Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallonsa, a yayinda Baba maigadi ya yi gaggawar dubansa yace “ Musaddiƙ ina zaka je?”, ya ja ya tsaya ba tare da ya juyo ba yace “ zan shiga na je na duba Haj da jiki ne”, Baba maigadi ya wage baki cike da ɗimbin mamaki yace “ yanzu Haj ce zaka je don duba lafiyarta? Kasan abinda ta yi maka kuwa?”, ananne ya juyo yana dubansa gaba ɗaya, shi kuma Afrah yake kallo yace “ Afrah, kin ko yi masa bayanin komai”, kafin ta yi magana Musaddiƙ yace “ Na sani Baba, ta kuma yi min bayanin komai, amma hakan bazaisa na ƙullaceta ko na wofintar da ita ba, a yanzu tana buƙatar kulawa, bani da wani abu da zanyi mata domin huce haushin abinda ta yi min, kuma tunda Allah ya yi min sakayya meye amfanin jin haushi, ko ƙullatarta”.
Afrah ta harɗe hannayenta a ƙirjinta tana yi ma Musaddiƙ wani irin kallo me cike da nuna jarumtarsa da kuma tsananin ƙaunarsa, sosai take alfahari da shi matuƙar alfahari.
Ya cigaba da cewa cikin rashin nuna damuwa da irin kallon namakin da Baba maigadi yake yi masa. “ Duk kuma abinda tayi kanta ta yi ma, tsakaninta da Allah kuma ya rage domin ni tuni na yafe mata har cikin zuciyata”.
Baba maigadi cike da ƙaunar halayyar Musaddiƙ da kuma ƙara tabbatar da cewa Ya dawo musaddiƙ ɗinsa, ya jinjina kai yace “ Ta ya ya Allah zai bar duk wanda ya taɓa mai kyakkyawan hali irin na ka, Allah ya yi maka albarka, sai dai kuma Haj bata gidan?”.
“ Ina aka kaita?” Lokaci ɗaya suka haɗa baki da Afrah da Musaddiƙ suka tambaya, Baba maigadi ya jinjina kai cike da jimami yace “ Ai abin na Haj ya ci tura, zama tare da ita tamkar ganganci ne don haka jiya Hassana da Hussaina suka kaita gidan mahaukata na cikin gari, tunda shi ma maigidan Hassanan yace bai yarda ta zauna ta yi jinyarta ba, sai dai ta zaɓa ko jinyar ko aurenta, dama Hassanar ce mai tausayin don Hussaina tunda ta zo ta ganta sau ɗaya bata dawo ba sai da zasu kaita gidan mahaukatan”.
Musaddiƙ ya nisa cike da ɗimbin damuwa yasa hannunsa ya shafi fuskarsa yana faɗin “ Hasbunallahu wani’imal wakil”, Afrah tace itama wannan karon akwai damuwa akan fuskarta tace “ Haj ce ke gidan mahaukata, ke duniya ina zaki da mu”.
Baba maigadi yace “Ta na can Afrah, domin halin da take ciki ya ƙazanta tunda harta fara duka ga uwa uba tonon asirin da take ta yi ma kanta”.
Wasu siraran hawaye suka zubo da ga idanun Musaddiƙ cikin mutuwar jiki yace “ Allah ya bata lafiya”, ya juya ya shige ɓangarensa, Afrah ta bi bayansa.
Baba maigadi su ka bari baki sake, yana jinjina zuciya irinta Musaddiƙ, lallle musaddiƙ mutum ne ya kuma cika ɗan halak wanda ba ya rama sharri da sharri, Haj kilishi dai yau babu wani boka da zai iya cireta daga wannan masifar da take ciki, kuɗi kuma gasu nan basu hana masifa faɗa mata ba babu wani rana da suka yi mata, dama kuma ƙarshen duk wanda ya kaucewa hanyar Allah kenan, mu da aka bamu kur’ani har me muke nema a duniya babu warakar da babu acikin kur’ani, ya Allah kasa mu fi ƙarfin zuciyar mu………..


Yar gidan Imam✍️
MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
( mrs Aliyu Mayare)

Page 11
Suna shiga gidan, ruwan wanka Afrah ta fara haɗawa Musaddiƙ, haka zalika tana ta ƙoƙarin korar damuwar da ke tare da shi, wanda ba ta raba ɗaya biyu damuwar halin da Haj kilishi take ciki yake yi. Bayan ta kai masa ruwan wankan Musaddiƙ ya daɗe a banɗakin yana wanke jikinsa, yana jin tamkar ya cire fatar jikinsa ya wurgar, domin ji yake babu wanda ya kai shi datti a duniya, yana juya lamarin ace wai mutum kamarsa ne ya yi shaye shaye, shi da ko ƙauri ba ya so balle harta kai shi ga shaye shaye.
Domin ba ya taɓa manta lokacin da yake zama hannun Inna Halima kullum ta yi girki da icce sai ya yi ciwon kai, dalilin hakanne yasa mahaifinsa ya ba da kuɗi Inna Halima ta sayo manyan risho na girki.
Tabbas yasan Haj kilishi ta cutar da shi, bata kyauta ba abinda ta yi masa, sam bai ji zafin rashin dukiyarsa ba irin yadda ya ji zafin ɓarin mutuncinsa da tasa ya yi, ta haɗa shi da ɗabi’un da basu da kyau, abin ƙyama, shin da wane ido zai dubi sauran jama’ar arziƙin da yaƙi su ya guje su, a dalilin baƙar halayarsa.sai dai ya yi ma Allah godiya da ya kuɓutar da shi daga wannan mummunar ɗabi’ar, Allah ya yi masa maganin komai ya kuma kori ƙarya ya tabbatar da gaskiya, wannan kaɗai ya isa hujjar da zai yafe ma Haj kilishi.
Bayan ya fito wanka, irin ɗabi’arsa ta da ya yi, wato doguwar jallabiya kawai ya zura ba tare da ya shafa mai ba, sai turare da yabi jikinsa da shi ya feshe, ya koma ya ɗauro alwalar magriba, kasancewar an kusa kira, yana rike da casbaha a hannunsa sai karamar hula da ta lafe a saman kansa, duk da ya rame amma sai ya ƙara matuƙar kyau.
A kicin ya tadda Afrah tana ƙoƙarin gama girkin da tun shigowarta ta ɗora, ya dan daɗe yana tsaye yana kallonta yana jin wani irin ƙauna da soyayyarta na ƙara kama zuciyarsa, cikin taushin murya yace “ sannu da aiki kanwata”. Ta waigo da sauri tana kallonsa ya yi mata matuƙar kyau, ta yi murmushi sosai tace “ yauwa, sannu da fitowa sai ina kuma?”. Ya yi ɗan murmushi wanda ya ƙarama fuskarsa kyau, sannan yace “Naga an kusa kiran sallar magriba ne, shi ne zan tafi masallaci na jira”, ta lumshe ido ta buɗe cike da tsananin jindaɗi tace “ To a dawo lafiya, Allah ya tsare”, ya gyaɗa kai ya wuce yana faɗin “Madallah”, da sauri ya fice, yayinda ta bishi da kallo cike da farinciki, yau dai dukkan mafarkinta ya cika, mojinta ya dawo Musaddiƙ ɗinsa, lalle komai lokaci ne, komai kuma yana da iyaka, tabbas yanzu ne za ta ƙara cin ribar haƙurin da ta yi da shi, da kuma biyayyar da ta yi ma mahaifinta, haka zalika yanzu ne zata ƙara sanin daɗin aure da irin farincikin da ake samu a gudan aure, domin ita kanta tasan ta yi dacen miji ɗaya da ɗaya.
Afrah tasa rai Musaddiƙ zai dawo bayan sallar magriba, amma sai ta ga saɓanin haka, domin bai dawo gida ba sai bayan sallar issha’i domin sai da ya yi shafa’i da wutiri sannan ya dawo gida. Ya tadda abincinsa a kammale cikin tsafta kamar kullum. Afrah na gyefe kan sallayarta, a tausashe tace “ sannu da dawowa”, ya amsa lokaci ɗaya ya na zama kusa da ita sosai, yace “yauwa”, ya na kallonta, ta yaye hijabin kanta da nufin tashi, amma sai ta ji yasa hannayensa biyu ya janyota jikinsa ya rungumeta tsam, tamkar zai tsaga jikinsa ya maida ta ciki, yana saukar da numfashi a hankali, Afrah ta sunne kanta cikin ƙirjinsa tana jin wani irin nishaɗi a tare da ita, shafa ko’ina na jikinta yake yana jin kamar bai taɓa shiga jikinta ba sai yau, jikinsa har wani rawa yake, fahimtar halinda yake ciki yasa Afrah ta ɗago da ƙyer cikin mutuwar jiki tace “ Yaya ga abinci nan fa”, girgiza kai ya yi ido jajir, ya miƙar da ita zuwa cikin ɗaki, ganin yadda ya rikice yasa Afrah bata da wani zaɓi da ya wuce ta yi masa abinda ransa yake so, hakan yasa babu wani musu ta bi shi a yadda ya ke so.
Sun daɗe suna faranta ran junansu, suna jin tamkar wannan shi ne daren su na farko, sai da suka kammala komai tare su kayi wanka,bayan sun kintsa suka fito tare zuwa inda abinci ya ke. Afrah na zuba abincin sai dai ko ya ya ta ɗago sai ta ga idanun Musaddiƙ na binta da kallon ƙauna da sha’awa. Tare su ka ci abincin, bayan sun kammala ne ta kwashe kwanukan ta fita da su, a yayinda Musaddiƙ ya tashi ya je ya wanke bakinsa sannan ya dawo ya zauna. Har Afrah ta dawo zata zauna ya yi saurin janyota kusa da shi ya zaunar da ita, sannan sanyin murya yace “Afrah ina ƙara jinjina miki ne, tare da ƙarin ganin darajarki, ta yadda ki ka juri zama da ni a cikin wannan ƙazantaccen yanayin da nake ciki, ina jin kunyarki sosai, tun muna asibiti bana iya kallon idanunki nauyinki nake ji”, ya janyo hannunta ya riƙe ya ɗora fuskarsa akan hannunta yace “ Ina sonki Afrah, son da bazai misaltu ba”.
Wasu hawaye masu ɗumi suka shiga fitowa daga idanun Afrah, Musaddiƙ ya ƙara matse hannunta yana cewa “ ki yi haƙuri, idan wani aibuna na da ki ke tunawa ya saki kuka ki taimake ni ki yafe min idan da dama ma ki manta ki goge shi da ga cikin zuciyarki…..”,
Afrah ta girgiza kai tace “ A’a yaya, kukan murna na ke ba na baƙinciki ba, saboda kafi kowa sanin ban taɓa ƙyamatarka ba, dama ina da yaƙinin cewa wata rana komai zai zama tarihi, domin kuwa nasan cewa addu’ar da nake maka kullum ba zata taɓa tashi a banza ba, tuni kuma na ga canji yanzu ragowa kawai aka ƙarasa nasan yanzu babu sauran wata damuwa, Alhamdulillah”. Musaddiƙ ya aje numfashi a hankali, yana yi mata wani irin gigitaccen kallo me cike da so da ƙauna yace “ Nagode ma Allah, sannan na gode ma kawu Mahmud da Inna Halima da suka zama sila suka kuma tabbatar da kasancewarki matata, domin kina ɗaya daga cikin matan da ko wane namiji zai yi fatan samu a matsayin matar aurensa, Allah ya yi miki albarka, ya ba ni kuma ikon da zan sauke nauyinki da ke kaina”.
Ta lumshe ido ta buɗe cikin murmushi tace “ Amin mijina”, ya saki hannunta gami da gyara zamansa ba tare da ya ɗauke idanunsa a kanta ba.
“Afrah, na yi wani tunani ne”

“Tunanin me?”

ta tambaya tana ƙoƙarin gyara zamanta, ya ɗan numfasa yace “ Ina ganin zan aje aikin nan da nake yi”, ta yi saurin kallonsa, a gaggauce tace “ saboda me?, wani abu ya faru ne yaya?”, ya girgiza kai gami da lanƙwasa yantsunsa har su ka yi ƙara sannan yace, “ A’a babu abinda ya faru, kawai dai na yi tunanin bai kamata ace ina aikin kare lafiyar macen da ba muharramata ba, haramun ne a gare ni na dinga kusantarta, haka zalika da karatuna da takarduna ina ganin bai kamata na yi aikin da bai dace da ni ba kaskantaccen aikin da baida ko daɗin faɗa a baki”. Ikon Allah lalle tunanin Musaddiƙ ya dawo, babu abinda Afrah take maimaitawa a zuciyarta sai Alhamdulillah.
Ta ƙara matsowa kusa da shi sosai tace “ yaya ina ganin ai mun gama wannan maganar tun kafin ka karɓi aikin nan, idan murtala ya samar maka wani aikin zaka saki wanda ka ke yi”, ganin ya tsaya sosai ya na sauraranta yasa ta cigaba da cewa “ kuma bayan ka fara aikin nan, na fahimci babu rufin asirin da ya fi shi, tunda kana iya ciyar da ni ka tufatar da ni, gami da ɗaukar nauyin karatuna, duk wata hidima da ta zo gabanka ba ka tsoron ka tunkareta, duk a sanadiyyar wannan aikin, to ko ka ga kuskure ne babba ka saki wannan aikin ba tare da ka samu wani ba”.

Musaddiƙ ya jinjina kai ba tare da ya katseta ba, ta yi shuru gami da haɗiye yawun bakinta ganin baida alamar zai yi magana yasa ta cigaba da cewa “ kuma kada ka manta karamci da mutunci irin na Haj Hudah, kaima kasan macece mai tsananin mutunci tausayi, da jin ƙai musamman ga ku ma’aikatanta, ka duba yadda ta dinga ɗawainiya da ni alokacin da na yi jinya mai wahala, sannan ka duba yadda ta kula da kai a lokacin da babu kowa kusa da kai da zai taimake ka, haka zalika ka da ka manta da cewa ta baka aiki a lokacin da kowa ya ke ganinka wulaƙantacce, ya ke gudunka su ke kuma ƙyamatarka,ita ta ɗauke ka a matsayin mutum ta mutuntaka ta baka aikin da ya fara zama silar shiryuwarka”. Ta ƙara nisawa tace “ A gaskiya ni banga wani aiki da ya fi maka rufin asiri da kwanciyar hankali ba , irin aikin ka ba, kuma a shawarce ka cigaba da aikinka, idan ka na tunanin kayi karatu ne, to akwai irinka da yawa da su ka yi karatun kuma suke aikin da baiyi dai dai da karatunsu ba, wasu ma acaɓa suke yi wasu garuwa wasu ma basu da aikin yin, kawai dai abinda ake fata ko mutum ya yi karatu ko baiyi karatu ba to ka da ya bari zuciyarsa ta mutu”.

Maganganun Afrah sun tsaya a zuciyar Musaddiƙ, ya ƙara yabawa da girman tunaninta, ya fahimceta sosai kamar yadda maganganun na ta su ka sami gurbi a cikin zuciyarsa. Ya numfasa yace “ madallah da tunani irin na ki Afrah, tabbas Haj Hudah macece mai hankali da natsuwa ta kuma san muhimmancin ɗan Adam, bata da matsala, don haka babu damuwa zan cigaba da aiki tare da ita har zuwa lokacin da zan samu wani aikin”.
Ta yi murmushi tace “ yauwa yayana” gaba ɗaya su kayi murmushi.
Lokaci ɗaya ya ƙara muskutawa yace “Afrah, lamarin Haj ya na matuƙar tayar min da hankali, bayan fitowata daga masallaci ɗazu Hassana ta kira ni ta na kuka ta na nemar ma mahaifiyarsu gafara a wajena, sannan ta ƙara gaya min matsanancin halin da take ciki a gidan mahaukata”.
Afrah ta numfasa tace “ zahiri Haj ta yi aikin da ya haramta, ta cutar da kai, ta ƙwari rayuwarka, bata kyauta ba kwata kwata, domin ta yi maka mafi munin zalunci, wannan kuma hauka da Allah ya ɗora mata ishara ce babba ga duk me hali irin na ta, kai kuma sakayya ce a gareka, don haka yakamata ka cire damuwar komai a ranka akan Haj, ta jira itama har Allah ya yanke mata wahala, kamar yadda kaima ka jira har Allah ya kawo ƙarahen al’amarin, don haka ka daina damuwa sakayyar Allah ce a kanta”, ya ɗan goge hawayen da ya gangaro daga kwarmin idonsa yace “ Allah yasa mu fi ƙarfin zuciyar mu”, ta amsa da “Amin ya Allah”.daga nan rufe maganar kowa su kayi su ka shiga tsara yadda rayuwarsu zata cigaba, cikin rufin asiri da kwanciyar hankali.

Sai dai hankalin Musaddiƙ bai ƙara tashi ba sai da ya ziyarci Haj kilishi a gidan mahaukata, Hassana ce ta yi mai jagora, sai dai masu tsaronsu sun tabbatar masa da cewa an daina buɗeta kamar yadda aka maidata ɗaki ita kaɗai a ciki saboda duka da take yi, ko masu basu abinci sai dai su tura mata basa shiga ɗakinta, masu bata magani da masu mata allura da masu sa mata shokin su kaɗai take ragama. Don haka wani waje aka nuna musu inda zasu tsaya suna iya hango Haj kilishi. Kuka sosai Musaddiƙ yake yi tausayinta yake ji har cikin zuciyarsa, yadda ta rame ta yi baƙi duk jar fatar nan babu,ta fita hayyacinta babu yadda za’ayi ka iya gane wacece ita, musaddiƙ bai iya ƙarasa ganinta ba yabar wajen, Hassana ta biyo shi tana ba shi haƙuri gami da jinjina kyawun zuciya irin nasa. Anan take gaya masa irin kuɗin da ake kashewa a wajen, da kuma yadda yan tsirarun danginta da suka rage suka kasa zuwa su dubata, domin acewarsu bata ɗauke su a bakin komai ba a lokacin da take cikin daula da mulki su ma don me zasu damu da ita a yanzu da take cikin haukar da ita tayi silar samuwarta, ta ƙara da cewa hatta Hussaina ta ƙi shiga lamarin tunda suka kawota gidan mahaukata ta ɗauke ƙafarta ita kanta a yanzu bata samun zuwa gunta yadda yakamata saboda tana samun matsala da mijinta akan hakan, wanda tun da ya san abinda ya haddasama Haj kilishi hauka ya tsaneta yake kyararta yana ganin halinta ɗaya da mahaufiyarta itama tana bin bokaye, Hassana ta goge hawayenta ta cigaba da cewa “ wannan abin da Haj ta aikata har rayuwata ya taɓa don ni yanzu ba ni da kataɓus a gidan mijina, ba ni kuma da halin taimakama mahaifiyata yadda yakamata duk so na da yin hakan”.
Tausayinta ya ƙara kama Musaddiƙ yace “ ki yi haƙuri, ki ɗauki wannan a matsayin ƙaddara, in sha Allah ni zan dinga zuwa ina ganin Haj ina kuma sanin halin da take ciki, ke kuma sai ki cigaba da biyan kuɗaɗen da ake buƙata tunda ba ni da su”,
Ta kasa magana sai kuka, tana ji aranta ina ma ita Allah ya ba zuciya irinta musaddiƙ, duk irin abinda Haj ta yi masa amma yau shi ne yake faɗin zai yi abinda yayan cikinta suka kasa yi mata, Hassana ta yi masa godiya mai yawa tare da ƙara ganin kimarsa da girmansa.

Tunda Musaddiƙ ya koma bakin aikinsa, sai Haj Hudah ta ke ganinsa tamkar wata sabuwar halitta, domin yadda kamewarsa ta fi ta da, ga shigar kamala ga shi addini ya ratsa shi duk inda zasu zaka same shi riƙe da casbaha ya na ja, ga wani abu da ya fi tsaya mata arai shi ne yadda a yanzu Musaddiƙ ko ido baya iya haɗawa da ita, yadda kuma idan sun je waje suke jerawa su tafi tare ya daina yanzu can nesa yake tsayawa, yadda kuma su ke tsayawa su ci abinci a tebur ɗaya shi ma duk ya daina domin ko abincin ne ma ba ya iya ci a gabanta, ta fahimci yanzu akwai tsananin tsoron Allah a tare da shi, shin idan hakan ya cigaba ya ya makomar soyayyarta a gare shi, shin ya ya zai ɗauki al’amarin a duk ranar da ta fallashe masa asirin da ke cikin zuciyarta, domin tasan idan ta cigaba da dakon soyayyar da ba’a san tana yi ba to zuciyarta tana iya fashewa. Domin dai kullum soyayyar Musaddiƙ gaba take ƙara yi ba baya ba harta kai a yanzu bata ko kallon Alh yusuf sanda a matsayin mijinta domin bata da sauran wani taɓi akansa. Ta fi kowa sanin wannan wauta ce zalla take yi son mijin wata a matsayinta na matar wani, sai dai kuma ta riga ta bari shaiɗan ya buga mata gangarsa don haka dole ta taka rawa, domin kuwa ta sha alwashin mallakar musaddiƙ ko ta wane hali, tana son ta mallake shi ko da na uni ɗaya ne, kuma ko ta halin ƙaƙa sai ta cika burinta.
A wannan tsakanin ne Afrah ta fara laulayi, gwajin farko likita ya tabbatar da cewa tana ɗauke da juna biyu, wai murna wajen musaddiƙ ai ba’ a magana sai dai kuma irin bayanin da likita ya yi masa yasa murnarsa ta ragu domin likita ya tabbatar masa da cewa ciwon ƙodarta ya kusa kaiwa matakin da ba’a so yanzu kuma da taimakon wannan cikin ciwon nata zai iya ƙarasawa matakin da babu wani zaɓi face ayi mata dashen ƙoda ko kuma a rasata gaba ɗaya. Tun suna asibitin Musaddiƙ ya ji ya haƙura da cikin, bai ɓoyema Afrah komai ba ya sanar da ita duk halinda ake ciki, yana rungume da ita yace “ Na sanar da ke halin da rayuwarki take ciki ne, domin ki ba ni goyon baya ki taimake ni a cire cikin nan domin na fi sonki da cikin, na fi son na rayu da ke domin idan na rasaki rayuwata ba ta da sauran wani amfani, don Allah ki yarda a cire cikin da ke jikinki, domin na fi buƙatarki fiye da cikin ,…………..




Yar gidan Imam✍️
MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
(mrs Aliyu Mayare)

Page 12



A gaggauce Afrah ta ɗago da idanunta da suka kaɗa su kayi jawur, ta ɗorasu akan Musaddiƙ tana cewa, “ A cire ciki yaya Musaddiƙ?”, ya gyaɗa kai shi ma damuwarsa ta ƙara yawa, a sanyaye yace “ Eh, ki yi haƙuri a cire domin samun lafiyarki, da kuma samun natsuwata”, duk yadda ta kai da tare hawayenta ka da ya sauka sai da ya gangaro saman kuncinta, cikin rawar jiki Musaddiƙ yasa harshensa ya shiga ɗauke hawayen na ta.
Ta runtse idanunta kam, tana jin nauyin faɗan abinda bakinta ke son faɗa, amma ba ta da wani zaɓi da ya wuce a yau ta bijirema umarnin mijinta abinda ba ta taɓa tunanin zata iya yi ba a rayuwarta. Ta buɗe idonta a hankali tace “ka yi haƙuri amma bazan iya zubar da cikin nan ba, bayan shi ne shaidar soyayyarka a gare ni, ko da zan rasa raina na yarda matuƙar ɗan da zan haifa zai rayu, domin ina da tabbacin zaka zamar masa uwa da uba, ba kuma zaka taɓa barinsa ya yi kukan rashin uwa ba”, nan da nan Musaddiƙ ya haɗe fuska, ya zare kansa daga kan gadon ya tashi tsaye, yayinda ta bi shi da kallo, ya dawo gefen da take kwance ya na kallonta yace , “ Kina tunanin zan iya yin wata kyakkyawar rayuwa ne ba tare da ke ba, me yasa ba zaki yarda da uzurina ba, tunda likita yace akwai matsala ai yakamata ki yi tunani babu yadda za’ayi na bari ki salwantar da rayuwarki saboda kawai ki kawo ɗana ko yata duniya, idan hakan ya kasance bazan taɓa yafewa kaina ba, don haka dole ki bari a cire cikin nan”. Ya ƙarasa maganar cikin fusata, Afrah ta goge hawayenta cikin dakewa tace “ Na shirya kawo ɗanka duniya ko da zan rasa raina, babu kuma abinda zai canja hakan, domin na riga na yankema kaina hukunci”, ya tsaida jajayen idanunsa akanta yace “ Ba zaki bi umarni na ba kenan”, ta girgiza kai tace “ wannan karon dai kayi haƙuri kayi min kuma uzuri, sannan ka fahimce ni”.
Ba tare da ya ce uffan ba ya juya ya fice daga ɗakin.
Lokaci ɗaya kuka mai ƙarfi ya ƙwacema Afrah yau itace rana ta farko da ta bijirema umarnin mijinta, haka zalika ba ta jin duk duniya akwai wanda zai sa ta ta zubar da cikin musaddiƙ.

Ba’a jima ba Musaddiƙ ya dawo tare da likitan, ya kawo shi ne musamnan domin ya yi mata bayani da bakinsa, amma wani abu mafi ɗaure kai shine yadda sam Afrah ta ƙi sauraron likitan, haka zalika abinda ya ƙara tsorata Musaddiƙ shi ne yadda duk bayanin da likitan ya yi mata bai tsorata ta ba, bai kuma sagar da guiwarta ba, domin dai ta dage tana nan akan bakanta na baza ta bari a cire

Please Login or Register in order to submit comment