira ta rube bakin sahibul hairi
da tafin hannunta tace
yakai abin kauna ba zaka mutu ba har sai ka karbi addinin
gaskiya
ka sani cewa tun a ranar farko da na ganka naji zuciyata
ta kamu da kaunarka don haka ba zanso ka mutu ka
barni ba
idan har ka karbi tayin soyayyata hannu biyu to ka karbi
addinin gaskiya
dajin haka sai sahibul hairi ya sake bude baki da kyau ya

karanta kalmar shahada kamar yadda yaji humaira ta
biyawa yarinya alfila a lokacin da ta musuluntar da ita
koda humaira taji sahibul hairi yayi wannan kalma
sai ta cika da tsananin farin ciki bata san sa adda ta
rungumeshi ba ta fashe da
kukan farin ciki
AA Misau Ke Magana. A daidai wannan lokaci ne shima
bawa haluf ya dawo cikin haiyacinsa koda ya ga shukura
a kwance gefe daya cikin jini kuma yaga humaira
rungume da maigidansa tana rusa kuksa sai shima ya
kama kukan domin a zatonsa maiginda ya mutu
dajin sautin kukan bawa haluf sai sahibul hairi ya
janye jikinsa daga cikin na humaira ya dubi bawa haluf
yace kukan me kakeyi yakai amintaccen bawana ai ban
mutu ba domin masoyiyata ta ceto
rayuwata
koda bawa haluf yaga maigidan sa a raye har yana
magana sai ya rarrafo da guiwoyinsa izuwa gareshi suka
rungume juna
cikin tsananin farin ciki
kwatsam ba zato ba tsammani sai suka ji an bushe da
dariya koda suka dubi inda shukura ke kwance sai sukaga
wajen ya zama wayam babu ita sai jinin kanta da
ya zuba a kasa amma sun ga wata guguwa tayi sama
ta fice ta cikin rufin dakin, cikin matukar damuwa
humaira ta dubi sahibul hairi tace
akwai sabon aiki a gabanmu kuma gashi kai da bawa
haluf kuna cikin wani irin hali dolene mu zauna a nan har
tsawon wadansu kwanaki domin kyi jinyar raunikan
jikinku
sannan mu tafi neman gimbiya shukura domin mu
tarwatsa shirinta mu karbo Alfila
yanzu ku jirani anan domin na shiga cikin gidan sarautar
nan na nemi inda shukura
ta boye mahaifin alfila da sarkinsu, koda gama fadin
hakan sai humaira ta mike tsaye ta goge
jinin dake bakinta da hancinta sannan ta nausa cikin
gidan sarautar, sannu a hankali humaira ta isa har cikin
turakar
sarki inda ta iske sarki da awaisu a kwance akan gado
kuma a daure da sarkokin sihiri
nan take humaira ta karanta wata addu a ta tofa musu sai
sarkokin
sihirin suka bace bata sannan suka dawo cikin haiyacinsu
suka mike zumbur a dimauce zasu ruga waje da
gudu sai humaira ta daaka musu tsawa
nan take ta sanar dasu du abinda ya faru garesu bisa
shirin gimbiya shukura kuma
ta basu labarin yadda suka zo gurin tare da alfila har
shukura ta so ta yaudaresu ta hallakasu da bata sami
nasara ba
tayi fito na fito daasu aka

Kafsa gagarumin yaki bayan tuni tasa aljanu sun dauke
alfila sun gudu da ita kuma karkashin yakin sai aljanu ska
sake zuwa suka dauke shukura
suka tafi da ita bayan ta suma a tsammaninmu ma
mutuwa
tayi ashe bata mutu ba
sa adda su sadauki awaisu suka gama jin wannan labari
sai suka cika da tsananin
al ajabi kuma hankalin sadauki awaisu ya kara
dugunzuma
fiye dako yaushe ya ce nikam tun

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment