Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana fafatawa da cikin garin
haluf ya san irinsu sarki sahibul hairi basa faduwa da wuri
sai dubunnan mazaje sun fadi abin tambayar a nan shine
shin har yanzu ana nan ana fafatawar ko kuwa an gama?
Haluf ya tuna cewa idan fa yace zai bi sahun maigidansa
kuma aka gane cewa tafiyarsu daya shima sunansa gawa
nan fa hankalinsaya kara dugunzuma musamman da ya
tuna cewa shifa bakin fata ne duk inda ya shiga a cikin

birnin Askandariyya ansan cewa shi bawa ne donhaka
kamashi za ayi kawai acigaba da bautar dashi
haluf na nan zaune cikin tunanin mafita kawai sai ya
hango wadansu dakaru bisa dawakai kimanin su dari uku
bisa dawakai a tafe suna kewaye wani keken doki
cikin firgici bawa haluf ya mike tsaye zumbur jikinsa na
karkarwa yana tunanin ya gudu ko ya tsaya
shidai yasan cewa wancan ayari sun hangoshi don haka
ma inyace zai gudu ai bashi da mafita don zasu iya kure
masa gudu bisa wannan daliline haluf ya rungumi
kaddara ya tsaya cak a waje daya yana jiran karasowar
ayarin inyaso kome zai faru ya faru
lokacinda ayarin ya iso daf da haluf sai sukaja tunga suka
tsaya cak a gabansa kawai saiyaga an bude labulen keken
dokin nan take wata kyakkyawar mace ta leko da fuskarta
waje sukayi arba kallo daya haluf yayiwa matar yasan
cewa mai sarautace saboda irin tufafin dake jikinta da
kuma sarka, da awarwaron dake jikinta
matar ta kurawa bawa haluf idanu tana mai murmushi a
gareshi tace yakai wannan bakin fata yaya akayi kazo
wannan gari namu kuma menene dalilin da yasa ka tsaya
a nan baka shiga garin ba ka sani cewa a cikin birninmu
gaba daya babu bakin fata koda guda daya kasancewar
mijina ya tsaneku ni kuma a duniya babu abinda nake
sha awa sama da na ajiye bawa baki ina kallonsa yana
min hidima
sa adda bawa haluf yaji wannan tambaya saiya risina
cikin biyayya yace yake wannan ma abociyar kyau kiyi
sani cewa a shirye nake na baki amsar tambayoyin da
kikamin amma sai idan kin yi alkawari cewa zaki shigar
dani cikin birninku a boye kuma cikin sirri ba tare da
sarkinku ya sani ba kuma zaki boyeni har izuwa lokacinda
zan kammala abinda ya kawoni kasarku
yayin da taji wannan batu saita bushe da dariya tace
karka damu duk zanyi maka yadda kake so yanzu saika
sanar dani sunanka
bawa haluf yayi murmushi yace sunana haluf ibn bilal'
kyakkyawar ta maida masa da murmushi tace nikuma
sunana gimbiya SHUKURA ni ce matar sarki barusa guda
daya jal a duniya
koda gama fadin haka saita kira shugaban dakarun dake
jagorantar wannan tafiya wani zabgegen kato mai kirar
sadaukai wai shi jamhas tace dashi yakai jamhas kasan
bukatata wadda na dade a kan nemanta don cikar burin
rayuwata
wannan bakin bawa shine zai zamo sanadin cikar burina
abinda nake so dakai shine ka sanar da gaba daya jama ar
dake cikin wannan ayari namu cewa duk abinda suka
gani ya faru a yanzu tsakanina da wannan bawa suyi shiru
da bakinsu su bar komai a cikin sirri idan kuwa sirrina ya
fasu gaba dayansu zasu zama gawa
jamhas yayi murmushi yace an gama ya shugabata nan

take yabi dakarun gaba daya ya sanar dasu sakon gimbiya
sannan ya koma izuwa wajen barorinta mata suma ya
sanar dasu
sa adda ya komo ga gimbiya saita sake dubansa tace kuje
da haluf izuwa keken dokin barorina mata ka umarcesu
da suyi masa shiga irin tamu ta mata kuma su sa masa
suturar mata
koda haluf yaji haka sai hankalinsa ya tashi yace a ransa
yanzu shi za a mayar mace aikuwa ba za a iya batar da
kamanninsa ba koda anyi masa siffar mata mutum mai
natsuwa da kula zai iya ganeshi
har haluf yayi nufin yaki yarda da wannan sirri sai kuma
ya hakura domin bashi da wani zabi wanda yafi yabi
umarnin shukura ba tare da wani bata lokaci ba jamhas
yakai haluf izuwa cikin keken dokin nan ya sanar dasu
bukatar gimbiya
nan take sukabi umarni suka kama aiki lokacinda barori
mata suka kammala aikinsu sai suka dauko babban
madubi suka sa a gaban haluf ya kalli kansa a ciki
nanfa haluf ya cika da tsananin mamaki domin shi kansa
bai gane kansa ba dukda kasancewarsa bakin fata saiya
zamo farar fata kuma ya juye..
Please Ku dinga daurewa kuna comments ko kun fara
gajiya da littafinne??????
DUK DA kasancewarsa bakin fata saiyaga ya zamo farar
fata kuma ya juye zuwa kyakkyawar budurwa hatta
gashin kansa anmaidashi dogo kuma baki sidik mai kyalli
kirjinsa ya cika fam irin na mata ita kanta rigar da aka
sanya masa irinta sarakaice abar a tsaya a kalla
haluf ya dubi kansa da kyau sai yace a ransa lallai ashe
inda mace aka yoni da na kasance daya daga cikin
kyawawan duniya koda kuwa an barni a matsayin bakar
fata
koda aka kammala sauyawa haluf kamanni daga da
namiji izuwa ya mace sai jamhas ya tafi dashi izuwa
keken dokin gimbiye shukura tunkafin su karasa gareta ta
zubo musu idanu tana murmushi gami da yiwa haluf
wani irin kallo mai cike da alamomin tambaya bisa dole
ya tsargu cewa lallai wannan mace nada wata babbar
manufa a kansa ba tare da ya bata lokaci ba gimbiya
shukura ta umarci haluf daya shiga cikin keken dokinta
haluf ya waiga gaba da baya yaga gaba daya jama ar
ayarin shi suke kallo cikin tsananin mamaki kawai saiya
shiga cikin keken dokin ya zauna a gefe daya suna
fuskantar juna shida shukura
koda isowarsu bakin kofa sai suka iske kofar a balle a kasa
makera na ta aikin kokarin gyarata don mayar da ita inda
take koda ganin haka sai gimbiya tabada umarnin a tsaya
a gaban sarkin kofa A lokacin da sarkin kofa da wadansu
sababbin abokan aikinsa suka risina ga gimbiya suna
masu yi mata barka da zuwa gimbiya shukura ta dubi
sarkin kofa tace menene kuma ya faru naga kofar birnin

nan a balle shin giwace tayi mana wannan barnar?
Sarkin kofa ya risina yace ranki ya dade ai wannan ba
aikin giwa bane wani shahararren mayakine waishi sarki
sahibul hairi
yazo don ya rabamu da gatarin mu na sihiri yanzu haka
ya zama gawa domin sarki ya jefashi cikin gidan masifa
na karkashin kasa dake fada
koda jin wannan batu sai hankalin bawa haluf ya tashi bai
san sa adda gumi ya tsatstsafo masa ba nan da nan
fuskarsa ta cika da alamomin tashin hankali yayinda
gimbiya shukura ta dubi fuskar haluf ta lura da sabon
yanayin daya shiga sai kawai tayi murmushi tayi umarnin
aci gaba da tafiya
nan take kuwa aka kara nausawa cikin birnin
askandariyya lokacinda su gimbiya shukura suka iso fada
sai suka iske an gama walimar da ake yi har sarki ya mike
ya shiga gida jama a sun fara watsewa kowa na kama
gabansa
koda aka ga zuwan gimbiya sai aka rabe aka bata hanya
kuma ana kwasar gaisuwa gaba daya dawakai suka iso
wajen tsayuwarsu aka tsaida su sannan su gimbiya da
bakuwarta suka fara gitowa daga cikin keken doki amma
bakuwar tasha lullubi ba a iya gane ko wacece nan dai su
gimbiya suka shige izuwa cikin gidan sarautar kuyanginta
da barorinta na take mata baya su kuwa su jamhas sai
suka watse koya ya tafi izuwa nasa gidan
A ka ida duk sa adda gimbiya shukura tayi tafiya ta dawo
saita aikawa da sarki cewar ta dawo yana jin haka zai tako
da kafarsa yazo har turakarta su zauna ta bashi labarin
abubuwan da suka faru yayin tafiyarta da dawowarta in
banda irin wannan lokaci sarki barusa baya zuwa
bangaren gimbiya shukura
A wannan karon kuwa sai al amarin ya sauya domin tana
shiga cikin turakarta bata zauna hutawa ba sai kawai ta
tafi izuwa bangaren da kanta amma kafin ta tafi ta umarci
kuyangi dasu yiwa bawa haluf wanka su cire masa tufafin
da aka sa masa na mata a takaice dai adawo masa da
siffarsa ta dai dai kamar yadda yake a matsayinsa na da
namiji
sarki barusa ya kishingide a cikin turakarsa cikin nishadi
yana hutawa kawai sai yaga gimbiya shukura ta taho
gareshi cikin tsananin mamaki ya mike tsaye ya tareta
cikin tsananin farin ciki suna annashawa gaba dayansu
A duniya babu abinda sarki barusa keso sama da gimbiya
shukura don haka ko kadan baya son abinda zai bata
mata rai komai kankantarsa
sarki barusa ya dubi gimbiya shukura cikin murmushi
yace yake abarkaunata yau kuma menene dalilinda ta
hanaki turo a sanar dani dawowarki domin na taho
turakarki mu zauna kamar yadda muka saba?
Koda jin wannan tambaya saita maida masa martanin
murmushin tace yakai rabin raina rabin jikina kayi sani

cewa ba komai bane ya haddasa hakan ba face tsabar
farin ciki domin wannan karon nazo ma ka da labari mai
dadi
ka sani cewa a wannan tafiya da nayi na ziyarci wani
mashahurin boka wanda ya bani magani yace indai na
sha wannan magani lallai zan samu ciki dakai na haihu a
cikin shekara guda
koda barusa yaji haka saiya cika da farin ciki ya sake
kankame shukura a kirjinsa yana dariyar murna
yau shekara goma sha biyar kenan da yin auran gmbiya
shukura da sarki barusa amma basu taba samun haihuwa
ba bayan shekara daya da yin auransu sukaga basu samu
juna biyu ba sai hankalinsu ya dugunzuma suka bazama
neman magani amma ba a dace ba
saboda ganin yadda barusa ya damu matuka da neman
haihuwa saita bashi shawarar ya sake yin wani auren ya
gani domin babu mamaki matsalar daga gareta ne da
farko da barusa yaki yarda da wannan shawara sbd
sonda yake mata amma data matsa saiya amince saida
sarki barusa ya auri mata goma sha daya lokaci guda
amma da aka shekara yaga babu haihuwa duk ya koresu
ya rungumi kaddara
017. SARKIN SARAKAI BOOK1
.
TUN daga wannan rana shukura ta cigaba da yin tafiye
tafiye izuwa kasa kasa da ziyarar manyan bokayen duniya
akan neman masalaha
ranar da taje wajen wani mashahurin boka waishi
KUMATU saiya yi bincike ya gano cewa matsalar
haihuwarna tare da sarki barusa har abada bazai taba
haihuwa ba
ita kuma gimbiya shukura bazaata taba samun juna biyu
ba face ta kwanta da namiji saurayi wanda shekarunsa
basu kai talatinba wanda bai taba tarawa da ya mace ba
kuma doleneya kasance bakin fata
lokacinda gimbiya shukura taji wannan batu saita kamu
da tsananin bakin ciki ta fashe da kuka saida ta dade tana
kuka sannan tayi shiru ta dago kai tana mai duban boka
kumatu hawaye na zuba a idonta.yace yakai wannan
boka ina sonka sanar dani yadda zan gane saurayi mai
wadannan suffofi duk sa ar da na hadu dashi
boka kumatu yace duk ranar da kika hadu da wannan
saurayi kina yin arba dashi zakiji ya kwanta miki a rai ma
ana nan take zakiji sonsa to lallai in kikaji haka sine kadai
saurayinda zaki tara dashi ki samu haihuwa in kuwa ba
hakaba harki mutu ba ke ba samun da
gimbiya shukura bata da wani buri wanda yafi ta haifi
danda zai gaji mijinta wato sarki barusa domin ta san
cewa duk ranar da sarki barusa ya fadi ya mutu dolene ta
bar gidan sarautar domin wanine daban daga cikin
fadawansa zai karbi mulkin
bayan gimbiya shukura da sarki barusa sun gama murnar

wanann labari datazo dashi sai tayi masa sallama akan
cewa zata tafi dakinta ta kwanta domin ta huta gajiyar
tafiya
ba tare da gardamar komaiba yayi mata izinin tafiya,
lokacinda gimbiya shukura ta iso cikin falon turakarta ta
iske bawa haluf a zaune an caba masa ado kyawunsa
yakara baiyana kururu a baiyane saita kamu da matukar
sha awarsa
kai tsaye ta nufo inda yake da zuwa saita yunkura da
nufin ta rungumeshi cikin tsananin tsoro ya zame jikinsa
ya mike tsaye ya koma can gefe daya ya dubeta cikin
biyayya yace haba ya shugabata shin kin mantane cewar
ke matar sarki ce sokike a tsireni idan aka kamani da
laifin yin wani abu dake?
Sa adda taji wannan batu saita kyalkyale da dariya sannan
tace yakai wannan ma abocin kyau da kwarjini ka saki
jikinka ka sani cewa duk abinda zamuyi a nan babu mai
ganinmu yanzu dai kafin wani abu ya wakana a
tsakaninmu ina son ka amsa min tambayoyin nan guda
biyu da nayi maka tun farkon haduwarmu'
kodajin haka sai haluf ya kirkiri karya ya shara mata yace
ai shi bawane ya gudo daga hannun ubangidansa da ga
can wata kasa da ake kira SHUBUR kuma ba komai bane
ya sa ya gudo ba sai don tsananin aikin wahalar da ake sa
shiyi kullum
lokacinda ya gama wannan jawabi sai gimbiya shukura ta
dubeshi ta kyallkyale da dariya tace haba dan samari ka
dubeni da kyau kai kasan cewa ni ba yarinya bace karama
kuma ina da kaifin tunani da lura ai fatar jikinta mutum
ya duba ya san cewa a dduk inda kake baka shan waahala
tun da dai ba zaka gaya min gaskiya ba ni yanzu zan sanar
dakai ko kai waye
.
Yakai haluf ka sani cewa tundazu da muka dawo gida
kafin naje ga mijina saida na shiga cikin wani daki na na
sihiri inda nake tafiyar da harkokin sihirina yi bincikena
na gano cewa kazo wannan birni namu ne tare da
maigidanka sarki sahibul hairi na birnin misra domin ya
rabamu da gatarinmu na sihiri sbd da wannan gatari ne
kadai zai iya balle kofar gidan boka SHAMZUBUL AZWAS
wanda ke can tsuburin tekun bahar zallus
domin ya dauko karamar yarinya Alfila wadda ta kasance
yace ga wani gagarumin sadauki waishi Awaisu
yakai haluf kayi sani cewa nima na dade ina neman
wannan yarinya alfila na rasa yadda zanyi na sameta
saboda na kwashe sirrikan tsafin dake jikinta na dawo
dasu jikina don cika burina na biyu a duniya
burina na farko shine na haifi da wanda zai gaji sarautar
birnin Askandariyya bincike ya nuna mini cewa kaine
kadai namijin da zan kwanta dashi na samu haihuwa don
haka ina bukatar hadin kanka ayanzu
sa adda shukura tazo nan a zancenta saitaga hawaye na

zuba a idanun bawa haluf al amarinda ya matukar bata
mamaki kenan
ta dubeshi tace kai kuwa menene dalilin zubarda wannan
hawaye a idanunka? Haluf yace aini yanzu bani da sauran
buri a duniya face mutuwa tunda babban masoyina
mutumin da nafi shakuwa dashi fiye da kowa babu shi
wato sahibul hairi naji dazu sarkin kofa yana bayanin
cewa an jefa shi cikin dakin masifa na karkashin kasa ya
hallaka bisa wannan dalili nake ganin cewa rayuwata bata
da sauran amfani don haka kashe kaina zanyi
koda gama fadin haka sai bawa haluf ya sa hannu cikin
rigarsa ya dauko wata zuka ya daga sama da nufin ya
caka a cikinsa aman sai gimbiya shukura tadubi
hannunsa da kwayar idanta take wata irin iska mai karfi
ta rike hannun haluf ya kasa cakawa kawai saiji yayi an
fisge waukar daga hannunsa anyi jifa da ita can gefe cikin
tsananin firgici da mamaki haluf ya zauna kasa dirshan
yana mai kallon gimbiya shukura ita kuwa saitayi
murmushi ta tako kafafunta tazo daf dashi ta tsugunna
suka fuskanci juna tace
GIMBIYA SHUKURA tacigaba da cewa
aibazan bari ka mutu ba face na cika burina dakai ka
kwantar da hankalinka ka sani cewa maigidanka sarki
sahibul hairii na nan a raye bai mutuba.
Yanzun nan zan nuna maka zahiri ka gani,
gama fadin haka keda wuya saitayi nuni da dan yatsanta
guda izuwa jikin bango take wani irin haske ya fito daga
cikin dan yatsanta ya dira a jikin bangon saiga hoton
sahibul hairi kwance a sume cikin dakin nan na maridai a
tsakiyar gawarwakin maridan A lokacinne ya farfado daga
dogon suman da yayi ya mike ya zauna da kyar yana ta
faman haki kamar zai mutu.
Ko ina a jikinsa rauni ne yai kaca kaca da jini
gimbiya shukura ta dubi bawa haluf tace kaga halin da
maigidanka ke ciki akwai dakuna goma sha biyu kowanne
dakina dauke da masifa iri iri masifunda suke dakunan
gaba sun ninka na baya yanzu ya wuce dakuna biyu saura
goma a gabansa.
Idan har ya wuce ta cikin ragowar dakunan goma yana
raye yaci jarrabawata, donhaka zan taimaka masa mu
sace gatarin sihiri tare mu tafi izuwa gidan boka
shamzubul Azwas dan dauko yarinya Alfila.
Abinda nake soka gane shine zamu hada karfi da karfe ne
domin nida shi kowa ya biya bukatarsa amma duk
wannan zata farune idan ka bani hadin kai ka sadu dani
yanzu'
'lokacinda haluf yaji wannan batu sai hankalinsa ya tashi
fiye da ko yaushe ya rasa abinda zaice kawai saiya kurawa
gimbiya shukura idanu yana mai al ajabin al amarinta
.
Wannan shine abinda ya faru tsakanin gimbiya shukura
da bawa haluf bayan ta sa an sauya masa kamanni an

shigar dashi ckin birnin askandariyya ba tareda sanin
sarki barusaba
++ ++
Al'amarin jarumi uban jarumai kuwa wato sahibul hairi
lokacinda ya farfado daga suman da yayi ya tsinci kansa
cikin tsakiyar gawarwakin maridannan guda dubu yaga
har yanzu gashi yana numfashi bai mutuba sai ya cika da
mamaki kuma ya shiga tunanin zuci yace a ransa.
'' wannan fa shine mataki na fardo da zanbi don biyan
burina Amma gashi bani da tabbacin zan kai gaci
yaushene zan samu nasarar daukar gatarin sihiri a cikin
wannan gidan sarautar sannan na tafi gidan boka
shamzubul azwas don dauko yarinya alfila na tabbata
cewa masifar dake can fadar boka shamzubul azwas ta
ninka wacce ke nan sau dubu
idan ma na sami nasarar dauko Alfila yay tafiyarmu zata
kasance nida sadauki Awaisu don neman wadannan 'yan
matan uku wadanda zan Aura na cika burina na duniya.
Shin zamu sami nasarar ganin yan matan kuwa Alhalin
babu wanda yasan a inda suke?
Koda sarki sahibul hairi yazonan a tunaninsa sai yaji
nadama tazo masa bisa gagarumin aikin daya daukowa
kansa nan take zuciyarsa ta karaya ya fara aiyanawa a
ransa cewa lallai a cikin wannan tafarki zai rasa
rayuwarsa,
gwarama ace ya rungumi kaddara ya zauna da talaucinsa
har ajalinsa ya riskeshi...
¤+++++++¤
SHIN BAWA HALUF ZAI AMINCE YA BIYAWA GIMBIYA
SHUKURA BUKATARTA?
.
SHIN SARKI SAHIBUL HAIRI ZAI IYA SHALLAKE MASIFUN
DAKE CIKIN RAGOWAR WADANNAN DAKUNA GUDA
GOMA?
.
INA LABARIN GALADIMA AMINUL HAS WANDA SARKI
SAHIBUL HAIRI YABAR MASA RIKON KASA, KUMA YA
KASANCE A CIKIN TASHIN HANKALIN MAHASSADA
.
marubucin yace mu hadu a SARKIN SARAKAI kashi na
biyu donjin ci gaban wannan kasaitaccen labari. anan
Nake cewa mu hadu a cikin littafi na biyu domin jin
yadda zata kasance a wannan kasaitaccen labari na
ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI KANO.

SARKIN SARAKAI
Littafi na biyu 2
Abdulaziz Sani m gini
Shuraih Usman
A.KA 99%

Daga:- www.hausaebooks.cf
http://keffiansonline.cf

.
BAYAN SARKI sahibul hairi ya sami karayar zuci bisa burin
dake gabansa na zama sarkin sarakai a cikin dakin
maridai saiya sake bajewa a kasa yana mai cigaba da
tunanin rayuwar daya tsinci kansa a ciki. Sahibul hairi ya
tuno da irin bakaken maganganun da sauran sarakuna
abokansa suke aiko masa dasu gamida habaici da gori
akan cewa' ya talauce bashi da cin yau bare na gobe
kuma bashi da lafiya tunda ya kasa aure. Ya sake tunowa
da yadda ya baro kasarsa bayan ya baiyana sirrin abinda
ya fito nema kuma kowa ya sani haka kuma ya tuno da
irin wahalar da ya sha a cikin wadannan dakuna biyu
dake karkashin kasa a cikin masarautar sarki barusa koda
yazo nan a tunaninsa sai zuciyarsa ta kama tafarfasa nan
take yaji wani irin kwarin gwiwa ya shigeshi dukkan tsoro
da fargaba suka yaye daga cikin zuciyarsa kawai saiya
mike tsaye ya tunkari kofar da zata shigar dashi izuwa
daki na uku.
Cikin zafin nama ya banke kofar da karfin tsiya take kofar
ta rufta ciki ta fadi kasa koda yayi arba da abindake cikin
dakin saiya kame tamkar gunki saboda tsananin firgita ba
wani abu bane sarki sahibul hairi yayi arba dashi a cikin
wannan daki na uku ba face wata murtukekiyar macijiya
mai kawuna dari da daya idan macijiyar ta bude
bakunanta duka babu abinda mutum ke gani a ciki face
kibiyoyin wuta haka kuma a cikin kowanne baki akwai
wani irin zarkalelen harshe mai tsananin karfi tamkar
zabira kowanne kai guda daya na macijiyar yakai kamu
dari haka shima wannan haske dake cikin bakin. Sa adda
macijiyar mai kawuna dari da dayataga sahibul hairi ya

kame a gabanta tamkar gunki sai itama ta tsaya cak tana
kallonsa kawai jira take yayi kyakkyawan motsi ta
kaddamar dashi tsawon dakiku sittin dayansu bai motsa
ba sarki sahibul hairi ya san cewa bai isa ya koma da baya
ba haka kuma bai isa ya wuce gaba ba don haka ya
tabbatar da cewa yana cikin TSAKA MAI WUYA domin
gabansa tsinine bayansa kuma siyaki daga can sai wata
zuciyar tace dashi'' Kai jarumi uban jarumai ita fa masifa
kafin tazo ne ake gudunta amma idan ta riga tazo saidai a
rungumeta ayi daya daga cikin biyu wato ko kai ko ita'
koda gama wannan tunani sai sahibul hairi yayi kukan
kura ya afkawa macijiyar da nufin ya dankara mata sara
nan take ta mako masa kanta guda ya makashi da jikin
bango saboda karfin dukan saida bangon dakin ya burma
ya fitar da shatar gaba daya surar jikinsa ya manne a
cikin ginin tsananin zafi da zugin da yaji kuwa sai da jiri
ya debeshi yaga taurarin wuya a idonsa koda macijiyar
taga ya manne a cikin garu saita jefa jelarta a karo na
biyu ta fincikoshi da karfin tsiya sannan ta fara
kanannade shi saita matse shita ragargaza kasusuwan
jikinsa. Tun a farkon lokacinda macijiyar ta fara
kanannadeshi sai yaji ya matsu ainun tamkar an daureshi
da sarkar karfe murtukekiya nan fa hankalinsa ya
dugunzuma domin ya tabbatar da cewa idan fa macijiyar
nan ta gama kanannade shi mutuwa zaiyi don kashin
dake jikinsa saiya karye hakika wata masifar na iya sa
mutum ya yi abinda bai taba tsammanin cewa zai iya ba a
dai dai lokacinda macijiyar ke daf da gama kanannade
wuyan sahibul hairi ne kawai saiya takarkare iya karfinsa
ya buda jikin macijiyar da karfin tsiya a wannan lokaci
inda mutum na nan yaga yanda kwanjin sahibul hairi ya
ciko da yadda jijiyoyin jikinsa suka tattashi sukayi burdin
burdin sai yayi tsammanin cewa jikin dutse gareshi karfin
buda jikin macijiyar ne yasa macijiyar taji kamar za a
yagata ba shiri ta warware jikinta daga nasa ta sake shi
amma kafin yayi wani yunkuri ta bude bakunanta duk ta
fara watso masa kibiyoyin wuta bisa mamaki sai yaga duk
kibiyar data sauka a jikinsa saita kasa hudashi ta fadi kasa
kawai abinda bai sani ba shine wannan naman zakin da
yaci a wancan dakin na farko shine ya bashi wannan
kariya amma ba karfin sihirinsa ba lokacinda macijiyar
taga cewa kibiyoyinta na wuta sun kasa yin tasiri a kan
sahibul hairi saita kara fito da harsunanta guda dari da
daya duka ta watso masa su da nufin ta daddatsashi
gunduwa gunduwa duk harshein da ya bugi jikinsa sai
kaji kal kamar karfe da karfe ne suka hadu amma ko
kwarzane jikinsa baiyi ba nan fa aka ci gaba da masifaffen
fada ya zamana cewa macijiyar na dukan jikin sahibul
hairi da harsunanta shi kuma yana saran harsunan da
takobin hannunsa sai da aka shafe sa'a guda ana wannan
artabu amma dayansu bai sami nasara ba da kanta
macijiyar taja da baya ta tsaya cak aka ci gaba da kallon

kallo ita tana huci shikuma yana haki hakika wannan
macijiyar tasan cewa yau ta hadu da iblishin bil adama
domin a tarihin rayuwarta tunda aka ajiyeta acikin
wannan daki fiye da shekaru talatin baya ko mutum dubu
aka watso mata a cikin dakika guda take hallaka su gaba
daya amma yau ga bil adama daya kwal ya gagareta
lokaci guda suka sake afkowa juna wannan karon dai
kokarin da macijiyar takeyi shine ta hadiye sarki sahibul
hairi da daya daga cikin kawunan nata koda ya fuskanci
manufarta saiyayi ta zulle da gocewa yana kai mata duka
hannu da kafa gami da kai mata sara.......
Yauba yawa amma Ku Tara gobe idan Allah yakaimu
Koda sarki sahibul hairi ya fuskanci manufar wannan
macijiyar sai yayi ta zulle da goce goce yana kaimata
duka da hannu da kafa gami da kai ma ta sara ita kuwa ta
dinga fyada masa jelarta kafin wani lokaci duk su biyun
sunji jiki haka dai aka cigaba da wannan gumurzun har
izuwa tsawon wata sa'a gudan Ana cikin hakane sarki
sahibul hairi ya shammaci macijiyar nan ya soki idonta
guda da tsinin takobinsa faruwar hakan keda wuya sai
ruwan idon ya fashe yace tus! Kamar an fasa kwan jimina
saiko ruwan jini yata kwarara tamkar teku ta balle
ammam saboda naci saida macijiyar taci gaba da kokarin
hadiye shi Abinda sahibul hairi ya lura dashi shine kanda
wannan ido ke jiki bashi da kuzari kamar sauran
kawunan koda ya lura da haka sai yaci gaba da fas a
sauran kawunan na jikin sauran kawunan dama a jikin
kowanne kan idanuwa biyune idan sarki sahibul hairi ya
sami nasarar fasa idanuwa biyu saikaga wannan kai ya
daina tasiri ya fadi kasa ya jabe tamkar jikakken tsumma
yayinda sarki sahibul hairi yaga ya samo lagon macijiyar
saiyaci gaba da fasa mata idanu har saida yafasa gaba
daya idanun nan take macijiyar ta baje kasa matacciya
jini kuwa ya rinka fita a jikinta saida ya kusan shanye
sahibul hairi yazo masa iya kirji kaikace a cikin kogi aka
tsomashi A sannanne shima ya langabe a jikin garu ya
kama nishin gajiya koda ya dubi jikinsa sai yaga ko ina yai
burdin burdin wato jini ya taru masa sakamakon dukan
da macijiyar nan ta ringa yi masa tana fyada shi da kasa
da kawunanta da jelarta saida sarki sahibul hairi ya
kwana ya yini yana jinyar jikinsa a cikin wannan daki na
muguwar macijiyar sannan ya sami kwarin jikinsa naman
macijiyar ne ya zamo abincinsa a iya tsawon wannan
lokaci bayan ya dawo cikin hayyacinsa sosai kuma ya
gama jinyar jikinsa sai ya tunkari kofa ta gaba wato daki
na hudu kamar yadda ya banke kofa ta uku haka ya
banke kofa ta hudu kawai ya kunna kai ciki shi dai
wannan daki na hudu ya sha ban ban da sauran dakunan
uku da ya wuce domin shi ya kasance mai tsananin tsawo
da babu alamar karshe sannan kuma babu wada taccen
haske a cikinsa daga shigar sahibul hairi cikin wannan
daki sai ya dinga jiyo wani irin gurnani mai ban tsoro irin

wanda bai taba ji ba a rayuwarsa koda jin wannan
gurnani sai sarki sahibul hairi ya tsaya chak yana waige
waige da nazarin gurnanin kawai sai sahibul hairi ya daga
takobinsa sama ya riketa da hannu biyu yaci gaba da
tafiya abinsa a hankali yana mai ci gaba da waige waige
da dube dubensa kwatsam sai ya tsinci kansa a tsakiyar
wani makeken fili wanda bashi da duhu ko kadan kuma
babu alamar wata kofa da za a fita isowarsa wannan

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment