Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya yi tamkar an ɗora masa bakin wuta akan fatarsa, sam yadda yake jin shauƙi da sha’awa mai tsanani a duk lokacin da ko da hannun Afrah ne ya taɓa jikinsa, sam baiji haka akan Haj Hudah ba, duk da ya daɗe bai kusanci matarsa ba yasan yana jin sha’awa amma a yanzu babu wannan sha’awar asalima a yau ji ya yi ya tsani harkar kwata kwata. Ita kuwa ji take kamar bata taɓa kasancewa da wani namiji ba sai musaddiƙ don yadda take jin yanayinta kamar zata zauce.
Ta ƙara kwantar da kanta sosai a jikinsa babu kunya ba tsoron Allah ta tura ɗaya hannunta saman bayansa tana shafawa, tayi zaton za taga musaddiƙ ya fara gigicewa kamar yadda ta fara, amma maimakon haka sai ta ji ya zare hannunta ya aje sannan ya matsa yadda dole ta cire kanta a jikinsa, ido jajir cikin fita hayyaci tace “Wai menene haka musaddiƙ, meye bani da shi da sam ba ka jina a cikin ranka, na rantse ban taɓa zaton akwai wani namiji a duniya da jikina zai taɓa nasa ba tare da ya gigice ba, amma ka duba kaga tsabar ka ɗora ma zuciyarka ƙyamata ka kasa gano irin tarin baiwa da ni’imar da Allah ya yi min, ni nake biyoka amma kana janye jikinka, kada kasa na muzanta, kada kuma kasa zuciyata ta fara raya min mugun abu a kanka”,Musaddiƙ ya numfasa ya na cigaba da ganin mugun ƙarfin halin Haj Hudah yadda ta muttsuke rashin kunyarta take abubuwan da suke ba shi matuƙar mamaki, ko kaɗan ya fahimci bata jin nauyin abinda take son yi da shi. Ta ƙara kallonsa cike da fushi tace “Ya zaka dinga buga ni kamar ƙwallo, ko don kaga na riga na faɗa komarka ne, to kada ka manta bafa alfarma zaka min ba, duk abinda zaka min biya zanyi don haka ya zama dole ka saki jiki ka yi min abinda zai faranta raina”,
Musaddiƙ ya ƙara numfasawa sosai yake son ya sami ƙarfin guiwa, domin ya riga ya gama karɓar kwangilar shaiɗan don haka baida wata mafita. Ya ɗan dubeta kaɗan yace “Bakya tsoron zargin masu gadinki, kada ki manta sunga shigowar mu gidan tare, idan suka ga mun daɗe a ciki tare zasu iya zargin wani abu”, tayi masa wani kyakkyawan kallo tace “Babu ruwansu da harkata, kada fa ka manta nan Abuja ce da babu wanda yake damuwa da rayuwar wani, kuma a gari irin wannan keɓewa tsakanin namiji da mace har wani abin ɗorarwa ne, meye aciki? Ko da igiyar aurena ta kai ɗari ba uku ba babu abinda ya dami wani da yadda nake tsara rayuwata, don haka nan gidana ne masu gadina kuma basu da wani hurumi na shiga abinda ya shafi rayuwata, a irin sheƙe ayar da ake yi a faɗin duniya wannan har wani abu ne”, ya yi mata kallon kin shagala da yawa yace “yanzu alaƙar matar aure da mijin aure ne har ki ke iƙirarin ƙaramun abu”, ta ɗaga masa hannu, “ya isa, kaga idan duk abinnan bazai yuwu ba mu bar maganar, zan koma minna, kai kuma ka wuce asibiti ka sanar da su Innarka cewar na fasa taimakon da nace zanyi idan yaso idan suka tambayi dalili sai ka yi musu bayani”, ta ƙarasa maganar ta na nuna masa ƙofar fita.
Da dai ace yana da ƙarfin hali, zai iya barin Afrah Allah ya yi ikonsa ba tare da ya yi wani hoɓɓasa ba to da kalaman Haj Hudah sunsa ya fita ya bata waje bayan ya yi mata wulaƙancin da bata taɓa tsammani ba, amma ina baida wannan ƙarfin guiwar. Maimakon hakama sai miƙewa ya yi ya nufi hanyar ɗakunan gidan, ta saki wani murmushi ta tashi da sauri ta bi bayansa, ya ɗan dakata har ta zo ta wuce shi kuma ya cigaba da binta har cikin wani ƙayataccen ɗaki wanda nanne ɗakin kwananta a gidan, sanyin A.C ya cika ɗakin, kai tsaye wadrof ta nufa ta buɗe ta fito da wata yar ƙaramar riga wacce ko guiwa ba ta kai ba.
A gaban Musaddiƙ ta shiga cire kayanta, a gaggauce ya juya bayansa, jikinsa na rawa yana tabbatar ma da kansa ya shiga matuƙar halaka, kawai ji ya yi hawaye na kwarara a saman kumatunsa, baida wata mafita, da ya wuce ya yi abinda ta ke so, ƙila ya rage tsoro da fargaba, a yau ya jinjina ma mazinata yadda suke iya yin zina da mata kala kala, ba tare da fargaba ba wannan babban laifi da baida na biyu, ko a mafarkinsa bai taɓa tsammanin zai taɓa riskar kansa a wannan halin ba, halin da yake ƙyamata fiye da komai.
Daga bayansa ya ji Haj Hudah ta ƙanƙame shi, jikinta na wani irin rawa, yasan a wannan yanayin da take ciki idan ya ƙara yi mata musu tabbas tana iya yin abinda bai taɓa tsammani ba. Yana ji ya na gani, duk imaninsa ya sayar ya yi garaje bai bar Allah ya yi ikonsa ba ya yi ma kansa zaɓi,lalle son zuciya ɓacinta, a wannan lokacin mai afkuwa ta afku,tsakanin Haj Hudah da Musaddiƙ. Ya aikata mummunan laifin da yake ganin dole ne, amma maganar gaskiya son zuciyarsa kawai ya bi domin ya na ganin yin hakan shine kaɗai mafitarsa, idonsa ya rufe ya manta da cewa Allah ne me yin komai a hannunsa kuma rayuwar Afrah ta ke, ya kasa fahimtar da ya aikata wannan mummunan laifin gara ya bar Afrah Allah ya ɗauki ranta, haƙiƙa Allah ya jarafce shi akan abinda ya ke da rauni a kansa hakan yasa ya kasa cinye jarabawar da Allah ya ɗora masa.
A haka cikin wannan baƙincikin Musaddiƙ ya gama biyama Haj Hudah buƙatarta, ya yi abin ba cikin jindaɗi ba, ya yi cikin bakinciki, damuwa gami da fargaba, hakan yasa babu abinda ya ji, domin dai baisan daɗin ko wace mace ba idan ba matarsa ba, haka zalika tunda ya zo duniya, yau itace mummunar rana ta farko da ya taɓa kusantar wata ya mace da ba matarsa ba. Baƙinciki da damuwarsa suka ƙara yawa babu abinda bakinsa ke furtawa sai istigfari, ga wani irin tsana da ya ji zuciyarsa ta cika da shi akan Haj Hudah ko kallonta ba ya son yi.
Ta ɓangaren Haj Hudah kuwa tana kwance ta yi lamau a cikin bargo, wani irin kallon so da ƙauna take ma Musaddiƙ, domin kuwa ta sami jindaɗin da ta daɗe ba ta sami irinsa ba, ta jidaɗin kasancewa da Musaddiƙ, ta sami farincikin da ta daɗe tana nema, hakan ya ƙara mata tsananin son Musaddiƙ tare da sha’awarsa, har ta tabbatar ma da kanta cewa za ta iya yin komai domin cigaba da zama tare da Musaddiƙ a matsayin me ɗebe mata kewa, wanda zai dinga sa ta farinciki da nishaɗi a ko yaushe, a yau ta ƙara yarda ta kuma amince da cewa Musaddiƙ gwarzon namiji ne abin kuma son ko wace mace, ya ƙara samun kima da daraja a wajenta fiye da kullum, ko kaɗan yadda musaddiƙ ke cikin damuwa da danasani ita babu hakan a tare da ita. Shi kam Musaddiƙ tun bayan gamawarsu ya shiga banɗaki ya yi wanka da alwalarsa ya fito, kayansa kawai ya maida, ya haye kan lallausan kafet ɗin tsakiyar falon ya gabatar da sallar la’asar, bayan idarwarsa bai tashi ba, haka ya cigaba da zama yana istagfari , zuciyarsa cushe da damuwa da tashin hankali, har yanzu ba ya iya kallon fuskarta, kunyarta yake ji sosai, ya kuma tsaneta ya tsani kansa. Ita kuwa ko wane motsi ya yi burgeta yake yi, ƙara sonsa take, asalima ta kasa ɗauke idonta akansa, komai nasa burgeta ya ke yi.
Abin takaici ma har wasu maganganu take masa ta na gaya masa yadda ta jidaɗinsa, amma ko kallonta baiyi ba balle ya tanka mata, har ta gaji itama ta shiga wankan wanda har ta fito ta kintsa cikin doguwar rigar atamfa Musaddiƙ bai ɗaga kai ya kalleta ba.
Dai dai lokacin wayarsa da ke gefensa ta ɗauki ruri, da sauri ya janyo wayar ganin sunan kawu mahmud ya fito a allon wayar ta sa ya faɗar masa da gaba ƙwarai da gaske, cikin mutuwa da sanyin jiki ya ɗaga wayar, “Musaddiƙ ina fatan dai lafiya?, kun daɗe baka dawo ba gashi kuma likita na buƙatar ku”, cewar mallam Mahmud, Musaddiƙ ya yi ƙoƙarin daidaita muryarsa yace “wani aiki ne ya taso ma Haj sai muka wuce wajen amma yanzun nan zan dawo”, mallam Mahmud yace “Babu laifi, sai kun dawo”.
Ya na aje wayar ya tashi da sauri, ya nufi ƙofar fita, ba tare da ya jiyo ya dubeta ba yake yi mata bayanin ya tafi asibiti, a hankali ta dakatar da shi, ya tsaya ba tare da ya juyo ba, ta tako har gabansa ta janyo hannunsa ta ɗora masa makullin motarta tace “ka tafi da motata, duk kuma abinda ake ciki ka sanar da ni ta waya”, babu musu ya damƙe makullin motar ya fice ba tare da yace uffan ba.
Murmushi kawai ta yi ta faɗa a fili “zaka saba da ni ne, duk wannan fushin zaka daina ne, domin ni na riga na ga waje, bana jin kuma akwai abinda zai nisanta ni da kai, in dai akanka ne ba zan taɓa yin fushi ba”.
Hakanan bayan fitarsa ya dinga jin muzanta, su kansu masu gadin su biyu Musaddiƙ ya kasa haɗa ido da su, domin gani yake kamar sun san abinda ya aikata, har ya kai asibitin haka yake jin kansa, domin su ma su Inna Halima babu wanda ya yarda ya haɗa ido da shi. Kai tsaye da shi da mallam Mahmud suka wuce ofishin likita, inda likitan ya yi musu bayanin sun gama duk gwaje gwajensu jikin Afrah kuma zai iya ɗaukar aikin, sannan abu mafi dasa farinciki shi ne yadda aka yi sa’ar samun ƙodar da ta yi dai dai da ta Afrah, ba sai an sha wahalar jiran a sami wata ba.
Hakan yasa likitan ya tabbatar da cewa gobe ƙarfe takwas na safe za’a shiga da Afrah aikin, don haka suna buƙatar a gaggauta biyan kuɗin aikin, likitan ya miƙo ma Musaddiƙ wata takarda mai ɗauke da bayanin komai da adadin kuɗin da ake buƙata sannan da inda za’asa hannu wanda zai tabbatar da sun amince ayi aikin, sannan kuma duk abinda ya biyo baya babu laifin hukumar asibitin.
A sanyaye Musaddiƙ ya amshi takardar, likita ya ɗan dube shi yace “Akwai account number a jiki ta nan zaku tura kuɗin”, Musaddiƙ ya jinjina kai yace “In sha Allah za’asa kuɗin yau”, ya ɗan ƙara kallon likitan yace “Amma dai babu wata matsala ko”, ya yi ɗan murnushi gami da gyara zaman gilashi a fuskarsa yace “kada ku damu, munyi aikin da ya fi wannan hatsari ma kuma mun dace, don haka wannan ɗin ma babu wata matsala, duk da komai na Allah ne amma muna da yaƙini mai kyau”. Cikin ƙarfafa guiwa musaddiƙ ya jinjina kai sannan suka fice tare da mallam Mahmud.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya kira Haj Hudah ya sanar da ita buƙatar likita, take ta umarce shi da ya tura mata account number ɗin, ya na tura mata ta sanya kuɗin a ciki ba tare da ɓata lokaci ba.Haka aka dinga kaiwa da komowa har sai da aka kammala duk wani shiri.
Sai dai har akayi komai aka gama haka musaddiƙ yake tamkar mara lafiya, babu karsaahi babu walwala babu farinciki ko ɗaya akan fuskarsa. Haka Inna Halima ke binsa da kallo tana tausaya masa tana jin kuma in sha Allah komai ya zo ƙarshe, domin tasan daga sanda Afrah ta sami lafiya to shikenan zai samu kwanciyar hankali da natsuwa sai dai abinda bata sani ba shine ya riga yasa kansa cikin tashin hankalin da ko bayan samun lafiyar Afrah da yuwuwar zai cigaba da zama a cikin wannan halin. Idar da sallar issha’i musaddiƙ ya daɗe zaune cikin masallacin asibitin ya yi addu’a mai yawa akan Allah yasa ayi aikin a sa’a.
Yana fitowa wayar Haj Hudah tana shigowa cikin wayarsa, nan da nan ya ji wani irin baƙinciki ya cika zuciyarsa, a sanyaye ya ɗauka, ya yi mamakin maganar da take yi masa, ransa a ƙufule yace “ Haba Haj, wai kin manta ke matar aure ce, sannan kin manta ina da me jinya ne da take buƙatata kusa da ita a ko wane lokaci, ta yaya zan iya tsallake su kawu da Afrah na taho wajenki na kwana”, Haj Hudah ta muskuta tana jin tamkar ta janyo shi ta wayar, yadda muryarsa kawai ta ke tada mata sha’awa, tace “Idan akwai abinda na tsana a duniya bai wuce musu ba, ko kana tunanin tunda na biya kuɗin aikin matarka shikenan zaka iya juyawa alƙawarin mu baya, a’a kada ma ka fara yin wannan kuskuren, kuma maganar matarka idan ma ka zauna bata sani ba idan ma ba ka zauna ba bata sani ba, don haka banga amfanin damuwa ba, don ka kwana a wajena, su kuma su kawunka yanzun nan zan tura maka kuɗi shi ma ka je ka kama masa hotel ya samu ya kwanta ya huta”.
Rai a dagule yace “Bana tsammanin kawu zai je wani waje ya kwana bayan da safe za’a yi ma Afrah aiki”, ta ɗan numfasa tace “zai amince, idan kana kusa da shi ne ka haɗani da shi a wayar”, ya girgiza kai kamar tana ganinsa yace “Bama tare yanzu dai zan ƙarasa inda yake”, tace “Idan ka ƙarasa ka kira ni”, tana gama faɗin haka ta aje wayar ba tare da ta jira amsarsa ba.
Ataƙaice dai da kanta da Musaddiƙ ɗin ya haɗata da mallam mahmud a waya ta shawo kansa ya amince da zuwa hotel ya kwana, taba musaddiƙ umarnin ya ɗauke shi ya kai shi ya kwanta bayan ya aje shi sai ya wuto gidanta inda zasu kwana tare kamar yadda take buƙata.
Musaddiƙ ya daɗe gaban gadon Afrah yana ƙare mata kallo, yana ji a ransa ya ci amanarta, nan da nan idanunsa suka fara sakko da hawaye, yana dubarar sharewa domin baya son asan yana kukan, daga bisani ya amshi Hanan a hannun Inna Halima da ta gama bata madara kenan, nan ma ya daɗe yana kallon yarsa yana jin tamkar ya tsaga jikinsa ya sanyata ciki saboda ƙauna, kafin daga bisani ya miƙata gun Inna Halima gami da yi mata sai da safe suka fito tare da mallam Mahmud.
Yadda yanayinsa ya canja sosai mallam mahmud yq so ya yi masa magana, amma da yake yafi yarda da cewa damuwar aikin da za’a ma Afrah ne ke damunsa shi yasa ya yi shuru, illa addu’a da yake yi masa acikin zuciyarsa akan Allah ya sassauta masa damuwar da yake ciki. Har ya sauke shi a hotel tare da sanar da shi zai zo gobe da safe ya ɗauke shi zuwa asibitin, ya nuna masa shi ma a hotel ɗin zai kama ɗakin.
Daganan yana fitowa ya nufi gidan Haj Hudah, rai da zuciya ba haka suka so ba.A wannan daren dai Musaddiƙ ya wahala, domin ko na minti biyar Haj Hudah ba ta bari ya huta ba, duk ƙishin ruwanta sai da ta magance shi, duk wutar sha’awar musaddiƙ da ta daɗe ta na ci a cikin zuciyarta sai da ta kasheta, ta manta da matsayinta na matar aure, ta manta ta na da wani miji, musaddiƙ ta ke so shi take son kasancewa da shi, wannan daren jinta ta yi tamkar wata sabuwar amarya. Shi kam musaddiƙ babu komai a zuciyarsa sai nadama da danasani tun kafin aje ko’ina ya faɗa komar nadama ya fara tuhumar kansa, babu wani abu ɗaya da ke masa daɗi asalima jinsa ya ke tamkar ba shi ba.

Washegari Haj Hudah ta ƙara barinma Musaddiƙ motarta, tun ƙarfe bakwai ya isa ɗakin mallam mahmud tamkar da gaske a cikin hotel ɗin ya kwana, babu ɓata lokaci suka wuce asibitin.
Babu wani ɓata lokaci domin kuwa lokacin da likitoci suka ɗiba ya na cika aka shiga da Afrah ɗakin tiyata, hankalin kowa a tashe, kamar yadda bakunan su ke ɗauke da addu’o’i. Musamman Musaddiƙ da ya sami gefe ɗaya ya zauna ya rasa abinda ke masa daɗi duk inda ya juya babu daɗi. Ƙarfe tara da rabi Mansur, kabir, Na’ima da mama Hauwa suka iso asibitin daga minna a motar mansur ɗin. Haka suke zaune zaman jiran tsammani.
Har zuwa lokacin da aka fito da Afrah, babu wanda aka amincewa ya shiga keɓaɓɓan ɗakin da aka ajeta.
Sai dai Alhamdulillah likitocin sun tabbatar da cewa an sami nasarar aikin, wanda hakan shi ne ya dasa farinciki ga musaddiƙ har ya so ya manta da ƙalubalen da yake ciki na Haj Hudah. Kowa ka kalla yana cikin farinciki mara misaltuwa, sai yamma Haj Hudah ta zo asibitin ta ga Afrah, sai dai duk motsinta yana kan idon mama Hauwa, sosai take son ta fahimci abinda ke tsakaninta da musaddiƙ domin dai har yanzu ba ta yarda da irin alaƙar da ke tsakaninsu ba, don ko yanzu ita take ta wahala da kowa a asibitin tun daga kan abinda zasu ci har zuwa wajen kwanansu, hatta su mansur haka suke faɗan halin haj Hudah na ƙwarai suna jinjina mata irin wannan namijin ƙoƙarin da take yi, ita kam mama Hauwa ta ja bakinta ta yi gum don bata son ta furta abinda zai zamar mata ɗan zani a wajen mallam Mahmud, sai dai duk da haka ta rasa damuwar meye da har yanzu ta ke gani akan fuskar musaddiƙ bayan yanzu ne ya kamata aga farinciki da walwala a tare da shi, to ko ma dai meye idan tayi wari ma ji, cewar mama Hauwa a cikin zuciyarta.
Ƙarfe ɗayan dare ne amma har yanzu Alh yusuf sanda bai runtsa ba yana ta sintiri a tsakiyar ɗakin, gaba ɗaya ya kunna duka wutar ɗakin tamkar rana, idanunsa na kafe akan saƙon da Haj Hudah ta turo masa tun ƙarfe sha biyun daren saƙon ya shiga wayarsa zuwa lokacin ya karanta saƙon ya fi sau ɗari, ya rasa murna zaiyi ko baƙinciki, domin saƙon ya na tabbatar masa da cewa Haj Hudah ta sami biyan buƙatarta a wajen musaddiƙ shi yasa ba ta da buƙatar sa a yanzu kusa da ita kamar yadda suka rabu.
Ya ƙara kallon saƙon yana maimaita duk kalma ɗaya da ke rubuce.

“ ka yi haƙuri da abinda ya faru tsakanin mu kafin tafiyarka, na amince ka cigaba da kasuwancinka da ƙasashen waje kamar yadda ka saba, ba ni da damuwa akan hakan”.

Ya yi murmushi mai kama da yaƙe, ya koma ya zauna yana maida numfashi kamar wanda ya shiga gasar gudu, dai dai lokacin kiran ɗaya daga cikin masu gadin gidan Haj Hudah na nan Abujan ya shigo wayar Alh yusuf sanda, da sauri ya ɗauka “ ya ya ake ciki?” Ya tambaya murya na rawa, daga ɗaya ɓangaren a hankali kamar me raɗa yace “Har yanzu yana cikin gidan, da alama yauma a gidan zai ƙara kwana”, Alh yusuf sanda ya huro iska daga bakinsa cike da tsananin baƙinciki yace “To shikenan, za muyi magana gobe”, ya riga shi kashe wayar.
Wani irin tuƙuƙin tashin hankali ke nuƙurƙusar zuciyarsa, kishi da tsanar Haj Hudah ya ƙara cika zuciyarsa, lalle shi kansa yadda yake son kasancewar lamarin ba haka yake tafiya ba, ta ya ya musaddiƙ zai zaƙe, tabbas sai ya yi danasanin duk abu ɗaya da ya aikata na keta masa haddi, duk da hakan shine mahaɗin cikar burinsa, domin zai mallaki abinda yake so a ruwan sanyi tare da jefa rayuwar musaddiƙ cikin garari da tashin hankali, shi zai yi dariya musaddiƙ kuma zai yi kuka, domin sai ya yi nadamar haɗuwa da Haj Hudah sai ya yi nadamar saninta.
Ya ƙara yin murmushi yace a fili “ shirin da na daɗe ina yi ya kusa zuwa ƙarshe, zan sami cikar burina”, ya buga ƙafa a ƙasa yana wata irin dariya, yana faɗin kowa ya ci ladan kuturu sai ya yi masa aski, muna ji muna gani muna kuma saurare……………………….


Yar gidan Imam✍️
MUSABBABI BOOK 2

NA


HABIBA ABUBAKAR IMAM
(Mrs Aliyu Mayere)

Page 20


Aikin da akayi ma Afrah kamar yadda likitoci suka faɗa ya yi kyau sosai. Domin a cikin kwanaki uku kacal har Afrah tasan inda kanta yake, asalima a kwana na huɗu har ta fara ba Hanan nono, kwana biyu su mama Hauwa su kayi a abuja suka koma gida, har zuwa lokacin zuciyarta cike take da tababa gami da tantama akan alaƙar Haj Hudah da musaddiƙ, domin duk kwanakin da su kayi komai Haj Hudah ce ke yi musu, haka zalika a lokacin da Afrah ta farfaɗo Haj Hudah ta na asibitin sai dai mama Hauwa ta kasa gane dalilin razana da canjawar fuskarta a lokacin da ta dawo hayyacinta, yadda kowa ke murna tare da yi ma Allah godiya, ba ta ga haka a tare da Haj Hudah ba, hatta fara’ar da ta takurawa kanta take yi ta fi kama da yaƙe, ga idanunta sun kaɗa sunyi jawur.
Har mama Hauwa ta koma gida tana mirgina maganar a cikin zuciyarta, zuciyarta ta fara kitsa mata wani abu da sam ba ta son ta yarda da shi.
Shin me yasa mijin Haj Hudah ba ya zuwa baya kuma shiga sabgar musaddiƙ, bayan a yadda Haj Hudah ta ke nuna muhimmancin musaddiƙ ɗin a gareta ya kamata ace mijinta yasan da zamansa ko don kuma girman da ta ba musaddiƙ ɗin ya ci shi ma ya shigo cikin lamarinsa?.
Babu wanda zata tattauna maganar nan da shi domin daga mijinta har yayanta su mansur babu wanda zai fahimceta, hakan yasa ta ƙara jan bakinta ta tsuke.
Tun farfaɗowar Afrah musaddiƙ bai iya matsawa ko nan da can, hatta wayarsa saboda fitinar Haj Hudah kasheta ya yi ya aje kwata kwata baya buɗewa saboda baya son ta kira shi, hakan ko ya fi komai tayarma da Haj Hudah hankali tana ganin Musaddiƙ nema yake ya yi mata butulci saboda ya riga ya sami biyan buƙatarsa, wanda a ganinta wannan shine kuskure na ƙarshe da zaiyi a rayuwarsa, domin bai isa ba, zaiyi mamakinta, samun lafiyar Afrah ya zama tamkar barazana a gareta, amma a yadda ta ɗanɗani zumar musaddiƙ ba zata iya rabuwa da shi ba, idan kuma tunaninsa kenan shi na ya rabu da ita to bai isa ba.
Duk hanyar da zata bi don ta sami keɓewa da musaddiƙ hakan ya ci tura, tunda ya kawo mata motarta ya ba kuma masu gadinta makulli su ba ta, ya yi tafiyarsa ya koma asibiti.
Duk yadda ta so ta yi magana da shi hakan ya faskara domin ya riga ya kashe wayarsa,

Please Login or Register in order to submit comment