Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tasan kuma ba zai saurareta ba ko ta je asubitin , domin tayi imanin cewa ba zai fito daga ɗakin da Afrah take ba don kawai ya saurareta. Duk inda ranta ya yi dubu to fa ya ɓaci, amma ta sha alwashin sai musaddiƙ ya taka rawar duk wani kiɗa da ta sa ma sa, zai gane ba irinta ake cin biredi a yaga musu leda ba.
Zaman Abujan ya yi mata zafi, ta ji tana neman ta yi yar ƙaramar hauka, hakan yasa ta kira direbanta daga minnna tace ya sameta a gidanta na Abuja. Motar haya ya biyo yana zuwa kuwa Haj Hudah ta fito, bayan ta gama kwashe duk abinda suka aikata da musaddiƙ ta cctv camerar da ke cikin ɗakin ta maida cikin wayarta, sannan ta goge na cikin cctv camera ɗin. Har suka ɗauki hanyar minna ji take kamar zuciyarta zata tarwatse saboda tsananin baƙin ciki da tashin hankali.
Ko minti biyu Haj Hudah ba tayi da barin gidan ba, megadin ya ɗaga waya ya kira Alh yusuf sanda, ya tabbatar masa da tafiyar Haj Hudah minna ita kaɗai ba tare da musaddiƙ ba.
Ya jinjina kai ya na murmushi ya aje wayar, Hudah kin ɗebo ruwan dafa kanki, zaki yi nadamar da ba ta da amfani, zaki yi danasanin duk abinda ki ka aikata da aurenki, kalaman da yake maimaitawa kenan. Lokaci ɗaya ya tuna yau kwanaki biyu kenan ba tayi magana da musaddiƙ ba a waya, domin duk wayar da suke yi yana ji shi ma, ya zuƙi sigarinsa ya fesar da hayaƙin sama yace “ Nasan za’ayi haka, na kuma san cewa matar musaddiƙ, ta dawo rayuwa ta sami lafiya don haka dole musaddiƙ zai ja baya da Hudah, tunda ya sami abinda yake so, ja bayan da ita kuwa shi ne zai sa su zama basa ga maciji da juna, zai haddasa faɗa a tsakaninsu”, ya saki dariya sosai yace “An zo wajen………
Ya kishingiɗa sosai a kan gado ya na cigaba da lissafin katin da yake bugawa a cikin wannan wasan, yana hango shi ne da nasara.

Haka Afrah ta cigaba da jinya tare da samun kyakkyawar kulawa daga malaman asibitin, domin a yanzu bayan nono da ta ke ba Hanan, tana takawa da ƙafafunta ta je banɗaki, tana kuma fita ta sha iska, ta kan iya daɗewa kuma tana magana, Afrah dai ta gwada tsawon rai. Shi kam Musaddiƙ ji yake tamkar wani ɓangare ne na rayuwarsa ya dawo, sau tari hakanan zai zauna ya ƙurawa Afrah idanu yana jin yafi kowa sa’a a duniya, kamar yadda itama Afran take jin tafi ko wace mace sa’ar miji, yadda Musaddiƙ ya nuna damuwa akan lamarinta da irin yadda take ganin ruwan ƙauna a cikin ƙwayar idonsa, takan ji bata da sauran wata damuwa a tare da ita.
Sai dai ta rasa dalilin da yasa da a duk lokacin data kalli cikin idanunsa bayan ƙaunarta da ke kwance a cikin su to akwai wata ɓoyayyiyar damuwa a cikinsu, tasan musaddiƙ takan iya hasashen abinda ke cikin zuciyarsa domin ta fi kowa sanin zuciyoyinsu na da alaƙa da juna, shin damuwar meye yake ta kokawa da ita shi kaɗai, ba ta son ta yi masa magana yanzu illa ta cigaba da ganin baƙon yanayi a tare da shi. Tuni mallam Mahmud ya koma minna cikin kwanciyar hankali da natsuwar zuciya, Inna Halima ce kaɗai a asibitin da musaddiƙ, shi kansa murtala zuwansa biyu yana duba Afrah, sai dai ko kaɗan babu abinda musaddiƙ ya tattauna da shi, maimakon hakama ƙoƙari yake yana ƙara ɓoye damuwarsa. Ita kanta Inna Halima wani lokacin ta na katarin ganin damuwar ta sa, amma kafin ta tabbatar da damuwar yake ciki sai ya yi saurin kau da ta, yadda ko ta ƙara kallon fuskar tasa ba ta ganin komai.Tun komawar Haj Hudah minna ta ƙara shiga wani irin mummunan yanayi, babu abinda ke mata daɗi, ta rasa lokacin da jikinta ya saba da musaddiƙ, ta rasa yadda zata sami yin magana da shi ta waya, me yasa musaddiƙ zaiyi mata haka, kullum kiransa take amma wayar ta na kashe, ya kusa kaita bango ya kusa ƙureta.
Shi kam musaddiƙ rashin ji daga gareta ya sanya ya fara samun nutsuwa ko kaɗan kuma ba ya son ya dinga tunawa da ita, duk da sau tari ko Afrah ya duba sai ya tuna da Haj Hudah, gabansa kuma sai ya faɗi, sannan yakan ji ya zama wani iri, kai wato gaibu ita ke riƙe duniya don da mutum yasan gaibu da babu wanda zaiyi saura a duniya yana faɗan hakane idan ya yi tunanin yau da Afrah tasan abinda ya aikata da ya ya za su kasance, lalle dole ya cigaba da ɓoye wannan mummunan sirrin a cikin zuciyarsa ba tare da ya bari kowa ya sani ba, domin tsira da mutuncinsa da darajarsa musamman a wajen matarsa da ta ɗauki yardar duniya ta ɗora masa. Da kawunsa da Innarsa da suka tallafi rayuwarsa suka tsaya tsayin daka domin ganin ya zama mutumin kirki.
Haka zalika musaddiƙ ya fahimci wani irin so da ƙauna da darajawa da Afrah ta ƙara masa, domin dai tun da Inna Halima ta ƙara labarta mata irin uƙuba da damuwar da ya faɗa a lokacin da tana cikin jinyar da ba tasan wanda ke kanta ba, bayan tashin hankalin da ta gani itama atare da shi kafin ta rasa gane wanda ke kanta, haƙiƙa samun miji irinsa sai an tona. Haka zalika karanci da bajintar da Haj Hudah ta yi na ceto rayuwarta shi ma abune da ba zai taɓa goguwa ba a cikin zuciyarta, duk da ta yi mata godiya amma gani take kamar ya yi kaɗan, don haka ba zata taɓa daina yi mata addu’a ba tare da fatan alheri, domin itace musabbabin samun lafiyarta, dukkan wani halacci da nuna ƙauna Haj Hudah ta yi mata, don haka ba zata taɓa mantawa da ita ba a iya tsawon rayuwarta, ( akace wai rashin sani ya fi dare duhu).
Hankula dai duk sun kwanta Afrah ta fara warwarewa, domin a yau likitoci suka tabbatar da sallamarta, domin lafiya ta bayyana a tare da ita, tamkar ba ita ba, duk ramar da tayi ta cicciko, ta yi kyan gani, duk wanda ya ganta a lokacin da ta yi jinya, idan ya ganta yanzu dole ya ji tsoron Allah, yasan kuma babu abinda ya gagari ubangiji shi ke saukar da cuta shi ke kuma saukar da waraka. An haɗota da magunguna gami da shawarwarin yadda zata cigaba da ba lafiyarta kariya da gudunmawa daga ɓangarenta. Murtala ne ya taho daga Minna ya kwashe su zuwa gida.
Sai dai Inna Halima gidanta tace a wuce da Afrah, wanda don dai musaddiƙ ba shi da yadda zai yi ne yasa ya yarda da zaman Afrah a gidan inna Halima, domin zahiri ya yi kewar matarsa ya na kuma so ya samu keɓewa da ita domin ya nuna mata yadda ya yi rashinta, cike yake da tsananin sha’awarta mara misaltuwa.
Haka ya koma gidan shi kaɗai, shi ya gyara ko’ina da kansa domin dai wajen ya yi ƙura da yawa, sai da ya kwana biyu yana aikin gyaran wajen.
Sai cikin dare ya ke kunna wayarsa wanda da ya kunna saƙonnin Haj Hudah ne ke cika masa wayar, wanda hakan ke ƙara tilasta masa ƙara kashe wayar, a yanzu dai kam baida matsala sai ta Haj Hudah, ya na ganin abinda ya aikata shi ne zai dawo ya ƙara zama damuwa a gare shi. Har yanzu baya jin daɗin rayuwarsa, gidan Inna Halima yake uni wajen matarsa da yarsa da ta ƙara girma saboda samun nono da take yi yanzu ga lafiya ga wata irin ƙiba da take narkawa. Bacci ne kawai ke maida shi gida. Hakan yasa yau Afrah ta tsare shi da ido har yanzu akwai wannan ɓoyayyiyar damuwar a tare da shi, ta ɗan numfasa ta kira sunansa cikin wani irin sauti “Yaya Musaddiƙ”.
Ya waiwayo ya na dubanta lokaci ɗaya ya na amsawa.
Ta ɗan kwantar da murya tace “yakamata zuwa yanzu ace ka koma bakin aikinka, tunda na warware, bai kamata ace ka wofintar da aikinka ba musamman a irin wannan bajintar da Haj ta yi, a yanzu ne ya kamata ka ƙara riƙe mata aikin nan da daraja”, gabansa bugawa kawai yake yi, da sauri ya kauda idonsa a cikin nata, ya kasa cewa uffan, ta miƙa tattausan hannunta ta kamo hannunsa ta riƙe tana bubbugawa da ɗaya hannun na ta, ta ƙara matsowa kusa da shi, yadda har yana fargabar ka da ta ji bugun da zuciyarsa take yi.
Ta cigaba da kallonsa sannan tace “yaya Musaddiƙ akwai damuwa ne?”, a gaggauce ya girgiza kai gami da damƙe hannunta sosai ya yi ƙoƙarin daidaita muryarsa yace “Babu wata damuwa Afrah, na bari ne sai kin dawo gida, hankalina ya ƙara kwanciya sannan sai na koma bakin aikina”, yau shine karo na farko da Afrah ta ji ba ta yarda da maganar da ya gaya mata ba, domin sam ba zata yi kuskuren fahimtar yana cikin damuwa ba, ta ɗan nisa tace “me yasa zaka dinga ƙoƙarin ɓoye min damuwarka, bayan ni a jikina ina jin kana cikin damuwa, asalima ina ji tamkar kana cikin wata halaka ne, jikina da zuciyata ba zasu gaya min ƙarya a kanka ba, domin kai ɗin ɓarina ne”.
Da sauri ya zame hannunsa a cikin na ta ya tashi ya na jin jikinsa kamar an canja masa, me yasa ba zai iya ɓoye damuwar da yake ciki ba, gashi nan har ta kai da Afrah ta fara zarginsa.
Yana juye da bayansa, ya ji Afrah ta taso ta kwantar da kanta akan bayansa tana sakin numfashi tana cewa “Ba ni da wani da ya fi ka a rayuwata, damuwarka damuwata ce, yadda ka tsaya akan lamarina haka ni ma zan tsaya akan lamarinka, me yasa ba zaka sanar da ni damuwarka ba”, ya juyo gaba ɗaya ya rungumeta tsan tsan a ƙirjinsa yana kokawar maida hawayen da ke son sauko masa, yace “Ba ni da wata damuwa da ya wuce na ga kin ƙara samun lafiya, bayan wannan banda wata damuwa”, zata yi magana ya yi saurin ɗora bakinsa a cikn nata, Inna Halima bata nan ta na gidan mallam Mahmud ta je ta sanar da shi batun maida Afrah ɗakinta tunda ta sami ƙarfin jikinta sosai.
Hakanne yasa a yau musaddiƙ ya sami damar shiga jikin Afrah, ita kanta ba ta yi masa musu ba, sai dai komai a hankali ya yi mata yana lallaɓata hakan yasa ba ta sha wahala ba. Sai dai har suka kammala komai musaddiƙ ya tafi tana jin wani baƙon yanayi a cikin tarayyar da suka yi, me yasa ta ji canji tamkar ba musaddiƙ ɗinta ba, irin ƙarfin son da ke tsakaninta da mijinta tana jin zata iya sanin komai a game da sirrin aurensu, sai dai kuma ta sa ma zuciyarta cewa ƙila ko don sun daɗe basu ba suyi mu’amalar aure ba ne yasa ta ji canjin, a haka ta ɗauka ta kuna barshi a hakan.

Tunda Musaddiƙ ya koma gida ya rasa inda zaisa kansa. Haƙiƙa dole ya yi taka tsan tsan, idan ba haka ba kuwa da kansa zai iya tonawa kansa asiri, wato dai shi mara gaskiya ko cikin ruwa ya ke dole ya yi zufa. Dai dai lokacin ya janyo wayarsa ya kunna tamkar ana jiran ya kunna wayar Hassana ta shigo cikin wayarsa, da sauri ya ɗauka, sai da ta gama ƙorafin me yasa kullum wayarsa a kashe, sannan ta tambayi jikin Afrah, daganan kai tsaye ta sanar da shi dalilin kiran na sa, wanda gaba ɗaya ya ƙara faɗawa cikin tashin hankali mara misaltuwa, domin Hassana ta tabbatar masa da cewa sunsa gidan da yake ciki a kasuwa sun kuma sami mai saye, domin duk abinda Haj kilishi ta tara ya ƙare a wajen jinyarta babu komai a yanzu babu abinda ya rage mata sai wannan gidan shi ne dalilin da zasu sayar da shi domin cigaba da kulawa da ita. Gida dai ba nasa ba ne babu yadda za’ayi ya hana a sayar da shi don haka ya nuna goyon bayansa, cikin jimami Hassana tace “yanzu ina zaku koma kai da Afrah”.
Ya jinjina kai yace “ka da ki damu, in sha Allah zamu sami ko da gidan haya ne mu koma can”, hakanan ta ji zuciyarta ta sare bata kuma ji daɗi ba amma bata da yarda zata yi, hakan ya zama dole ne, ko sallama ba ta iya yi da shi ba ta kashe wayar.
Ya lumshe ido bakinsa na faɗin innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, ya rasa ma tunanin da zaiyi, har zuwa lokacin da wayarsa ta ƙara carkewa da ƙara ya bude ido a hankali ya na kallon allon wayar, ganin sunan Haj Hudah yasa ya ƙarasa buɗe idanunsa sosai ya ƙurawa wayar ido, harta tsinke bai iya ɗauka ba lokaci ɗaya ta ƙara ɗaukar ruri, wata zuciyar ce ta ce ɗauki ka yi mata kashedin ta fita harkarka.
Cikin ƙarfin hali ya ɗaga wayar tun kafin ya yi magana tace “ina ƙofar gidanku, ka fito muyi magana ko kuma na shigo ciki, domin megadinku ya tabbatar min da cewa kana cikin gidan”, tana gama faɗan haka bata jira amsarsa ba ta kashe wayar.
Ya saki wani dogon numfashi bai da wani zaɓi da ya wuce ya je su yi fito na fito da ita, ya kawo ƙarshen komai domin dai zahiri ba zai iya cigaba da saɓon ubangiji ba, kamar yadda ba zai iya cigaba da zaman ɗar ɗar ba. Da sauri ya tashi ya fito ya nufi get, duhu ya yi sosai, yana fitowa maigadi ya nufi inda yake yana ƙara tabbatar masa da cewa “Ranki ya daɗe ce da kanta ta zo nemanka”, bai bi ta kansa ba ya buɗe get ɗin ya fice, can nesa da gidan ya hango motarta, ya taka da sauri yana isa bakin motar ƙofar motar ta buɗe,
Haj Hudah ta bayyana cikin ƙayatacciyar kwalliyarta mai ɗaukar hankali, ƙamshin turarenta tuni ya baibaye wajen, ita ce ta tuƙo motar da kanta, sun daɗe ba suyi ido biyu ba, hakan yasa Haj Hudah ta dinga jin tamkar ta rungume musaddiƙ ta gaya masa yadda ta yi rashinsa, sai dai ba taga fuskar yin hakan ba, don yadda musaddiƙ ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da manzon ɗaukar rai.
“Baka maraba da ganina ko? Bayan ka nisanta kanka da ni, ka sauka daga kan alƙawarin mu, ka kuma saɓama dokokina, kana ganin zan haƙura ne na rungumi hannu a tafi a na tafka asara?”, ya watsa mata wani irin kallo yace “Har gadara ki ke da alƙawarin da aka yi shi saboda saɓon Allah, sannan ai ba kiyi asara ba tunda kin sami biyan buƙatarki, shi yasa na yanke shawarar yanke duk wata alaƙa dake tsakanin mu, ina so gami da fatan ki manta da duk wani abu da ya shiga tsakanin mu ki daina bibiyata, domin iya abinda zan iya yi miki kenan, a yanzu matata da ya ta ce a gabana”.
Haj Hudah ta cigaba da kaɗa ƙafafunta duk da maganganunsa sunyi mata zafi, daurewa ta yi ta haɗiye, sannan ta zuba masa ido tace “Duk abinda zaka faɗa kana da damar faɗa, ni kuma ina da damar yin koma menene domin na cigaba da mallakarka”, ya saki tsaki yace “kinyi nisan da bakya jin kira, ni na gama wannan wasan babu kuma wanda ya isa ya maida ni ruwa”, yana gama faɗan haka ya juya ya fara tafiya, da sauri Haj Hudah tace “Daga wannan daren zuwa gobe da safe, da kanta matar da kake yin komai dominta zata san abinda ka aikata ba tare da saninta ba, tunda na fahimci Afrah ita kaɗaice kasawarka”. Cak! Ya ja ya tsaya yana jin bugun zuciyarsa ya ƙaru, da sauri ya juyo ya dawo gabanta, cikin rawar murya yace “me ki ke nufi?”.
Ta yi murmushi tace “Ina nufin yanke alaƙa da ni tamkar sanar da Afrah cin amanar ta da kayi ne”, ya ɗan gyara tsayuwarsa yace “ka da ki fara wannan kuskuren, kuma ma ina ki ke da shaidar da zai gamsar da ita ko kin ɗauka matata ƙaramar ƙwaƙwalwa gareta”.
Ta yi dariya sosai tace “Idaj ita ba ta da ƙaramar ƙwaƙwalwa to kai kana da ƙaramar ƙwaƙwalwar da ka kasa gane duk abinda muka aikata camera ta kwashe, ni kuma na kwaahe zuwa wayata kafin na goge”, tana magana tana fito da vedion ta kunna ta kuma nuno masa, gaba ɗaya ji ya yi yawun bakinsa ya ƙafe sosai sune kwance a gado cikin bargo suna aikata alfasha. Durƙuahewar da ya yi a ƙasa ne yasa ta kaahe vedion, tana cewa “wannan shi ne abinda yake ɗebe min kewar rashinka, shine kuma zai taimaka min wajen rabaka da Afrah, za kayi biyu babu ba ni ba ta, domin zuwa gobe duk hanyar da zanbi zanbi domin ganin wannan vedion ya sauka a cikin wayar matarka, nasan idonta ne kaɗai zai iya kalla ba zata bar wani ya kalla ba don haka ni banda fargabar ɓacin suna ba ni kuma da fargabar rasa kowa”.
Wasu hawaye masu ɗumi sune suke sauka a kumatunsa, kuskure ɗaya zai jawo rushewar rayuwarsa, ina ma ya yi haƙuri da hukuncin ubangiji, abinda yake faɗa kenan a cikin ransa.
Ya ɗago ido sharkaf da hawaye yace “Yanzu me ki ke so…………………


Yar gidan Imam✍️
MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
(Mrs Aliyu Mayere)

Page 21

Ya faɗi maganar cikin raunanniyar murya mai cike da fargabar amsar da zai samu daga Haj Hudah.
Ta ɗan saki murmushi tace “Bana son ina sa ka damuwa, saboda ina sonka ina jinka a zuciyata fiye da tsammaninka”, har yanzu durƙushe yake a gabanta, yace “ki daina maganar so, domin na yi imani da cewa ni bakya sona , don duk wanda ka ke so ba zaka jefa shi cikin musiba ba, son zuciyarki ne kawai yasa ki ke ganin kina so na”, ta jinjina kai tace “ko ka kira abinda nake yi son zuciya ko soyayya wannan duk ɗaya, tunda nasan abinda ke cikin zuciyata”.
Cikin ƙagauta yace “Nace me ki ke so, wanda zaisa ki goge wannan vedion a cikin wayarki, ba tare da ya isa ga matata ba, saboda duk soyayyar da nake ma matata bazan iya kallonta da idanuna biyu ba bayan ta ga wannan mummunan vedion”.ta ƙara murmusawa sannan tace “kafi kowa sanin abinda nake so, don haka ya zama maka dole ka cigaba da biya min buƙatata ka cigaba da kwantar min da hankali tare da maida ni wata sarauniya, matuƙar kana son asirinka ya cigaba da rufuwa a wajen matarka to ya zama dole mu cigaba da mu’amalar mu kamar yadda ya zamar maka dole ka cigaba da yin aiki a ƙarƙashina”.
Zufa ta lulluɓe musaddiƙ numfashinsa ya fara wahalar fita yana jin wani irin tuƙuƙi a cikin zuciyarsa, ya ƙara jin tsana da ƙiyayyar Haj Hudah fiye da kullum, idanunsa jajir, ya miƙe daga durƙuson da yayi, yana mata wani irin mugun kallo yace “Na so ace ina da ƙarfin guiwar da zan iya maida abinda kike son yi mai sauƙi, ta hanyar riga ki gayama matata ainihin gaskiya, ko don na tsira daga barazanarki, amma nasani a hankali zan kori tsoro da shakkar da ke hanani tunkarar matata da maganar, nasan kuma daga lokacin da na gaya mata ke ce zaki fi kowa shiga damuwa idan wannan maganar ta fito ta fuskoki da dama na yi imani sai kin muzanta, zan kuma jira zuwan lokacin tare da yin abinda ki ke so a yanzu, sai dai ki sani ba zaki taɓa samun jin daɗi ba”.
Ta maida ƙafafunta cikin mota tana cigaba da murmushi, “zan kiraka gobe domin sanar da kai inda zamu haɗu, domin babu amfanin rufe wayar da ka ke yi, don haka zan ba ka shawara idan ma don ni ka ke kashe wayarka to gara ka daina, domin ko da waya ko ba waya duk inda ka shiga zan nemoka, don haka gara ka daina wahalar da kanka”. Abinda ta faɗa kenan lokaci ɗaya ta na tada motar ba tare da ta ƙara tofa komai ba ta juya kan motar ta tayi tafiyarta, tana jin wani irin nishaɗi a tare da ita, zuciyarta cike da farinciki.
Daƙer Musaddiƙ ya iya ciɓa ƙafarsa ya nufi gida, bala’i goma da ashirin, ga masifar Haj Hudah, ga tunanin barin gidan da ya daɗe ya na rayuwa a cikinsa, gidan da mahaifinsa ya sha gwagwarmaya a cikinsa, gidan da duk wani alfaharinsa yake ciki. Ta yaya zai iya barin gidan da shi ne alfaharin mahaifinsa, ina ma ya na da damar da zai sayi gidan. Cikin wannan tunanin na tashin hankali ya koma gida, shi kansa baba maigadi binsa ya yi da kallo yana mamakin abinda uwarɗakin na sa ta gaya masa da ya haddasa masa shi ga wannan mummunan yanayin, ya kasa yi masa magana har ya shige cikin ɓangarensa.
A hankali saminu ya fito daga cikin duhuwar da ya ɓoye, wanda dama tun fitowarta yake biye da ita a mashin a bisa umarnin Alh Yusuf sanda. Hankalinsa a tashe yana jinjina kai cike da tsantsar mamaki, duk maganganun da su Haj Hudah suka yi akan kunnansa su kayi. Babu abinda bai ji ba, ya daɗe a tsaye yana cikin kaɗuwa, bai taɓa tsammanin ta’addancin Haj Hudah ya kai ta dinga tsoratar da mutum saboda biyan buƙatarta ba, bayan irin saɓon Allah da ta sa bawan Allah nan ya aikata, daga dukkan alamu ya yi nadama ya tuba amma ba zata bari tuban na sa ya tabbata ba dole sai ta ƙara maida shi ruwa, karo da dama kenan da ya ji mutuncin Haj Hudah ya ƙarasa zubewa gaba ɗaya a wajensa.
Ya zaro wayarsa ya zuba mata ido tamkar ya na shakkar kiran wanda ya ke so ya kira. Ya saki ajiyar zuciya, yana jin ta ya ya zai iya yi ma Alh Yusuf sanda bayanin abinda kunnuwansa su ka ji, a matsayinsa na mijinta ya ya zai ji wannan maganar, ƙarar da wayarsa ta carke da shi ne yasa ya yi saurin dawowa daga duniyar tunanin da ya faɗa, gabansa ya faɗi ganin sunan Alh Yusuf sanda ya fito, a daburce ya ɗauka
“Ina fatan bata tsere maka ba”

Ya faɗa cikin ƙaguwa

Saminu yace “A’ah bata tsere min ba, na sami nasarar binta kuma tabbas gidan musaddiƙ ta je, sai dai abinda ta je masa da shi ya ɗore min kai ƙwarai da gaske, kaima kuma ina ganin da ka haƙura kawai da jin abinda ya kaita ɗin, saboda samun natsuwarka”.

Alh Yusuf sanda ya yi murmushi sosai gami da ƙara lafewa a jikin kujera, ya na jin duk ma abinda saminu zai gaya masa da yuwuwar yasan

Please Login or Register in order to submit comment