Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsammanin su sarki Sahibul Hairi suka tafi?".
Humaira ta ce, "ina kyautata zaton sun shiga daji farauta
ne domin su samo mana abincin kalaci".
Alfila ta ce, "hakane. Amma dai kuwa sun dade basu
dawo ba, tun gashiharrana ta fara takewa, na fara jin
yunwa".
Da jin haka sai Humaira ta zura hannunta a cikin jakarta

ta debo dabino sai ta ga ashe saura guda bakwai kacal!
Kawai sai ta mikawa Alfila duka ta ce, "ungo wannan ki ci
ko kya rage yunwar, in ya so mu ci gaba da jiran
dawowar su sarki Sahibul Hairi".
Alfila ta kar6i dabinon ta cinye cikin murna, sannan ta
daga butar ruwa ta kwankwada
Sai da sa'a biyu ta shude su Humaira na zaune suna jiran
dawowar su sarki Sahibul Hairi amma shiru babu su babu
labarinsu.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin su Humaira ke nan
suka yanke shawarar su tashi su bi sawunsu izuwa cikin
daji.
Har sun mike tsaye suna shirin tafiya ke nan sai suka
hango wani katon tsuntsu a can sama ya nufo bakin
kogon da suke ciki. Cikin hanzari Humaira ta zare
takobinta ta fito kofar kogon tana mai umartar Alfila da
cewa kada ta kuskura ta fito daga cikin kogon.
Sannan a hankali tsuntsun ya dinga saukowa kasa har ya
dire nesa kadan da inda Humaira ta tsaya bai yarda ya
kusanceta ba.
Abln da ya sa Humaira bata afkawa tsuntsun ba shi ne, ta
ga wasikara bakinsa.
Nan take tsuntsun ya saki wasikar ta fadi kasa, sannan ya
sake bude fuka-fukansayai sama ya bar wajen gaba daya.
Cikin hanzaro Humaira ta je ta dauki wasikar ta
warwareta a lokacin da Alfila ta fito daga kogon dutsen ta
tsaya daf da Humaira
ba tare da 6ata lokaci ba Humaira ta fara karanta wasikar
a fili kamar haka.
Takarda daga sarki Barusa mai cikakken iko zawa ga
gimbiya Humaira ma'abociyar addinin musulinci. Ina mai
sanar da ke cewa a halin yanzu ina nan a cikin wannan
daji da kike kuma na kama sarki Sahibul Hairi da Bawansa
Haluf na tsaresu a nan kan katon tsauni wanda babu
kamarsa a wannan daji. Na baki kwana daya da yini daya
rak ki kawo mini yarinya Lafila. Bajirewa wannan umarni
dai-dai yake da salwantar rayukan su sarki Sahibul Hairi.
Idan kuwa kika ki zuwa zan zo da kaina na halllakaki na
dauki Alfila bayan na kashe su sarki Sahibul Hairi. A
karshe ina mai yi miki tuni da cewa ki taho da cikakken
shirin yaki domin na tanaji dakaru na musamman masu
lakani da GUGUWAR ANNABA.
Lokacin da Humaira ta zo nan a karatun wasikar sai tayi
jifa da ita cikin tsananin fushi, sannan ta dubi Alfila ta ce,
"to mene ne ya shalleni don sarki Barusa ya kama su
Sarki Sahibul Hairi? Ai 'yan uwansa kafurai ya kashe".
Ya ke Alfila shiga cikin kogon ki dauko mana kayammu
mu ci gaba da tafiya domin ni babu komai a gabana face
na cika alkawari na kaiki kasarku na sadaki da
mahaifinki".
Ya yin da Alfila taji wannan batu sai hankalinta ya
dugunzuma ta dubi humaira cikin tsananin damuwa ta

ce, "ya ke 'yar uwa ina rokonki da kada ki tafi ki bar su
Sarki Sahibul Haira a cikin wannan hali na kak na ka yi,
domin ni a ganina idan kika yi haka kin yi babbar asara.
Dalilina na fadin haka shi ne, ki tuna cewa Sarki Sahibul
Hairi ne mai mulkin babbar kasa mai dauke da maliyoyin
mutane. Idan har kika ci gaba da jan hankalinsa har kika
sami nasara a kansa ya kar6i addinin musulinci tamkar
kin musuluntar da dukkanin jama'ar da ke kasansa ne,
kin ga kuwa wannan ba karamar nasara ba ce.
Abu na biyu da nake son na sanar da ke shi ne, sarki
Sahibul Hairi yana mutukar sonki, domin na lura shi yana
yawan yi miki wani irin kallo mai nuna tsantsar so da
bege.
Shun idan ya musulunta ba za ki aureshi ba? Sa'adda
gimbiya Humaira taji wannan tambaya sai kunya ta
kamata, kuma jakinta yayi sanyi, domin tasan cewa abin
da Alfila ta fadi gaskiya ne. Humaira ta yi shiru tana
tunanin har izuwa wani lokaci mai dan tsawo, daga can
sai ta dubi Alfila tayi murmushi sannan ta ce, "shi kenan
'yar uwata na kar6i shawararkim sabo da haka zamu fara
shirin yaji tun daga yau, domin muje mu ceto rayuwar su
sarki Sahibul Hairi. Yanzu zo ki rakani cikin daji mu samo
wadansu abubuwa". Nan take Humaira ta kama hannun
Alfila suka ruga izuwa cikin daji.
Sai da Humaira da Alfila suka shafe sa'auku a cikin dajin
suna saro itatuwa sannan suka dawo cikin kogon dutse
suka hau fere itatuwan suna yin tsini da su. Bayan sun
kammala hakansai suka kwashi itatuwan suka fito da
wajankogon dutsan suka fara kafa mugwayan tarkuna,
suna binne su a cikin karkashin kasa, wasu kuma suka
rika dana su a sama cikin bishiyoyi, suna kukkula su da
siraran zarurruka wadanda idanu ba zasu ankare da su
ba.
Tun safe da su Humaira suka fara wannan aiki sai da dare
ya raba sannan suka kammala ya zamana cewa sun cika
dajin gaba daya da irin wadannan muggan tarkuna ba
adadi, kuma su biyu ne kadai suka san a inda kowane
tarko yake. Kai bama mutum ba komai kankantar dabba
idan ta yi kuskure ta taka wani gurin sai dai kaga ta afka
cikin tarkon zai zamo sanadin ajalinta. Bayan sun
kammala wannan aiki ne sai Alfila ta dubi Humaira ta ce,
"ya ke 'yar uwata yanzu idan Allah ya kaomu gobe wace
irin gudummawa zan baki a wannan gagarumin yaki da
za kiyi?" ko da jin haka sai mamaki ya kama Humaira ta
ce, "ai kin gama bani gudummawa tun da kin taimaka
min da hada wannan muggan turaku". Alfila ta cem "a 'a
ina son nayi abin da yafi haja, domin na sami lada mai
tsika a wajan irin na shashidai, wadanda suka rasa
rayukansu a wajandaukakakalmar Allah, kamar yadda
kika bani Labari. Lallai a goben nima ina son nayi wannan
yaki tare da ke, gashi kuma ni ban ta6a kashe koba kwaro
da wannan hannun nawa ba, ke hasalima ban iya sarrafa

kowane irin makami ba". Yayin da Humaira taji wannan
batu sai tayi murmushi ta ce, "kada ki damu ya 'yar
uwata, da izonin Allah a yanzu zan koya miki yadda ake
harba kwari". Nan take kuwa Humaira ta baiwa Alfila
baka ta rike sannan suka harba ta. Bayan nan sai Humaira
ta sassaka mutum-mutumi na ita ce, ta tsaida shi a tsaye
can nesa kadan, ta dubi alfila ta ce, "ina so kiyi ta jarraba
harbin wannan mutum-mutumin, amma a tsakayar
idanunsanake son kwarin ki ya cake". Nan fa Alfila ta
samu aikin yi ta yi ta jarraba cake idanun mutummutumin, amma ta kasa. Sai da ta shafe sama da sa'a
biyu tana ta jarrabawa sannan daga karshe ta yi nasara. A
dai dai wannan lokaci asuba ta riske su. Basu kwanta
sunyi barci ba sai bayan sunyi aallar Asuba har Alfijir ya
keto, ai kuwa suna kwanciya sai barci mai nauyi ya dauke
su, sakamakon gajiya dake jikinsu da kuma dadewar da
sukayi a jiyan basu yi barci ba.
Bayan rana ta take sosai, suna cikin yin barcin ne a cikin
kogon dutsen sai kawai suka ji wani irin gurnani mai ban
tsoro. Cikin firgita suka farka, ai kuwa sai Alfila ta yi arba
da wani katon biri tsaye a gabanta. Cikin zafin nama Alfila
ta dauki kwari da bakanta, ta dana zata harbrshi, sai
Humaira ta daka mata tsawa ta haneta. Humaira ta mike
tsaye ta nufi inda birin ya ke tsaye va tare da shakkar
komai ba, suka tsuarawa juna idanu shi da ita. Al'amarin
da ya baiwa Alfila mamaki ke nan, ta fara kiran sunan
Humaira tana cewa, "ki daina kusantar wannan birin kada
ya cutar dake fa".
Ita dai Humaira bata saurari nasihar Alfila ba har ta isa
daf da birin ta dafa kafadarsa, kawai sai birin ya risina a
gabanta yana mai nuna alamin biyayya.
Cikin murna Humaira ta waigo ta dubi Alfila ta ce, "ai
wannan birin ba mai cutarwa bane a garemu, domin shi
ne wanda ya ceci rayuwar mu ni da sarki Sahibul Hairi a
lokacin da mahaifinsa ya kamamu ya kaimu gidansa ya
kullemu cilin wani keji, muka kasa budewa mu gudu.
Hakika mun samu mataimaki na uku a wannan
yaki".Koda jin wannan batu sai fuskar Alfila ta fadada da
murmushi, ta cika da farin ciki.
Ba tare da 6ata lokaci ba su Humaira suka shiryawa kansu
abincin kalaci, suka kimtsa cikinsu. Bisa mamaki sai suka
ga wannan bitin yana tande baki, don haka sai suka zuba
masa abincin suka mika masa. Ai kuwa sai ya kama ci
sosai tamkar ya sami ayaba. sabo da mamaki sai abin ya
baiwa Alfila dariya, ta rinka kwakwatawa. ko da birin yaga
Alfila na yi masa dariya sai shima ya kwaikwayeta, ya
wangame baki zai yi dariyar, amma sai dariyar tasa ta
zamo abi. tsoro, domin tayi kama da kukan jaki. Cikin
firgici Alfila ta ruga izuwa bayan Humaira ta 6uya, domin
azatonta birin so yake ya cutar da ita. Ko da ganin haka
sai Humaira ta bushe da dariya, sannan ta dubi Alfila ta
ce, "saki jikinki ya ke 'yar uwata, ai ba cutar dake zai yi ba,

wasa yake miki shima kwaikwayon dariyar ki ya yi. Nan
take sai Humaira ta kama hannun Alfila ta jata izuwa
wajan birin ta kama hannun birin ta hada da na Alfila,
suka gaisa. Biri. ha jinjina hannun Alfila ya yi dan tsalle
yana
mai nuna alamun sun zama aboki da kawa.
Koda ganin haka sai Alfila ta cika da farin ciki. Nan take
Humaira ta shiga cikin kpgo. dutsen ta yk damarar yaki,
ta dukkanin makamai a jokinta ta fito, koda ganin haka
sai itama Alfila ta shiga ta dakko kwari da. aka ta rataya,
dama ta tanadi wani karin kuttun kwari a cike shima ta
ratayashi a kafadarata. yayin da wannan birin yaga su
Himaiara sun debo makaman yaki sai ya fuskanci cewa
lallai yaki zasu tafi, sabo da hama shima sai ya sunkuya ya
dauko wadansu dogwayan itatuwa guda biyu,daga
fikakke mai tsini, daya ba fikakke ba. ko da gani. haka sai
Humaira ta dubi birin tayi murmushi ta cee, "lallai kaima
zaka bada gudummawaka a yakin daukaka kalmar Allah ".
kamar birin yaji abin da Humaira ta fada sai yayi gurnani
kuma ya. risina a gareta.
Humaira ta dubi Alfila ta ce, "ni ce zan wuce gaba ke da
wannan birin ku bini a baya, duk Inda nasa kafa kuma ku
sanya naku. ki yiwa biri. nan birin nan jagora kada ki bari
ya wuce ki har mu isa inda za muje mu ceto rayuwar su
Sarki Sahibul Hairi.
Duk inda na umarceku da tsayawa ku tsaya komai runtsi
da tsanani kada ku ketara umarnina kinji ko?"
Alfila ta ce, "naji 'yar uwata I. Allah ya yarda ba zamu
ketare ba". Koda jin haka sai Humaira ta karanta wadansu
addu'oi tana mai neman taimakon Allah, sannan ta wuce
gaba ta durfafi cikin dajin tana mai yafito Alfila da hannu.
ko da ganin haka sai Alfkla ta. kama ta kama hannun
wannan biri ta jashi suka bi bayan Humaira. Duk inda
Humaira ta dauke sawuta nan Alfil da birin ke sanya
nasu,domin kada su taka inda zasu ta6a mugayen
tarkunan da suka kafa.
.
SARKIN SARAKAI
Littafi Na Huɗu (4)
Part E.
.
Marubucin littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa
HAKA DAI SUKA WANZU SUNA TA KETA DAJIN HAR
TSAWAN LOKACI, SANNAN SUKA ISO KUSA wannan katon
tsauni wanda suka hango gida. dutse a kansa. cikin sauri
suka kwanta kasa cikin ciyayi suka 6uya, domin sun
hango mugayen halittun nan masu kama da dodanni
akan tsaunin rike da makaman yaki suna ta kai kawo akan

tsaunin, don tabbatar da. tsaro. Humaiara ta kurawa
halittun idanu da kyau ta yi nazarin yawansu ta tabbatar
da cewa adadin su ya wuce misali sai ta yi shiru tana
tunani. Daga can sai ta dubi Alfila ta ce, "yake 'yar uwata
abin da. ake so daku shi ne ku ci gaba da 6uya a nan cikin
wannan ciyawa, ni zan tafi na tunkari wannan gida da
izinin Allah sai na shiga har cikinsa na fitl da su Sarki
Sahibul Haifi, kada ku kuskura ku biyo bayana, ku kawai
ku zuba ido da zarar kun hango mu a guje ni da su sarki
Sahibul Hairi ku tashi ku ruga baya da gudu izuwa can
baki. kogon dutsenmu. Ku tabbatar da cewa baku taka
inda tarkunan zasu cutar ba ku ba". Sa'adda Alfila taji
wannan batu sai tayi murmushi gami da gyada kai tana
mai nuna alamun gamsuwa da fahimta.
Nan take Humaira ta goy i wani dankarami. mutum
mutumi a bayanta ta daure shi tamau, sannan ta zare
takoninta guda biyu ta dirfafi wannan tsauni kai tsaye a
guje tana mai kabbara.
Tun daga nesa da mugayen halittun nan masu kama da
dodanni suka hango Humaira ta taho da gudu izuwa kan
tsaunin taka kwala kabbara sai suka fara harbo mata
kibau, tamkar ruwan sama ake yi. A nan fa Allah ya nuna
ikonsa, domin sai gashi Humaira tana kade kibiyoyin da
takobin hannunta, ba'a samu daya data soketa ba, duk da
cewa yawan kibiyoyin ya wuce musali. Wasu kibiyoyin
ma sai sun taho izuwa kanta sosai, amma sai kaga sun
juya akala sunje sun cake a kasa. Kai da ganin wannan
al'amari kasan cewa kariya ce daga Allah ba wai dabarar
Humaira bace.
Lokacin da mugayen halittun suka ga sun kasa harbin
Humaira kuma sai dada tunkararsu take, sai suma abin ya
basu mamaki, don haka sai da yawansu suka zare
takobinsu suka rugo da gudu izuwa kasan tsaunin, domin
su tareta tun gabanin ta isa kan tsaunin.
Kaico! hakila ta kai mace mai kamar maza, komai
jarumtakar namiji idan yaga wadannan mugayen halittu
a wannan lokacin dole ya razana saboda sun kasance
manya-manya masu kirar sadaukantaka da mutukar
muni, sannan gashi yawansu ya wuce misali tamkar fasa
kasa suke suna fitowa suna dada karuwa, amma duk da
hakan bai sa Humaira ta razana ba bare ta juya da baya,
kawai ma sai ta kara karfin gudunta tana ta dauki. ta riske
su kafin su risketa
Ai kuwa tana shiga cikinsu ta hausu da sara da suka, su
kuma suka yanyameta suna masu kai mata hare-haren,
amma saboda karfi da zafin nama irin na Humaira sai
gashi tana daddatsasu suna zubewa kasa tamkar tana
sassabe a gona. Duk inda ta sa gaba sai kaga tana
samarwa da kanta hanya, kuma bata fasa gudum ba, suka
rasa yadda zasuyi da ita. inbadda ihun halittun babu abi.
da kunne ke ji sai karar karafa. Nan fa Humaira ta ci gaba
da saran halittun, sai dai kaga sassan jikinsu na shawagi a

sama, jini kuwa ya rinka tsartuwa a sama daga kofofin
jikinsu yana fantsama da malala a kas. kafin kafi. Humaira
ta isa kan tsaunin gaba daya jikinta ya rine da jini har
fuskarta tamkar wadda aka tsoma a cikin kogin jini. Babu
abin da zai baiwa mutum mamaki face yadda mugayan
halittun suke da mugun naci, gashi sjna ganin Humaira
na ta kashe 'yan uwansu amma ko tsoro basa ji, sai dada
rugowa suke izuwa gareta. Da karfin tsiya Humaira ta iso
har gaban kofar gidan dutsan da ke kan tsaunin. Da zuwa
tayi arba da kofar gidan a rufe kuma an ginatane da wani
mulmulallan karfe wanda daga ciki yana dauke da skatoci
guda tara, wanda dole sai an zaresu sannan kofar zata
budu. koda Humaira tayi nazarin kofar taga bazata budu
ba da karfin damtse, sai ta shiga karanta wata addu'a da
ban ta musamman tana mai ci gaba da yaki harta kusa ta
iso daf da kofar.
Da zuwanta sai tasa kafarta guda ta naushi kofar, take
kofar ta tum6uko daga jikin ginin dutsan ta fadi kasa
rikica.
Gaba daya sai da gida. ya girgiza tamkar zai ruguje. Ganin
wannan abu daya faru dukkanin mugayen halittun suka
firgita ainun da jarumtakar Humaira suka jajja baya daga
gareta, suka kama nokewa. Humaira ta wuce kai tsaye
izuwa cikin gidan tana dube-dube. Duk wannan gumurzu
da ta sha fama haryanzu tana goye da wannan mutummutumi a bayanta, kuma a lullu6e yake ba'a ganin ko
menene.
Da shigar Humaira ciki. gidan sai tayi arba da sarki Barusa
zaune bisa kasaitacciyar karagar mulki yana kallonta cikin
murmushi. Kawai sai ya mike tsaye ya kama yi mata
jinjina, yana mai cewa, "Lale marhaban da babbar
jaruma, 'yar ma'abota addinin musulinci. Bani abin. da
nake bukata kema na baki abin da kikazo nema".
Humaira ta kalli Barusa cikin raini ta ce, "ta ya ya zan
baka abin da kake bukata alhalin ni kuma banga wanda
nazo dominsa ba?". Koda jin sai sarki Barusa ya kalli
shugaban wadannan mugayan halittu dake tsaye daf da
shi. Take shima ya dubi wadansu yaransa guda biyu sai
sukaje izuwa cikin wata kofa. Jim kadan sai gasu sun fito
da sarki Sahibul Hairi da Bwa Haluf a daure tamau, cikin
wannan murtukekiyar sarkar karfe ta sihiri
Kallo daya Humaira taiwa darki Sahinul Hairi ta fuskanci
sun sha muguwar wuya, domin duk jikinsu rauni ne, kai
da gqni kasan sun sha bakar azaba. In badan ma an
tukesu ba bazasu iya tsayawa bisa duga-dugansu ba,
domin layi suke yi kamar zasu 6ingire kasa. cikin tsananin
fushi Humaira ta kwance goyon da ke bayanta ta cillawa
sarki Barusa mutum-mutumin a kirjinasa tana mai daka
nasa tsawa ta ce, "Ban zo da Alfila ba kuma sai na tafi
dasu sarki Sahibul Hairi". ko da jin haka sai sarki Barusa
ya fusata ainun, zuciyarsa ta kama tafarfasa, kamar zata
kone. Daga can kuma sai ya fashe da mahaukaciyar

dariya ya ce, "yanzu ni zaki rainawa hankali kizo mini da
mutum-mutumi a matsayin Alfila, kuma ki ce zaki
daukesu sarki Sahibul Jairi ki tafi dasu. To ai shikenan ga
fili ga mai doki, muzuba mu gani, ina. son inga yadda zaki
tafi dasu alhali. ina numfashi a doro. kasa". ko da jin sai
Humairat ta nufi inda su sarki Sahinul Hairi suke tsaye. Ai
kuwa sai mutagun halittun suka yunkura zasu sake afka
mata, sai sarki Barusa ya daka musu tsawa, suka ja baya.
sai da ha rage saura baifi taku uku ba tsakanin Humaira
da su sarki Sahinul Hairi, sai Barusa ya daka tsalle sama
daga inda yake tsaye tamkar an harboshi daga baka.
Tun a saman ya zare takobinsa ya kawa Humaira
mummunan sara a wuya da nufin tsinka mata kai, in. a
dan humaira tayi sauri ta sunkuya ba da tini ya gama da
ita, amma sai takobin tasa ta sati iska, duk da haka sai da
ya juya ya gabza mata naushi a fuska
Take hakorin Humaira guda na tsakiyar sama yayi futar
burtu daga cikin bakinta. Jini yayi tsartuwa ta fadi kasa a
galabaice, domin ba'a ta6a yi mata irin wannan mugun
naushi ba a rayuwarta, tabbas tasan cewa ta hadu da
namijin kwarai.
Ko da ganin wannan abu da ya faru ga gimbiya Humaira
sai hankalin sarki Sahibul Hairi da Bawa Halif ya
dugunzuma ainun, suka saduda, domin sun fuskanci
cewa Humaira baza ta iya ceto rayiwarsu ba a wajan sarki
Barusa. Barusa ya bushe da dariyar mugunta a lokacin da
ya fara kewaye Huaira wacce ke kwance a kas, shi kima
na kewayeta yana bugun kasa da yakoninsa. ya ce, "maza
ki fada mini inda kika 6oye yarinya Alfila ko kuma yanzun
nan na sare kansu sarki Sahinul Hairi da Bawansa a gaban
idanunki, sannan na dawo kanki".
Sa'adda Humaira taji wannan batu sai tayi murmushi
sannan ta goge jinin dake zu a bakinta ta dubi sarki
Barusa ta ce, "ai kada mage ba yanka bane, zaifi kyau ka
fara sare kaina tukunna idan har zaka iya, kafin kayi
tunanin sare kan wasu". Kafin Barua yace wani abu tuni
Humaira ta mike taaye zumbur ta gyara tsayuwarta,
kuma ta daga takobinta guda biyu tana mai fuskantarsa.
koda ganin haka sai Barusa ya kurma uban ihu mai firgita
mazaje a filin yaki, sannan yariga kanta da dukkan
karfinsa. Suka ruguntsume da azababban yaki, ya zamana
cawa suna kaiwa juna sara da suka cikin matukar zafin
nama, juriya da bajinta.
koda fara wannan artabu sai Humaira ta raina kanta,
domin kafin saran Barusa ya ninka nata sau uku, haka ma
zafin namansa, domin a duk sa'adda da yakai mata sara
ta kare da takobinta sai ta durkushe kasa dakyar kuma ta
maida martani.
Haka dai suka ci gaba da yin wannan gumurzu. har
tsawon sa'a guda ya zamana cewa dayan su bai sami
rauni ko guda daya ba amma a sannan Humaira ta gaji
Likis. Shi kuwa Barusa tamkar ma a sannan ya fara

gumurzu.
Koda Himaira ta fahinci in dai taci gaba da wannan fada a
haka sai Barusa ya sami nasara a kanta sai ta sauya salon
fada ta fata guje-guje da tsalle-tsalle tana wahalar da
Barusa. Nan da nan ya fara haki wato gajiya ta riskeshi.
Kawai dai ya tsaya cak! a waje daya ya ki ci gaba da binta
kuma ya yi jifa da takobinsa ya lumshe idanunsa yana
mai karanta dalasuman tsafi sai ga kibiyoyin tsafi sun fitu
da cikin hannayansa. Duk kibiyar da ta nufeta sai ta kone
kurmus ta zama toka. Haka dai Barusa ya yi ta watsawa
Humaira mugwayan abubuwa don ya hallakata amma bai
sami nasara ba har tsawon rabin sa'a.
Ana cikin haka ne Humaira ta sake yin wata addu'ar sai
gidan gaba daya ya kama rugujewa, duwatsu suka dinga
wadowa kasa suna danne wadannan mugwayan halittun
suna mutuwa. Al'amarin da ya firgita kowa ke nan aka
shiga guje-guje kowa yana kokarin ficewa daga cikin
gidan har shi kansa sarki Barusa kuwa.
Damar da Humaira ta samu ke nan ta karanta wata
addu'ar ta shafa sarkar data daure su sarki Sahibul Hairi,
take sarkar ta bace 6at! daga jikinsu. Nan take su ukun
suka ruga waje da gudu a lokacin da ginin gaba daya ya
karasa rugurgujewa ya nutse izuwa kafkashin tsaunin.
Humaira Sarki Sahibul Hairi da Bawa Halif suka gangaro
kasan dutsan a guje a lokacin da shi kansa tsaunin ya
kama girgiza gaba dayansa yana shirin yin bindiga ya
farfashe.
A wannan lokacine su Humaira suk yi arba da sarki
Barusa tare da mugayan halittun a tsaitsaye a can gefe
daya suna nesa da tsaunin. Koda su Barusa suka hango su
Humaira suna sakkowa daga kan tsaunin sai suka rugo
izuwa kansu suna harbo musu kibiyoyi. Nan fa aka kasa
azababban tsere, Humaira ce a kangaba, sarki Sahibul
Hairi da Bawa Haluf na biye da ita. Tana cikin gudun ne ta
waigo ta dubi su sarki Sahibul Hairi, ta ce da su, "Duk inda
kukaga na dauke sawina to ku sanya naku. Kada ku kus
kura ku dorashi wani gurin daban. Ai kuwa sai suka bi
wannan umarni har suka iso gurin da Humaira ta bar
Alfila da Birin nan a la6e cikin ciyawa.
Gama fadin haka ke da wuya sai ga su sarki Barusa sun
iso, kwai sai suka tsaya daga nesa kadan aka kara kallonkallo. Dama tuni sarki Sahibul Hairi da Bawa Halif sun
sami makaman yaki sun ruke. shi dai sarki Sahibul Hairi
wadansu addina guda biyh ya rike, shi kuwa Bawa Haluf
takobi da garkuwa ya rike. Alfila tana rike da kwarinta ta
dana baka, shikuwa birin yana ruke da itatuwa guda biyu
daya mai tsini daya mara tsini.
A dai-dai wannan lokacine tunani ya fadowa sarki Sahibul
Hairi a cikin zuciyarsa ya ce, "wai shin shi sarki Barusa
wana irin sabon shiri ya yi ne alhalin ni kai na a can baya
na sami nasara a kansa amma yanzu gashi na ga ya gagari
wacce ta gagareni?"

Bayan an yi kallon-kallo tsakanin sarki Barusa da Humaira
sai Barusa ya daga hannusa sama yana mai bada umarni
a afka musu. Nan take mugayan halittun nan suka zare
muggan makamansu suka ruga kansu sarki Sarki Sahibul
Hairi suna ruri da kururuwa.
Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf, Alfila da birin suma sai
suka ruga kan mugayan halittun suka ruguntsume da
azababben yaki.
.
AA Misau Ke Magana
SHIN WAZAI SAMI NASARA A WANNAN AZABABBAN YAKI
DA AKE GWAZAWA.
.
SHIN SARKI SAHINUL HAIRI ZAI CIMMA BURISA KUWA.
.
WACCE SHAWARA ZAI YANKE AKAN KARBAR ADDININ
MUSULINCI?
.
A WANE HALI SARKIN BARAYI ZAI KASAN CE TUNDA
ANBATA MASA TARIHINSA NA SATA?
.
A WANE HALI AMINUL HAS YAKE CIKI.
.
Mu Hadu A Littafin Sarkin SARKIN SARAKAI
Littafi Na Biyar (5).
Don jin Karahen wannan littafin

Sarkin sarakai
Littafi na Hudu 4
Na Abdulaziz Sani m Gini
Typing:- Alamin Ahmed Misau
Ebook creator:- Shuraih 99%
.
You can download more Adventure hausaebooks at http://shuraih.waphall.com
Domin downloading na wasu littatafanmu amatsayin eboook sai ku ziyarci shafinmu na yanar gizo
gizo akan adireshi www.shuraih.waphall.com

SARKIN SARAKAI
Littafi Na Biyar (5)
Abdulaziz Sani m gini
Ebook creator:- Shuraih Usman
Daga:- http://hausaebooks.cf

.
Marubucin littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa..
LOKACIN DA AKA RUGUNTSUME DA AZABABBAN YAKI
TSAKANIN wadannan Halittu da sarki Sahibul Hairi, sai
gurin gaba daya yaruguntsume yazama babu Kyan gani,
banda ihun Halittun da karar karafuna babu abinda make
iya ji. kura kuwa ta turnuke dajin gaba daya.
Nan sarki Sahibul Hairi, da Bawa Haluf da yarinya Alfila
suka zame musu alakakai, domin duk Inda suka durfafa
sai kaga Halittun suna zubewa kasa.
A duk lokacin da sarki Sahibul Hairi ya sari Halittun sai
kaga suna rabewa biyu yana tsargesu idan wiyansu ya
Sara sai dai kaga Wiyan ya fita fit yayi same sannan ya
fado kasa.
Shima wanan gwaggwan birin haka ya rinka ragargazar
Halittun da wadannan dogayan itatuwa guda biyu da ke
hannunsa.
Ita kuwa yarinya Alfita kan wata doguwar bishiya mai
tsawon gaske ta hau harta isa izuwa karshanta sannan ta
ci gaba da harbin Halittun da bakanta tana sakar musu
kibiyoyi, sai dai kaga kibiyoyi na cakewa a cikin idanun
Halittun, ko a wiya ta samesu sai kaga sun fadi kasa
matattu.
Duke wannan Abu da ke faruwa sarki Barusa da jaruma
Humaira na tsaye a can gefe da gefe suna kallon juna
kuma suna kallon abida ke faruwa.
Koda sarki barusa yaga irin gagarumar barnar da akai

masa, wato yaga wannan Dakar nasa suna zubewa kasa
ya zamana cewa a kaso uku babu kaso biyu sai ya
harzuka ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa
sanna ya rugo inda jaruma Humaira ke tsaye domin ayi
ta ta kare.
Ya yin da Humaira taga sarki Barusa ya dirfafo a guje rike
da takobinsa sai itama ta ruga gareshi tana mai kwala
kabbara Kuma ta zare takubbinta guda biyu.
Suna haduwa suka kacame da azababban yaki suna masu
kaiwa juna sara da suka cikin zafin nama, juriya da
bajinta.
Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda suke
da mutukar zafin name tankar jikinsu bana jini da tsoka
bane, kai kace na karfe ne.
Sai

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment