Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaure a cikin baƙar leda, ya ɗan muskuta ya gyara zamansa gami da gyara murya, ya cigaba da maganar wanda daga dukkan alamu ya daɗe ya na yinta, “Ne ma ma Afrah lafiya ya zama dole a gare ni, don haka banga amfanin wani abu da na mallaka ba matuƙar ba zaiyi min maganin lalurata ba kamar yadda na gaya miki a baya”.
Ya ƙara dawo da kallonsa ga Mama Hauwa, da bai damu da harare hararen da take ta yi ba, ya nuna ledar gabansa ya cigaba da cewa “ Don haka naga ya dace na sanar da ke cewa ragowar gonakina da nake noma a cikinsu guda uku da ragowar filina guda ɗaya na sayar da su, dama su kaɗai suka rage min a rayuwata, kinga yanzu an kakkaɓe ba ni da komai sai wannan gidan da muke ciki ga kuɗinsu nan”, girgiza ƙafafu kawai ta ke yi cike da fusata, gaba ɗaya ta yi zaman dirshan a kan tabarmar. Bai damu da ganin halinda ta shiga ba ya cigaba da magana “Itama Halima gonarta ta gado ta ba da damar a sayar, itama an sayar duk ga kuɗin a nan”.
A nanne cikin matuƙar fusata tace “To meye nawa da ka kirani kana gaya min, tunda daga ni har yayana bamu da wani kima ko mutunci a cikin rayuwarka, kamar yadda ka faɗa ne rannan cewar dukiya dukiyarka ce kana da damar yin komai da ita to ka je kaya ba kayan kowa ba ne kayanka ne, amma kamar yadda ka ke ji Afrah yarka ce, haka suma sauran yaran suke yayanka, babu wanda na zo da shi a gaban gara, don hakq ba na ganin dacewar ka kwashe duka kadarorinka ka salwantar da su akan Afrah ita kaɗai ba, bayan duk waɗanda ka sayar saboda ita a baya”.
Baƙinciki ya ƙara kama mallam Mahmud ya yi mata wani irin kallo yace “Gaskiya Hauwa lamarinki yana matuƙar ɗaure min kai, ki na yin abu tamkar wacce ba ta da imani, kadarorin nan da aka sayar ba kuɗin za’a tasama Afrah ta cinye ba,
Lafiya za’a nemar mata wanda ina ganin ko ke da kina da sauran ɓurɓushin imani zaki iya sayar da naki kadarar ki taimaketa, amma abin mamaki ke ba ki taimaketa ba kuma kina hassadar mahaufinta ya taimaketa, wanda ke kanki kinsan haƙƙina ne na taimaketan”
Mama Hauwa a harzuƙe tace “kai ka sani rashin adalcinka kuma kai zai kai ga halaka, kuma ko dai me zaka ɗaga ka sayar idan Allah bai yarda da ta warke ba, babu abinda zaisa ta warke…..”, cikin ƙurewar haƙuri mallam Mahmud ya daka mata tsawa yace “Idan ki ka ƙara yi ma yata fatan rashin warkewa na rantse sai na lahira ya fi ki jindaɗi”. Cikin ɗaga murya ta cigaba sa maganganu, dai dai lokacin manyan yayanta kabir da Mansur suka shigo gidan, gaba ɗayansu ransu da hankalinsu a ɓace, a dalilin jin kace nacen da mahaifansu ke yi, itama Na’ima tuni ta fito daga ɗaki ta dogare tana kallon abinda ke faruwa.
Ran Mansur a ɓace ya dubi mama Hauwa yace “Haba don Allah mama , menene haka, ki na ɗaga murya ana jinki tun daga ƙofar gida, da girmanki da komai, ki na yin abinda yakamata ace kece ki ke yi ma wani faɗa idan ya yi”.
Ta juya ta sakar masa harara tace rai ɓace “Ai dama a kullum mahaifinku shine mai gaskiya a tsakaninmu, ni kuma duk abinda nayi laifi ne, bayan ku nake ƙoƙarin ƙwatoma yanci da haƙƙi”.
Kabir ya girgiza kai yace “Haba Mama duk abinda kika lissafa ai ta lalama da haƙuri zaki bi ki samu bata faɗa da tashin hankali ba, kuma ma wane yanci zaki ƙwato mana da hakki bayan babu wanda ke cikin wata matsala”.
Mallam Mahmud ya dubesu sosai yace “Kabir ku zo ku zauna nan, ku ji dalilin kiran da nayi muku, ku ƙyaleta ta yi duk abinda ta ga damar yi”. Bata ƙara cewa uffan ba harsu mansur suka zauna gami da gaida mahaifinsu, sannan mallam Mahmud ya fara magana da cewa “Duk abinda mahaifiyarku take faɗa magana take kawai ta son rai”, ya maida numfashi sannan ya cigaba da cewa “Kuna sane da halinda ƙanwarku take ciki, kuna kuma zuwa kuna ganinta don ko jiya duk kuna asibitin, kunsan irin kuɗaɗen da ake nema domin yi mata aiki ko?, wanda nasan da a cikinku akwai mai kuɗin zaku iya biya ayi mata aikin, mijinta baida wani abu kunsan haka, don haka ya zama dole musa hannu domin nema ma Afrah lafiya”.

Ya numfasa kafin ya cigaba da yin maganar “Adalilin haka na ɗaga duka gonakina da filina da gonar goggonku Halima na sayar kasancewar anga mun matsu duk a wulakance aka sayesu, domin gaba ɗaya naira miliyan ɗaya da dubu ɗari bakwai aka saya, kuma mahaifiyarku tana faɗa ne a dalilin na sayar da gonakin nawa, a nata hangen tana ganin bai kamata na sayar ba saboda kuma kuna da haƙƙi tunda kayan naku ne, banda iko na sayar”, mansur ya nisa gami da kallon mallam mahmud yace “Haƙiƙa Baba wannan huluncin shine ya kamata, domin babu amfanin da kayam zasu yi maka da ya wuce wannan amfanin, don haka muna goyon bayanka, Allah ya bata lafiya”. Kabir ya kauda kallonsa daga fuskar mama Hauwa da take huci kamar kumurcin maciji yace “Tabbas mijinta baida ƙarfin da zai ɗauki nauyin wannan aikin shi kaɗai, dole sai mun haɗa ƙarfi da ƙarfe mun taimaki Afrah, to mu ma bamu da shi amma munyi ɗan namu ƙoƙarin ni da mansur” ya dubi mansur yace “ka bashi kuɗin”.
Ƙirjin mama Hauwa har ɗagawa yake saboda tsabar baƙinciki, har mansur ya fito da kuɗin ya miƙama mallam mahmud yace “Gashi Baba nera dubu ɗari biyar ne”. Mama Hauwa ta dafe ƙirji tana maimaita yawan kuɗin, cikin farinciki ya amsa yana sa musu albarka mara misaltuwa, natsuwa da jindaɗin kaɗai da suka ga ni a fuskar mahaifinsu ya wadatar da su. Ayayinda mama Hauwa murya na rawa tace “yanzu kuna da irin wannan kuɗinne zaku barni a ƙasƙance, babu wanda ya taɓa bani ko dubu hamsin a cikinku amma yau kum ba da dubu ɗari biyar saboda Afrah, tiƙisa lalle ne duniya mai abin mamaki”.
Kafin su ce wani abu ta juya tana dukan iska ta shige ɗaki cike da matuƙar ɓacin rai.itama Na'ima juyawa ta yi cike da takaici ta koma daki ,ko mako biyu ba'ayi ba ta rokesu su taimaketa da dubu goma zata canja screen ɗin wayarta da ya fashe amma duk cikin su biyun babu wanda ya iya bata ko kwandalarsa sai alkawarin banza da su kayi mata, na zasu ba ta, amma yanzu sun zo sun kawo har dubu dari biyar saboda Afrah.Ranta ya yi matukar ɓaci.
Basu damu ba suka cigaba da tattauna yadda za’ayi a samu cikon kuɗin ko muce uwar kuɗin. Sun tsaida maganar za’a cigaba da buga bugar neman taimako ko za’a dace.

Ƙwarai matuƙa musaddiƙ ya yaba da ƙoƙarinsu mallam Mahmud, domin tabbas sun gama nasu ƙoƙarin sun tara abinda zasu iya tarawa, amma shi a matsayinsa na mijinta ya kasa taɓuka komai, babu wata hanya da yake ganin zai iya samun kuɗin, domin duk fafutukar da yake yi har yanzu ko dubu ashirin bai samu ba ta ɓangarensa, wannan wace irin naƙasa ce, hatta wajensu Hassana ya nemi taimako amma babu abinda ya samu. Ga abin tsoron kullum ciwon ƙara kusanto gejin da ba’a so yake yi, domin a kullum ciwon yana ƙaruwa da ɗigo biyu, kullum likita yana cikin tsoratar da su.
Musaddiƙ ya ƙara ramewa ya fita hayyacinsa ya yi wujuga wujuga duk wasu ƙofofi sun kulle masa yana cikin jarabawa wacce ya fara sarewa yana tsoron tamkar bazai iya cin jarabawar ba, domin tsanani ya yi tsanani yana kan siraɗin rayuwa.
A wannan lokacin kuma Haj Hudah ta yi ɗif ta daina kiransa a waya tunda ko ta kira baya ɗauka, ta daure da zafi da tafasar zuciyar da take ciki kullum, ta sa rai da fatan tana nan musaddiƙ zai kawo kansa, domin duk halin da ya ke ciki ta sani duk kuma matakin ciwon da Afrah take ciki ta sani, shi yasa take mamakin taurin kan musaddiƙ domin bata taɓa tsammanin za’a kawo wannan lokacin bai zo gareta ba, domin tasan ko da wasa ba zata iya haƙura da shi ba duk wani burinta ta ɗora shi akansa ne. Komai na ta ya tsaya saboda tunanin musaddik hatta fita sai ta zamar mata dole take yi. Babu wata kulawa da take ba Alh Yusuf sanda, wanda shi ma tuni ya sanya mata idanu, yana ji a ransa an kusa zuwa inda yake so a kai.

Makonni huɗu cif har zuwa lokacin ba’a haɗa kuɗin da ya kai miliyan uku ba, kuma a cikin su ne ake cigaba da kulawa da ita a asibitin. a wannan lokacin kuwa Afrah ta gama komawa daga ƙashi sai fata, duk wanda yaga halin da take ciki sai ya tausaya ya kuma zubar da hawaye, wani ikon Allah kuma Hanan lafiya ƙalau take sai girma take madara ta amsheta.
A yau shigowar likitan Afrah kenan asibiti amma ya kasa ƙarasawa office har sai da ya dangana da ɗakin Afrah, saboda tun jiya gaf da zai tashi sakamakon gwajin da aka yi mata ya fito, ya amsa ya tafi dashi gida, wanda akan sakamakon ya kwana yana nazari, hankalin sa ya tashi matuka da ganin abinda sakamakon ya kunsa, ya yi sa’ar samunsu duka, yana gama dubata ya buƙaci ganinsu, bai ko bari sun je office ba a waje ya sanar da su maganar da ta ƙarasa rikita musaddiƙ, domin ya tabbatar musu Afrah ba ta da wani sauran lokaci, duk da ya kasa warware musu komai abinda kawai ya gaya musu kenan ya wuce office, to amma fa ba musaddiƙ ba har su mallam mahmud sun gasgata abinda likitan ya faɗa, domin duk wani alamu na ƙarewar rayuwa ya gama bayyana a tare da Afrah. Gaban Afrah ya koma ya kifa kai ya yi ta kuka daƙer mallam mahmud ya shawo kansa ya yi shiru.
Zuciyarsa ta ƙeƙashe idanunsa sun kaɗa sunyi jawur yana jin a yanzu babu abinda ba zai iya yi ba domin samoma matarsa da yafi so da komai lafiya.
Miƙewa ya yi baya ko ganin hanya ya fice , ko a daidaita sahu bai nema ba, haka yake tafiya a ƙasa kamar wani bugagge ga rana amma bai san ana yi ba haka ya kama hanyar gidan Haj Hudah a ƙasa, ya na jin ya riga ya ƙuna komai ta fanjama fanjam………………..



Yar gidan Imam✍️
MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
( mrs Aliyu Mayere)

Page 18

Hajaran majaran yamma liƙis ya isa gidan Haj Hudah, su kansu masu gadin gidan da suka daɗe basu ganshi ba, gani su kayi gaba ɗaya ya canja musu matuƙa, ga rama da ya yi, ga wannan yanayin da ya shigo mai cike da tashin hankali, duk fara’ar da ya saba yi da kowa yau babu alamar fara’a a tare da shi, kallon kowa yake bibbiyu kamar bai taɓa ganinsu ba, shi yasa da ya buƙaci su yi masa iso a wajen Haj Hudah, ba su ɓata lokaci ba wajen shiga gidan domin sanar da ita zuwan na shi.kasancewar wayarsa babu caji tun yana hanya ta kashe kanta, shi yasa bai iya kiranta ya sanar da ita zuwansa ba.
Ɗaya daga cikin hadiman gidan maigadi ya sanar da ita ta gayama Haj Hudah, Musaddiƙ ya zo wajenta ya na waje, ya ɗan tsaya jiran amsar da za’a ba shi, hakan yasa hadimar ta haye sama da sauri zuwa ɗakin uwarɗakin nata, Haj Hudah tana kwance kan resting chair ɗin dake cikin ɗakin , tana sanye cikin koriyar baƙar riga, ta ɗaure dogon gashin kanta da ɗankwalin rigar. Idanunta na rufe, zuciyarta cike take da azalzala na zafi da ƙuna. Idan ta tuna awa ɗaya da yan mintoci da suka wuce, irin tashin hankalin da su kayi da Alh yusuf sanda kafin ya wuce filin jirgi domin tashi zuwa germany.
Idanunta sunyi jawur alamar ta ci kuka ta gaji, ta rasa inda Alh yusuf sanda ya sa gaba, dukiya dai ta tace ita yake taimako kamar yadda kullum yake iƙirari, to meye aibu ko illa idan tace ya daina yawan fita waje, asalima tana da buƙatar ya dawo da duka kasuwancin da yake yi a waje zuwa gida Nigeria, wanda tayi haka ne saboda ya dinga zama tare da ita, domin tana ganin duk da baya cikin ranta baya gabanta a yanzu, hakan zaisa ta sami sassaucin ƙauna da son kasancewa da musaddiƙ, wanda tunda ya ƙaurace mata ta rasa sukunin rayuwa, tana son ta samu natsuwar da ta rasa, duk da bata cire ran musaddiƙ zai dawo gareta ba.
Amma yadda Alh yusuf sanda yau ya runtse idanunsa ya gaggaya mata magana mara daɗi ya kasa fita a ranta, har yana kiranta da mara godiyar Allah, sai dai duk da haka ya gaya mata zai je ya tattaro komai ya dawo da shi nigeria,idan ma tana son ya maido mata da duka kuɗinta ne to zai dawo mata da shi, har ya na gaya mata dama ya gaji da yi mata wahalar da sam bata gani, asalima ba ta taɓa gode masa ba, a haka suka rabu baram baram dutse a hannun riga. Tunda kuma ya tafi bata ko motsa daga inda take ba tana kan kujerar sai da ta gama kukanta sannan ta kishingiɗa tana jin matuƙar damuwa a ranta, tana jin dole fa yau sai ta sauke alwashin da ta sha na ba zata ƙara zuwa asibitin ba don ganin fuskar musaddiƙ ne kaɗai zai lafar mata da ɓacin ranta, duk da tasan ba zata ga farincikin ganinta a fuskarsa ba……. Sallamar hadimarta ya katse mata tunanin da take yi, cikin muryar da bata son a dameta ta amsa gami da tambayarta menene. Cikin ladabi ta sanar da ita musaddiƙ ke nemanta ya na waje. A gigice ta buɗe idanunta, tana ƙara maimaitawa “ Musaddiƙ?”, ta amsa “Eh Ranki ya daɗe”, ta zubo ƙafafunta ƙasa tace “ kice ya shigo ƙaramin falon sama”, ta amsa gami da juyawa da sauri ta koma.

Cike da tsananin mamaki ta tashi, nan da nan ta faɗa bandaki ta yo wanka, haka zalika sai da ta ɓata lokaci mai yawa tana kwalliya, zuwa lokacin har Musaddiƙ ya gaji da zaman falon, duk da tuni aka cika gabansa da kayan ciye ciye da shaye shaye, har da su gashasshiyar kaza, amma babu abu ɗaya da Musaddiƙ ya ko duba, duk da yunwar da yake ji wacce har ta fara galabaitar da shi. Sai ya kai gauro ya kai mari a tsakiyar falon, yana jin duk second ɗaya tamkar shekara ɗaya ne, ya ƙosa matuƙar ƙosawa Haj Hudah ta shigo. Ƙamshin turarenta da ya bugi hancinsa shine ya tabbatar masa da cewa ta shigo falon, a gaggauce ya juya suka haɗa ido, tasha kwalliya cikin riga da siket na atamfa exculusive super, ɗaurin ɗankwalin ya ƙara fitowa da kyawun fuskarta.
Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke idonsa a kanta, ita kuma tana ta ƙoƙarin maida murnar ganinsa cikin zuciyarta, duk da ta na jin kamar mayen ƙarfe ne ke ƙara fisgar ƙaunar musaddiƙ zuwa cikin zuciyarta, duk da ta ji rashin jindaɗin ganin yadda ya ƙara kwantsamewa to fa ta ɓoye komai a ranta ciki harda murna da zumuɗin ganinsa, don haka ta zaɓi ɗaya daga cikin kujerun da suka mamaye falon ta zauna gami da harɗe ƙafafunta, ta na yi masa wani irin kallo wanda a yanzu musaddiƙ ya rasa gane wane irin kallo ne. Ta nuna masa kujera da hannu tace “ka zauna mana”, ba tare da musu ba ya zauna, ta ƙara kallonsa tace “ya ba ka ci komai ba”.
Ya girgiza kai yace “Bana jin cin komai, na zo ne muyi magana”.
Ta ɗan gyara zamanta tace “ wace magana?, ina jinka”.
Sakko da guiwoyinsa duka biyu ya yi ƙasa, cikin muryar kuka yace “Ba ni da shi, ba ni da halin samun kuɗin da za’a yi ma Afrah aiki, babu buƙatar na sanar da ke wane irin matsayi ta ke da shi a guna, illa dai nace miki Afrah rabina ce, haka zalika idan bata babu ni, sannan idan na gaza taimaka mata alokacin da tafi buƙatar taimakona to bani da sauran wani amfani a rayuwata”.
Duk da kalamansa da yadda ya ƙasƙantar da kansa, sun taɓa zuciyarta baisa ta nuna komai a fuskarta ba, ta ɗan dube shi tace “Duk wannan abin ka so ne, musaddiƙ idan har da gaske kake iƙirarin kana sonta to da duk ba azo wannan gaɓar ba”, ya girgiza kai yana ƙoƙarin maida hawayensa yace “ Ina son ki taimake ni ne don Allah ba don wata manufarki ba”, Haj Hudah ta miƙe tsaye cike da ƙarfin hali tace “ kada ka fara cewa zaka yi min wa’azi, kuma duk abinda ka ke so zanyi maka, amma bayan ka amince da sharaɗina”, ta juya ta fara tafiya, da sauri musaddiƙ yace cikin galabaitacciyar murya, “ Don Allah ki taimaka min Afrah tana cikin wani mugun hali, ki dubi girman Allah ki tausaya mana”, ta juyo fuska tamke tace “Idan ita kenan maganar zan koma ciki”, ta faɗa ne kawai amma bata ƙi su kasance a haka ba har gari ya waye.
Ta cigaba da tafiya, sai da ta kawo daf da ƙofar fita, sannan cikin wata nannauyar murya da ba tayi kama da tashi ba yace “ Na yarda na amince zanyi yadda ki ke so”, yana faɗan haka ya sulale ya yi zaman dirshan a ƙasan kafeta ya dafe kansa da hannu biyu, yana jin wasu zafafan hawaye na fita daga idonsa.
Ita kuwa ji tayi numfashinta na ƙoƙarin suɓucewa, lokaci ɗaya kuma wani irin daɗi ya shiga ratsa dukkan sassan jikinta ta lumshe ido ta buɗe tana jinta tamkar wata sabuwar halitta, duk wata danuwarta ta yaye, a hankali ta juyo ta tako har inda yake zube, itama ta zube a gabansa, hawayen da ta gani ya na malala a kuncinsa, yasa nan da nan itama ta ji na ta hawayen ya ɓalle, kyakkyawar zuciyarta ɗaya na gaya mata me yasa ta bari shaiɗan ya ci galaba a kanta, shin tasan hatsarin da take ƙoƙarin jefa kanta ciki kuwa?, za kuma ta iya dakon zunubin da take ƙoƙarin ɗorawa kanta?. Bata sami amsar tambayar ba, ɗaya baƙar zuciyarta tace, koma menene ai Allah bai rufe miki ƙofar tuba ba, don haka duk abinda kika aikata sai ki tuba. Hmmmm lallle Haj Hudah kin faɗa rijiya gaba dubu.
Cikin rawar murya tace a yayinda ta ke ƙara matsantar musaddiƙ, shi kuma ya na ja baya, “ me yasa kake kuka, haba musaddiƙ, menene abin damuwa a wannan lamarin”, ya kauda kansa yace “saɓon Allah fa za muyi ta ya ya bazan damu ba, ina son ki sani tun da nake a duniya ban taɓa shiga tasku irin na wannan lokacin ba, ko sanda nake cikin baƙar rayuwar shaye shaye ban damu ba kamar wannan, da zan aikata zunubi da gangan, ina jin tsoron sakayyar Allah akaina da azabarsa”, ta ƙara matsowa tana goge hawayenta, tace “Shi fa Allah mai rahama ne me jin ƙaine, don Allah ka kwantar da hankalinka komai za muyi babu mai sani”, ya waiwayo ya dubeta yace “ Allah fa”. Sauri tayi tace “ Don Allah kabar wannan maganar, tunda dai ka amince shikenan, gobe in sha Allah, za’a gama komai, ko kana ganin waje za’a fitar da ita?”.
Ya girgiza kai, daganan ya yi mata duk bayanin da likita ya yi musu, yana share hawayensa ya ƙara da cewa, “yanzu Abujan muka yanke shawara za’a kaita zenith hospital babu matsala komai nasu kamar na ƙasar wajenne”, tace “To shikenan amma ni nafi son a yi mata aikin a ƙasar waje, amma koma nenene goben zamu sami likitan mu ji yadda za’ayi”.
Musaddiƙ ya miƙe da sauri domin yadda Haj Hudah tasa hannunta cikin nasa tana murzawa.
Da sauri ta dube shi tace “ ya ya kuma ka tashi?”, muryarsa na rawa yace “ina son na koma asibiti ne”, ta yunƙura ta tashi tasha gabansa tace “Ina son gobe ka zo da shirinka na ma’aikacina, zamu tafi Abuja gobe bayan na gama magana da likita”, ya dubeta da sauri yace “ Abuja?”,
Ta gyaɗa kai tace “Eh, megidana baya nan ɗazu ya wuce germany, saboda haka a Abuja nake son komai ya tafi yadda na tsara”.
Gabansa ya yi mummunan faɗuwa, yace “Bani da natsuwar yin wani abu, don haka ba na jin zaki sami abinda ki ke so, ki bari har sai Afrah ta sami lafiya tukuna”, ta yi masa wani sakaran kallo tace “kada ka maida ni wata sakarya, babu abinda za’ayi har sai na mallaki muraɗina, kuma kada ka ɗauka daga ɗaya shikenan, a’a kamar yadda na gaya maka mai ɗebe min kewa nake nema to haka zaka zama mai ɗebe min kewa a duk sanda na buƙata”. Ji ya yi jiri yana fisgarsa gabansa ya tsananta faɗuwa, ba tare da ya ƙara furta komai ba ya nufi ƙofar fita, ta bi bayansa tana gaya masa “ Gobe ƙarfe tara ta yi maka anan, zamu koma asibiti tare agama magana kafin wucewar mu Abujan”. Nan ma baice uffan ba, haka ya fice kai a ƙasa tamkar wanda babu hankali a tare da shi. Zuciyarsa na gaya masa ka yi wauta da ka karɓi tayin Haj Hudah.shin ashe yana da ƙarfin halin da zai iya tozarta dokar ubangiji?, to amma idan bai yarda da sharaɗin Haj Hudah ba shikenan yana ji ya na gani Afrah zata rasa ranta, tunda abinda ya sanine babu inda waɗannan maƙudan kuɗin zasu fito, tabbas yana cikin tsanani, (amma ba hujja bane na saɓama Allah).
Ko a hanyar komawa asibitin tafe yake yana kuka kamar wani ƙaramin yaro ko zautacce, da yawa wasu mutanen ma sukan tsaya suna bashi haƙuri da nasihar rayuwa sai haƙuri. A haka ya kai asibitin wanda tun a hanyarsa ya ji ana kiran sallar magriba, isar shi masallacin asibitin ma har an fara shirin kiran sallar issha’i, alwala ya yi ya shige masallacin domin sauke farali, duk da yana jinsa tamkar wani mutum mutumi.
Har aka idar da sallar issha’i musaddiƙ na cikin masallaci, ya rasa ma me zaice ma ubangijinsa, wace hujja zai bashi akan saɓonsa da yake son yi.ya daɗe da hannunsa a sama amma ya rasa abinda zaice, maimakon hakama sai hawaye suka shiga zuba masa. Daga bisani ne ya tashi ya fice a hankali yake takawa kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ga dai yunwa yana ji amma bai son cin komai, farinciki yakamata ya yi sabida Afrah zata fita daga wannan masifar ta ciwo, amma sam baya jin wannan farincikin domin idan ya tuna dalilin samun lafiyar ta ta sai ya ji matuƙar damuwa da baƙinciki mara misaltuwa, ya na jin kamar ya ci amanar Afrah.
A daddafe ya shiga ɗakin wamda tun kafin

Please Login or Register in order to submit comment