Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da hankalinki ya ke Alfila kiyi
sani cewa ni da maigidana mun san komao bisa
al'amarinki, kuma akan hakan ne ma muka zo nan fadar
Shmzabul Azwas domin mu sace ki mu kaiki gida ga
abbanki domin muma munada muhimmiyar bukata
wacce muka son ya biya mana".
Koda jin wannan batu sai Alfila tayi murmushi ta ce, "shin
maigidanaka shi ne sarki Sahibul Hairu na Birnin Misra?".
Cikin mamaki Bawa Haluf ya ce, "kwarai kuwa shi ne, ya
ya aki yi kika sani?".
Alfila ta ce, "Ai tuntuni mahaifina ya bani labarinsa da irin
matsalar da ta addabi rayuwarsa cewa bashi da wani buri
wanda yafi ya ga yafi gaba dayan sarakunan duniya
arzuki, daukaka da yawan mata sabo da gorin da sauran
sarakina suke yi masa akan cewa shine mafi talauci da
kaskanci a cikin sarakuna.
Lallai yanzu na aminta da kai don haka sai ka fito da
wadannan kwalabe na nuna maka wadda za kayi amfani
da shi."
Cikin murna da hanzari Bawa Haluf ya fito da sauran
kwalaban daga cikin aljihunsa. Nan take Alfila ta dauki
kwalba da ke dauke da shudin ruwa ta karasa in da su
sarki Sahibul Hairi suke a tsaye jikam cikin suffar gumaka.
Da zuwan ta sai ta bude kwalbar sai ta digawa
kowannensu.
Faruwar haka ke da wuya sai Sarki Sahibul Hairi ya fara
motsawa.
Idanunsa ne suka fara budewa, sannan 'yan yatsunsa na
hannu da na kafafunsa, sannan ragowar jikinsa. Faruwar
haka ke da wuya sai jikin gimbiya Humaira ya motsa gaba
daya.
Koda Humaira ta bude idanun ta sai ta rafka salati.
Al'amarin da ya janyo gaba daya gidan ya kama girgiza

yana rugurgujewa ke nan.
Kwatsam! Sai ga aljani Shamzabul Azwas ya kara bayyana
a gabansu cikin firgici da tsananin mamaki. Ita kuwa
gimbiya Humaira sai ta lazamci karanta wadansu addu'o'i
na musammam bata yadda ta daina ambatonsu.
Ya yin da Shamzabul Azwas ya yi arba da Bawa Haluf sai
ya ciji yatsa cikin tsananin takaici domin ya san cewa
mantuwar da ya yi da shi ita ce babban kuskurensa.
Ita kuwa Alfila sai ta ruga bayan sarki Sahibul Hairi ta
6uya tana mau cewa da shi, "ya kai wannan sadaukin
sarki kada ka bari azzalumi Shamzabul Azwas ya maidani
cikin kwalbarsa ta tsafi, domin kuwa idan hakan ta faru
kaima har abada burinka ba zai ta6a ciki ba."
Koda wannan batu sai Sarki Sahibul Hairi dada kankame
Alfila a bayansa sannan ya zare takobinsa yana mai
fuskantar Shamzabul Azwas.
Shamzabul Azwas ya dubi sarki Sahibul Hairi ya dubi
gimbiya Humaira kawai sai ya bushe da mahaukaciyar
dariya sannan kuma ya murtuke fuskarsa tamkar wnda
aka aikowa da sakon mutuwa ya daka musu tsawa wadda
ta sa suka ji hantar cikinsu ta kada kamar zata fito waje.
Ya ce, "ku kananan sadaukai ku yi sani cewa hakika ku
tsokano tsuliyar dodo, dan haka yau zakuga bala'i da
masifa irin wadda baku ta6a gani ba a rayuwarku. Kun
katse mini aikina a karo na farko alhali na kusa idashi,
nakamaku na sanyaku a cikin tarkona wanda babu wani
mahaluki da ya isa ya ketareshi ya kai labari amma sai
gashi ku yanzu kun tarwatsa tarkon nawa, har ma kun
katse mini aikin nawa a karo na biyu. To ku sani cewa
wannan karon ba wai zan sanyaku a cikin tarko bane sai
dai na zaremuku ruhin numfashinku gaba daya tunda
kun zamo dan hakin da ka raina maitsokane mini ido".
Kafin Shamzabul Azwas ya gama rufe bakinsa sai gimbiya
Humaira ta daka masa tsawa ta ce, "ya kai tsohon
munafikin Allah wanda ya gaji cin amanar Allah da
bayinsa, ka sani cewa kai kana kan hanyar 6ata
mabayyani, ni kuwa ina kanhanyar shiriya kuma a ko
yaushe Allah na tare da bayinsa masu tsoransa da bin
dokokinsa, don haka nasan cewa komai wuya, komai
gumu sai na sami nasara akan ka, don haka sai ka shirya
ga MACE MAI KAMAR MAZA nan bisa kan ka".
Kafin Shamzabul Azwas ya kara mai da martani tuni
Humaira ta falfala da azababban gudu izuwa gareshe,
kawai sai gani ya yi ta daka tsalle guda daya tayi sama ta
dure a gabansa tana mai kawo masa mummunan sara da
nufin ta zarga masa kafada gida biyu. Shamzabul Azwas
ya goce cikin zafin nama, amma duk da haka sai da
takobinta ta zabtare rabin gashin kansa, shi kuwa ya
hantsila gefe daya.
Koda Sha,zabul Azwas ya g rabin gashin kansa a kas, sai
hankalins ya dugunzuma domin tunda ya mallaki wannan
damara ta kugunsa bai ta6a haduwa da wani jarumi ba

wanda ya iya kai masa wannan mugun hari ba face
Humaira.
Cikin tsananin rudewa ya daga rigarsa ya shafa damarar
kugun nasa don yaji wai shin yana tare da ita kuwa.
Ai kuwa sai yaga damarar na nan.
Al'amarin da ya kara furgitardashi kenan ya mie tsaye
zumbur! Ya ja da baya ya gyara tsayiwa sannan ya zare
takobinsa sannan ya fuskanci Humaira.
Koda ganin haka sau Humaira tayi murmushi ta ce, "ya
kai tsohon munafikin Allah kai sani cewa komai na da
lokacinsa.
Tabbas Allah ya ara maka lokaci a baya kayi budurinka ta
hanyar amfani da wannan damara da ke kugunka wacce
ke dauke da sunayansa tsarkaka, to ka sani cewa lokaci ya
kare a yanzu.
A yau sai na hallakaka na rabaka da wannan damara ta
zama tawa domin shi kansa Ubangiji yana kishin
Addininsa da bayinsa, don haka nayi imani cewa sai ya
bani nasara a kanka.
Lallai zai bani karfin da ya fi wanda kake amfani da shi
wajan zaluntar bayinsa, burinka na son ka mallaki
duniyar nan gaba dayanta ba zai taba cika ba."
Koda gama fadin haka sai Humaira ta sake daka taalle irin
na baya ta dire gaban Shamzabul Azwas suka sake
ruguntsimewa da azababban yaki suna masu kaiwa juna
sara da suka cikin mutukar zafin nama, juriya da bajinta
gami da nuna kwarewa.
A duk sa'adda takobin suka sai kaga tartsatsin wuta na
tashi gami da tsawa da walkiya.
Duk wanda aka kaiwa sara ya goce, to fa duk abin da
takobin ta sara sai abin ya dare gida biyu kuma ya kama
da wuta. Nan da nan suka hargitsa fadar gaba daya suka
dugunzuma hankalin duk wani abu mai rai da ke cikinta.
Su kansu su sarki Sahibul Hairi daka tsaye suna kallon
artabun da ake sai da kallon ya gagresu suka kama gujeguje suna neman ma6uya domin ginin ya ci gaba da
rushewa yana fadowa kasa zai dannesu.
Sai da Shanzabul Azwas da Humaira suka shafe sa'a uku
cur! Suna wannan gumurzu ya zamana cewa gini fadar
fadar ya ruguje ya zama fili fetal har ma 6angorin sun
danne sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf da yarinya Alfila
sun kasa tashi, kuma suna ihu suna kiran sunan Humaira
ta kawo musu dauki domin rayuwarsu tana cikin tsaka
mai wuya.
A wannan lokaci Huamaira da Shamzabul Azwas babu
wanda ya sami rauni ko daya a jikinsu, kuma babu mai
nuna almar gajiya a tare da shi, tamkar ma a sannan suka
fara gumurzun.
Koda Humaira ta hango hali da su sarki Sahibul Hairi suke
ciki sai ta fusata ainun ta ci gaba da karanta addu'o'i da ta
fara yi a dazu, sannan ta afkawa Shamzabul Azwas da
dukkan karfinta tana mai kai masa mugun sara da suka.

Wannan karon sai labari yasha banbandomin karfin
saran nata da nauyinsa sai ya ninka na Shamzabul Azwas
sau uku har ta kai cewa baya iya mai da martani kuma da
kyar yake iya kare harin.
Ana cikin haka ne da ta kawo masa wannan sara a ka ya
kare da takobinsa sai da ya durkuahe kasa bisa
gwiwoyinsa. Take takobinsa da tata suka rabe gida bibiyu.
Karfin saran ya sa Shamzabul Azwas ya fadi kasa ya
mirgina baya sau uku, sannan ya mike zaune zumbur! A
lokaci guda duk su biyun suka dubi gutsiran takobin da
ke hannunsu suka yi jifa da su. Kawai sai Shamzabul
Azwas ya mike tsaye yana murmushin mugunta sannan
ya dunkule yatsun hannunsa yana shirin a fara
gumurzuwa da hannu. A tunaninsa ya tabbatar da cewa
ya fi Humaira karfin dantse, don haka dolene wannan
karan ya gama da ita.
Koda Humaira ta gane nufin Shamzabul Azwas sai ita ma
ta dunkule yatsun hannunta ta daga hannayen sama tayi
shirin fara dambe, kuma ta ci gaba da karanta Addu'o'i a
cikin zuciyarta. Shamzabul Azwas ya falfalo da gudun
tsiya irin nasu na aljanu tamkar walkiya izuwa gareta ya
kawo mata wawan naushi a fuska kawai sai yaga ta kare
naushin da hannunta. Koda hannunsa da nata suka hadu
sai yaji kamar nasa hannayan za su rugurguje, ba shiri ya
juya da baya zai kare amma sai ta damko wuyansa da
hannun daya ta daga shi sama tamkar ta dau jariri ta
fyada da kasa sannan ta kuma dau kansa da hannu biyu
ta cillashi sama kamar takarada. Shamzabul Azwas ya
fado kan rusassun tubalin gini a galabaice. Kafin ya sami
damar mikewa Humaira ta bayyana tsulum a gabansa ta
tallafo kansa da hannunta na hagu sannan ta dinga gabza
masa lugude naushi a fuskarsa da hannunta na dama.
Nan da nan ta hada masa jini da majina ta sauyawa
fuakarsa kamanni. Nan take Shamzabul Azwas ya sume,
Humaira ta sakeshi sai ya baje a kas tamkar gawa.
Kawai sai ta sunkuya tana mai karanta Bismillah, ta
kwance wannan damara daga kugunsa mai dauke da
sunayen Allah tsarkaka ta daura a kugunta. Gama hakan
ke da wuya sai ta ruga wajan su Sarki Sahibul Hairi domin
ta ceci rayuwarsu.
Gunguma-gunguman tobalin dutse ne ya danne su sarki
Sahibul Hairi wanda inda karti goma za su taru baza su
iya dagashi ba, amma sai ga Humaira tana dauke tubalan
duwatsun tana wurgi da su can gefe daya. Cikin dakika
kadan ta zaro sarki Sahibul Hairi, Alfila da Bawa Haluf sai
suka tsandara ihu sabo da abin da suka hango a bayanta.
Kafin Humaira ta juya taga abin da yake tahowa tuni
Shamzabul Azwas ya soka mata wani dogon mashi a
gadon bayanta. Mashin ya faso ta cikinta. Bisa mamaki sai
Humaira ta ga babu ko digon jini da ya zuba daga jikinta
sakamakon wannan mashin da ya tsira ma ta. Humaira ta
juya tafuskanci Shamzabul Azwas ta ga ya tsaya cak! Yana

kallonta cikin tsananin mamaki, nan take Humaira ta sa
hannunta ta zare mashin daga cikinta sai gashi sai gashi
ramin da mashin ya yi a jikinta sai gashi ya 6ace 6at! Ko
alamar rauni babu a wajan.
Humaira tasa hannunta biyu ta lankwasa mashin duk da
cewa an yishi da karfe mai kwari da kauri, amma sai gashi
ta kanannadeshi ta cureshi waje daya tamkar an daka
fura a turmi, sannan tayi jifa da shi.
Koda ganin wannan abin al'ajabi sai Shamzabul Azwas ya
juya da sauri da nufin ya gudu amma sai Humaira ta sake
cafo wuyansa. Wannan karon da ta daga shi sama sai da
ta yi filfilwa da shi sannan ta fyadashi da kasa ta sa kafarta
guda ta take wuyansa sai gashi yana kakarin mutuwa, jini
na zuba ta hancinsa da bakinsa.
Allah sarkin iko, yanzu in ba Allah ba wazai iya bawa
Bil'adama irin wannan gagarumin karfi wanda zai iya yin
fada da aljani har ya sami nasara akansa.
Lokacin da aljani Shamzabul Azwas ya fara wannan
kakarin mutuwa sai ya dubi humaira cikin karfin hali
sannan ya bushe da dariya. Al'amarin da ya mutukar bata
mamaki ke nan ta daga kafarta daga kan wuyansa sabo
da tasan bashi da wani kuzarin da zai iya yin komai.
Koda Shamzabul Azwas ya yi tari sai ga gudan jini ya fado
daga bakinsa mai kauri tamkar hantar cikinsa ce ta fado.
A wannan lokaci idanunsa sunyi jawaur babu kyan gani
tamkar wutace ke ruri a cikinsa.
Shamzabul Azwas ya bude baki dakar ya dubi Humaira ya
ce, ya ke wannan 'yar sarki, ki sani cewa koda kin sami
nasarar hallakani to fa baku isa ku fita daga cikin gidan
nan ba a raye, idan ma kum fita har abada burin dayanku
ba zai ta6a cika ba. Ke na sani cewa so kike addinin
musulinci ya bazu ko ina a duniya ya danne sauran
addinai? To ki sani cewa munyi mummunar 6arna a
boron kasa, kadan ne daga cikin mutane da aljanu za su
baka goyan baya.
Kai kuma sarki Sahibul Hairi kayi sani cewa burinka bazai
ta6a cika ba na shahara da daukaka feye da sauran
sarakunan duniya face ka auri wadannan 'yan mata uku
da aka yi maka da aka yi mka bayanin su tun da farko.
Idan kuwa kana tare da wannan ma 'abociyar addinin
musulincin har abada bazaka ta6a haduwa da wadannan
'yammata ba koda kuwa ka kai Alfila wajan mahaifinta ya
tai maka maka ku tafi neman 'yan matan. Shawarar da
zan baka ita ce duk yadda zakai kayi ka rabu da ita domin
burinka ya cika, ina ba haka ba kuqa duk wahalar da ka
sha a baya zata zamo ta banza.
Koda gama fadin haka sai Humaira ta fusata ta sake take
wuyan Shamzabul Azwas ya ci gada da kakarin mutuwa.
Kafin cikar dakika dari ya daina motse, komai na jikinsa
ya sandare.
Faruwar hakan ke da wuya sai gidan gaba daya ya fara
nutsewa izuwa karkashin kasa.

Cikin tsananin zafin nama Humaira ta goya Alfila ta kama
hannun Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf tana mai kiran
sunayan Allah tsarkaka. Kawai sai ji tayi an yi sama da ita,
a lokacin da gidan ya ci gaba da nutsewa izuwa cikin kasa.
Hakika abin al'ajabi baya karewa a duniya. Humaira na
dauke da su Sarki Sahibul Hairi a cikin iska sai su kaji an
tsai da su cak! Don haka sai suka kallo kas suna ganin
yadda fadar Shamzabul Azwas ke ci gaba da nutsewa
izuwa cikin kasa. sai da fadar ta gama nutsewa kaf sannan
kasar wajen ta koma ta hade tayi lebur tamkkar wani abu
bai ta6a faruwa ba a wajen.
A sannan ne su Humaira suka ji an sakko da su kas a
hankali sun dire bisa turba. Nan take Humaira ta yi wa
Allah godiya bisa wannan tai mako da ya bata ta sami
nasara akan azzalumi Shamzabul Azwas wanda ya dade
yana cutar da musulmi a doran kasa. Bayan ta kammala
wannan godiya ga Allah sai ta juya ta dubi Sarki Sahibul
Hairi, da Bawa Haluf da yarinya Alfila ta ce, "to yanzu ku
ganau ne ba hiyau ba, hakika kunga iko da isa irin na
Ubangijina bisa yadda ya bani gagarumin karfi na hallaka
boka Shamzabul Azwas, kuma sannan ya tserar da
rayuwarmu daga cikin fadarsa.
Wannan ya isa hujja a gareku wacce za ta sa kuyi imani
cewa babu wani sarki da ya cann canta a bauta masa face
Ubangijin Musulinci kuma shi ne kadai mai yin dud abin
da ya so. Arziki da Talauci duk nasa ne. Rayuwa da
mutuwa na hannunsa, shi ne mai mayar da sarki ya zama
bawa, kuma ya daukaka bawa ya zama sarki. Idan har
kun gamsu da bayanina ina son a yanzu take ku kar6i
addinina mai daraja.
Koda jin wannan batu sai hankalin Sarki Sahibul Hairi ya
dugunzuma ainun yana tunowa da wasiyar da Boka
Shamzabul Azwas ya yi masa kafin Humaira ta hallakashi
cewar muddin yana tare da Humaira har adaba burinsa
ba zai cika ba.
Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf da Yarinya Alfila suka
kurawa Humaira idanu aka rasa wanda zai ce da ita kala.
Koda ganin haka sai Humaira tayi murmushi sannan ta
dubi Sarki Sahibul Hairi ta ce, "ya kai wannan sarki mai
babban buri, kayi sani cewa musannan sabo da kai na
baro kasata na yia wannan tafiya bisa umarnin mahaifina
dan na sanyaka bisa tafarkin gaskiya, don ha lallai sai ka
ce wani abu a yanzu in a haka ba kuwa zan datse maka
dukkan shirinka bisa neman biyana bukatarka".
Lokacin da Humaira tazo nan a zancenta sai sarki Sahibul
Hairi ya yi ajiyar zuciya gami da gyaran murya sannan ya
dubeta ya ce, "ya ke wannan jaruma mai abin mamaki,
kiyi sani cewa hakika akwai dumbin abin al'ajabi a cikin
lamarun Ubangijinki, to amma duk da haka ina bukatar
dan lokaci ka domin na yanke hukunci a cikin zuciyata.
Ina son son ki bani dama mu isa birnin su Alfila domin in
dankata a hannun mahaifinta. Na yi miki alkawari lallai a

sannan ne zan kar6i addininki. To amma wane alkawari
za ki yi mini cewa nima nawa burin zai ciki?.
Sa'adda Gimbya Humaira taji wannan tambaya sai tayi
murmushi ta ce, "ya kai wannan sarki kayi sani cewa,
duniya, mulki da mata da kake son ka mallaka fiye da
kowa ba komai bane a wajen Ubangijin musulinci, domin
da ya so zai iya baka kamarsu cikin duniya sau ba adadi
domin da duniyar da duk abin da ke cikinta da wanda ke
wajanta shi ke da ikonsa.
Na yarda na amince da duk sharadin da ka zo dashi,
kuma kuma zan yi hakuri mu isa har garin su Alfila. Ina
mai sanar maka da cewa ko a yanzu ka kar6i addini
musulinci to zamu roki Ubangijin musulunci da ya cika
maka birinka cikin gaggawa ba tare da ka sha wata
wahala ba.
Ina gargadarka da kada ka dauki Shawarar wannan
fandararran Boka Shamzabul Azwas gafalalle, domin
bazata kai ka ko ina ba face izuwa ga halaka. Lallai kayi
tunani kuma kayi hattara. Ka sani cewa tsalle daya mutun
yake ya fada rijiya."koda gama wannan jawabi sai
Gimbiya Humaira ta juya baya ta ci gaba da tafiya tana
mai cewa, "ku biyoni mu tafi, domin akwai dogon zango
a gabanmu".
Ba tare da gardamar ko mai ba kuwa su ukun suka bita a
baya suka nufi inda suke tsammanin cewa za su ga
aljanin da yya kawosu wannan wuri.
Wannan shi ne abin da ya faru ga su Sarki Sahibul Hairi
bayan san sami nasarar shiga fadar Boka Shamzabul
Azwas sun hallakashu kuma sun dauko yarinya Alfila.
.SARKIN SARAKAIA
Littafi Na Huɗu (4)
Part B.
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa
A CAN BIRNIN MISRA KUWA, LOKACIN DA SU WAZIRI
SUKA ISA WAJAN ABINDOGARONSU kuwa, wato boka
suka sanar da shi duk irin abin da ya faru tsakaninsu da
dokin Aminul Has sai ya cika da tsananin mamaki yai
shiru ya shiga tunani.
Daga can kawai sai ya runtse idanunsa ya shiga karanta
wadansu dalasiman tsafi. Yana cikin haka ne awani irin
turaren hayaki ya fara fitowa ta ckin kunnuwansa, nana
take ya kwala ihu ya daina karanta dalasiman tsafin.
Al'amarin da ya mutukar furgita su Waziri ke nan su kaji
kamar su tashi su ruga da gudu amma sai suka yi ta
maza.
A sannan ne bokan ya dubi Waziri ya ce, "ya shugabana ai
babu yadda za a yi ka sami nasarar hallaka Aminul Has

face anyi abu guda. Dole ne ka tura a sato awannan
takalmi da yake sanyawa kullum a kafarsa wanda ko barci
zai yi baya cireshi, sannan a sato tsohuwar Alkebbassa
wadda ya ke sawa kullum a jikinsa da kuma sanda da
yake dogarawa kullum.
Ku sani cewa irin sihirin da yake jikin wannan Doki nasa
da ya gagareku kamuwa shi ne a jokin wadannan
abubuwan uku nasa. Da zarar kun sani nasarar rabashi da
wadannan abubuwa uku tolallai zaku iya hallakashi a
kowane lokaci".
Sa'adda su Waziri suka gama jin wannan jawabi sai
Hanlalinsu ya dugunzuma suka rasa abin da ke musu dadi
domin sun san cewa sato wadannan abubuwa uku daidai yake da tafiya ne man jiki mai kaho tun da de dare da
rana sarki Aminul Has na tare da su sannan kuma akwai
kyakkyawan tsaro na dakaru a cikin gidan sarautar don
haka basu san yadda za a yi ba a shiga har cikin turakar
Aminul Has a sato abubuwan uku.
Bayan su Waziri sun yi nazarin maganar boka sun yi
tunani akan al'amarin sai dukkaninsu suka rasa abin
cewa. Daga can sai Waziri ya dubi bola ya ce, "ya kai abin
dogaranmu kayi sani cewa mu kammu ba mu ga
mahalukin da zai iya sato wadannan abubuwa uku ba
sabo da haka wannnan bukata tafi karfimmu sai dai mu
hakura gaba daya, in ya so mu yi hijira mu bar garin
domin ba zamu iya ci gaba da zama ba muna ganin abin
takaici".
Ya yin da boka yaji wannan batu sai ya bushe da dariya.
Al'amarin da ya baiwa su Waziri mamaki ke nan. Daga
can kuma sai bokan ya hada rai ya ce, "ya ku wadannan
sarakai kuyi sani cewa akwai mani shahararran
kungurmin 6arawo a birnin kisra wanda zai iya wannan
aiki ana kiransa da suna Baruzul Damsus.
Ina tabbatar muku da cewa wannan 6arawon yana da
karfin Sihiri mutuka kuma a halin yanzu duk duniya babu
wani 6arawo da da ya fishi kwarewa da sa'a kan sata,
domin yafi shekaru arba'in yana sata amma ko sau daya
bai ta6a haduwa ba da 6acin rana ko rashin sa'a.
Ina mai shawartarku da ku gaggauta zuwa can Birnin
Kisra ku gana da wannan 6arawo. Amma ku tabbata kun
tafi da Durhami mai ya wan gaske, domin aikinsa na da
mutukar tsada, idan attajiri bai bunkasa ba farat! Daya
yake talautashi. Asalin Baruzul Damsus baya harka da
kananan Attajirai da kananan sarakai sai wandanda suka
gawurta a duniya".
Lokacin da Boka ya zo nan a zancensa sai Waziri ya bushe
da dariyar farin ciki ya ce, "ai wannan abu ne mai sauki,
domin idan so yake na shimfida Durhami a ko ina a cikin
8irni Kisra ya zamo abin takawar jama'a zan iya yin
hakan".
Nan take Waziri ya yiwa boka sallama sannan ya kawo
zinare guda dari ya bashi suka tafi suka barshi.

Kashegari kuwa tun da duku-dukun safiya Waziri tare da
magoya bayansa mutum biyu suka ya shirin kama hanya
suka nufi birnin Kisra
Lokacin da suka isa birnin suna tambayar gidan 6arawo
Baruzul Damsus aka sa su akan hanya domin gidan ba
6oyayye bane amma a karshen gari yake. Tafiyar rabin
sa'a suka yi kacal suka isa kofar gidan. Da zuwa sai suka
iske gaba daya kofofin gidan a bude suke kuma babu
masu gadi a kofar gidan, sannan duk inda suka duba basa
ganin komai face buhunhuna cike da lu'u-lu'u, da zinare,
jahurma da sauransu. Kai har a kasa ma an zubar da
wannan dukiya ga ta nan birjik! Ga ta nan birjik ba adadi
sai mutun ya takata da kafafuwansa sannan zai iya shiga
gidan. Al'amarin da ya baiwa su Waziri mamaki ke nan
suka tambayi kansu a cikin zuciyoyinsu cewa Baruzul
Damsus ba ya tsoran wasu 6arayin su zo su yashe shi ne?
Amsar da suka baiwa kansu ita ce, "ai kura ta san gidan
mai babbar sanda."
Nan dai su Waziri suka ja linzamin dawakansu suka tsaya
cak! A kofar gidan kamar masu jiran a basu umarni.
Kwatsam! Sai suka ji an bushe da mahaukaciyar dariya
amma kuma ba su ga mai yin dariyar ba. Daga can kuma
sai aka daina yin dariyar aka ce, "lale marhaban da
manyan sarakai daga birnin Misra, ku yi sani cewa na
dade ina jiran wannan rana da zaku kawo mini wannan
babbar ziyara sabo da haka ku manyan baki ne masu
mutukar mahimmanci a gareni.
Na umarceku da ku shiga gidan nawa, domin mu gana".
Koda ji wannan batu sai farin ciki ya lullube su Waziri
suka sauko daga kan dawakansu suka dauresu, sanna
suka kunna kai izuwa cikin gidan. Sai da suka yi 'yar
doguwar tafiya sannan suka isa wata kasaitacciyar fada ta
gaban kwatance wadda ko fadar sarkin birnin Kisran bata
kai ta ba a kyau da tsaruwa. Kuyangi da barori na tai
kawo a cikin fadar suna ta hidima. Can kuma ga wani
mutunnan zaune akan wata kasaitacciyar karagar mulki
ta kasita 6arawo Baruzul Damsus ne fuskarsa cike da
annuri, a gabansa an ajiye wani tebur cikie da kayan
abinci da na sha iri-iri.
Koda shi gowar su Waziri sai Baruzul Damsus ya mike
tsaye da kansa ya tarbesu yana mai rungume Waziri cikin
mutukar farin ciki kamar wanda ya ga babban amininsa,
bayan dan lokaci sai ya janye jikinsa daga cikin na Waziri,
sannan ya jasu inda karagar mulkin tasa take ya zaunar
da su kuma ya yi musu tayi abincin da ke gabansu. Ba
tare da gardamar komai ba suka hau kintsawa har sai da
suka ji sun gamsu amma basu cinye kaso daya ba cikin
kaso goma na abincin da ke gabansu.
Lokacin da 6arawo Baruzul Damsus ya ga su Waziri sun
sami nutsuwa sai yai gyaran murya sannan ya dubi Waziri
ya ce, "na san cewa baku zo gareni domin komai ba sai
domin na yi muku gagarumin aiki na sato takalmi da

Alkebba da sanda na Sarki Aminul Has, ko ba haka bane?
Cikin tsananin mamaki duk su ukun suka bude baki suka
ce, "tabbas maganarka dutse ce".
Damsus ya yi murmushi sannan ya ce, "hakika wannan
aiki da kuka zo min dashi na san dashi fiye da shekara
goma baya kuma na san cewa duk ranar da Sarki Sahibul
Hairi ya bar ksarsa za ku zo gareni, domin aikin, inaso ku
sani cewa wannan aikin yana da mutukar hadari, dole ne
cikin biyu ayi daya. Ko dai ayi nasara ko dai na rasa
rayuwata. Lallai zanyu wannan aiki, amma bisa sharadi
guda.
Shadin kuwa shi ne, idan har na sami nasara kammala
aikin da zarar kun hau kan karagar mulki zaku raba
dukiyar birnin Misra kaf biyu ku bani kaso guda. Wannan
shi ne babban burina a duniya."
Koda jin haka sai su Waziri suka yi tsuru-tsuru da idanu
suka cika da tsananin mamaki.
Daga can sai waziri yayi ajiyar zuciya ya ce, "ya kai
wannan kungurmin 6arawo, kayi sani cewa kazo mana da
babban al'amari sabo da haka akwai bukatar muyi
shawara."
Koda jin haka sai Baruzul Damsus ya yi murmushi ya ce,
"na baku kwana biyu kuyi shawara. Yanzu zan sa a kaiku
masaukinku dan ku huta sosai".
Gama fadin haka ke da wuya sai Damsus ya kira wata
kuyanga ya umarceta da ta kai su Waziri masauki.
Nan take su Waziri suka mike tsaye suka wanke
hannayansu da ruwa sakamakon abincin da suka ci.
Sannan suka bi bayan kuyangar izuwa masauki.
Da shigarsu cikin wannan katon daki wanda aka
kawatashi da gadaje da shinfidu na alfarma sai suka cika
da tsananin mamaki, suka tabbatar da cewa ba a cikin
karamar daula suke ba.
Cikin su6utar baki daya daga cikin su ya ce, "hakika kai
gidannan ba karamin attajiri bane. Ai ko a gidan sarautar
birnin Hindu bana jin akwai dakin da yakawatu kamar
wannan".
Koda jin wannan batu sai kuyangar tai murmushi ta ce,
"ai in ba dan matarsa ta ci amanarsa ba ta gudu da rabin
dukiyarsa da sai in ce da ku bana tsammaninza a sami
wani mutun guda daya mai karfin arziki tamkarsa a
duniya".
Koda jin wannan batu sai Waziri ya dubi kuyangar cikin
kaduwa

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment