Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ce, "ya ke wannan kuyanga mai zai hana ki
zauna ki bamu wannan labari yadda akayi har matar
Baruzul Damsus ta yaudareshi ta sace rabin dukiyarsa
alhalin yana kan matsayin sarkin 6arayi na duniya mai
karfin sihirin tsafi?"
Kuyangar ta sake murmushi a karo na biyu ta ce, "hakika
kuna wasa da kaidi irin namu na mata, domin inda ka ji
kaidin da matar Baruzul Damsus ta kulla ta sami nasarar
sace dukiyar kuma ta tsira da ita da kun sallamawa mata.

Ku yi sani cewa dokace babba akan duk hadiman gidan
nan na baku wannan labari, domin labarin ya kunshi
sirrin Baruzul Damsus. Wata kila nan gana bayan
bukatarku ta biya shi da kansa ya iya baku labarin da
bakinsa.
Da wannan furuci nake yi muku sallama, ku huta lafiya".
Koda fadin haka sai kuyangar ta juya ta fita daga cikin
dakin, ta janyo musu kofa ta rufe.
Nan da nan kuwannansu ya hau kan gado guda suka
bararraje suna more lahinsa da ni'imarsa domin su yi
barci. Amma sai barcin ya gagara, domin hirace ta sarke
a tsakaninsu.
Da farko dai Waziri ne ya dubesu ya ce, "hakoka duniyar
nan da fadi take, kuma abin cikinta yawa gareshi. Ni kam
na fuskanci cewa in dai da rai da nuntashi to har abada
buri ba zai yi karshe ba.
Ku tsaya kuyi tunanin irin dukiyar da wannan 6arawo ya
tara ku dubi irin daular da yake ciki, amma duk basu ishe
shi ba yana hankoran ya sami wata. Wai shin me zai yi da
dukiya ne? Gashi dai bashi da mata a yanzu, kuma bashi
da 'ya'ya, shin baya tunanin cewa komai dadewa sai
mutuwa ta riskeshi. A yau idan ya fadi ya mutu waye zai
gaji gidan da dukiyar da ke cikinsa?".
Sa'adda Waziri ya zo nan a zancensa sai ya ran nasa biyu
guda biya sai suka yi ajiyar zuciya. Daya daga ciki mai
suna shumar ya ce, "ya shugabana ai baka san sirrin da
ke zuciyarsa ba, sabo da haka bai kamata kayi mana
wannan tambaya ba. Tabbas akwai wani abun da yake
shiryawa rayuwarsa da dukiyarsa.
Itkanta wannan rabin dukiya ta birninmu da yake son ya
mallaka akwai wani burin da yake son ya cika da ita. Ni
dai kawai abinda ya daure min i kai da al'amarinsa shi ne
batun matarsa wadda ta shammaceshi ta gudu da rabin
dukiyarsa".
Koda jin wannan batu sai Waziri ya yi murmushi ya ce,
"ai inda ka san matsayin kaidin mata a duniya da baka
fadi haka ba. Ina tabbatr maka da cewa duk wani tashin
hankali da ke faruwa a duniya babu mai haddasa shi face
mata. Idan mata suka so za ai zaman lafiya, idan kuma
basu so ba sai dai ayi ta tashin hankali.
Shin ka ta6a jin labarin sarkin Rum shi ne mutumin da
yake kaunar 'yarsa fiye da kansa, wanda a sabo da haka
ya shiga duniya neman wadansu gagaruman abubuwa
don ta daukaka a duniya, ya yin da matansa suka dauki
aniyar ruguza wannan shiri nasa tare da kawar da
yarinyar daga doron kasa?".
Waziri ya ce, "ai kuwa ban ta6a jin wannan labarin ba,
kuma zan so in ji shi".
Sumar yai murmushi ya ce, "ai kuwa labarin yana rubuce
a cikin wani littafi wai shi DAKAKKIYAR ZUCIYA amma zan
datsi labarin ne na ci maka gaba soda yawansa.
"Sarkin Rum ya co gaba da keta gudu a cikin daji tamkar

bazai tsaya ba har duhun dare ya fara shigowa. Bisa sole
ya ja linzamin dokinsa ya tsaya, ba don ya gajo ba, kuma
ba don ya so ba face sai domin dokinsa ya dan huta ya yi
kiwo, shima ya ci daga guzurinsa, ya sha ruwa, ya dan
kishingida yana hutawa. Bayan kimanin sa'a data ya tashi
ya ci gaba da tafiya.
Bayan ya shafe tsawon sati guda yana tafiya a cikin
mugwayan dazuzzukan da ke nahiyar ba tare da ya sake
haduwa da wani mugun abu ba tun daga muyagun arnan
dajin nan masu karfin sihiri da suka kwabza azababban
yaki da su, face namun daji wadanda ko damuwa da su
baiyi ba, domin ya raina jarumtakarsu. Amma a zuciyarsa
yana fata ya sake haduwa da wani mugun abun wanda
yafi arnan dajin, domin shi yana ganin a haka zai ci gaba
da baiwa kansa horon yaki da miyagun abubuwan da
suke cikin wadannan dazuzzuka.
Yana tsaka da tafiya sai ya zo bakin wata sahara mai
tsananin zafi da nisan tsiya, ko ina ka kai dubawarka
saharace, ba za ka ta6a hango karshenta ba. Kuma sau
tari zazzafar iska kan buso daga cikin saharar ta yanyame
sagarar sai ka daina ganin komai, wanda ko wacce halitta
indai tana wajen.
Sa'adda ya zo dai-dai bakin saharar ne, ba tare da wata
shawara ba, ko kuma tunanin abin da zai biyo baya ba, ya
banna kansa kawai cikin saharar ya fara tafiya tinkis-tinkis
bisa dokinsa yana kallon gefe da gefensa. Bai yi nisa da
fara tafiya ba wata kishirwa mai tsanani ta soma
addabassa, dan haka ya dakko silkassa ta ruwa ya kafa a
bakinsa ya shanye ruwan cikinta. Koda ya sake ci gaba da
tafiya sai ya sake jin wata kishirwar wadda ta fi ta farko a
karo na biyu. Ya sake dakko silkar ruwan nasa ya sha
ruwa. A takaice dai bai yi nisa da tafiya a cikin saharar ba
ya shanye gaba daya ruwan guzurinsa. Haka ma dokinsa
ya gaza tafiya a cikin saharar. A fusace ya tsaya cak, ya
dire daga kan dokin, kafarsa ta nutse a cikin saharar, wata
kura ta tashi.
A dai-dai lokacin ya ji wata kakkarfar iska a saman kansa.
A nutse ya daga kansa ba tare da fargaba ba. Wani
jibgegen mummunan aljani ya gani mai suffar mikiya ya
yi masa rumfa.
Fuskar aljanin irin ta biri ce, wadda take dauke da wani
ta6a66an hanci, tare da katon baki masu dauke da
manya-manyan hakora kamar kashin guiwa. Haka
idanunsa jajawur kamar wuta ce ke ruri a cikinsu. Haka
kuma fuskar duk a dabai baye take da wani bakin gashi.
Kan aljanin dan karami ne kamar na karamin biri, sai dai
akwau wadansu kahuhhuna guda hudu a jere akai. Yana
da manya-manyan fuka-fukai guda takwas.
Aljanin ya tsuke fuka-fukansa ya dire kasa. Wani
tsamurraran dattijo wanda a kalla ya yi rubda ciki akan
shekaru dari biyu da 'yan kai ya sauko daga kan
tsauntsun tamkar ya sauka daga kan doki, yana fadada

mummunar fuskarsa da wani kodaddan murmushi
wanda shi a ganinsa shi ne murmushin kure adaka,
murmushin da ba kowa zai iya yiwa irinsa ba. Abin da bai
sani ba da ya yi irin wannan murmushin gwara ya fashe
da kuka, domin da kuka da murmushin basu da maraba,
musamman ganin yadda fatar kumatunsa ta tatta6e
tamkar ana nannade Tabarmar karauni.
Jarumin sarkin baiyi wani yunkurin komai ba balle ta kai
da ya yi shirin ko ta kwana, ya dai kurawa halattar
tsamurarran tsohon yana dubansa, yana jiran ya karaso
gareshi dan jin da wacce ya zo.
Ya yin da tsohon ya kusanto gareshi, sai ya ce da shi da
muryarsa da take satar kwaikwayo da kukan dan marakin
saniya.
" An gai da mai shirin zama gwarzo. Na zo na taimaka
maka a wajen cimma burin rayuwar ka."
"bana bukatar temakonka. ! Ka yi gaggawar 6ace mini da
gano!!" ya yi mai tsawa a fusace yana da karkarfar murya
yana nunashi da dan yatsa.
"Ba a sannu dan samari. Ba'a yi min tsawa kuma ba'a
nunani da hannu. Idan na fadi magana ta zauna, dole a
amince da ita. Kuma kaima dole ka kar6i taimakona."
Tsohon ya ce dashi da karkarfar murya.
"karyarka tasha karya gafalallan banza! Baka isa ba, ba ka
kai matsayin da zaka tai maka min bz. Kai! Ba ai wani da
namiji ba, akan burin rayuwata. Zan iya sada zai iya sada
kuntuwar rayuwarka da ajalinta mutukar baka 6ace mini
da gano ba." A fusace yake gaya masa maganar cikin
kunfar baki.
Ya tuntsure da wata karkarfar tsawa.
"Lallai yaro baia san wuta ba sai ya taka! Na san baka san
koni waye ba shi yasa kake gaya min gafalallun
maganganunka kai tsaye ba tare da fargaba ko sha yi ba.
Dan haka zan yi maka afuwa, na san kayi ne bisa
kuskure."
"Bana bukatar a tarihina ace wani ya yi min afuwa bisa
wani kuskure da na yi masa, zan bukaci ya dauki fansa
mutukar zai iya. Ka sani cewa na girmi in yaki karkarfan
sadauki shi kadai, balle gafalallan tsoho da jikinsa ya
gama kasalantuwa, babu kuzari da karfin jiki a tare da shi.
Sadaukantakata ta girmi in kai hannu jikinka da nufin
yaki. Dan haka kaje ga wani sarki ka nemi alfarmagareshi
ya ara maka gayyar rundunonin yaki a kalla mutum sama
da dubu daya ku taho gareni tare da gyara a kai, anan ne
na san zan iya sauraronka da nufin yaki.
Yana gama maganganunsa ya haye dokinsa, ya yi gaba ba
tare da ya dubi tsohon ba. Taku daya, biyu uku, ya yi ya
ga tsohon a gabansa yana masa murmushin mugunta ya
ce, "Dan samari na girmi tunaninkagigin yarinta ya daina
dibanka ga furta gafalallun furci ga maigidanka. Koda ka
ganni tsoho ka yi tunani ka fini tsagwaran sadaukantaka
ko jarumtaka. Ka daina tunanin kana karar da adadin

ragwaye har kana tutiya da alfahariba maza a gabanka, ba
za ka yaki mutun daya ba sai mutun dubu. Da sannu zan
nuna maka yadda tsoho yake dakawa karamin sadauki
gumba a hannu, ya sanya shi yin dana sanin zuwa duniya,
ya sanya shi yin ihun azaba.
Ko kallonsa bai yi ba, ya kada kan dokinsa ya ratse shi zai
wuce. Ya ce da shi, "Ba zan yarda da ka cika kai cikakaen
ne ba sai kazo da adadin runduna da na gaya maka, su
doraka a matsayin gyara, in ya so a nan sai ka nina min
ko kai waye".
Kai yaro ne. Ban zo gareka da nufin na yake ka ko na
hallakar da kai ba, na zo ne domin na taimaka maka bisa
abinda ba zaka iya ta6awa iyawa ba mutukar ban taimaka
maka ba. Domin miliyoyonka sun gaza. Amma kafin nan
zan nuna maka matsyina da na kai. Na shallake tunaninka
da hangenka. Idan ka saduda zan baiyana gareka na sanar
da kai sunana da irin taimakon da zan yi maka."
Ba tare da ya ko kalleshi ba ya kada ya yi gaba tsohon ya
bishi da kallo cikin murmushin mugunta yana girgiza kai.
Sarki Jurhama ya ci gaba da tafiya ba tare da waigo ba. Ya
ma manta da batun wannan tsoho. Saharar da yake tafiya
a kanta ta dau zafi sosai, kishirwa ta dameshi daga shi har
dokinsa, babu ruwa, kuma babu wani tsiro a kan saharar.
Dan haka ya sauka daga kan dokin ya rike linzamin dokin
suka kama tafiya a hankali-a hankali.
Can bai ankara ba sai ji ya yi an fincike linzamin dokin
daga hannunsa. Ya jiyo bayansa a fusace dan ganin wane
mai tsautsayin ne ya aikata wannan babban lefi a gareshi?
Wadansu irin halittu ya ga ni kimanin goma sha biyu
masu mutukar girma tamkar tsauni. Sai gani ya yi guda
ya jefa dokinsa a baki ya yi masa tauna daya ya hadiye,
tamkar dan adama ya sa tsokar nama guda ya lunkuma a
bakinsa, haka halittar nan ta dauki dokin ta lamushe.
A dai-dai lokacin ne ya jiyo dariyar wannan tsohon nan
da ya bayyana a gareshi dazu. Bayan daukewar dariyar
tasa sai ya ce da shi, "ga wani dan abu daga cikin
matsayina sai ka zuba ka gani, su kansu nafi karfinsu
shiyasa nake sarrafasu, wabda ina da tabbacin kaima sun
fi karfinka. Ba ma kai ba, daya daga cikinsu zai iya kifar da
kasa a cikin sa'a daya. Don haka a bada homma mai
burin zama gwarzo". Ya kima budlshe da dariya, saharar
ta kuma amsa amon sautin muryar daryarsa.
Daukewar tasa ta yi dai-dai da surarsa da akai aka
gwarashi a jikon wani abu mai kama da tsini. Aka gara
gwarashi da tsauni a karo na biyu. Anan yaji numfashinsa
ya dauke, bai kuma sanin halin da yake cikin ba.".
Shumar ya bakata a dai-dai nan sakamakon kwankwasa
kofar da yaji ana yi. Nan take shumar ya mike yaje ya
bude kofar sai ga saikon Harayi Baruzul Damsus ya shigo
fuskarsa cike da annuri yana murmushi. Al'amarin da ya
mutukar basu mamaki ke nan gaba dayansu.
Baruzul Damsus ya ce, "kuyi hukuri na katse muku

hanzari, amma naga kun manta da abin da ya kamata ku
fara yi mafi mahimmanci a gareku. Bawani abu bane face
yanke shawara bisa sharadin da na gindaya muku akan
bukatar da kuke son na biya muku. Ku rabu da baiwa
junanku labari ko kuma son jin labarin yadda matata ta
ci amanata. Lallai ina son ku yanke wannan shawara a
tsakanin yau zuwa gobe domin 6ata lokaci a tsakaninmu
na da hadari, saboda nayi bincike na gano cewa saura
kwanaki kadan Sarki Sahibul Hairi ya sami nasarar abin
da ya tafi nema ya dawo gida. Kun ga kuwa idan kuka yi
sakaki har ya dawo baku kawar da Aminul Has ba har
abada burinku ba zai cika ba".
Koda gama fadin haka sai Baruzul Damsus ya nufi jikin
bango ya shafa shi da hannunsa na hagu. Take bangon ya
tsage ya wuce kamar yadda danshi ke tsatstsafowa daga
cikin kasa, ya fice fit daga cikin dakin.
Koda ganin haka sai su Waziri suka sake tsorata da
al'amarin Baruzul Damsus suka shiga sabon tunani
domin sun san cewa abin da ya fada musu gaskiya ne.
Bisa wannan dalili ne daya daga cikinsu cikin tsananin
damuwa ya ce, "Ya kai shugabana mene ne abin yi, shi
zamu aminta da sharadin Baruzul Damsus ne ko kuwa
zamu hakura da bukatar tamu ne gaba daya?."
koda jin wannan tambaya sai Waziri ya yi ajiyar zuciya ya
ce, "Ai tun da muka kawo izuwa wannan matsayi ina
ganin cewa bamu da wani za6i na Baruzul Damsus
Ku tuna cewa matsoraci baya zama gwani har abada.
Haka kuma ita duniya ba'a samunta a banza, shi kuwa
nema kugiya ne ba'a san abin da zai janyo ba sai an
jarraba. Kawai mu karfafi zukatammu mu mika wuya mu
jira muga abin da zai faru".
Gama fadin haka ke da wuya sai farin ciki ya lullu6esu
suka ce, "Tabbas mun gamsu da wannan jawabi naka
bamu da wani haufi a kansa.
Kashe gari da sassafe bayan su Waziri sun yi kalaci sai
Baruzul Damsus ya sa ala sake kai su fadarsa. Da zuwa sai
suka iskeshi cikin mutukar farin ciki tamkar wanda ya
gama cika burinsa na duniya. Ko zama su Waziri ba su yi
ba sai ya dubesu cikin murmushi ya ce, "Na yi murna da
naji kun yanke shawara akan cewa kun amince da
sharadina sabo da haka na urmarceku da ku kama hanya
ku koma birninku na Misra ni kuma zan biyo bayanku
zuwa gobe, ina mai tabbatar muku da cewa a cikin kwana
uku rak! Zan sato Takalmi, Alkyabba da Sandar Aminul
Has na kawo muku. Lallai ku kasance masu cika alkawari
a gareni, odan kuwa ku ka sa6a, ina tabbatar muku da
cewa dayanku ba zai tsira da rayuwarsa ba. Yanzu sai ku
tashi ku yi haramar tafiya na sallameku".
Dajin wannan sai su Waziri suka yi sallama da Baruzul
Damsus cikin murna suka fice daga fadar sannan suka
hau dawakansu suka durfafi birnin Misra.
¤¤¤¤¤¤

A can birnin Misra kuwa, a ranar da wannan al'amari ya
faru ne Aminul Has ya yi wani mummunan mafarki mai
ban tsoro.
A cikin mafarkin nasa an nuna masa wani bakin jaki ya
take mutum ya kashe shi. Faruwar haka ke da wuya sai
jini ya kama zuba daga jikin mutumin ya yi ta kwarara
yana jika gonakai. Nan take duk shukar garin ta kone
kurmus, sakamakon wannan jinin da ya jika kasa.
Cikin rusa ihu da firgicewa Aminul Has ya farka daga
wannan mafarki ya mike zaune zumbur!
Karar da ya yi ne yasa matarsa ta farka, dama tare suke
kwance bisa gado a wannan lokaci. Cikin firgici itama ta
farka. Koda ta fahimci cewa Aminul Hasa ne ya yi mafarki
na ban tsoro sai ta rungumeshi tana shafarsa ta ce, "Ya
kai mijina bani labarin irin mafarkin da kayi".
Ba tare da 6oye komai ba Aminul Has ya zaiyane mata
duk abin da ya gani a cikon mafarkin nasa.
Koda jin haka sai hankalinta ya dugunzuma ainun, tayi
shiru tana tunani da nazari. Daga can sai tai ajiyar zuciya
ta daga kai ta dubeshi ta ce, "Ya kai mijina kayi sani cewa
kakana ya sanar da ni ilimon fassarar mafarki, tabbas
wannan mafarki naka yana nuni da cewa makiyanka suna
nan suna dana maka tarkon yadda za su sami nasarar
hallakaka.
Wannan bakin jaki da ka gani a cikin mafarkin shi ne
makiyinka. Mutumin da ya danne kuma kaine. Wannan
jini da ka gani ya malala gonakai ba komai bane face
zaluncin makiyanka akan jama'ar gari. Shukoki da ka ga
sun kone yana nuna cewa makiyanka za su kwashe duk
arzikin wannan birni su tsiyatar da kowa".
Lokacin da matar Aminul Has ta zo nan a jawabinta sai
hankalinsa ya dugunzuma fiye da ko yaushe har tausayin
jama'a yasa idanunsa suka ciko da kwalla.
Cikin alamun karayar zuciya ya dubeta ya ce, "Ya ke
matata kin sani cewa nayi imani da ke dari bisa dari
domin in ba don taimakon da kika bani ba da tuni yanzu
na dade da mutuwa. Yanzu wacce shawara za ki bani
domin na tsira daga muggan tarkon da wadannan makiya
nawa suka dana mini, ko don sabo da na ceci rayuwar
jama'a da dukiyoyinsu?".
Koda jin wannan magana sai matar Aminul Has tayi shiru
tana tunani har izuwa lokaci mai dan tsaho, sannan ta ce
da shi, "abin da za a yi shi ne, duk abin da ka ga na yi kada
ka tambayeni dalili. Kuma abin da na umarceka da yi ka
yi shi kawai koda kuwa cewa na ce ka shiga cikin wuta
Aminul Has ya kyada kai ya ce, "ai ko cewa za ki yi na
cakawa kaina wuka a ciki ba zan ki ba".
Daga wannan rana Aminul Has ya zuba ido kuma ya kasa
kunne yaji ko matarsa za ta umarceshi da yin wani abu
sa6anin wanda ya saba yi kullum ko kuma ita da kanta za
ta yi wani abun wanda bata saba yi ba, amma shiru,
kamar maye ya ci shirwa har izuwa tsawon kwana uku.

A safiyar kwana na uku ne bayan sarki Aminul Has ya
gama shiri tsaf zai tafi fada sai matarsa ta zo gareshi rike
da wata katuwar jakar fata. Kawai sai ta mika masa jakar
fatar ya kar6i, sannan ta ce da shi, "ya kai mijina kayi sani
cewa ba komai bane a cikin wannan jaka ba face takalmi,
alkyabba da sanda iri daya sak da wanda ke jikinka yanzu
tamkar an tsaga kara babu digon bambanci. Ina son ka
tafi da wannan jaka a sirrince, kafin ka isa fada ka sami
ka6a66en waje ka 6oye jakar inda babu wanda zai gani.
Kada ka taso daga fada sai dare ya soma sannan ka biyo
ta inda ka 6oye wannan jaka ka sauya takalminka,
alkyabbarka da andarka, ma'ana ka sanya na gaskiyar a
jakar ka 6oyesu ka dawo gida sanye da na karyar ka
kwana da su a jikinka".
Koda jon wannan umarni sai Aminul Has ya cika da
mamaki. Har ya bude baki zai tambayi dalilin bashi
wannan umarni sai ya tuno da sharadin da ta kafa masa,
sabo da haka sai yai shiru bai ce komai ba ya kar6i jakar
kawai ya juya ya tafi.
Kamar yadda matar tasa ta umarceshi ya yi hakan ya yi
bai karya ka'ida ba. Wato sarki Aminul Has bai baro fada
ba sai da dare ya yi, kuma ya 6oye ta inda ya 6oye
wannan jaka ya sauya takalminsa, alkyabbarsa da
sandarsa ya nufi gida kai tsaye cikin tsananin tsoro da
fargaba. Gani yake a ko yaushe za a iya hallakashi tun da
baya tare da abubuwa uku da ya gamsu cewa su ne suka
kareshi daga dukkan masifa.
Lokacin da Aminul Has ya shigo cikin turakarsa ya iske
matarsa a zaune akan gado tana jiransa, hankalinta a
tashe sakamakon ganin cewa ya dade da yawa bai dawo
ba.
Koda ta hangoshi sai ta ruga gareshi ta rungumeshi cikim
matukar farin ciki, sannan ya sa bakinta dai-dai kunnensa
tayi masa magana cikin rada ta ce, "idan mun kwanta
muna barci karufe idanun ka kamar kana barcin, amma
kada kayi barcin, kuma kanutsu kaji abinda zai faru a
jikinka. Kai za ma ka iya byde idanunnka kadan domin ka
ga abin da zai faru, amma kada ka kuskura kayi ido biyu
da abin da ya shigo".
Koda gama fadin haka sai ta jashi izuwa kan gado suka
kwanta. Dama kafin su kwanta din ta kashe fitilun
turakar, turakar ya yi duhu dumdum! Ko tafin hannu
mutun ba zai iya gani ba. Nan fa suka yi lamo tamkar
suna barci har ma jan munsharin karya auke yi.
Bayan kamar rabin sa'a da kwanciyarsu sai suka ji wata
irin iska mai sanyi ta buso cikin cikin turakar. Al'amarin
da jefa matukar tsoro ke nan a cikin zukatansa. Amma sai
sukadaure suka ki su motsa jikinsu.
Cikin mutukar karfin hali sarki Aminul Has ya bude
idonsa guda kadan kawai sai ya ga wani abu kamar inuwa
ya ratso bango ya shigo cikin turakar ya tsaya dai-dai
kansa.

Koda abin ya dafa kafarsa sai yaji takalminsa ya cire, abin
ya sake dafa jikinsa da hunnunsa, sai alkyabbarsa ta 6ace,
sandarma da yake ruke da ita sai ta 6ace 6at.
Faruwar haka ke da wuya sai itama inuwar ta 6ace 6at!
Bayan kamar dakika dari da ashirin sai Aminul Has ya ga
matarsa ta mike zumbur! Taje ta kaunna fitilun turakar
haske ya gauraye turakar. Sai gashi kuwa Aminul Has
bayatare da abubuwa uku a jikinsa.
SARKIN SARAKAI
Littafi Na Hudu (4)
Part C.
.
Marubucin littafin
Abdul Aziz sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa
NAN TAKE MATAR
TASA TA BUSHE DA DARIYA SANNAN TA RUNGUMESHI TA
CE, "YA KAImijina, kayi sani cewa gobe kana da
gagarumin yaki a fada, domin a gobe ne za ka ga
makiyinka a fili wadanda suke son su yi maka juyin mulki
su hallakaka.
Abin da na ke so da kai shi ne, ka tashi da duku-dukun
safiya ka tafi izuwa inda ka boye wannan jaka ka sanya
alkyabbar da takalmin, sandar ka wuce kai tsaye izuwa
fada. Duk irin sauyin da za ka gani kada ka ji tsoron
komai, kaje ka zauna a kan karagar mulkinka."
Koda gama jin wannan batu sai Aminul Has ya sumbaci
goshin matarsa ya ce, "madallah da matar da take kaunar
mijinta fiye da uwa take son danta. Hakika kina bina
bashin da ban san yadda zan iya saka miki ba."
Nan take suka sake kashe fitilun tirakar kamar yadda suka
saba kwanciya a kullum, har barci ya kwashe su basu sani
ba.
Da asubar fari zakara ya baiwa Aminul Has sa'a ya tashi ya
yi wanka ya kintsa, ya sanya tufafinsa wanda ya saba
sawaa kullum, sannan ya sulale ya fice daga cikin gidan
sarautar ba tare da kowa ya shaida shi ba.
Kai tsaye ya wuce can cikin wani lambu mai yawan
dogayan bishiyoyi da dogayan ciyayi masu duhuwam
inda ya hoye jakar.
Da shigar Aminul Has lambun sai ya wuce izuwa cikin
wata duhuwa ya bankada ya dauko ajiyarsa. Cikim
hanzari ya bide jakar ya fiddo da sandarsa, takalminsa da
alkyabbarsa. Nan take ya sanya takalminsa da
alkyabbarsa sannan ya dogara sandar ya fice da sauri ya
nufi fada.
Da zuwan Aminul Has fada sai ya cika da mamaki, domin
ya iske kofar cike makil da dakaru, dukkaninsu sun yi
shigar yaki ta musamman, sunyi sahu-sahu biyu.
Aka'ida wadannan dakaru basa fitowa sai bayan sarki ya

iso, amma yau gashi sun riga sarki fitowa.
Nan fa Aminul Has yaji a jikinsa cewa lallai akwai
makarkashiyar da ka killawa amma sai ya dake ya ratsa ta
tsakiyar dakarun ya wuce izuwa cikin fadar.
Koda ya yi nazzarin fiskokin dakarun sai ya gane cewa
basu bane wadanda suka saba tsayawa ba a bakin kofar,
lallai an sauyasu.
Da shigar Aminul Has cikin fadar kuma sai ya ga abin
mamaki. Ba komai ya gani ba face Waziri da dukkanin
mukarrabansa a tsaitsaye cikin shigar yaki sun yiwa fadar
kawanya kimunin su dari daya.
Gaba daya sauran fadawa da barori wadanda suka saba
hidima a fadar babu ko mutum daya daga cikinsu.
Da shigar Aminul Has sai aka yi sauri aka rufe gaba daya
kofofin fadar ya zamana cewa babu ta inda mutun zai iya
fita.
Faruwar hakan ke da wuya sai Waziri da mukarrabansa
suka bushe da dariya gaba dayansu suka yi ta kyalkyalawa
kamar ba za su daina ba.
A wannan lokaci Aminul Has ya tsaya cak! A tsakiyar fadar
yana kallonsu kawai.
Daga can sai suka ga shima ya 6arke da dariyar yana
tayasu. Al'amarin da ya sa suka tsuke nasu bakin ke nan
suka kura masa idanu, domin da farko sun yi tsammanin
ko ya sami ta6in kwakwalwane.
Aminul Has ya daina dariyar sannan ya dubi Waziri cikin
murmushi ya ce, "me kuke nufi dani?".
Koda jin wannan tambaya sai Waziro ya sake bushewa da
dariya a karo na biyu domin ya gane cewa Aminul Has ba
zautuwa ya yi ba
Waziri ya hada fuska sannan ya nuna Aminul Has da
hannu ya ce, "Ya kaia wannan shashashan sarki kayi sani
cewa mun gaji da walakancinka na banza da wofi, wanda
mataccen sarkinmu ya bar maka domin ka takuremu ka
hanamu walwala da jin dadi a cikin mulkinmu. Sabo da
haka yanzun za mu yi maka kisan wulakanci na haye
karagar mulkinka.
Kayi sani cewa tuntuni mun dade muna ta kokarin halaka
ka amma mun kasa sabo da kana tare da abubuwan sihiri
guda uku wadanda suke kareka.
To ka sani cewa a jiya mun sa sarkin 6arayi Baruzul
Damsus ya shiga har cikin turakarka ya sace wadannan
abubuwa guda uku a jikinka kana barci baka sani ba har
ma mun konasu a daren jiya.
Yanzu ta ya za ka iya kare kanka daga mugun kisan da
zamu yi maka?".
Sa'adda Aminul Has yaji wannan batu sai yai murmushi,
sannan dubi Waziri ya ce, "Shin kai makaho ne ko kuwa
mai idanu? Ka dubeni da kyau ka gani, abubuwa ukun
nawa da kuka sa aka sace irin su ne sak a tare da ni yanzu
ko basu bane? Ga sandar a hannuna, da alkyabbata a
jikina, kuma ga takalmina a kafata!

Ina mai sanar da kai cewa kayan da sarkin 6rayi ya sace
mini a jiya da daddare ba su bane na gaskiya ba. Tun a
jiya na cire na gaskiyar na 6oyesu

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment