Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

domin bata san soyayyarsa ta yi mata mugun kamu ba sai da ya ƙauracewa ganinta, tana son musaddiƙ, wannan damuwa da tashin hankali da yake ciki ji take kamar ta raba shi da su, sai dai kuma ba zata iya yin hakan ba, har sai Musaddiƙ ya amshi tayinta, ta kuma san idan tsanani ya yi tsanani dole ya amshi tayinta.
Kai tsaye gadon Afrah ya wuce yana kallonta yana gyara mata zaman hannunta a saman ƙirjinta. An canja mata robar janyo fitsari, an canja mata robar cin abinci tana dai kwance kamar yadda ya barta.
Rashin kula Haj Hudah da musaddiƙ ya yi baisa Inna Halima tunanin wani abu ba, ta dai fi tunanin damuwar da yake ciki ta riga ta ɗauke tunaninsa, don haka ta yi gyaran murya tace “ Musaddiƙ, ga Haj Huda nan sai ka yi mata godiya, domin itace ta shigo akan gaɓar da likita yake faɗan rashin sayo allurar, bayan ya rubuta wasu magungunan ya fita ne ta ba da wannan kuɗin domin a sayo maganin, sai ka yi mata godiya”, ya juyo amma ya kasa haɗa ido da Haj Hudah, duk da ita idon ta ƙura masa, Inna Halima ta miƙo masa dubu ɗari tace “ Ga kuɗin sai ka je ka hanzarta ka sayo”, a hankali ya miƙe daga bakin gadon yana yi ma Haj Hudah godiya, murmushi kawai ta yi tace “ babu komai, Allah dai ya bata lafiya”. Duka suka amsa da “ Amin”, ya amshi takardar maganin zai fita kenan Haj Hudah ta miƙe, ta dubi Inna Halima tace “Allah ya sauwaƙe, bari mu rage masa hanya saboda ya samu damar dawowa da wuri, don naga yadda likitan ya fusata idan ya ƙara dawowa ba’a sayo ba a kwai matsala”, godiya sosai Inna Halima ta ke ƙarama Haj Hudah. Wanda kafin ta fito Musaddiƙ har ya yi nisa da fara tafiya a harabar asibitin.

A gaggauce Haj Hudah ta bi bayansa ta yi saurin shan gabansa, wanda dole tasa Musaddiƙ ya ja tunga ya tsaya, ya na kallon irin ƙarfin halinta na rashin kunya, “wai menene? Me yasa ki ke ƙoƙarin ƙara min damuwa da
tashin hankali akan wanda nake ciki”, ta girgiza kai gami da sakin gauruwar ajiyar zuciya a hankali kamar mai yin raɗa tace “ka yi min tsawa, ka kyare ni,ka kuma gaya min duk maganar da ka ga dama hakan ba zai taɓa canja min tunani ba, ba kuma zai yi sanadiyyar da zan tsaneka ba, illama ya ƙara min ƙarfin guiwar cigaba da sonka da kuma tunkararka, har sai na sami biyan buƙatata”.
Musaddiƙ ya saki salati yace “wai ke ko musulmar ƙwaraice? Me yasa ki ke sha’awar dakon babban zunubin da babu inda zaki iya kai shi saboda girmansa, ki dinga tuna mutuwa da kwanciyar kabari, ki dinga tuna zaki haɗu da Allah”. Jin bata ce uffan ba ya sa ya cigaba da magana tare da sa ran nasiharsa zata shiga jikinta.
“ me yasa ki ka dage dole sai kin watsar da kima da darajar da ki ke da ita a wajena, duk duniya kina ɗaya daga cikin mutanen da nake mutuntawa tare da ganin girmansu, bana son alaƙarmu ta ƙare a irin wannan siraɗin don Allah ki barni na ji da guda ɗaya, ki sani kuma domin bazan fasa gaya maki gaskiya ba, duk abinda ki ka aikata abin tambaya ne a gaban Allah ranar ƙiyama”. Haj Hudah ta numfasa sosai idanunta duk sun canja wato dai wanda Allah ya ɓatar ya ɓatar wanda kuma ya shiryar ya shiryar domin dai ita kanta ta yarda da cewa abinda take ƙoƙarin aikatawa babu kyau bai kuma dace da ita ba amma me yasa ba zata haƙura ta karɓi nasihar musaddiƙ ba, domin dai kallonsa ta yi sosai tace “Na so ace nasiharka ta sami gurbi a cikin zuciyata, domin ni kaina nasan abinda kake gaya min ɗin gaskiya ne, kuma itace hanyar tsirata, amma ya zanyi musaddiƙ yadda kake ji agame da Afrah haka nake ji a game da kai a zuciyata, ina sonka ina son kasancewa da kai komai runtsi”.
Musaddiƙ yace “ Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un, ba zaki taɓa jin wa’azin da nake miki ba saboda haka Allah ya shiryeki”, ya juya da sauri ya fara tafiya ta biyo shi tana cewa “ ka daina ba kanka wahala, musaddiƙ jinyar Afrah tafi ƙarfinka, ba zaka iya ba, ka saduda ka dawo ka karɓi hanzarina kaga aiki da cikawa, bana son ganinka cikin wannan tagayyarar domin ina jin kamar kasawata ce”, ya cigaba da tafiya ba tare da ya tsaya ba yace “ Allah zai sa min hannu zai taimake ni”, ta yi ɗan murmushi tace “ka daina yaudarar kanka, kai da ganin matarka kasan bata da wani sauran lokaci don haka ya rage naka”, ji ya yi zuciyarsa kamar zata buga saboda tashin hankali, Haj Hudah ta canja matuƙar canjawa.
Tafiya kawai yake yi bai ƙara tanka mata ba, tace “ ka zo mu kaika wajen sayen maganin a mota” ya girgiza kai “A’a nagode”.
Sai da ya fice daga asibitin sannan ta haƙura ta daina binsa, ta tsaya kamar wacce aka dasa, baƙinciki ya gama cikata, musaddiƙ ya na buga mata kai sai dai ba zata taɓa ja da baya ba har sai burinta ya cika.
A ranar Hassana ta je asibitin mahaukata domin ganin halinda Haj kilishi take ciki, wanda sai da ta zubar da hawaye domin a ƙazantaccen yanayin da ta ganta abin ya kai maƙura, sai da ta biya makudan kuɗade kafin likitocin asibitin da suke kula da marasa lafiya su fara bata taimakon gaggawa, sannan shuwagabannin asibitin mahaukatan sun tabbatar mata da cewa idan batq biya kuɗaɗen da ake binsu ba ba zasu ƙara kulawa da ita ba asalima zasu sallameta daga asibitin. Kai tsaye daga nan asibitin da Afrah ke kwance Hassana ta wuce, nan ma wani tashin hankalin ta tarar domin yadda taga Afrah abin sai addu’a, hakan yasa ta kasa gayama musaddiƙ asalin halinda Haj kilishi take ciki domin bata son ta ƙara masa damuwa, ta dai gaya masa da sauki an kuma fara bata magani babu matsala.
Makonni biyu cif tsakani, babu komai a cikin rayuwar musaddiƙ face damuwa da alhini, duk wani ƙashi ya gama fitowa a jikinsa maganar damuwa ma ba’a yinta, karatun kur’ani da nafiffilu su musaddiƙ ya maida wani ɓangare na rayuwarsa, al’amura babu sauƙi, ga babu ga buƙatu kullum ƙara taruwa suke, kowa ya yi iya yinsa, hatta Murtala ya taimaka da kuɗaɗe masu yawa har ya sare, mallam Mahmud ya kusa gama kakkaɓe duk wata tsohuwa da sabuwar ajiyarsa, ciwon Afrah ƙuɗi kawai yake lashewa.
Har zuwa yau da likitoci suka tabbatar da cewa gobe a biya wasu maƙudan kuɗaɗen da za’a yi ma Afrah domin fito da abinda ke cikinta, domin bata da wani sauran lokaci suna son suga matsayin da ƙodojinta suka kai domin sun gano cewa babu aiki ɗaya da ƙodar ke yi a jikin Afrah, domin hatta fitsarin sai sun fito mata da shi, robar fito da fitsarin bata aikin komai bata iya janyo fitsarin, bayanan da aka yi suna da yawa sun kuma ƙara jefa musaddiƙ da su mallam mahmud cikin matuƙar tashin hankali, sannan hankalinsu ya tafi ga tunanin inda za’a samu waɗannan maƙudan kuɗin.
Cikin tsantsar tashin hankali mallam Mahmud ya tattara filinsa guda ɗaya da gona ya sayar, tun da Mama Hauwa ta fahimci hakan, ta tada hankalinta ta shiga bala’i da masifa, har zuwa dawowarsa sallar issha’i bata haƙura ba, yana zaunawa kan tabarma ta fito ta ɗora daga inda ta tsaya.
Mallam mahmud ya gyara zamansa cike da takaici da haushin yadda mama Hauwa ba ta da tausayi yace “Nema ma Afrah lafiya ya zama dole a gare ni, don haka banga amfanin kadarata ba matuƙar ba zata rufa min asiri ba, da kuma ki ke wannan ɓaɓatun an danne haƙƙin yaranki, yanzu don Allah ba ki ji kunya ba, maganar fa rai ake yi idan da akwai ragowar imani a tare da ke ina ganin ko ke ai kya biya kuɗin da za’ayi ma Afrah aiki, saboda haka ka da ki ƙara min maganar banza, ina kuma roƙon Allah ya canja miki wannan mugun halin”. Mama Hauwa ta ƙara haɗe rai tace “ Dama ai nasan ba zaka taɓa fahimta ta ba, tunda ita Afran ita kaɗai ka ke so a cikin yayanka shi yasa su baka tunanin haƙƙunsu dake cikin kayan sai haƙƙin Afrah”. Bai tanka ba har ta cigaba da cewa “Idan abin gaskiya ne, ba mugunta aka sama yayana ba, ai Haj Hudah babu abinda ba zata iya yi masa ba, duk ciwon da Afrah tayi da wanda musaddiƙ din ya yi ai duk ita ta ɗauki nauyinsu, idan banda mugunta irin na musaddiƙ ɗin da ganin ka dage kai ke yin komai, ai yana yi mata magana zata ɗauki nauyin komai, abarka da dukiyarka”.
Ya yi mata kallon tsaf yace "To babu wanda zai roƙeta ta taimaka, saboda duk abinda kika lissafa ta yi a wancan lokacin to itace ta ga dama ta yi babu wanda ya roƙeta, idan kuma har muna da abinda zamu iya sayarwa to zamu sayar mu biya buƙata ba tare da mun roƙi kowa komai ba”.
Mama Hauwa ta taɓe baki tace “ Na rasa irin wannan so da fifiko da kake ba Afrah fiye da kowa”.
Mallam Mahmud ya saki tsaki yace “ Dole na sota yarinyar da ta sadaukar da kanta domin yi min biyayya, duk kuma cikin yayan naki sai ki gaya min wanda ya taimake ni wajen samun wani abu na rayuwa, kuma an gaya miki su nake ajema kayana, dukiyata ce kuma ina da damar yin abinda naga damar yi da su, Afrah ya ta ce abar alfaharina kuma sanyin idaniyata ba dukiyata ba ni kaina zan iya saida kaina domin Afrah ta samu lafiya”.
Ɗif mama Hauwa ta yi ta na jin me ma yasa tayi wannan maganar, da ta haƙura ta danne damuwarta da kunnuwanta ba su samu damar jin waɗannan mugayen kalaman nasa ba da suke neman tarwatsa zuciyarta, yayanta duka basu kai darajar rabin Afrah ba a wajen mallam Mahmud. Jiki a sanyaye ta tashi ta shige ɗaki.
Mallam Mahmud yasan musaddiƙ na can cikin damuwar yadda za’a samu kuɗin aikin Afrah wanda idan aka biya kuɗi yau gobe zasu shiga da ita emergency a yi aikin a ciro abinda ke cikinta. Hakan yasa a daren ya tashi ya koma asibitin da kuɗin aikin.
Bai tadda Musaddiƙ a asibitin ba duk da dare ya yi yana can fafutukar samun kuɗin. Hakan yasa da kansa ya kira musaddiƙ akan ya dawo suje a biya kuɗin aikin. Tun a hanyar dawowarsa musaddiƙ ke rusar kukan murna, yana jin duk duniya baida kamar kawunsa da Innarsa haƙiƙa dangin uwa abin rufin asiri ne, halinsu da banne. Ko a gaban mallam mahmud ɗin zubewa ya yi ya cigaba da kuka kamar ƙaramin yaro daƙer suka shawo kansa ya yi shuru. Sai da mallam mahmud ya tabbatar da ya sami natsuwa sannan suka wuce wajen biyan kuɗin suka biya, an tabbatar da cewa ƙarfe shida na safe za’a yi ma Afrah aiki.
A ranar musaddiƙ a cikin masallaci ya kwana yana yi ma Afrah addu’ar samun dacewa. Ƙarfe shida da minti biyar aka gama shirya Afrah, hannun musaddiƙ na cikin nata har ƙofar ɗakin tiyatar kafin hannun nasa ya zame daga nata aka shige da ita, musaddiƙ ƙasa ya durƙushe ya rasa duk wani ƙarfin guiwarsa, mallam mahmud ya matso ya dafa shi yana ƙoƙarin ƙarfafa masa guiwa, ita kam Inna Halima tana gefe ɗaya kuka take itama sosai tana addu’ar Allah yasa suna da rabon ganawa da Afrah………………………


Yar gidan Imam✍️
MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
( mrs Aliyu Mayere )

Page 17


Tunda aka shiga da Afrah ɗakin tiyata, Musaddiƙ yake kai gauro ya kai mari a ƙofar ɗakin, duk ya yi wujuga wujuga, babu irin addu’ar da baiyi ba, gaba ɗaya har yawun bakinsa sai da ya ƙafe.
Mallam Mahmud ya taso daga kan kujerar da yake zaune ya ƙaraso inda musaddiƙ yake, hannunsa yasa ya janyo shi, babu musu musaddiƙ ya biyo shi har zuwa wajen kujerun ƙarfen da ke girke a wajen ya zaunar da shi, lokaci ɗaya ya juya gefen da robar ruwan da ya sha ya rage take, ya ɗakko ya buɗe ya miƙa ma Musaddiƙ, tabbas yana buƙatar ruwa saboda irin zafin da zuciyarsa take masa, don haka da sauri ya amsa ya kafa kai sai da ya shanye tas sannan
ya yi ƙasa da robar. Mallam Mahmud ya ƙara dafa kafaɗarsa yace “Duk abinda ya samu bawa ka sani ƙaddara ce daga Allah, yakamata ka sassauta ma kanka wannan damuwar, ka yi ƙoƙari ka zama namiji, da ba haka kake ba kana da jarumta amma yanzu duk ka bi ka sukurkuce, don Allah ka tattara hankalinka waje ɗaya ka samu natsuwa”. Inna Halima daga gefe ta amshe maganar tana ƙoƙarin goge hawayenta tace “ Gaskiya ne, duk da dai damuwar yin kanta take, amma ka sassauta don Allah”.
Shuru kawai ya yi yana jin zafin da zuciyarsa take, ya kasa cewa uffan.

An ɗauki tsawon lokaci kafin a fito da Afrah daga ɗakin tiyata, anyi nasarar ciro yarinya sankaceciya mai kama da mahaifinta, babu wanda ya bi ta kan jaririyar, duk kan Afrah su kayi musamman Musaddiƙ da ya kama gadon da ake gungurata ya riƙe ƙam, bai saki gadon ba sai da likita ya dube shi yace “mu je office muyi magana”, a sanyaye ya sakin gadon ya wuce ya bi bayan likitan, a yayin da Mallam Mahmud ya bi bayansu, Inna Halima kuma ta bi su Afrah zuwa ɗakin da aka ware mata.
Zaman dirshan musaddiƙ ya yi akan kujerar office ɗin likitan, mallam mahmud ya jingine jikinsa a jikin bango gami da harɗe hannayensa a saman ƙirjinsa ya ƙagu ƙwarai ya ji bayanin da likita zaiyi. Wanda baiyi magana ba har sai da ya kammala cire rigar da ya fito tiyata da ita ya koma ya zauna sannan ya fuskance su sosai, ya gyara zamansa ya fara magana cikin natsuwa yace “Mun samu ciro abinda ke cikin matarka lafiya, sai dai ina mai baƙincikin sanar da ku cewa ya zama dole sai anyi ma matarka dashen ƙoda saboda babu sauran wani amfani a gare su ko nace ƙiris ya rage ta kai stage 5 yanzu tana stage 3b zuwa stage 4, duka a wamnan stages ɗin ana yin dashen ƙoda ko ayi dialysis, amma mu a shawarar mu dashen ƙoda ya fi zama tsaro fiye da a yin dialysis ya kuma fi samun lafiya da rashin wahalarwa, samnan dashen shine zaisa mutum ya yi rayuwa mai tsawo saɓanin dialysis da ako wane lokaci mutum na iya rasa rayuwarsa, saboda haka mu na ba da shawarar kafin ta ƙarasa stage 5 a yi hanzarin ceto rayuwarta ta hanyar yi mata dashen ƙodar, idan ba haka ba gaskiya babu sauran wata rayuwa a gareta”.
Duka suka haɗa baki suna faɗin “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”. Gaba ɗaya kai Musaddiƙ ya dafe yana cikin wani irin tsananin tashin hankali mara misaltuwa, cikin ƙarfin hali mallam Mahmud ya tako da ƙafafunsa da suka yi sanyi daƙer yake takawa, ya dafa hannayensa a teburin likitan , cikin rawar murya yace “ likita, yanzu kamar nawa ne ake nema domin yi mata aikin? Sannan ana yin irin aikin a nan gida Nigeria?”.
Likita ya gyaɗa kai yace “Eh an sami cigaba, domin a yanzu ana yin dashen ƙoda a Nigeria a asibitoci kamar su, st. nicholas hospital legos da legos state University teaching hospital da Aminu kano teaching hospital akwai ibadan univasity college hospital. Sannan akwai zenith medical & kidney center Abuja wanda a zahiri ya fi duk sauran asibitocin kyau da iya aiki don duk wanda ke da wannan matsalar mu kan mu can mu ke ba shi shawarar ya je , 2011 suka fara yin dashen ƙoda kuma ba’a taɓa samun wata matsala ba ko kuskure”.
Ya ɗan numfasa gami da kallon Musaddiƙ wanda har cikin zuciyarsa tausayinsa yake ji sosai domin tun kwanciyar Afrah a asibitin yana ganin irin yanayin da yake ciki kullum na tashin hankali da damuwa, ya maido da kallonsa ga Mallam Mahmud ya cigaba da cewa, “ƙuɗin aikin da asibitin zenith ke karɓa nera miliyan bakwai ne da dubu ɗari uku, akwai kuma wasu kuɗin na gwajin ƙodar da ta dace da ita da kuɗin magunguna wanda sai kun je asibitin zaku sani, alhakkin samo ƙodar kuma yana hannun team ɗin masu dashen ƙodar, itama kuma sai anyi mata gwajin ko jikinta ma zai iya karɓar dashen, da kuma gwajin da za’ayi na gano jerin da irin ƙodarta ta ke”.

Taga taga Mallam mahmud ya yi yana neman ya faɗi, musaddiƙ yasa hannu ya ruƙo shi, duka babu abinda suke maimaitawa sai miliyan bakwai, a wannan halin da suke ciki ko dubu bakwai babu mai shi a aljihunsa.
Daga musaddiƙ har mallam Mahmud sun faɗa wani mugun yanayi mai wuyar fassara, hawayen ma ya ƙafe a idanun musaddiƙ sai wani gululun abu da ya tokare maƙogwaransa. Cikin tausayawa likitan ya cigaba da yi musu nasiha gami da ƙoƙarin kwantar musu da hankali. Idanu jajir Musaddiƙ ya ɗago ya dubi likitan yace “ zuwa tsawon wane lokaci ake da buƙatar yin wannan aikin”. Likita yace “ Babu wani lokaci ƙila dai wata ɗaya da kwanaki, idan kun shirya kuma zamu iya kiran zenith hospital mu sanar da su, mu kuma mai da ku can Abujan”. Ɗif duka sukayi kafin daga bisani a daddafe suka fice da ga office ɗin ba tare da sun ba likita amsar tambayarsa ba, cike da matuƙar kaɗuwa suka shiga ɗakin da Afrah take, sai a lokacin Musaddiƙ ya dubi abinda aka haifa masa, tana hannun Inna Halima, yana ƙoƙarin wucewa wajen Afrah, Inna Halima ta miƙa masa jaririyar, sai da ya yi jim kamar ba zai ƙarɓeta ba, mallam Mahmud yace “ka karɓi yarka ka yi mata addu’a kayi mata huɗuba”.sannan a sanyaye yasa hannu ya amsheta ya ƙura mata ido yana jin ƙaunarta har cikin zuciyarsa, ya yi mata addu’a sannan ya yi mata huɗuba da sunan Inna Halima. Gefen gadon da Afrah take kwance ya je ya zauna yana rungume da Halimatu, ya maida idanunsa kan Afrah, idanunta a buɗe suke tana ji tana kuma ganin komai, sai dai har yanzu allurar da akayi mata bata saketa ba domin ba ta iya motsa daga saman cikinta zuwa ƙafafunta.
Ta kafe musaddiƙ da ido, duk da halin da take ciki to fa tana tausayin musaddiƙ, ya kara mata Halimatu a jikinta, cikin wani mawuyacin hali ta saki ɗan wani murmushi, tana jin ko yanzu Allah ya ɗauki ranta to ta gama cika burinta tunda ta kawo yar musaddiƙ duniya, ta maida idanunta ta rufe domin bata son ganin damuwar da ke lulluɓe kan fuskarsa. mallam mahmud ya dubi Inna Halima yace “zo nan Halima”. Ya wuce zuwa waje ita kuma ta bi shi da sauri jikinta na rawa domin ta ji a jikinta a kwai damuwa.
Cikin tashin hankali ya gama sanar da ita komai, hannu kawai ta ɗora aka tana tsuma tana maimaita wannan makuɗan kuɗi da tunanin inda za’a samu wannan kuɗin, mallam mahmud ya shiga ƙoƙarin kwantar da hankalinta, da ƙarfafa guiwar Allah zai rufa asiri.Inna Halima cikin kiɗima tace “Yanzu yaya menene abin yi?,maganar kuɗin nan suna da yawa ina zamu samo su?”.
Mallam Mahmud ya saki numfashi yace “Tashin hankalin kenan, damuwata ta ƙara tsananta, ina ƙoƙarin rufewa ne kawai saboda na ƙarfafa guiwar Musaddiƙ, ina cikin damuwar yadda zanyi a samu kuɗin, ba ni da kuɗi Halima ba ni da su”,ya ƙarasa magana cike da gazawa, Inna Halima ta gyara tsaiwarta ido jajir tace “Yaya kaje kayi tunani, idan akwai ragowar wasu kadarorinka sai a haɗa a sayar, ni ma abinda ya rage min duk zan sayar, sai mu ga abinda zamu iya tarawa, don dai kasan musaddiƙ baida wani abu shi yasa damuwarsa take yin yawa”, mallam Mahmud ya daidaita tsayuwarsa yace “Hakane Halima Allah yasa mu dace, ya rufa mana asiri duniya da lahira”…………

Kwana takwas da haihuwar Afrah, jikinta da ɗan sauƙi, Har asibitin Haj Hudah ta zo ta ga abinda ta haifa da kaya akwati guda na jaririya da kuɗi dubu ɗari. A ranar Mama Hauwa tana asibitin, haka ta saki baki tana kallon ƙaton akwatin Inna Halima na ɗaga kayan tana bi da kallon mamaki, lokaci ɗaya zuciyarta na bijiro mata da wani tunani na daban, tasan kyautar irin wannan kayan a wajen mutum kamar Haj Hudah yar majalisa ba wani abu bane, amma tambayar da take yi ma kanta shine, wane irin matsayi musaddiƙ ya ke da shi a wajenta da har take ɓarnatar da dukiyarta akan duk wani abu da ya shafe shi?. Wace irin alaƙa ce tsakaninsu?, anya kuwa babu lauje cikin naɗi?, irin wannan kyautatawa da ɓarin nera da Haj Hudah ke yi ya yi yawa, sannan me yasa ba ta ga wani jindaɗi ko farinciki ba a fuskar musaddiƙ a lokacin da ta kawo kayan, maimakon hakama tun kafin Haj Hudah ta tashi tafiya, musaddiƙ ɗin ya sulale yabar ɗakin, sannan wane irin shauƙi take gani a fuskar Haj Hudah a duk lokacin da ta dubi fuskar musaddiƙ?, sannan me yasa da Haj Hudar ta fahimci musaddiƙ ɗin yabar ɗakin, duk ta canja fuska damuwa ta bayyana a fuskarta?, tana kuma gane cewa yabar ɗakin itama ta tattara ta tafi?. Tabbas da zata samu wanda zai bata amsar tambayoyinta da ta jidaɗi ta kuma gano bakin zaren, amma har ta bar asibitin bata samu amsar tambayar ta ba ko ɗaya, haka ta koma gida cike da saƙe saƙe a ranta.

Duk a cikin waɗannan kwanakin Musaddiƙ fafutukar neman yadda za’ayi yake yi,amma ya rasa wace hanya zai bi domin ganin ya samu kuɗin aikin Afrah, ya tuntuɓi Murtala ko akwai hanyar da za’abi a samu kuɗin, amma iya hangen murtala baiga mafita ba, illa shawara da ya ba shi akan ya je ya tuntuɓi Haj Hudah domin ita kaɗaice yake da yaƙinin zata iya taimaka masa, idan kuma ba zata iya bada duka kuɗin ba yana da tabbacin zata iya nemo masa taimakon a gomnatacce, sam musaddiƙ baya son ya gayama kowa halinda yake ciki da Haj Hudah, don haka nuna masa kawai ya yi tunda tana yi masa baya son ya ƙureta, shi yasa bazai iya kai mata wannan koken nasa ba.
Ga abubuwa sun ƙara zafafa domin kullum ƙara cin kuɗi ake a asibitin, wanda Allah ne kaɗai yake rufa asiri, hatta Halimatu wacce suke musaddiƙ ke yi mata laƙabi da Hanan saboda girmama me sunan, tunda aka haifeta ake cacar sayen madara saboda babu ruwan nonon da zata sha.

Mama Hauwa tana tsugune akan tabarma, fuskarta tamke cikin fushi da ɓacin rai, tamkar wacce akayi ma wani gagarumin laifi. Zaune kan tabarmar Mallam Mahmud ne, gabansa ƙuɗi ne masu yawa

Please Login or Register in order to submit comment