Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

driver ɗaya kuma yana gefen drivern.
Suka tada motar suka miƙi titi ɗoɗar dan daga wajen da suke zaune zuwa fada wani dogon titine ya haɗa, babu ko kwana ɗaya har suka iso ƙofar fada.
*
Tijjani direba ne durƙushe gaban, Turaki, Ciroma da sarki, dukansu sun kasance ƴaƴan sarkin haɗejia Abubakar Masu na da, kuma sarki Abdullahi shine babba a cikinsu, kaf ƴaƴan sarki abubakar ɗin Tafida da Mairama ne kawai babu a ciki, kasan cewar shi Tafida ya rasu, ita kuma Mairama macace, dan wannan maganar bata mata bace.
Tijjani sai juya maganar da Ciroma ya faɗa masa yake, to tayama akayi suka ga ƴar tasa?, kuma me yasa suke san aurawa ɗansu ita ?, kuma wai a yau, yau ɗin nan fa ?, duk waɗannan tambayoyin kansa yakewa, dan bai isa ya furta musu ba.
“Malam Tijjani kayi shiru?”
Tijjani ya ƙara gyara zamansa, ya kuma durkusawa kamar zaiyyi musu sujjada sannan ya furta abinda ya zama sanadin sauyawar rayuwar mutum biyu.
“Shikenan Malam Tijjani, ga wasu kuɗaɗe nan, tunda an saka lokacin auren a ƙurarren lokaci sai ayiwa yarinya abinda ya kamata”
Da rarrafe tijjani ya isa ga Turaki ya karɓi kuɗin, sannan Ciroma ya faɗa masa daidai lokacin da zaizo masallaci.
Haka ya tashi ya fice suna binsa da kallo.
“Yanzu mai martaba kanaga wannan ita kaɗaice mafita ?”
Mai martaba da tun zuwan Tijjani beyi magana ba sai yanxu ya kalli turaki
“Ita kaɗaice mafita Turaki, ita kaɗaice hanyar da zan iya ceto rayuwar ɗan ɗan uwana”
“Hakane, to yanxu shi Tafida yasan halin da ake ciki ?”.
TAFIDA POV.
_“Eshaan”_ muryar ta fito cikin dariyarta, fiskokinta daya saba gani a kullum sune suke giftawa a hankali, a hankali kuma cikin mabanbantan lokuta. Sai kuma hoton wani lokaci da sam baima san ya auku ba, wata mota ƙirar honda civic ta wancan zamani tana juyawa akan titi, tareda wasu mutum biyu a ciki mace da na miji.
_“Eshaan”_ ita ce kalma ta ƙarshe da ta fita daga bakin macen, har ranta ya fita daga gangar jikinta. Daga can wani kogo kuma wani mutum ne, kansa duk ya tara gashi ga wani farin gari zane a gaoshinsa da ɗugon ja a tsakiya yana ta watsa wani abu a cikin wutar dake ci a gabansa.
Sai kuma fuskarta ta dawo tana dariya tareda faɗin _“Eshaan”_*
“Maa!!, Maa!!!”
Sai kuma ya buɗe idonsa, ya kalli inda yake, a cikin ɗakinsa ne na turakar Fulani Khadija, kamar de kullum mafarkine kamar yanda ya saba, a hankali ya fara ƙoƙarin miƙewa, sai yaji wuyansa ya ƙage, hannu ya kai zai taba wuyan nasa, sai yaga wutar nan, daya saba gani a kullum tana ci a tafin hannunsa, hannun ya dunƙule sannan ya buɗe nan take wutar ta b'ace k'arasa miƙewa yayi, dan yashe yake a tsakar ɗakin, yabi ɗakin da kallo.
Gaba ɗaya yau ɗakin a hargutse yake, wasu kayan ma sun farfashe, mikewa tsaye yayi sannan ya ɗaga hannayensa ya shiga meda kayan da suka faɗo ma ajinsu kuma ba tareda ya ta6a komai a cikinsu ba, yana amfani da ƙarfinsa ne, har ya maida komai inda yake sannan yaje gaban mirror ya tsaya yana kallon kansa, sumar kansa duka ta sauƙo kan goshinsa ta barbaje, gabrigar jikinsa duk ta faffarke, ga raunikan dake jikinsa, hannu ya kai ya cire rigar, a hankali ya lumshe idonsa, gaba ɗaya raunukan dake jikinsa suka fara haɗewa da kansu, kamar bai taba rauniba, sai kuma ya buɗe idonsa, wani abun mamaki yau idonsa beyi ja ba yana nan a blue ɗinsa.
Banɗaki ya shiga yayi wanka haɗi da alwala ya fito yayi sallah sannan ya samu ya sauya kaya, yau juma'a kuma yau za'a ɗaura aure, dan haka ya saka wata farar shadda ƙal, kuma sabuwace dan bai ta6a sakawa ba, ya kawo falmara zabuni maroon color ya ɗora rigar an mata aiki da milk ɗin zare, ya saka hula dara itama maroon, ya saka wani farin takalmi halp cover, ya fito a ainahinsa na jinin sarauta, ya feshi jikinsa da turare, ya tsaya yana kallon kansa, kamar shine angon, sai kuma yaji gabansa ya faɗi, amma me yasa ?, kai ba wannan zancen, wani bangare na zuciyarsa ya ayyana ma sa, ya ɗaura digital watch ɗinsa sannan ya ɗauki wayoyinsa ya fita.
A parlo na biyu ya iske Fulani tana tsaye tana bada umarnin yanda za'a gyara mata parlon, sai kace itace take auren ƴar ba Fulani sadiya ba, ya ayyana hakan a ransa, ƙarasawa yayi ya gaisheta ta amsa tana masa ya jiki, dan Nadra ta faɗa mata komai.
“Baki zakiyi ne ?”
“Ba biki muke a gidan ba?”
Ya gyaɗa kansa a hankali
“Hakane”
Ta ɗan juyo tana kallonsa, a kullum Tafida ƙara girma yake haɗi da kyau, ga wani kwarjini da yake ƙarawa saide kuma a bayan wannan kyan, girman da kwarjinin akwai wata fuska, fuskar da babu wanda ya santa sai makusantasa, idanta ne ya kai kan wani rauni dake gefen kansa.
“Akwai rauni a gefen kan ka”
Ta faɗi a hankali kamar ba ita tayi maganar ba, kuma yaji ɗin, dan a zuciya ne kawai mutum zeyi magana in har kana kusa da shi bai ji ba, a hankali ya lumshe idonsa, nan take raunin ya haɗe jikinsa, kamar wajen bai taba fashewa ba, dama haka yake inde har yaji rauni lokacin da baƙin ruhin ke jikinsa to da zarar ya dawo hayyacinsa yana haɗewa inde har rauni bai haɗe ba a jikinsa to ainahin jikinsa ne yaji raunin.
“Ina zaka je baka ci abinci ba? ”
“Asibiti, zanci a can”
Ta gyaɗa kanta
“Kada ka makara sbd ɗaurin auren da za ayi”
Bai san dalili ba, amma tana maganar auren gabansa ya faɗi, hakan yasa ya ɗigawa maganar auren ayar tambaya amma sai ya gyaɗa mata kai, ya kaɗa kai ya fice bayin dake wajen sai gaisheshi suke yana amsawa.
Kamar yanda ya faɗi ɗin asibitin ya tafi yaje sukayi abinda za suyi shida Muktar sannan suka haɗu gaba ɗaya suka wuce babban masallacin juma'a na garin haɗejia, dan duka ƴaƴan sarki a nan ake ɗaura musu aure.
Tsabar cikar da masallacin yayi kwata-kwata basu samu damar shiga ciki ba, a waje suka samu, can kusa da tsohuwar kotu a nan sukayi sallar juma'ar tasu kafin aka sannar da cewa za'a ɗaura auren, sai suka koma kan motocinsu, suna ɗan hira shida Muktar jifa-jifa samari na wucewa suna miƙo gaisuwa, dan Tafida akwaI farin jini matasa.
An ɗaura aure na farko, wanda ya kasance shine auren Amina Abdullahi Abubakar da angonta Adam Isma'il, su Tafida sun samu sunji sanarwar ɗaurin auren ta hanyar lasifikokin dake manne a kowani b'angare na titin masallacin.
Sai kuma akace akwai wani na gaba, kowa ya kasa kunne yana jiran yaji wani aure za'a ɗaura.
Sunan da aka sanar shine ya saka kowa a shock, an ɗaura auren Eshaan Auwal Tafida da amaryarsa Maryam Tijjani Muhammad.
Damm!, gaban Tafida ya faɗi, a hankali ya sauƙo daga kan motar da yake, wasu abubuwa na masa yawo a akai, shifa kansa ya kulle, kamar ma baya ji da kyau, kuma kamar ya kurmance, aure ?, wai aure aka ɗaura masa ?, to waima da wa aka ɗura masa auren ?.
MARYAM POV.
Yau suka tashi da abun mamaki, dan da wajejen ƙarfe sha ɗaya saiga Abba ya dawo, yazo yana ta wata fara'a da suka kasa gane mata, yau rabonsa da kwana a gidan wajen kwana huɗu kenan.
Ya shiga ɗakinsa ya ɗauko kaya yayi wanka ya saka kayan daya sama ɗin rabonsa da ya saka su tun auren Fati, farar shaddace hadda babbar riga (malum-malum), Maanmu da Maryam dai kawai binsa suke da kallo har ya gama ya fice. Har maanmu na zaton kode aure zai ƙara to in ba baka b me zaisa yana wannan abubuwan ?.
Bayan fitarsa saiga Hassan da Hussain sun dawo tareda muhsin ɗin da suka kaɗo shi a waje yana wasa, suma shiryawa sukayi har Maanmu na basu labarin Abbansu yazo ya fita, suma shirin zuwa masallacin juma'a su kayi, kasan cewar babu nisa sosai daga unguwarsu zuwa masallacin fada, domin titine kawai ya taba fadar da masallacin.
Bayan an sauƙo daga masallaci Maryam na alwalal sallar azhar, yayinda Maanmu ke zaune a rumfar gidan nasu tanajin radio, dan ana rahotone na musanman akan bikin ƴar me martaba, Maryam ta gama alwalar ta zo zata shiga ɗaki Maanmu ta tambayeta ƙarfe nawa, ta tsaya ta ɗauki wayar tata akan window tana faɗo mata lokacin sai wani magana da ake a radio ya ɗauki hankalinta, dan haka tayi shuru tana saurare.
_“Bayan an ɗaura auren gimbiya Amina da angonta Adam sai kuma aka ɗaura wani aure me ban mamaki, saurayin da ƴan matan haɗejia ke ribibi, samarin haɗejia ke ƙaunarsa an ɗaura masa aure a yau ɗin nan bayan na ƴar uwarsa, a da mutane suna tunanin auren ɗaya za'a ɗaura amma kuma sai gashi an ɗaura biyu, haƙiƙa wannan aure ya bawa mutane da yawa mamaki, wannan aure de ba kowani aure bane face auren Eshaan Auwal Tafida, wanda akafi sani da Tafida, ɗa a wajen tsohon Tafidan hadejia, da amaryarsa Maryam Tijjani Muhammad, ƴa a wajen Tijjani driver......._
Iyaka abinda ta iya tsinkayi kenan, wayar hannunta ta sub'uce ta faɗo a dandaryar ƙasa, sabon screen gard ɗin da hassan ya sako mata ya fashe har screen din wayar ma.
🌸-SAI KASKA CE-🌸.


⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*BABI NA GOMA SHA DAYA (11)*
*Bayan Shuɗewar Awa ɗaya*
Malam Tijjani yayi sallama a ƙofar gidansa, kuma ba tareda ya jira an amsa masa ba ya sa kai. Da kallo yabisu ɗaya bayan ɗaya, Maanmu ce sai hassan da hussain da suka zo suka ƙara tabbatar musu da gaskiyar batun ɗaurin auren.
Maanmu ta ɗaga kai ta kalleshi, hannunsa riƙe da huhun goro da kwalin alawa a kai, tunda Maanmu taga haka ta san cewa Shikenan, ta faru ta ƙare. Hawayen da ba ta samu tayi ɗazuba sune suka sulalo mata, alawa da goron ya aje sannan yace.
“Ku shiryata, anjima za'a zo a ɗauketa, kuma gobe zasu wuce lagos”.
“Wai dan Allah malam me kake nema ?, anya ma kuwa kaine ka haifemu?, me yasa zaka siyar mana da ƴar uwar mu ?, dan na tabbatar da siyara mana da ita kayi, dan wannan sunansa kasuwanci ba aure ba, kum.....”
“Ya isa hassan!”
Tsawar da Maanmu ta daka masa ce tasa yayi shiru da maganar da yake, sai aka koma kallon-kallon tsakaninsa da mahaifin nasu, hussain ne ya miƙe shima ya ja hannunsa zuwa ɗakinsu, dan yana ganin hakan itace mafita, dan idan ba hakan yayi ba a yanda hussain yake ji zai iya kaiwa abban nasu duka.
Maanmu ta tsaya tana kallon cikin idon Tijjani.
“Allah ba azzalumin sarki bane, ka riƙe wannan Tijjani”
Tana kaiwa nan ta shige dakinta, shime rigarsa ya kaɗe ya fice daga cikin gidan, ai yau ganima ta samu.
Maryam da ke zaune a ɗaki itada Anti Fati wadda bayan an ɗaura auren kai tsaye mijinta ya wuce gida ya sanar mata kuma bata jira komai ba ta taho gidan ta rushe da kuka, Anti Fati ta riƙota.
“Maryam wai miye na kukan ?, inde har Tafidan da kowa ya sani ne to bakya bina bashin rantsuwa kan zai kula dake, Tafida ba irin ko wani na miji bane, kawai kiyi haƙuri ki ɗau haka a matsayin YADDA ƘADDARA TA SO ”
Maryam taja hanci, daga ɗazu zuwa yanzu har idonta yayi ja tsabar kukan da ta sha.
“Anti Fati ba wannan bane abunda ke damuna, taya za'ayi a aura maka mijin da baka sanshi ba?, wanda baka tab'a ganinsa ba, kuma Anti Fati ko kaffara bazanyi ba kan kuɗi suka bawa Abba ya aura musu ni, Anti Fati me yasa Abba zai min haka ?, me yasa ?”
Ta faɗi tana nuna kanta, cikin muryar kuka, sai kuma ta share hawayen dake zubo mata.
“Anti Fati kinsan de yanda gidan sarauta yake, yanzu daga na shiga gidan ganina zasu dingayi da wannan tabon da Abba yayi min, zasu dinga min kallo ƙasƙanci, above all ƴan matan dake haɗejia sai ni?, Anti Fati why me ?, why ?, shikenan rayuwata ta zo ƙarshe anti fati, garinma zan bari zan bar kowa nawa na bar karatuna na barku, mutafi can ta yanda zaiji daɗin min gori”
Anti Fati ta rungume ƙanwar tata, ta san Maryam kamar yunwar cikinta, Maryam tanada haƙuri da kuma b'oye abinda ke ranta, tunda kuwa take faɗin hakan lalle abin ya kai ta ƙarshe.
“Ina imanin ki ya tafi Maryam ?, kiyi haƙuri ki ɗau hakan a matsayin ƙaddara...”
Guɗarn Badarce ta tsayar da Anti Fati daga ban bakin da take ma Maryam ɗin, ta shigo ɗakin sai wani fara'a take kamar itace amaryar.
“Iskanci, miye na wani kuka ?, ai ƙawata farin ciki zakiyi ba kuka ba, Tafida ?, hmmm Tafida fa kika aura Maryam”
Ta ƙarasa shigowa ɗakin tana wannan batu, batun da ya ƙara karyar da zuciyar Maryam ta fashe da wani sabon kuka, hakan yasa Badar ta fuskanci cewa abun ba na wasa bane, dan haka ta zauna itama aka ɗora sabon shafin rarrashin da ita.
Kan kace kwabo har gidan yacika da ƴan uwan Maanmu dana Abba, Anti Fati ce ta saka Badar ta tsefe mata kai, ira kuma ta mata kitso, zuwa lokacin ta dena kuka dan taga koma me zatayi ba fasa auren za'ayi ba, tunda an riga an ɗaura, wai itace ta auri Tafida, abun ya tsaya mata a rai. Gaba ɗaya ta rasa takamemen tunanin da za tayi.

*Hadejia emirates*
"Wai Tafida yayi aure ?”
Muryar Fulani ta fito cikin wani irin nishaɗi da bazaka iya musaltawa ba, ƴaƴanta ne biyu zaune a gabanta cikin dakinta da babu wanda yake shiga sai ita da yaran nata, Galadima da Maimun, Galadima yayi murmushi.
“Ai ni abun ya min daɗi, duk irin wannan so da ƙauna da ake nuna masa amma haka akayi aurensa lami”
“To ni so nakema na san dalilin yin auren” cewar Maimun
“Zai wuce so suke su halaka ƴar mutane, yau in ba haka ba sa aura mata Dodo”
Gaba ɗayansu suka saka dariya, Fulani Sadiya tana cikin farin ciki domin yau an ɗaura auren ƴarta ga kuma maƙiyin ɗanta anyi masa aure irin wanda ba kowani ɗan sarauta za'ayiwa ba.
A daidai wannan lokacin da suke wannan dariyar a wani b'angare na fadar, Tafida ne zaune a ƙasan lallausan carpet ɗin dake falon Me Martaba, wanda yake ganawa da iyalansa, a zaune akan kujera kuma Sarki ne, da Turaki, Ciroma da kuma Mairama sai Fulani Khadija.
“Eshaan”
Ciroma ya kira sunansa, chikakken sunansa, a hankali ya ɗago da kansa ya kalli iyayen nasa, sannan ya amsa.
“Na'am”
Gaba ɗaya ya sauya a cikin yinin nan kawai, ya cire zabunin dake jikinsa ɗazu, kansa babu hula gaba ɗaya gashin kansa ya sauƙo ya baje a goshinsa dan har ya rufe girarsa sai idonsa kawai ake gani.
“Munsan cewa mun isa da kai, shiyasa ma muka yanke wannan hukuncin ba tareda munji ra'ayinka ba, munsan cewa kanada hankali da kuma biyyaya, munsan cewa kai ba kamar ɗan uwanka Habibu kake ba, kana mana biyyaya a koda wani lokaci, bamu tab'a aje kara munce kada ka tsallaka ka tsallaka ba, kana binmu sauda ƙafa, to dan hakama a wannan karon muna so kayi mana biyyaya kamar yanda ka saba, muna so ka kakarb'i auren nan hannu bibbiyu, ka riƙe yarinyar nan da amana, munsan ka san cewa aure ba abun wasa bane, inshaallah idan kayi biyyaya a gaba sai kayi alfahari da wannan auren, ka ɗauki wannan auren a matsayin YADDA ƘADDARA TA SO ”.
A lokacin shi kaɗai yasan abinda yake ji, sam ya kasa wani tunani me kyau, ya rasa a wani matsayi zai saka wannan auren.
“Inshaallah zaku sameni a matsayin me bin umarninku kamar yanda na saba”.
Masomin kaddarar kenan, Daga haka aka soma.
*Da misalin 09:00pm*
Tafida ne zaune a parlon gidansa, tunanuka barkatai a kansa, shi ya rasa inda kansa yake, baya gane komai tun bayan da amace an daura musa aure.
“Me yasa baka san auren nan ?”
Muryar Muktar ta tambaya, wanda yake zaune a gefensa, Tafida ya gyara zamansa, tareda kai hannu ya tura sumar kansa baya, dan yau ta sauƙo masa kan goshi.
“Muktar su Me Martaba sun tafka babban kuskura, ni sam ban cancanci zama da kowa ba, kaɗaici shine abinda ya kamaceni, bai kamata ace ina rayuwa da wani a kusa dani ba, yarinya tana can tana rayuwarta suka rabota da danginta da farin cikinta suka aura mata ni, ni bancanci zama da kowa ba Muktar, sun lalata rayuwar ƴar mutane a banza”.
“A'a Tafida ba haka bane, tunda de har kaga hakan ta faru to tabbas akwai abinda Allah ya hukunta a ciki, kuma Tafida duk wadda ta sameka a matsayin miji itace tayi sa'a ba kai ba”.
Tafida yayi wani bussashen murmushi yana tura sumar kansa baya, sai kuma ya dawo da hannun nasa ya dunƙule ya ɗora a bakinsa.
“Inaso ka nemo min bayanai akan yariyar me suna Maryam ”
“Me yasa ?”
Sai ya ɗago ya kalli Muktar
“A tsarin gidanmu babu saki da na saketa taci gaba da rayuwarta kamar yanda ta saba, amma tunda har hakan ba zata samuba zan yi yanda zanyi na temaki rayuwarta bazan bari wani ya cutu sbd ni ba”.
MARYAM POV.
Zaune take a bakin makeken gadon da aka bata, babu abinda take tunawa sai yanda aka rabota da gida, tana kuka tana komai, wani abu daya tsaya mata a rai shine maganar da sukayi da Maanmu ta ƙarshe.
_“Maryam, bance kada kiyiwa mijinki biyyaya ba, kiyi masa biyyaya iyaka bakin iyawarki, ni misalice a wajenki, kinga yanda naci tarin baƙin cikin mahaifinki, kada ki duba sigar da aurenki ya faru kawai kiyiwa mijinki biyyaya, wannan shine kaɗai abinda zan iya faɗa miki” _
Sai taji wata sabuwar kwalla na zubo mata, daga wannan magana ta Maanmu wasu manyan mata da aka aiko daga fada wanda suka shiryata cikin alkyabba suka fita da ita daga gidan, suka sakata a cikin mota suka kawota fadar haɗejia, tunda take a rayuwarta bata tab'a shigowa cikin fada ba, dan bataga dalilin da zaisa ta shiga fadar ba, kuma suna kawota ne kaitsaye akayi turakar Fulani da ita, duk da tanajin fadar babu hayaniya sosai alamun ƴan wancan bikin suna gidan dinner, kuma tunda aka kawota bangaren da take ciki kai tsaye wannan ɗakin da take ciki aka kawota, daga ita sai jakar kayanta guda ɗaya, kuma yawancin kayan ciki Anti Fati da Badar ne suka bata shi, dan gaba ɗaya nata cewa sukayi bazata tafi da suba, hijabanta kawai suka bar mata.
Tunda tayi sallar isha har yanzu hawaye bai yanke a idonta ba.
Jin kamar ana motsa kofar ɗakin ne yasa gabanta yayi wata wawuyar yankewa ya faɗi, ta tsirawa kofar ido sai taga Fulani ta shigo, a sirrance ta sauƙe a jiyar zuciya, Fulani na mata murmushi ta ƙaraso har cikin ɗakin tana zama a kusa da ita, Maryam ta zabura zata sauƙa kasa Fulani tayi saurin riƙota tana girgiza mata kai.
“Haba!, haba! Maryam ai yanzu kin zama ƴar gida”
Maryam ta share hawaye tana zama amma a ɗarare ta zauna sai kama jikinta take, zama kusa da matar sarki ai abun azimun ne.
“Maryam, inasan nayi miki magana a matsayina na uwa wadda take fatan samawa ɗanta lafiya, ba a matsayin Fulani Khadija matar sarki ba”
Sai Maryam taji abun banbarkwai, itafa dama tasan cewa dole dai wanna auren na manufa akayi, in ba haka ba taya za'ayi a zab'ota ita ɗaya kaf cikin tarin ƴaƴan masu kuɗi da mulki na garin nan ace sai ita, ita kaɗai, Fulani ta kamo hannayen Maryam.
“Maryam, Tafida ya taso ne cikin wata hautsinnaniyar rayuwa, tun yana yaro ya rasa iyayensa, Raruwarsa gaba ɗaya lillub'e take da wani baƙin duhu, Kuma a yanda aka sanar mana babu me iya kawar da wannan duhun na rayuwarsa sai ke”.
Sai kuma tayi shiru, hawayen da Maryam taga a idonta shi yafi ruɗata fiye da maganganun da ta faɗi.
“Ina me roƙonki Maryam, dan Allah ki temaki ɗana, ki ceto shi daga cikin wannan kogin da yake ciki, Nasan zakimin kallon me san kai, amma ina roƙonki dan Allah....”
Maryam ta shiga girgiza mata kai, ita bakinta ma ya kulle, ta kasa cewa komai, maganganun sunwa ƙwaƙwalwata nauyi. Ta masa fahimtar maganganun nata gaba daya, da kyar ta iya lalubo muryarta.
“Ni ban isa na warkar da kowa ba, Allah shine me waraka, kuma shine me warkar da kowa”.
_ya ne ?, my people, garifa ya kama da wuta, kamar wani abu yana ƙauri a nan, labari ya dauki zafi🔥_
_To ki biyoni domin jin karashen labarin, a har kullum nice taku Salma Ahmad Isah, wato SAI, Ina miƙa godiyata zuwa gare ku🙏_.
🌸-SAI KASKA CE-🌸.

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*BABI NA GOMA SHA BIYU (12)*
*Washe gari*
*Malam Aminu international airport*
*Da misalin 10:00am*
Tafida ya fito daga wani shagon snakes, inda ya saba kaiwa ajiyar key kafin Muktar yazo ya karb'a, wasu lokutan ma tare suke tahowa idan ya aje shi sai ya juya da motar, to yau sun taho da wata shi yasa bai biyo shi ba, tun jiyama da sukayi sallama bai ƙara ganinsa ba, kawai de da zasu taho ya kirashi akan zai bayar a aje masa keyn inyaso sai yaje ya karb'i motar.
Inda yasan ya bar Maryam ya dawo, zaune take akan daya daga cikin wasu kujerun dake wajen, ga jakukunansu a kusa da ita, sai yanxu ya samu damar ƙare mata kallo, dan yau da safe da yaje fada sarki ya fara zuwa ya gaisar,sannan yayi masa sallama sai ya fita yaje ya yiwa Fulani sallamar itama, kuma itace tace masa yaje ya jira Maryam ɗin a mota, yana zaune a motar suka ƙaraso ita da Nadra.
Kuma har ta shiga motar bai kalleta ba, gaisuwar da ta masa ma da ƙyar ya samu ya amsa, kuma bai kalleta da kyau ba sai yanzu.
Bata cika fari ba, amma kuma farar ce, bata da wani kyau na tashin hankali, saide bata da muni kyanta daidai ita, kuma bata da jiki duk da abayar dake jikinta tanada faɗi, amma hakan bai hanshi ganin sirirantar ta ba, wani abu dayafi komai kyau game da ita shine idanunta, farare tar, duk da sun ɗanyi ja, alamun tayi kuka, wani irin innocent face gareta, kuma akwai nutsuwa da kamewa a tareda ita, Kuma daga ganinta kasan cewa akwai ƙarancin shekaru a tareda ita, sai yaji tausayinta ya ƙara kamashi.
"Muje ko ?”
A hankali Maryam ta ɗago ta kalleshi, gabanta yayi wata iriyar muguwar faɗuwa, taji kamar tana nitsewa a cikin wani abu, kamar yanda shima bai kalleta ba itama bata kalleshi ba sai yanzu, ta saba jin hirar Tafida a bakin mutane da yawa bata san ashe haka Tafidan yake ba, lalle kuwa Tafida, ai wannan bai dace da wannan sunan na Tafida ba, wannan sunansa Eshaan, dan shine yafi dacewa da shi, ashe duk abunda Badar ke faɗa mata gaskiyane.
Kuma tana kallon fuskar tasa sai maganganun da sukayi da Fulani yau da safe suka faɗo a cikin ƙwaƙwalwarta.
_“Maryam, nasan da cewa Allah shine me temakon kowa da komai, amma ke kece sanadiyyar temakon Tafida, akwai wani abu dake damun rayuwarsa da bayasan karatun alqur'ani ko addu'a, nasan cewa ke me ilimice dan haka ki riƙi addu'a, ga wannan qur'an ɗin ki lazimci karantashi a kullum, na tabbatar da Allah zai temakeku, ya kuma baku zaman lafiya, Allah ya miki albarka”_
A ɗazun sai ta kar6i qur'an ɗin ta kuma mata godiya, bayan fitar Fulani wata ta shigo wadda ta bayyana mata kanta a matsayin Nadra, ta bata wata brown abaya, kuma itace bayan tayi wanka ta saka dan har yanzu ma itace a jikinta, saida suka fitone taga tarin wasu akwaituna guda shida, Fulani ta sheda mata da kayan aurenta ne da aka mata, a lokacin ma saida tayi hawaye, kuma wasu bayine da Nadra suka rakata har motar da akace Tafida na ciki, suka saka kayan a baya, sannan ita ta shiga motar.
Kuma tun bayan gaishe shi da tayi bata ƙara cewa komai ba, shima kuma baice ɗinba, sannan batayi gigin kallonsa ba har suka iso kano, amma kuma gaba ɗaya a takure take a cikin motar.
Kuma bayan sun zo ne ya saka aka shiga musu da kayansu ciki yace ta zauna ta jirashi yaje ya dawo shine har yanzu yake tsaye a gabanta.
*
Kamar yanda a mota sukayi tafiyar kurame

Please Login or Register in order to submit comment