Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daji na kwana nan na tashi can
sannan na koma gida wato birnin misra.
Sa adda sarki sahibul hairi yazo nan a labarinsa tuni sun
gama cinye abincin dake gabansu haluf ya jinjina kai yace
hakika ya shugabana ka cika jarumi uban jarumai ina ba
don wasu dalilai ba da sainace idan akwai irinka goma a
birnin misra da munci duniya da yaki.
Koda jin haka sai sarki ya bushe da dariya ba tare da yace
komaiba ya mike ya fita wajen tantin koda ganin haka sai
bawa haluf ya mike da sauri ya harhada kayansu gaba
daya sannan suka hau ababan hawansu suka nausa daji.
Kamar yadda sarki sahibul hairi ya fada haka lamarin
yakasance wato basu isa birnin askandariyya ba sai
kwana talatin da bakwai har suka isa can din kuwa basu
sake haduwa da yan fashi ba saidai muggan dabbobin
dawa wadanda nan take sarki sahibul hairi keyi musu
kisan farat daya.
Lokacinda suka iso kofar birnin Askandariyya dare yayi

tsaka har bawa haluf ya nufi kofar birnin da nufin yaje ya
kwankwasa a bude masa sai sarki ya dakatar dashi yace
saurara yakai haluf aini kadai zan shiga cikin birnin nan
kuma indai na shiga ba zan tsaya ko ina ba har saina
dangana da fadar sarki barusa naje har inda aka ajiye
gatarin nan na lu'u lu'u na daukoshi ka sani yaki da
daddare na matsoraci ne lallai gobe da safe ido na ganin
ido zan shiga cikin wannan birni na nufi gidan sarautar
gadan gadan duk wanda ya tsaya a gabana sai dai
gawarsa abinda nake so dakai mu kwana nan kofar gari
kuma idan gari ya waye ka jirani a nan har naje na dawo
bayan cikar burina idan kuwa kayi kuskure ka biyoni lallai
zaka rasa rayuwarka.
Koda gama wannan jawabi sai bawa haluf ya sauko daga
kan dokinsa sannan yarike taguwar sarki shima ya sauka
cikin hanzari ya daure ababan hawansu a jikin wani dutse
ya kafa musu tanti suka shiga ciki suka kwanta suka kama
aikin rago.
Da Asubar fari sarki ya farka daga barci koda bude idansa
yaga bawa haluf yanata barci har da munshari saiya mike
ya kama yin damarar yaki ya kwaso makamansa ya
shiryasu a jikinsa da ya gama wannan shiri sai ya rufe
fuskarsa da wani rawani ya zamana cewa idanunsa kadai
ake iya gani ba tare da ya tashi bawa haluf daga barci ba
sai ya fita daga tantin yaje ya kwance taguwarsa ya haye
kanta ya durfafi kofar birnin Askandariyya a lokacinda
gari ya waye sosai rana ta fito.
Koda ya iso daf da kofar birnin wacce akayita da bakin
karfe sai yaja dunga ba tare da ya sauko daga kan
taguwar ba ya zare takobinsa ya kwankwasa kofar da ita
faruwar hakankeda wuya sai yaji an tambayeshi da
kakkausar murya wanene nan yake kwankwasa mana
kofa da sassafe haka? Hala kai bakone baka san ka'idar
shigowa birnin mu ba.
.
011. SARKIN SARAKAI BOOK1
.
Koda budar bakin sarki sahibul hairi sai yace Ubankane
yake kwankwasa kofar tun muna shaida juna ka bude
kofar nan in kuwa ka kuskura na banke kofar na shigo sai
mataccen dake kabari yafika kwanciyar hankali
maimakon abi umarni a bude kofar sai aka kyalkyale da
dariya Al amarinda ya fusata sarki kenan kawai ya sauko
daga kan taguwar tasa yaja da baya kimanin taku Ashirin
sannan ya rugo da gudu ya hada karfinsa gaba daya ya
doki kofar garin da kwanjinsa take kofar ta fita fit! Shi da
ita suka burma ciki kai kace giwace ta rugo ta bangaji
kofar
.wOHoHO nikain
Cikin hanzari sarki sahibul hairi ya mike tsaye sai yayi
arba da wani murjejen kato a gabansa katon sanye da
suulken yaki kuma ga wani shafcecen gatari a hannunsa

amma duk jikinsa karkarwa yake ya kurawa sarki sahibul
hairi idanu kawai cikin firgici kamar ace kyat ya fita da
gudu sbd razana
shidai wannan kato ba kowa bane face sarkin kofa
sahibul hairi ya dubi katon yace, kai kuma waye kuma me
kake jira dani ba tare da ka afko mini ba tunda ga
makami a hannunka' cikin murma mai rawa katon yace
nine sarkin kofar birnin Askandariyya yau shekarata
arba'in ina gadin wannan kofa amma a tsawon wadannan
shekaru ban taba ganin sadaukin mutum tamkarka ba ka
sani cewa an taba kokarin balle wannan kofa da karfin
giwaye biyu amma abu ya faskara yau gashi kai bil adama
kai daya ka banketa anya kuwa kaiba aljan bane? Idan kai
mutum ne wanene kai kuma menene yazo dakai wannan
birni namu' sarki sahibul hairi yace nine sarki sahibul
hairi na birnin misa kuma nazo wannan birni nakune don
biyan wata bukata tawa, kayi mini jagora izuwa fadar
sarkinku inba haka ba kuwa yanzun nan zaka bakunci
barzahu, lokacinda sarki yazo nan a zancensa sai sarkin
kofa yai ajiyar zuciya yace hakika biri yayi kama da
mutum ni kam nasan cewa duk duniya babu wani
sadauki da zai iya bangaje wannan kofa ta fadi face sarkin
misra tuni labarinka yazo mana nan to amma ina mai
shawartarka da ka janye duk irin bukatar dakazo da ita
domin na tabbata cewa sarkinmu bazai yarda da ita ba na
sani cewa kai jarumine uban jarumai amma kada ka
manta cewa sarkin yawa yafi sarkin karfi
kodajin haka sai sarki sahibul hairi ya dakawa sarkin kofa
tsawa yace ai ragon maza shike tsoron yawan maza kabi
umarnina ko kuma na tabbatar da alkawarina akanka
sarkin kofa yace nikam bazanbi umarninkaba saidai nabi
na sarkina domin idan na saba masa masifarda zan shiga
saina gwammace Ajalina
kafin sarki yace wani abu tuni sarkin kofa ya zare wani
kaho ya busa faruwar hakan keda wuya saiga dakaru
suna ta bullowa a guje tako ina duk sun zare makamai
ashe tun dazu ma a lallabe suke suna ganin abinda ke
faruwa tsakaninsu lokacinda sarki ya balla kofar birnin
saida karar kofar ta cika birnin gaba daya amma da
yawan jama a basuyi tsammanin cewa kofar birnin bace
wasuma sun zata fashewar dutsen wuta ne
kafin sarki ya ankara tuni sama da mutum dari uku sun
kewaye shi rike da makamai tsirara sahibul hairi ya
dubesu yai murmushi kawai saiya yunkura da nufin ya
ratsa ta cikinsu yai gaba aikuwa sai suka rufar masa gaba
daya da nufinsu daddatsashi suyi gunduwa gunduwa
dashi
hakika rashin sani yafi dare duhu inda wadannan dakaru
sunsan abinda zai biyo baya da basuyi gangancin afkawa
sarki sahibul hairi ba domin a cikin dakika dari da ashirin
ya rugurguzasu tamkar an kwankwasa gilashi ya zamana
cewa sarkin kofa ne kawai a tsaye kikam kamar gunki

idanunsa sun zazzaro kamar zasu fado kasa gaba daya
jikinsa rawa yake ya firgita fiye da dazu sa adda ya gaya
balla kofar birnin ya fado ciki
sahibul hairi ya dubi sarkin kofa yace maza ka gayawa
sarkinku abinda ya faru yanzu kuma kace dashi idan ya
bani abinda nazo nema zamu rabu lafiya idan kuma ya ki
a yau dinnan zan baje wannan birni yadda ko a tarihi
baza a tuna dakuba.
Koda gama fadin haka sai sarkin kofa ya ruga inda
dokinsa yake ya kwance ya haye sannan ya sukwaneshi
izuwa cikin birnin Askandariyya
shikuwa sarki sahibul hairi sai ya koma inda yabaro
taguwarsa yahau sanna ya shigo cikin birnin ya kara gaba
++
A can fadar sarki barusa kuwa fadar ta cika makil da
fadawa da talakawan gari domin a yaune sarki barusa ke
walimar cikar shekaru talatin akan karagar mulki banda
shagali babu abinda akeyi a fadar masu kida nayi masu
rawa nayi abinci kuwa da abin shaye shaye gasu nan
birjik babu adadi kowa abinda yake so shi yakeci kallo
daya mutum zaiyiwa sarki barusa ya gane cewa a cikin
tsananin farin ciki yake A wannan lokaci Barusa na zaune
shirim kamar giwa a kan karagar mulki yanata
kwankwadar giya sai rusa dariya yake yana kallon
wadansu yan mata dake ta tikar rawa a gabansa yana
annashawa.
Ana cikin tsakiyar wannan haline akaga sarkin kofa ya
shigo a guje yanata faman haki Al amarinda ya
dugunzuma hankalin kowa kenan akayi tsit tamkar
mutuwa ta gifta kowa kuma ya kame kamar babu mai rai
a wajen
++
.
Ana cikin tsakiyar wannan haline akaga sarkin kofa ya
shigo a guje yana ta faman haki Al amarinda ya
dugunzuma hankalin kowa kenan akayi tsit kamar
mutuwa ta gifta kowa ya kame kamar babu mai rai a
wajen
Da zuwan sarkin kofa saiya fadi gaban sarki yayi gaisuwa
sannan yace ya shugabana kayi sani cewa yanzu haka
jarumi uban jarumai ya shigo kasar nan ya banke kofar
gari da karfin sadaukantakarsa kuma ya kashe dukkanin
abokan aikina yana nan tafe izuwa nan fadarka don biyan
wata bukata tasa ni kaina ya kyaleni ne kawai don nazo na
isar da sako'
cikin tsananin fushi sarki BARUSA ya dakawa sarkin fada
tsawa wacce tasa dukkanin jamar wajan suka fadi kasa
suka kwanta da ruf da ciki don tsananin razana
sarki barusa ya kasance lafcecen katon mutum mai surar
mutanen farko gashi dogo kuma gashi kakkaura duk
jikinsa a murde yake ya tara jijiya da kwanji komai
tsawon mutum sarki barusa na iya dora abinci a kansa

yaci yana da jajayen idanuwa ababan tsoro yanada
wawakeken hanci da katon baki a takaice dai idan ana
batun muni to sarki BARUSA kurunkus ne!
Sarki barusa ya nuna sarkin kofa da yatsa yace wai shin
wanene jarumi uban jarumai harda ya isa ya banke kofar
birnina ya kashe min dakaru har yace lallai sai ya shigo
fadata bidar wani abu?
Sarkin kofa yace Aiba wani fane face SARKI SAHIBUL
HAIRI na birnin misra
kodajin wannan batu sai sarki barusa ya mike tsaye ya
takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya ita kanta
dariyar abar tsoroce domin zata iya firgita mai ciki tayi
bari zata iya sa mutum gudawa kuma zata iya zamo
sanadin yin hijirar dukkanin tsuntsayen daji
bayan sarki barusa yai dariya ya gaji saiya koma kan
kujerarsa ya zauna su kuwa fadawanda gaba daya sun
tsure sun dimauce tunda sukaji ance sarki sahibul hairine
yazo
wazirin sarki barusa wanda ake kira YARKUS ya matso daf
da sarki yace ranka ya dade yanzu menene abinyi? Ka
sani cewa sarki sahibul hairi ya shahara fagen jarumtaka
da samun nasarar yaki shinefa mutuminda ya gagari
rumawa da hindu shine wanda ya shiga har birnin farisa
ya sare kan sarkinsu kuma shine sarkinda ba a taba cin
kasarsa da yaki ba sai sau daya a yakin da suka gwaza da
rumawa amma dukda cewa an kashe gaba daya
dakarunsa saura shi kadai saida yayi musu mummunar
barna kuma ya tsira da rayuwarsa
lokacinda waziri yarkus yazo nan a zancensa sai sarki
barusa ya sake bushewa da dariya a karo na biyu daga
can kuma ya murtuke fuskarsa yace ya kai yarkus kayi
sani cewa baka fini sanin ko waye sahibul hairi ba na
sanshi kamar yadda na san kaina abinda nake so daku
shine kowa ya nutsu ya koma mazauninsa
idan sahibul hairi ya shigo nan ya iskemu muna
harkokinmu kamar yadda muke yi dazu tamkar labarinsa
bai riskemu ba ina son naji abinda ya zo nema a kasata
sannan na san hukuncin da zan dauka akansa
koda gama fadin haka saigaba daya jama ar dake fadar
suka dawo cikin hayyacinsu aka ci gaba da sharholiya
tamkar babu abinda ya faru
jim kadan da faruwar haka saiga sarki sahibul hairi bisa
taguwarsa ya shigo da ita har cikin fadar babu abinda zai
baiwa mutum mamaki face ganin yadda ita kanta
taguwar take tafiyar kasaita tamkar akan sahara shi kuwa
sarki sahibul hairi na zaune a kanta cikin wannan shigata
bakaken kaya fuskarsa arufe idanunsa kadai ake gani sbd
tsabar kwarjinin sahibul hairi saida masu rawa da kida
suka kasa cigaba da aikinsa fadawa da sauran jama ar
gari kuwa saida kowa ya natsu ya kurawa sarki sahibul
hairi idanu duk wanda ka duba saikaga bakinsa a bude
tamkar shashasha.

Taguwa taci gaba da tafiya har ta iso daf da karagar sarki
barusa sannan ta tsaya cak aka fara kallon kallo a
tsakanin sarakan biyu sarki barusa ya murtuke fuska
tamkar an aiko masa da sakon mutuwa dama tuniya kule
saboda ganin jama arsa sun firgita da ganin sarki sahibul
hairi.
Tsawon yan dakiku fadar tayi shiru kamar ba mai rai a
cikinta daga can sai sarki sahibul hairi ya risina kadan ga
sarki barusa yace tsakanin sarki da sarki akwai
girmamawa yakai mai birnin Askandariyya kayi sani cewa
ban shigo kasarka da nufin cin zarafinka ba ko zalunci ba
zan la anta kowa ba face wanda yaso la antani
ina hadaka da girma da arziki ka bani abu guda daya rak
na tafi dashi idan kayi haka nayi alkawarin ba zan cutar
da ko kazar garinnan ba idan kuma kaki nayi alkawari
saina karar da dukkanin dakarunka na biya bukatata koda
kuwa a sanadin hakan zan baje gidajenku su zamo
turbaya
koda jin wannan batu sai sarki barusa ya bushe da dariya
sannan ya hade fuska yace yakai mai birnin misra ka fadi
abinda kake bukata daga gareni na baka domin ina da
labarin cewa fatara da talauci sun isheka idan na abinci
ne zan sa a baka wanda zakaci kaida jama arka na
shekara goma idan kuma sutura ce kake so zan baka
wacce zata kaika shekara arba in kana sawa kullum
sa adda sarki sahibul hairi yaji wannan batu sai ya
murtuke fuskarsa yace ai ba bara nazo yi wajenka ba
abinda nake bukata a wajenka ba komai bane face
gatarin lu'u lu'u wanda kuke bautawa
. 013. SARKIN SARAKAI BOOK1
.
Koda jin wannan batu sai sarki barusa ya sake bushewa
da dariya a karo na hudu sannan ya mike tsaye ya dubi
sahibul hairi cikin murmushi yace ai wannan abune mai
sauki kabi waccen hanyar zaka isa dakin da gatarin yake
saika dauko cikin salama kazo kayi tafiyarka'
ba tare da tsayawa yin wani nazari ko tunani ba kawai
sarki sahibul hairi yabi wannan hanya wadda sarki barusa
ya nuna masa koda ya kusa isa wata kofa sai kasa ta dare
ya rufta cikin wani dakin kasa mai tsananin zurfi yana
fadawa sai kasar ta hade ta rufe ruf tamkar bata taba
darewa ba
sarki barusa ya tuntsure da dariya yace lallai wannan ya
cika mahaukaci to inbanda mahaukaci wane ne abokin
gabarsa zai nuna masa hanya yabi? Tabbas yakai kansa
izuwa mahallakarsa
sa adda sauran fadawa da jama ar gari sukaji haka sai
suma suka kama kyalkyala dariya suna cewa tabbas sarki
sahibul hairi ya cika mahaukaci
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU A FADAR SARKI
BARUSA
++

AL AMARIN SARKI SAHIBUL HAIRI kuwa lokacinda kasa ta
dare ya fada kasanta sai yaji ya fadi cikin wani faffadan
daki mai tsananin zurfi fadowarsa keda wuya yaji ana
tayin wani irin gurnani mai ban tsoro kasancewar dakin
akwai duhun gaske baiga abubuwanda ke gurnanin ba.
Bazato ba tsammani sai dakin ya haske fayau yaga
abubuwan dake gurnanin ba komai bane face wadansu
rikakkun zakuna wadanda a kalla adadinsu yakai guda
dubu dukkaninsu a kwance suke sunyi wa dakin kawanya
ma ana a tsakiyarsu sarki sahibul hairi yafado
koda zakunan nan sukayi arba dashi sai suka fara zazzago
harshe suna tamde baki alamar cewa sun jima suna fama
da yunwar abinci kawai suke nema tunda sahibul hairi
yazo duniya bai taba ganin zakuna masu girma da tamkar
wadannan dukda dakakkiyar zuciya ta mazan jiya saida
hankalinsa ya dugunzuma yasan cewa lallai yau ya gamu
da gamonsa sai abinda hali yayi
kamar hadin baki sai zakuna suka daka tsalle lokaci guda
gaba dayansu suka yi kan sarki sahibul hairi suka
tumurmusheshi da nufin su cinyeshi
sahibul hairi ya yunkura da dukkanin karfinsa ya watsar
dasu sai gashi sun tarwatse a sama suna buguwa da
garun dakin kafin su sake kawo masa farmaki tuni ya zare
takubba biyu a jikinsa hagu da dama ya hausu da sara
duk zakin da ya sara sai yaji kamar dutse ne saidai kaji
wani irin sauti ya tashi kall.
Al amarinda ya dugunzuma hankalinsa kenan ya tabbatar
da cewa lallai maganar sarki barusa ta tabbata cewa ya
kawo kansa izuwa mahallakarsa
nanfa zakunan nan suka kara kaimi wajen daka tsalle
suna kai masa hari suna kokarin ya kusarsa da kokarin
cinyeshi inba don sahibul hairi ya kasance mai tsananin
zafin nama da sadaukantaka ba da tuni sun gama dashi
amma dukda hakan saida suka fara karkarce jikinsa da
faratan hannunsu
kafin ya ankara tuni jini ya fara zuba a jikinsa koda ya
fuskanci cewa zai hallaka ba da dadewa ba in akaci gaba
da wannan gumurzu sai yayi jifa da takkubban hannunsa
sannan ya takarkare ya kwarara uban ihu mai tsananin
firgitarwa ihune ya sa zakunan sukaja da baya sukayi
cirko cirko
ihun yaci gaba da amsa kuwwa har sarki barusa da jama
arsa dake zaune a can fada saida suka jiyo ihun amma sai
sukayi zaton cewa wahala ce tasa sahibul hairi yake
wannan ihu don haka sai suka kama kyalkyala dariyar
mugunta
lokacinda zakunan nan suka firgice da jin wannan ihu na
sahibul hairi sai aka fara kallon kallo tsakaninsa dasu
tamkar sunji tsoro bazasu sake afka masa ba daga can sai
suka sake daka tsalle gaba dayansu sukayi masa rubdugu
wohoho! A sannan ne fa tsagwaron karfi da jarumtaka
sukayi ranarsu domin sahibul hairi wanzuwa yayi tamkar

shaidani a tsakiyar zakunan nan duk wanda ya nausa sai
dai kaga yai sama ya fado kasa kafin ya mike sai yasa kafa
ya tatsile kansa take zakaga kan zakin ya dagwargwaje
tamkar an kwankwatsa shida dutse wani lokacin idan ya
naushi zaki a gadon baya saidai kaji bass! Wato ya karya
masa kashi nan fa zakunan nan suka ringa bajewa a kasa
suna zama gawa
koda sahibul hairi yaga ya samo lagon zakunan saiya kara
kaimi a kansu yaci gaba da ragargazarsu da karfin damtse
cikin zafin nama da juriya da jarumtaka kai saida takai
cewa yana kama kawunansu yana murde musu wuya da
karfin tsiya saidai kaga yayi jifa da gawar zaki.
Hakika karfi jarine domin inda sarki bai kasance sadaukin
gaskeba da tuni zakunan sun zamo sanadiyar Ajalinsa duk
da cewar ya samo lagon zakunan ba su fasa yi masa rauni
ba domin kartar jikinsa suke da farata nan da nan jikin
nasa yai fata fata tamkar da kaifin takobi ake saransa
saboda zafin yankan da suke masa ne ya dinga kwarara
ihu yana ci gaba da kakkarya gabban jikinsu.
Saida aka shafe kusan rabin sa'a ana wannan dauki ba
dadi sannan ya samu ya kashe gaba dayan zakunan nan
aikuwa yana gamawa dasu ya yanke jiki ya fadi a
lokacinda jiri da jini ke dibarsa, dama tun lokacinda aka
fara wannan gumurzu su sarki barusa na jiyo ihunsu da
gurnanin zakunan amma daga bisani sai sukaji shiru ba
ihun sarki bana zakuna .
.
Dama run lokacin da aka fara wannan gumurzu tsakanin
sahibul Haiti da zakunan su sarku barusa Na jiyo ihunsu
da gurnaninsu amma daga bisani sukaji shuru ma ana
babu ihun sahibul Haiti kuma babu Na zakunan
Al,amarinda ya baiwa sarki barusa mamaki kenan kawai
sai ya dubi wadansu dakaru dubu uku tace maza kuje
cikin wannan dakin Kasan su gano masa abindake faruwa
shinn zakunann nan sunn kashee sarki sahibul hairii ko
kuwa shine yakarkashesu.
Yayinda dakaru sukaji wannan umarni Na sarki barusa sai
hankalinsu ya dugunnzuma suka tsaya suka yi charko
charko suna kallon junansu aka rasa Wanda zai wuce
gaba
Ba wani dalili bane yasa wadannann dakaru suka kasa
zuwa wqnnan daki ba sai saboda bala,in dake cikinsa
Shidai wannan wuri an tanadeshine musamman son
hallaka iron mutanan da aka yankewa hukunncin kisa
hakika sarrki barusaa karyaa yayiwa sahibull hairi cewaa
a wannan bangareen gatarinn sihirinn yakee
A cikin wannan gidaan kasa India sarki sahibul hairii ya
fadaa akwai dakuna gomaa sha biyuu a cikinn kowanne
dakinwl akwaii masifa iri dabann masifar dakina farko ta
bata kai wacce take dakii nabiyu baa wadda ke dakin Na
uku tafi ta daki nabiyu

Wato dai abin bi dabi be har zuwa dakin karshe wato Na
gomaa sha biyu
Idan mutun ya kuskura ya fada daki Na farkoo toga babu
wata hanya da zaibi ya fito dolene sai yabi ta cikin
ragowar dakunaa goma sha dayann
Lokacinda sarkibarusa yaga dakarunsa sunnoke sun kasa
lafiya cikin wannan wuri sai ya tuntsure da dariyar far in
ciki yace lallai kun Sani cewa ba a Shigaa wannan wuri a
fito a rayee
Ko shakka babu wannan makiyi namu tuni yanzu ya
hallaka,,
Koda fadawa da jama at gari sukaji wannan batu sai suka
bushe da dariya nan take aka cigaba da shagali tamkarr
babu wata miskila data task
++. +++. ++. ++
Al amarin sarki sahibul haiiri kuwa lokacinda yaga ya
kashe zakunan nan gudaa dubu saiya fadii kasa yana haki
saboda tsananin gajiyaa
Visa dole ya yanke hukuncin ya tsaya yayi jinyar jikinsa
kafinnan kafin ya tunkari daki Na gabaa tunda dai baisan
masifar dazai iske ba a cikinta nan take ya kwance wata
karamar jakaa dake kugunsa ya fiddo wani Baron magani
ya shashahafa a jikinsa sannan ya kwanta a cikin
gawarwakin zakunan nan son ya huta
Faruwar hakan keda wuya sai bacci ya saceshi bai saniba
aikuwa bai farka ba sai da rana ta fadi kodaya bude
idonsa ya tsinci Kansas cikin gawarwakin zakuna kuma ya
fuskancii cewaa ya Dade yana wannan bacci sai ransa ya
baci domin yaso ace duk bala inda zaiyi ya dauko Gagarin
sihirin a cikin abinda vai wuce ss a biyarba har yabarr
kasar Askandariyya
Nan take kuma sahibul haiiri yaji yanajin yunwa gashi
kuma bai taho da jakar guzuri ba ya barta a can bayan
gari wajan bawa haluf nanfa hankalinsa ya tashi SBD
yasan cewa Indaii yacigaba da Shiva dakunan wannan
gida a haka zai jya rasa rayuwarsa tunda gajiya da yunwa
a jikinsa babu kuzarinda zai iya yin yaki
Yana cikin wannan haline dabara ta fado masa nan take
ya farke cikin zakuna ya fiddo kayan cikinsu yakama
cinsu danye bataree da gashiba tunda babu wutarda
zaigasa run yana yamutsa fuska SBD rashin jin dadin
naman a bakinsa harma yajiyasaba da rashin dadin
Bai gusheba yanacin naman harsaida yaji ya koshi sannan
ya mike tsaye yasake daukar takubbansa guda biyu nan
ya banke kofar dakina biyu da kafarsa ya kunnna kai ciki
Da shigarsa sarki sahibul haiiri cikin dakinn Na biyu sai
yayi arba da wadansu iron zagba zabgan maridai
wadanda girmansu ya wuce kima da tunanin bill adama
kowanne daga cikin su ya ninka sarki barusa a tsawo sai
biyu hakama fadinsu da kaurinsu
Dukda cewa sarki sahibul haiiri Nada dakakkiyar zuciya
saida ya tsorata ainun da ganin wadannan maridai Dan

ko a labaran dayasha ji baitaba jincewa akwai maridai
kalan suba
Wadannan maridai dai su dubu ne cif kuma kowannensu
Na rike da zabgegiyar makamai guda Inda za a ajiye
makamin mutum daga daga cikinsu makamin ba zai
dauuku ba face antara karti majiya karfii mutum arba in
Sudai wadannan maridai suna da mummunar siffa
maiban tsoro tamkar dodanni kallon daga zakayiwa kirar
jikinsu kasan cewa karfafane domin duk naman jikinsu a
cure take tamkar an shirya mulmulallen diwatsu gashi
sun Tara many an damatsa jijiyoyin kwanji hakika idan
aka Tara irinsu goma zasu iya yakar babban birni
suciahida yaki a cikin Rabin ss a
Yayinda sarki sahibul hairi yai arba da wadannan maridai
sai zuciyarsa ta karaya ya juya d baya da nufin ya koma
wajan da ya fito wato dakina farko aikuwa saidaya daga
cikin maridan ya zuro zungureren hannunsa ya cafkoshi
yai samaa dashi ya fyada da kasa
Saboda tsananon radadi da zugi saida sahibul hairi
yatakarkare yaji kamar an karya Massa duk kasusuwan
dake bayansaa don haka saiya kasa tashi
Maridin ya daga wani faskeken gatari Dame hannunsa ya
dankarawa sahibul haiiri Sara a cikii aikuwa koda gatarin
ya dira akan cikin sahibul haiiri saiya kakkarye amma
karfinn saran yasa cikinsa ya kulle yaji kamar zai suma
Kosa faruwar haka sai mamaki ya kama maridannan gaba
dayansuu saboda ganin yadda karfin gatarinsu yake yasiri
a cikin duk wani .wahaluki amma yau gashi bill adama
yaki yayi tasiri a jikinsa harma ya zauna lafiya bayan a
tarihin Gagarin ba a taba saran wani abuba Wanda ya
kasa rabewa gida biyu
Aikuwa sai maridannan suka taso Masa gaba dayansu
shikuma yahau maridannan da Sara da suka sukuwa suka
dinga kai masaaa cafka yana gocewa
Babban abinda yatayarwa da sahibul haiiri hankali shine
gashidai yana saransu jikinsu nadarewa yana zubar da
jini amma ko kadan basa gezau kai wani lokacima harr
caka musu adduna yake a cikinsu amma da ya zaree
saikaga sun cigaba sa yaki saboda taurin rai da naci iron
nasu
Al,amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan ya
tabbatar da cewa indai akaci gaba da wannan gumurzu a
haka izuwa wani lokaci mai tsawo zai iya gajiya su sami
damar hallakashi
Su kansu maridan sunsan cewa yau sun hadu da
shahararren bill adama domin tinda suka wanzu a
wannan wuri ba a taba jeho musu mutun ya gagaresu
hallakawa a cikin dakika sittin yau gashi sun shade kusan
Rabin sa a suna artabu da mutum daga kacal alhali
sunsha ragargaza mutane dubu cikin kankanin lokaci
Ana cikin wannan dauki ba dadi ne sahibul haiiri ya sari
daga daga cikin maridan a tsakiyar kai kawai sai yaga

wannan maridin ya sulale kasa ya zama gawa koda ganin
haka sai murna ta kama sahibul haiiri don yagano
lagonsu nan fa ya wanzu yana saransu aka suna faduwa
kasa matattu
Yayinda .maridan su kaga yanayi musu wannan barna
suma sai suka kara kaimi wajen kokarin hallakashi
maimakon koka Inda suke su cafkeshi sai suka fara
kaimasa Sara da suka da bugu da naushi
A wannan lokaci nefa yakin ya sauya salo domin idan
suka sameshi da. Naushi saikaga kamar an cillashi daga
cikin kibiya
Saidai kaga yaje ya manne da jikin garu akwai lokacinda
babban cikin maridan yayiwa sarki wawan naushi a ciki
saiyaga sahibul haiiri a sama ya manne da rufin dakin
yana aman jini amma SBD juriya irin namaza bai yarda
sun cafkeahi ba sai yaci gaba da saransu aka sukaci haba
da mutuwa
.
.
Hahahaha kaji many an sarakuna sahibul hairi mazajen
duniya
. 015. SARKIN SARAKAI BOOK1
.
YAYINDA maridannan sukaga suna dada cigaba da
mutuwa sai suka rude kuma suka firgice suka rinka kaiwa
sahibul hairi mummunan sara da suka shikuwa ya wanzu
yana mai zilliya da goce goce a tsakaninsu a hakanne fa
suka rike kashe kansu basu saniba
saida aka shafe sa a uku ana wannan dauki ba dadi
sannan gaba daya maridannan suka kare wato dai suka
zama gawa
shikuwa sahibul hairi saiya bingire kasa a sume saboda
tsananin jigata wannan shine abinda ya shiga cikin fadar
sarki barusa don daukar gatarin sihiri
++
Al amarin bawa haluf kuwa lokacinda ya farka daga barci
sai ya nemi ubangidansa bai ganshiba kuma baiga
taguwarsa ba saiya tabbatar da cewa aikin gama ya gama
wato tuni sarki sahibul hairi ya shiga cikin birnin
Askandariyya
nanfa hankalin sahibul hairi ya dugunzuma ya rasa
abinda ke masa dadi kawai saiya zauna yana shawarwari
a cikin zuciyarsa abu na farko dai shine bai san halinda
sarki sahibul hairi ke ciki ba a yanzu, zata iya yiwuwa ya
hallaka kuma ko

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment