Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayan dana ga yaata
alfila
sa adda ta kwanta a kaina tana kuka sai hankalina ya
gushe sakamakon azabar da shukura tayi mini ta matse
mini jiki da sarkar sihiri
har kafata ta karye
koda fadin haka sai duk suka dubi kafar awaisu sukaga
har ta kumbura nan take
sarki ya kwallawa wani hadiminsa kira ya shigo cikin
turakar
da shigowar hadimin sai sarki ya daaka masa tsawa yace
duk ina dakarun gidan nan suke har wata matsafiya ta
shigo ta kamani ta daureni
basu sabi ba
hadimin ya risina yace ya shugabana ai mu bamu ga
kowa ya shigo gidan nan
ba kuma kullum kai muke gani kana harkokinka kamar
yadda ka saba
koda jin haka sai sarki ya sake cika da mamaki ya tsinke
da al amarin hatsabibancin gimbiya
shukura
ba tare da bata lokaci ba aka tura aka kirawo likita yazo
ya gyara karayar sadauki awaisu sannan likitan yaje ya
duba
sahibul hairi da bawa haluf suma yayi musu magani
aka kaisu masauki mai kyau, sai da su sahibul hairi
suka kwana goma sha tara suna jinya sannan suka sami
lafiyar jikinsu sosai
A wannan rana ne sarki yasa aka yi shela gaba daya jama
ar
garin suka taru a fada
nan take sarki ya baiwa jama alabarin sarki sahibul hairi
tun daga lokacinda ya baro
kasarsa domin neman matsayi da daukaka har izuwa
lokacin
da ya hadu da gimbiya humaira a can garinsu suka
dunguma suka tafi fadar shamzubul azwas da duk irin
fafatawar da sukayi har suka iso
wannan gari suka yi bakin gumurzu da gimbiya shukura
har ta sake guduwa tare da
Alfila
lokacin da sarki ya gama bayar da wannan labari sai gaba

dayan
mutanen garin jikinsu yayi sanyi nan take kowa yayi
imani da addinin musulunci
sarki sahibul hairi ne ya karanta kalmar shahada
sannan gaba dayan jama ar garin suka maimaita
farin ciki a wajen gimbiya humaira a wannan rana ba zai
misaltuba
bayan an kaddamar da addinin musulunci ne a kasar
humaira ta shiga koyar da jama a yadda zasu
bautawa allah sai da ta shafe kwana bakwai tana
wannan hidima sannan aka sami masu basira suka
lakanci abin da ta koya musu suma suka dinga koyar
da wasu
A wannan lokacine sadauki awaisu, sahibul hairi da bawa
haluf suka yi zama na musamman suka shiga tattaunawa
akan yadda zasu tafi neman yarinya alfila domin suyi
gumurzu na karshe da gimbiya
shukura
suga bayanta a sannan ne sarki sahibul hairi zai sami
damar
komawa kasarsa ya jaddada addinin musulunci ga jama
arsa daga nan kuma sai su tafi izuwa garinsu gimbiya
humaira domin ya nemi auranta a wajan iyayanta
sahibul hairi ya dubi humaira cikin alamun damuwa yace
yake abar kaunata yanzu tayaya kike ganin zamu iya
zuwa inda shukura takai alfila harmu yaketa mu karbo
alfila?
Sa adda humaira taji wannan tambaya sai tayi ajiyar
zuciya tace babu wanda zai iya yi mana jagora izuwa
wannan tafiya face Allah
domin don haka zamu rokeshi akan ya taimakemu kuma
ya bamu sa'a bisa abindake gabanmu , bawa haluf yai
ajiyar zuciya yace a gaskiya ni dai na tsorata
da al amarin gimbiya shukura kuma ina tsoron karonmu
da ita na biyu domin
na tabbatar dacewa shirin da zatayi yanzu kanmu sai ya
ninka na baya sau dari
AA Misau Kenan Sunana, Sa adda humaira taji wannan
batu
sai tayi murmushi tace ai duk shirin da shukura zaatayi
ba zata sami nasara akanmu
ba
tunda dai mu akan tafarkin gaskiya muke ita kuwa akan
tafarkin karya take
duk abinda take takama dashi kafin ita anyi manyan
kafirai a duniya wadanda sukafita komai da komai, amma
a karshe sai da suka wulakanta suka zama mushe
ina tabbatar maka da cewa babu wani abu madawwami
face
Allah
Sarki guda daya wanda bashi da abokin tarayya
shine wanda ya halicci sammai da kassai da duk

abubuwan
dake cikinsu
kunga kenan shine mai ikon Tafiyar da mutane da aljanu
a doron kasa da izininsa ne kowa ke yin abinda ya ga
dama
idan Allah ya so ya kawar da mutum ko aljan take yake
kawar dashi sai dai kawai ayi masa jinkiri izuwa iyakar wa
adin da aka diba masa zaiyi a
duniya
lokacin da humaira tazo nan a zancenta sai taga sarki
sahibul hairi da sadauki awaisu sun fara hanmma
alamar cewa suna jin barci Don haka sai tayi shiru
ga barin zance tace ya kamata mu tsaya a nan sai wani
lokaci kuma idan mun sami dama saimu cigaba da
wannan labari
Kuma ku sani cewa a daren yau zanyi Addu a da rokon
Allah Akan yayi mana jagora bisa tafiyar da zamuyi
gobe don neman inda fadar gimbiya shukura take domin
mu yaketa mu kawar da ita sannan
mu karbi Alfila daga Hannunta
Koda jin haka sai murna ta kama sadauki Awaisu yace da
izinin ubangin musulunci saimun sami nasara kuma lallai
dani za ayi wannan tafiya
Sarki yace Ai nima dani za ayi wannan tafiya domin na
sami irin ladan da ake samu na JAHADI...
SARKI YACE AI NIMA DANI ZA AYI WANNAN TAFIYA
DOMIN NA SAMI IRIN LADAN DA AKE SAMU A JAHADI
humaira ta dubi sarki tace to yanzu idan ka bimu izuwa
wannan tafiya wane ne kuma zaici gaba da mulkin jama
arka
kayi hakuri ka zauna ka jagoranci jama arka har Allah ya
dawo da sadauki awaisu
lafiya mu kuwa a can zamu rabu dasu awaisu mu tafi
birnin Misra domin sarki sahibul hairi ya jaddada
addinin musulunci a can, da wannan furuci aka tashi
daga taron kowa ya je ya kwanta
Kashe gari da sassafe kuwa humaira , sahibul hairi da
bawa haluf da sadauki
awasiu sukayi gagarumar shigar yaki sannan suka yi
bankwana da sarki da sauran jama ar gari kuma suka
bukaci jama a da su tayasu da addu a bisa wannan
JAHADI da zasu tafi
koda jama ar gari suka ga su humaira zasu tafi su barsu
sai suka kama kuka saboda sabon da sukayi dasu
al amarinda ya karya zuciyar su humaira kenan suma
suka kama kuka
nI kaina AA Misau Saida na Tausaya Musu, Nan dai suka yi
musu sallama sarki ya sa aka kawo dawakai ingarmu
guda hudu gami da isashshen guzuri yace ga nawa
gudumawar
humaira ta dubi sarki tayi murmushi sannan tace mun
gode da wannan kyauta taka

amma bama bukatar wadannan dawakai kamar yadda
Allah ya kawomu birninka a kafafunmu muka shafe
tafiyar watanni a cikin kwanaki kadan haka Allah zai
kaimu inda Gimbiya shukura take
wannan guzuri dai daka bamu na abinci shi muke da
bukata
koda gama fadin haka sai kowannansu ya karbi jakar
guzurin ya rataya a bayansa sannan suka kama hanya
suka fice daga cikin garin tun jama a na hangensu har
suka kule
su humaira suka wanzu suna masu tafiya dare
da rana cikin karanta addu l'i na daurin kasa da neman
taimakon Allah akan ya kaisu inda fadar Gimbiya shukura
take
da yake Allah maji rokon bawansa ne nan da nan kuwa su
humaira suka shafe tafiyar watanni da dama a cikin
kwanaki kadan
su shiga nan su fita can wani lokacin ma sai su kera kwale
kwale sun shiga sun ratsa ta cikin koguna da koramai
wani iko na Allah tunda suka fara tafiyar sai wani
kankanin tsuntsu ya zamo tamkar jagoransu
duk inda tsuntsun yabi nan suke bi dalili kuwa shine
humaira tayi mafarki da wannan tsuntsun tun kafin ya
baiyana garesu kuma a cikin
mafarkin tsuntsun yayi magana da ita yace
duk inda kukaga nabi kuma kubi insha Allahu zan kaiku
fadar Shukura
Wata rana kwatam sai suka hango wani katon gida akan
wani dogon tsauni a tsakiyar dokar daji
Girman gidan ya wuce misali domin ya ninka gidan boka
shamzubul azwas sau goma
tunda ga nesa su humaira suka tsaya suka yi cirko cirko
suna kallon gidan suka sha jinin jikinsu akan cewa lallai
wannan shine
fadar gimbiya shukura
bayan sun gama nazarin gidan sai humaira ta dubi
sahibul hairi, bawa haluf da
sadauki awaisu tace ku bini a baya duk inda na dauke
sawuna ku sa naku da
izinin Allah harmu shige cikin gidan can babu wanda zai
ganmu, da zarar mun tsinci kanmu a ciki kowa yayi iya
kokarinsa wajan kwatar kansa gami da neman tsari daga
Allah akan makiya
koda gama fadin haka sai humaira ta wuce gaba tana
karanta
wata addu'a ta musamman, sahibul hairi bawa halu da
awaisu, kuwa suka rinka bin sawunta kamar yadda ta
umarcesu
AA Misau Nake, haka dai suka ci gaba da tafiya har suka
hau kan tsaunin
da zuwansu gaban katon gidan sai suka ga dakarun
Aljanu sama da guda miliyan dubu daya sun yiwa gidan

kawanya
wasu a sama wasu a kasa
kuma gaba dayansu muninsu da kwarjininsu ya ninka na
wadancan aljanu da suka fafata dasu a garin su Awaisu
bisa mamaki sai su sahibul hairi sukaga sam aljanun basa
ganinsu
abinda ya basu matsala shine, kwata kwata babu kofa ko
taga a jikin gidan gaba daya bare su bude su shiga
koda ganin haka sai humaira ta dafa bangon gidan ta
karanta wata addu ar daban
take bangon ya tsage suka shiga ciki wohoho ! Da
shigarsu ciki suka tsinci kansu cikin Aljannar duniya
domin irin kayan
alatun da suka gani da kuma dukiya iri iri ko a tarihi basu
taba jin kamarsu ba domin sai dai a kwatanta yawanta da
karuna
sai da suka shafe sa a tara suna tafiya a cikin gidan suna
wuce
fadoji kala kala suka iso fadar karshe inda suka yi arba da
yarinya Alfila a cikin wata katuwar kwalba cike da ruwa
ko motsi batayi a ciki kamar gawa
dakarun aljanu da suka kewaye kwalbar suna tsaronta
sun kai su dubu saba'in
kuma girmansu da kwarjininsu ma ya ninka na aljanun
dake wajan gidan sau goma
sannan sai ga karagar mulki a gefe daya wacce aka kerata
da zallar lu'u 'u'u
babu kowa a kanta
koda humaira tayi arba da wannan kwalba wacce alfila ke
ciki sai ta zare takobinta karar
zare takobince tasa wadannan dakarun aljanu suka juyo
sukayi arba dasu
ai kuwa sai aljanun suka taso musu gaba daya suna wani
irin gurnani da ihu wanda ka iya sa mutum ya zautu ko ya
mutu nan take
ai kuwa suma su humaira sai suka kwala kabbara suka
tari Aljanun aka ruguntsume da azababben yaki
sai da aka kwana aka yini ana wannan yaki sannan
humaira ta sami nasarar saran wannan kwalbar sihiri
cikin kiran
Sunan Allah
take kwalbar ta fashe ruwan cikin kwalbar ya cika fadar
gaba daya
tamkar tekuce ta balle
koda ruwan ya lullube wadannan dakarun Aljanu sai
dukkaninsu suka zagwanye a cikinsu dabansu bai rayu ba
humaira ta tsamo Alfila daga cikin ruwan ta tofa mata
Addu'a
ta farfado daaga dogon suman da tayi sannan ta goyata a
bayanta
A sanna ne suka ji ihu da kururuwar gimbiya
shukura

tsulum sai gata ta baiyana a cikin ruwan tana sanye da
kayan yaki na bakin sulke kuma ta rike takubba guda biyu
humaira da shukura suka kurawa juna ido
sannan shukura tace yaune za ayita ta kare koni koke
kafin humaira ta budi baki ta maida raddi tunu shukura
ta afka musu su ukun da azababben yaki
nan fa ta zame musu alakakai suka rasa yadda zasuyi da
ita sai da suka sake shafe sa a bakwai ana wannan bakin
gumurzu
ya zamana cewa shukura ta yiwa dukkaninsu mugayen
raunika a jikinsu duk ta bazar dasu a kasa harda ita kanta
humairan babu mai iya mikewa tsaye
Amma banda Jarumi AA Misau hahaha A sannan ne
humaira ta sake yiwa Allah kirari irin wanda tayi masa a
wancan karon ai kuwa nan take ta sami wannan
gagarumin karfi ta dinga ragargazar shukura
har sai da ta daddatsa sassan jikinta filla filla A karshe
humaira ta yanke jiki ta fadi kasa
sai da suka kwana ashirin a cikin wannan gida suna jinyar
jikinsu sannan suka warware suka fita
cikin tsananin farin ciki sadauki awaisu ya karbi
yarsa Alfila ya koma garinsu
Sahibul hairi, bawa haluf da Humaira kuwa sai suka je
birnin misa aka kaddamar
da addinin musulunci sannan suka tafi garin su humaira
aka
daura auransu suka sake komawa birnin misra suka ci
gaba da rayuwa mai cike da farin ciki, bisa mamaki a
wannan lokaci sai arziki mai tarin yawa
ya samu ga sarki sahibul hairi da tarin daukaka a tsakanin
sarakunan dake nahiyar, ya zamo shine babban Sarki
kuma yaci gaba da yake yake na
jaddada addinin Islama har zuwa karshen Rayuwarsa !!!
ALHAMDULILLAH !!!
Bayan nan kuma sai Sadauki AA Misau ma aka daura
Auransa Da yarinya Alfila inda suka ci gaba da rayuwarsu
cikin jin dadi da kwanciyar hankali hahahahaha
------------------------------------------------Alhamdulillah Anan ne muka zo karshen Littafin sarkin
sarakai 1-5
dafatan littafin ya kayatar daku wanda AA Misau Ya
jagoranci typing dinshi,
sannankuma nake cewa ku huta lafiya
marubucin littafin
Abdul aziz sani madakin gini kado
typing AA Misau ke Magana
Nake cewa
saimun hadu daku
a cikin wani sabon littafin idan mai duka ya nupemu !!!
Signed AA Misau.....


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment