Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakan ma kenan ina son haɗuwa da ke, ai dama nayi imani da cewa addu’ar da na kwana na uni ina yi Allah ba zai bamu ikon haɗuwa da juna domin saɓa masa ba”, kalaman Musaddiƙ su na yi mata ciwo amma sun kasa sawa ta ga laifinsa ko ta tsane shi, maimakon hakama saita kwantar da murya tace “Duk da a irin kalamanka sun tabbatar min da baka son sanin dalilin da yasa ba mu haɗu ba, na ga ya dace na gaya maka cewar maigidana ne ya yi min dawowar bazata yanzu haka ina tare da shi a abuja kuma bansan ranar dawowata ba”.
Wani murmushi ya suɓuce a fuskar Musaddiƙ, Allah kawai yake ma godiya mara misaltuwa.

“Ka yi shiru, ko baka ji me nace ba ne”

Cewarta cikin wata irin raunanniyar murya.

Musaddiƙ ya numfasa yace “Na ji daɗin hakan, domin mijinki shi ne halak ɗinki ni kuma haramun ne a gare ki, ya kamata ki farka ki fita daga duniyar shagalar da ki ka faɗa, saɓama Allah da mu kayi a baya mu je mu cigaba da neman yafiyarsa, zaifi miki sauƙi ki manta da ni ki cire ni a ranki, domin na rantse miki ban taɓa jin so ko ƙaunarki a raina ba, asalima ban taɓa kyamatar wata mace ba sama da ke, matata kaɗai ce a raina itace agabana, ina kuma nadamar duk abinda muka aikata tare, kamar yadda na ke neman tsari da ke, kin ganni nan ba ki taɓq burgeni ba domin a idona babu wata mace sama da matata, me yasa ba zaki gane hakan ba ki rabu da ni, ki taimake ni ki taimaki kan ki, ki goge wannan vedion a wayarki ki kuma manta da ni”.

Daka masa tsawa ta yi cikin kukan da ba ta san sanda ta fara ba tace “Na rantse yau da a gabana ka ke gaya min irin waɗannan maganganun masu ɗaci da na koya maka hankali, kalamanka sun illata min zuciya, domin ni ina sonka ina sonka ina sonka, kuma duk abinda zaka faɗa ba zai hana ni sonka ba, kamar yadda bazan taɓa goge vedion ba domin shi ne makamin da zan cigaba da yaƙar ka da shi”, sai da ta gama maganar ne ta fahimci ma ashe tuni ya kashe wayarsa.zubewa ta yi ƙasa tana sharar hawaye tamkar wata ƙaramar yarinya, kalaman Musaddiƙ na cewa bai taɓa sonta ba sun taɓa masa zuciya. Sai dai ba ta jin zata iya rabuwa da shi domin ta riga ta yi zurfi a son sa da ƙaunarsa ta na jin koma me ya yi ba zai zama laifi ba, sai dai ta ji damuwa me yawa a ranta domin duk duniya a yanzu ba ta da wani buri da ya wuce ace yau Musaddiƙ ya so ta ko da kwatan son da take masa ne.
Alh Yusuf sanda ya saki tsaki bayan katsewar wayar, tsanar Haj Hudah ya ƙara sarsuwa a cikin zuciyarsa, ya kauda kansa daga wayar zuciyarsa na wani irin ƙuna, ya na ƙara jin a ransa bazai taɓa bari Haj Hudah ta ƙara kusantar Musaddiƙ ba, ta riga ta ci taliyar ƙarshe sai kuma ta jira hukunci daga gare shi da ita har Musaddiƙ ɗin duk sai sun bambance tsakanin aya da tsakuwa, zasu gane ɓakko miya ce. Vedio kuma da ba zaki goge ba ni zai ma amfani ba ke ba, abinda ya faɗa kenan a hankali.

Musaddiƙ ya ɗan sami kwanciyar hankalin kiran Murtalq ya yi masa bayanin komai, sosai ya kwantar masa da hankali ya kuma tabbatar masa zai lalubo masa gidan haya mai kyau, kada ya damu.
Taɓangaren Inna Halima kuwa yau yammaci ta yi ma gidan Mallam Mahmud, su biyu a ƙofar ɗakinsa kan tabarma suke tattauna maganar da ta kawota,ya fahimceta tsaf, ya dubeta yace “Babu damuwa Halima, ko nawa ne gidan hayan ya nemo zamu biya tunda akwai kuɗi a ƙasa, babu abinda na taɓa na yi da su, ko cefane ban taɓa yi a ciki ba, dama na bari komai ya lafa ne Afrah ta koma gidanta sannan sai muyi maganar yadda za’ayi”.
Kafin Inna Halima ta yi magana, mama Hauwa da take kashe da kunne ta ke jin duk abinda suke faɗa.

Tayi saurin tsame hannunta a cikin ruwan wankin da ta ke yi , ta taso a fusace ta ƙaraso inda suke zaune, tana kallonsu tace,”Ni fa mallam bangane ba, me yasa kullum Afrah kaɗai ka ke bautama da mijinta, bayan ka yi masa aure, sannan yanzu ace har gidan da za su zauna kaine zaka kama mu su, ba fa ita kaɗai ka haifa ba ka da kq manta haka, amma duk damuwar sauran yayanka ba damuwarka ba ce damuwar Afrah ce kaɗai damuwarka, ko wane ɗa ya na da haƙƙi a kanka, tsakani da Allah ka dubi Na’ima a gabana gote gote har ysnzu babu mijin aure amma babu abinda ya dameka, duk hankalinka da damuwarka su na kan Afrah da mijinta”

Inna Halima za tayi magana Mallam Mahmud ya rigata, inda ya yi mata wani irin kallo yace “Ina mamaki da har yanzu ba ki daina nuna hassada da baƙinciki akan Afrah ba, to ina son ki sani bazan gaji da gaya miki ba dole damuwata ta ta’allaka akan Afrah da mijinta, domin sunyi min biyayya a lokacin da na rasa me yi min biyayya, Afrah ta nuna min farincikina shi ne na ta ba ta damu da komai ba sai kwanciyar hankalina, don haka dole ni ma na kyautata mata na kuma taimaketa ita da mijinta”.

Ya dakata ya na ƙara kallon yadda ta ke wani girje girje ya cigaba da cewa,

“Rashin samun mijin Na’ima kuma ya kamata ki sani ishara ce, tunda ta ƙi yi min biyayya ta na ganin zata yi zaɓin da ya fi nawa to shi yasa Allah ya barta ta yi zaɓin da kanta, to don me ni kuwa zan damu da damuwar wanda bai damu da ni ba, don Allah Hauwa ki sakarma Afrah mara ta yi fitsari , na sha gargaɗarki akan ki daina shiga harkarta tunda babu alheri a kan harshenki, ya kamata kuma ki dinga kallon darussan da ke zagaye da ke gudun ka da ki faɗa komar nadama da danasani me yawa”.
Mama Hauwa ta ƙara turo baki tace “Gaskiya ce dai ba’a son na faɗa , to ka cigaba ka yi ta fifita Afrah, ni ba ka burge ni ba idan ba ka babbaka nawa yayan ba , ƙarewar ƙiyayya kenan”.

Shirun da ya yi ya ba Inna Halima damar yin magana tace,

“Babu mai babbaka su, domin su ma ana son su, su ma kuma yaya ne, ke ce dai ya kamata ki hankalta ki maida Afrah ya a wajenki kamar sauran yayanki”
Ta taɓe baki tace “To na ji gwana ta gwanaye, na ƙi na maidata yar tawa, dama ko wane kisisina da makirci ai ke ce sila, kin gama da shi huɗubarki kawai ya ke ɗauka , to ki je ki cigaba da nuna masa ni maƙiyiyar yarsa ce, kai kuma Allah ya ba ka cigaba da fahimta”, ta saki tsaki ta wuce tabar wankin ta shige ɗaki cike da takaici da baƙincik. Basu damu ba suka cigaba da tattaunawa sai gaf da magriba sannan Inna Halima ta tafi gida.

Murtala ya yi dacen samo mu su gida mai kyau, sabo ne mutum ɗaya ne ya taɓa shiga shi ma bai daɗe ba ya tashi saboda canjin wajen aiki da akayi masa.
Gidan flat ne me ɗauke da falo da ɗakuna guda biyu da wajen cin abinci da kicin da store, da kuma banɗaki a ko wane ɗaki, ga get ga haraba mai girma gida dai ya yi kyau baida wani makusa.
An ba su gidan akan nera dubu ɗari uku,Mallam Mahmud ne ya biya kuɗin, cikin ƙanƙanin lokaci aka gama kwashe kayan Afrah tas zuwa gidan.

Bayan duk an gama kintse kintse, inna Halima ta ƙara yi ma ta yan saye sayen ƙananan abubuwa da na ta su ka lalace.Afrah ta tare a gidanta , gwanin ban sha’awa ga lafiya ga yarta a hannu komai tsaf tsaf. Kwanaki uku da tashin su, su Hassana su ka saida gidan domin cigaba da kulawa da Haj kilishi da har zuwa wannan lokacin ta ke cikin mawuyacin hali. Musaddiƙ ya saki jiki wata irin sabuwar soyayya suka ɓalle tsakaninsu da Afrah tun tarewarsu a gidan babu komai a cikin gidan sai kwanciyar hankali da soyayya, tunda ya daina ji da ga Haj Hudah ya sanya ya fara jin natsuwa a tare da shi, yasan kuma rashin ji daga gareta ba ya rasa nasaba da ƙila har yanzu mijinta ya ns gari, bata da wata sakewa, duk da jefi jefi tana wurgo masa saƙon waya ta na nuna yadda take cikin kewarsa, shi kam ya rasa wace irin macece Haj Hudah.
Me yasa ba zata rabu da shi ba?.

Tuni Afrah ta koma makaranta ta cigaba da gyara duk abinda ta rasa a dalilin jinyat da ta yi.
Makonni uku da komawar Afrah Mallam Mahmud ya buƙaci ganin Inna Halima, Musaddiƙ da Afrah.
Duk a ɗakin mallam Mahmud ɗin suka zauna, Hanan na hannun Mallam Mahmud, wanda tunda mama Hauwa ta ga wannan taron ta kasa sukuni, sai ta kai gauro ta kai mari a ƙofar ɗakin ta na son ta ji abinda zasu tattauna. Mallam Mahmud ya ɗakko kuɗi ƙulle a baƙar leda kimanin naira miliyan ɗaya da rabi ya miƙama Musaddiƙ, cikin sanyin jiki ya amsa yana kallonsa alamun neman ƙarin bayani.

“Mun riga mun gama magana da Halima,wannan kuɗin mu ne, ni da Halima wanda mu ka saida kadararmu, nera miliyan ɗaya ne da rabi”, musaddiƙ da Afrah suka fiddo idanu waje suna maimaita yawan kuɗin, mallam Mahmud ya cigaba da cewa “ Mun ba ka ne domin ka je ka ja jari, ka yi tunanin irin kasuwancin da zaka yi mai tsafta, wanda zaka sami alheri, mun mallaka maka kuɗin , tunda ka nuna mana burinka na son yin wata sana’a ko aiki maimakon zama ƙarƙashin wata da sunan aiki, ka juya su duk sanda ka ga wani abu da zaka amfana da shi to ka yi, amma ina son kasa tsoron Allah akan ko wace irin sana’a da zakayi, domin tsoron Allah shi ne matakin nasara”.

Hawaye ne kawai ke fitama Musaddiƙ ya ɗora kansa akan cinyarsa yana sharar hawaye, haƙiƙa da haka kowa ya riƙe zumunci, to da babu wani ɗan-uwa da zai shiga damuwa ko da zaiyi maraici har yasan cewa shi maraya ne. Cikin kuka ya ke yi musu godiya mara misaltuwa. Inna Halima ta ɗaga masa hannu alamar ya isa yabar kuka, ita kanta Afrah jikinta ya yi sanyi ta ƙara yarda mahaifinta ya na ƙaunarta, yau da ba ta yi masa biyayya ba da ta taɓe duniya da lahira. Cikin sanyin murya itama take musu godiya.
Mallam Mahmud ya dubi Afrah yace “Mamana, yan-uwanki kabir da Mansur sun ba da gudunmawar kuɗi a lokacin da za’ayi miki aiki, Bayan kuma Haj Hudah ta ɗauki nauyin aikin, na yi yunƙurin maida musu da kuɗin musamman da na ga yadda mahaifiyarsu ta sanya ido akan kuɗin, amma da na mayar musu sai su ka ƙi karɓa, sun tabbatar min da cewa sun ba baki kuɗin idan kin tashi ya zama mallakinki”. Ya janyo wata baƙar ledar ya miƙa mata yace “Don haka ga su kema ki ja na ki jalin, ki nemi sana’a Allah ya yi musu albarka”. Ta numfasa tace “Allah ya saka mu su da alheri Allah ya bar zumunci, nagode sosai, amma Baba mai zai hana ki riƙe kuɗin kaima ka yi wani abu da su”, ya girgiza kai cikin murmushi yace “A’a babu abinda zanyi da su Afrah ke yafi cancanta da ki yi amfani da su, ina cikin rufin asiri yadda nake iya ciyar da gidana, don haka ke ce nake son na ga kin tsaya da ƙafafunki”, Inna Halima tace “ki karɓa Allah yasa mu su albarka Afrah”. Tasa hannu ta ƙarɓa ta na cigaba da yin godiya.
Haƙiƙa samun iyaye irin mallam mahmud da inna Halima ma su son yayansu da son zumunci , sai an tona, a yau dai sun sanya Afrah da mijinta cikn cikin jin daɗi da farinciki mara misaltuwa.

Duk iya yadda Haj Hudah ta so ta yakice Alh Yusuf sanda a jikinta ta kasa domin tun tana ɗaukar abin da wasa harta tabbatar da cewa da gaske fa Alh Yusuf yake ya dawo gareta gaba ɗaya, ya na kuma son kasancewa da matarsa. Tayi tayi ta ganar da shi, ta yarda ya cigaba da kasuwancin da yake yi da ƙasashen duniya kamar yadda ta tura masa saƙo tun yana germany, amma ya dage akan shi fa a yanzu ita kawai ya ke buƙata fiye da komai a rayuwarsa.

Wannan furuci ya ƙara tayar da hankalinta ƙwarai da gaske, a ƙalla sai da su ka yi mako uku a abuja, a wannan lokacin ne Alh Yusuf sanda ya yi duk yadda zaiyi domin ganin ya sami nasarar ciro wannan mummunan vedion daga cikin wayarta, a ranar da ya kalla duk da mugun nufin da ke cikin zuciyarsa sai da ya ji tamkar ya shaƙeta ta mutu har lahira saboda tsananin ƙiyayya ko kallonta ya yi shi kaɗai yasan baƙin cikin da yake yi, amma haka nan ya cigaba da yaudararta ya na nuna mata tsantsar ƙauna wanda ita kuma abin sam ba ya burgeta domin duk wannan abin da ke faruwa son musaddiƙ da tunaninsa ne fal a ranta.
Ga shi kwata kwata baya barinta bare ta sami damar kiran musaddiƙ, sau tari idan abin ya dameta banɗaki ta ke shigewa ta kira musaddiƙ amma baya ɗauka, babu amfanin ta cigaba da yi masa barazana tunda babu halin ta haɗu da shi, hatta aiki idan ya taso mata bai barinta fita ita kaɗai tare suke tafiya, duk inda tasa ƙafa nan yake mayarwa, ta rasa wannan wace irin masifa ce.
A ƙalla Alh Yusuf sanda ya sami watanni biyu bai fita Nigeria ba yana maƙale da matarsa kamar cingam. Har wata yar ƙwarya ƙwaryar rama ta yi.

Zuwa wannan lokacin kuwa abubuwa duk sun fara yi ma Musaddiƙ da Afrah kyau, domin Musaddiƙ ya kama ƙaton shago da kansa yake zuwa legos yake shigo da wayoyi da kwanfitoci, ya samu oga acan legos ɗin me kirki da karamci. Sau biyi kawai musaddiƙ ya sayo kaya a hannunsa ya yaba da hankali da natsuwarsa, domin Alh Nasiru wanda yayan Murtala ne ya haɗa shi da shi a legos ɗin yake. Ya na fahintar amana irin na Musaddiƙ, sai ya buɗa masa yakan bashi kayan dubu ɗari shida ba tare da ya ba da kuɗi ba, sai ya sayar ya ɗauki ribarsa ya kuma maida masa da uwar kuɗin, Hakanne yasa shagon musaddiƙ ya cika sosai da duk kalar waya da kwanfitoci na zamani ga sauƙi hakan yasa cikin ƙanƙanin lokaci shagon nasa ya fara sanuwa.
Daga bisani itama Afrah Musaddiƙ ɗin ya amshi kuɗin hannunta ya fara saro mata sarƙoƙi da jakunkuna da takalma da lesses a legos ɗin, nan da nan itama kasuwancin na ta ya fara faɗaɗa, har makaranta take zuwa da kayan tana tallatawa ta na kuma samun masu saye.
Zahiri da alama Allah ya sa ma kasuwancin na su albarka. A wannan lokacin hankalin musaddiƙ ya kwanta sosai har ya na jin tamkar matsalolinsa sun zo ƙarshe……….. sai dai kash akwai sauran rina a kaba……..

Yar gidan Imam✍️
https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk

Ina masu son samun sayen kaya cikin farashi mai sauki, sayan daya ko sari, tun daga kan kayan kicin, supliment masu kyau, leses, shoes and bags, abayas Kala kala, kayan yara,kayan Ƙamshi, kai wannan kasuwar duniya ce, harda counselling na matsalolinku duk ana yi a ciki, Yar Gidan Imam Empire ya haɗa komai,ku shigo domin mallakar burinku 🙏


MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
(Mrs Aliyu Mayere)

Page 23

Komai fa ya gama cabewa Haj Hudah duk yadda ta ɗauki lamarin ya wuce nan,ba ta da Wani sukuni ko kwanciyar hankali, tashin hankali take ciki sosai amma ta na ƙoƙarin dannewa. Sai dai a wannan tsawon lokacin da ta ɗauka ba tare da ta ga Musaddik ba ko samun kebewa da shi ta fahimci a zahiri ba zata iya rayuwa babu Musaddik ba, idan kuma ta rayun to zata rayu cikin matsanancin rashin hankali ne da rashin natsuwa.
Duk yadda Alh Yusuf sanda ya so ta ga farinsa to fa kullum baƙinsa take ga ni,ko kallonsa ba ta yi, shi kansa ya fahimci yadda ya ke ɗaukar abin ya wuce haka, ya gane da gasken gaske ta riga ta faɗa soyayyar Musaddik,kiris yake jira ya lale katinsa na ƙarshe.
Sai dai kuma baisan zuwa yanzu tuni Haj Hudah ta gama yi ma kanta tunanin mafita tsakaninta da Musaddik ta ji a ranta ta kuma aminta da hukuncin da ta ke son yankewa,sai dai kuma dole ko Alh Yusuf ya so ko ya ki sai ta sami damar ganin Musaddik domin su tattauna yadda al'amarin zai kasance, duk da ta na ji a jinkinta cewa dole zata sami matsala daga Musaddik tana jin tamkar bazai yarda da abinda zata je masa da shi ba.
Amma ko ma dai menene ya zama dole ta ga Musaddik.

Hakanne yasa tun safiyar yau asabar take shiri, ta sanar da Alh Yusuf cewar zata je gida ne ta duba Haj shafa'atu, kallonta kawai ya yi cikin ɗan murmushi yace "Badamuwa ba sai kin ɗauki direba ba, da kaina zan sauke ki daganan ni ma sai na gaida ta, don na kwana biyu bamu gaisa ba", wani takaici ya gama cika mata zuciya, a hankali ta dawo kusa da shi ta zauna ta na fuskantar sa, sannan tace "Ni ko Alh,na kasa gane maka duk waɗannan watannin, sau tari nakan yi tunanin kulawa ka ke ba ni wacce ko lokacin sabon auren mu ba ka ba ni irinsa ba, amma kuma a can ƙasan zuciyata ina jin tamkar wani abu ne da ban". Ta tsaida idanunta akansa sosai cike da nazari tace "Me yasa ka ke yi min duk abinda ka ke min a irin wannan lokacin da banyi tsammani ba?".
Jin tambayar ya yi ta zo masa a bazata, hakan yasa ya yi saurin gyara zamansa, ya na kokarin tattaro duk wasu kalamai na yaudara.
Yace "Yanzu idan miji zai ba matarsa kulawa dole sai da hujja?", Ba ta yi magana ba illa kallonsa da ta cigaba da yi,ta na jin ina ma ta na da damar hango gaskiyar komai a Kasan kwayar idanunsa da tabbas tasan akwai sirrika da dama.
Ya ɗan matso sosai kusa da ita ya na ɗan murmushi ya cigaba da cewa "Ina ji a tsawon shekarun da mu ka yi tare, tamkar kulawata ki ka rasa, ina jin kuma daga bakinki ma irin wannan furucin ya fito babu adadi, tabbas a lokacin da ki ka ce na dawo da harkokin kasuwancin mu gida Nigeria na ji babu dad'i a raina don ina ganin tamkar na gaza ne sannan kuma ba ki da godiya akan duk dawainiyar da na ke yi da dukiyar ta ki", ya numfasa ya na ƙoƙarin gano tasirin da maganar ta sa ta ke yi a gareta.
Ya cigaba da cewa "sai da ga baya, da na zauna nayi tunani sai na ga abinda ki ka faɗa gaskiya ne,na ji kuma na aminta da yin hakan, gami da son faranta ranki, tare da kasancewa kusa da ke a ko wane lokaci,shi yasa ko da ki ka janye da ga kudirin ki ni ban janye ba, zan zauna tare da ke, zan kuma kula da ke, haka zalika zan cigaba da kulawa da dukiyar ki, domin ina son ni ma na amsa sunan miji nagari".
Hakanan ta ji zuciyarta ta na neman tsinkewa.
Kalaman Alh Yusuf sanda sun nemi su taɓa zuciyarta sai dai kuma bakin alkalami ya riga ya bushe, zuciyarta ba ta hango kowa sai Musaddiq, ba ta jin kuma zata sami farinciki a wajen kowa sai Musaddiq, daker ta kirkiro ɗan murmushi tace"To Nagode, sai dai yau ina rokon a barni na fita ni kaɗai don ina son samun sakewa da Haj ", ya ɗan numfasa yace "yi Miki rakiya shi ne zaisa ki kasa sakewa da Haj?".
Yadda ya yi tambayar cikin rauni yasa ta ɗan ji babu dad'i, don haka ta yi saurin girgiza kai tace "A'a ba haka ba ne", yace "To mu je na sauke ki, idan ya so sai na barki ki yi mata yini, da yamma sai na koma na dauko ki". Yanzu hukuncin nasa ya yi mata domin ko ba komai zata sami lokacin da zata aiwatar da abinda ke cikin zuciyarta.

Cikin kankanin lokaci ta ƙarasa shiryawa, Alh Yusuf sanda ya dauketa zuwa gida, bayan ya gaida Haj shafa'atu ya ɗan zauna kaɗan kafin ya yi musu sallama ya tafi acewarsa sai zuwa yamma idan ta kammala zai zo ya dauketa.

Haj shafa'atu ta dade tana kallon yanayin ƴarta da sam babu walwala ko natsuwa a tare da ita, yan kwanakin da ta yi ba ta ganta ba sai ta ga ta yi rama da yawa hasken fatarta kuma ya ƙara fitowa sosai, hatta karsashinta ya ragu, Haj shafa'atu tsaye take da karantar ko wane hali ƴarta take ciki, hakan yasa cikin kankanin lokaci ta fahimci akwai matsala.
Ta ɗan dafa saman kafadarta cike da kulawa tace "Me yasa kullum zaki zo gidan nan sai kin taho min da fuskar damuwa, me ke damunki?, Kin canja sosai".
Ta girgiza kai tace "Ba wata damuwa,kawai ayyukan mutane ne su kayi min yawa",Haj shafa'atu ta jinjina kai tace "matsalar gidanki fa?".
Gaban Haj Hudah ya fadi ta yi saurin kallonta, duk duniya ba taga mai saurin gano damuwa da matsalarta ba irin mahaifiyarta, gaba ɗaya sai ta kwanta a saman kafafunta, kamar kullum ta na jin tamkar ta gaya mata abinda ke damunta sai dai tasan ba zata sami goyon baya ba maimakon hakama suna iya batawa har abada, wannan sirrinta ne da babu wanda ya kamata ya ji har ƙarshen rayuwarta.
"Ki gaya min Hudah, komai lafiya ko tsakanin ki da Yusuf ɗin, ko har yanzu akwai wata matsalar ne, ita fa haihuwa ta Allah ce, damuwa baisa a samu sai addu'a da maida lamari ga Allah", Haj Hudah ta numfasa tace "Tuntuni na maida komai ga Allah akan samun cikina, kuma ba wannan ba ne damuwata, kawai ina damuwa ne a bisa yadda Yusuf ke son maida ni wata ƙaramar yarinya wacce duk abinda zanyi sai ya sani sai kuma na yi da shi, saboda me?".
Haj shafa'atu ta jinjina kai tace "Ban fahimce ki ba".
Sannu a hankali Haj Hudah ta gaya mata irin yadda Alh Yusuf ya canja halinsa yanzu.

Ta yi murmushi sosai gami da shafar gefen fuskarta tace, "Wannan ai ba abin damuwa ba ne abin farin ciki ne,idan ban manta ba wannan ya na daya daga cikin abinda ke kawo muku sabani, to mai zaisa yanzu kuma ya zama damuwa, mijinki yana tare da ke yana ji da ke, ya aje komai domin ya saki farinciki to menene kuma?".

Ta ɗan yamutsa fuska tace "Ni kuma sai ina ganin kamar abin ya yi yawa", haka dai Haj shafa'atu ta

Please Login or Register in order to submit comment