Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cigaba da fahimtar da ita gami da nuna mata a irin wannan halayyar da Alh Yusuf sanda ke nuna mata, sai gwarzo namiji ne Kaɗai zai iya nunawa, don haka kamata ya yi ta riƙe mijinta hannu biyu, su zama kwatance na alheri.
Jin ta kawai ta ke yi, domin dai ba nan hankalinta yake ba, ta kosa kwarai ta kira Musaddiq, hakan yasa ta tashi da nufin shiga banɗaki.
A banɗakin ta yi ta kiran Musaddiq amma bai daga ba, daga bisani ta tura masa sakon cewa tana son ganinsa duk runtsi, idan ba haka ba zai yi mamakin abinda zai biyo bayan kin daga wayarta.

Tana dawowa falon,mai aiki ta cika gabanta da kayan abinci amma ba ta iya cin komai ba idanunta na kan wayarta kiran Musaddiq kawai take son ga ni. Haj shafa'atu ta na gefe kafafunta na cikin na'urar da ke matsa mata kafafu domin cire mata ciwo,amma duk da haka hankalin ta na kan Haj Hudah, ta na ji har yanzu akwai damuwar da ta kasa gaya mata, gashi nan rubuce a saman fuskarta.
Kiran da ya shigo wayarta yasa ta tashi da sauri cikin rawar jiki ta shige daki, Haj shafa'atu ta girgiza kai gami da yi ma ƴarta addu'a a cikin zuciyarta.

Sai da ta kulle daki sannan ta dauki wayar.

"Don me zan dinga kiranka a waya amma ba zaka daga ba?"

Ta yi maganar ne cikin fusata, Musaddiq ya aje numfashi yace "Ba na tare da wayar ne"
Ta lumshe ido ta bude tace "To ina fatan kaga sakona ko?".

Yace "Eh na gani shi yasa na kiraki, domin na sanar da ke cewar ba na gari ina Legos, babu yadda za muyi mu iya
haɗuwa", gaba ɗaya ji ta yi kafafunta sunyi sanyi, yaushe zata ƙara samun irin wannan damar na fita ba tare da Alh Yusuf sanda ba.

"Ka na Legos?".
"Kwarai da gaske ina Legos "

Ya faɗa cikin ƙarfin guiwa, ta ɗan yamutsa fuska tace "Idan nayi bincike na gano cewa karya kayi min kana gari kasan abinda zai iya biyo baya ko?". Cike da tsanarta da kuma tsanar magana da ita yace "Na ba ki damar ki bincika, karya ba dabi'ata bace, ke ma kinsan haka", ta koma ta zauna a gefen gado turus, sosai take jin ba zata iya riƙe maganar da ke cinta a rai ba, tana jin ko ta wayar ne ya kamata ta sanar da shi, hakan yasa ta muskuta tace "Dama magana na ke son yi da kai mai muhimmanci",
Musaddiq ya runtse ido cike da takaici yace "Don Allah ki sa tsoron Allah a cikin lamuranki, me yasa ki ke son cigaba da takawa gangar shaidan rawa, a lokaci mai tsawo na fara samun farinciki da natsuwa, don Allah na roke ki ka da ki ƙara raba ni da farincikina".

Itama ta numfasa tace "Na so ace irin waɗannan maganganun na ka suna yin tasiri a gare ni, amma ka sani wanda ya yi nisa ba ya jin kira,na riga na ɗorawa kaina kaunarka banda burin da ya wuce na kasance da kai muddin raina,aurena dai shi ne kaɗai matsalar ko?, to shi ne dalilin da yasa nake son yin magana da kai, ga shi kace baka nan, don haka nake jin ko awaya ne mu yi maganar kawai".
Cikin kosawa da maganar Musaddiq yace "To wace magana ce?".
Ta kishingida sosai akan gadon ta cigaba da magana a hankali yadda sautin a kunnanta kawai take ji.

"Musaddiq na jaraftu da kaunarka a dalilinka na zama kaskantaciya,duk ɗaukakar da Allah ya yi min amma na zama raƙumi da alaka sai yadda ka yi da ni, tun daga ranar da ka fara kusantata rayuwata ta koma mara amfani, idan ba tare da kai ba,a yanzu kuma da aka nisanta mu ta dalilin maigidana sai nake jin tamkar bazan iya rayuwa ba
ba tare da kai ba,don haka na yi ma kaina tunanin mafita".

Da sauri yace "mafita! Wace irin mafita kenan?".

Ta ɗan yi murmushi tace "Musaddiq ina son na kashe aurena,domin ka aure ni". Wani irin zillo Musaddiq ya yi har sai da wayar ta nemi faduwa a hannunsa. Cikin rawan murya yace "wace irin magana ce wannan sai kace kin fado daga kan gado, ki kashe auranki na aure ki a ina aka taɓa wannan kwabar, ta ina zan iya yin auren sabon Allah, kuma ma waye ya gaya Miki cewar ina da sha'awar yi ma matata kishiya da ita kaɗai na ke son ƙare rayuwata,me yasa ki ke da son zuciya ne?".

Ta ƙara yin ƙasa da murya tace "Ba son zuciya ba ne, Musaddiq ina ganin abinda Allah ya ƙaddara min a rayuwata kenan, ka yi min uzuri ka tsaya ka saurareni da kunnan basira, wannan itace damar da idan ka ba ni zaisa na goge wannan vedion na kuma nemi duk hanyar da zan bi don ganin Yusuf sanda ya sake ni ba tare da hannunka ya fito a cikin maganar ba, asalima zan kara binne duk abinda muka aikata yadda babu wanda zai sani har abada".
Cikin karaji da faɗa Musaddiq yace "Hudah na gaji da ƙoƙarin maida ni bawa da ki ke yi, na gaji da son maida ni mai laifi da ki ke yi, na gaji kuma da mulkin mallakan da ki ke yi a cikin rayuwata, me ki ka ɗauke ni ne?, Wawa, ko sakarai wanda zai bari ya shiga wuta kiri kiri tare da murkushe dukkan darajata, to ina so ki sa ni ba ki isa ba".

Cikin kaduwa da maganganun Musaddiq wanda ba ta taɓa tsammanin zai iya gaya mata irin su ba ta mike tsaye.

"Ka sami natsuwa Musaddiq,za ka ji dad'i,zan baka damar da ban ba mijina irinsa ba,ina son ka sani ina da dukiya mai tarin yawa a hannun Yusuf, sirrina ne nake son na gaya maka, sirrin da ko mahaifiyata bata sani ba, ina da tsabar kudi Naira miliyan dari takwas da hamsin gadon da na samu daga mijina na farko, bayan aurena da Yusuf na bashi nera miliyan ɗari biyar domin ya cigaba da juyawa saboda ni hankalina yana wajen siyasata,
Kada ka manta kuma hatta ta ɓangaren mahaifina na samu gado na kudi da kadarori masu yawa a matsayina na 'yarsa ɗaya tilo.
Yusuf ya cigaba da juya kudin ana samun riba a tsawon shekarun da ya yi yana juya kudin, a cikin asusun ribar akwai bera miliyan dari shida, ribar ce muke rabawa, itama kuma ban taɓa karbar ko sisi ba a ciki suna wajensa a ajiye idan wani kasuwancin ya taso yakan hada da su ya yi."
Musaddiq ya katseta da cewa "Duk da ki ke min wannan bayanin menene amfanin yi min shi?,ina ruwana da sirrin da ke tsakaninki da mijinki?".
Ta numfasa cike da son ta shawo kansa tace "Ina gaya maka ne saboda na tabbatar maka da cewa zan rabu da Yusuf zan kuma amshi dukiyata a hannunsa zan mallaka maka ita har abada matuƙar zaka zauna da ni a matsayin matarka ta har abada".

Musaddiq ya girgiza da jin maganganun Haj Hudah, shin me ta dauke shi? Me take tunani kuɗin ta sune zasu dinga bata komai, ya girgiza kai yace "Ban shirya shiga wannan halakar ba,babu abinda sanyi da kuɗin ki, wancan ma da na roka ki ba ni saboda banda yadda zanyi ne na ceto rayuwar matata a wannan lokacin kuɗin aikin da ki ka biya na Afrah ya fi min wadannan makudan kuɗin da ki ka faɗa don kawai ki sayi yancina, to ki dakata ki ji"

Shiru ta yi ta kasa cewa uffan har ya cigaba da cewa "Kuɗin ki basa gabana, ni yanzu magana ce ta yancina da kuma mutunci na, daga yau kuma na gama yi Miki duk abinda ki ke so, kaskancina bai kai na sayar da kaina a wajenki ba, ki sa ni duk arzikinki akwai abinda ba zaki iya saya ba, domin soyayyata da nagartata har abada ba zaki iya sayensu ba, don haka na datse duk wata alakar da ke tsakanin mu", kawai ji ta yi hawaye ya na malala a saman kumatunta.

Wata irin damuwa mara misaltuwa ta cika zuciyarta, jinkinta ya yi matuƙar sanyi, a sanyaye tace "kada ka manta da vedion da ke hannuna cikin ko wane lokaci komai ya na iya faruwa". Ya saki ajiyar zuciya cikin matsanancin ɓacin rai da tashin hankali yace ",ki kai shi duk inda zaki kai, ki nunawa duk wanda zaki nunawa, amma ki sani ɓacin sunana kema ɓacin sunanki ne, a wurare da dama ma ke zaki fini muzanta da tashin hankali, ki yi tunanin makomar siyasar ki da mutunci ki , da makomar rayuwarki, ki sani shi kansa mijin naki idan ya sa ni da kansa zai sake ki tare da horo mai tsanani, a lokacin kuma ba ni ba ko wane namiji zai guje ki babu ke ba kara wani auren".

Cikin hawaye tace "me ka ke nufi kenan?"

Yace "Ina nufin ki turawa matata vedion ni kuma daga lokacin banki duk duniya su san abinda na yi ba, don haka ni ma zan karbi vedion a hannunta zan watsawa duk abokan siyasar adawar ki , sannan zan turawa mahaifiyarki".

Yana gama faɗin haka ya kashe wayarsa.

Itama wurgi ta yi da ta ta wayar tana sharar hawaye da zufa.
Lalle Musaddiq ya shiryawa yakin, wannan karon kuma idan ta yi wasa itace zata rasa makaman yaƙin.
Duk barazanar ta na turawa Afrah vedion yau ba shi da wani tasiri, shin Musaddiq wane irin mutum ne, duk wadannan kuɗin basu sa ya girgiza ba, ta dauka abin mai sauki ne ashe wata fitinar zata kara barkowa, domin dai a yanzu duk tunaninta ya tsaya cak! Sannan bata jin zata yarda da hukuncin Musaddiq duk runtsi duk tsiya sai ta same shi sai dai kuma ita kanta tasan babban aiki ne a gabanta.

Dai dai wannan lokacin Alh Yusuf sanda ya saki wayarsa ƙasa yana jin numfashinsa na sama da kasa tamkar zai dauke, idanunsa sun Kada sunyi jajir, ya na jin haushin Haj Hudah amma bai taba jin tsana da haushinta irin na wannan lokacin ba, shi yake lale katin ya kuma raba, amma yau Hudah ce ta lale katin , bai taɓa zaton tunaninta zai kai na ta rabu da shi ta kuma raba shi da duk dukiyar da ya sha wahala akanta, ta ya ya take ganin zai rabu da ita, bayan dimbin dukiyar da ke hannunsa, ta yaya zai yi watsi da damar da ya samu na fantamawa a cikin dukiyar, saboda tsabar rashin adalci ta raba shi da komai,ba haka ya tsara abinda, duk kuma wasan da yake bugawa ba akan haka yake bugawa ba, don haka ya zama dole ya kawo karshen wasan da gaggawa tun kafin teburin ya juye da shi.
Domin ya yi imani idan Musaddiq ya ki yanzu zai iya yi anjima domin kuɗi siddabarunsu ya na da yawa, zai iya maida abinda ke da wuya ya zama mai sauki.
Don haka kafin hakan ya kasance ya zama dole ya yi abinda ya dace.................



Yar Gidan Imam ✍️
https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk

Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam,ina masu son kaya cikin farashi mai sauki,sayan daya ko sari, tun daga kan supliments, kayan kicin,lesissika, shoes and bags, abayas Kala kala da kayan yara, kayan kamshi, kai wannan kasuwar duniya ce, harda counselling na matsalolinku duk ana yi aciki, Yar Gidan Imam Empire ya haɗa komai, ku shigo domin mallakar burinku 🙏


MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
(Mrs Aliyu mayere)

Page 24

Lokacin da Alh Yusuf sanda ke cikin wannan dimuwar, ita kam Haj Hudah tana can zazzaɓi mai zafi ya rufeta, daker ta iya shiga banɗaki ta wanke fuskarta, don bata son ko kaɗan mahaifiyarta ta gane halin da take ciki.
Cikin mutuwar jiki bayan fitowar ta daga banɗakin ta murza key ɗin kofar dakin ta fito zuwa falo, a daddafe ta faɗa kan kujerar ta na maida ajiyar zuciya,Haj shafa'atu ta dubeta sosai tace "shurun ya yi yawa yanzu nake shirin sawa a kira ki,lafiya na ganki a haka?".
Daker ido jajir Haj Hudah ke sanar da ita zazzaɓi ne yanzun nan ya kamata.
Haj shafa'atu ta yi mata kallon tsaf sannan tace "Hudah ki sassauta ma kanki damuwa,ita rayuwar nan komai ɗan hakuri ne, kada ki ɗorawa kanki abinda zai zo ya zamar Miki illa,duk mai harkar jama'a sai ya haɗa da hakuri, ke dai ki ji tsoron Allah a kowane mataki na rayuwa".
Kafin Haj Hudah ta yi magana Haj shafa'atu ta mike ta nufi inda suke aje magunguna ta dakko mata maganin zazzaɓi ta bata,ta ɗauki ruwan roban da aka aje mata tun dazu ta bude ta tsiyaya a kofi ta mika mata.

Kafin Alh Yusuf sanda ya zo daukarta ta ɗan sami sauki, sai dai tashin hankalin da ke kwance a cikin zuciyarta, zahiri yau Musaddiq ya bata mamaki sai dai ba zata taɓa hakura ba har sai ta mallake shi.

Ko da suka koma gida tun daga cikin mota har zuwa gidan babu wanda ya yi ma wani magana, tsakanin ita da Alh Yusuf sanda kowa zuciyarsa a wuya ta ke, musamman Alh Yusuf da yake jin tamkar yasa hannu ya shaketa har lahira, sai dai abinda ya sani ne bata isa ta bata masa wasa ba, zaiyi maganinta. Ta yi zaton ko zai kira likita ya duba ta amma sai taga ko ajikinsa maimakon hakan ma yana ajeta duk da dare ya yi ficewa ya yi daga gidan, ya barta abinda ya dade baiyi ba, bata damu ba domin itama tana son ta sami lokacin tunanin mafita.

Shi ma ɗin Alh Yusuf sanda wani hotel ya wuce wanda ya saba zuwa ya zauna ya yi tunani gami da kulle kullen mugun nufinsa, daki ya kama musamman da ya kan biya duk wata idan ya na gari .
Sau tari ma'aikatan hotel din suna mamaki har gulmarsa suke yi saboda yadda duk zaman da zai zo ya yi a hotel din bai zuwa da mace bai zuwa da kowa yadda mafi yawanci su ke yi, shi hakanan yake zuwa daga shi sai shi.
Ta bangaren sa kuwa a yanzu dai ba lokacin mace ba ne, domin yasan idan ya haɗa da mace a cikin sabgarsa ba zai taɓa kai labari ba. A yanzu lokaci ne na tunanin yadda mafarkinsa zai zama gaske, wanda daga lokacin da hakan ya kasance idan mata dubu ne zai iya da su. Kulle kansa ya yi a dakin babu abinda yake busa sai sigari ƙwaƙwalwarsa na caji. A wannan dare ya tabbatar ma kansa da cewa haɗa Musaddiq da Haj Hudah faɗa shi ne zaisa cikar burinsa. To ko Meye manufar yin hakan oho?.

Dawowar Musaddiq daga Legos ya yi matukar canjawa, damuwar sa na neman ta dawo amma yana kauda hakan, musamman ga Afrah da duk kulawarta take kansa.
A ranar tare da Afrah suka ci abincin dare, cikin so da kaunar juna, sai dai zaman hirar da suka saba yi, kafin su kwanta yau Musaddiq baiyi ba.
Ya bata uzurin kansa na ciwo nan da nan Afrah ta rude tana ganin gajiyar tafiya ce, don haka ta tilasta masa ya sha panadol sannan ta haɗa masa ruwan wanka ya yi, bayan kwanciyarsa nunawa ya yi yana bacci amma idanunsa biyu, zuciyarsa kuma na cushe da tsananin tunanin badakalar da ke tsakanin sa da Haj Hudah.
Tunaninsa daya shin Haj Hudah ta yanke shawarar tona musu asiri ne ko ta yanke shawarar rufa musu, domin dai ko wanne ta yi a ciki yana da wuyan dauka, zuciyarsa ta riga ta kekashe ko ya ya ne ya na bukatar ya fita daga kangin bautar ta , don haka koma menene a shirye ya ke, babu tsoro ko shakka zai kuma yi fito na fito da ita ko da hakan na nufin faruwar abubuwa da yawa ne.
Da wuri yau ya fito shago saboda ya shirya kayan da ya shigo da su da ga Legos.
Sai dai tunda ya isa shagon wayar Haj Hudah ke shigowa wayarsa, ya na katsewa.

Daga bisani ma gaba ɗaya sai ya kashe wayar tasa

Ya cigaba da yin abinda ke gabansa, ran yan maza fa ya ɓaci, baya jin akwai wata kalma da Haj Hudah zata yi amfani da shi wajen shawo kansa asalima idan akwai abinda ya tsana bai wuce jin muryarta ba, har yanzu abin daure masa kai yake yi idan ya tuna wai shi Haj Hudah zata saya.
Ya kwashi lokaci mai tsawo yana gyaran shagon nasa, daga bisani kuma masu sayen kaya da suke ta tururuwar shigowa sayayya su ka ƙara dauke hankalinsa har ya manta da ya ma kashe waya.
Masha Allah kullum dama haka shagon Musaddiq ke cika da abokan cinikayya, ya na ciniki sosai saboda sauƙin kayansa, baya tsauwala riba.

Sai da ya dawo sallar la'asar sannan ya fito da wayar ya kunna, yana daga zaune kan kujerar zamansa ya dora hannunsa kan tebur din gabansa, ya kunna datar wayarsa ya shiga dudduba social media Yana cigaba da amsar order mutane na sabbin kayan da ya dora dazu.
Sakonnin da suke ta shigowa ta WhatsApp dinsa yasa ya shiga WhatsApp din.
Sakon da ya fi ko wane sako jan hankalinsa shi ne wanda ya shigo ta wata bakuwar number da bai sani ba, da alama vedio ne, da sauri ya shiga ya danna domin ganin vedion.
Wani irin faduwar gaba ya ji me tsanani, nan da nan yawun bakinsa ya kafe yadda har bakin nasa ya fara yi masa daci.
Idanunsa suka kada su kayi jawur kamar yadda jikinsa ya dauki rawa,ba shi ba ne ganinsa nafarko da vedion don haka mamakinsa ya fi tafiya ne akan wanene wanda yasan sirrinsa da Haj Hudah bayan su biyun.
Sannan ta yaya aka canja fuskar Haj Hudah aka maye gurbin ta da wata fuska da bai taba gani ba a rayuwarsa.
Vedion sa ne shi da Haj Hudah amma kuma ba fuskarta bace yanzu akan vedion. da sauri ya maida kallonsa ga rubutun da ya biyo bayan vedion kamar haka.
Baka Sanni ba amma ni na sanka ta dalilin uwardakinka yar majalisa Haj Hudah, itace kuma ta ba ni umarnin na yaɗa wannan vedion a ko'ina ciki harda wajen matarka da yan'uwanka, sai dai kamar yadda idanunka suka nuna maka matar da ke jiki ba Haj Hudah bace da wannan vedion kai kadai kasan gaskiyar wacce ke cikin vedion,duniya kuwa kai kadai suka sani a cikin vedion don haka ɓacin sunanka ne kai kadai banda na Haj Hudah.
Don haka ka shirya cikin ko wane lokaci wannan aikin ya na iya tabbata.
Matuƙar baka koma ga Haj Hudah ka karbi tayinta ba, kun kuma cigaba da mu'amalarku kamar yadda ku ka saba ba.

Tun kafin ya gama karantawa ya ji zufa ta gama wanke masa bayan riga .
Tsanar Haj Hudah ta ƙara kama shi har tsuma jikinsa yake yi. Wato shi zata ci amana.ta samu masana computer sun canja komai ta kuma barshi a ciki. Saboda kawai ta na son ta cika burinta, tana ganin wannan itace hanyar da zata iya dawo da shi mummunar turbar da ya bari?,
Da sauri ya shiga kokarin kiran wayar ta amma wayar ta na kashe.
A gaggauce ya sallami sauran masu sayen wayar, ya kulle shagon.
Kai tsaye shatar adaidaita sahu ya ɗauka zuwa gidan Haj Hudah cikin matukar fusata da rashin mallakar fushinsa. Yana jin idonsa idon Haj Hudah sai ya yi mata abinda har ta mutu ba zata manta da shi ba.
Bai damu ba ko da mijinta na nan yadda take son ta kaskantar da shi haka shi ma zai kaskantar da ita, ya riga ya yarda Duk tarayyar da ba ta Allah bace tarayyar banza ce.
Ya umarci me adaidaita sahu ya jira shi ya fito, cike da fusata ya shiga get din gidan.
Masu gadin suka taso cike da mamaki da murnar ganinsa kasancewar sun dade ba su hadu ba, amma babu wanda Musaddiq ya bi ta kansa, tunda ya ya tambaye su Haj Hudah na ciki suka ce eh, ya wuce su kamar zai tashi sama, hakanne yasa suka bi shi da kallon mamaki,saminu ko da ya riga yasan tsakanin su, gefe ya samu ya na kakabin lamarin, ya na Kuma mamakin abinda ya hado su domin tabbas wannan zuwan nasa ba na alheri ba ne.

Falon Musaddiq ya faɗa ya na kwala mata kira iya karfinsa.

Wanda hakanne ya janyo hankalin hadiman gidan duk cikin firgita suke, sai leke su ke suna son gasgata cewa Musaddiq ne ya shigo gidan a cikin wannan mummunan yanayin.

Duk a kwanakin nan zazzaɓin da ke damun Haj Hudah ya kasa barin ta karfin hali kawai take yi, ta na kuma kan shan magungunan da likita ya dorata a kai.

Kamar saukar aradu ta ji Muryar Musaddiq na kiran sunanta, har cikin zuciyarta ta ji sautin, lokaci ɗaya kuma ta ji tana neman ta rikice, domin Muryar Musaddiq ɗin ta ji ta ne a wani irin baƙon yanayi me wuyar fassara.

Kiran da ya cigaba da yi ne babu

Kakkautawa yasa ta yi saurin durowa daga saman gado, ko takalmin da ke gefen gadon ba ta tsaya dauka ba ta sakko kasa da sauri.
Turus ta yi su na kallon juna ita da Musaddiq,
Yana tsaye gaba ɗaya a rikice yake, ta yi masa wani irin kallo tace "Haba Musaddiq menene haka zaka shigo min gida cikin wannan yanayin, kada kaga na baka muhimmanci ka nemi watsar da darajata, sanin ko kai waye yasa har ka iya wuce jami'an tsarona ka shigo min gida a cikin irin wannan mummunan kamannin, Meye ya yi zafi?".

Ya tako zuwa gabanta sosai ya na yi mata wani irin wulakantaccen kallo, yace "Har wace daraja gare ki da ki ke ƙoƙarin karewa, ta na ina darajar, na rantse da ace babu hukuma da kin raina kanki don idan na shake ki sai na kai ki lahira, makira mara tsoron Allah". Nan da nan Haj Hudah jikinta ya shiga rawa, ta shiga ƙoƙarin lekawa ko hadiman gidan suna jin abinda ke faruwa, su kam ko wanne ya lafe ko kwakkwaran motsi babu wanda yake yi a cikinsu, illa tsantsan mamaki mara misaltuwa da suke yi.
Ta dawo da kallonta kansa tace "Ni ka ke gayawa waɗannan maganganun, dama ka koma shaye shaye ne ban sani ba?, A buge ka ke ko Musaddiq?".

Ya ƙara fusata yace "kamfanin giya na sha, kada ki raina min wayau, kinsan abinda ki ka yi sarai, ki na ganin don kin canja fuskarki a jikin vedion zaisa na yi abinda ki ke so, to ina son ki sani ki kuma rubuta ki aje babu wata barazana da zaki min wacce zata yi tasiri a gare ni da har zaisa na yi Miki abinda kike so, ba matata ba ba dangina ba don Allah kisa a manna a duka duniya,na tsaneki na tsaneki".

Jikinta a sanyaye ta cigaba da kallonsa tace "Don Allah kayi kasa da muryarka,bana son jama'ar gidan nan su ji abinda ka ke faɗa".
Ya watsa mata harara yace "Me yasa ki ke tsoron wani ya ji, ina ce tonon asiri ki ke so".
Ta yi rau rau da ido hawaye na kokarin cika mata idon,tace "Musaddiq na rantse maka bansan inda maganganunka suka dosa ba, babu abinda na sani akan wani vedio".
Yace "Ai da yake baki san Allah ba dole ki fadi haka ".
Ya fito da waysrsa ya kuma fito da vedion da sakon da aka tura masa ya mika masa yace "Har wannan ma baki san da su ba, ko so ki ke ki maida ni mahaukaci ". Cikin rawar hannu ta amsa ta shiga kallo.
Bata ƙarasa ba ta sulale kasa dirshan ta zauna kan kujera

Please Login or Register in order to submit comment