Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da suka shafe awa uku cur suna dauki back dadi
dayansu bai sami nasarar koda kwarzanar daya ba. A daidai lokacin ne Sarki Sahibul Hairi, Bawa Haluf, Gwaggwan
birin da Alfila suka gama kashe gaba dayan halittun.
Koda suka hango mugun artabu da akeyi tsakanin
Humaira da Sarki Barusa sai hankalinsu ya dugunzuma
ainun.
Nan take sai Sarki Sahibul Hairi ya ce "ya kamata
mukaiwa Humaira dauki domin Ina ganin cewa bazata iya
hallaka Sarki Barusa back".
Koda jin haka sai Bawa Haluf ya dubi sarki Sahibul Hairi
cikin damuwa ya ce, "ya shugabana shin kamanta
Humaira ta gargademu da cewar Kada mukuskura mutari
sarki Barusa idan ana wannan gagarunin yaki? Ai kawai
muci gaba da zuba ido domin muga abin da zai faru".
Koda jin haka sai sarki Sahibul Hairi ya zauna kasa
durshan ya city gaba da ganin artabun Humaira da sarki
Barusa. Alfila kuwa sai ta ci gaba da zamanta akan
wannan doguwar bishiya.
Ya yin da sarki Barusa da Humaira suka ga sun shafe
wannan lokaci suna kaiwa juna sara da suka ba tare da
samun nasarar komai ba sai suka ja da baya suka yi
carko-carko kamar zakaru sun haki da kallon juna.
Tsawon 'yan dakika suna tsaye a haka sai sarki Barusa ya
fara amfani da karfin tsafi ya watsowa Humaira
garwashin wuta mai yawa. Kafin garwashin wutar ya zuba
a jikinta tuni ta kama karanta wadansu addu'o'i na
musamman na neman tsari.
Duo garwashin da ya ta6a jikinta sai ka ga Kamar a cikin
ruwa ya fada.
Nan take garwashin wutar zai mutu ya fado kasa a jike.
koda ganin haka sai ya sake yin wani tsafin ya watsa ma ta
6angorin kankara mai tsananin sanyi.
Duka kankarar da ta ta6a jikinta sai ta narke ta zama
ruwa mai dumi.
Haka dai sarki Barusa ya yi ta jefawa Humaira mugayan
abubuwa iri-iri har kala Dari ba daya amma bai sami
nasar komai ba.

Al'amarin da ya mutukar fusatashi Kenyan ya kara
kwarara uban ihu a karo na uku sannan ya yi jifa da
takobin hannunsa ya gyara tsayuwarsa gami da dunkule
hannayansa yana mai nuni da su.
Koda ganin haka sai itama Humaira ta gyara tsayuwarta
Kumar ta dunkule hannayanta.
Sarki Barusa ya dubi Humaira ya yi murmushi ya ce,
"idan ina son na tabbatar da ce wa za ki yi wan an
gumurzu ne zallan karfin dantsenki said dai ki cire
wannan damara da me kugunki saboda na San cewa
darajarta ne kika iya samun Laguna".
Koda jin haka sai Humaira ta sa hannu zata kwance
damarar da ke kugunta.
Cikin tsawa sarki Sahibul Hairi yace da ita, "kada kiyi
hakan.
Lallai sarki Barusa yana son ya yaudareki ne ya sami
nasara akanki.
Idan har yana ganin damarar ce abin dogaranki me yasa
shima bai mallaki damarar ba? ai kar6ar wannan damara
a hannun mai ita sai cikakken jarumi mai sadaukantaka
ta ban al'ajabi".
Humaira ta kalli Sarki Barusa cikin murmushi ta ce, "kaji
abin da sarki Sahibul Hairi ya fadi, me zaka iya cawa?"
Sarki Barusa ya bushe da dariya sannan ya ce, "ai bada
tsagwaran karfin damtsanki kika kar6i damarar ba a
hannun Shamzabul Azwas face kin yi amfani da Marfin
sihiri irin naku na ma'abota addinin musulinci.
Humaira ta ce, "ai mu bama da wani sihiri face taimakon
Ubangijimmu."
Barusa ya ce, "haka dai kika ce, amma ban yarda ba. idan
Ubangijin naki ne yake baki sa'a ki cire damarar mana na
gain".
Kafin sarki Barusa ya gama rufe bakinsa tuni Humaira ta
kwance damarar daga kugunta ta ajiyeta gefe daya.
Nan take ta shiga kiran sunayan Allah tsarkaka a cikin
zuciyarta tana mai Neman taimakon Ubangiji".
Koda sarki Barusa ya ga Humaira ta kwance wannan
damarar ta ajiye a gefe daya sai ya bushe da dariyar farin
ciki, sannan ya ruga gareta da dukkan karfinsa cikin
mugun nufi. Ita Kuwa ta tsaya cak tana jiran karasowarsa
harya iso kusa da ita ko gezau ba ta yi ba.
Sarki Barusa ya kawo mata wawan naushi a fuska da
dukkan karfinsa. Ko kaucewa bata yi ba, Hannun nasa na
naushin fuskarta sai yaji kamar dutse ya nausa, kuma yaji
kamar 'yan yatsun hannunsa sun karye.
Basan sa'adda yayi kara ba gami da yarfar da hannu ya ja
da baya cikin tsananin mamaki da firgici.
Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf , Alfiya da ke can gefe
daya suma kallo suma sai da suka cika da tsananin
mamaki bisa ganin abin da ya faru.
Jaruma Humaira ta kalli Sarki Barusa cikin murmushi ta
ce, "yanzu gashi na ajiye damarar da kake tunanin da ita

nake dogaro kuma na sami sama da karfin da nake da
shi. Sirrin shi ne, na karanta addu'ar da keep jikin
wannan damara ne na naimi taimakon Ubangijina.
Ita kuwa wannan addu'a ba komai bace face wadansu
ke6antattun sunaye tsarkaka na Ubangiji wadan da
bakowa ne ya san su ba.
Idan kayi imani da abin da name fada yanzu ka tuba ka
daina shirka da tsafi ka kar6i addinina kuma mukoma
kasarka ka kaddamar da addinin nawa ga jama'arka Idan
kuwa ka ki ni da kai babu sauran sulhu sai dai mu ci gaba
da yaki har dayammu ya ga bayan daya.
Koda jaruma Humaira tazo nan a zancenta sai sarki
Barusa ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya
tur6ne fuska ya ce, "Ai ni tsakanina da ma'abota addinin
musulunci sai yaki.
Ina son kisani cewa iyaye na da kakannina duk sun shude
bisa tafarkin tsafi don haka babu wani dan zamani da ya
isa ya gusar dani daga kanwannan tafarki na iyayena
wanda nai imani da shi dari bisa dari.
Dan haka ga maza nan bisa kanki yarinya komai
shaidancinki sai naga bayanki".
Koda gama fadin haka sai sarki Barusa ya durkusa ya
dauki takobinsa ya tafi izuwa kan jaruma Humaira yana
wani irin ihuda ruri mai firgitarwa.
Hatta kasar wajan sai da ta kama motsi kamar zata rufta.
Tsuntsaye da ke sama kan bishiyoyin kuwa suka kama yin
hijira.
Wannan abu kuwa ya daurewa such sarki Sahibul Hairi
kai shi ne, Jaruma Humaira dai ko motsi ma batayiba
bare ma ta Naomi takobinta ta dauka amma bakinta na
ta motsi alamar cewa tana karanta addu'ointa.
Ai kuwa sarki Barusa na isowa daf da ita sai ya kai mata
wawan sara a weya da nufin ya tsage mata kai, cikin zafin
nama ta kare saran da hannunta.
Take takobin ta 6alle gida biyu, al'amarin da ya mutukar
razana sarki Barbuda ke nan ya juya da baya da sauri
domin ya ruga da gudu, amma sai Jaruma Humaira ta
shako wiyansa ta baya da hannu biyu tayi hajijiya da shi
sannan ta dagashi sama tayi filfilwa da shi ta kwala da
kasa.
Sarki Barusa ya baje a kasa a lokacin da yaga taurarin
wuya a idanunsa kuma jiri ya kwashe shi ya yunkura da
nufin ya mike tsaye amma sai ya Ji ya kasa. Humaira ta
kafarta guda ta take wuyan sarki Barusa.
Nan take ya fara kakarin mutuwa, wani irin jini ya fara
fitowa ta cikin kofofin hancinsa.
Koda ganin halin da sarki Barusa ya shiga sai Humaira ta
fara jin tausayinsa ya dan darsu a zuciyarta, dan haka sai
ta dan durkusar da kanta kasa dai-dai fuskarsa ta ce, "ya
kai wannan sarki, idan har za ka yi imani da Ubangijina a
yanzu zan Dauke kafata data kan wuyanka domin ka ray.
Koda jin wannan batu sai sarki Barusa ya tofawa Humaira

jinin bakinsa ya dubeta cikin tsananin kiyayya da fushi ya
ce, "Had abada ba zan kaunaci addininki ba domin na
tsaneshi fiye da yarda na tsani mutuwata.
Kawai ki kashe ni shi ne abin da zai fiye miki alheri domin
ba zan ta6a daina adawa da Ku ba har na mutu zan
kasance a cikin tunanin kawar da addininku".
Koda jin wannan batu sai zuciyar Humaira ta kama
tafarfasa kamar zata kone ta dubi sarki Barusa taga ya yi
mata muni tamkar dodo, kawai sai ta kama kansa da
hannayanta biyu ta murde masa wuya.
Sai da karar karyawar ta cika dajin gaba daya.
Nan take sarki Barusa ya zama gawa ko motsi bai kara yi
ba.
Humaira ta mike ta nufi inda sarki Sahibul Hairi da Bawa
Haluf suke tsaye a lokacin da suka kura mata idanu suna
yi mata jinjina bisa ganin gagarumar bajinta da tayi ta
ban al'ajabi.
A dai-dai wannan lokacine yarinya Alfila ta sakko daga
kan wannan doguwar bishiyar da ta hau. Humaira na
isowa daf da su sai ta tsaya ta dubi sarki Sahibul Hairi ta
ce, "yanzu mun rage daya daga cikin manyan abokan
gabarmu saura guda daya wanda yafi kowanne hadari"
Cikin mutukar mamaki sarki Sahibul Haiti ya dubi Jaruma
Humaira ya ce, "wanene Kuwa wanda ya fi sarki Barusa a
garemu?"
Humaira tayi murmushi ta ce, " ba wani bane face
matarsa Gimbiya Shukura.
Ka sani cewa ita mace ce Kuma bata da burin da ya fi a
yanzu ta illa ta mallaki yarinya Alfila domin ta hada sihirin
da za ta iya mallakar duniya.
Tabbas sai munyi da gaske wajan kula da Alfila domin
nasan cewa a ko yaushe Gimbiya Shukura zata iya
shammatarmu, ta zo ta saceta.
yanzu dai babu abin da ya kamacemu face mu hanzarta
kai Alfila wajen mahaifinta domain na kawo karshen
tafiyata da ku.
Koda gama jin haka sai Jaruma Humaira taji sarki Sahibul
Hairi ya kirawo sunanta.
Cikin mamaki itama ta juyo ta dubeshi, sarki Sahibul Hairi
ya ce, "kin manta da waccan Damarar".
Koda jin haka sai Humaira ta dubi can inda Damarar take
sannan ta dubi Alfila ta ce, "ya ke 'year uwata maza ki
ruga inda Damarar take ki daukota muci gaba da tafiya".
Cikin hanzari kuwa Alfila ta ruga da gudu taje ta dauko
wannan Damara ta kawowa Humaira tana mai mika
mata.
Humaira bata kar6i damarar ba sai ta dubi Alfila ta ce,
"daura a kugunki tunda kema yanzu kina da ikon
daurawata tun da kema musulmace".
Ba tare da gardamar komai ba kuwa Alfila ta daura
Damarar a jikinta.
Faruwar haka ke da wuya sai Alfila taji wani irin

gagarumin karfi ya shigeta kamar zata iya daga gammo
tayi dakon duniyar gaba daya amma sai tayi shiru da
bakinta bata fadawa kowa sauyin yanayin da taji ba.
Nan fa aka ci gaba da tafiya ba sassauci, domin tun kafin
a fara tafiyar Humaira ta gayawa sarki Sahibul Hairi da
Bawa Haluf cewa su tabbatar da cewa sun bita sahu da
sahu, duk inda ta dauke kafarta to su sa ta su.
Ai kuwa ba su yi sanya ba said suka dinga binta sau da
Kafa. Humaira ta ci gaba da tafiya tana mai karanta
wadansu addu'o'i na musamman, nan da nan su sarki
Sahibul Hairi suka ga tafiyar ta su tana mutukar sauri
tamkar a sama suke yinta bisa aljani saboda gani suke
suna ta gifta dazuzzuka Tamar walkiya.
Nan da nan suka sun shafe tafiyar sa'a bakyai a rabin sa'a.
Tun safe suka fara tafiya, amma basa tsayawa face idan
lokacin sallah ya yi.
Sannan Humaira da Alfila suka yi Alwala suka gabatar da
sallah sai suka ci gaba da tafiya.
Bisa mamaki sai suka ga har sun gifta ta manyan
garuruwa guda biyu.
Daf sallar magariba suka isa birnin su Alfila.
Koda Alfila ta fara hango gine-ginen garunsu sai farin ciki
mara misaltuwa kuma ta cika da mamaki yadda aka yi
suka shafe wannan doguwar tafiya.
Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf kuwa dama tun sa'adda
suka ga yadda Humaira ta sami nasara akan sarki Barusa
sai suka tsinke da al'amarinta kuma suka Jim zuciyoyinsu
sun fara gamsuwa da gaskiyar addininta gamma saboda
burin da ke zuciyarsu bass son su yi saurin nuna yardarsu
don Kara burin nasu ya tarwatse.
Da isowar su Humaira kofar garin sai suka iske kofar a
kulle, masu gadi kimanin dakaru arba'in na tsaitsaye a
bakin kofar birnin sun yi shirin yaki kowannansu na rike
da makami sai muzurai suke kamar za su ci babu.
Da yake Humaira ce a kangaba sai ta dubi masu gadin ta
ce, da su "ku bude mana kofa mu shiga birnin ku, mu
bakine na salama kuma mun zo muku da alheri".
Koda jin haka sai shugaban dakarun wani narkeken kato
mai kirar mutanan farko ya dubi Humaira ya ce, "Sarkin
mu bamamu umarni kada mubudewa bako kofa ya
shigo.
Wannan karamar yarinya da Luke tare da ita kadai zamu
iya budewa ta shiga domin itace 'yar gari".
Sa'adda Humaira taji wannan batu sai ranta ya 6aci,
kawai sai ta juya ta kalli Alfila ta ce, "ya ke 'yar uwata jeki
ciki ki sadu da mahaifinki, ki bashi labarinmu in ya so shi
yazo ya shigar damu cikin birnin naku idan sarkin naku
ya bashi izini".
Alfila ta yi murmushi ta ce, "angama ya 'yer uwata".
Koda fadin haka said masu gadin kofar suka bude kofar,
Alfila ta shiga ciki tana ta waigen Humaira kamar zata yi
kuka, kai da gani kasan ba a son ranta aka yi haka ba, taso

a ce anbar such Humaira sun shigo cikin
garin gaba daya. Alfila na shiga cikin birnin sai masu gadi
suka mai da kofa suka rude.
A lokacin Humaira da sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf
suka raka6e a gefe daya suka zauna domin su huta a
lokacin ne hira ta fara wakana tsakanin sarki Sahibul Hairi
da Humaira inda ta dubeshi ta ce, "Amma fa nayi
mamakin irin wannan doka. Akan wana dalili sarkin
wannan gari zai kafa dokar cewar baki baza su shiga
garinsa ba.
sarki Sahibul Hairi ya yi ajiyar zuciya ya ce, "ni kaina na yi
mamakin wannan al'amari, amma babu mamaki akwai
mugun abu da wani bakon ya zo ya yi, kin san ance wake
daya 6ata gari, babu mamaki wani bakon ne ya shafa
mana kashin kaji."SARKIN SARAKAI
Littafi Na Biyar (5)
Part B.
.
Marubucin littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa..
HUMAIRA TA YI AJIYAR ZUCIYA SANNAN TAYI SHIRU NA
DAN WASU DAKIKOKI KADAN SANNAN TA CE, " YA KAI
WANNAN SARKI SHIN HARYANZU BAKA YANKE SHAWARA
BANE a zuciyarka bisa kar6ar addinina?
Ka sani cewa nifa na gaji yin wannan tafiya tare da ku, in
da back don ina kwadayin in ga ka kar6i musulinci ba da
tuni mun rabu.
Ba komai ne yasa kaga ina so ka sami wannan babban
rabo ba face saboda naga cewa kai adalin mutunne mai
tausayi da jin kan talakawa Kuma kasar ka ta kunshi
muliyoyin al'umma. Idan ka kar6i addinin musulinci
tamkar muliyoyin jama'a sun kar6i addinin ne.
Sa'adda Humaira ta zo nan a zancenta sai sarki Sahibul
Hairi yai ajiyar zuciya gami da Sunkui da kansa kai sannan
ya dago ya dubeta cikin alamun tsananin dimuwa ya ce,
"ya ke wannan jaruma mai karamci da ban al'ajabi kiyi
sani cewa na sha bakar wahala tun daga lokacin da na
baro kasata har name gamu da ke kawo i yanzu kuma
gashi har yanzu abin da na fito dominsa ban samu ba
Zuciyata ta kwadaitu da son ganin 'yammata ukun da aka
ce sai na auresu sannan burina zai cika.
Yanzu gashi har nazo garin su sadauki Awaisu wanda
shine kadai mutumin da zai iya kai ni inda wadannan 'yan
mata uku suke.
Yanzu fa idan na kar6i addininki shi ke nan ba zan ta6a
ganin wadannan 'yan mata ba har abada.
Saboda me zan bar wannan dama ta wuceni alhali aski ya
zo gaban goshi saura kiris ya kammalu".
Sa'adda jaruma Humaira taji wannan batu sai takaici ya

kamata, zuciyarta ta yi bakikkirin nan take taji tayi
nadamar biyo sarki Sahibul Hairi tun daga kasarta domin
Jan hankalinsa izuwa addinin musulinci tun da gashi har
yanzu ya ki kar6ar addinin duk da cewar ya ga abubuwan
al'ajabi na gas gata Allah".
Cikin tsananin fushi Humaira ta kalli sarki Sahibul Hairi ta
ce, "Ai shi ke nan ni dai na gama cika nawa aikin kuma
lallai a yau ne zan rabu da Ku.
Abin da ya tsai dani kawai a nan shi ne, na tabbatar cewa
Alfila ta sadu da mahaifinta kuma ina kwadayin na ga
mahaifin Alfila shima ya kar6i addinin musulinci kamar
yadda 'yar sa ta kar6a.
Lallai zan so na gana da shi domain naga inda ra'ayinsa ya
karkata.
Idan har sadauki Awaisu ya kar6i addinin musulinci, sarki
garin nan ma zai iya kar6a, idan kuwa sarki ya kar6a
tamkar mutanan birnin ne gaba daya ne suka kar6a.
Wannan shi ne iyakar Burina".
Koda jin wannan batu sai hankalin sarki Sahibul Hairi ya
dugunzuma yai shiru ya rasa abinda zai ce da Humaira,
ya sunkwi da kansa kasa yana tunani.
Babban abin da yasa hankalinsa ya tashi shi ne, jin cewar
a yau ne Humaira zata rabu da shi.
Nan take sarki Sahibul Hairi ya ji kamar ya fashe da kuka
domin kauna da bergen Humaira ne ya taso masa ya cika
masa zuciya, kuma ya rasa abin da ke masa dadi.
Shima Bawa Haluf sai ya ji ya kamu da tsananin damuwa
kamar roki Humaira akan ta ci gaba da zama tare da su
har izuwa lokacin da maigidansa zai cika burinsa, amma
sai ya kura ma ta idanu kawai ya kasa cewa komai.
Ya yin da Humaira taga Bawa Haluf ya kura mata idanu
sai ta daka masa harara ta ce, "kai kuma fa lafiya ka kura
mini ido haka? ko kuwa baka ta6a ganina bane sai yau".
Koda jin wannan tambaya sai Bawa Haluf ya yi murmushi
ya ce, "ki gafarcene ya shugabata wani Abu na tuno
wanda me da sarkina kuka manta da shi."
Cikin mutukar mamaki Humaira ta ce, "wana abu ke
nan"?
Bawa Haluf ya ce, batun goggon birin da ya taimaka
mana a yakin da mukayi da sarki Barusa.
Tun sa'adda muka gama yakin bamu sake ganinsa ba,
kuma dayanmu baiyi zancensa ba. shin an kasheshine a
wajan yakin ko kuwa sulalewa ya yi yayi tafiyarsa bamu
sani ba ko ya ya?"
Koda jin wannan batu sai Humaira da sarki Sahibil Hairi
suka kalli junansu cikin tsananin mamaki sannan sarki
Sahibul Hairi ya ce, "Hakika Haluf maganarka gaskiyace,
domin duk mun sha'afa mun manta da batun wannan
biri, amma ni a tunanina wannan birin ya mutu domin
kuwa inda yana raye bazai daina biyomu ba, said dai idan
ya koma wajan 'yan uwan sa inda ya fito".
Humaira tayi ajiyar zuciya ta ce, "ai wannan biri bazai

koma inda ya fito ba, domin idan ya koma wajansu
kasheshi zasuyi tunda sun san cewa ya za6imu a Kansu.
Ni dai abinda nake zargi shine, lallai an kasheshi a lokacin
da Mike wannan yaki amma Kuma abin mamakin shi ne
bamu ga gawarsa ba a wajan".
Koda gama fadin haka sai Humaira ta kashingida saboda
gajiya tayi shiru bata kara cewa komai ba.
Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka yi shiru basu kara
cewa uffan ba.
WANNAN SHI NE ABIN DA YA FARU GA SU SARKI SAHIBUL
HAIRI BAYAN DA JARUMA HUMAIRA TA KAWOSU GARIN
SU ALFILA A CIKIN KANKANIN LOKACI BISA TAIMAKON
ALLAH.
Al'amarin yarinya Alfila kuwa, lokacin da aka bude mata
kofar garinsu ta shiga sai ta nufi izuwa hanyar gidan
mahaifinta sadauki Awaisu cikin farin ciki tana dokin ta
isa ta sadu da shi.
A sanin Alfila daga bakin kofar garin zuwa gidansu
tafiyace ta a kalla sa'a uku, amma bisa mamaki sai taga ta
share tafiyar a cikin abin da wuce wadansu 'yan dakiku
ba. Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki ke nan.
Abin da ta manta shine, wannan damara ta Shamzabul
Azwas tana nan a daure a kugunta.
Sa'adda Alfila ta isa kofar gidan mahaifinta sai ta iske
gidan a kulle kuma dakarun sarki sama da mutum dubu
sun kewaye gidan sai muzurai Duke.
Al'amarin da ya mutukar bata mamaki ke nan, jikinta ya
yi sanyi, kuma hankalinta ya duguzuma ainun.
Alfila ta karasa da sauri zawa ga dakarun ta Dubi daya
daga cikinsu ta ce, "mene ne yake faruwa ne, ina
mahaifina?"
Koda jin wannan tambaya sai badakaren nan ya dubeta
cikin tsananin tausayi ya ce, "ya ke Alfila ai tunda aka
saceki mahaifinki ya kamu da rashin lafiya saboda bakin
cikin rabuwa da me da sanin cewa bazai iya zuwa inda
kike ba ya Kar6oki.
Bisa wannan dalili ne ya kwanta rashin lafiya kullum sai
dai a kwantar a tayar. Babu irin kokarin da 'yan uwansa
basu yi ba na nema masa magani amma abun sai ya ci
tura.
Kinsan cewa mahaifinki shine sarkin ya ki a garin nan
kuma sarki na mutukar kaunarsa bisa hakanne sarki yasa
aka daukeshi aka kaishi can gidan sarauta domin ya yi
jinyarsa da kansa kuma ya umarcemu da muyi gadin
gidan naku saboda kin san cewa akwai tarin sirrikan
tsafinsa a cikin gidan Wanda duk duniya babu kamarsu.
an ce ke kadai kike da irin sirrikan tsafin a jikinki"
Lokacin wannan badakare ya so nan a zancansa sai
hankalin hankalin alfila ya dugunzuma fiye da ko yaushe,
nan take hawaye ya zubo mata, tai shiru tana tunani.
Babban abinda ya tayar mata da hankali shi ne, a iya
saninta da mahaifinta bai ta6a zuwa gidan sarki ba.

Koda yaki za'a fita sai dai a tura a gaya masa ya shirya ya
taho a hadu da shi a filin daga.
Asalin sadauki Awaisu shima dan gidan sarauta ne kuma
ubansu daya da sarkin garin, amma ko kadan shi baya
sha'awar harkokin sarauta.
A rayuwar sadauki Awaisu shi ba shi da wani buri wanda
yafi ya gawurta a harkokin tsafi da jarumta a duniya,
amma ko kadan dukiya da mulki basa gabansa.
Sarkin garin da sadauki Awaisu su kadai ne 'ya 'ya a wajan
mahaifinsu, amma awaisu ne babba tun mahaifinsu yana
da rai Awaisu ta ce shi bazaiyi sarauta ba ya barwa dan
uwansa kuma tun daga sannan ya hada nasa i nasa ya bar
gidan sarautar ya gina nasa a can bayan gari ya tare.
A wannan lokaci mahaifiyar Alfila na dauke da cikin Alfila.
A ranar da ta haifi Alfila ne ta mutu.
Alfila ta taso bata San kowa ba sai mahaifinta da kuma
hadimansa.
Sa'adda ta fara girma ne ya bata labarin mahaifiyarta da
kuma labarin dangantakarsa da gidan sarauta.
Koda sau daya bai ta6a daukarta ya kaita gidan sarautar
kuma shi sarki ba a garin bai ta6a zuwa gadansu ba a
matsayin ya kawo ziyara ga dan uwansa
Wata rana Alfila ta dubi mahaifinta Sadauki Awaisu ta ce,
"ya abbana ka gaya mini cewa sarkin garin nan dan
uwanka ne to me yasa baka zuwa wajansa shi ma baya
zuwa wajanka?"
Lokacin da yaji wannan tambaya sai ya sunkwi da kansa
kasa ya yi shiru kamar banzai ce komai ba, sannan ya yi
ajiyar zuciya ya dago ya dubi Alfila ya ce, "ya ke 'yata abar
soyuwa a cikin raina kiyi sani duk ranar da naje gidan
sarki ko kuma shi yazo gidana to daga wannan rana sai
daya data cikinmu ya rasa matsayinsa. ko dai ni na rasa
dukkan sihirin tsafina ko kuma shi sarki ya rasa mulkinsa.
Sa'adda Alfil ta zo dai-dai nan a tunaninta said zuciyarta
ta buga da karfi, domin tasan dolane cikin biyu dolene ayi
daya.
Ko dai mahaifinta ya rasa dukkani. sihirin tsafinsa ko
Kuma sarki ya rasa karagarasa.
Nan take taji bata gamsu da bayanin da wannan
badarakare ya yi ma ta ba sabo da haka sai ta juya da
gudu ta nufi hanyar da za ta kai ta gidan sarautar garin.
Nan da nan kuwa Alfila ta isa kofar gidan sarautar.
Da zuwa sai ta iske mahaifin ta tsaye a kofar gidan idanun
sa sharkaf da hawaye ya kura mata idanu.
Al'amarin da ya mutukar girgizata Ke nan ta cika da
tsananin mamaki ta tsaya cak! daga nesa suna kallan juna
tace a ranta, "ya ya mutunin da aka ce da ita yana kwance
magashiyan bashi da lafiya kuma gashi yanzu a tsaye a
gabanta bisa duga-dugansa. Kuma ina dalilin zubar da
wannan hawayen a idanunsa ko kuwa name farin cikin
ganinta ne?
Alfila ta tambayi kanta a cikin zuciyarta kuma ta kasa

baiwa kanta amsa.
Koda Sadauki Awaisu yaga Alfila ta tsaya a nesa ta ki
karasowa gareshi sai ya durkusa bisa gwiwoyinsa ya bude
hanyansa ya ce, "Rugo gareni ya ke 'yata na ji ki a kirjina
ashe zamu sake saduwa a wannan duniya?.
Rugo gareni ya ke rabin jikina, rabin ruhina Kuma
cikamakin Burkina".
Koda jin haka sai Alfila ta ruga da gudu saboda ta San
cewa mahaifinta ne kadai yake mata irin wannan furuci.
Sai da ya rage saura kiris ta isa gareshi sai taga ya 6ace
daga inda yake durkushe ya bayyana a bayanta yana mai
kyalkyala dariya.
Al'amarin da ya mutukar firgita Alfila ke nan ta juya a
tsorace ta dubi Awaisu ta ce, "wanene kai ina mahaifina
take?"
Koda jin wannan tambaya sai Awaisu ya rikide koma
gimbiya Shukura matar sarki Barusa tana kyalkyala
dariya.
Daga can kuma sai ta murtuke fuska ta dakawa Alfila
tsawa ta ce, "ke yarinya kiyi sani cewa rayuwar mahaifinki
da ta dan uwnsa duk suna hannuna
Idan kina so su tsira da rayuwarsu to ki big dukkanin
umarnina.
Ki sani cewa a halin yanzu mulkin wannan gari a hannuna
yake domin nazo na yaki garin nan gaba daya ni kadai na
ci su da yaki".
koda jin wannan batu sai Alfila ta tsandara ihu ta ce, "ya
ke wannan hatsabibiya ki sani cewa karyarki ta sha karya
domin baki isa kiya yaki da mahaifina ba har ki cishi da
yaki domain duk abinda kike takama da shi ya Fiji."
Shukura ta bushe da dariya sannan ta hade fuska ta ce,
"Ai ba fito na fito mukayi da shi ba, kamar yadda na
yaudareki a yanzu haka na yaudari Kowa a garin nan na ci
su da yaki.
Yanzun nan zan nuna miki halin da mahaifinki yake ciki.
Idan kika bi umarnina ya ku6uta, Idan kuwa kika bijire
mini ya hallaka.
Koda gama fadin haka sai sukura wuce izuwa cikin gidan
sarautar, Dakaru suka rinka ratsewa suna bata hanya
cikin dari-dari.
Alfila ta bita a baya har suka shiga cikin turakar sarki.
Babu abinda ya daurewa Alfila kai face yadda daya
Dakarun gidan hadimai ki ta ratsewa shukura cikin
girmamawa tamkar itace sarkin birnin.
Alfila ta tambayi kanta cikin zuciyarta ta ce, "wai shin
gimbiya shukura da karfin tsiya ta kar6i birnin ne ko
kuwa da karfin sihiri?"
Amsar da ta kasa baiwa kanta ke nan.
Da shigarsu cikin turakar sai Alfiya tayi arba da
mahaifinta sadauki Awaisu kwance akan gado an
daureshi tamau da wata irin sarkar tsafi wacce ta
kanannade jikin gaba daya tana ta zagayeshi.

A 6angaren kudancin dagon da yake wani gadon ne
daban sarkin garin na kwance shima an daureshi tamau
da irin wannan sarka.
Koda shukura tayi nuni da hannunta izuwa kan sadauki
Awaisu sai sarkar tsafin ta daureshi tamau ya kwalla ihu
sakamakon zafin da yaji tamkar kasusuwan jikinsa za su
kakkarye.
Gimbiya shukura ta bushe da dariyar mugunta ita kuwa
Alfila ta ruga da gudu izuwa kan mahaifinta ta
rungumeshi kuma ta fashe da kuka tana mai duban
shukura ta ce, "ya ke

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment