Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta na maida nunfashi daker, cikin rawar baki tace "Bansan waye ya tura maka wannan sakon ba, Bansan waye ya ke bibiyar mu ba da har yasan sirrin da mu ne kaɗai muka sani, ta yaya zan yi haka? Waye yake son haɗa mu, tabbas ina son na samu cikar burina a kanka amma bata wannan hanyar ba".
Ya miƙa hannu ya fisge wayar sa yace "Bata wannan hanyar ba?, Inace ke ce ki ka fara yi min irin wannan barazanar, sannan ke kadai ke da wannan vedion to ina wani zai same shi, waye zai yi wannan idan ba ke ba".

Ta daga hannu sama wannan karon kuka take yi sosai wanda ba ta san sanda ta fara yi ba.

Tace "Ka yarda da ni da magana ta babu abinda na sani......,..?".

Ya daga mata hannu yace "Ki je duk abinda za kiyi ina daidai da ke, sai dai ki sani yadda ki ke son sabauta rayuwata tabbas saina sabauta taki rayuwar sai na maida ke abin kwatance karshe kuma sai na shafe labarinki a doron kasa ".

Yana gama faɗin haka ya juya a fusace ya fice, cirko cirko ya tadda masu gadi da jami'an tsaron gidan duk hankalinsu na cikin gidan da alama duk abinda ke faruwa suna ji. Baibi takan kowa ba ya fice abinsa.
Firgita da gigita babu wanda Haj Hudah bata sami kanta ciki ba, gaba ɗaya zazzaɓinta ya dawo, jikinta ya dauki zafi, tambayar da ke kai kawo a cikin zuciyarta shine, waye ya haɗata da Musaddiq?, Waye ya mallaki sirrin da su kaɗai suka sani?, Waye yake ƙoƙarin rushe kwanciyar hankalin ta, bayan tashin hankalin da take ciki, tabbas baki shi ke yanka wuya,da bata fara ba babu wanda zai zo ya ƙarasa mata. Lalle tana cikin tsaka me wuya, ta na cikin tashin hankali idan wannan vedion ya yadu ina zata sa kanta?, Shin ta yaya zata gano wanda yayi mata wannan makarkashiyar, sannan me yasa ya tunkari Musaddiq bai tunkareta ba don idan don kuɗi ya yi ita ya kamata ya fara nema don itace take da abinda zata bashi ba ba Musaddiq ba.

A haka ta kira duka hadiman gidan da masu gadi ta tabbatar musu duk abinda ya faru tsakanin ta da Musaddiq yanzu duk wanda ya fita da maganar to a bakin aikinsa. Hakan yasa su ka ƙara tabbatar da cewa lamarin babba ne, sannan irin furucin da Musaddiq ya yi ya na da girma da yawa abin a dauki mataki ne, amma tunda tace abar maganar dole suka barta.
Sai dai saminu da kansa ya kira Alh Yusuf sanda ya tabbatar masa da hakkinsa ya fara taɓa Musaddiq da Haj Hudah domin yadda yau su kayi uwar watsi da juna, saminu yace ina rokon Allah yasa ƙarshen tarayyar su kenan. Cikin wata muguwar dariya, Alh Yusuf sanda ya kashe wayar.
Yana Kada Kafa yana jin mataki na farko ya samu kammaluwa cikin nasara.
Haj Hudah ta faɗa cikin matsanancin tashin hankali da damuwa burinta ta gano wanda ke cin dunduniyarta.

Kamar yadda Musaddiq ya ke cikin tasa damuwar har ya koma gida. Sam damuwarsa a yau ta ƙasa boyuwa, ta ya ya Haj Hudah zata raina masa wayau tace wai ba ita tasa a tura vedion ba?, Kiri kiri ta na son ta kashe masa rayuwa, babu mafi girman nadama da yake yi a rayuwa irin nadamar haduwarsa da Haj Hudah.
Ita kanta Afrah ta gane ya na cikin damuwar da ta tsani ganinsa cikinta.Bayan ta kwantar da Hanan ne ta dawo kujerar da yake kishingide a kai, ta kama hannayensa duka biyun ta rike tana kallonsa hakanne yasa shi ma ya tattara hankalinsa a kanta, lokaci ɗaya kuma ya na ƙoƙarin boye damuwarsa.
Ya ɗan daga mata gira yace "Ya ya dai?". Ta yi taushi da muryarta tace "Ba na son ganinka cikin damuwa, domin na kanga kamar na gaza ne wajen sanyaka farinciki, bayan ni kuma kullum burina bai wuce ganinka cikin farin ciki ba domin ta haka ne kaɗai nake samun natsuwa, yanzu dai gaya min menene ya sanyaka cikin damuwa?".
Musaddiq ya zuba mata ido, sonta na ƙara kama zuciyarsa, ya na jin a wannan dare tamkar ya sanar da Afrah komai, ya na jin yau kamar ya saukema kansa mugun nauyin da ke kansa, sai dai kuma idanun Afrah suna yi masa kwarjinin da bazai iya yin hakan ba.
Shi ma ya riƙe hannunta kam! Yana ɗan murmushi yace "Me yasa ko na boye damuwata sai kin gane?", Ta yi ɗan murmushi tace "saboda kaunar da ke tsakanin mu,da kuma yadda zuciyoyin mu su ke da alaka da juna, hakanne yasa nake jin damuwarka ko da ba ka furta ba, nake kuma fahimtar damuwarka ko da ka boye min". Ya kama karan hancinta ya ja kaɗan sannan yace "madallah da samun mata irinki", ta yi murmushi tace "Yanzu dai gaya min damuwarka, menene ke damunka, daga shago ne ko daga mutanen da ka ke mu'amala da su?". Ya girgiza kai yace "Babu ko ɗaya matata, kawai dai dabi'a ce irin ta ɗan Adam musulmi, ka kan sami kanka wani lokacin da jin damuwa da shiga kunci hakanan ko da babu abinda akayi maka, to irin hakane na sami kaina ciki".
Afrah tace "mun godewa Allah da kasancewar mu cikin musulunci, kuma wannan halin sai musulmin kwarai ne ke shiga irinsa, saboda haka da Zarian ka sami kanka cikin wannan halin sai ka yi ta maimaita Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, da ikon Allah zaka sami sauki". Ya yi mata wani kyakkyawan kallo gami da kwantar da kanta a kan kirjinsa yana shafa gadon bayanta, yace "Nagode Allah ya yi Miki albarka",itama lamau ta yi a kirjin nasa tana jin yadda kaunarsa ke ƙara kama zuciyarta.
Zuciyar Musaddiq ta bushe ya na jin matukar nadama agame da duk abinda ya aikata, haka zalika ji ya yi yana fatan Allah ya rufa masa asiri a wajen Afrah domin duk sanda wannan maganar ta fito baisan da wane ido zai kalleta ba yadda take mutunta shi tare da ganin girmansa baya fatan wani abu ya bayyana wanda girman nasa zai zube, karo da dama ya ji ya tsani kansa, ya kuma kara yin dammarar yaki da Haj Hudah ko da hakan zai haifar da faruwar abubuwa masu muni.

Lalle kuwa akwai abubuwan da zasu faru masu munin, muje zuwa dai.............

Yar Gidan Imam ✍️
https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk

Yar Gidan Imam Empire karshen zance kenan wajen sayayyar ko wane nau'i na kaya cikin aminci da rahusa.ku shigo domin yin sayayya cikin aminci.

MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
(Mrs Aliyu mayere)

Page 25

Tun faruwar abinda ya faru tsakanin Haj Hudah da Musaddiq,ta rasa dukkan wani farinciki da natsuwarta, tunaninta ya yi nisa hankalinta ya fara gushewa, burinta ta gano wanda ya mallaki wannan vedion bayan ita, burinta ta gane wanda yake bibiyar rayuwarta ba tare da cikakken saninta ba, domin ta hakane zata san matakin da zata dauka domin kare kanta daga sharrin koma waye, sannan ta hakane zata tabbatar ma da Musaddiq gaskiyar ta da ya kasa gasgatawa ya kuma kullaceta akan hakan, yadda har yanzu ya hanata dama da lokacin da zai saurareta domin ta wanke kanta, domin dai tun barinsa gidanta take kiran waysrsa kullum amma baya ɗauka duk kuma sakon da take tura masa babu ɗaya da ya taɓa bata amsa, wannan dalilin ne ya ƙara jefata cikin damuwa duk da ta ji saukin zazzaɓin da ta kira zazzaɓin damuwa to fa yanzu zuciyarta ce ta kamu da zazzaɓin.
Har gidan su Musaddiq ta je amma sabon maigadin da ta gani ya tabbatar mata da cewa yanzu gidan ba mallakin su Musaddiq ba ne sun kwana biyu da tashi, wannan maganar ta fi komai tayar da hankalin Haj Hudah,ta fahimci da gaske Musaddiq so yake ya barta, bayan ita da gaske zuciyarta take zata kashe aurenta saboda shi, domin a yanzu ne ma ta ji ba ta bukatar zama da Alh Yusuf sanda domin ta yi imani da cewa duk halakar da ta shiga akwai sa hannunsa a ciki, don da ya so ta ya nuna mata kulawa da damuwa bata jin akwai wani gurbi da zata ba wani namijin da ba muharraminta ba a cikin zuciyarta har kuma ta faɗa irin wannan masifar. Don haka zama da shi hakika ba alheri ba ne a gareta.
Tabbas zata cigaba da farautar duk wanda ke da hannu wajen nakasar da alakarta da Musaddiq ko da hakan na nufin salwantar komai na ta ne.
Daga kuma lokacin da ta gane komai to alokacin zata hutasshe da zuciyarta daga dukkan matsala da damuwar da ke neman kaita ƙasa,zata haƙura da auren mijinta zata cigaba da bi gami da addu'ar Allah ya mallaka mata Musaddiq a matsayin mijinta.
Tabangaren Musaddiq kuwa duk da ya nisanci Haj Hudah to fa kullum cikin tunani da fargabar abinda zai iya biyo baya yake, sannan sau tari ya na mamakin yadda bai kara ji daga number da ta tura masa vedion ba asalima ya fahimci number ta yi blocking dinsa domin kuwa ko ya tura magana bai shiga , sannan ya kira number babu adadi amma ana cewa number ma ba ta aiki kwata kwata,
Sau tari ya na mamakin yadda har yanzu wanda ya turo vedio bai ƙaddamar da aikin da yace an sa shi ba, wanda zuwa yanzu ya ci ace ya yi abinda yake ikirarin zai yi din, shin ko dai da gaske babu sa hannun Haj Hudah a cikin maganar?, Ko kuwa kawai anyi hakan ne don a jefa damuwa da tashin hankali gami da rashin natsuwa a tare da shi.
Wanda idan hakanne kuma sunyi nasara domin kullum haka yake fita gida ya kuma dawo cikin fargaba da zullumin ko Afrah ta sami sakon, shi yasa yake addu'ar Allah ya tafi masa da tsaro da fargabarsa ya samu ya zauna da matarsa ya gaya mata gaskiyar lamari.

Ita kanta Afrah, ta sami natsuwa saboda ako yaushe Musaddiq na nuna mata yana cikin farin ciki da kwanciyar hankali ba shi da wata damuwa, amma kuma a can ƙasan zuciyarta ta na jin ta kasa gasgsta hakan tana jin akwai wani gagarumin abin da ya ke boye mata baya son ta sani.
Sai dai tunda ta fahimci baison ta sani ko ya gaya mata yasa ta bi da shi a yadda yake so wato ta watsar da komai sai dai kullum cikin addu'a take akan koma menene Allah ya yi masa maganin damuwar sa. Take kuma nuna masa tana cikin farin ciki itama.
Gefe ɗaya kuma kasuwancinta sai kara haɓaka yake saboda yanzu har gidanta an gane kai tsaye mata ke zuwa sayayya, haka a makaranta kowa ya san ta akan kasuwancinta akan nemeta ayi mata ciniki, masu biki sukan bata kwangilar kawo musu anko, haka akan bata kwangilar cika kicin din amarya da kayan kicin, sannan ta online ma duk tana sayar da kaya, nan da nan Allah yasa mata albarka ta fara sanuwa cikin kankanin lokaci ta fara kama kuɗaɗe masu kauri,wanda kullum take kokarin sanya mahaifinta da Inna Halima farinciki.
Wannan cigaba kuwa da ya sameta mama Hauwa ji ta ke kamar ta hadiyi zuciya ta mutu, a duk lokacin da Afrah ta aiko ma mahaifinta da kaji sai dai Na'ima ta dafa masa, domin kuwa a yanzu Na'ima ta sakko neman hanyar da zata sami miji ta yi aurenta tabar gaban Mama Hauwa kawai take yi, wacce kullum suke cikin faɗa alamar kowa ya gaji da kowa.
Ba ta da yadda zata yi domin hakika a yanzu ta fara tabbatar da cewa Afrah kainuwa ce dashen Allah akwai nasibi a cikin rayuwarta, idan kuma hakane to tabbas sai dai baƙin ciki ya kasheta.

Shi kansa Musaddiq ɗin babu abinda yake gani sai budi, fargaba dai taki barinsa kullum kamar wani girgitacce, haka zalika duk yawan kiran da Haj Hudah ke yi masa har yanzu bai ɗauka ba,duk da zuciyarsa na raya masa ya ɗauka ya ji abinda zata gaya masa.sai dai a wannan lokacin sai Haj Hudah ta lafa daga kiran da take masa, hakan ya faranta ransa yana tsammanin ko ta aro zuciyar masu zuciya ne ta ɗora a kirjinta, sai dai abinda bai sani ba shi ne bata daina kiransa don baya dagawa ba ko don ta daina sonsa ba, a'a ta daina kiransa ne saboda tana son sai ta samo shaida ta kuma binciko gaskiyar komai sannan ta tunkare shi domin wanke kanta don tabbas a irin fusatar da Musaddiq ya yi tasan matukar ba da shaida ta je masa ba babu yadda za'ayi ya saurareta, wanda hakan yafi komai tayar da hankalin ta, bincike take me zafi ta karkashin kasa ba tare da sanin kowa ba.

Ranar wata Laraba , wacce ta zamo ranar tashin hankali, ƙarin nadama da danasani, ranar da Musaddiq da duk wani masoyinsa bazai taba mantawa da ita ba,
Ranar da idan aka Kirata da bak'ar rana ga Musaddiq ba'a yi kuskure ba,domin ranar itace musabbabin canjawa da fadawar Musaddiq wata irin ukubar da babu zato babu kuma tsammani.
Tun wayewar garin ranar ya samu kansa da faduwar gaba da fargaba , wanda ya rasa dalili, haka zalika a ranar Gaban ta tashi da zazzaɓi me zafi, Afrah na ta hidimar ta, an bata magunguna da zasu taimaka wajen lafar da zazzaɓin na ta, sai dai duk da haka waje ya samu ya yi zamansa yana rike da Hanan baida niyyar zuwa shago,Afrah da kanta take rokonsa ya tafi shago tunda ta ɗan fara jin sauki, amma ya ki, dole ta haƙura ta kyale shi.
Karfe goma da rabi Murtala ya kira shi a gaggauce yake sanar da shi ya aje duk abinda yake yi ya wuce kamfani sunansa ya fito a cikin wadanda za'a yi ma tambayoyi kuma yanzu haka har an fara shi ma yanzu ake kiransa cewa ba'a ga Musaddiq ɗin a wajen ba.
Cikin faɗa kuma yake tambayar sa me yasa baya duba email dinsa, domin tun kusan mako ɗaya baya aka ce an turawa duk wanda ya cancanta takardar gayyata.
Jikin Musaddiq a sanyaye yake bashi hakuri kan cewa baisan abinda ya dauke masa hankali ba.
Murtala yace "Ka canja da yawa Musaddiq babu wani abu mai muhimmanci a gabanka,gaba ɗaya ka zama wani iri,hatta shagon ma ba ka maida hankali akansa,zuwa nayi shagon na tadda kai cikin tunani da tagayyara kuma abin haushi baka son faɗan matsalarka balle a taimaka maka ko da da shawara ne", sauri Musaddiq ya yi ya kauda maganar da Murtala ke yi domin baya son Afrah ta ji abinda yake faɗa,"kabar wannan maganar gani nan dai tahowa yanzu in sha Allah".
Kafin yace komai ya aje wayar, ya mikama Afrah Hanan ya na yi mata bayani, nan da nan ta shiga masa addu'a tare da fatan nasara,har kofar get ta yi masa rakiya, yana fita kuwa ya sami mai adaidaita sahu yayi shata zuwa kamfanin.
Ya tadda mutane ba lefi duk da layin ya ja.
Amma sai kusan karfe goma sha biyu aka zo kansa.Bai wani jima a ciki ba saboda duk tambayoyin da aka masa ya san amsarsu ya kuma ba su amsa kamar yadda Yakamata.karfe ɗaya da minti biyar ya fito sosai yake ji a ransa in dai amsa waɗannan tambayoyin ne zaisa a bashi aiki to tabbas ya fara hango kanshi a matsayin ma'aikacin kamfanin, ya yi ma Allah godiya.

Yana gefen hanya ya na jiran adaidaita sahu ne, wayar Haj Hudah ta fara shigowa cikin wayarsa, ya dade ya na kallon wayar ya na tuna rabon da ta kira shi, ya so yaƙi daukar wayar amma yadda ta nace da kira ya fara canja masa ra'ayi ya na jin kamar ya dauka bayan ya ji dalilin kiran da ta yi masa sai ya yi mata mummunan kashedin ta fita daga rayuwarsa.
Sai dai hakanan ya ji a duk lokacin da ya yi yunkurin daga wayar sai ya ji gabansa ya fadi. Ta kira ba adadi da yake rabon wahala ya ratsa masa ji ya yi tamkar an hankada hannunsa ya danna cikin sanyin jiki ya kara a kunnansa, dai dai lokacin mai adaidaita ya tsaya Musaddiq ya faɗa ciki.

Cak! Ya ji numfashinsa ya harba da karfi a dalilin jin Muryar Haj Hudah a cikin wani irin yanayi da bai taɓa ji ba, cikin karaji da haki gami da rawar murya take faɗin "Musaddiq ka ceci rayuwata duk inda ka ke ka zo ka same ni a martaba hotel kayi sauri ka zo rayuwata ta na cikin garari" , a daburce yace "menene ke faruwa,na ji muryarka na rawa me ke faruwa?".
Cikin shakewar murya tace "Ba ni da lokacin batawa Musaddiq idan ba kayi saurin zuwa ba komai ya na iya faruwa da ni,ka sani ina cikin mummunan yanayi, ka yi sauri ina daki me lamba talatin da shida,babu abinda zan gaya maka a waya"..... Zai yi magana kenan ta cigaba da cewa "Rayuwata ta na cikin siradi Musaddiq kai kaɗai zan iya gaya ma gararin da nake ciki, kafin na samu shawarar yadda zanyi, na rokeka ka aje duk abinda ke zuciyarka a kaina, ka taho na samu damar wanke kaina domin na gano komai na tun daga kan me yi maka barazana da vedio zuwa wanda ke farautar rayuwa ta...........

Kit!, Ya ji wayar ta katse a daburce ya cigaba da danna nambar amma sai ya ji ta akashe, jikinsa ya kara yin sanyi da gaske rayuwar Haj Hudah na cikin tsaka me wuya.
A gaggauce ya dubi dureban a daidaita sahun ya ce "wuce da ni martaba hotel".
Ji yake kamar ya rufe ido ya bude ya gan shi a cikin hotel ɗin saboda kaguwa.
Hakan yasa suna isa ko canji bai tsaya karba ba ya wuce ciki da saurin gaske. Har ya na bangaje ɗaya daga cikin ma'aikatan amma bai ko tsaya ba ya wuce da sauri hakan yasa mutumin ya bi shi da kallon mamaki.yana nazarin firgici da tashin hankalin da ya gani a saman kuncinsa.
Ko a reception bai wani tsaya tambaya ba tunda ya riga yasan nambar dakin . Sai dai a yanayin da yake ciki yasa ma'aikatan da ke reception din suka bi shi da kallon har ya bacema ganinsu.

Kai tsaye jerin dakunan ya bi yana duba ko wace lamba, har ya zo lamba talatin da shida, cike da fargaba ya fara buga dakin, amma ba amsa, daga bisani ya murda hannun kofar,ga mamakinsa kawai sai ya ga kofar ta buɗe.
Ya yi saurin waigawa bayansa da gefen sa amma babu kowa, don haka kai tsaye ya tura kansa ciki ya na kiran sunanta a hankali cikin tsoro. A hankali yake taka cikin dakin yana kokarin karewa dakin kallo ko zai hango Haj Hudah ciki.
Ƙafarsa ce ta yi kwallo da wani kofi karar kofin ya kara firgita shi, a hankali ya kai hannu wajen makunnin wutar dakin ya kunna nan da nan haske ya wadaci dakin. Daganan ya dawo da kallonsa cikin dakin.
Tun daga kan gado har kasan dakin anyi biji biji da shi alamun kamar anyi dambe a dakin, har yanzu kiran sunanta yake yana kuma zagaye dakin.
Nan da nan Ya ji numfashinsa ya fara wahalar fita, wani irin matsanancin tsoro ya bayyana a gare shi, duk inda jikinsa yake rawa ya ke yawun bakinsa ya kafe, duk a dalilin ganin Haj Hudah kwance a kasa a gefen gado cikinta dauke da wuka wacce a ka burburma mata waje da yawa,

A sukwane ya zube a gabanta cikin matsanancin tashin hankali mara misaltuwa.yake kiran sunanta gami da girgizata, duk ya fita hayyacinsa ya rasa a wace duniya ya ke, ya rasa tunanin da zai yi domin gaba ɗaya kansa ya kulle, komai ya tsaya masa cak.
Dukkan alamun mutuwa sun gama bayyana a gareta,da ƙarfi yasa hannu ya fincike wukar da ke cake kan cikinta.yana cigaba da kiran sunanta.

Yana cikin wannan halin ne dai dai lokacin,bai ankara ba, ya jiyo murya da hayaniyar mutane, a kusa da Kofar dakin, wata murya ke fadin "wannan shi ne lambar dakin da aka sanar da mu", wata murya tace "Amma kuma kamar babu wani alamun faruwar wani ta'addanci a nan, domin idan hakane mu jami'an hotel din mu zamu fara sani kafin akai ga hukumar yansanda, wannan kuma dakin da yar majalisa Haj Hudah Yunus ta kama ne babu dadewa sosai na uni daya kaɗai, da alama meating zata gabatar domin ita kaɗai ta shigo bayan ita kuma babu wanda ya shigo nemanta.
Cikin Musaddiq ya ba da kululululu!!!, Matsanancin tsoro ya sake lullube shi sai yanzu ya gano irin dimbin hatsarin da yake ciki.
"To zamu shiga domin yin bincike domin dai mun sami kiran waya da tabbacin akwai ta'addacin da ya faru, kamar yadda muka yi muku bayani shi ne dalilin zuwan mu".
Gaba daya Musaddiq ji ya yi ya na neman sankarewa, ya rasa abinda Yakamata ya yi saboda rudewa, har zuwa lokacin da ya ji an turo kofar an shigo suna fadin "Ai kofar ma a bude take".

Yansanda da manajan hotel din suna shigowa cikin dakin, cike da gigita Musaddiq ya mike ya daga hannunsa sama yana girgiza kai amma bakinsa ya kasa furta komai.

Cikin daka tsawa insifekta Nura yace " you are under arrest" daya daga cikin yansandan ya wuto da sauri ya fito da farin kyalle ya yi kan Musaddiq zai karbi wukar hannunsa, sai alokacin Musaddiq ya tuna ashe har yanzu hannunsa na rike da wukar, ananne ya sami damar yin magana cikin rawar murya
"Ban san komai akai ba, na rantse ba ni na aikata hakan a gareta ba,ni ma haka na shigo na ganta.........
Bai karasa faɗan abinda yake son faɗa ba kawai ya ji yansandan sun rufe shi da duka ko ta ko'ina, har sai da suka kai shi ƙasa, tun yana iya kare dukan da hannunsa, har ya rasa karfin da zai daga ko da ɗan yatsansa ne.

Sai da suka tabbatar da ya galabaita yadda musun cewa ba shi ya aikata ba ma bazai iya yi ba, sannan suka buga masa ankwa a hannu, sannan suka fito da shi. Wanda hayaniya tasa sauran jama'ar hotel din su kayi dafifi, suna kallon Musaddiq waɗanda su kaga a yanayin da ya shigo hotel din dazu suka fara faɗan dama abinda ya zo yi kenan dubunsa ta cika aka kama shi, wace irin bakar zuciya ce wannan da zaisa mutum ya yi kisan kai. Sai yi masa tofin Allah tsine jama'a ke yi, haka aka jefa shi a motar yansandan, mutum uku suka tsaya da shi. A yayinda guda biyu suka koma kan Haj Hudah suna jiran amblulance din asibiti ta karaso da suka riga suka Kirata........................


To ga Musaddiq dai a cikin wani tsaka me wuyan.

KARSHEN MUSABBABI NA BIYU KENAN RANAR LITININ ZAMU DORA CIGABANSA 3 inda zaku ji yadda zata kaya.


Yar Gidan Imam✍️




An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da

Please Login or Register in order to submit comment