Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gwammace bai zo duniya ba yanzu
a gaban idanunki zan yiwa wannan sarki da bawansa
kisan wulakanci irin wanda baki taba gani ba.
.
Duk wannan bayani da sarki barusa ke yi sarki sahibul
hairi na zaune akan aljani dabarus ya zuba musu idanu
kawai ko gyara zaama baiyi ba maganganun da yake yma
jinsu yake kamar tatsuniya ( kunji fa yarda da kai wajan
sarki sahibul hairi) ita kuwa gimbiya shukura sa adda taji
barusa ya gama jawabinsa sai ta kyalkyale da dariya
lokaci guda kuma ta murtuke fuska tace kai barusa
dakata kaji ka yi sake dan zaki ya girma ina tabbatar maka
da cewa baka isa kayi mini komai ba domin dama na
dade ina yin tanadinka.
.
Nima kuma a yanzu ban isa nayi maka komai ba tunda
ban mallaki sihirin tsafin da zan iya ganin bayanka ba
kafin na tareka mu gwabza yanzu ga dan uwanka nan
sarki SAHIBUL HAIRI GAGARA BADAU saiku fara karawa
mu gani ko zaka iya dashi ''
koda jin wannan batu sai sarki barusa ya juya ya dubi
sarki sahibul hairi ya bushe da dariya sannan kuma ya
murtuke fuska kawai sai yaga wata irin walkiya ta fito
daga cikin idanun barusa ta bugi jikin sahibul hairi take
rigar karfen da yake jikin sahibul hairi ta bace bat barusa
ya bushe da dariya a karo na biyu yace yanzu saimu
gwabza gaskiya da gaskiya.
.
Kafin sahibul hairi yayi wani yunkuri tuni barusa yayi tsafi
saiga wani narkeken aljani nan ya bayyana a gabansa
wanda a girma da kwarjini ya ninka Aljani dabarus sau
uku.a lokacinne kuma wata katuwar takobi ta bayyana a
hannun sarki barusa.
Cikin abinda baifi kiftawar ido ba sarki barusa ya haye
kan narkeken aljanin suka afkawa sahibul hairi.
Nanfa aka fara azababben yaki ya zamana cewa sahibul
hairi na kaiwa sarki barusa sara da gatarin sihiri shi kuma
yana karewa da wannan katuwar takobin yana maida
martani
wannan fada dai a sama suke yinsa bisa aljanun biyu
cikin isa gimbiya shukura da bawa haluf kuwa sai suka

daga kawunansu sama suna kallon abindake faruwa a
cikin sararin samaniya.
Al amin ne sunana. Sa adda takobin sarki barusa ta hadu
da gatarin sihiri sai kaji wata irin kara mai firgitarwa
tamkar saukar aradu sannan kuma sai tartsatsin wuya
gami da hayaki sun tashi al amarin da ya janyo girgizar
gidan sarautar kenan gaba daya jama ar dake cikin gidan
sai da hankalinsu ya dugunzuma saida aka shafe sa a uku
ana wannan gumurzu dayansu bai sami nasarar taba jikin
daya ba amma tuni sun rugurguza ginin fadar domin a
duk sa adda dayansu ya kaiwa daya sara ya goce duk
abinda ya sama sai wannan abu ya rabe gida biyu koda
kuwa dirkar gini ce shi kansa tartsatsin wutar da ke zuba
daga jikin makaman fadan nasu sai da ya haddasa gobara
in ba don gimbiya shukura na kashe wutar ba da karfin
sihiri da tuni fadar ta kone gaba dayanta. ....
LOKACIN DA SAURAN JAMA'A DAKE
CIKIN FADAR SUKAJI FADAR NATA
GIRGIZA KAMAR,
zata rufta cikin kasa sannan karar
haduwar makaman su sarki sahibul
hairi,
ta cika musu dodon kunne sai suka rude
suka firgice aka kama iface iface,
da guje guje domin ba a taba ganin
tashin hankali ba irin wannan,
kafin a jima wannan tashin hankali ya
isa har cikin gari ko ina da ina,
don haka sai gaba daya birnin ya
hargitse kai bama mutane ba hatta,
dabbobin gida da na daji saida suka
firgice suka kama koke koke da,
guje guje tsuntsaye kuwa tashi suka
rinkayi suna barin shekarsu suna kaara
nausawa cikin daji,
domin neman maboya manyan dabbobi
irinsu kura zaki damisa da sauransu,
cikin ramuka da koguna suka ringa
shigewa suna boye kansu,
kai a wannan rana duk dabbar dake
cikin ruwa bata yarda ta leko saman
ruwa ba,
tun sa adda aka fara azababben yakin
tsakanin sarki barusa da sarki sahibul
hairi,
sai bawa haluf ya yanke jiki ya fadi kasa
sumamme saboda tsananin razana,
ko kadan gimbiya shukura bata lura da
halin da haluf ya shiga ba domin,
gaba daya hankalinta na kansu sarki
sahibul hairi sa adda sarki barusa,
ya ga an shafe kusan sa a uku ana

wannan dauki ba dadi amma ko sau
daya,
bai sami nasarar taba jikin sahibul hairi
ba sai ransa ya baci zuciyarsa tayi
bakikirin,
kawai sai yai jifa da takobin hannunsa
yai nuni da hannunsa guda,
izuwa ga sahibul hairi take wadansu
masun tsafi suka fito daga cikin,
hannun nasa kimanin guda dari suka
tafi da gudu kamar an cillosu daga
cikin kasa zasu cake a cikin jikin sarki
sahibul hairi kawai sai shukura ta nuna
masun da yatsantsa guda take suka
tsaya kyam a cikin isa kuma suka kone
kurmus suka ruburbushe, koda ganin
haka sai sarki barusa ya kara fusata
ya juyo kan shukura suka fara musayar
tsafi a tsakaninsu kowa na jefawa
kowa mugayen abubuwa shi kuwa
sahibul hairi sai ya zama dan kallo .
Sai da barusa da shukura suka jefi
junansu da muggan makamai sama da
guda dari
amma dayansu bai sami nasarar
lahanta dan uwansa ba daga nan kuma
sai
suka jefawa juna wata irin iksa mai
karfin tsiya sai gashi suna wujijjiga
juna a sama suna ta katantanwa a cikin
iska a wannan lokaci iskar sarki barusa
tafi ta shukura karfi don haka sai tayi ta
wulwulata da karfin tsiya cikin
kankanin lokaci shukura ta fita daga
cikin hayyacinta kawai sai iskar ta
makata
a jikin gini sannan ta saketa sai ga jini
yana zuba a goshin shukura ta fado
kasa
magashiyan babu alamar tana numfashi
koda ganin abinda ya faru sai
hankalin sarki sahibul hairi ya
dugunzuma shi kuma sarki barusa sai
ya
tuntsure da dariyar farin ciki yace yanzu
na gama da wannan munafukar maci
amana
saura kai karamin alhaki ina mai
shawartarka daka bani wannan gatarin
sihirin
dake hannunka kuma ka durkusa bisa
gwiwoyinka ka tuba gareni muddin

kana son kaci gaba da rayuwa a doron
kasa in ba haka ba kuwa yanzun na
zan yi daga daga da sassan jikinka na
batar dakai yadda har abada babu mai
iya shaida barin jikinka guda
yayinda sarki sahibul hairi yaji wannan
batu sai yayi murmushi irin na manyan
mazaje
wadanda basa karayar zuci yace yakai
tsohon azzalumi kayi sani cewa
babu wani da mai jini a jiki wanda ya isa
ya firgitani walau mutum ko aljan
domin ban san tsoro ba kuma ban san
jada baya ba ina tabbatar maka da
cewa
babu wani bala'i ko wata masifa da ta
isa ta rabani da wannan gatarin sihirin
dake hannuna don haka ina mai
shawartarka daka kauce ka bani hanya
na fice daga cikin fadarka salin alin in
ba haka ba kuwa zaka riski ajalinsa
koda jin wannan batu sai sarki barusa
ya bushe da dariya kawai sai ya
watsawa
sahibul hairi kibiyoyin tsafi da nufin su
cake dukkan jikinsa koda kibiyoyin
suka diro a kan jikin sahibul hairi sai
duk suka narke suka zama jini shikuwa
jikin nasa ko kwarzanewa baiyi ba ko
da ganin haka sai ran sarki barusa ya
baci ya dubi sahibul hairi yace amma
kayi farar dabara daka sha jinin
dodannina
a dakin azaba na karkashin kasa ba
don haka ba da tuni yanzu kibiyoyin
tsafina sun nutse a cikin gangar jikinka
tabbas yanzu ba zan iya hallaka ka ba
da karfin sihiri amma idan ka ci
maganin kaifi da tsini ai bakaci na karfin
damtse ba koda gama fadin haka sai
sarki barusa ya daka tsalle daga kan
aljaninsa ya dira akan aljani dabarus
ya gwabzawa sahibul hairi naushi a
baki saboda karfin naushin saida
sahibul hairi
ya baje a kan aljani dabarus wani irin
gudan jini yai tsartuwa daga cikin
bakinsa sai yai shame shame kamar ya
suma sarki barusa ya raba kafafunsa
akan sahibul hairi kuma ya dunkule
daya hannun nasa da nufin ya yiwa
sahibul hairi fashin albasa aka bazato

ba tsammani sai yaji sahibul hairi
ya gwabza masa naushi a fuskarsa
sarki barusa ya tafi da baya taga taga
kamar zai rikito kasa daga kan aljani
dabarus take idonsa guda ya kumburo
saboda karfin naushin da sahibul hairi
yayi masa amma sai ya sake rugowa
kan sahibul hairi yaci gaba da
tumurmusashi yana naushinsa hannu
da kafa. Cikin zafin nama ba
kakkautawa
tun da sarki sahibul hairi yake fada da
sadaukai
bai taba haduwa da sadaukin daya yi
masa mahaukacin
duka ba irin wannan har saida ta kusa
cewa sahibul hairi baya iya mai da
martani sai dai kokarin
kare duka kai da dukan ma yayi masa
yawa saiya
kasa karewar yanaji yana gani sarki
barusa yayi laga
laga dashi ya hada masa jini da majina
sahibul hairi ya
sake yin wanwar akan aljani dabarus ya
zamo tamkar
gawa sai numfashi yake yi dakyar
hakika barusa ya fi karfin
sahibul hairi
nesa ba kusa ba domin ko tsaywa
sukayi mutum ya dubi
girmansu da kirar sadaukantakarsu
yasan cewa banbancin a bayyane yake
lokacin da sarki barusa ya ga ya sumar
da sahibul
hairi a karo na biyu sai ya sake zuwa
kansa ya tsaya ya sunkuyya
da nufin ya kamo kansa ya karya masa
wuya
koda ya kai hannunsa zai kamo kansa
sai yaga sahibul hairi
ya goce cikin zafin nama yayi dungure
ta karkashin kafafunsa
ya bulla bayansa kafin dabarus ya juya
tuni sahibul hairi ya
naushi bayan barusa da dukkan
karfinsa nan take sarki barusa
ya fado kasa daga kan aljani dabarus
fadowar da zaiyi kuwa
sai ya fado kan wata rusashshiyar
dirkar gini koda buguwar
kansa sai ya sume a wannan lokacine

sahibul hairi ya mike tsaye da kyar ai
kuwa sai ya hango bawa haluf
da gimbiya shukura kwance a sume
cikin tsawa sahibul
hairi ya umarci aljani dabarus daya
dauko gimbiya da bawa
haluf ya fitar dasu daga cikin
wannan fada kafin dakika biyu tuni
aljani dabarus ya cika
wannan umarni tuni sun luluka sama
cikin gajimare
bayan kaamar dakika dari da ashirin da
bacewar su sahibul
hairi sai sarki barusa ya farfado daga
suman da yayi cikin
razana ya mike tsaye zumbur ya kama
dube dube baiga kowa ba
a wajan face wadannan narkeken aljani
nasa zaune waje daya yai
tagumi sarki barusa ya dakawa
aljanin tsawa yace ya kai shumakaru
ina abokan gabata
shumakaru ya risina yace ai tuni
wannan aljani nasu ya kwashesu
yayi sama dasu sun bace a cikin
gajimare cikin tsananin fushi sarki
barusa ya sake dakawa shumakaru
tsawa yace me yasa ka kyalesu suka
gudu shumakaru
ya ce ya shugabana ai bana zartar da
aiki face da umarninka
koda jin wannan batu sai sarki barusa
ya takarkare ya kwarara uban ihi
mai tsananin firgitawa cikin nuna takaici
tamkar ya fashe da kuka
sannan ya sunkwi da kansa kasa yace
yanzu yau ni aka zo har fadata aka cini
da yaki hakika mata
shaidanu ne in ba don shukura taci
amanata ba da babu yadda
za ayi sarki sahibul hairi ya sami
ikon satar gatarin sihirina na sani cewa
yanzu babu inda zasu nufa face gidan
boka shamzubul azwas
don dauko yarinya Alfila abinda zanyi
kawai shine nayi gagarumin
shiri nabi bayansu in yaso sai na labe a
kusa da gidan shamzubul
azwas sai bayan sun gama shan
wahalarsu sun dauko alfila ni kuma na
taresu na kwaceta na hallakasu
koda gama wannan zance sai sarki

barusa ya kama kyalkyala dariyar
mugunta yaci
gaba da yin dariyar kamar ba zai daina
ba nima kuma saina
ci gaba da tayashi wannan dariyar ni
guyson muje zuwa
wannan shine abinda ya faru tsakanin
sarki barusa da sarki
sahibul hairi bayan sahibul hairi ya sami
nasarar dauko gatarin sihiri
Al amarin sarki sahibul hairi da aljani
dabarus kuwa....
AL AMARIN SARKI SAHIBUL HAIRI DA ALJANI
DABARUS KUWA SAI DA SUKA SHAFE SA A
HUDU
SUNA TAFIYA A CAN KOLOLUWAR SAMA
SANNAN sahibul hairi ya umarci
dabarus daya sauko kasa ba tare da
wata gardamar komai ba
kuwa sai aljani dabarus ya cika umarni
har suka sauko kasa suka
dira a cikin wani tafkeken jeji mai
dogayen bishiyoyi da manyan
tsaunika da fadamomi da koramai
gimbiya shukura da bawa haluf basu
farfado daga dogon suman
da sukayi ba koda ganin haka
sai hankalin sarki sahibul hairi ya
dugunzuma ya fara jijjigasu don
tsammaninsa sun mutu ne aljani
dabarus ne ya dubi sahibul hairi
yace ya shugabana ka kwantar da
hankalinka ba mutuwa sukayi ba
dogon suma sukayi kaje ka samo ruwa
ka yayyafa musu ni kuma sai
nayi musu fifita da fuka fukaina in muka
yi haka zasu farfado
koda jin wannan shawarar sai sarki
sahibul hairi ya ruga izuwa
cikin wata korama ya tsoma wani
mayafi nasa a ciki sannan ya daw
a guje ya daddana mayafin akan
fuskokin su shi kuwa dabarus sai
ya kamayi musu fifita da fuka fukansa
bayan dakika biyar
da faruwar hakan sai duk su biyun suka
farfado suna masu yin tari
da atishawa koda ganin haka
sai farin ciki ya lullube sarki sahibul
hairi shukura da haluf
suka kama kalle kalle da waige waige
suna masu mamakin yadda aka

yi suka tsinci kansu a cikin wannan daji
koda sarki sahibul
hairi ya fahimci halin da suke ciki sai ya
bushe da dariya yace kuna
mamakin ne bisa yadda kukazo nan?
Shukura ta dubeshi tayi masa
murmushi tace bana mamaki da
al amarinka ya kai jarumi uban jarumai
amma ina so ka gaya mini
abinda ya faru tsakaninka da mijina
shinka kashe shine??
Koda jin wannan tambaya sai sarki
sahibul hairi yayi ajiyar
zuciya sannan yace ai a rayuwata ban
taba haduwa da sadauki
mai tsananin karfi ba kamar mijinki
tabbas in ba don ina da nisan
kwana ba da tuni ya hallakani ina sanar
dake lambo nayi masa kamar na suma
sannan na shammaceshi na dokeshi
daga kan. Daga kan aljani dabarus ni
dai naga sa adda ya fado kasa
kansa ya bugu da wani rusashshen
tubalin gini harma
goshinsa ya fashe jini ya zuba abinda
ban sani ba shine
shin suma yayi ko kuwa mutuwa yayi sa
dda gimbiya shukura
taji wannan batu sai tayi ajiyar zuciya
cikin takaici tace yakai
wannan sarki kayi sani cewa kayi
babban kuskure da baka
tabbatar da mutuwar mijina ba ai kaima
kasan cewa manyan
mazaje basa saurin mutuwa ina
tabbatar maka da cewa
sarki barusa na nan a raye kuma zaiyi
gagarumin shiri
ya biyomu duk inda zamu je ko shakka
babu duk sa adda
muka sake yin arba da shi sai ya sami
nasarar hallakamu
yayinda sahibul hairi yaji wannan batu
sai yayi murmushi
yace yake shukura kiyi sani cewa a
rayuwata ni
,utum ne mai tsananin sa a bisa duk
abinda nasa a gabana
don haka ina tabbatar miki da cewa
komai RINTSI DA
TSANANI sai na cika burina na zama
SARKIN SARAKAI

na duniya lallai sai mun dauko yarinya
alfila a
cikin gidan boka shamzubul azwas
kuma sai na sadu
da sadauki Awaisu ya taimaka mini
mun nemo
wadannan yan mata guda uku wadanda
zan auresu
na sami daukakar dana ke nema
Koda jin wannan batu sai gimbiya
shukura ta jin jinakai
tace tabdijam ashe kuwa kana da
gagarumin aiki
agabanka ina tabbatar maka da cewa
wahalar da
kasha a baya tamkar kaso daya ce
daga dubun wacce
zaka sha a nan gaba yakai wannan
sarki kayi sani
cewa nemo wadannan yan mata uku
dai dai yake da
nemo jaki mai kaho domin babu wanda
yasan inda suk )
saboda sun boye kansu da karfin sihiri
irin na
sadauki awaisu tabbas in ba sadauki
awaisu ba
babu wanda zai iya laluben inda suke
shi kansa
babu tabbacin cewa zai iya gano inda
suke a cikin
karamin lokaci yakai wannan sarki idan
har dukiya
kake bukata da kuma daukaka aiko a
yanzu ka
samesu
domin wannan gatarin sihirin kadai
daka mallaka
ya isa ya baka duk abinda kake bukata
ina tabbatar
maka da cewa idan kaje ka ajiye
wannan gatarin
a cikin gidan sarautarka saika sami
dukiya mai
yawan da tafi cikin RIJIYA GABA DUBU
arba'in
kasancewar kayi babbar bajinta wacce
babu wanda ya
yi ta a wannan zamani don haka dole
ne labarinka
ya bazu ko ina
a cikin duniya mai zai hana yanzu ka

koma kasarka
kaci gaba da sabuwar rayuwa?
Amma ina mai rokonka alfarma guda
daya
Alfarmar kuwa itace ka daure muje
gidan boka
shamzubul azwas mu dauko yarinya
Alfila
ka mallaka min ita
koda jin wannan batu sai sarki sahibul
hairi
ya bushe da dariya sannan ya dubi
gimbiya
shukura yace kai duniya ba gaskiya
wato dai kina
nufin duk wahalar da nasha a baya ta
zamo ke nayi wa kenan
idan na hakura da gatarin sihirin kadai
ke kuma
na baki yarinya Alfila ne zaki sami
wadannan
sirrikan tsafi
guda dari idan kuka samesu kuwa sai
kinfi kowa
arziki da daukaka a duniya shin kin
manta ne
cewa nima matsayin da nake nema
kenan?
Ai so nake nafi dukkan sarakunan
duniya dukiya
mata da daukaka ya kasance ana
kirana da suna
SARKIN SARAKAI
Hakika ba zan taba samun wannan
matsayi ba
face na auri wadannan yan mata uku
kamar
yadda boka hadimul Asur ya yi mini
bayani
ke yanzu na san so kike nayi miki
wahalar banza
ki samu abinda kike nema kin taimakeni
a cikin
gidan sarautar sarki barusa na sami
nasarar dauko
gatarin sihiri nima na ceci rayuwarki
dana
daukoki daga can domin inda na baroki
a can
din sarki barusa ya farfado ya ganki da
tuni kin
zama gawa

guyson naci gaba da cewa
ina mai shawartarki da mu rabu anan ki
tafi can
wani bangare daban na duniya kici
gaba da bina
har mu dauko yarinya Alfila ki iya rabani
da ita muje
zuwa mahaukaci ya hau kura' ai wanda
baiji
bari ba shine yake jin hoho !!!
Sa adda sarki uban sadaukai sarki
sahibul hairi
yazo nan a zancensa sai hankalin
gimbiya
shukura ya dugunzuma
nan take idanunta suka ciko da kwalla
taji
gaba daya ta
tsani kanta kuma ta tsani rayuwar
duniya
gaba daya
domin ta fuskanci cewa zatayi biyu
babu
ma ana bata ga tsuntsu
kuma bata ga tarko... !!!!!!!
.
SHIN SARKI SAHIBUL HAIRI ZAI SAMI
NASARAR SHIGA CIKIN GIDAN BOKA
SHAMZUBUL AZWAS HAR YA DAUKO
YARINYA ALFILA??
.
YAUSHE NE SAHIBUL HAIRI ZAI HADU
DA SADAUKI AWAISU??
.
SHIN IDAN SUN HADU SADAUKI
AWAISU ZAI YARDA SU TAFI NEMAN
YAN MATAN UKU?
.
SHIN SU WAZIRI AKIYANU ZASU SAMI
NASARAR SATO WANNAN DOKI NA
SARKI AMINUL HAS SU KAIWA BOKA
SHUBURUL UZUB?
.
IDAN SUN KAI MASA DOKIN ZAI CIKA
ALKAWARIN YAGAYA MUSU HANYAR
DA ZASU BI SU SAMI NASARAR
HALLAKA AMINUL HAS?
.
YAUSHE NE BURIN SARKI SAHIBUL
HAIRI ZAI CIKA YA ZAMA SARKIN
SARAKAI?
.

SHIN SARKI AMINUL HAS DA
MATARSA SHULAIBA ZASU SAMI IKON
YIN KWANA SITTIN AKAN GADON
SARAUTAR BIRNIN MISRA DON SU
SAMI HAIHUWA?

SARKIN SARAKAI
Littafina Uku 3 complet
Na Abdulaziz Sani madakin gini
Typing by Al'amin Ahmed misau
Post And Ebook creator by Shuraih Usman 99%

You can download more Hausaebooks at http://shuraih.waphall.com


LOKACIN DA SARKI SAHIBUL HAIRI YA GAMAwannan
jawabi ga gimbiya Shukura, sai kawai ya dauki Bawa Haluf
ya daurashi a bayan aljani Dabarus din ya zauna yana rike
da gatarinsa da wannan garkuwa. Take ya yiwa aljani
Dabarus umarni da ya tashi sama da su.
Cikin alamun tsoro aljani Dabarusa ya dubi sarki Sahibul
Hairi sannan ya dubi gimbiya Shukura ya sake duban
sarki Sahibul Hairi ya ce, "ya shugabana yanzu ayi haka
kuwa? Ai bai kamata mu bar gimbiya anan ba. Ka tuna fa
cewa in ba don itaba da baka sami nasarar dauko
wannan Gatarin ba."
Sarki Sahibul Hairi ya dakawa Dabarus tsawa ya ce, "maza
ka bi umarnina ko kuma yanzun nan mu gwabza ni da
kai".
Koda jin haka sai Dabarus yai sauri ya bude fuka-fukansa
yai sama jikinsa na kyarma.
Ita ko gimbiya Shukura wadda ke zaune a kas dirshan, sai
ta daga kai sama ta bisu da kallo kawai cikin alamun
takaici da nadama har hawaye na zuba a idanunta.
Al'amarin da ya sa sarki Sahibul Hairi yaji ya kamu da
matsainaicin tausayinta ke nan. Amma da ya tuna irin cin
amanar da ta yiwa mijinta sarki Barusa, sai ya tsaneta fiye
da komai a duniya. Har ya aiyana a ransa cewa hakika
mata abin tsoro ne, kuma abin shakka ga duk da namiji
komai karfin mulkinsa.
Haka dai Gimbiya shukura ta ci gaba da kallon su sarki
Sahibul Hairi suma suna kallonta har suka kule a cikin
sararin samaniya suka daina ganin juna.
Bayan bacewarsu da kimanin dakika dari da ashirin, sai
gimbiya shukura ta tuntsure da dariyar farin ciki ta ce, "ai
idan ka san wata baka san wata ba. Zamu hadu ne a can
gidan Boka shamzabul Azwas tsakanin ni da kai da Barusa
na ga wanda zai mallaki Alfila". Koda gama wannan
jawabi sai gimbiya shukura ta yi girgiza, take ta rikida ta
zama farin hayaki, shi kuwa hayakin sai yai sama ya bace
bat a cikin gajimare.
Al'amarin sarki Sahibul hairi Bawa Haluf kuwa,lokacin da
suka ci gaba da tafiya bisa aljani Dabarus a can
kokolowar sama, sai da suka shafe rabin sa'a dayansu bai
ce uffan ba.
Daga can sai Haluf ya dubi sarki Sahibul Hairi ya ga ya yi
jugum al'amarin da ya shiga tunani mai zurfi. Cikin
biyayya Haluf yai gyaran murya sannan ya ce, "ya
shugabana, kai kuwa tunanin mai kake yi haka. Shin kana
nazarin gagarumin aikin da ke gabanka ne ko kuwa kana
tuno irin wahalar da ka sha a bayane?".
Koda jin wadannan tambayoyi sai sarki Sahibul Hairi ya yi
murmushi ya ce, "ya kai Bawa Haluf, kayi sani cewa bana
tunani bisa duk abubuwa biyu da kake zato. Abin da na ke
tunani shi ne gida. Hakika ina cikin fargaba, zullumi bisa
halin da Aminul Has zai shiga bisa jagorancin da bashi na
rike min kasata kafin na dawo. Na san halin su waziri
Akiyanu, su a tunaninsu wannan tafiya da na yi na tattare
da mugun hadari, dom haka suna ganin cewa ba zan taba
komawa gida a raye ba. Bisa wannan tunani dole na su yi
shawarar kawar da Amirul Has gada kan karagar mulkin
zalunci. Babu mamaki ma a ahalin yanzu tuni sun kawar
da shi kuma sun fara azabtar da jama'ata."
Lokacin da sarki Sahibul Hairi ya zo nan a zancensa sai
jikin Bawa Haluf ya yi sanyi, kuma shima hankalinsa ya
dugunzuma, ya ce, "ya shugabana hakika abin da kake
zargi zai iya faruwa. Amma me zai hana ka bincka mana a
cikin madubin tsafika don mu ga zahiri?".
Sarki Sahibul Hairi ya gyada kai ya ce "tun da muka baro
gida ka ga na duba madubin tsafina ko sau daya?".
Bawa Haluf ya ce, "A a ban taba gani ba".
Sarki Sahibul Hairi ya ce, "ni a tsarin rayuwata in nai gaba
bana baya koda kuwa zan hadu da ajalina a gabana. A
rayuwata ban taba sa bukata a gabana ta gagareni ba. Ao
idan na ga abin da ya faru a madubin tsafina zuciyata za
ta iya karaya nayi tunanin komawa da baya. Bisa wannan
dalili ne na ki duba madubin tsafi. Ina mai tabbatar maka
da cewa ba zan taba waiwayan gida ba face na mallaki
abin da na fito nema. Idan kuwa ban sami biyan bukat
ba, to har abada ba zan koma gida ba sai dai ajalina ya
riskeni a wani wuri daban".
Gama fadin hakan ke da wuya sai aljani Dabarus ya sauka
kasa yana shirin dira bisa turba. Cikin fishi sarki Sahibul
Hairi ya daka masa tsawa ya ce, "kai kuma wane ne ya yi
maka umarnin saukowa kasa?".
Koda jin wannan tambaya sai jikin aljani Dabarus ya
kama kyarma, ya ce, "ka yafeni ya shugabana, ai ba laifina
bane. Dubi gabanmu da kyau, ina kyutata zato mun fada
tarkon wasu manyan bokayen ne".
Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka leko kasa da sauri,
sai suka ga tarin wadansu mutane a cikin wani
kayataccen birni a tsatsaye cikin shigar kamala, mazansu
da matansu, yara da manya sun daga kawunansu sama
suna kallon aljani Dabarus.
Wani dattijon mutun mai dogon farin gemu, kuma roke
da sanda sanye da fariren tufafi na tsaye a gaban dukkan
jama'ar, yana rike da wata goguwar cazbaha yana ta
motsa bakinsa. Ga dukkan alamu yana karanta wadansu
kalmomi ne.
Abin da ya daurewa sarki Sahibul Hairi kai shi ne, yadda
aljani Dabarus ke ta kokarin kada fuka-fukansa domin ya
yi sama ya ci gaba da tafiya amma ya kasa.
Koda sarki Sahibul Hairi ya fuskanci abin da ke faruwa, sai
ya dubi aljani Dabarus ya ce, "saki jikinka ka sauka kasn
mu abin da wadannan mutane ke nufi damu. Tabbas
sune suka hanamu ci gaba da tafiya".
Take aljani Dabarus ya bi umarni ya sauko kasa a cikin
kayataccen birnin. Ai kuwa yana sauka sai sarki Sahibul
Hairi da Bawa Haluf suka kama kalle-kallen gine-ginen
birnin suna masu al'ajabi domin basu taba ganin irinsa
ba.
Dattijon mutumin mai farin gemu ya taho ga su sarki
Sahobul Hairi fuskarsa cike da murmushi ya ce, "ale
marhabun da jarumi uban jarumai, sarki Sahibul Hairi na
birnin Misra. Ina ui maka barka da zuwa birnin Hairin
Nur! Sunana Imam Sadiku Ibni Harais. Ni ne shugaba a
wannan birni, kuma gaba dayanmu mun kasance
ma'abota addinin Musulumci.
Ya kai wannan sarki, kayi sani cewa ubangijina ya yi mini
nuni sa zuwanka a cikin mafarkina, kuma ya sanar da ni
gaba dayan labarinka da duk abin da ka ke son ja cimma
buri. In da ka ba da gaskiya da addinina da Ubangijina ya
baka duk abin sa kake nema a saukake ba tare da ka ci
gaba da shan wahalar da kake sha ba".
Ya yin da sarki Sahibul Hairi yaji wannan batu, sai jikinsa
ya yi sanyi, ai shiru ya rasa abin da zai fadi. Daga can sai
ya gana da Bawa Haluf suka yia kus-kus, bayan nan sai ya
dubi imam Sadik sai ya ce, "ina bukatar kabani lokaci, in
yi shawara da zuciytz da kuma wannan dan uwan nawa."
Imam sadik ya ce, "na baka kwana uku ka yanke shawara.
Kuma ina tabbatar maka da cewa zamu baka masauki da
kulawa mai kyau a tsawan wadannan kwana uku. Yanzu
sai ku taho a kai ku izuwa masaukinku, amma ku baiwa
wannan hadimin aljani naku shawara da kada ya kuskura
ya taba daya daga cikin jama'ata, domin zai iya konewa
kurmus ya zama toka.
Koda jin haka sai Sarki Sahibul Hairi ya dubi aljani
Dabarus ya yi shiru bai ce da shi komai ba. Shi kuwa
aljani Dabarus ya sunkuyar da kai kasa ya sake rabewa a
waje guda kamar dan almajiri cikin alamun tsoro tamkar
ka ce kyat! Ya zura da gudu.
Ba tare da bata lokaciba Imam sadik ya umarci wani
hadimi da ya kai su sarki sahibul Hairi izuwa masukinsu.
Nan take kuwa wannan hadimi ya wuce gaba suka bishi a
baya har izuwa wani gida a gefan garin.
Bayan sarki Sahibul Hairia da Bawa Haluf sun ci abinci
sun huta, sai suka fara sabuwar hira inda sika shiga
tattaunawa bisa wannan sabon al'amari da ya samesu na
tsintar kansu a wannan birni na ma'abota addinin
musulinci.
Sarki Sahibul Hairi ya dubi Bawa Haluf yana cikin yanayin
damuwa ya ce, "ya kai Hauf kai sani cewa hakika na
tsorata da ak'amarin wadannan mutane, yanzu kai a
tunaninka mene ne ya dace nayi? Shin zan yar da na karbi
addinin nasu ne na duk abinda na fito nema a saukake
kamar yadda suka fada kokuwa na yi kokari murabu
lafiya mu ci gaba da tafiya harbukatarmu tabiya? No dai
banda tabbacin cewa abin da suka fadi zai yiwu, amma
na yi imani cewa da karfin jarumtaka da kuma juriyata
komai rintsi komai tsanani sai na cimma burina".
Ya yin da Sarki Sahibul Hairi ya zo nan a zancansa, sai
Bawa Haluf ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce, "ya kai
shugabana kayia sani cewa hakika muna cikin tsaka mai
wuya, domin idan mula ce zamu bujirewa wadannan
mutane zasu iya wargaza mana duk shirinmu ya zamana
dul wahalar damuka sha a baya ta zama ta banza. Haka
kuma ina tsoran kada mu saki reshe mufada kan ganye.
Ko kuma muyi biyu babu, ni aganona abin da za ka yi shi
ne ka raba kafa. Kana neman taimalon wadwnnan
mutane bisa gagarumin aikin da ke gabanka na shiga
gidan Boka Shamzabul Azwas don dakko yarinya Alfila, da
kuma batun zuwa naiman Sadauko Awaisu, da wadannan
'yn mata

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment