Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tuna inda kuɗin zasu tafi da abinda zata mallaka bayan sun tafin sai ta ji wani sanyi ya cika zuciyarta.
Ta maida kuɗin cikar baƙar leda ta ƙulle sannan ta fito ta miƙama Babaye ya amsa yana kallonta yace “ zan je na yi musu balance, kisa hannu a takardar da zaran kin dawo sai ki kira ni”, ta jinjina kai gami da yi masa godiya.
Bayan fitarsa, ta yi dariya tace a fili “ kilishi na kusa fita daga ƙangin bautar ki, domin na dawo daga rakiyarki yau itace rana ta ƙarshe da zan saurari kokenki ko na yi miki aiki, domin duk abinda nake nema na riga na samu, zan tuba zan kuma cire musaddiƙ daga sauran masifar da ki ka sa shi ciki, karshe ma idan ba kiyi wasa ba zan tona asirinki a wajen kowa”. Ta ƙara yin dariya, lokaci ɗaya ta janyo gyalenta ta yafa, sannan ta ɗakko waya ta kira maigidanta Tasi’u wayar bata daɗe tana kuka ba ya ɗaga, ya yi mamakin yadda yau ya ji muryarta cikin mutunci da mutuntawa tana kuma wai tambayarsa izinin fita, Tasi’ u ya gyara zamansa a gaban sabuwar amaryarsa da bai wuce makonni biyu da aurota ba, ba tare da sanin Haj Rakiya ba, yace “ ikon Allah yau kuma kece ke neman uzinin fita Rakiya, lafiya kuwa?” .
Ta yi ɗan murmushi tace “ Lafiya ƙalau mallam, ina dai neman izini don Allah”, cike da tsantsar mamaki yace “ Na baki izinin Allah ya dawo da ke lafiya”, tace “ Amin” lokaci ɗaya ta kashe wayar ta fice.
Tasi’ u ya wangame baki yana kallon amaryarsa,lokaci ɗaya yana tunanin idan ma nadama Haj Rakiya ta yi to ta makara, yadda ya zauna ya haɗiye zama da ita ba girma ba arziƙi duk da duk yayan da ta haifa masa sun rasu, ta hana masa ƙara aure, yau kadarinta ya karye , tunda gashi nan ya ƙara aurensa yana zaune da matarsa cikin kulawa da mutuntawa ba tare ma da ta ko sani ba, idan tana ganin itace ta hana masa ƙara aure, to lokaci ne kawai baiyi ba, domin da Allah ya kawo lokacin gashi ya yi. Gaba ɗaya Haj Rakiya ta daɗe da fice masa a rai, kawai dai yana zama da ita na dole ne.

Isarta gidan Haj kilishi, ta taddata cikin wani irin gigita da ƙaɗuwa, haɗe da tsoro, Haj Rakiya ta zauna kusa da ita tace “ Haj lafiya kuwa ko jikin ne?” Ta girgiza kai ido jajir tace “Eh akwai jikin ma amma ina cikin damuwa ne sosai”, ta ɗan matsa kusa da ita tace “ Damuwar me?”.
Ta ɗora mata ido sannan tace “ wani irin mummunan mafarki na yi da boka mai Rakwacam yana gaya min na jefa shi cikin masifa, Haj ina kallo wuta ke cinsa yana kuma faɗin saura ni, sannan kuma duk ranar da aka tone tukunyar ƙasan kuka to tawa ta ƙare,”, Haj Rakiya ta numfasa tace “ kai Haj yanzu saboda mafarki ƙarya shi ne ki ka gigice haka, wannan ai shirme ne irin na mafarki”.
Ta girgiza kai tace “ Bana jin hakan a jikina komai ya bayyana a gare ni ne tamkar idona biyu, babu bambanci da gaskiya”.
Cikin ƙosawa da maganar tace “ To shikenan, yanzu me ki ke so ayi miki kika kira ni”.
Tace cikin rawar murya, “ Bazan iya tuƙi ba, ba kuma zan iya tafiya da direba saboda sirri, saboda haka ki kira mai taxi ɗinki ya zo ya kaimu rugar mai Rakwacam lalle ina son na ga halinda yake ciki”. Gaban Haj Rakiya ya fadi sosai, ko kaɗan bata son Haj kilishi tace zata je domin idan har yana cikin wannan halin to ba ta son ta gan shi a haka, don tabbas tasan zata iya sa zargi da zato a cikin zuciyarta.sai dai duk yadda ta so ta dakushe tafiyar to fa Haj kilishi ta ƙi yarda ta dage dole sai sun tafi, Bata son ta cigaba da yi mata musu, don tasan shegen kafiya irin na ta don haka waya kawai ta ciro ta kira direban ta gaya masa inda zai taddata.
Wanda ba’a ɗauki wani dogon lokaci ba direban ya iso.
Haj Rakiya da kanta ta riƙe Haj kilishi har cikin motar, yayinda Baba maigadi ya bita da sannu don a tunaninsa ma ko asibiti zasu tafi.
Sun kai Rugar da wuri domin mai taxi ɗin ya yi gudu sosai.
Sun tadda Boka mai Rakwacam a inda aka saba aje shi, wannan karon ma babu kowa a tare da shi, alamar kowa ya gaji da lamarinsa. Idanun Haj kilishi suka buɗe sosai, tunda ya faɗa wannan masifar bata taɓa ganinsa ba sai yau, ita kanta Haj Rakiya da yake tun zuwan da ta yi bata ƙara zuwa ba, ko Haj kilishi ta aiketa bata zuwa, tunda ta fahimci hatta wayarsa ta daina aiki balle Haj kilishi ta kira shi ta gane inda ta dosa.
Hakan yasa itama taga mai Rakwacam ya ƙara rakwacamewa, babu abinda ya ƙara tada hankalin Haj kilishi sai irin yadda ta ga duk jikin mai Rakwacam a ƙone yake duk ya sabule sai tashin wari kawai yake yi, wani farin gurɓataccen ruwa ya na fita daga ko’ina a cikin jikinsa.
Cikin rawar jiki da murya Haj kilishi ta riƙo Haj Rakiya tace “ Dama haka mai Rakwacam ya koma amma ki ka ce wai kunyar rashin samun nasara a ayyukan da yake min ne ya sa shi cewa baida lafiya, ki dubi jikinsa irin wutar da naga tana cin sa a jikinsa a cikin mafarkina ce, haka jikinsa ya koma ko a mafarkin nawa, dagaske ne mafarkina, na shiga uku, saura ni ……”, jikin Haj Rakiya itama ya yi sanyi, a sanyaye tace “ Me ki ka gani a game da ni a cikin mafarkin na ki…” Haj kilishi ta yi mata kallon tsaf, wasu tarin tambayoyi da wani abu mai kama da zargi Haj Rakiya ta gani kwance a cikin idanunta, tayi saurin ɗauke kanta, sannan Haj kilishi tace “ Kada ki damu banga komai a game da ke ba, amma ki sani duk abinda ya ci doma ba ya barin awai”.
Shuru Haj Rakiya ta yi ba ta son ta cigaba da furta duk wani abu da zai dasa zarginta a ran Haj kilishi.
A haka suka baro rugar ba tare da ko sau ɗaya sunga mai Rakwacam ya yi motsi ba, kamar yadda har suka bar rugar ko matarsa basu gani ba a matsayin me kula da shi, lalle wannan duniyar shirme ce, shin ina bokancin nasa? Ina taimakon da yake ba mutane? Me yasa bazai iya tsinanama kansa komai ba bayan a yanzu babu wanda ya kaishi neman taimakon?.
Irin tambayoyin da Haj kilishi ke yi ma kanta kenan. Lokaci ɗaya kuma tana kashe Haj Rakiya da wani irin kallo wanda ke haddasama Haj Rakiya kaɗuwa, hakan yasa tun daga Rugar har cikin gari babu wanda ya yi ma wani magana, suna shiga gari Haj Rakiya tace “ Ina jin zan sauka anan, akwai uzirin da nake son yi”, Haj kilishi ta girgiza kai tace “ A’a ki jira mu je gida tukuna, akwai tambayoyin da nake son na yi miki”.
Cikin Haj Rakiya ya shiga ƙugi, tsoro ya bayyana akan fuskarta,
Haj kilishi ta ɗauke idonta daga kallon fuskarta ta da ta gama bayyanar da rashin gaskiyarta, hakan yasa gaba ɗaya motar ta ƙara yin tsit, ko ƙwaƙƙwaran motsi Haj Rakiya ba ta yi don ji take kamar idan ta yi motsi Haj Kilishi zata faɗo wata maganar da zata ƙara dugunzumata.
Hakanan a daddafe su ka kai gida, Haj kilishi ta sallami me motar. Sannan ta shiga dafa bango domin shiga cikin gidan, Haj Rakiya na ƙoƙarin riƙeta ita kuma tana ƙoƙarin tafiya.
Baba maigadi bai fahimci komai ba a tsakaninsu, sai sannu da yake cigaba loda yi mata, irin tashin hankalin da ya gani a tare da Haj kilishi zahiri bai taɓa ganinsa a tare da ita ba. Haka ya bisu da kallo har suka ɓacema ganinsa.

Suna shiga falo Haj kilishi ta zauna daƙer tana aje ajiyar zuciya me ƙarfi, sannan ta dubi Haj Rakiya wacce ta zauna a kujerar da ke kusa da ita sai dai ta kasa haɗa ido da ita kamar yadda zuciyarta ke bugawa tana addu’ar Allah yasa ba ganota Haj kilishi ta yi ba, wani abin ban takaici kuma shine yadda ta zuba mata ido ba tare da ta ce mata uffan ba.
Dai dai lokacin murtala ya sauke Afrah a ƙofar gida daga makaranta, ta yi masa godiya sannan su kayi sallama, tana tura kai cikin gidan, Baba maigadi ya tareta da sannu da zuwa, cikin mutuntawa ta amsa masa har ta nufi ɓangarenta, magamar Baba maigadi ta dakatar da ita, “ Jikin Haj fa ina tunanin ya matsa, don basu daɗe da dawowa daga asibiti ba, kuma ko da suka dawo na fahimci ta fi yadda suka tafi ƙara galabaita, ta wahala sosai”, Afrah ta dan yi jim sannan tace “ Allah ya bata lafiya, bari na shiga na dubata kafin na shige gida”, yace “ Eh hakan ma na da kyau”.
Ta juya ta nufi ɓangaren Haj kilishi, amma hakanan sai ta sami kanta da jin faɗuwar gaba, mai tsanani, ta ji tana neman ta rikice, duk da haka dai haka ta cigaba da tafiya harta isa cikin gidan, muryar Haj kilishi da Afrah ta ji cikin ƙaraji da fusata ya tilasta mata tsayawa jikin windo,
“Ina tambayarki duk irin kuɗin da kike ƙarɓa a cewar boka mai Rakwacam ne ya ce a bayar, gidan uban wa ki ke kaiwa, bayan da shi da matacce basu da wani bambanci………………..



Yar gidan Imam✍️
https://chat.whatsapp.com/GDRWLrj1Z7QCDfSxoE8hE2


MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
( mrs Aliyu Mayere)

Page 6

Tambayar ta zo ma Haj Rakiya a bazata, hakan yasa ba ta tanadi amsar da zata ba ta ba, cikin kame kamen magana tace “ wa ko nake kaima idan ba shi ba, domin sanda nake zuwa ba a haka na tadda shi ba, ina ganin cikin ɗan lokacin da ban je ba ne ya koma haka”, Haj kilishi ta watsa mata harara tace “ jiya ko shekaranjiya ya koma haka domin dai na ga ko kwanaki uku da suka wuce na baki kuɗi kin kai masa akan musaddiƙ da Afrah”, shurun da tayi yasa Haj kilishi ƙara gasgata abinda take zargi, ta gyara zamanta daƙer tana cigaba da yi mata wani irin kallo.
Cikin rawar hannu Afrah ta fito da wayarta daga cikin jaka ta maidata silent sannan ta buɗe camera ta ɗora akan su Haj kilishi, daga inda take tana iya ɗaukar komai.
Haj kilishi tace “ Tabbas Haj Rakiya akwai lauje cikin naɗi, duk irin kuɗaɗen da kike amsa a hannuna ke ce ke amfana da su, na ji a jikina tunda na daina zuwa wajen boka da kaina na ɗoraki akan harkar kike cinye duk kuɗin da na ke baki”, Haj Rakiya ta ɓata fuska tace “ Au zargina ki ke yi?”, ta gyaɗa kai tace “ ƙwarai kuwa ina zarginki, domin duk rashin gaskiya ya gama bayyana a fuskarki, sannan sam bana jin shauƙin da nake ji na yarda da ke a cikin zuciyata”. Haj Rakiya ta fahimci dai tuni Haj kilishi ta gama ganota, ta tabbatar babu wani sauran kwana kwana da zata yi mata, don haka ji tayi ba zata iya cigaba da ɗaukar maganganun da Haj kilishi ke soka mata ba, don haka ta ƙara haɗe rai cikin fusata tace “ To ba sai kiyi ta zargin nawa ba, ko an gaya miki ni baiwarki ce, da iya rana iya ruwa zaki kirani ki sani bautarki, na ci kuɗin na ki idan kina da hujja ai sai ki kai ni ƙara”, cikin mugun mamaki Haj kilishi ta fiddo ido waje tace “ lalle tsintacciyar mage bata mage, har kece ki ke iya gaya min wannan maganar, bayan kuɗina da kika ci bayan kinyi min zamba cikin aminci”, Haj Rakiya ta saki tsaki tace “ ke har za kiyi maganar zamba cikin aminci, bayan babu wanda ya kaiki yin zamba cikin amincin, ko kin manta zambar da ki kayi ma musaddiƙ ki ka haɗa hannu da yar’uwarki kuka raba shi da dukiyarsa, ko kin manta zambar da ki kayi masa ki ka haɗa aurensa da Hannatu ta hanyar malamai, ko ko kin manta zambar da ki ka yi masa ta raba shi da kyakkyawan halinsa ki ka haɗa shi da shaye shaye, ko kin manta zambar da ki kayi ma Afrah na son rabata da musaddiƙ, ke har kina da bakin magana”.
Gaban Afrah ya cigaba da faɗuwa, hannunta ya cigaba da rawa kamar wayar hannunta zata faɗi, a yayinda Haj kilishi ta yi matuƙar harzuƙa tace “ Duk abinda ki ka lissafa a shawarar wa aka yi, ai ke ki ka ba da shawara, mara mutunci kinibabbiya, barauniya” Haj Rakiya ta miƙe tace “ Ga ki nan babbar ɓarauniya ko kin manta kuɗin musaddiƙ da ki ka sace, ke ni fa na dawo daga rakiyar ki, kuma ki sani tun daga kan Tsiduhu zuwa duk wasu bokaye da na haɗaki da su duk ƙarya ne, kuɗin da ki ke bani ni na ke hidimata da su, don na fita daga cikin sabgarki,”.
A zafafe tace “ Allah ya isa tsakanina da ke, yau da ina da lafiyar ƙafafu da ƙarfin jiki da sai na yi miki dukan tsiya yadda duk kuɗin da kika damfare ni zasu ƙare a wajen neman lafiyarki don saina karairayaki, na tsaneki yar aiken shaiɗan”, Haj Rakiya ta yi shewa ta tafa hannu tace “ Idan ni yar rakiyar shaiɗan ce to ke shaiɗan ɗince, kuma ko lafiyarki ƙalau ya za kiyi da ni, ai sai dai mu buga, Allah ya isan ki kuma ta banza ke Allah ya isa nawa ce a kan ki, ta riga ta ƙare miki amma kin kasa hankalta, halin da mai rakwacam ya ke ciki irinsa zaki shiga idan baki tuba ba, wannan ciwon na ki duk sakayya ce daga Allah, ni dai na cire hannuna, kuɗi kuma na ci asalima har gida na saya, ki haƙura kawai ki kyale musaddiƙ da matarsa domin sun fi ƙarfinki ki sani kadarinki ya karye”.
Wani irin zafi zuciyar Haj kilishi ta ke yi yau ta yi mamakin da bata taɓa yin irinsa ba, Haj Rakiya ta ci amanarta. Ido jajir ta dubeta tace “ ki je duk abinda ki ka ci min ban yafe miki ba”, ta miƙe tana harare harare ta tsaya a gabanta tace “ kada Allah yasa ki yafe, kema ai na Allah ya isan ne, kuma ka da ki manta da asirin da muka binne a ƙasan kuka wanda yasa musaddiƙ shaye shaye, ina son kisa a ranki cikin ko wane lokaci ina iya zuwa na tone ko don na kawo karshen zaluncin da kike yi ma musaddiƙ”, tana gama faɗin haka ta buga tsaki ta juya zata fita, dai dai lokacin Afrah ta yi gaggawar ɓoyewa ta bayan falon, hakan yasa har Haj Rakiya ta fice daga gidan cike da fusata ba ta ga Afrah ba.
Kamar yadda tabar Haj kilishi cikin tsananin tashin hankali da alhini gami da damuwa, yau komai ya kwakkwafe tsoro ya ƙara kamata data tuna furucin Haj Rakiya agame da abinda suka binne a ƙasan kuka, ita kanta tana jin wani abu mai kama da nadama sai dai tana jin tsoron a tono asirin don rashin sanin abinda zai iya biyo bayan tonewar wanda batq sani ba. Gabanta ya ƙara faɗuwa babu yarda tsakaninta da Haj Rakiya don haka tasan zata iya tonewa ko don taga bayanta, wannan wace irin masifa ce, hawaye masu zafi suka shiga sauka mata, ta faɗa cikin wani irin mugun yanayi, tuni ƙirjinta ya ɗauki zafi kamar ana soya shi da wuta, damuwa mai tsanani da nadama ta ƙara rufeta, halinda mai Rakwacam yake ciki ya taimaka wajen sanya nadama a tare da ita, ita kanta tana jin zata iya tone sihirin da ta yi ma musaddiƙ amma tsoro take ji matuƙa bata san me zai faru da ita ba, hakan yasa saboda tsabar son kai ta gwammace asirin ya cigaba da zama a inda yake, wanda hakan na nufin musaddiƙ ya ƙare rayuwarsa bai zama cikakken mutum ba.
To amma ya zata yi da Haj Rakiya, ya zata yi ta rufe bakinta daga tona mata asiri?, lalle tana cikin tsaka mai wuya.

A sukwane cikin tsumar jiki Afrah ta fito daga inda ta ɓoye bata saurari komai ba ta yi waje, ganinta a kiɗime yasa Baba maigadi tasowa ya tareta, a gaggauce yace “ Afrah ya ya lafiya kuwa? Ko jikin Haj ne, gama naga itama Haj Rakiya ta fito a kiɗime”, Afrah ta girgiza kai tana ƙoƙarin share hawayen da ta kasa riƙewa, tace “ Baba ina cikin ruɗani ƙwarai da gaske, akwai damuwa”, ya ƙara matsowa kusa da ita, duk da baisan matsalar ba shi ma sai ya ji damuwa sosai, yace “ki gaya min menene?”, ta ɗaga kai tana kallon saman ɗakin Haj kilishi sannan a hankali tace “ mu je”, da sauri ya bita cikin ɓangarenta.
Har cikin falonta suka shiga, har zuwa lokacin kuma a kiɗime take , haƙurin Baba maigadi fa ya fara gazawa ya dubeta a ƙagauce yace “ ki gaya min menene ke faruwa”,
Afrah ta gpge hawayenta sannan sannu a hankali ta sanar da shi komai tana hawaye ta ƙara da cewa “ Batun yau na ke zargin Haj ba akan duk abinda ke faruwa da yaya musaddiƙ, sai dai rashin shaida yasa ban tada maganar ba, amma yau komai ya fito, yanzu Baba ashe har akwai ƙeƙasasshiyar zuciyar da zata iya cutar da mutumin da baiyi mata komai ba, meye laifin yaya musaddiƙ don ya fito a matsayin ɗan kishiya, wace irin al’umma mu ke ciki ne da son kai da son zuciya ya yi mana yawa, wannan wane irin zalunci ne”.
Hankalin Baba maigadi ya ƙara dugunzuma ya sauke ajiyar zuciya yace “ Duk abinda akace Haj zata yi to zata iya, don na rayu da ita a gidan nan tun kafin a haifi musaddiƙ nasan wacece ita nasan irin mugun zaman da tayi da mahaifiyar musaddiƙ, don haka ƙiyayyar musaddiƙ ya zama tamkar wani ɓangare ne na rayuwarta, don haka ko kaɗan banyi mamakin jin hakan ba, kawai dai ina mamakin yadda duk da tsanar da ta yi masa amma babu wanda ya taɓa jefa mata zargin sa hannunta a cikin lalacewar nagartaccen mutum irin musaddiƙ”.
Kuka Afrah take sosai, tausayin mijinta ta ke ji, Baba maigadi yace “ ki yi haƙuri in sha Allah komai ya zo ƙarshe, ki natsu ki tashi ki tafi gida ki sami mahaifinki ki sanar da shi komai”.
Dama abinda take tunani kenan, don haka Baba maigadi yana fita ta tashi ta wanke fuskarta ta gyara kanta.
Sannan ta ɗakko waya ta kira musaddiƙ bugu ɗaya ya ɗauka, yana tambayarta lafiyarta da makaranta, ta yi ɗan murmushi tace “ komai lafiya yaya, ina son ka yi min izinin zuwa gidan mu ne”, yace “ Bakomai Allah ya tsare hanya”, sai bayan da suka aje wayar ne sannan musaddik ya tsinci alamun damuwa a cikin muryarta, sai dai bai ƙarfafa hakan ba.
Cikin sauri da zafin rai Afrah ta nufi gidansu, cike da tsana da ƙyamatar Haj kilishi, tun kafin ta isa gidan ta kira mallam mahmud domin tabbatar da yana gida, ya yi shirin fita amma wayar Afrah ya dakatar da shi daga fitan, duk da daga Mama Hauwan har Na’ima basa san ota mama Hauwa ta tafi dubiya cikin unguwa, ita kuma Na’ima ta tafi gyaran gashi.
Hakanan ya ji ya ƙosa Afrah ta ƙaraso domin ya fahimci damuwa a cikin maganarta, musamman yadda ta ƙara kiransa ta sanar da shi ya kira Inna Halima zuwa nan gidan nasa, ananne ya kasa jurewa yace “ Afrah wai lafiya kuwa”, tace “ Baba ka dai kirata sannan kayi haƙurin jin komai har na ƙaraso”.
Bai ja maganar ba, yana kashe wayar ya kira Inna Halima ya tabbatar mata ta nemi izinin maigidanta ta taho gidansa yanzu, itama ta so sanin dalilin kiranta amma bai tsaya yi mata wani bayani ba ya dai gaya mata ta taho yanzu.
A waya ta kira maigidanta ta nemi izini sannan ta taho, tayi sa’a yaronta Abdullahi tsayawarsa kenan da mashin ɗinsa a ƙofar gidan ya zo gaisheta, babu ɓata lokaci ta haye mashin ɗin tace ya kaita gidan kawunsa mahmud.

Abdullahi bai shiga gidan ba saboda wani uzuri yana ajeta ya juya.
Inna Halima ta tadda Mallam mahmud da Afrah zaune a kan tabarma a ƙofar ɗaki jugum jugum fuskar Afrah sharkaf da hawaye, mallam mahmud kuwa tagumi ya zuba hannu biyu. Cike da firgita ta ƙaraso tana maimaita tambayar da tun da ta shigo gidan take yinta, “ Meya faru?”.
Mallam Mahmud ya zame tagumin da ya yi yana kallonta yace “Halima yau dai gaskiya ta bayyana, dama ance kwanaki casa’in da tara na ɓarawo kwana ɗaya tak na me kaya”, ta ƙara shiga wasi wasi, tace “ yaya bangane maganar ka ba”, mallam Mahmud ya dubi Afrah yace “ kiyi shuru, ki sa ma Halima video ta gani”. Afrah ta buɗe wayarta ta fito da vedio itama ta sa mata kamar yadda ta sa ma mallam mahmud.Tun Inna Halima na tsugune sai ga ta ta yi zaman dirshan tana share zufar da ke keto mata ko ta ko’ina.
“ Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, amma kilishi ta gama da asara, Afrah sannu da ƙoƙari lalle yau kin samo shaidar da zata gamsar da kowa, da kuma wannan shaidar babu inda ba zamu je ba domin ƙwatoma musaddiƙ haƙƙinsa”, mallam Mahmud ya jinjina kai yace “ kwarai kuwa Halima, duk yadda za’ayi ya zama dole kilishi ta tone asirin da ta yi ma marayan Allah, ni na rasa abinda ma zance tun da na ga wannan vedio na rasa a duniyar da na ke”, cikin kuka Afrah tace “ wannan wane irin mugunta ne, wane irin zalunci ne”, Inna Halima ta janyota ta rungume tana faɗin “ komai ya zo ƙarshe da ikon Allah”.

Nan da nan suka fara shawarar yadda zasu ɓullowa lamarin, Sai dai shawarar da mallam Mahmud ya ba da duk ita suka bi, wato ba zasu tunkari Haj kilishi kai tsaye ba har sai sun fara danganawa da ofishin jami’an tsaro, dalilin hakan yasa Afrah ta kira Murtala ta sanar da shi komai da kuma taimakonsa da take nema na shige musu gaba wajen shigar da matsalar wajen yansanda. Duk inda hankalin Murtala yake sai da ya tashi, tabbas shi ma batun yau yake tunanin akwai sa hannu a cikin lamarin musaddiƙ ba sai dai bai taɓa kawowa a ransa Haj kilishi ke da hannu a faruwar komai ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci Murtala ya iso gidan Mallam Mahmud, haka zalika babu ɓata lokaci suka ɗunguma zuwa police station ɗin gangare inda murtala yake da tabbacin zai sami taimako, kasancewar akwai ƙaninsa a wajen da bai daɗe da fara aiki ba.
Shi yasa babu wani ɓata lokaci aka karɓi ƙararsu haka zalika aka haɗasu da motar yansanda domin zuwa a kamo Haj Kilishi da Haj Rakiya, saboda

Please Login or Register in order to submit comment