Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata ciki ba.
Likita ya dubi Musaddiƙ yace “ ka yi haƙuri babu wani abu da muka isa mu yi ba tare da amincewarta ba”, ya na gama faɗin haka ya buɗe ƙofar ɗakin ya fice, cikin jin zafi da fushi Musaddiƙ ya dubi Afrah, ita kuma ta yi saurin kau da kanta domin ba zata juri ganin damuwar da ke cikin idanunsa ba, ya kasa magana sai kallonta da yake yi yana jin kamar ya yi mata kaca kaca amma ba zai iya ba, bai taɓa zaton Afrah ta na da kafiya haka ba, duk kallon mace mai sauƙi yake mata amma yau gaba ɗaya ta goge masa hadda. Shi ma ficewa ya yi ya na son ya sami wani keɓaɓɓen waje da zai je ya zauna ya yi kukansa sosai, ko ya samu sauƙin damuwar da ke damfare a cikin zuciyarsa. Itama can Afrah kukan take ta fi jin zafin yadda ta karyama Musaddiƙ zuciya fiye da abinda ke faruwa da ita domin dai tasan komai daga Allah ne ta kuma yarda da ƙaddara, mutuwa kuma tasan babu wanda zai tsallake sai dai idan lokacin mutum baiyi ba, don haka kare cikinta da kawo shi duniya shi ne abu na farko dake gabanta a yanzu.

Har aka sallami Afrah daga asubiti babu wani jituwa tsakaninta da Musaddiƙ, domin duk hanyar da zai bi ta yarda a cire cikin ya bi amma ta ƙi yarda, don kuwa har Mallam Mahmud da Inna Halima ya kawo mata asibitin suka yi zama na musamman, amma fa Afrah ta ƙi yarda maimakon hakama cikin sani da hikimar iya zance irin na ta ta sami nasarar karkato da hankalinsu suka kuma yarda da cewa faɗen likita ba faɗen Allah ba ne, sannan Allah ba ya ɗorawa rai abinda ba zata iya ɗauka ba, don haka ya ga zata iya ne yasa ya bata cikin, idan kuma ta rasa ranta a wannan sanadin tabbas ta yi shahada ne, mutuwa kuma dama tana kan kowa.
Zuciyar musaddiƙ ta yi zafi ta yi ƙuna yadda yake ganin kowa ya kasa fahimtarsa, sun kuma kasa gane mugun halin da zai shiga idan ya rasa Afrah, wani ƙarin damuwar ma shi ne yadda yanzu ne ya ji yana sonta so na ban mamaki, yana ji aransa matuƙar ya rasa Afrah to sai dai ayi gawa biyu, don tabbas zai iya bin ta shi ma.
Nan da nan ya rame ya fita kamanninta, damuwarsa ba ta ɓoyuwa ako’ina, duk yadda Afrah ta so ta kwantar da hankalin musaddiƙ to yaƙi ba ta dama, don fushi yake yi da ita sosai.

Iya kulawa dai kam musaddiƙ ya na ba Afrah, ko da yake cikin fushi ko ya ya tace wani abu na yi mata ciwo zai kwasheta zuwa asibiti, ciki kam ya zo da lalura domin kullum Afrah cikin ciwo ta ke mai tsanani, ga watannin ciki sai gaba suke tun Musaddiƙ na sa ran Afrah zata haƙura ta bari a cire cikin har ya saduda, ya rungumi ƙaddara ya fauwalama Allah komai kamar yadda Afrah ta fauwala masa, kullum cikin addu’a yake da sallar dare baida wata buƙata data wuce Allah ya ja masa da kwanan Afrah, Allah ya sauketa lafiya, dole ya sakko daga fushin da yake yi, domin baya son ganin ta cikin damuwa ya kuma fahimci fushin da yake yi da ita yana jefata cikin damuwa, ya rungumi matarsa, tausayi da ƙaunarta sun rinjayi fushinsa. Ji yake hatta numfashi kamar ya yi mata, shi yake yin komai a gidan, ko ta ɗan sami ƙarfi tace zata yi wani abu baya bari, ta zama tamkar sarauniya.
Hatta Mama Hauwa a wani zuwa da tayi gaidata, tsayawa tayi ta sama sarautar Allah ido, ta zuba tagumi tana kallo gami da kakabin yadda musaddiƙ ya zama bawan Afrah.
Sai tsuma da rawar jiki yake yi, komai tana daga kwance shi yake yi mata, ta dai ƙare ta dube shi tace “ Ikon Allah, sannu Musaddiƙ da ɗawainiya”, ya ɗago cikin murmushinsa yace “sannu Mama”, ta jinjina kai tace “ yau ba ka da aiki ne?”, ya ɗan dubeta yace “ Ai yanzu ba kullum nake zuwa ba, saboda bana son ina barinta ita kaɗai, nafi so koma menene ace ina kusa da ita”.
Mama Hauwa ta yi jugum zuwa can tace “ lalle ka cika mijin marainiya”.
Har Mama Hauwa tabar gidan zuciyarta cike take da kakabi, lalle Afrah ta yi dace da miji na nunama sa’a, tana tafe tana jin wasu siraran hawaye na fita mata, na takaici da ƙarin nadamar yadda rashin rawakkali da kuma rashin hangen nesanta yasa ba Na’ima bace yanzu a wannan gurbin.
Har cikin zuciyarta tana jin dama Na’ima ce a wannan matsayin ba Afrah ba, lalle son zuciya ɓacinta, ta kai hannu tana sharar hawaye, tana tunanin yadda zata yi da Na’ima da har zuwa wannan lokacin babu ƙwaƙƙwaran saurayi balle ayi maganar aure.
Ko sallama da ita ba’ayi haƙiƙa wannan lamari yana tayar da hankalin mama Hauwa, musamman yanzu da gaba ɗaya itama Na’iman ta canja, ko kaɗan bata jin daɗin zama da ita.
A ɗan wannan lokacin bata isa tace tashi rana koma inuwa ba, ta dinga zumɓure zumɓuren baki kenan tana ƙunƙuni abinda duk duniya mama Hauwa ta ƙi jini kenan ga yaro.
Ga uwa uba Mallam Mahmud ta lura har yanzu yana da ƙullinsu a zuciyarsa, domin yadda gaba ɗaya baya bi ta kan duk wani lamari na Na’ima, tsakaninsa da ita ta gaishe shi ya amsa.
To yanzu ne Mama Hauwa ta fara jin damuwa akan hakan.
Abubuwa duk sun juye ta inda bata taɓa tsammani ba, danasani kawai take yi, bata taɓa yi ma Afrah fatan samun miji irin Musaddiƙ ba domin bata son ta huta amma ya ta iya, haka Allah ya tsara babu kuma mai iya warwarewa.

Haj Hudah ta ƙara gyara kwanciyarta akan makeken gadonta mai barazanar cinye duk faɗin ɗakin, ba wani zafi ake yi ba, saboda tun shekaranjiya alamun shigowar sanyi ya nuna, amma zafin da take ji a cikin jikinta na danuwa yasa gaba ɗaya ta ƙure A.C ɗin ɗakin, fuskar wayarta ta ƙurawa ido, inda hoton Musaddiƙ ya bayyana cikin fara’a ya yi kyau har ya gaji , kwana uku kenqn bai samu ya zo aiki ba, amma ji take kamar shekara uku ya yi. Kuka take sosai tana jinta a cikin jerin matan dake cikin ƙuncin rayuwa, duk da rufin asiri data ke da shi, bata nemi komai ta rasa ba amma soyayya ta maidata fakira mara komai tana jin tamkar duk duniya babu wanda ya kaita talauci.
Ta kifa kanta akan wayarta kuka take sosai, ta so da musaddiƙ ta fara haɗuwa kafin Alh yusuf sanda.
Zuciyarta ta yi rauni da yawa bata da wani tunanin da ya wuce na musaddiƙ, don haka ya zama dole ta sanar da shi abinda ke cikin zuciyarta ko da hakan na nufin faruwar wani mummunan abu, domin nauyin soyayyarsa ya yi ma zuciyarta yawa, dole ta na buƙatar taimakonsa.

Don haka ta shirya sanar da shi komai, ta dafe kanta da yake sarawa, ɗayan hannun kuma ta dafe gefen zuciyarta da yake bugawa da saurin gaske, bakinta ya yi mata ɗaci, sai alokacin ta tuna yau tun abincin safe babu komai a cikinta sai ruwa.
Lalle so guba ne, ta zuro ƙafafunta ƙasa ta, dai dai ƙarfe goma da minti shida na dare, tana sha’awar ta sha ko da madara ne ko ta samu bacci ya ɗauketa.
Zaune a kqn kujera ta tadda Alh yusuf sanda ya ɗora kafafunsa a saman tebur ɗin gabansa, yana riƙe da rimot ya danna wannan tasha ya cire ya maida wannan tasha, sai dai kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci cewa gaba ɗaya hankalinsa ba kan talabijin ɗin yake ba, yana can duniyar tunani.
Motsin fitowar Haj Hudah yasa ya dawo hayyacinsa, ya juya yana kallon yadda take tafiya tamkar kazar da ƙwai ya fashema a ciki.
Ya jinjina kai yana cigaba da kallonta harta buɗe frij ta ɗakko hollandia ta juya zata koma ɗaki kenan, muryar Alh yusuf sanda ta dakatar da ita, “ Haj zo mu yi yar wata magana”.
Juyowa ta yi ta dawo ba tare da tace uffan ba, ta zauna tana kallonsa, a hankali tace “ Lafiya dai ko”.

Yace “Lafiya lau, magana dai zamu yi”

Ta aje hollandia a saman tebur tana ƙoƙarin gyara zamanta.

Tace “ To ina jinka”,

A hankali ya aje rimot ɗin hannunsa ya miƙe ya nufi wani ɗan lungu dake cikin falon ya ɗakko wani ɗan madaidaicin akwatin magunguna, tun kafin ya dawo ya zauna Haj Hudah ta canja fuska, domin ganin akwatin a hannunsa.
Ya dawo ya zauna gami da buɗe akwatin ya kwaso wasu kwalayen magunguna ya buɗe ya fito da su babu guda ɗaya da aka buɗe aka sha.

Ya ɗago idanunsa ya ɗora akan nata a yayinda ta kauda kanta.

“ me yasa ki ka daina shan maganinki”

Ya tambayeta fuska tamke,

Haj Hudah ta yi shuru gami da sadda kanta ƙasa, harga Allah bata son yin wata doguwar magana yanzu, domin halinda take ciki ya fi na tuhumar da Alh yusuf sanda yake mata.

Ta ɗago ta dube shi, fuska ba yabo ba fallasa tace”Don Allah mu bar wannan maganar sai zuwa gobe”.
A fusace cikin ɗaga murya yace “ me yasa zamu bari sai gobe, yanzu nake son sanin dalili, na haƙura na jure irin canjawar da kika yi tun bayan cin zaɓenki, to amma bazan juri wannan ba, ya zama dole ki gaya min dalilinki na daina shan waɗannan magungunan……….




Yar gidan Imam✍️
MUSABBABI BOOK 2

NA


HABIBA ABUBAKAR IMAM
( mrs Aliyu mayere )

Page 13


Cikin tsananin mamakin yadda Alh yusuf sanda yake ɗaga mata murya ta dube shi da idanunta da suka fara canja launi, sannan tace, “ ka daina yi min ihu aka, don banga dalili ba, magani na daina sha, don na gaji da ɗurawa cikina ƙwayoyi bayan ko na sha babu abinda zai taimake su wajen yin aikin da ya kamata su yi”, ya aje wani nannauyan numfashi yace “ kina nufin kice a yanzu baki da buƙatar haihuwa tare da ni?”, da ace zata iya buɗe baki ta gaya masa gaskiya to da ta sanar da shi, hakane bata da sauran wata buƙatar haihuwa da shi, domin yanzu ba shi ne a zuciyarta ba ba shi take so ba.
Jin tayi shuru ta kasa magana yasa Alh yusuf sanda ya dawo kusa da ita ya zauna ya na yi mata wani irin kallo sannan yace, “ me ke faruwa ne Hudah, me ke damunki, me yasa ki ka canja?”, nan ma shuru ta yi tana jin wani irin ƙunci a zuciyarta.
Ya ƙara matsantarta yadda suna iya jin bugun zuciyar juna.

Yace “ kin canja, matuƙar canjawa

Ki gaya min me ye tunaninki?”

Nanne ta ɗago ta dube shi tace “ wane tunani kuwa gare ni, kawai na ga gara abar ma Allah ikonsa”.

Ya runtse idanunsa ya buɗe ya ƙara tarwatsa su kan fuskarta yace “ Amma kin fi kowa sanin lalurarki ta rashin haihuwa waɗannan magungunan kuma sune zasu taimaka wajen samun cikinki, tuntuni kina sha ba tare da wata matsala ba, to me yasa yanzu rana tsaka zaki daina sha, bayan da ga ni har ke haihuwar muke nema, ko ma menene wannan ba abinda za kiyi wasa da shi ba ne”, ta yi shuru na ɗan wasu daƙiƙai sannan tace “ Idan na sha magani kana tare da ni ne balle kayi abinda ya kamata asamu cikin, kawai na gaji da sha na kuma daina wahalar da kaina, ina fatan kuma ba zaka takura min don na cigaba da sha ba, kasanni kasan halina ka kuma san kafiyata akan abu”.

Tana gama faɗin haka ta miƙe ta ɗauki hollandia ɗinta ba tare da ta ko dube shi ba ta yi shigewarta ɗaki.
A yayinda ya bita da wani mugun kallo tana ɓacewa ganinsa ya koma ya zauna sosai yana wannan murmushin nasa kai ba kace shi ne wannan da ya haɗe rai yake muzurai yanzu ba.

Ya janyo kofin lemonsa ya cigaba da kurɓa yana girgiza ƙafa.

“Hudah, Hudah”, ya ambaci sunanta a fili a hankali, sannan ya ƙara murmusawa yace “ ƙaramin tunani gare ki Hudah, ko kina tsammanin bansan ainihin dalilin da yasa baki son ki haihu da ni ba ne yanzu, kamar yadda nake ganin baki san dalilin da yasa nake son haihuwa da ke ba, wanda a yanzu na sami hanya mafi sauƙi na cikar burina, don haka ko ki haihu da ni ko kada ki haihu da ni duk ɗaya, wai mamaci ya karye. Ya yi wata doguwar miƙa, a hankali yace “ Allah ya kai damo ga harawa”………..

Cikin Afrah ya yi girma cikin wahala da jigatuwa, kullum suna hanyar asibiti, yanzu kuwa da cikin nata ya kai kusan wata takwas, gaba ɗaya sai Afrah ta ƙara zama abin tausayi, domin kuwa wahalar tafi ta kullum, kusan kullum Inna Halima na gidan Afrah, a yayinda Mallam Mahmud ya shiga damuwar da a ko yaushe yake ƙoƙarin ɓoyewa domin baya son sagar da guiwar musaddiƙ da damuwarsa ta ƙara yawa, kullum ya na cikin sallar dare tare da roƙarma Afrah sassauci a wajen Allah, duk da a tsorace yake domin kuwa yasa maganar likita a ransa ƙwarai da gaske, ya kasa cire damuwa ko fargaba a ransa.

Ranar wata talata, Musaddiƙ na gidan Haj Hudah yana zaman jiran fitowarta domin tana da wani taro da zata halarta na mata, amma a zahiri yau itace ranar da Haj Hudah ta sha alwashin sanar da musaddiƙ gaskiyar zuciyarta.
Ta ɓata lokaci mai yawa tana kwalliya ta ɗaukar hankali.
Kafin ta fito ne, musaddiƙ na zaune a fararen kujerun da ke girke a harabar gidan, hakanan yake jin faɗuwar gaba da tsoro hankalinsa gaba ɗaya ya karkata wajen tunanin wane hali Afrah take ciki, domun yasan duk duniya babu abinda zai sa shi cikin wannan halin sai idan Afrah na cikin tashin hankali da damuwa. Yana ƙoƙarin fito da wayarsa ya kirata ne ya ji wayar tasa ta ɗauki ƙara da sauri ya ɗauka ganin sunan Inna Halima ya bayyana a allon wayar tasa. Cikin ɗimauta take sanar da shi suna asibiti da Afrah jikinta ya tashi matuƙa, itama ta je domin ta dubata ne ta taddata cikin mawuyacin hali, shi ne ta wuce da ita asibitin da take zuwa.

Nan da nan hankalin Musaddiƙ ya tashi, domin ko wayar ba su gama ba ya kashe wayar, ba tare da ya damu da komai ba ya wuce da sauri ya fita, kai tsaye asibitin ya wuce, sai dai ya tadda Afrah cikin mawuyacin hali bata ko gane wanda ke kanta, yadda numfashinta ke wahalar fita dole aka sanya mata oxcigine, na’urar dake taimakama numfashi. Gabanta Musaddiƙ ya zube gaba ɗaya duk ya gama karaya, kuka yake sosai kamar ba namiji ba.
Inna Halima cikin damuwa ta dafa kafaɗarsa tace “ Haba Musaddiƙ me yasa tun bayan samun lalurar Afrah kuka baya yi maka wahala, bayan a da kafin aga kukanka sai an yara, ka daure ka samu natsuwa mana, komai fa nufin Allah ne”, ya girgiza kai yace “ Inna irin abinda nake nunama Afrah kenan, tun farko ta bari a cire cikin nan saboda hatsari ne a gare ta amma ta ƙi, ta zaɓi mutuwa da rayuwarta, saboda kawai ta kawo ɗa na duniya, saboda me zata min haka, waye ya bata wannan damar, bayan tasan itace komai nawa”.
Inna Halima ta saki numfashin tausayi da damuwa tace “ kayi haƙuri, babu wanda ya isa ya canja abinda ke rubuce acikin ƙaddarar bawa, don haka mu fauwalama Allah komai, sannan muyi addu’a”. Ya janyo hannun Afrah ya riƙe ƙam yana kallonta, cikin wata siga nai ban tausayi.

Fitowar Haj Hudah cikin takun ƙasaita, ita kanta tasan ta yi kyau matuƙa da gaske, ta ƙosa ƙwarai ta ƙarasa wajen musaddiƙ ya ganta, domin dai yau za’ayita ta ƙare. Amma ga mamakinta tana ƙarasawa harabar gida bata ga musaddiƙ ba, ta shiga juya idanu alamar nemansa amma bata gan shi ba, a hankali ta kira ɗaya daga cikin security ɗinta ta tambaye shi ina musaddiƙ, anan ya tabbatar mata da ya fita tun ɗazu. A harzuƙe ta maimaita “ ya fita?”, ya gyaɗa kai yace “ Eh”, ɗauke wuta ta yi ta ji zuciyarta na yi mata wani irin zafi, musamman da ta ɗakko waya ta shiga kiransa, amma ta kira shi ya fi sau goma babu waya ɗaya da ya amsa. Ji tayi jiri yana fisgarta.

“Haj, a matso da motar nan ne”

Cewar direban cikin ladabi

Ta dube shi ido jajir tace “ Eh”
Bata jin zata iya komawa cikin gidan, tana buƙatar samun nutsuwa domin yadda take jin zuciyarta na tafasa, shin ina musaddiƙ yaje ba tare da izini ko saninta ba?. Abinda ba ya yi.
Direba na ɗaukarta kai tsaye umarnin ya kaita gidansu ta bashi. Ko da suka ƙarasa gidan, haka ta shiga fuska turɓune cike da damuwa, Haj shafa’atu kyakkyawar macece wacce a yanzu kiɓa ta maida kyawun nata muni, saboda irin muguwar kibar da ta yi, domin kuwa daƙer take iya motsawa. Tana daga zaune kan wata luntsumemiyar kujera ta miƙama Haj Hudah hannu, ta riƙeta kam lokaci ɗaya ta faɗa kan jikinta ta kwanta sosai gami da runtse idanunta.

“ ki na da damuwa ko Hudah”

Cewar Haj shafa’atu tana ƙoƙarin ƙara rungumeta.

Ido ta ƙara runtsewa tace a hankali “sosai kuwa mummy”, Haj shafa’atu ta shafi saman kanta tace “ Nasan hakan, domin bazan taɓa manta irin yanayin da ki ke shiga ba idan kina cikin damuwa”
Jin bata da niyyar magana yasa Haj shafa’atu ta cigaba da cewa “ Na ɗauka ai baki da sauran wata damuwa Hudah” ananne tace “ Ina da ita mummy ina da damuwa”, Haj shafa’atu ta juyota tana kallon fuskarta tace “ menene kuma yanzu, ina dai fatan ba damuwar Yusuf bace ta ƙara kunno kai”.
Ta yi jim! Tana jin ba zata iya gaya mata danuwar da take ciki ba, domin tayi imani idan ta sake ta faɗa mata sai ta ci mata mutunci sai ta ganar da ita kuskurenta, domin tafi kowa sanin Haj shafa’atu ba zata taɓa ɗaukar wannan baƙar ɗabi’ar ba, musamman a irin tarbiyyar da take tutuniyar ta ba Haj Hudah, ko siyasa da ta bari ta shiga duk da tasan burinta kenan tun tana yar ƙaramarta, to fa sai da tasa ta tayi alƙawarin killace kanta tare da tsare dokokin ubangiji kafin ta yarda ta faɗa harkar siyasa, to ko ta yaya a yau zata zo mata da saɓanin alƙawarinsu.
Don haka ba ta da zaɓi da ya wuce ta fake da saɓanin da suke samu yanzu da Alh yusuf sanda akan ƙin cigaba da shan maganin da zai taimaka mata ɗaukar ciki, wanda tun daga lokacin da likita ya tabbatar musu da cewa itace ke da matsalar haihuwa, ya ɗorata akan magungunan, haka zalika bata taɓa daina sha ba sai yanzu da take jin ba ta da buƙatar haihuwa da shi.

“ ina tambayarki menene ke faruwa tsakaninki da mijinki”,

Haj Hudah ta tashi ta zauna sosai tana kalkonta, sai yanzu Haj shafa’atu ta lura da irin ramar da Haj Hudah tayi cikin ƙanƙanin lokaci, fuskarta ta yi fayau.
A hankali ta warwarema mahaifiyarta komai, Haj shafa’atu ta ƙura mata ido tana nazarin abubuwa da dama a tattare da ita, sannan ta jefo mata tambayar da ba zata iya bata amsar gaskiya ba, “ Hudah meye dalilin da yasa ki ka daina shan maganin, bayan ada kinfi kowa zumuɗi da addu’ar son ki haihu?”, Haj Hudah ta aje numfashi a hankali tana tattaro abinda zata gaya mata wanda zata gamsu da shi. Daga bisani ta dubeta tace “ kawai mummy na gaji da shan magungunan ne, saboda har yanzu ni banga wani canji ba, shi yasa kawai nabar Allah ya yi ikonsa”.
Haj shafa’atu ta muskuta ta gyara zamanta tana cigaba da kallonta tace “Idan wannan ne tunaninki, me yasa ba zaki kwantar da kanki ki yi masa bayani ba yadda zai samu gamsuwa”, tace “Bai ba ni wannan damar ba”, tace “ To ke ki bashi damar, ki zauna ki fahimtar da shi dalilinki, idan duk bai gamsu ba to ki cigaba da shan maganin domin samun zaman lafiya, da kuma ba’a san inda za’a dace ba, domin ka da ki manta miji ba abin wasa ba ne, yana da kima da daraja biyayya ake ma miji komai kaskancinsa, ki dinga tuna irin kyakkyawan zaman da na yi da mahaifinki da ko musu bai taɓa shiga tsakanin mu ba, don Allah ki dinga haƙuri da rayuwa”.
Maganganun Haj shafa’atu sun ratsa zuciyar Haj Hudah.
Ta tsaya ta yi shuru gami da zuba tagumi tana jin kamar ta canjama kanta zuciya, domin tabbas itama tasan abinda zuciyarta ke umartarta da aikatawa ba ƙaramin kuskure ba ne , sai dai ya zata yi bayan ba ta da iko da zuciyarta ta, “ kinji abinda nace miki”, Haj shafa’atu ta katse mata tunaninta, a hankali tace “ Na ji mummy”.
Ta ƙara zuba mata ido sannan tace “ko akwai wani abu ne bayan wannan”, a sanyaye ta girgiza kai tace “Babu komai”,
Haj shafa’atu ta canja maganar ta su da cewa “ Ina musaddiƙ yau bazai shigo ya gaishe ni ba ne?”, sunansa kaɗai da aka ambata saida gabanta ya faɗi, dama tasan dole Haj shafa’atu ta tambayi musaddiƙ, domin sun riga sun saba ko aike ne Haj Hudah zata yi gidansu na kayan abinci in dai ba zata sami zuwa ba musaddiƙ ɗin take ba ya je ya kai mata, Haj shafa’atu bata ƙara ƙaunar musaddiƙ ba sai da Haj Hudah ta bata labarin irin zaluncin da Haj kilishi ta yi masa, alokacin har kiransa ta yi ta bashi addu’oi na tsari tace ya dinga yi.
“ ko ba da shi ki ka taho ba yau?”
Haj shafa’atu ta ƙara katse tunaninta, ta yi saurin gyara zamanta tace “ Dashi zamu taho , amma bansan abinda ya faru ba kafin na fito ya tafi, na kira shi kuma babu iyaka amma bai ɗaga wayar ba”, kamar amsar tambayarta, Haj shafa’atu zata yi magana kenan wayar Haj Hudah ta ɗauki ƙara.
Ganin Musaddiƙ ne yasa da gaggawa ta ɗaga wayar, lokaci ɗaya tana jero masa tambayoyi.
Amma jin muryarsa cikin tsananin damuwa da tashin hankali yasa ta yi ƙasa da murya tana tambayarsa abinda ke faruwa.
Sannu a hankali ya gama sanar da ita halin da yake ciki, ya ƙara da cewa “Ina cikin matsanancin tashin hankali Haj, dole sai kin taimake ni, domin ba ni da isasshen kuɗin da zanyi maganin wannan matsalar, domin likita ya tabbatar da cewa nan asibitin Afrah zata cigaba da zama domin nan da makonni biyu zuwa uku

Please Login or Register in order to submit comment