Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shigarsa ɗakin ya fahimci ɗakin cike yake da mutane, sama sama yake jin kukan Inna Halima, da sauri cikin gigita ya faɗa ɗakin duk jikinsa rawa yake, kai tsaye Afrah ya nufa ya na nurfarfashi, likita ya ɗago yana kallonsa bayan ya gama daidaita oxcigine ɗin da ya sanya mata a hanci. Musaddiƙ ya tsorata da irin kallon da likita yake masa, don sai da ya jinjina abinda yake son faɗa kafin yace “Ina mai baka haƙuri domin Bata da wani sauran lokaci me tsawo nan gaba, daga yanzu zuwa ko yaushe komai na iya faruwa”.
Mallam Mahmud ya yi taga taga yana shirin faɗuwa Mama Hauwa da ke gefensa ta taro shi, ita kanta yau itace rana ta farko da ta ji tausayin Afrah har cikin zuciyarta, ta ji kuma tana da buƙatar ta cigaba da rayuwa tare da su, har da ƙwalla a cikin idanunta, ita kanta Na’ima ta yi laƙwas duk wannan isgilajcin nata babu, tausayin yar’uwarta ne fal a ranta, tana yi mata fatan samun lafiya. Jin furucin da likita ya yi fa ya gigita duk wanda ke cikin ɗakin, ciki harda ya sayyadi Habib da tun magriba yake asibitin a gabansa ciwon Afrah ya yi mummunan tashi, dama kuma akai akai yana yawan zuwa dubata, idanunsa cike da damuwa ya jingina jikin bango bakinsa na cigaba da yi mata addu’a.
Musaddiƙ na tsaye kamar wanda aka dasa, har likitan ya juya zai tafi sannan kamar wamda aka tsikara yace “likita an samu kuɗin aikin nata”, gaba ɗaya jama’ar ɗakin suka dawo da kallonsu ga musaddiƙ, Inna Halima ko da sauri ta miƙe zuwa gaban musaddiƙ, alokacin da likita cike da murna da farinciki yace “Alhamdulillah, idan hakane akwai yuwuwar ceto rayuwarta”, musaddiƙ ya numfasa yace “Gobe zamu zo office domin jin yadda za’ayi”, likita ya ƙara murmusawa yace “Allah ya kaimu”, ya juya ya fita.
Inna Halima ta ruƙo hannun Musaddiƙ tana yi masa wani kallo don tana son ta tabbatar ba hauka ya fara ba, tace “kana cikin hayyacinka kuwa musaddiƙ? kada fa damuwa ta zautaka kasan abinda ka ke faɗa? Waye zai biya kuɗin aikin aɗan wannan ƙanƙanin lokaci duk yawansu”, Mallam mahmud shi ma ya dawo kusa da shi yace “ka yi mana bayani, muna jinka”.
Ya numfasa, ƙafafunsa ba zasu iya cigaba da tsayuwa ba, don a wahalce yake, kan kujerar robar ya zame ya zauna sannan yace “Bayan fitata nan, gidan Haj Hudah na tafi neman alfarma, saboda ita kaɗai nake da yaƙinin zata iya taimakona, kuma Alhamdulillah an dace dama tace tana ta tunanin ta fitar da ita ƙasar waje ne a dubata a can tun kafin ma na je neman taimakon, yanzu gobe zanje mu taho zata ga likita zata yi magana da shi”. Gaba ɗaya sai mallam mahmud ya zube ƙasa ya kalli alƙibla yayi sujjadar shukur, sannan ya ɗago yana cigaba da yi ma Allah godiya. Haka ɗakin gaba ɗaya kowa sai murna yake, a cikin hakane su ma su kabir da mansur suka iso, domin tuni mallam mahmud tun ɗazu da jikin ya rikice ya kirasu a waya ya sanar da su, su zo idan suna da rabon ganawa da yar’uwarsu su gana, shigowarsu kuma sai suka tadda abin farinciki, suma nan suka shiga nuna nasu farincikin. Tun a wannan daren mallam mahmud yace su tafi su yi mata godiya. Musaddiƙ ne ya hana da cewar Haj Hudah ba ta son baƙin dare, dole tasa suka haƙura akan zasu jira zuwa gobe idan ta zo asibitin sai suyi mata godiyar. Ya sayyadi ne ya fara tafiya bayan anyi ma Afrah addu’a .
Su mansur ne suka ɗauki su mallam mahmud zuwa gida, tun a mota har gida yabon Haj Hudah mallam mahmud da su kabir suke yi, saɓanin mama Hauwa da tun a asibiti ta nutsa kogin tunanin da a duk lokacin da abu makamancin haka ya faru take yi, wai wane matsayi Haj Hudah ta ba musaddiƙ ne? Domin dai wannan matsayin ya wuce matsayin uban gida da yaro, ya wuce matsayin taimako don Allah, wannan abinda takema musaddiƙ ko ɗan’uwanta da suke ciki ɗaya ba zata iya yi masa ba, shin waye musaddiƙ a wajen Haj Hudah?, taso ace akwai mai bata wannan amsar amma babu, domin tasan ba mai iya bata amsarta sai lokaci, don haka zata cigaba da jiran lokacin da zata sami dukkan amsoshinta cikin natsuwa. Sai dai duk da haka ta kasa jurewa, ko ɗan ya ya ne tana son ta yi maganar, don haka ta juya ta dubi mallam Mahmud da yake cike da farinciki tace “Mallam ka ga gajen haƙuri ko, sai da ka gama salwantar da kadarorinka sannan sai ga wata hanyar ta fito”, bai ba maganarta wata fassara ba yace “ Haka Allah ke ikonsa, mun dai godema Allah, sannan mun gode ma wannan baiwar Allah”.
Ta ɗan muskuta tace “Gaskiya ina matuƙar mamakin irin wannan ƙauna da wannan matar takema musaddiƙ, sai ina ganin kamar abin ya yi yawa, ace irin wannan makudan kudaɗen ta ɗauki nauyin bada su, harda tunanin kaita ma ƙasar waje, gaskiya abin ya yi yawa, anya kuwa ba ta da wata manufa a can ƙasan zuciyarta?”.
Nan da nan mallam Mahmud ya canja fuska gami da watso mata wani irin kallo, shi kansa kabir da yake bayan motar kusa da ita sai da ya dubeta, a hankali yace “Mama wace irin magana ce wannan”, mallam Mahmud yace “Barta ta cigaba da ƙoƙarin aibata yayan mutane abinda ta saba kenan dama kullum, yi ma yayan wasu sharri, maza itama Haj Hudan ki lalubo wani sharrin ki liƙa mata don kawai ta taimaki maƙiyiyarki Afrah”.
Mama Hauwa ta canja fuska, wannan karon babu komai a ranta me kama da hassada ko baƙinciki gaskiya ce kawai take son nuna musu, tace “A’a ka da ka ɗora min magana, yanzu meye laifi don na yi tunani na kuma fito da tunanin na faɗa, ai dole ayi mamaki ace babu dangin iya bare na Baba amma mace ta yi ma namiji irin wannan bajintar, dole akwai hanyar da zata fanshe………”, a fusace mallam Mahmud ya katseta “bana son na ƙara jin wata magana ta fito daga bakinki akan wannan maganar idan ba alheri ba”, mansur ya aje numfashi yace “Don Allah mama ka da ki ƙara yin wata magana”, ta ƙara haɗe rai tace “To ai shikenan, tunda bakwa hango abinda nake hange”. Duka shuru su kayi, har suka kai gida babu wanda ya ƙara magana.

Tun watsewar kowa a ɗakin musaddiƙ ya koma kan gadon Afrah ya kifa kansa ya ɗora wani sabon kukan, yana jin ya gama cin amanarta a duniya. Shigowar Inna Halima kenan tun bayan rakiyar da tayi ma su mallam Mahmud, fuskarta da ragowar Fara’a amma ganin musaddiƙ a wannan halin ya tilasta fara’ar barin fuskarta, ta ƙaraso kusa da shi da sauri tana ƙoƙarin gyara goyon Hanan, ta dafa saman bayansa gami da kiran sunansa a sanyaye, da sauri ya ɗago ya dubeta fuska sharkaf da hawaye, damuwa ta ƙara yawa tace “Haba musaddiƙ me kake son maida kanka ne, inace kuma yanzu damuwar ta ka ta kusa zuwa ƙarshe, kuɗin nan gashi an same su a lokacin da duk muka yanke tsammanin samu, ai kamata ya yi a ganka cikin farinciki ba a ganka a wannan yanayin ba”, shuru ya yi don shi kansa yasan dole ya yi ƙoƙarin mallakar hankalinsa, don tabbas idan aka cigaba da tafiya a haka to za’a fahimci halinda yake ciki a yanzu ba damuwar ciwon Afrah bane kawai ke damunsa ba.
Ya kasa cewa uffan, har Inna Halima ta cigaba da yi masa nasiha, daga bisani ta ƙare da sa ma Haj Hudah albarka tare da tabbatar da ita acikin mutane na gari abin koyi. Kai kawai yake gyaɗawa domin inda tasan sadaukarwar da zaiyi asanadiyyar kuɗin da zata bayar da ta kwashe mata albarka ta kuma sata a layin la’anannu. Daga bisani da kanta ta takura masa akan ya wuce gida yau dai ya kwana ya yi wanka ya gyara kansa, saboda ya sami natsuwar zuwa ya taho da Haj Hudah a goben, ya yarda zai tafi amma kafin tafiyar tasa sai da ta matsa masa ya ci abinci ya ɗan dawo hayyacinsa, ya karɓi Hanan ya gama kalleta tsaf sannan ya miƙata ga Inna Halima, daganan ya wuce gadon Afrah da har zuwa yanzu bata san wanda ke kanta ba, addu’a ya yi mata ya tofa mata sannan ya kama hanya ya fice bayan ya yi ma Inna Halima sai da safe.

Tunda musaddiƙ ya koma gida wanka kawai ya yi ya yi sallolin nafilarsa akan sallayar ya kwanta, gaba ɗaya rayuwarsa ta yi baƙi, tunda yake bai taɓa yin zina ba sai gashi a yau yana tunanin yin zina ba ma da budurwa ba da matar aure zunubi biyu, babu abu ɗaya da ke sanyaya ransa, damuwa ta yi masa yawa, jarabawar tasa ta yi tsauri da yawa, yana kuma baƙinciki da ba zai iya cinyeta ba, ya riga ya faɗa halaka, baya jin zai iya yin bacci a wannan daren.
Kamar yadda Alh yusuf sanda ke kaiwa da komowa a tsakiyar falo, ya sha karan sigari yafi goma amma baya jin zuciyarsa ta lafa daga baƙincikin da ke addabar zuciyarsa, yau Haj Hudah ta gaya masa maganganu masu ƙona zuciya matuƙa da gaske, ya ƙarema falon da yake ciki kallo sheraton hotel ne dake Abuja, maganar zuwa germany tuni ta sha ruwa, ya yi cancelled ɗin ticket ɗinsa, domin yana cikin filin jirgin saman na abuja kafin a fara boarding saminu ya kira shi ya tabbatar masa da cewa, musaddiƙ a yanzu haka yana cikin get ɗin gidan Haj Hudah anje yi masa iso da ita, ya saki fara’a baƙincikin da ya fito da shi daga gida ya kau yace “To saminu duk yadda za’ayi kayi ka samu ka gano min duk abinda suka tattauna”, yace “Angama Ranka ya daɗe”. Ba’a jima ba saminu ya ƙara kiransa ya sanar da shi babu yadda za’ayi ya san abinda suke tattaunawa domin falon sama suka shiga”, ya saki ɗan murmushi, sannu a hankali ya gama yi masa kwatancen inda zai bi har ya kai ga windon falon inda zai iya jin duk abinda suke cewa, idan anyi sa’ar labulen windon ma na buɗe har vedio zai iya yi.
Ƙarfe bakwai da minti arba’in da biyar na daren za’a fara yima fasinjoji screening an fara kenan saminu ya turo masa vedion da ya yi sanadiyyar fasa tafiyar tasa, da kansa ya je ya yi cancelled, ya yi shatar taxi zuwa sheraton hotel, sannan ya maida layin wayarsa yadda idan an kira za’a ji tamkar yana ƙasar waje ne, ya daɗe yana ƙara kallon vedion duk da bakomai bane ya fito to ya fahimci abubuwa da dama a cikin vedion ciki harda musaddiƙ ya karɓi kwangilar Haj Hudah ne saboda babu yadda zaiyi a ƙoƙarinsa na son ceto rayuwar matarsa, ya yi murmushi ya faɗa a fili “ wannan shine kuskure mafi munin kuskure da zakayi a rayuwarka, ban sadaukar da Hudah ba sai da na tabbatar da duk wanda ya sameta sai ya ɗanɗana kuɗarsa sai ya sha wahala fiye da daɗin da ya sha”. Sosai ya ji ya ƙara tsanar Haj Hudah yadda take rawar jiki akan musaddiƙ ya tabbatar masa ko me daran daɗewa akan musaddiƙ Haj Hudah na iya rabuwa da shi kafin ko faruwar hakan ya na da tabbacin ya riga ya gama cika dukkan burinsa da ya daɗe da shi a cikin zuciyarsa, ya koma ya zauna ya ƙara kunna wani karan sigarin ya zuƙa ya fesar da hayaƙin ya girgiza kai yace “lalle Hudah kin iya zaɓin wajen zuwa ku ci amanar aure, ina nan ina jiran zuwan ku Allah ya kawo ku lafiya”. Ya maida kansa ya kwantar gami da lumshe idanunsa tun yanzu har ya fara jin ƙyamarta, ya buɗe idonsa da ya yi jawur a fili yake magana yace “ Na ɗauka ba zanji zafi ko kishi ba, amma me yasa na ke jin zafi da ƙunci a cikin zuciyata tun kafin ma komai ma ya shiga tsakaninsu”. Ya saki tsaki, lokaci ɗaya ya ɗakko waya ya kira wani mutum da yake masa komai akan layin waya, yasan sirrin layin waya fiye da tunanin kowa, basu daɗe suna magana ba akan yana son a ɗora masa layin Haj Hudah a wayarsa yadda duk wanda ya kirata ko ta kira shi ko ta yi magana da shi zai ji duk abinda suka ce, ba tare da ta sani ba, nambar kawai Idi master ya nema ya tura masa, nan da nan ya tura masa nambar da Haj Hudah take amfani da ita, ya kuma tabbatar masa a daran nan yake so ya gama yi masa wannan aikin duk abinda yake so ya bashi zai ba shi. A taƙaice dai a wannan daren Alh yusuf sanda baiyi baccin ko da minti goma ba saboda ɗorawa kai masifa, ya na jin komai ya kusa zuwa ƙarshe, a cikin daren kuwa Idi master ya gama yi masa aiki akan layin Haj Hudah, ya gaya masa nambobin da zai danna a wayarsa haɗe da nambar Haj Hudah, a wannan daren bai runtsa ba har sai da ya tabbatar komai ya yi dai dai.
Washegari ƙarfe takwas na safe a cikin get ɗin gidan Haj Hudah ya yi ma Musaddiƙ, ya na sanye cikin ƙananan kaya, riga fara me gajeran hannu, da jeans baƙi kai kauri, da takalminsa kambas shi ma baƙi, ya yi kyau ƙwarai sai dai damuwa da rama da rashin natsuwar zuciya, domin kallo ɗaya zaka yi masa kasan yana cikin tashin hankali.
Bai ɓata lokaci ba wajen zaman jiranta, ta fito cikin ƙayatacciyar kwalliyarta ta nunama sa’a ta yi kyau harta gaji, sai kace an ɓarota a leda, sai tashin wani ƙamshi take na musamman, kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci tana cikin farinciki mara misaltuwa, fahimtar hakan da Musaddiƙ ya yi ne ya ji wani irin haushinta ya kama shi, ta ya ya zata yi farinciki bayan ta jefa shi cikin baƙinciki. Ita kam kyau ya yi mata sosai da kwarjini ta daɗe tana kallonsa tana jin tamkar ta faɗa kan faffaɗan ƙirjinsa wanda a kullum idan idonta ya kai kai takan ji tamkar ƙaunarsa zata kasheta. Ta umarci direba ya ba Musaddiƙ makullin motar tare zasu fita zasu je wajen matarsa mara lafiya. Duka jami’an gidan sunyi musu fatan dawowa lafiya tare da yi ma mara lafiyan fatan samun lafiya.suna fita saminu ya koma gefe ya kira Alh yusuf sanda ya sanar da shi fitarsu, tare da nuna alhinin yadda taƙi tafiya da kowa balle ya sami damar sanar da shi abinda ke faruwa, kai kawai ya jinjina yace “ kada ka damu, babu inda Zasu shiga da bazan sani ba”, ya fadi maganar cike da ƙarfin guiwa. daga bisani suka aje wayar tare, lokaci ɗaya saminu na yin irin tunanin da yake yi a kullum, Alh yusuf yana ƙoƙari da yake bibiyar matarsa ya kuma san abinda take aikatawa idan miji yasan matarsa tana aikatawa zai iya haɗiyar zuciya ya mutu, to amma abinda yake ɗaure masa kai shine yadda kwata kwata baya jin damuwa a tare da shi balle kishi, shin me hakan ke nufi? Don me yake bibiyarta idan bazai iya ɗaukar mataki ba tun kafin me faruwa ta afku? Me yasa baya kishin matarsa?, irin waɗannan tambayoyin saminu ke yi ma kansa a ko da yaushe. Don sau da dama duk da kuɗin da Alh Yusuf sanda yake cika shi da su, yana ji a zuciyarsa babu dad'i yana jin tamkar yana cin amanar uwardakinsa ne.
Duk yadda ta so ta ja Musaddiƙ da hira ya ƙi bata haɗin kai, tana bayan mota yana gaba ya na tuƙi, har suka isa asibitin babu kalma ɗaya da musaddiƙ ya furta a cikin motar. Sai da suka fara isa ɗakin da Afrah take, suka ga jikinta suka kuma gaisa da Inna Halima, Haj Hudah ta sa hannu ta sa hannu ta ɗauki Hanan ta ƙura mata ido tana ji a ranta ina ma yarta ce ita da musaddiƙ, yarinyar tana da kyau, gashi duk da ba nono take sha ba, sai girma take, da alama tana da lafiya, ta daɗe a hannunta kafin Inna Halima ta karɓeta, daga bisani Haj Hudah da Musaddiƙ suka wuce ofishin likita.
Wanda ya tarbi Haj Hudah cikin girmamawa, sunyi maganganu masu yawa akan yadda za’a ceto rayuwar Afrah sai dai Haj Hudah ta fi nuna buƙatar a fitar da ita ƙasar waje,
Likita ya dubeta sosai yace “A matsayina na likitan Fatima Mahmud, wanda nasan aikin nan, na kuma san ciwon Fatima da irin matakin da ciwon ya kai a jikinta, a gaskiya a yanayin jikinta ba zata iya jurar tafiya ta sama da awa uku ba, don haka kiyi haƙuri, ayi mata aiki anan tunda muna da ƙwararrun likitoci, kamar zenith hospital ɗin nan sun iya aiki, suna kuma da kayan aiki, da na’urori na zamani, kuma tun jiya muka fara magana da asibitin, babu wata matsala, ita kawai suke jira, don haka gara ayi aikin anan zai fi muku sauƙi daga ku har mara lafiyar”.
Haj Hudah ta juya ta dubi musaddiƙ da yake zaune tamkar an dasa shi.
Ta katse masa tunaninsa da cewa “ka ji abinda likita yace”, ya ɗago ya rasa abinda yasa ba ya son kallonta yace “Ni ma nafi so ayi mata aikin anan, lafiyarta kawai na ke buƙata, don haka idan har fita da ita waje zai iya yin wata illa ga Afrah, to yi mata aikin anan shi ne abinda Ya dace saboda haka a maida mu can Abujan kawai”. Likita yace “ hakan ya fi, batun maida ku zenith hospital kuma babu damuwa kamar yadda na gaya muku ne tun jiya muka fara magana da su, saboda haka yanzu zamu haɗa duk report ɗin ciwon zamu tura musu, ta email kafin ku isa sun riga sun gama duba komai,saboda haka ko yanzu kuna iya wucewa da ita Abujan saboda komai cikin gaggawa take buƙata”.
Babu ɓata lokaci aka shiga shirin wucewa da Afrah Abuja, Inna Halima ta kira mallam Mahmud, wanda kafin agama shirin har ya iso asibitin, tare suka tafi da mallam mahmud Haj Hudah da musaddiƙ a motar Haj Hudah, ambulance ɗin asibitinne suka ɗauki Afrah da Inna Halima, kai tsaye suka yi ma Abuja tsinke.
Wanda kafin isowarsu tuni likitoci har sun shirya ita kaɗai suke jira su fara aikinsu akanta.
Hakan ko akayi, suna isa suka fara nasu gwaje gwajen a kanta. Daga bisani Haj Hudah tasa musaddiƙ ya fita ya sayo ma su mallam Mahmud abinci, daga bisani ta buƙaci musaddiƙ da ya kaita masaukinta, haka mallam Mahmud da Inna Halima suka rakata da addu’a da sa albarka mara Musaddik ya tsaya gaban Mallam Mahmud da wata irin fuska me kama da yana neman ɗauki,cikin dishewar murya yace "kawu zanje na sauketa, yanzu zan dawo", ya yi saurin kallonsa yace "kada ka damu, ko ma menene ai gamu, ka tafi ka kaita duk inda take so", kai kawai ya jinjina, ba tare da ya iya yin magana ba, Inna Halima tace "Don Allah ka saki ranka, kaga yadda fuskarka ta koma, kawai ka ɗorawa kanka damuwa ka takurawa kanka, ka kasa ganin duk irin taimakon da Allah yake mana balle ka yi hamdala, iye fisabilillahi ko dai ya ya ne ai ka saki ranka,komai fa na Allah ne,yadda bamu tsammani zuwan waɗannan makudan kuɗin ba hakanan za kaga anyi aikin nan lafiya, an kuma samu dacewa da ikon Allah, amma wannan baƙin ran da kake yi na menene?", Ta karasa magana cikin tukewa da lamarin Musaddik, wanda kuma bai ce uffan ba illa bin bayan Haj Hudah da yayi jiki a sanyaye. Inna Halima ta dawo da kallonta kan Mallam Mahmud tace "kana ji na da Musaddik,ba kace komai ba yaya, haba na rantse maka ya fara kaini bango bana son rashin tawakkali wallahi", ya numfasa yace "To me zance Halima, halinda yaron nan yake ciki na damuwa yayi yawa,ina dai addu'ar Allah ya tashi kafadar Afrah, don idan wani abu ya sameta bansan halin da zai shiga ba kuma", da sauri Inna Halima tace "In sha Allah babu abinda zai sameta, lafiya lau za'ayi aikin nan", ta ƙara rungume Hanan a kirjinta, tana jin kamar tafi kowa bukatar Afrah ta rayu.
Suna fita kai tsaye, wajen cin abinci Haj Hudah ta umarce shi da ya wuce.
Ko da suka je wajen cin abincin Musaddik ya kasa cin komai duk da abinci mai rai da lafiya da tasa aka cika gabansa da shi, sai cokali kawai yake juyawa a cikin abincin, ya rasa abinda ke yi masa dad'i a rai, ita kam tana jin tafi kowa son ya ci abincin ko ba don komai ba don ya sami ƙarfin biya mata bukatarta, domin yau jinta take a wata irin duniya ta daban me cike da yanayin da bata taɓa samun kanta ciki ba.jin wannan rana take babbar rana mai cike da tarihi a cikin rayuwarta.sabanin Musaddik da yake jin ranar tamkar bak'ar rana, babu wani abu dake masa dad'i, ransa da zuciyarsa duk a jagule suke. Daga wajen cin abincin kai tsaye gidan Haj Hudah suka nufa, suna isa masu gadi suka buɗe musu get. Yadda musaddiƙ ke ɗari ɗari kai kace bai taba zuwa gidan ba. Tun a falo Haj Hudah ta yada gelenta, ta faɗa kan doguwar kujera tana maida wani irin rikitaccen numfashi, gaba ɗaya musaddiƙ ji ya yi ya na neman ya rikice, ya rasa abinda ke masa daɗi, komai baƙi yake masa, kamata ya yi ace yana can tare da matarsa a cikin wannan rikitaccen lokaci amma gashi anan da ƙoƙarin cin amanarta. Ji ya yi lallausan hannun Haj Hudah ya janyo shi gaba ɗaya bai yi aune ba ba zato ba tsammani ya ji ya faɗa kan jikin Haj Hudah, a gaggauce ya yi zumbur ya tashi tsaye, jikinsa na tsuma.
Haj Hudah ta buɗe idanunta sosai tana yi masa wani irin kallo, tace “Ka tuna matarka dake can kwance rai a hannun Allah, idan har baka biya min buƙatata cikin daɗin rai, da so da ƙauna ba kamar yadda kake tarayya da matarka ba, to ina tabbatar maka sai dai ka ɗauki matarka kasan yadda zaka yi da ita domin nerata ba zan bayar ba”, ido ya ƙura mata ya na ganin gaskiyar abinda ta faɗa a cikin idanunta, duk ɗan tausayin nan da ya kan gani a idonta yanzu babu komai a cikin idanunta face tsananin son cikar birinta ko ta halin ƙaƙa. Ya runtse idonsa ya buɗe cikin rawar murya yace “zanyi abinda ki ke so, zanyi………………



Yar gidan Imam✍️
MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
( mrs Aliyu Mayere)

Page 19

Ya na gama faɗin haka ya koma ya zauna tamkar wanda bashi da laka, Haj Hudah ta saki murmushi lokaci ɗaya ta tashi daga kujerar da take zaune ta dawo hannun kujerar da Musaddiƙ yake yadda har suna iya jin bugun numfashin juna, nan da nan jikin Haj Hudah ya shiga wani irin rawa kamar ana kaɗata da ruwan hanji, tana jin wani irin muguwar sha’awar musaddiƙ na fisgarta, a hankali ta ɗora kanta a kafaɗarsa, wanda ji

Please Login or Register in order to submit comment