Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

siraɗin Hudah a lokaci ɗaya ba, haka zalika ban taɓa zaton akwai namijin da zai ƙi karɓan tayin Hudah ba a rana ta farko, nayi zaton a duk ranar da Hudah ta nemi musaddiƙ da irin wannan maganar ba zai bijire duk da na fahimci itama ta tanadi makaman yaƙinta , a yadda kuma na san Hudah da kafiya da naci to ba zata haƙura ba har sai ta cimma burinta, ni kuma cikar burinta akan musaddiƙ shi ne cikar burina akanta”.
Ya koma ya zauna yana girgiza ƙafafu yana wata irin muguwar dariya.

Ta ɓangaren Haj Hudah kuwa Musaddiƙ ya na fita ta tashi tana jin tamkar zata yi hauka, yau duk mutunci da kwarjinin da take da shi a wajen Musaddiƙ ya manta shi ne har yana tureta, kuma a haka yake tsammanin ta haƙura da shi bayan ta gama asarar duka mutuncinta a gunsa, ko kaɗan bata taɓa tsammanin zai yi mata haka ba, kan kujera ta faɗa ta na watsar da numfashin tashin hankali, kwata kwata duk maganganun da Musaddiƙ ya gaya mata babu kalma ko ɗaya da ta nuna alamun zaisa ta sauka daga dogon ƙudurinta, dole ta mallaki Musaddiƙ komai runtsi komai wuya, domin ta yi nisan da ba ta jin kira in dai akan Musaddiƙ ne, ta sha alwashin sai ya dawo gareta in dai ta amsa sunan Hudah. Sannan tana da yaƙinin cewa irin son da Musaddiƙ yake ma Afrah in dai akanta ne babu abinda ba zai iya aikatawa ba, ta kuma yi imani da cewa a cikin irin wannan tsananin rayuwar da ake ciki babu wani mutum ɗaya da zai iya taimakama da Musaddiƙ kuɗin da zai kula da lafiyar Afrah.
Ta yi wani murmushi tace “ Dole sai ka dawo gare ni domin ni kaɗaice zan iya ba ka kuɗin da zasu isa share hawayen ka, hawaye ya zubo mata, “ Ina sonka Musaddiƙ, Ina sonka Musaddiƙ”, abinda bakinta yake furtawa kenan, lokaci ɗaya kuma kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata.

Musaddiƙ ji yake duk abinda ya faru tamkar mafarki, cikin matuƙar tashin hankali da damuwa ya ƙarasa asibitin, shi ma ɗin ya ƙasa shiga ciki kujera ya samu ya haɗa kai da guiwa, gabansa na matuƙar faɗuwa, gaskiya ne tun farko ya yi kuskuren yin aiki a ƙarƙashin macen da ba muharramarsa ba, shi yasa shaiɗan ya yi tasiri a zuciyarta, me yasa Haj Hudah ta kasa jurewa ta yaƙi zuciyarta tun kafin ta yi masa wannan maganar, bayan ta fi kowa sanin irin yadda yake ganin kima da mutuncinta, wanda a yanzu babu komai face tsana da ƙyamatar halinta, gaba ɗaya mutuncinta ya gama zubewa.
“ shin ina zan samo kuɗin da zan kula da Afrah?”.
Tambayar da yake yi ma kansa kenan, gaba ɗaya ya zama wani abin tausayi, hawayen da yake ta ƙoƙarin fita masa ya barshi ya zubo, ya yi kuka sosai domin shi kaɗai yasan halin da yake ciki a wannan lokacin na damuwa.
Wannan shine karo na farko da ya ji ya samu damuwa a dalilin salwantar dukiyar sa a dalilin Haj kilishi, ba don haka ba da tuni zuwa wannan lokacin yana ƙasar waje tare da Afrah domin nemar mata magani.
Shin idan ya rasa Afrah ya zaiyi a rayuwarsa?”.
Dai dai lokacin kiran Inna Halima ya shigo cikin wayarsa, da sauri ya ɗauka inna Halima tace “ ka bari sai goben zaka dawo ne?”.
Ya yi saurin girgiza kai kamar tana ganinsa yace “A’a Inna ina ma cikin asibitin yanzu zan shigo ɗakin”, babu amfanin ta yi masa faɗan rashin ba kansa hutu da yake yi, domin tasan bazai taɓa ji ba balle ya yi hakan. Ya goge hawayensa ya tattaro dukkan natsuwarsa, gami da ƙoƙarin ɓoye damuwarsa sannan ya nufi ɗakin.
Ya tadda an cire oxcigine ɗin fuskar Afrah, da sauri har yana tuntuɓe ya ƙarasa bakin gadon ya ja hannunta ya riƙe a hankali ta buɗe idanunta da suka rine su kayi jawur kallo ɗaya zaka yi mata ka gamsu da cewa ta na cikin matuƙar galabaita.
Musaddiƙ ya cika da fara’a tuni ya nemi damuwarsa ya rasa, ya waiga yana kallon Inna Halima da take tsaye a kansu tana murmushi, yace “ Inna yaushe suka cire mata oxcigine ɗin?” Inna Halima tace “ Ba’a daɗe ba, likitoci sun shigo sun duba ta shi ne suka cire mata zuwa ɗan wani lokaci su ga ko numfashin zai dinga fita dai dai ba tare da taimakon robar ba”, ya dawo da kallonsa kanta ya matse hannunta sosai yace “ sannu Afrah, ciwon akwai zafi sosai ko?”, a hankali ta mirgina kai, don ba zata iya magana ba, sai dai idanunta babu abinda suke bayyanarwa face
Tsananin tausayin mijinta, ta na jin tausayin kanta tana jin tausayin musaddiƙ don yadda taga nan da nan ya rame ya fita hayyacinsa.
Ta maida idanunta ta rufe, da sauri Musaddiƙ ya ƙara matsantarta yace “Buɗe idonki Afrah, buɗe su don Allah” daurewa ta yi ta ƙara buɗe idon gaba ɗaya suka zubama junansu ido, a hankali Inna Halima ta juya tana sharar hawaye cike da tausayinsu ta fice daga ɗakin.
Tana fita gaba ɗaya sai ya kwantar da jikinsa a kan Afrah yadda ba zai ɗora mata nauyin jikinsa ba, ya rungumeta gaba ɗaya kuka su ke yi, cikin nauyin murya yake faɗin “Afrah ki yi haƙuri, mu ɗauki wannan a matsayin jarafta, Allah zai ba ki lafiya domin ya na sane da ke, shi kuma zai duba ki”, Inna Halima ta barsu sun sami sakewa da juna sosai, daga bisani ta dawo ɗakin, wanda ya dawo da musaddiƙ hayyacinsa ya matsa daga jikin Afrah, wacce da ace zata iya buɗe baki ta yi magana da ta tambaye shi dalilin damuwarsa domin kuwa ta gani acikin idanunsa ta kuma tabbatar bayan damuwar ciwonta akwai sauran wata damuwar a tare da shi, a hankali Inna Halima ta miƙo masa takardar magani tace “ Ga takardar magani nan da zasu fita suka ce a sayo zuwa gobe da safe”.
Gabansa ya faɗi sosai ya na addu’ar Allah yasa ba irin allurar da ake mata ba ne tunda suka zo asibitin, me shegen tsadar tsiya, jiki a sanyaye ya karɓa, ya ƙurama takardar ido ya na jin gabansa na matuƙar bugawa yana jin gaba da baya nera dubu biyu ya rage masa a cikin aljihunsa. Inna Halima ta ɗan dube shi cike da tausayi tace “Allah ya ba da yadda za’ayi “, ya amsa da “ Amin ya Allah”, ta ƙara kallonsa tace “ Ga koko nan da Yaya Mahmud ya kawo bayan fitarka, an ba Afrah ta robar ba da abinci, kaga da duminsa ka samu ko shi kasa, don nasan duk tsawon ranar nan zuwa wannan daren ba ka ci komai ba”, zaiyi magana kenan wayarsa ta ɗauki ƙara da sauri ya duba mai kiransa, gabansa ne ya faɗi a lokacin da ya ga number Haj Huda, me kuma take nema? Me take so daga gare ni?”, abinda ya faɗa kenan a cikin zuciyarsa.
Ya maida wayar cikin aljihunsa cike da zafin zuciya, tana katsewa ta ƙara carkewa da ƙara, itace dai ta ƙara kira a silet ya jefa wayar, lokaci ɗaya ya miƙe da nufin fita, Inna Halima ta yi sauri tace “Don Allah Musaddiƙ kasa wani abu a cikinka, ka daina ƙara min damuwa”.
Yadda ta yi ƙasa da murya alamun kuka yasa musaddiƙ ya yi saurin cewa “ba ni kokon Inna”.
Da sauri ta ɗakko kofi ta zuba ta miƙa masa, haka ya dinga sha kamar yana shan guba, don dai kawai ya faranta ran Inna Halima yasa ya shanye kokon.
Ya waiwaya ya na duban Afrah da tuni ta koma bacci.
Kamar wanda aka tsikara ya tashi, Inna Halima ta dube shi tace “ Ina zaka”, yace “ zanje neman maganin ne” ta girgiza kai tace “ Tunda basu tsauwala ba sunce ko zuwa gobe ne a kawo, da ka yi haƙuri ka huta tunda dare ya yi sosai zuwa gobe sai ka sayo”, ya girgiza kai yace “ Gara dai na je na nemo, idan yafi ƙarfina sai nasan yadda zanyi”, ta gyaɗa kai tace “Hakane, to Allah dai ya rufa asiri”, ya daɗe yana kallon Afrah da ƙaton cikinta sannan ya fice cikin wani irin yanayi.

Kiran da Haj Hudah take masa kamar ta sha ƙwaya, ya sa shi ƙara jin haushinta, akalla ta kira shi fiye da sau hamsin har sai da ta ƙarar masa da caji wayar ta mutu sannan ta haƙura. Wajen sai da magunguna na asibitin ya fara zuwa, su ba su ma da allurar, daganan ya fice waje a ƙalla sai da ya je shagunan sai da magani kusan shida sannan ya sami allurar, sai dai ana gaya masa kuɗinta ya ɗauke numfashi kamar kazar da ƙwai ya fashema a ciki ya fito daga shagon, duk da dare ya yi sosai bai hana shi zama a kan wani kwalbati ba, ya dinga sharar hawaye kamar wani ƙaramin yaro, bakinsa da zuciyarsa suna ambaton addu’ar, (ya hayyu ya ƙayyumu bi rahmatika astaghisu aslihlee sha’ani kullah wala ta ƙilli ila nafsi tarfata ainin) sannan ya na ƙarawa da (la haula wala ƙuwwata illa billah) , domin waɗannan addu’o’in suna taka rawa wajen fatattakar dukkan damuwa.
Lokaci ɗaya ya cigaba da nanata kuɗin allurar nera dubu ashirin duk guda ɗaya kumq guda uku aka rubuta a saya, a ƙalla nera dubu sittin kenan, ina ya gansu, ya taɓa aljihunsa dubu biyun da ta rage masa a yanzu bayan zirga zirgar neman allurar da ya yi a adaidaita sahu saura ɗari tara, ya zuba tagumi ya na tunanin yadda zaiyi. Ya yi tunanin kiran Hassana ya nemi taimakonta, domin yasan Hussaina ba ta da kirki bama zai fara sa ta a sahun masu share masa hawaye ba.Ya duba agogon wayarsa ƙarfe biyu ne da minti huɗu na dare, yasan babu yadda za’ayi ya kirata a cikin wannan daren dole sai dai ya bari sai gobe da safe.
A haka a daddafe ya koma asibitin, bai ɓoyewa Inna Halima komai ba, ita kanta ta firgita da jin kuɗin allurar da tafi wacce ake mata tsada, ganin yadda ta tada hankalinta da tunanin inda za’a samu kuɗin yasa ya yi mata bayanin ya na jira gari ya waye ne ya kira Hassana ya ji ko zai sami taimakon kuɗin a wajenta, Inna Halima ta tsare shi da kallo domin ta yi tsammanin zata ji ya ambaci Haj Hudah ne, amma sai ta ji saɓanin hakan, ta ɗan gyara zamanta tace “Me yasa ba zaka yi ma Haj Hudah magana ba, nasan itace za’a samu kuɗin a hannunta babu tantama”.
Gabansa ya faɗi da jin ambatar sunan Haj Hudah, amma ya dake saboda ba ya son Inna Halima ta fahimci wani abu, yace “ Bana son na takurama wanda ke tsaye akan buƙatata, kuma ita da kanta take yi ba tare da na nemi taimakonta ba, ta zo ta ga halin da Afrah take ciki, idan ta so ta taimaka zata taimaka ba tare da na roƙeta ba kamar yadda ta saba”, cike da gamsuwa Inna Halima tace “Hakane kuma, kada muyi gajen haƙuri ƙila akwai abinda take shiryawa domin taimakon mu”, kai kawai ya gyaɗa yana ƙara jin zafin Haj Hudah gami da yin tir da tarayyarsa da ita da bata da amfani.
Ficewa yayi ɗan sauran daren da ya rage ya yi alwala ya shige masallacin asibitin ya cigaba da yin sallar nafila domin roƙama kansa da Afrah sassauci na halinda suke ciki. Anan ya ƙarasa sauran darensa.
Washegari kasancewar yasa cajin wayarsa a cikin masallacin yasa tun ƙarfe bakwai yake kiran wayar Hassana amma wayarta tana kashe. Har mallam Mahmud ya kawo musu abin karyawa, ya lura da damuwar da Musaddiƙ yake ciki, ya kuma san dalili domin a gabansa likitan ya shigo yana tambayar allurar da yace a sayo, ya matsa kusa da shi ya dafa bayansa cikin raunanniyar murya yace “ ka kwantar da hankalinka, duk wani mumini da ƙaddara rayuwarsa take tafiya, Allah zai kawo yadda za’ayi, ina ganin zan je na sa wata kadarata a kasuwa”. Inna Halima ta numfasa tace “yaya wannan hali da ake ciki, kayan na ka ma ko ka ɗaga waye zai saya, idan kuma an samu mai saya sai dai a saya a wulaƙance, bayin Allah da suke mutuwa da cuta a yanzu da basu da yadda zasu yi babu kuma mai taimaka musu ai suna da yawa, muna cikin wani lokaci ne mai wahala, amma wannan lokacin ya yi kama da nafsi nafsi kowa ta kansa yake”. Mallam Mahmud yace “Hakane”, ta ɗan ƙara dubansa tace “ Da nace ko wajen Haj Hudah ya je ya nemo taimako to amma ya kawo min uzurin idan ta ga damar taimakawa ba sai an nemi taimakon ta ba, da kanta ma zata taimaka”, ya jinjina kai yace “ wannan gaskiya ne, saboda duk taimakon da ta yi a baya ina ganin ai babu wanda ya roƙeta, don haka wannan ɗin ma babu mai roƙonta, tana sane nasan kuma zata taimaka, don ina ganin idan mutum na yi maka ba sai ka ƙure shi ba”.
Jinsu kawai Musaddiƙ yake, yana tunanin da sun san mugun halin Haj Hudah da babu wanda zai dinga mata irin wannan ƙyakkyawan zaton, da sun ganeta yadda ya ganeta da tuni sunyi tir da ita, sun kuma ƙyamaceta.
Musaddiƙ ya dubesu idanu jajir yace “In sha Allah idan na sami Hassana nasan zata taimaka min, bansan dai dalilin sa yasa wayarta ke kashe ba, saboda haka zan tafi gidan nata yanzu na sameta”, Inna Halima tace “ Eh hakan ya yi kaje gidan kawai, Allah yasa ka taddata”, ya tashi da sauri, cike da tausayawa Mallam Mahmud ya kamo hannunsa ya maida shi ya zaunar, ya dubi Inna Halima yace “zuba masa koko da ƙosan nan ya sha kafin ya tafi”,
Musaddiƙ ya buɗe baki zaiyi magana ya katse shi, “Nasan me zaka ce, kada ka ce min komai, dole ka sha kafin ka tafi, ko don ba ka kallon kanka a madubi da ka ga yadda ka rame ka fita hayyacinka bayan wannan abin yin ubangiji ne sai dai mu karɓa mu kuma ce Alhamdulillah”, ido kawai ya runtse yana ƙoƙarin maida hawayen da ya fara taruwa masa, har Inna Halima ta zuba masa kokon a kofi ta bashi gami da ƙosan, amma kokon kawai ya iya sha ba tare ƙosan ba.
Yana shan kokon nan Haj Hudah ta kira shi baisan iyaka ba, bai bi ta kanta ba, yana gamawa ya fice zuwa gidan Hassana, zuciyarsa cike da matsananciyar damuwa. Yana cikin adaidaita sahu, wayarsa ta cigaba da kuka wannan karon ya na dubawa ba Haj Hudah ba ce, number asibitin mahaukata ne inda Haj kilishi ke zama, da sauri ya ɗauka, yana addu’ar Allah yasa ba wani bala’in ba ne.


Yar gidan Imam✍️
MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
( mrs Aliyu Mayere)

Page 16


Daga ɗaya ɓangaren, ɗaya daga cikin masu kula da su Haj kilishi tace “ Muna magana da Musaddiƙ ne?”, da sauri ya amsa da cewa “ Eh ni ne, lafiya ko?”, tace “ To lafiya ba lafiya ba, kilishi ce ke cikin mawuyacin hali na ciwo kusan kwana uku kenan bata ci ba ta sha ga ƙafafunta sun kumbura ƙwarai da gaske, munyi ta kiran Hassana amma bamu sameta ba, sannan yau wata biyu kenan ba’a biya kuɗin kula da ita ba, bamu san matsalar ba”, gaban Musaddiƙ na cigaba da faɗuwa yace “ zamu taho asibitin yanzu in sha Allah”, bata jira komai ba ta aje wayar, gaba ɗaya musaddiƙ ji ya yi yana neman sukurkucewa abu goma da ashirin, ya ƙosa ƙwarai ya ƙarasa gidan Hassana domin ya ji halin da ake ciki.

Ya yi sa’ar tadda Hassana a gida, yana shigowa maigidanta na fita zuwa office, don haka da ƙarfin guiwarsa ya shiga gidan, ganinsa wujuga wujuga yasa ta shiga tambayarsa jikin Afrah, ya ɗan numfasa yana kallonta yace “ Alhamdulillah zance akwai sauƙi amma na musulunci”, ta ɗan gyara zamanta tace “ Amma kana cikin damuwa da yawa, kaga yadda ka fita hayyacinka kuwa, ka dinga haƙuri, ni fa tun da mummy ta shiga wannan mugun halin gaba ɗaya naji duniya ta fita kaina komai ya fita a raina, domin tabbas duniya ba matabbata bace, dole mutum ko ba yama Allah ya koma ga ubangijinsa”, Musaddiƙ ya muskuta ya kwashe duk yadda su kayi da asibitin mahaukata ya sanar da ita, ya ƙara da cewa “ Haba Hassana kawai yan kwanakin da nayi ban samu naje ba saboda lalurar Afrah, shi ne zaki manta da ita, duk fa yadda Haj ta kai ga lalacewa dole mahaifiyarki ce, bana som ki zama Hussaina da gaba ɗaya ta zare ma kanta kauna da tausayin mahaifiyarta, kada ki fifita mijinki ki wofintar da mahaifiyarki, don Allah ki dawo hayyacinki”, ta goge hawayenta tace “ Ba zaka gane ba Musaddiƙ, ba zaka gane tsaka me wuyar da nake ciki ba, mijina bansan tunaninsa ba sam ba ya son na raɓi mahaifiyata ba, kasan matsalar na gaya maka yadda aurena yake lilo tun faruwar abubuwan da suka faru, ina son aurena bana son ya mutu saboda wannan dalilin, shi yasa nake ja baya a kan lamarinta”.
Ya girgiza kai duniya kenan yau ɗan da ka haifama sai ya iya juya maka baya idan Allah yaso jaraftarka da nuna maka kuskurenka, shi kam duk irin mugun abun da Haj kilishi ta yi masa bazai iya wofintar da ita ba ko don martabar mahaifinsa da kuma kallon da yake yi mata na uwa.
Babu wani amfanin cigaba da nunama Hassana kuskurenta don ya fahimci ta riga ta zaɓi mijinta akan mahaifiyarta, dama itace mai dama me kuma zuciyar musulunci fiye da Hussaina da ita tun farko ma ba ta sa kanta cikin hidimar Haj kilishi ba, kuma ko shi ta ƙi saurara akan hakan.
Musaddiƙ ya numfasa yana kallon Hassana yace, “ me yasa har watanni biyu ba’a biya kuɗin da ake biya ma Haj duk wata ba a asibiti”, ta sakko da ƙafafunta ƙasa gami da lanƙwashe yatsun hannayenta har sai da su kayi ƙara sannan tace “ Idan na gaya maka cewa kuɗin da suka rage ma mummy basu da yawa zaka yarda?”, kai kawai ya gyaɗa ba tare da yace uffan ba.
Ta cigaba da cewa “ Ni kaina nayi mamaki da naga sauran ɗan abinda ya rage mata, wanda tuni suka ƙare, kasan cewa zuwa yanzu kadararta ake ɗagawa ake sayarwa sannan a yi mata biyan bukata, ni kaina kuɗina duk sun gama shiga ciki”, musaddiƙ ya dubeta cike da kaɗuwa yace “ yanzu dai kina nufin cewa babu kuɗin da za’a cigaba da kulawa da lafiyar Haj”, ta gyaɗa kai tace “ Eh kusan haka ne”. Shuru ya yi duk wani tunaninsa ya tsaya. Duk sauran bayanan da ta cigaba da yi masa baima san abinda take faɗa ba tunaninsa ya yi nisa, ga damuwar Afrah ga ta Haj kilishi da yake jin ba zai iya barinta rayuwarta ta ƙare a haka ba. Shin ya zaiyi ya na buƙatar kuɗaɗe masu kauri, amma ina zai same su.
Ya muskuta yana kallonta yace “Duk na ji uzurorinki, amma kinsan cewa Haj tana cikin wani mugun hali na ciwo?”, ta maimaita da sauri “ ciwo?”, daga nan ya sanar da ita kiran da asibitin su kayi masa.
Ya ƙara da cewa “ ko kina ganin duk da haka ba zaki iya ɗaukar nauyin kulawa da ita ba, bayan kinsan ni a yanzu bana cikin nutsuwata saboda ciwon Afrah, yadda nake samun lokacin zuwa na kula da ita ba zan samu ba yanzu,”. hassana ta goge hawayenta tace “ Zan je asibitin yanzu naga halin da take ciki”, Musaddiƙ yace “Don Allah ki hanzarta ki je ko me ake ciki ki sanar da ni, saboda yanzu ma taimako nake nema na kudi nera dubu sittin za’a sayi allurar da za’ayi ma Afrah ne, ko aro ko kyauta duk wanda na samu ina godiya”. Hassana ta ɗanyi jim, sannan tace “ Bani da kuɗi a hannuna, ga kuma hidimar da zan je na tadda na mummy yanzu, amma ina zuwa”, ta miƙe da sauri ta shige ɗaki, Musaddiƙ ya zuba tagumi ya na bin sawunta da kallo.
Bata daɗe ba ta fito riƙe da kuɗi ta miƙa masa tace “ kayi haƙuri Musaddiƙ abinda ya samu kenan, dubu talatin”.
Da sauri ya amsa ya na jin tamkar miliyan talatin ta ba shi, ya yi mata godiya sosai, sannan ya yi mata sallama har ya kai ƙofar falon ya tsaya ya juyo yana kallonta yace “ Na gamaki da girman Allah ki tashi yanzu ki tafi kiga halin da Haj take ciki”, kai kawai ta jinjina har ya fice tana mamakin kyakkyawan hali irin na Musaddiƙ, yadda ya damu da Haj kilishi duk irin baƙar muguntar da ta yi masa ba duka mutum ba, ko ita da take mahaifiyarta komai tana yi mata ne kawai don dole don babu yadda zata yi ne, domin ta fi kowa sanin ta gama tona musu asiri, a yanzu bata da wani kima ko daraja a gun mijinta, ga shi hatta dangin miji yanzu ta daina shiga saboda yadda kai tsaye ake goranta mata.
Fitar Musaddiƙ kai tsaye chemist ya wuce domin sayen allurar, duk da zuciyarsa na raya masa ya kira Murtala ya ji ko zai iya samun cikon kuɗin a hannunsa.
Yana tsaye ya miƙa dubu ashirin kuɗin allura ɗaya kenan wayarsa ta ɗauki ƙara, yasan ƙila Wannan fitinanniyar ce Haj Hudah domin tun a gidan Hassana take aikin kiransa, a fusace ya ɗakko wayar amma saɓanin haka ya gani, domin yana dubawa nambar Inna Halima ya gani, da sauri ya ɗauka a firgice ya ke tambayar jikin Afrah, cikin natsuwa ya ji tace masa” ka dawo asibiti an sami kuɗin allurar, likita kuma ya ƙara rubuta wasu magungunan”, kamar ana jira ta gama faɗan abinda take faɗa aka katseta alamar kuɗinta sun ƙare, bai damu da ya kirata ba da saurin gaske ya amshi maganin cike da murna da tunanin inda aka samu kuɗin, duk da ya fi tunanin ƙoƙari ne irin na Mallam Mahmud da Inna Halima da kullum suke kan yi.
Kai tsaye asibitin ya nufa, tun daga ƙofar ɗaki ya ji jikinsa ya shiga rawa, ya ji wani irin faɗuwar gaba a tattare da shi ya riƙe murfin ƙofar yana shakkar turawa ya shiga, domin yadda ƙamshin turaren Haj Hudah ya cika hancinsa, ko daga bacci ya tashi yasan wannan ƙamshin turarenta ne.
Ƙuru kawai ya yi ya tura ƙofar ya shiga cikin sallama. Da Haj Hudah ya fara yin tozali tana zaune kan kujerar roba ta sha kwalliya cikin wata tsadaddar abaya mai ruwan ƙasa, tayi kyau sosai duk da fuskarta ta faɗa alamar rama ta bayyana a zahiri. Idanunta na ɗore akan nasa tana jin tamkar ta janyo shi zuwa gareta, ramar da ya yi kyau ya ƙara masa. Tana jin zata iya ba da duk abinda ta mallaka don kawai ta mallaki musaddiƙ,

Please Login or Register in order to submit comment