Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baragurbin ƙwan komai warinsa.
Cike da tashin hankali ta isa gidan Haj kilishi mai taxi yana tsaida motar, wani a daidaita sahu yana tsayawa a gaban gidan, a hankali cikin galabaita Afrah ta fito daga ciki, daƙer ta iya bashi kuɗinsa ya karɓa yana cewa “Allah ya sauwake”. Da sauri Haj Rakiya ta fito daga cikin motar dama ta riga ta biya shi kuɗinsa don haka da sauri ta yi wajen Afrah da take neman faɗuwa ta tarota ta rungumota zuwa jikinta, “ Afrah lafiya me ke damunki”, ta kasa magana sai cikinta da take dafe da shi. Tuni Haj Rakiya ta fahimci ba ta da lafiya ne, don haka ita tq riƙeta da jakar ta ta makaranta zuwa cikin gidan, ganin halin da Afrah take ciki yasa damuwa ta cika masa zuciya ya bisu har cikin bsngaren Afrah yana son sanin abinda ya faru, musamman da ya ganta da Haj Rakiya, sam mutanen nan bai yarda da su ba, kamar Haj Rakiya ta fahimci abinda ke cikin zuciyarsa yasa ta yi masa bayanin komai, Afrah tana kwance tamkar matacciya saboda galabaita, Haj Rakiya ta bi shawarar maigadi inda ta ɗauki wayar Afrah ta kira musaddiƙ bugu ɗaya a cikin na biyu kamar yana jira ya ɗauki wayar.
Jin muryar Haj Rakiya cikin damuwa ya gigita musaddiƙ ya shiga tambayarta ina Afrah, a gaggauce ta gaya masa halinda take ciki, bai gama jinta ba ya kashe wayar ya miƙe a gaggauce yana fitar da numfashi, Haj Hudah ta bi shi da kallo yadda ya gigice yasa tace “ meke faruwa ne”, murya na rawa yace “ Matata ce ba lafiya, zan tafi gida na kaita asibiti”, kafin ta yi magana tuni ya buɗe ƙofar motar ya fice bai saurari komai ba ya buɗe get ya fita, cikin mugun yanayin da Haj Hudah bata taɓa ganinsa a ciki ba.
Ta saki baki tana kallon ƙofar get ɗin, wani irin takaici ya kamata, karo da dama kenan da ta ji haushin Afrah, wannan karon ma har da wani abu mai kama da tsana. Ƙarya kawai ta yi ma musaddiƙ na cewa akwai inda zasu amma gaskiyar magana yau so kawai ta zauna tare da shi a keɓaɓɓen wajen da zata su daɗe zaune tare tana jin sautin muryarsa, amma Afrah ta rushe mata jin wannan farincikin na yau, ji tayi hawaye ya cika zuciyarta, direban ya juyo yace “ haj mu tafi ne”, ta girgiza kai a sanyaye gami da buɗe ƙofar motar ta fito, ba tare da tayi magana ba ta shige cikin gida, zuciyarta cike da duhu.

Da Taxi musaddiƙ ya ƙarasa gida, yana shiga gidan kuma bai saurari komai ba matarsa ya ɗakko cak zuwa mota, Haj Rakiya da Baba maigadi na binsa a baya, har suka bar ƙofar gidan kai tsaye asibiti ya wuce ba tare da ya jira komai ba, yana girgizata yana jin tamkar ya maida ciwon kansa, amma wani abu mafi tashin hankali Afrah ko motsi bata iyawa gashi dai tana numfashi amma babu wani ƙarfi a tare da ita, tunda musaddiƙ yazo duniya bai taɓa shiga tashin hankali ba irin na yau.
Suna zuwa asibitin gado aka ba Afrah, Allah yasa akwai kuɗi a jikinsa, da su ya yi ta biyan kuɗalen asibitin. Likitoci suna kanta domin gano abinda ke damunta, anata gwaje gwaje.

Tun shigar Haj Rakiya falon Haj kilishi take labarta mata halin da taga Afrah, sai dai bata gaya mata ta taimaketa ba asalima cewa tayi tana dawowa ta ga musaddiƙ ya tafi da ita asibiti, ba kunya ba tsoron Allah kuma ta karkace ta zubo ƙaryar cewa “ Dama Tsiduhu ya gaya min ina dawowa zan sami Afrah rai a hannun Allah”, cikin fara’a Haj Kilishi ta dubeta tace “Tsiduhu kuma? Amma kuma ai wajen mai Rakwacam na tura ki mai ya haɗaki da Tsiduhu kuma?”.
Sannu a hankali ta gaya mata halin da ta sami mai Rakwacam, dalilin da yasa kuma kenan ta wuce wajen Tsiduhu da maganar ko ciwo ne ya ɗora mata , tunda dai damuwa ake so su shiga.
Haj kilishi ta fashe da dariya harda ƙyaƙyatawa, ta miƙama Haj Rakiya hannu suka tafa, tace “Aikin ki na kyau aminiyata, kinyi dai dai nagode ƙwarai da gaske”,
Haj Rakiya tace “ sai dai kuɗin aikin da yawa don dama nace masa ba zamu ba da ko sisi ba sai aiki ya ci tukuna, kuma gashi aiki ya yi Haj”,
Ta dubeta cikin dariya tace “ Nawa yace za’a bashi, ta muskuta tace “ Dubu dari uku “, ta ce “ Ai yama yi sauƙi zan baki ki kai masa”, Haj Rakiya ta numfasa tace a ranta, a haka zan gama haɗa kuɗin gidana ba tare da kin gane komai ba. Haj kilishi tace “ shi mai Rakwacam ɗin ya ake ciki da shi”, Haj Rakiya ta taɓe baki, bata son ta gaya mata gaskiyar komai domin bata son ta karaya kamar yadda itama ta karaya, tafi son ko zata tuba ta bari sai ta gama yasheta ta gama kwasar rabonta, don haka tace “ Ke nifa sai daga baya na fahimci kamar kunyar yadda ya kasa yi miki aiki ne yasa ya ƙirƙiri wannan ciwon tunda yasan yau ce ranar da yace mu dawo”, Haj kilishi tace “ kuma fa hakane, tunda ko shi da kansa ai ya yi ma kansa aiki ya samu waraka, ni dai yau ai ina cikin farinciki rabom da ayi min irin wannan aikin harna manta lalle Tsiduhu ya haɗu”.
Haj Rakiya ta yi dariya tace “ sosai kuwa ai Tsiduhu ba daga baya ba”, ta janyo wayarta ta kira musaddiƙ, yanayin muryarsa kawai da ta ji, mai cike da ɗimbin tashin hankali da firgici, shine ya ƙara jefa mata tsananin farinciki da jindaɗi. Muryarsa na rawa sosai tamkar ma kuka yake yi yace “ Haj Afrah ba lafiya, gata nan cikin mawuyacin hali”, ta dubi Haj Rakiya tana murmushi tace “ Kayi haƙuri ka natsu zata sami lafiya, yanzu me likita yace yana damunta,” ya girgiza kai “ Har yanzu basu ce komai ba suna ta dai gwaje gwaje”, ta yi dariya sosai, sannan kuma ta shiga kwantar masa da hankali, ta kuma tambaye shi asibitin ya gaya mata, tana jin muryar Mallam Mahmud da muryar inna Halima, haka zalika tana matuƙar jindaɗin yadda take tsintar damuwa da tashin hankali a cikin muryoyinsu.
Bayan ta aje wayar ne, ta ƙara rushewa da dariya, ta tashi daƙer ta bi bango ta shiga ɗaki, Haj Rakiya ta bita da kallon takaici, a ranta tace “ zanyi maganinki”. Dubu ɗari uku da ashirin ta ɗakko ta bata, sam bata rabo da kuɗi a gida domin tasan cikin ko wane lokaci zata iya buƙatar manyan kuɗaɗe, ta karɓa ta kuma yi godiya sannan ta tafi tabar Haj kilishi cike da farincikin da ta rabu da jin irinsa.
Daga musaddiƙ har Mallam mahmud da Inna Halima sun kasa zaune sun kasa tsaye, cikin tashin hankali su ke, burinsu ɗaya su san abinda ke damun Afrah.
Amma har sai yamma sannan wasu daga cikin sakamakon gwaje gwajen Afrah suka fito.
Inda da kansa likitan ya buƙaci ganinsu a ofishinsa, gaba ɗaya musaddiƙ a rikice yake addu’arsa ɗaya ce Allah yasa ba wani mugun ciwo Afrah take da shi ba. Sai dai addu’arsa ba ta ci ba. Domin takardar da likita ya miƙo masa ta ƙarasa jefa shi cikin mawuyacin hali ya ƙurawa takardar ido, a yayin da likita ya fara bayani…………….


Yar gidan Imam✍️
https://chat.whatsapp.com/JUeJeOL9kA8AHOGOfXOnSZ


MUSABBABI BOOK 2
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM
(Mrs Aliyu Mayere)

Page 5

Likitan ya cigaba da cewa “ko wane ɗan adam yana da ƙoda guda biyu a jikinsa, sai dai mutum zai iya rayuwa da ƙoda guda ɗaya, hakan yasa ko da ɗaya ta samu matsala to ɗaya zata iya riƙe shi ya cigaba da rayuwa, to a zahirin gaskiya duk a gwaje gwaje da binciken da mu kayi, mun gano cewa Afrah tana fama da ciwon ƙoda”, Inna Halima da Mallam Mahmud suka fiddo da idanu waje cike da kaɗuwa gami da tashin hankali, suka haɗa baki gaba ɗaya su ka maimaita, “ ciwon ƙoda likita”.
Shi kam musaddiƙ takardar hannunsa kawai ya ke cigaba da juyawa yana kuma jin zuciyarsa na matuƙar bugawa, likita ya gyaɗa kai yace “Eh, kuma wani abin mamakin shine bakasafai ƙoda guda biyu ke kamuwa da ciwo lokaci ɗaya ba, amma ta Afrah gaba ɗaya guda biyun duk sun harbu sun kamu da ciwo, sai dai ɗaya tafi ɗaya lafiya”. Sai alokacin musaddiƙ ya runtse idanunsa a hankali ya ji hawaye ya fara ƙoƙarin fita masa, sai dai baya son hakan ta kasance a gaban su Inna Halima, domin yasan zai iya karyar musu da guiwa.
Mallam Mahmud ya matso gaban likitan sosai yace cikin rawar murya “ yanzu likita meye abinyi? Wane taimako zaku iya ba ta domin samun lafiyarta?”.
Likita ya ɗan dubi musaddiƙ, duk da baiyi magana ba, ya fahimci irin tashin hankalin da yake ciki.
Yace “ ka kwantar da hankalinka, ko nace duk ku kwantar da hankalinku, a yanzu zamu ɗorata akan magunguna da kuma shawarwari, amma ku sani, a duk lokacin da ƙodojinta biyu suka daina aiki, to ya zama dole sai anyi mata dashen ƙoda”,
A hankali mallam mahmud ya lalubi kujera ya zauna domin ji ya yi yana neman faɗuwa, Inna Halima kuwa baki ta rufe ta shiga kuka.
Musaddiƙ ya ɗago ya dubi likita lokaci ɗaya yana ƙoƙarin tsaida hawayensa, yace cikin wata irin murya, “ Dashen ƙoda? Zuwa tsawon wane lokaci za’a ɗauka kafin hakan ya kasance?” Likita ya gyara zamansa yace, “ Eh to gaskiya bazan iya cewa ga lokaci ba domin ya danganta da yadda ciwon ke tasiri a cikin jikinta, zai yuwu zuwa watanni ko shekaru kai koma kwanaki, sai dai ka sani nata ciwon ya yi tsanani, don da alama ya daɗe yana cin jikinta ba tare da kun an kara ba, ko kuma rashin sanin alamomin cutar”.
Duka shuru su kayi na wani dogon lokaci kafin likita ya gama rubutunsa ya miƙa ma musaddiƙ yace “ A samo waɗannan maguungunan, sannan a tabbatar ta na shan ruwa sosai, kada kuma ta dinga matse fitsari ba tare da ta yi ba, wannan maganin kuma akwai nurse da zata zo ta dinga bata bisa ƙa’ida”.
Ya amshi takardar lokaci ɗaya ya tashi cikin ƙarfafa guiwa ya dubi su mallam mahmud ya ce “ kawu mu je”, ya riga su fita daga ofishin, bai koma ɗakin da Afrah take ba ya wuce ya tafi sayo maganin cikin matuƙar tashin hankali mara misaltuwa, yana tafe yana sharar hawaye tamkar wani ƙaramin yaro.

Hankula fa gaba ɗaya sun tashi, jinya sosai Afrah take yi,a yayinda gaba ɗaya musaddiƙ ya tare a asibitin shi ne yake jinyarta, duk da ga Inna Halima, amma baya yarda ya je ko nan da can, yana manne da Afrah, duk da ta fara samun sauƙi ta kuma san irin ciwon da ke damunta, a hakan ma itace ke ba musaddiƙ haƙuri a duk lokacin da ta ga ya faɗa cikin damuwa da tunani. Ita tuni ta fauwalama Allah komai domin tasan shine me yin yadda ya so, kuma ta ɗauki wannan ciwon a matsayin kaffara a gareta.
Zuwan Mama Hauwa biyu asibitin tana dubata, duk da babu wata damuwa a tare da ita na halin da Afran take ciki.
Haka zalika itama Haj kilishi direba ya kawota ita da Haj Rakiya sun dubata, sosai Haj kilishi ta nuna damuwarta, sai dai ko sisinta bata bayar ba don a cigaba da duba Afrah, duk da tasan musaddiƙ ɗin ba wani abu ya aje ba, haka su Mallam Mahmud.
Don ma Allah ya rufa asiri duk kuɗin da ake kashewa musaddiƙ ke badawa bai taɓa gazawa ba, tunda duk irin kuɗaɗen da Haj Hudah take bashi baya almubazzaranci, yana ajewa don yana tsoron buƙata ta taso musamman buƙatar Afrah ace bashi da yadda zaiyi.
Ranar da Haj kilishi ta je asibitin har suka kai gida cike take da farinciki yadda taga Afrah haka take son ta cigaba da kasancewa, ita kam Haj Rakiya a zuciyarta tausayin Afrah take ji amma a zahiri sai ƙara ƙarfafa aikin Tsiduhu take tana ƙara tabbatarma da Haj kilishi cewa duk aikinsa ne, tunda dama yace zai sa mata ciwo mai wuya ne, to gashi nan ya haɗata da ciwon ƙoda.Haj kilishi fa ranta ya yi mata fes ta ƙara gasgata duk abinda Haj Rakiya ta faɗa mata.
Taɓangaran Haj Hudah kuwa damuwa ce ta addabi ruhinta, ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta kuma rasa dukkan farincikinta, a dalilin rashin zuwan musaddiƙ aiki, domin da kansa ya kirata ya sanar da ita cewar bazai iya dinga zuwa wajen aiki ba saboda yana jinyar matarsa.
Haj Hudah bata jin zata iya jure rashin ganinsa, haka zalika ta rasa wane irin muhimmanci da so musaddiƙ yake ma matarsa da baya iya ganin kowa sai ita.
Adalilin hakan ta shirya ta tafi asibitin domin ta duba jikin Afrah, idanunta kuma su yi mata tozali da abinda suke son gani. Wannan shine karo na farko da tayi ido biyu da Afrah, ta zauna a gefen gadon tana ƙare mata kallo, duk yadda take fasalta Afrah a cikin zuciyarta ta fi haka, Afrah kyakkyawa ce sosai bata da wata makusa, wani irin kishi ne yake ta cika zuciyarta, ko yaya ta dubi Afrah sai ta ji kamar damuwa zata yi ajalinta.
Bata ƙara jin damuwa mai tsanani ba sai da ta ga yadda musaddiƙ ya rame duk ya fita hayyacinsa, tamkar shine baida lafiyar, ga shi sai tsuma yake da rawar jiki akan Afrah, hankalinsa baya kan kowa sai kan Afrah, ko ita bata jin ya dubeta sau biyu, ji tayi gaba ɗaya ba zata iya zaman asibitin ba. Don haka ta tabbatar ma da musaddiƙ cewar ta ɗauki nauyin duk hidimar asibitin, sannan kuma ta aje musu kuɗi masu yawa wanda musaddiƙ zai riƙe a hannunsa ko da wani abu zai ta so. Kwarai matuƙa Mallam Mahmud da Inna Halima sun yi ma Haj Hudah godiya mara misaltuwa, kimarta ta ƙara yawa a zuƙatansu.
Shi kansa musaddiƙ ya ji daɗin wannan karamci da gudunmawayar da Haj Hudah ta ba su, domin duk yan kuɗaɗen nasa sun tasarma ƙarewa, dama don farincikinsa ta yi ganin kuma farincikin nasa kaɗai ya wadatar da ita. Haka ta dawo gida cikin wani irin yanayi, tunda kuma ta dawo gidan take zaune a falo ta kasa shiga ɗaki, duk kuma irin abinci da kayan marmarin da hadimanta suka jera a gabanta, babu abu ɗaya da Haj Hudah tasa a bakinta, damuwa ta bayyana sosai a tattare da ita. Dai dai lokacin Alh yusuf sanda ya shigo falon yana gyara zaman babbar rigar da ke jikinsa, tsayawa ya yi ya zuba mata ido, ya daɗe yana kallonta kafin ya yi ɗan murmushin da ya zama tamkar ɗabi’ar rayuwarsa ne, sannan ya gyaɗa kai ya ƙaraaa cikin falon, amma har ya zauna Haj Hudah bata san da shigowarsa ba.
Shi ma kuma bai damu da tasan ya shigo ɗin ba, domin yadda ya miƙa hannu ya ɗauki tufar dake cikin farantin kayan marmarin da ke gabanta, ya shiga sha hankali kwance, haka nan ya zubama fuskarta ido, ko kaɗan baya neman sanin duniyar tunanin da ta faɗa. Karar da wayarsa ta carke da shi ne ya dawo da Haj Hudah duniyar tunanin da ta faɗa, nan da nan ta gyara zamanta tana tunanin iya tsawon wane lokaci ya ɗauka da shigowa falon, domin ko kaɗan ba zata so ya ganta cikin yanayin da take ciki ba. Hankalinsa kwance yake waya, maganar kasuwanci yake yi har suka gama idonta na kansa.
Ya aje wayar yana kallonta yace “ kin dawo kenan”, ta ɗan gyara zamanta tana jin nutsuwar rashin tsintar wani abu mai kama da zargi a muryar Alh yusuf sanda, tace “ Na dawo tun ɗazu, ai ban daɗe ba”, ya ƙara miƙa hannu ya ɗauki ayaba ya cigaba da ci, yace “ ya me jikin”, tace “ Ta ji sauƙi, ta dai sami ciwo mai wahala ne”, ya ɗan dubeta yace “ me ke damunta?”, ta ɗan yamutsa fuska tace “ ciwon ƙoda take, kuma duka biyun”, ya girgiza kai yace “ Lalle kuwa ciwo mai wahala Allah ya bata lafiya”, Hakanan ya ƙara zuba mata ido yana wani irin nazari, lokaci ɗaya ya maida bayansa ya kwantar akan kujerar, gami da girgiza ƙafafunsa zaman shurun duk ya damu Haj Hudah don haka ta miƙe ta shige ɗaki yayinda ya bita da wani rikitaccen kallo cikin murmushi.
Tun daga wannan ranar Haj Hudah ta kafama kanta zuwa asibiti duba Afrah, ba don wai ta damu da ciwon nata ba a’a sai don kawai ta samu ta dinga ganin musaddiƙ tunda yaƙi dawowa bakin aikinsa, idanunta kuma ba zasu juri rashin ganinsa ba. Haka ta dinga kashe lokacinta tana zuwa asibitin duk da tana da abubuwan yi , har zuwa lokacin da Afrah ta sami sauƙi aka sallameta, tare da magunguna da kuma shawarwarin yadda zata taimaki kanta,
Ko bayan da aka sallami Afrah, musaddiƙ kin fara zuwa aiki ya yi, ya zauna a gida yana cigaba da kulawa da matarsa.Daƙer Afrah ta shawo kansa ya fara zuwa wajen aiki, tunda ita kanta ta ji sauƙi sosai, don har tana tunanin fara zuwa makaranta. Afrah tana da matuƙar tawakkali shi yasa bata sama kanta damuwa ba sam agame da lalurar da Allah ya ɗora mata.

Damuwa mai yawa ta shiga mallam Mahmud, duk da yana ƙoƙarin boyewa, domin duk abinda zai taɓa Afrah baya ƙaunarsa, Mama Hauwa dai babu yabo ba fallasa, ma’ana bata jin tausayin Afrah haka zalika kuma bata jin daɗin abinda ya sameta.
A ranar da Afrah ta fara zuwa makaranta kuwa Haj kilishi ji ta yi kamar ta yi hauka saboda damuwa, ko kaɗan bata so samun sauƙin Afrah ba, duk da itama jikin nata ya matsa mata kwana biyu, zafin zuciya da raɗaɗin jiki da matsanancin ciwon kai mai tsanani, sai uwa uba yanzu ƙafarta da ciwon ya ci uban na da, don yanzu saboda tsabar ciwo da azabar zafi da take yi mata ko tana zaune sai dai asa ruwa me sanyi a baho ta sanya ƙafarta ciki wanda kafin wasu yan mintoci ruwan yakan koma tamkar ruwan zafi, saboda azabar zafin ƙafar, ko yaya ne kuma bata taɓa iya rufe ƙafarta saboda azabar zafi hakanan zaka ga ƙafar tana zufa.
Likitan da ke dubata babu gwajin da baisa ta yi ba amma har yanzu babu abinda su kayi nasarar gani domin komai lafiya ake nuna masa, ga azaba tana ciki amma ba’a san ta ina za’a fara ba, dole sai dai pain reliver suke bata wato maganin da ke lafar da ciwo, wanda shi kansa shan zai iya zamar mata illa zuwa gaba.
Kuɗi take kashewa sosai wajen nemo lafiyarta amma babu biyan buƙata kamar yadda take ta narkar da kuɗin wajen malamai da bokaye domin ganin bayan musaddiƙ da Afrah, amma har yanzu babu wani cigaba, ance zara bata barin dami sannan taken masu bin bokaye ne yin asarar komai da rasa komai duk abinda suka tara sukan rasa hakance ta fara faruwa ga Haj kilishi, domin dai duk yawan kuɗin da ta tara na cuta da na ta yanzu komai ya fara kakkaɓewa, hankalinta ya ƙara tashi matuƙa, domin dai rayuwa tafiya take tana da burika da yawa amma ta fara karaya, tunaninta ya ƙara nisa.
Wanda take son ganin tashin hankali da tagayyararsa shine kullum yake cigaba a gaban idonta, mu’amalar da musaddiƙ ya yanke da mutanan kirki duk ya dawo da su, domin dai tare ya ke yawo da Murtala da zaran ya tashi aiki to gunsa yake wucewa, shaye shayensa ya yi baya sosai, don a yanzu ma tun fara ciwon Afrah yake matuƙar taka tsan tsan da duk abinda zai tada hankalinta, ga azkar da kansa yanzu yake yi ko da Afrah bata sa shi ba.
Idan Haj kilishi tace tana cikin natsuwa to ta yi ƙarya, ita kanta Haj Rakiya yadda take sintirin zuwa gidanta da yanzu ta rage, idan ba aikenta zata yi gurin malamai ba bata zuwa.
Sai dai abinda bata sani ba, Haj Rakiya tuni ta dawo daga rakiyarta lokaci kawai take jira, ta buga wasanta na ƙarshe.

Alh yusuf sanda yau laraba jirginsa ya tashi zuwa paris, domin shigo da wasu kaya masu muhimmanci na maƙudan kuɗaɗe.
Washegarin alhamis kuwa Haj Hudah cike take da zumuɗi domin tana da taro har biyu a Abuja, so samu ne ta kwana ko da biyu ne a can, amma ƙwaɗayin tafiya tare da musaddiƙ yasa ta haƙura da kwanan ta gwammace su je da wuri su dawo ranar, tunda tasan babu yadda za’ayi musaddiƙ ya yarda ya kwana don ƙa’idarsa ce hakan.
Duk sammakon da musaddiƙ ya yi sai da ya tabbatar da Afrah ba zata sami damuwa ba wajen zuwa makaranta kasancewar sun fara jarabawa, baya son tana wahala duk da tana cikin lafiya amma lallaɓata yake yi sosai. Murtala ya kira ya roƙe shi ya zo ya ɗauki Afrah zuwa makaranta idan lokacin zuwanta ya yi, ya kuma taimake shi ya dawo da ita idan ta kammala zana jarabawar. Murtala ya tabbatar masa bashi da wata damuwa zaiyi duk abinda ya buƙata. Hakan yasa musaddiƙ ya sami ƙarfin guiwar tafiya, bayan ya sanar da Afrah inda zasu tafi tare da Haj Hudah.
Har kullum irin ƙaunar da musaddiƙ ke nunama Afrah, gami da damuwa da ita ya fi komai faranta ran murtala, domin dai shi kansa yasan musaddiƙ ɗin ya yi dacen mata.

Cikin gigita Haj Kilishi ke faɗin “ Duk abinda ki ke yi ki barshi, ki taho yanzu ina son ganinki”, Haj Rakiya ta taɓe baki tace “ Lafiya dai ko Haj” ta girgiza kai tace “ Maganar bata waya bace, ki dai taho yanzu”, tana gama faɗin haka ta kashe wayar. Haj Rakiya ta saki tsaki ta juyo ga Dillali Babaye, ta miƙa hannu ta amshi takardar tace “ Zansa hannu idan na dawo zan kiraka, sai mu ƙarasa” Dillali Babaye ya girgiza kai yace “ Haj gidan nan akwai masu so da yawa, duk da kin bada kuɗi fin rabi gaskiya idan baki cika kuɗinki yanzu ba ana iya samun matsala, gara koma meye ki cika kuɗin duk wani sa hannu ai mai sauƙi ne”. Haj Rakiya ta girgiza kai babu abinda ta tsana da ya wuce a furta cewa tana iya rasa gidan da ta ƙallafama rai, irin gidan yan gayu da take mafarkin shiga.
Tace “ Daina wannan maganar Babaye idan na rasa wannan gidan ai an sami matsala, ina zuwa”, ta miƙe da sauri ta shiga ɗaki, ƙasan katifa ta ɗaga ta ciro ƙuɗi da ta baza a ƙasan katifar, ta yi zaman dirshan ta gama ƙirga kuɗin, bata tashi da ko sisi ba, duk sun shige cikin kuɗin da zata cika, sai dai da ta

Please Login or Register in order to submit comment