Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwantar mata da
hankali gami da bata tabbaci cewa Hurbas bazai ci
amanarsa ba. Lallai zai dawo masa da damarar bayan ya
kawo matar Shaharuz zaman ya kone gidansa.
Har su Saif suka gama binne shahidai suka koma gida bai
ga dawowar abokinsa Hurbas ba. Nan fa hankalinsa ya
dugunzuma ya kama wasu-wasin zuci. Da farko sai ya
fara tunani ya hau doki yabi bayan Hurbas, amma sai
wata zuciyar ta ce da shi.
"Haba sai wai shin shakkar me kake yi? Tun da kasan
Hurbas ba zai ha'in
ceka ba ai ba sai kabi bayansa ba. Ba shakka bai gama
abinda ya je yi bane shi yasa har yanzu bai dawo ba".
Haka dai Saif ya yi ta tunani har dare ya yi barci ya sace
shi bai sani ba.
Da tsakar dare Saif na bacci sai yaji ana luma masa
makami a ciki. Take makamin ya burma cikinsa ya burma
shimfidar gadon, jini yai tsartuwa.
Cikin kiran sunan Allah ya bude idanunsa da kyar, kawai
sai yaga Hurbas a tsaye a kansa yana yi masa murmushi
mugunta. Cikin tsananin mamaki da takaici Saif ya bude
baki ya ce, "ya kai abokina yanzu ashe zaka iya cin
amanata?"
Koda jin wannan tambaya sai Hurbas ya bushe da dariya,
sannan ya ce, "kayi hakuri ya aminina, ka gafarceni bisa
wannan cin amana da nayi maka, domin ba zan iya barin
daular da na gani ba a gidan Boka shaharuz zaman ba.
Tabbas na za6i duniya akan lahira..... Idan baka manta ba
ai dama na gaya maka cewa ina tsoran ranar da zan iya
cin amanarka, sabo da na san halinmu na aljanu bamu
da amana.
Da wannan furci nake maka bankwana. Ina fatan zaka
yafe min baza ka mutu da kullatata ba?".
Koda gama fadin hakan sai Saif ya ce, "ina damarata ta
yaki?"
Hurbas ya ce, "ai wannan damara ta zama tawa har
abada. Gata nan a jikina, da iata zanci gaba da yakar
musulmin duniya har sai na karar da su. In kuma ajali ya
riskeni kafin na cika burina tabbas dana ne zai gaji
wannan damara".
Koda Hurbas ya gama wannan jawabi sai ya 6ace 6at! Shi
kuwa Saif sai hawaye ya zubo masa ya ce, "tabbas babu
amana ga mara amana Allah ka sa amana ta ci abokina
kamar yadda ya cita.
Gama fadin haka ke da wuya sai Saif ya yi kalmar shahada
ya rasu.
Duk wannan abu da ya faru a wannan tsakar dare
tsakanin Saif da Hurbas babu wanda ya gani ko ya ji sai
da gari ya waye sai matar Saif da dansa suka shiga
turakarsa suka iske gawarsa.
----<<<<>>>>----
Al'amarin Hurbas kuwa, a wannan dare sai ya koma gurin
Harfiza suka ci gaba da sheke ayarsu. Hurbas ya zauna da
Harfiza har tsawan shekara goma, sa'adda ta haifi da aka
sa masa Shamzabul Azwas. Ranar da aka haifi wannan
yaro ne Harfiza ta kashe Hurbas ya yin da suke ta nishadi
da murnar wannan haihuwa. Wato sai ta shammace shi
ta burma masa wata wuka ta sihiri a cikinsa. Dama a
lokacin ya cire damarar nan ta yaki daga kugunsa ya ajiye
ta gefe guda. Nan take Hurbas ya sulale kasa yana kakarin
mutuwa.
Cikin tsananin dauriya ya dago kai ya dubi Harfiza ya ce,
"ya ke masoyiyata sabo da me za ki kasheni?"
Koda jin wannan tambaya sai Harfiza ta bushe da dariya
ta ce, "ai baka da sauran amfani a wajena tunda ka biya
min bukatata. Akan wana dalili zan ci gaba da zama dakai
na baka amanata alhalin na san cewa mu alajanu bamu
da amana? Shin ka manta cewa mahaifiyarka ta ci
amanar mahaifinka, ta kashe hsi, kai kuma ka ci amanar
abokinka ka kashe shi, nima tabbas nan gaba zaka iya cin
tawa amanar shi yasa na yanke hukuncin na kawar da kai
kafin ka kawar da ni.
Ni kam a yanzu na ci riba biyu, domin ka biya mini
bukatata, kuma ga shi na sami gadon wannan damara ta
yaki wacce dana zai gada."
Koda Harfiza tazo nan a zancenta sai nimfashin Hurbas ya
fara sarkewa. Cikin karfin hali ya dubeta ya ce, "tabbas
amana bata barin amana. Kema ki kiyayi bibiyar tawa
amanar."
Yana gama fadin haka sai komai na jikinsa ya sandare ya
daina motsi, wato ya zamo gawa.
Daga wannan rana Harfiza ta ci gaba da rainon danta har
ya fara girma, tama koyar dashi ilimin tsafi har ya iya duk
irin saihirin da Shahauz zaman ya iya.
Shamzabul Azwas ya taso sadauki, kuma azzalumi mara
imani. Nan da nan ya shahara a tsafi, har ma yaso yafi
uwarsa Harfiza sanin ilimin tsafi.
Tun bayan mutuwar Hurbas sai Harfiza ta 6oye wannan
damara ta yaki, kuma bata ta6a bawa Shamzabul Azwas
labarin mahaifinsa ba da yadda ya mutu.
Wata rana sai Shamzabul Azwas ya shiga binciken tarihin
rayuwar mahaifinsa a cikin madubin tsafi. Ai kuwa take
yaga duk irin aminantakar da ta kullu a tskaninsa da Saif
tun daga farkon haduwarsu har izuwa lokacin da suka yi
yaki da Boka Shaharuz zaman da kuma sa'adda da
Hurbas ya ci amanar Saif ya rabashi da damararsa ta yaki
yaje ya yi zina da Harfiza, sannan ya koma ya kashe Saif.
Shamzabul Azwas yaga yadda akai Harfiza ta sami cikinsa
har ta haifeshi, da kuma sa'adda ta kashe ubansa Hurbas
a daran da aka haifeshi.
Koda gama ganin wannan al'amari sai Shamzabul Azwas
ya fashe da matsanaicin kuka ya ce, " hakika mahaifiyata
ta ci amanata da ta 6oye mini wannan labari, dole ne
itama tabi bayan mahaifina".
Nan take Shamzabul Azwas ya mike tsaye ya fita daga
cikin dakinsa na tsafi ya wuce izuwa dakin mahaifiyarsa
Harfiza, inda ya isaketa zaune a kan gado tana kwalliya.
Cikin fara'a ya matsa gareta kamar zai rungumeta kawai
sai ya caka mata wukar sihiri a ciki.
Wannan wuka itace wadda ta kashe mahaifinsa da ita.
Cikin kalarin rai ta dubeshi ta ce, "me yasa ka kasheni ya
kai dana?"
Shamzabul Azwas ya ce, "sabo da kinci amanata, kuma
kinci amanar ubana. Lallai amana bata barin amana. Me
yasa baki bani labarin ubana ba? Me yasa baki ta6a yin
mini batun damararsa ta yaki ba? To ki sani cewa bayan
kin mutu zandauko wannan damara a duk inda kika
6oyeta in ci gaba da amfani da ita ina ruguza musulimci
da musulmai. Lallai sai na ciki burin Baka Shaharuz
zaman domin shi ya kamata ya zamo ubana na kwarai ba
Hurbas ba maci amana".
Lokacin da Shamzabul Azwas ya zo nan a cikin labarinsa,
sai yai shiru ga barin zancen. A lokacin ne ya ga Humaira
ta kura masa idanu tana zabga masa harara.
Shi kuwa sarki Sahibul Hairi, sabo da tsananin mamakin
labarin sai yai shiru yana juya al'amarin a ransa.
Shamzabul Azwas ya bushe da dariya ya ce, "ya ke
Humairat yanzu kin fahimci cewa ubana ne ya yaudari
kakanki ya ci amanarsa har yaga karshensa? To ku sani
cewa nima sai naga karshan dukkanin ma'abota addinin
musulinci. Kin rigaya kinji nasabata da wannan damara
wacca aslinta ta kakanki ce. Idan har zaki iya sai ki kar6i
abarki yanzu, idan ba za ki iya ba kuwa shi ke nan.
Ina tabbatar miki da ke da Sarki Sahibul Hairi ba za ku
ta6a cika burinku ba. Kuna ba za ku ta6a fita daga cikin
wannan fada tawa ba a raye. Nikam baku isa ku kasheni
ba muddin ina da wannan damarar yaki. Ku sani cewa
babu wani sirrin tsafi da bam malka baface na jikin
yarinya Alfila, kuma yau saura kwana arba'in nagama
dibar sirrin tsafin jikin na ta, don haka baku isa ku tsayar
da wannan aiki ba.
Koda gama wannan jawabi sai Humairat ta dakawa
Shamzabul Azwas tsawa ta ce, "kai tsohon kafuri karyarka
ta sha karya. Ka sani cewa babu mai kashewa da rayawa
face Ubangijin Musulinci, don haka kai baka isa ka kashe
mu ba face kwanan mu ya kare. Ka sani cewa duk
abubuwan da kake dogaro da su da izinin Allah suke
tasiri, idan babu izini ba za su yi tasiri ba. tabbas faduwar
gaba asarar namiji ce, don haka ko kadan bana tsoranka,
kuma bana shakkarka. Zan fafata da kai da zuciya daya,
idan ka kasheni zanyi shahada, idan na kasheka na rage
mugun iri doron kasa, kuma na karawa Musulinci karfi a
wannan nahiya tamu."
Koda jin wannan batu sai aljani Shamzabul Azwas ya
kyalkyale da mahaukaciyar dariya. Sannan ya ce, "ka
yarinya tsaya kiji, yadda kikayi imana da Ubangijin
Musulinci haka mu ma muka yi imani da shi. Amma fa ba
zamu fasa tsafi ba, kuma baza mu fasa morewa rayuwar
Duniya ba. Yadda zaki roki Ubangiji Musulinci bukata ya
biya miki ita, haka muma zamu rokeshi ya biya mama."
tabbas mun san gaskiya amma mun take tane dan
kwadayin duniya".
Kafin Humairai ta sake bu6e baki ta kara cewa wani abu
tuni Shamzabul Azwas ya daka tsalle ya dire a tsakiyarsu
ita da Sarki Sahibul Hairi. Nan fa ya fara kaimusu sara da
sukacikin tsananin zafin nama irin wanda basu ta6a gani
ba. Sabo da karfin saran sai ya zana cewa da kyar suke iya
karewa, ko martani basa iya maidawa. Tabbas jarumtakar
Shanzabul Azwas ta ninka ta Humairat da Sarki Sahibul
Hairi. Bambamcin a bayyane yake. Nan fa ya kuntata su
ya hana su sakat har takai cewza ya kadar da makamansu
daga hannunsu. Koda yaga babi makamai a hannunsu sai
shima ya yarda takobinsa da garkuwarsa. Nan fa ya fara
naushinsu yana bugunsu hannu da kafa. Abin ka da
naushi irin na aljanu, nan da nan ya lugwe-gwetasu, in ba
dan karfin addu'a ba da ma basu isa su tareshi ba, inda
matsalar take shi ne, kamar yadda suke addu'a shima
haka yake yinta.
Hakika Allah ya kasance mai hakuri da bayinsa, shi yasa
duk shegantakar da bawa zai yi sai ya ara masa rana ya yi
ta yi. Amma idan yaso sai ya kama shi a rana daya ya
raina kansa kamar yadda ya yiwa sarki Fir'auna sarkin
Misra.
A halin yanzu Allah ya arawa Shamzabul Azwas lokaci, shi
yasa yake kan sharafinsa, duk abinda yasa gabansa sai ya
sami nasara.
Lokacin da Shamzabul Azwas ya ci gaba da dukan su Sarki
Sahibul Hairi da Humairat, sai ya sumar da su suka zube
kasa wanwar babu mai nunfashin kirki a cikinsu.
Koda yaga ya sami wannan nasara sai ya kyalkayala
dariya mugunta, nan take ya yi tsafi, sai jikin Sarki Sahibul
Hairi da jaruma Humairat ya sandare, suka zamo
gumaka. Fatuwar hakan ke da wuya sai ya juya da baya
ya shiga wani daki na musamman inda yake tafi da
harkokin na tsafi. Burinsa shine ya kammala wannan tsafi
na cire sirrikan tsafi da ke jikin yarinya Alfila ya mai da su
cikin jikinsa.
Kash! Duk wannan nasara da aljani Shamzabul Azwas ya
samu akan su Sarki Sahibul Hairi ya yi tuya ya manta da
albasa. Dalili kuwa shi ne, Allah ya mantar da shi batun
Bawa Haluf wanda tun a farkon shigowarsu gadan ya fadi
sumamme. A she wannan gumurzu da akayi tsakanin
aljani Shamzabul Azwas da su Sarki Sahibul Hairi Bawa
Haluf na la6e a wani sako yana kallo jikinsa na
makyarkyata sabo da tsananin razana.
Bayan Shamzabul Azwas ya tsafance su Humairat sun
zama gumaka kuma ya shiga cikin dakin tsafinsa sai Bawa
Haluf ya shiga tunanin hanyar da zai ceci su Sarki Sahibul
Hairi, amma sai ya kasa yanke hulunci bisa abin da ya
kamata ya yi ya sake fadawa kogon tunani.
Wannan shi ne abin da ya faru da su Sarki Sahibul Haira
ya yin da suka sami damar shiga Fadar Aljni Shamzabul
Azwas dan Dauko Yarinya Alfila.
.
A CAN BIRNIN MISRA KUWA, BAYAN SU WAZIRI AKIYANU
SUN DAWO DAGA WAJAN Boka Shiburul Uzab sai suka
sake yin zama na musamman a cukin sirri domin su
tattauna akan yadda za su sami nasarar sato wannan Doki
na Aminul Has ba tare da sirrinsu ya tonu ba. Sao da suka
shafe sa'a biyar suna mahawara sannan daga karshe suka
tsaya akan shawara guda.
Shawarar kuwa ita ce za'a sato Dokin ne da duku-dukun
safiya sa'adda mai kula da bargar Dawakan ke baiwa
Dawakan Abinci. A ka'ida kullum kafin a baiwa Dawakan
Abinci sai an fita da su daga cikin birgarsu an sakesu su
dan yawata a harabar sai a mai da su cikin bargar sannan
sai a zuba musu Abincinsu.
Dabarar da aka shirya shi ne, a kwai wani babban
hadimin gidan sarautar wanda babu inda baya shiga a
gidan, ana kiransa da suna kumais. Tuni su Waziri sun
baiwa Kumai Dukiya mai yawa sun gaya masa bukatarsu
cewa suna so a sato wannan Doki na sarki Aminul Has.
Koda Kumais yaga an bashi dukiya irin wadda bai ta6a
mallaka ba a rayuwarsa, sai ya amince zai sato Dokin.
Nan take yasa aka nemo wani dokin daban, wanda
kamarsa daya da Dokin sarki. Hatta tswansu, kibarsu da
launin jikinsu dyk iri daya ne sak babu banbanci kai kace
tagwaye ne.
Da sassafe sai ya ja wannan Doki na karya ya shiga dashi
cikin gidan sarautar ya nufi bargar Dawakan sarki kai
tsaye.
A wannan lokaci mai kula da bargar ma bai iso bargar ba
dan yin aikin sa na kullum da ya saba. Da yake mutane
basa gilmawa a wajan sai kawai ya yi sauri ya shiga bargar
dawakan da wannan Doki na karya, sannan ya kamo na
gaskiya ya fito da shi.
Bisa mamaki sai yaga Dokin bai yi masa gardama ba ko
sau daya har ya fita dashi daga cikin gidan sarautar gaba
daya.
Koda kumais yaga ya smi wannan nasara sai ya cika da
tsananin farin ciki, domin ya san cewa indai ya kai dokin
nan ga su Waziri Akiyanu za su bashi kada ninkin baninkin
abin da suka bashi a baya.
Kumais na cikin jan dokin sai yaji dokin ya cije, kumais ya
yi iya yinsa dan yaja dokin gaba su ci gaba da tafiya,
amma sai yaji ya kasa. Kawai sai ya jiyo a fusace domin
ya tursasa dokin. Waigowar da zai yi sai yaga linzamin a
jikin wani mumunan gutun aljani mai ban tsoro, bao san
sa'adda ya saki futsari a wando ba jikinsa na karkarwa.
Aljanin sai ya daka masa tsawa ya ce, "maza kaje ka
gayawa wadanda suka turoka satar dokin sarki ka gaya
mu su cewa wannan dokin ba zai satu ba. Koda duk
duniya zata taru akan yin hakan.
Koda gama wannan jawabi sai aljanin ya 6ace 6at! Ya bar
kumais tsaye rike da linzamin duki a hannu babu doki.
Nan take kumais ya sulale kasa sumamme.
Sai da kumais ya kusan shafe rabin sa'a a kwance cikin
halin suman sannan ya farfado. Koda ya bude idanu ya
dubi gabas da yamma, kudu da arewa yaga babu wannan
guntun aljani sai ya mike zumbur ya furgice ya cika
wandansa da iska. Bai zami a ko ina ba sai a gaban Waziri
Akiyanu.
Da zuwa ya wuce kai tsaye zuwa cikin turakar Waziri yana
tafiya buguzum-buguzum. Kai da ganinsa kasan a cikin
mumunan tashin hankali yake. Yana shiga cikin turakar
ya iske Waziri Akiyanu a zaune cikin nishadi suna walimar
farin ciki bisa samun tabbacin lallai yau ne za'a kawo
musu wannan doki na sarki wanda za su kaiwa boka
domin su sami damar kawar da Aminul Has daga kan
karagar mulki.
Koda ganin kumais sai Waziri Akiyanu da sauran jama'ar
tasa suka mike zumbur a firgice. Waziri Akiyanu ya
tareshi da sauri ya zaunar da shi gefe daya sannan ya
tambayeshi abinda ya faru
Nan take kumais ya kwashi labarin duk abin da ya faru
gareshi tun daga lokacin da ya sami nasarar dakko dakin
sarji daga cikin burgar har izuwz bayan gari sa'adda yaji
dokin yaki jawuwa a hannunsa yana waigawa sai ya yi
arba da wannan guntun aljani. Koda gama wannan
jawabi sai hankalin Waziri Akiyanu ya dugunzuma, haka
ma na sauran jama'ar tasa, suka rasa abin da yake musu
dadi. Al'amarin da ya janyo fadar tayi tsit kenan kamar
mutuwa ta gifta. Waziri Akiyanu ya kama kai komo a cikin
fadar yana tinani mai zurfi. daga can sai ya tsaya cak ya
dubi jama'ar tasa daya bayan daya ya ce, "ya ku
abokanan kuka ku yi sani cewa masu iya magana sun ce
ta inda aka hau tanan ake sauka. Ni ina ganin cewa tunda
al'amarin nan yafi karfin tunaninmu babu abin da ya
kamata muyi face mu koma gurin wanda ya umarcemu
da dauko wannan doki, shi ka dai ne zai iya yi mana
maganin wannan aljani da ya hana a dauko dokin."koda
jin wannan batu sai gaba daya 'yan majalisar suka
ce,"tabbas kayi tunani mai kyau, lallai hakan za'a yi, kuma
ai da zafi-zafi akan daki karfe ba sai ya huce ba". Koda
fadin haka sai 'yan majalisar suka amnice da haka. Ba
tare da 6ata lokaci ba Waziri Akiyanu da tsoho Kilzim
suka yi shiri suka tafi zuwa gidan abin dogaronsu.
Da yake akwai tazara mao tsaho a cikin tafiyar tasu sai
hira ta 6arke a tsakanin Waziri Akiyanu da tsoho Kilzim.
Inda Kilzim ya dubi Waziri ya ce, "ya kai Waziri yanzu idan
ka sami sarkin Misra wana buri ne da kai na farko wanda
zaka fara kawar da shi?
Ya yin da Waziri yaji wannan tambaya sai ya bushe da
dariyar farin ciji, sannan ya ce, "ya kai Kilzim kayi sani
cewa ina da wasu burika uku wadanda suka dade suna yi
mini yawo a cikin zuciyata.
Burina na farko shi ne, ina so na sauya gaba dayan
rayuwar mutanan birnin Misra, ya zamana cewa in ba
attahirai ba ko mai mulki babu mai samun nutsuwa da
kwanciyar hankali.
Abu na biyu, ina so na tsauwala haraji ga kowa domin na
tara dukiya mai dimbin yawan gaske a cikin kankanin
lokaci, domin sauran sarakunan da ke mulki a sauran
kasashe su jani a jiki su dinga harka tare da ni, sa6anin
yadda suke kyamatar sarkinmu a yanzu.
Abu na uku shi ne, ina so na shirya gagarumin yaki wanda
zan murkushe manyan kasashe da ke wannan nahiya
tamu su dawo karkashin mulkina sabo da na tara karfin
tattalin arzikin kasar tawa. A sannan ne zamu zauna cikin
jin dadi, arziki da kwanciyar hankali".
Sa'adda Waziri Akiyanu ya zo nan a zancensa sai tsoho
Kilzim ya rage gudun dokinsa ya sassaita tafiyar tazo dai-
dai da dokin Waziri Akiyanu, sannan ya ce, " ya
shugabana yanzu naji naka burin. Mukuma da muke
makusantanka a wane matsayi zaka ajiyemu?".
Waziri ya yi murmushi, sannan ya dubi Kilzum ya ce, "ka
ga kai yanzu shekarunka sun haura casa'in a duniya, na
tabbatar da cewa dukiya da kyakkyawar mace basu dame
ka ba, domin babu irin arzikin da baka gani ba, haka ma
matan, komai kyan mace babu irin macen da baka gani
ba. Bukatarka kawai ita ce ko baka nan kada bayanka ta
tozarta. Nayi maka alkawari muddin ina numfashi a
doran kasa iyalinka ba za su walakanta ba. Kuma dulk
abinda suka bukata nayi alkawarin zan basu har izuwa
karshen rayuwata".
Lokacin da Waziri Akiyanu ya zo nan a zancensa sai ya ga
hawaye ya zubo daga idanun tsoho Kilzim. Al'amarin da
ya mutukar bashi mamaki ke nan. Ya dubeshi ya ce, " ya
kai Kilzim, kai kuwa menene dalilin zubar da hawayanka?"
Tsoho Kilzim yasa hannu ya share hawaye, sannan ya yi
ajiyar zuciya ya ce, " ya kai Waziri Akiyanu, kayi sani cewa
ba komai ne ya sani zubar da hawaye ba face tunowa da
yadda mutuwa take yanke jin dadin rayuwar duniya.
Tabbas insa ace akwai maganin mutuwa da komai
tsadarsa, ko kuma wahalar nemansa ba zan karaya ba
akan nemansa. Gaba daya matsafan duniya sun yi iyakar
kokarinsu akan samar da maganin mutuwa da na tsufa
amma abu ya gagara tunda daga farkon duniya kawo
yanzu. Ni dai yanzu kaga tun ina saurayi nake da burin
shiga cikin majalisar kasar nan, amma ban sami wannan
dama ba sai da girma ya fara kamani bayan mutuwar
ubana. Yanzu gashi dama zata samu wacce mulki gaba
daya zai dawo karkashin sarrafawarmu, amma sai yazu
mini a lokacin da tsufa ya riskeni. Ba lallai ne ma naji
dadin mulki tun da a ko yaushe zan iya barin duniyar duk
da cewa ina cikin koshin lafiya".
Ya yin da tsoho Kilzim ya zo nan a zancensa sai Waziri
Akiyanu ya bushe da dariya, sannan ya ce, "ai shi jin dadi
ko nace arziki ko na kwana daya ne yafi talauci na
shekara dubu. Ka sani cewa idan muka sami nasara akan
abin da muka sa a gabanmu har a bada bayanka bazata
wulakanta ba, ka ga ashe ko mutuwa kayi ka san cewa
baka tafi ka barsu a cikin takura ba da halin kaka na kayi."
tsoho Kilzom yai ajiyar zuciya ya ce, "ai wani baya yiwa
wani maganin yunwa, domin ita rayuwa ba ta da tabbas
domin komai na iya sauyawa a ko yaushe. Idan kayi
tunani za kaga cewa shi dan adam baya daina buri har sai
ya bar duniya. Shin ka ta6a zaton cewa sarki zai tunanin
barin kasar nan ya tafi neman arziki? To kaima nan gaba
ba mamaki ka tafi neman wani abun daban wan da yafi
wan da sarki ya tafi nema wahalar samu. Ka tuna cewa
sau da yawa sarki yana zama bawa, bawa kuma ya zama
sarki".
Koda jin wannan batu sai Waziri Akiyanu ya fusata ya
dakawatsoho Kilzim tsawa ya ce, "kada ka saki yin furci
irin wannan a gareni, domin ni tunda na taso a rayuwata
duk abin da nasa a gaba sai na sami nasara, ban ta6a
samun mushkila ba. Indai na zama sarki sai dai na mutu
akan karaga ba dai wani mahaluki ya iya sauke ni ba. In
dai akwai dukiya, kuma akwai boka babu abin da ba zai
yiwu ba a wannan zamani".
Tsoho Kilzim ya jinjina kai ya ce, "ya kai Waziri kayi sani
cewa kamar yadda ka taso da samun sa'a bisa duk abin
da kasa a gabanka haka sarki Sahibul Hairi ma ya kasance.
Shin baka tsoran cewa zai iya samun nasara a bisa abinda
ya tafi nema ya dawo gida cikin koshin lafiya. Idan kuwa
ya dawo ya iske kaine akan karagar mulkinsa taka ta
kare."
Koda jin haka sai Waziri Akiyanu ya bushe da dariya,
sannan ya ce, "kai a zatonka zan zauna akan karagar sarki
Sahibul Hairi haka kawai ne? Ai duk abin da zanyi sai na
yishi don na tabbatar da cewa sarki Sahibul Hairi bai
dawo ba, in kuwa ya dawo sai dai gawarsa ta dawo.
Yanzu dai babban abu mai muhimmanci shi ne, mu fara
samun nasarar kawar da Aminul Has akan karagar
mulki".
Tsoho kilzim ya yi murmushi ya ce, "nikam na tabbatar
da cewa zamu sami nasarar kawar da Aminul Has ta
kowana hali. Yanzu idan bulata ta biya ni wana matsayi
zaka bani a fada?"
Waziri Akiyanu yai dariya ya ce, "abin da kake so shi zan
baka".
Koda jin haka sai shima kilzim yai murmushi ya ce,
"tabbas babu wanda ya san abin da nake so sama da kai,
kuma nayi imanai da cewa kai mutunne mai cika
alkawari. Lallai idan ka zamo sarki zan zamo Waziri.
Amma kai me yasa ka za6i na zama Wazirinka?"
Waziri Akiyanu ya ce, "ai mulki ga shekarun da basu
haura arba'in ba basa tafiya dai-dai sai da jagorancin
manya masu tunani da hangen nesa. Ni nafi kowa sanin
muhimmancinka a cikin majalisata. Ko ba komai ka ga
jiya kuma ka ga yau, sannan kuma babu wanda ya san
sirrin gidan sarautar birnin nan sama da kai".
Koda jin wannan batu sai tsho kilzim ya yi dariyar farin
ciki ya ce, "hakika duk abin da ka fada gaskiya ne, kuma
ba karamar dabara kayi ba da ka za6eni a matsayin
Wazirika, domin na san wadansu abubuwa ma wadanda
baka ta6a tsammanin na sansu ba. Domin akwai wani
sirri guda daya na sarki Sahibul Hairi wanda duk duniya
babu wanda ya san shi face ni.........
.
Hmm AA Misau Ke Magana
.
SHIN BURIN WAZIRI AKIYANU YANA CIKA KUWA NA
GANIN YA KAWAR DA AMINUL HAS DAGA KAN KARAGAR
MULKIN BIRNIN MISRA YA HAU?.
.
SHIN BAWA HALUF ZAI IYA CETON SU SARKI SAHIBUL
HAIRI A FADAR ALJANI SHAMZABUL AZWAS WADANDA YA
MAYAR DA SU GUMAKA?
INA LABARIN SARKI BARUSA?
.
WANA IRIN SHIRI GIMBIYA SHUKURA ZA TA YI?
YAUSHI SARKI SAHIBUL HAIRI ZAI SADU DA SADAUKI
AWAISU HAR YA CIKA BURINSA?
.
Mu hadu a littafin SARKIN SARAKAI na hudu (4) dan jin
cigaban wannan kayataccen labarin.
SARKIN SARAKAI
Littafina Uku 3 complet
Na Abdulaziz Sani madakin gini
Typing by Al'amin Ahmed misau
Post And Ebook creator by Shuraih Usman 99%

You can download more Hausaebooks at http://shuraih.waphall.com

Date of ebook created: 8/6/2018
Time of ebook created: 8:15 AM

Sarkin sarakai
Littafi na Hudu 4
Na Abdulaziz Sani m Gini
Typing:- Alamin Ahmed Misau
Ebook creator:- Shuraih 99%
.
You can download more Adventure hausaebooks at http://shuraih.waphall.com

Domin downloading na wasu littatafanmu amatsayin eboook sai ku ziyarci shafinmu na yanar gizo
gizo akan adireshi www.shuraih.waphall.com
SARKIN SARAKAI
Littafi Na Huɗu (4)
Part A.
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa
NAN TAKE BAWA HALUF YA GOYATA A BAYANSA SUKA
TAFI INDA AKA KAMAR DA su Sarki Sahibul Hairi.
Kafin su karasa gurin sai suka ga wani kare wanda shi ma
aka kamar da shi kamar yadda aka kamar da su Sarki
Sahibul Hairi.
Bawa Haluf ya tsaya a dai-dai kan karen sannan ya sauke
Alfila daga bayansa ya fito da wannan kana nan kwalabe
masu ruwan sihiri a aljihunsa.
Kawai sai ya bude guda ya yunkura zai kwara akan
wannan kare.
Cikin sauri Alfila ta ruke Hannunsa ta ce da shi a cikin
rada.
"me kake shirin yi ne?"
Haluf ya ce, "so nake na jarraba wannan ruwan sihirin
akan wannan karen ko ruhinsa zai dawo domin nayi
amfani da shi wajan tashin 'yan uwana da Boka
Shamzabul zwas ya mai da su gumaka."
Koda jin wannan batu sai Alfila tayi murmushi ta ce, "Ai
inda ka zuba wannan shidin ruwa akan wannan karen da

nan take zai rugurguje ya zama gari."
Cikin mamaki Haluf ya dubeta ya ce, "ya ya akayi ki ka san
wannan?".
Alfila tayi murmushi ta ce, "Ai mahaifina yana da duk irin
wadannan ruwan sihirin guda dari ba daya ne kuma ko
wanne na san amfaninsa".
Koda jin haka sai murna ta kama Bawa Haluf ya ce, "To
yanzu wanne ne zan zubawa 'yan uwana ruhinsu ya
dawo?".
Alfila ta ce, "ba zan gaya maka ba face kayi mini alkawari
guda."
Haluf ya ce, "fadi duk irin abinda ki ke son nayi miki, lallai
zan zama mai ciki alkawari a gareki".
Alfila ta ce, "ina son ka yi mini alkawari cewa zaka mayar
da ni kasarmu wajen mahaifina, domin na tabbatar da
cewa a halin yanzu yana can cikin tsananin damuwa da
taahin hankali bisa rashin ganina.
Tabbas inda yana da ikon zuwa nan ya kar6eni da tuni ya
zo."
Bawa Haluf ya ce, "kwantar

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment