Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kama labe labe
yana tunanin hanyar da ya kamata yabi yaje inda aka
ajiye gatarin sihirin inda matsalar take shi bai san a ina

aka ajiye gatarin sihirin ba haka dai ya ci gaba da labewa
a cikin wani sako mai duhu yana tunani a lokacin da
hadimai da dakarun gidan sarautar ke kai komo wasu
mata gabansa suke wucewa amma basu ganshi ba.
**
wannan shine abinda ya faru ga sarki sahibul hairi bayan
ya sha bakar wahala a cikin gidan halaka wanda ke
karkashin kasa a masarautar sarki barusa
++
++ ++ ++ ++
ACAN BIRNIN MISRA KUWA kashe gari da sassafe fada ta
cika makil da jama a tare da dukkan fadawan sarki kowa
ya zuba idanu yana jiran fitowar sabon sarki wato mai
rikon karaga AMINUL HAS.
don aga yadda zai tafiyar da nasa tsarin mulkin ana cikin
wannan haline aka hango shi a tafe shi kadai a bayansa
kafarsa sanye da wadansu tsofaffin takalma wadanda
saboda tsufa har sun fara lalacewa sannan kuma yana
rike da wata tsohuwar sanda itama duk ta fara
farfashewa rigar dake jikinsa ma ba wata mai kyau bace
rigace irin wadda kowanne irin talaka zai iya sawa
.
Koda ganain Aminul has a cikin wannan shiga sai su
waziri suka shiga duban junansu suka fara dariyar farin
ciki jama ar gari kuwa sai suka cika da dumbin mamaki
suka kurawa aminul has idanu a lokacin da jama a suka
dare suka bashi hanya ya nufi kan karagar mulki dama a
wannan lokaci kowa a tsaitsaye yake har saida aminul has
ya zauna a kan karaga sannan fadawa suka zazzauna a
mazaunansu suma mutanan gari sai kowa ya nemi wuri
ya zauna take fadar tayi tsit kamar mutuwa ta gifta
.
Cikin nutsuwa sarki aminul has ya mike tsaye ya dubi
jama arsa cikin fara a da walwala yace yaku jama ar
birnin misra kuyi sani cewa adalin sarkinku wato sarki
sahibul hairi wanda yai tafiya bai tafi ba yana nan
.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama kowa da kowa
fadar ta sake rude wa da hayaniyar jama ah koda ganin
haka sai Aminul has ya daga hannu aka yi tsit sannan yace
nasan kun shiga rudani bisa jin abinda na fada yanzu to
amma abin da na ke nufi anan shine sarki ya tafi amma ni
wakilinsa ne duk irin mulkin da yasaba yi akansa zanci
gaba ba zan sauya komai ba
.
Ban yarda mai mulki ko wani attajiri ya zalunci talaka ba
duk mutumin da yayi laifi za a hukuntashi kamar yadda
za a hukunta kowa da kowa.
Sa adda jama a sukaji wannan batu sai suka barke da
shewa suna tafi kowa ka dubi fuskarsa sai kaga ta cika da
annuri amma ban da ragowar fadawa su waziri Akiyanu
wadanda suka murtuke fuskokinsa sai muzurai suke

kamar zasu fashe da kuka don bakin ciki musamman
waziri Akiyanu ji yayi kamar ya tashi yaje ya soke aminul
has da takobi yayi juyin mulki nan take
.
Sarki aminul has yaci gaba da bayani yana mai tabbatar
da cewa za aci gaba da yiwa jama a adalci da kuma
taimakon marasa shi haka dai yayi ta bayanai har ma
yana kirkiro sababbin abubuwa don farantawa talakawa
haka dai taro ya watse kowa yana farin ciki aminul has ya
mike tsaye ya shiga cikin gidan sarauta inda ya wuce kai
tsaye izuwa cikin turakar sarki sahibul hairi.
Da shigarsa cikin turakar sai ya iske matarsa shulaiba
zaune a gefen gadon taci ado fuskarta cike da annuri ya
yinda ta dago kai suka dubi juna sai kowannansu ya
Kama murmushi saboda tsananin farin ciki aminul has ya
matsa gareta ya zauna daf da ita sannan ya ajiye sandarsa
akan gadon a gefe daya koda ya sunkuya da nufin ya cire
takalman kafarsa sai tayi wuf ta tare hannayansa tace A
kul ka cire wadannan takalma lallai dasu zaka yi barci
akan wannan gado mai Albarka.
Yayinda Aminul has yaji wannan batu sai yayi murmushi
yace ki gafarceni yake abar kaunata hakika na sha afa da
dokokin da kika shimfida mini bisa wadannan takalma da
kuma wannan sandar amma ba komai bane ya haddasa
hakan ba face tsananin farin ciki kasancewar yau ne
zamu shafe dare daya daga cikin dare sittin na farin ciki
akan wannan gado na sarauta
.
Yayinda shulaiba taji wannan batu sai tayi dariya sannan
ta mike tsaye taje ta rufe kofar turakar ta kuma kashe
gaba dayan fitilun dake cikin turakar dakin yayi duhu
matuka yadda ko tafin hannu mutum ya daga ba zai iya
ganiba.
++ ++ ++
Al amarin waziri Akiyanu kuwa sai suka kasa tashi daga
filin fadar saboda tsabar bakin ciki ya zamana cewa kowa
ya watse an barsu a zaune su kadai a cikin fadar har dare
ya raba basu koma gidajensu ba sai da suka tabbatar da
cewa babu kowa a cikin fadar sai su kadai a lokacin ma
masu gadin kofar fadar sunrufe kofa sannan suka fara
tattaunawa akan yadda zasu ga bayan sarki Aminul has.
Waziri akiyanu ne ya fara magana yace yaku yan uwana
yan majalisa kun gani kuma kunji abubuwan da babban
makiyinmu ya fada lallai ya zama wajibi muyi saurin
kawai dashi in ba haka ba kuwa gaba dayanmu zamu
wulakanta sai mun kaskanta a idon talakawa saimun
talauce mun zama abin tausayi
.
Yayinda yan majalisa sukaji wannan batu na Akiyanu sai
duk sukayi shiri aka rasa wanda zai ce kala daga can sai
tsoho kilzam yayi gyaran murya yace yakai waziri Akiyanu
kayi sani cewa dolene a dawo kan maganata ta farko

wato dolene mu yiwa aminul has juyin mulki a dare daya
idan ba hali kawai muje mu kashe shi yanzu yanzu a cikin
wannan dare
.
Waziri Akiyanu yayi murmushi yace kai kuwa dadina
dakai kenan ka cika gaggawa na yarda da shawararka
cewa mu sa a kashe shi a cikin darennan amma ba mu da
kanmu za muyi wannan aiki ba domin aikin ne mai
hadari manufa ta anan inda bamuci nasara ba asirinmu
zai tonu a hallaka mu amma idan wasu muka sa sukayi
wannan aiki kome za ayi musu ba zasu fadi cewa mune
muka sasu ba
.
Abinda za ayi kawai shine yanzu idan muka bar nan zan
tura a kirawo mini manyan yarana amintattu bakwai
wadanda zasuyi wannan aiki a gobe da daddare ina
tabbatar muku da cewar sai dai a wayi gari sarki ya mutu
kun san kuwa yana mutuwa nine zan hau karaga kasa ta
zama tamu
.
Koda jin wannan batu sai gaba dayansu suka bushe da
dariyar mugunta dariyar da suke ce masu gadin kofar
fadar suka jiyo suka fahimci cewa akwai mutane a ciki
dan haka sai suka rugo da gudu suka bude kofar suka
haska fitilu koda sukayi arba dasu waziri akiyanu sai suka
zube kasa suka kwashi gaisuwa nan dai su waziri Akiyanu
suka tarwatse kowa ya tafi gidansa cikin farin cikin
muguntar da suka kulla.
.
Lokacin da waziri Akiyanu ya isa gida sai ya tsaya cikin
wani babban falonsa inda ya saba ganawa da jama arsa
ya zauna nan take ya kira wani bawanda mai suna JAMASI
ya umarceshi daya hau doki a cikin wannan dare ya tafi
izuwa gidajen wadansu barade su uku musabu, Akaifu da
samar yace ya gaya musu cewa suzo yanzu yanzu yana
son ganinsu a gidansa cikin rawar jiki jamusi ya fita daga
cikin falon ya tafi cika umarni
.
waziri akiyanu na nan zaune a falonsa har tsawon kusan
rabin sa a sai ga musabu da akaifu da samar sun bayyana
kamar wadanda aka jefosu daga sama cikin biyayya su
duka suka zube kasa gaban waziri Akiyanu suka kwashi
gaisuwa.
Su dai wadannan barade uku sune manyan mayakan
birnin misra wadanda sarki sahibul hairi ke takama dasu
domin duk sa adda zai bita yaki sune suke take masa baya
kasancewar waziri akiyanu mai dukiyane saiya dinga siye
zuciyoyinsu da abin duniya ya zamana cewa yana yi
musu kyauta da alheri mai yawa fiye da tunaninsu su
kansu sun dade suna mamakin dalilin da yasa yake musu
wannan alheri bisa dalilin haka ne suke matukar yi masa
biyayya duk abinda ya umarcesu dayi ba zasu ketara ba A

zahirin gaskiya ba wani abu bane yasa yake musu alheri
ba face tanadin irin wannan rana wacce ya san cewa ko
ba dade ko bajima zatazo amfaninsu zai taso.
.
Bayan su barde musabu sun gama kwasar gaisuwa ga
waziri akiyanu sai ya dubesu cikin murmushi da
girmamawa ya yi musu izinin zama akan kujeru na
alfarma ba tare da gardamar komai ba kuwa suka zauna
cikin nutsuwa ya sake dubansu yace yaku wadannan
zaratan jarumai kuma dirkokin misra ina mai mika
godiyata gareku da kuka amsa wannan gayyata tawa ta
bazata kuma a cikin wannan dare na san zakuyi mamaki
matuka to amma idan kuka dubi sabon yanayin da muka
shiga na mulkin kasar nan bai kamata kuyi mamaki ba ku
duka kun sani cewa sarkinmu yayi gagarumar tafiya mai
tsananin hadari da kowa ya san ba zai taba dawowa ba
hakane ko ba hakaba!?
.
Gaba dayansu ukun suka amsa da cewa wannan haka ne
gaskiya kam Waziri Akiyanu yayi murmushi sannan yaci
gaba da cewa a halin yanzu galadima Aminul has ne
sarkinmu maimakon ace nine na hau karagar mulkin.
Ina tabbatar muku da cewa idan yaci gaba da mulkinmu
ba zan iya ci gaba da muku alherin da na saba yi muku ba
domin kuwa zan talauce na zama fakiri..
Abinda nake so daku shine ku bani hadin kai mu kawar
da gwamnatin Aminul has mu kafa tamu idan har mukayi
nasarar hakan nayi muku alkawarin zan sanyaku a cikin
manyan yan majalisata kuma na baku dukiya mai yawa
irin wacce baku taba mallaka ba a rayuwarku idan aka
sami akasi akan wannan aiki to kada ku kuskura ku fada
sunana domin kun san illar da hakan zata iya haifarwa ina
mai dada tabbatar muku da cewa dani da sauran yan
majalisa duk bakinmu daya muna da goyon bayansu dari
bisa dari
.
Lokacinda su barde musabu suka ji wannan jawabi daga
bakin waziri sai duk suka bushe da dariya a lokaci guda
kamar hadin baki Al amarin da ya bashi mamaki kenan
musabu ya dubi Akiyanu cikin nutsuwa yace ya
shugabana kayi sani cewa yadda muka yarda da kanmu
ko sarki sahibul hairi kace mu yiwa juyin mulki zamu iya
bare galadima Aminul has wanda bashi da jarumtaka
kuma bashi da karfin sihiri na kare kansa muna tabbatar
maka da cewa cire silin gashi daga cikin tandun mai yafi
wannan aiki wuya a daren gobe zamu je har cikin turakar
sarki mu kashe shi salin alin ba tare da kowa ya ganmu ba
hatta iyalansa kuwa
.
Cikin mamaki waziri akiyanu ya dubi musabu yace tayaya
zaku iya wannan aiki alhalin ciki da wajen gidan sarautar
a zagaye yake da dakaru masu tsaro dare da rana

musabu ya sake yin dariya shi kadai a karo na biyu yace
ai kowa akan aikinsa sarki ne wannan aikinmu ne ba naka
ba.
Don haka ka kyalemu muyi aikinmu kawai sai dai akwai
wani hanzari ba gudu ba'
waziri akiyanu ya zazzaro ido yace wanne hanzari ne
daku?
Musabu yace duk da cewa wannan aiki mai sauki ne a
wajanmu amma hadarinsa na da matukar yawa dalilina
anan shine koda bayan ka zama sarki ne idan bisa
tsautsayi wani ya ganmu a sa adda muke wannan aiki tofa
sai sirrinmu ya tonu har abada jama aba zasuga kimarmu
ba da mutuncinmu ba sbd haka ba zamu fara wannan
aiki ba face ka bamu dukiya mai yawan gaske ta kimanin
rakuma dari dari da shanu hamsin hamsin da kuma
gonakai goma goma
.
Koda jin wannan batu sai waziri ya bushe da dariyar farin
ciki har da tafa hannaye sannan yace gobe da safe zan
dankawa kowannenku wannan dukiya a hannunsa idan
aka wayi gari na samu labari cewa galadima ya mutu zam
kara muku rubi uku na wannan dukiya yayinda su barde
musabu sukaji wannan lafazi sai suka cika da murna nan
take suka yiwa waziri sallama suka tafi.
Kamar yadda waziri akiyanu ya yi alkawari haka al amarin
ya kasance wato kashe gari da safe ya sake turawa aka
kirasu baradan uku ya basu wannan dukiya su kuwa suka
tafi suka zauna suna ta shirye shiryen yadda zasu sami
nasara bisa wannan gagarumin aiki dake gabansu
.
Lokacin da dare ya fara rabawa sai musabu Akaifu da
samar sukayi wata irin shiga ta bad da kama gaba
dayansu bakaken kaya suka sa sama da kasa suka fufe
fuskokinsu da babaken rawani ya zamana cewa idanunsu
kadai ake gani hatta kufen takubbansu da kakalminsu
bakake ne bayan sun gama wannan kimtsi sai suka nufi
gidan sarautar yayinda suka isa daf da gidan sai suka
hada hannayansu waje guda sukayi kawanya faruwar
hakan keda wuya sai ga wata guguwa ta zagayesu
guguwar ta suresu a sama ta rika yin katantanwa dasu
nan take suka rikide suka zama guguwar ta bace dasu
bat !!
A can cikin gidan sarauta kuwa yaune dare na biyu ga
sarki Aminul has tare da matarsa da samun wannan
kwanciya yin barci a gadon sarauta tun a farkon
darensuka yi barci suna ta shara mafarkai masu dadin
gaske shulaiba na cikin yin mafarki ne ta farka daga bacci
kawai sai taji bawali ya kamata don haka saita sauko daga
kan gadon ta shiga kewaye ta bar Aminul has a kwance
bisa gadon yana ta shara barci abinsa
.
Shigarta cikin kewayen keda wuya sai ga guguwa ta

bayyana tana mai kewaye gadon karfin guguwar yasa
gashin kan Aminul has ya kama tashi sama maimakon ya
farka daga barci sai ya kara gyara kwanciya saboda jin
dadin iskar guguwar da ke kadawa nan take kuma sai
guguwar ta rikide ta zama su musabu suna zagaye da
gadon kowannansu na rike da takobi ya dagata sama
tsininta na kallon kasa
.
Lokaci guda suka dubu juna kawai sai suka yunkura da
nufin su tsire cikin sarki aminul has da takubbansu bisa
mamaki sai sukaji an ruke hannayansu tamau a sama sun
kasa saukesu kasa nan fa suka ci gaba da kokarin sauke
hannayen amma sai abu ya gagara sai da suka jarraba
soke cikin shi sau uku amma suka kasa bisa dole suka
hakura suka rikide izuwa guguwa suka bace bat faruwar
hakan keda wuya saiga shulaiba ta fito daga cikin
kewayen duk abinda ya faru bata sani ba koda ta hau
gadon da nufin ta kwanta sai taga gashin kan Aminul has
duk ya tarwatse kuma matashin kai ya fado masa
mamaki ya kama ta amma dataga cewa Aminul has ya
sauya wuri daga inda ya ke kwance saita yi tsammanin
cewa garin mirgin murgin Ne ya jeho matashin kan kasa
har gashin kansa ya barbaje kawai saitayi kwanciyarta
taci gaba da barcinta
Al amarinsu barade kuwa lokacinda suka zama guguwa
suka bace bat sai suka bayyana a can nesa da gidan
sarautar su ukun suka dubi juna cikin matukar mamaki
da razani masabu yace yaya akayi aminul has ya sami
tsari da sihiri.
Akaifu yai ajiyar numfashi yace ni dai a tunanina kafin
sarki sahibul hairi ya bar gida ya taimaka masa samar
yace sam sam ba haka bane shin kun mantane cewa sarki
sahibul hairi ya taba gaya mana cewa babu wani
mahaluki da zai taba yin amfani da irin sirrikan tsafinsa
ai duk yadda akayi ya sami wannan tsari ne daga wajan
wani mutum daban kun san cewa tun da ya zama sarki
dole ne shima ya mike tsaye ya nemi tsari musabu yace
to yanzu menene abin da zai fishshemu?
.
Akaifu yace bamu da abinyi face muje mu sanar da waziri
akiyanu duk abinda ya faru kuma mu bukaci ya bamu
dama ta biyu in ba haka ba kuwa kun san cewa duk
dukiyar da ya bamu karbeta zaiyi.
Ai kan wannan shawara baradan suka rabu kow aya tafi
izuwa gidansa
Kashe gari da safe tun kafin alfijir ya keto su musabu
sukaje wajan waziri akiyanu suka zayyane masa duk
abinda ya faru sa adda sukaje hallahaka aminul Has
koda jin wannan batu sai bakin ciki ya turnuke Akiyanu
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone har saida
kallar takaici ta fado masa cikin tsananin fishi ya dubi su
musabu yace ku tashi kuje na bamu dama ta biyu lallai

kuyi tunanin duk hanyar da zaku bi kuga bayan wannan
mutum kafin nan kafin kwana bakwai in ba haka ba kuwa
duk dukiyar da na baku sai kun dawo mun da ita.
Cikin sanyin jiki da tsananin damuwa su musabu suka
mike tsaye suka tafi sai da su musabu suka shafe kwana
uku suna tunanin hanyar da zasu bi su hallaka sarki
Aminul has amma basu sami mafita ba a rana ta ukuce
da yammaci suka tsinci dami a kala a wannan lokaci suna
zaune su ukun a can bayan gari suna tattauna wa
matsalar kawai sai suka hango sarki Aminul has tare da
mai dakinsa da kuma dakaru kimanin mutum dari kacal
sun fito ran gadi.
Da yake suna labe ne a bayan wani dutse babu wanda ya
hangosu har tawagar sarki ta wuce bayan wucewar sune
musabu ya dubesu yace.
Yauwa ga tsuntsu daga sama gasashshe yanzu menen
abinyi Akaifu yai ajiyar zuciya yace ai ba hawan ba saukar
kun sani dai cewa koda munyi gaba da gaba da sarki ba
zamu iya hallakashi ba tunda mun jarraba mun gani
duk su ukun sukayi shiru suka shiga tunani mai zurfi daga
can sai dabara ta fadowa samar yace ku bani dama na
san abinda zanyi Ni kadai zanje na aiwatar da wannan aiki
bana bukatar taimakonku.
.
Hm cikin matukar mamaki musabu ya dubesu yace haba
samar tayaya zaka iya yin aikin da mu uku ya gagaremu
samar yace ai ka san ance kowanne mutum da irin tasa
hikimar kuma ai ita hikima baiwace don haka saiku
kyaleni na jarraba sa ata
musabu ya dubi Akaifu yace yaka gani Akaifu yace aiba a
kwacewa yaro garma mu bashi dama mu gani
koda jin wannan batu sai samar yayi girgiza ya bace bat
su kuwa sai suka ci gaba da labewa a bayan dutsen suna
jiran dawowar samar.
.
Lokacin da tawagar sarki aminul has sukayi nisa da bayan
gari sukayi nisa da bayan gari sukayi nisa a cikindaji sai
suka yada zango a bakin wata koramar koramar mai
kyawun ruwa garai garai nan take aka kafawa sarki tanki
aka sauke kayansa aka zuba a ciki
.
A rayuwar Aminul has babu abinda yake sha awa sama da
harbin tsuntsaye dan haka ana sauka a bakin wannan
korama sai yaga tsuntsaye iri iri suna ta shawagi a cikin
dajin nan take yasa aka dauko masa kwari da baka ya fara
kaiwa tsuntsaye hari bisa sa a kuwa sai yaga yana harbo
tsuntsayen suna fadowa kasa ana debewa ana tarawa a
cikin wani babban kwando Al amarin da ya jefashi cikin
farin ciki kenan yaji zuciyarsa tayi fari ana cikin wannan
hali ne samar ya baiyana a wajan ba tare da kowa ya
ganshi ba cikin sanda ya isa inda dokin sarki ke daure.
Ba tare da kowa ya ganshi ba sai ya fiddo bakar ciyawa ya

baiwa dokin ya cinye koda fruwar haka sai samar ya bace
.
Sarki aminul has yaci gaba da harbo tsuntsaye cikin farin
ciki da nishadi har sai da ya harbo guda dari a sannan
gajiya ta riskeshi ya bada umarnin a tashi a tafi gida nan
da nan kowa ya haye kan dokinsa aka juya da baya don a
koma cikin gari koda fara tafiyar sai kawai aka ga dokin
sarki yai turjiya yana mai dag kafafuwansa sama yana
haniniya tamkar ya ga wani abin tsoro da ya firgitashi.
.
Kafin a yi wani yunkuri tuni dokin ya juya da baya sarki
na kansa ya zabura da gudu ya nausa cikin dawa cikin
tsananin tashin hankali dakaru sukabi bayansa a sukwane
don su tsayar da dokin.
Ita kuwa gimbiya shulaiba kida taga abinda ya faru da
mijinta sai ta sulale ta fado daga kan dokinta a sume
saboda tsananin razana.
Guyson ke magana
dakaru da dokin sarki aka kasa tsere suna ta kokarin
cimmasa amma abu ya gagara domin na gaba yai gaba
na baya sai labari.
Aminul has yayi ta jan linzamin dokin don ya tsaya amma
kamar ma kara masa gudu yake yi don haka sai ya
rungumi kaddara ya zuba ido yaga inda...Ya zuba ido yaga
inda dokin zai kaishi dokin yaci gaba da azababben gudu
ya zamana cewa ya baiwa dakarun tazara mai yawan
gaske babu yadda za ayi su cimmasa babu abinda zai
baiwa mutum mamaki face yadda dokin yake ratsawa ta
cikin kwazazzabai da kayoyi ba tare da wata damuwa ba
rami kuwa komai girmansa yana yin tsalle ya haye shi
.
A iya sanin Aminul has bai taba ganin doki mai tsananin
karfin gudu ba kamar wannan doki amma abin da ya
bashi mamaki shne ya mallaki wannan doki fiye da
shekaru ashirin kuma babu wanda ya taba hawansa face
shi kadai yaya akayi wannan doki ya zama maguji haka
alhalin bai taba yin tseren gudu da shi ba dokin yaci gaba
da gudu irin gudun da idan aminul has yace zaiyi
gangancin dira daga kansa sai iya hallaka kansa.
.
Haka dai dokin yai ta tsala gudu har ya iso bakin teku
suka lume a cikinsa su biyun a dai dai wannan lokacin
dakarun suka iso wajan bakin tekun sukaja tunga cikin
thanzari wadanda suka iya ninkaya suka sauka kasa daga
kan dawakansu suka fada cikin tekun suka hau lalube.
Saida aka shafe sa a uku suna lalube a cikin tekun amma
ba a ga sarki da dokinsa ba bisa dole aka hakura aka fito
daga cikin tekun aka juya da baya,
.
Lokacin da labari ya riski gimbiya shulaiba cewa da sarki
da dokinsa sun lume a cikin teku an nemesu sama da
kasa an rasa sai ta fashe da kuka da kyar kuyanginta suka

dauketa suka dorata akan doki aka tafi da ita gida,
.
Nan da nan labari ya cika gari cewa sarki da dokinsa sun
hallaka a can bayan gari cikin teku nan fa hankalin jama a
ya dugunzuma aka kama kuka cikin kankanin lokaci fada
ta cika makil da jama a ana ta koke koke da zullumi cikin
tsananin bakin ciki ba komai ne yasa jama ar gari suke
wannan bakin ciki ba face sanin cewa yanzu fa mulkine
zai koma hannun waziri akiyanu idan kuwa mulkin ya
koma hannunsa talakawa sun shiga uku babu wadanda
zasuji dadi face masu mulki da tajirai.
Lokacin da labari ya riski waziri akiyanu da mukarrabansa
cewa sarki ya hallaka a cikin teku sai farin ciki ya
lullubesu sukaji kamar su zuba ruwa akasa su sha tun
kafin su iso fada suka fara rabawa makada da mawaka
dukiya suka shiga aikinsu kafin a jima kuwa tuni su waziri
Akiyanu sun hallara a fadar don kaddamar da bakin
nadin sarautarsa kafin ya hau karagar ne makada da
mawaka wuka yi ta cashewa bayan nan sai waziri akiyanu
ya mike yayi bayanin tsautsayin da ya sami sarki Aminul
has har ma ya matso hawayan karya yana mai nuna
bakin cikinsa duk da ya san cewa jama a sun san cewa
murna yake da faruwar tsautsayin
.
Bayan ya gama jawabin sai ya tafi izuwa kan karagar
mulkin don ya zauna ba zato ba tsammani sai aka jiyo
sukuwar doki gaba daya jama ar dake fadar suka waigo
suka dubi bakin kofa saiga sarki Aminul has bisa wannan
dokin a sukwane
.
Da shi da dokin duk a jike suke sharkaf da ruwa Al amarin
da ya jefa kowa a cikin mamaki kenan shi kuwa waziri
akiyanu sai ya kasa zama a kan karagar mulkin ya kame
kamar gunki sbd tsananin mamaki da jin kunya,
Da shi da mukarraban nasa duk sai ido ya raina fata sarki
Aminul has yazo har gaban karagar mulkin fuskarsa cike
da annuri da zuwa sai yaja tunga ya sauko daga kan
dokinsa ya nufi kan karagar
.
Waziri akiyanu ya matsa gefe daya ya bashi hanya
a wannan lokaci gimbiya shulaiba na can cikin turakarta
tana shara kukan bakin ciki tana cikin hakanne wata
kuyanga tazo ta tabbatar mata da cewa ai ga sarki can ya
dawo a cikin koshin lafiya koda jin wannan batu sai ta
mike zumbur ta ruga izuwa fada da zuwanta bakin kofar
fada saita hango Aminul has a zaune bisa karagar mulki
jama a na kewaye da shi suna tayashi murnan tsira da
rayuwarsa
.
Kawai sai ta tsaya a bakin kofar ta na ta kyalkyala dariyar
farin ciki bayan sarki Aminul has ya gama karbar jajen
murna sai ya mike tsaye ya fuskanci jama a yace'

yaku jamar wannan birni na misra na fuskanci cewa
kunyi matukar mamaki da kuka ga na dawo gareku a
raye?
Hakika akwai alajabi a cikin wannan al amari don haka
akwai bukatar nayi muku bayanin yadda akai na kubuta
da rayuwata
da farko lokacin da dokina ya zabura dani ya kama gudun
tsiya dani sai hankalina ya dugunzuma ainun domin nine
nayi kiwon dokin tun yana karami kuma ko sau daya ban
taba jarraba yin gudu dashi ba haka kuma babu wanda
ya taba hawa dokin in baniba
.
Ko da naga na kasa sarrafa wannan dokin don na tsai
dashi sai na rungumi kaddara na zuba ido kawai naga
inda zai kaini ban ankara ba sai gani nayi ya afak dani
cikin teku kafin nayi wani yunkuri dani dashi mun lume
izuwa karkashin tekun
ba zato ba tsammani kuma sai naga munci gaba da tafiya
a karkashin ruwa tamkar akan doron kasa muke ba a
ruwa ba nan ne fa na dada cika da mamaki ainun.
Haka dai dokin nawa yayi ta tafiya dani a karkashin teku
har tsawon sa a biyar kawai sai naga ya juyo da baya cikin
tsananin gudu fiye da na farko tamkar giftawar
tauraruwa mai wutsiya nan da nan muka iso bakin gabar
tekun muka fito waje fitarmu keda wuya ..Sai dokin ya
tsugunna kasa ya kama kumallo nan take ya amayar da
wata irin bakar ciyawa duk wannan abu da ya faru hannu
na na rike da wannan sanda ta hannuna shi kuwa
takalmin nan dake kafata bai bar jikina ba kwatsam sai
naga wani danguntun Aljani ya bayyana a gabana wanda
baifi na kifeshi da kwando ba.
Aljanin yayi sujjada a gareni yace an gaisheka ya wakilin
adalin sarki ka kwantar da hankalin ka ka sani cewa indai
kana tare da wannan sanda ta hannunka da kuma
wannan takalmi na kafarka babu wani tsautsayi da zai
sameka
.
Koda naji wannan batu sai na cika da mamaki nace kai
kuma waye yaya akayi kasan wannan al amari?
Koda jin wannan tambaya sai aljanin ya bushe da dariya
yace ni sunana MAKANUL URUD kuma na kasance mai
tsaron wanda duk yake tare da wannan sanda da
takalmin in baka mance ba asalin wadannan abubuwa
biyu na mahaifin matarka ne wato Abu hakim a wajansa
ta gajesu
.
Labarin wadannan sanda da

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment