Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin ne Aryaan ya canyara kuka, bata bi ta kan Aryaan ba ta fara faɗin.
“Dan na mareka shine kasa aje a satomin ɗa ko ?”
Cike da mamaki kowa ya shiga kallonsu, sai kuma taci kwalarsa
“To da kasa a sato maka shi uban me zaka masa huh?, faɗa min mana ?”
Ta faɗi tana jijjiga shi sai kuma ta sake shi, ta nuna shi da ɗan yatsa “kana ji ko ?, idan har ka kuskura ka taba koda silin gashi ɗaya na ɗana ne, sai na ɗaye maka fata, sai na tabbatar da na koya maka darasin da baka ta6a sanin da akwai irinsa ba a duniya, ɗana yafi ƙarfin ta6awarka”
Ta matsa gaba dashi dab da dab, ta ɗora ɗan yatsanta akan sa tana faɗin.
“Put this at the back or no, not at the back, put it at the front of your mind”
Tana kaiwa nan ta bar wajen a fusace tayi sama, ta bar kowa na wajen da mamaki, tanajin Abba daya rufeshi da faɗa, mahaifiyarsa kuma tana kareshi kamar kullum.
Kai tsaye ɗakinta ta shiga, wanda komai na cikinsa yake kalar fari da brown, fari shine kalar datafi so, dan a gaba ɗaya kayan datake sakawa babu wanda babu kalar fari a ciki, ɗakin Aryaan wanda yake haɗe da nata ta shiga.
A da ɗakin maƙotan ɗakinta ne, bayan ta dawo daga USA ne Abba yasa aka rufe kofarsa ta waje, aka fasa masa ƙofa daga ɗakinta. Kasan cewar ɗakin bashi da kofa kanta tsaye ta shiga, hand bag ɗinta ta aje akan kujera, har lokacin Arya na canyara kuka, belt ɗin baby carrier ɗin nasa ta shiga ballewa sannan ta sauko dashi.
Ta zauna akan wata kujerar da ban da wadda ta aje jakarta ta saka masa mama a bakinsa, nan take yayi shiru ya shiga tsotsa, tana shafa kansa tana faɗin
“Sssssshhhhhhhh!”
Ta sunkuyar da kanta tana kallon cikin kwayar idonsa, wadda take tuna mata da wani dare daya faru a rayuwarta a baya, a har kullum Idan ta kalli blue eyes ɗin nasa yana tuna mata da daren.
Sai kuma ta kawar da idonta ganin shima yana kallonta, hannunsa ya ɗago ya saka a cikin bakinta, tayi kamar zata cijeshi yayi sauri ya cire daga bakin nata, tayi dariya tana taba kumatunsa
“Ka dena kuka Arya, babu wanda zai rabaka da Ammin ka, Amminka tana tareda kai, bazan taba bari wani abu ya sameka ba, haza wa'adi ilak (wannan shine alƙawarina gareka)”.
***
“Maman babanta”
Muryar Abba ta faɗa cikin shirun da ɗakin nasa ya ɗauka, bayan Aryaan ya gama shan maman tashi tayi tai masa wanka, tun tana masa wankan ya fara bacci, dan haka tana shafa masa mayukansa ta kwantar dashi a cot (gadan yara na katako), wanda ke cikin ɗakinta, babu bata lokaci ya fara bacci.
Itama wankan ta shiga sai kuma kiran Abba ya sameta, dan baka ta fito ta saka kayanta ta fita.
“Maman babanta magana fa nake!”
muryar Abba ta ƙara katse mata tunanin da take neman zurmawa ciki, a hankali ta ɗago da kanta ta kalleshi, yayinda take zaune a kasan ƙafafunsa, kwata-kwata idan ka kallesu bazakace ƴa da uba bane, sbd shi Abban baƙine wulik, ko a cikin baƙaƙen africa shi baƙine, ita kuma farace, fara sosai farinta yafi irin farin fararen africa, amma kuma farin nata irin na indiyawa ne, kasan cewarta halp cast.
“Na'am abba”
“Maman Babanta ɗazu Jabeer ya kirani, kuma ya faɗa min duk abinda ya faru tsakaninku, Maman Babanta me yasa bazakiyi aure ba ?, ya kamata ace kinyi aure, 25 kike fa ya kamata ace kinyi aure”
Hanam tayi murmushi me ciwo
“Kasan ɗazu da safe daya zo office me yace min ?”
Abba ya girgiza kai, taci gaba
“Cewa yayi ya kamata ace na tuna alƙawarin da mukayiwa juna, zamuyi aure, mu rayu tare, mu tsufa tare, mu gina gidanumu dagani sai shi, sai kuma yaran da zamu haifa”
Abba yayi wani irin murmushi
“To Hanam miye abun aibu anan ?, ai wannan abun farin cikine Maman Babanta”
Ta girgiza kai
“A'a Abba wannan ba abun farin ciki bane”
“amma me yasa Hanam?”
Abba ya tambaya girarsa na haɗewa waje guda, alamun kokonto.
“Lakin abba fi kul hazal kalam wain Arya ?"
(Amma abba a duka wannan zancen ina arya ?) .
Ta faɗi tana hawaye, kuma cikin harshen larabci, Abba ya ruɗe yana sauƙowa kasa kan carpet kusa da ita, duk abinfa zai saka Hanam kuka to ba ƙarami bane, akwaita da jajircewa, ta iya haɗiye baƙin ciki tun tana ƙarama.
“Abba wain Arya?, huwa biddu ya illi unu iza jawazna ana rah utruk Aryaan ?”
(Abba ina arya?, yana nufin idan munyi aure zan rabu da Aryaan?)
Tayi maganar a sigar tambaya, amma ba tambayar bace.
“ihdi Hanam shrahili kilshi bi tafsil”
(Nitsu Hanam, kiyimin bayanin komai dalla-dalla)
Shima ya tambayeta da larabcin, dan shine ma wanda ya koya mata, sbd shine mother tongue ɗinta, Hanam ta ɗora hannu akan goshinta tana kurzawa, wanda hakan sararta ce tun tana ƙrama, sannan ta share hawaye wani na, sauƙo mata.
“Abba nima fa mutumce, inada feelings, inajin bacin rai, nasan farin ciki, inajin haushi idan aka bata min rai, Abba duk rayuwar da babu Arya bazan iya yinta ba, Abba bana san rayuwar da babu Arya sam, abba Arya shine komai nawa bayan kai bani da wani kamarsa”
Ta ja majina tana share wani hawayen.
“Yanzu Abba ƙaddara nida jabeer munyi aure, kuma na haifa masa yara, kana ganin zaiso Arya kamar yanda zaiso sauran yaransa ?, ko iyayensa zasu soshi kamar yanda zasu so jikokinsu na jininsu ?”
Abba ya girgiza mata kai cike da tausayin ƴar tasa
“Abba duk mijin da zan aura baya san Arya nima bana sansa, kuma bazan iya na aureshi ba, Abba Arya shine gobena, Arya ya zama wani ban gare na labarina wanda bazai cikaba idan babu shi”.
Ta kuma jan majina tana share hawayen dayaƙi tsayawa taci gaba da cewa.
“Abba me yasa kowa yake wasan kura da zuciyata ?, me yasa ni tawa ƙaddarar tazo da tsauri ?, abba me yasa komai nawa babu abu me daɗi ?, kaida Arya kune kaɗai abu me kyau da kuka faru a rayuwat me yasa ake so na rabu da ɗaya ?”
Abba ya rungumeta yana hawaye shima, fashewa tayi da kuka tana riƙe shi, daga mahaifiyarta ya kamata ace ta samu hakan, amma sbd san zuciyarta ta tafi ta barta.
Abba yaji zuciyarsa tayi nauyi ji yake inama akwai yanda zeyi ya cire kowace damuwa data faru a cikin rayuwar ƴar tasa domin tayi rayuwa me kyau, ta sami farin ciki, ta haɗiyi baƙin ciki kala-kala, yana fatan Allah ya bata wani sabon fata wanda zai sata farin ciki a nan gaba.
“Kiyi haƙiri Hanam, ki ɗauki hakan a mafsayin YADDA ƘADDARA TA SO ”.
_godiya ta musanman zuwaga makaranta wannan littafi, ina muku godiya sosai wanda suka shiga group din YADDA KADDARA TA SO NOVEL GROUP, hakika naji dadin ganinku sosai, Allah ya saka da Alkairi_
_kuyi share, and comment pls_
_Na kara gode muku_
🌸-SAI KASKA CE-🌸.
⭐️ YADDA ƘADDARA TA SO⭐️
⭐️ شاء القدر⭐️
-By Sai Kaska
*Proud of my first novel*
My wattpad page @Sai_Kaska.
*BABI NA BIYAR (6)*
*MASARAUTAR HAƊEJIA*
Da misalin ƙarfe biyu da rabi na rana.
Ɗan masani ne zaune a kan lallausan carpet ɗin dake malale a parlo na biyu wanda yake bangaren Fulani, hannunsa na dama riƙe da wani makeken littafi, wanda sarkin haɗejia Sule Karo ya rubuta da kansa, kasan cewar mutanen da sun riƙi tsafi da duba a matsayin al'ada hakan yasa ko bayan zuwan musulunci basu watsar da wasu al'adun nasu ba.
Sai bayan zuwan Shaihu Usman ɗan Fodio, to hakama tsohon sarkin haɗejia Sule Karo a nasa zamanin an faɗa masa abunda zai faru da wani daga cikin ahalinsa da zasu zo a gaba, kuma tun a lokacin yasa aka masa bincike aka gano maganin matsalar.
Tun a lokacin da Tafida ke ƙarami alamomun baƙin ruhin dake jikinsa suka fara bayyana, kuma tun a lokacin ne sarki ya gano cewa tabbas shine wanda ɗaya daga cikin iyayensu na da yayi rubutu akai.
Sannan tun a lokacin suka duba maganin matsalar, kuma sun gano cewar aura masa wata yarinya da za'ayi shine maganin wannan baƙin ruhin, a lokacin sam bai kai aure ba, dan haka sukayi haƙuri suka duƙufa akan masa magunguna da addu'o'i.
Kuma sai aka dace, ya zamana sam abun baya tashi sai idan ransa ne ya baci, amma a kwanakin nan abun ya ta'azzara, hakan yasa Fulani taji ba zata iya jurewa ba, dolene ta nemi Ɗan Masani, wanda ya kasance shine masanin Tarihin fada.
Daga wata kujera dake nesa da ɗan masani kuma Fulani Khadija ce zaune, cikin zama irin na ƙasaita da mulki, kallon Ɗan Masani kawai take, tana jiran ya buɗe littafin ya faɗa mata menene mafita.
Ɗan masani yayi gyaran murya, yana shimfiɗe katoton littafin a kan carpet ɗin, sannan ya shiga buɗewa, yana wuce tarihin abubuwa masu muhimanci da suka faru a masarautar haɗejia a wancan zamani, Da haka har ya ƙaraso shafin da bayanai akan bakin ruhi yake.
“Na samoshi ranki ya daɗe”
Fulani tayi a jiyar zuciya a ranta, a fili kuma sai ta gyara zamanta, alamun ina jinka.
“Kamar yanda muka faɗi a wancan lokacin yanzu ɗinma hakane, wannan yarinyar data dace ya kamata a nemo a haɗashi aure da ita, ita wannan yarinyar Allah ya temakeki itace makarin bakin ruhin dake jikinsa, daga zarar sunyi aure, ya samu ya kusanceta koda sau ɗayane, to baƙin ruhin zai fara rauni, a hankali a hankali kuma zai bar jikinsa”
Fulani ta ƙara numfasawa a ranta, a fili kuwa ko gezau batayi ba, ta kafe Ɗan Masani da idanuwanta tana nazarin kalaman dayake faɗa mata, kafin muryarta ta fito cikin izza da kasaita.
“Taya zamu iya gane yarinyar data dace ?”
“Allah ya temakeki ai kawai alamomin yarinyar a nan”
Ya faɗi yana ƙara ƙanƙan da kai, kuma Fulani batace masa komai ba, dan haka yaci gaba.
“Alamomin sune, tanada tawadar Allah me faɗi a wuyanta, kuma shekarunta basu wuce 22 ba, a sanda za'ayi auren kenan, sannan kuma akwai wata tawadar Allar a gefen gashinta, sai sirin farin gashin guda daya a a kanta daga gaba”
Yanxuma Fulani batace komai ba, taya za'ayi su iya samo yarinya me waɗannan siffofin a faɗin garin haɗejia, bama haɗejia kawai ba a duniya ma baki ɗaya, shin wanyama kuwa suna kan daidai ?, ganin sun amince da abinda yake gaibu, Dan wannan gaibu ne, to yaya zasuyi ?, Idan aka bashi addu'a matsala, idan aka barshi babu addu'a ma matsala, a ganinta wannan ita kaɗaice mafita.
***
“Jakadiya Babba Ɗan Masani ya bani alamomin yarinyar da za'a aurawa Tafida, saide ina ganin kamar bazamu sameta ba”
Muryar Fulani khadija ce ke koro wannan jawabi, bayan ta sallami Ɗan Masani, Jakadiya Babba ta ƙara dunƙule hannunta sama tana ƙara duƙar da kanta ƙasa.
“Allah ya ƙara miki yawan rai, uwar jigiyata ai wannan me sauƙi ne”
“A'a Jakadiya, wannan abun bame sauƙi bane, a ina zamu samu Yarinyar ?, kawai dan munsan cewa akwai tawadar Allah a wuyanta da kuma gashinta sai shekarunta, farin gashin dake kanta sai mu samota ?”
“Ba haka nake nufiba uwar gijiyata, insha allah zamu samota da yardar Allah, Allah ya ƙara miki girma, Fulani matar sarki Abdullahi Abubakar Masu, uwar gimbiya Nadra da Tafida”
Fulani ta kawar da kanta tana meda dubanta ga tv, abun duniya yabi ya isheta.
“Yashi ki tafi na sallameki”
“Godiya nake matar Saifullahi takobin allah”
Jakadiya ta faɗi tana miƙewa haɗi da ci gaba da korowa Fulani kirari. Tana fitowa bangarensu na bayi ta nufa domin ta shirya, dan yau za'a gabatar da bikin kamu na gimbiya Amina, kuma dole dasu za'ayi komai.
MARYAM POV.
Cikin nutsuwarta data zamemata jiki take tafiya, kuma kamar kullum sanye take da hijabi har ƙasa, kuma fuskarta babu kwalliya dan dama can batayi, hannunta na dama riƙeda baƙar ledar data siyawa irfan, ɗan gidan anti fati karas.
Tris taja ta tsaya, sbd kofar gidan Tafida da take iya hangowa, kuma ga wasu mutane a ƙofar gidan, hakan ke nuna mata cewar yana gidan, sa6anin da da bazaka tadda kowa a ƙofar gidan ba sai masu gadu.
Kuma ganin mutanen ya nuna mata cewar an sauƙo daga kilisa. A da tana san ta wuce ta ƙofar gidan kodan ta samu ta kalli kyakyawan gidan dayafi kowanne kyau a cikin jerin gidajen dake layin, amma yau sai taji bata san wucewa ta ƙofar gidan, dan haka ta juya ta shiga wani layi tayi wani uban zagaye kafin ta samu ta ƙaraso gidan Anti Fati, duk tabi ta gaji, kuma dama daga gidan Tafidan zuwa gidan Anti Fatin akwai nisa amma kuma zagayen da tayi shine ya ƙara mata nisan tafiyar tata.
Da sallama a bakinta ta shiga gidan, babu kowa a tsakar gidan dan haka ta shiga cikin parlon, inda muryar Anti Fati take fitowa cikin amsa sallamar da tayi, a parlon kuwa ta sameta zaune tana kwalliya.
Itama kujera ta samu ta zauna tana gaisheda Anti Fatin, sai kuma tabi parlon da kallo tana mamakin sanda aka sauya kujerun parlon, koda yake ta jima bata zo gidan ba, kuma dama mijin Anti Fatin yanada rufin asirinsa dan yaron Kawu Usman ne, kuma shine ya haɗa su auren, hatta da kayan ɗaki dana kitchen shine yayi mata.
“Anti fati ina Luluwa?”
Tana nufin ɗan anti fatin, dan haka suke kiransa a gidansu, sbd yaron yanada jiki ga kuma kumatu, shine Hussain ya saka masa Lulu suma kuma suke kiransa da Lulun.
“Yana ɗaki yana min ta'adin daya saba”
Maryam tana dariya ta miƙe ta shiga ɗakin aiko a bakin gado ta sameshi yana wargaza kayan da suke cikin wani kwando
“Ƙaunar Anti Maryam”
Ta kirashi da sunan da ita kaɗai take kiransa dashi, yaron ɗan wata tara ya jiyo ya kalleta sai kuma ya 6an gale baki yana dariya, Maryam ta ƙarasa inda yake ta saka hannu ta ɗaukeshi.
Wani ikon sai Allah, idan ka kallesu tare cewa zakayi Maryam ce ta kawo shi duniya, komai na fuskarta ya d'auko, hatta da tawadar Allahn dake goshinta shima yanada akwai.
Parlon suka dawo suka zauna, sai ta iske Anti Fati ta gama kwalliayar, tana yafa mayafi.
“Kije ki zubo abinci a kitchen kici sai mu tafi”
“A'a saida naci abinci sannan na taho, idan kin gama kawai muje”
Maryam ta faɗi tana zama a kan kujera, yayinda take bawa imran karas ɗin data siyo masa, galala Anti Fati take kallon Maryam ɗin da bata ma san tanayi ba.
“A haka zamu tafi?”
ta faɗi tana nuna Maryam ɗin, Maryam ta kalli jikinta da kyau.
“Eh mana...”
Tun kafin ta karasa ta katseta da cewar.
“Muje ina a hakan ?, kinsan kuwa inda zamuje Maryam ?”
Ta faɗi cikin kama baki, kuma bata jira cewar Maryam ɗin ba tace.
“Bikin ƴar gidan sarki fa za muje”
Girar Maryam ta haɗe waje guda alamun kokwanto.
“Ba haka kikace bikin dangin mijinki bane ?”
“Eh mana, ai mijin da zai auri ƴar sarkin shine dan uwan su habib ɗin”
Maryam ta juyar da kai gefe, tasan yanzu Anti Fati zata sakata ta cire hijabin jikinta, kuma tunanin nata bai je ko ina ba, abinda take saƙawa a ranta ya faru.
“Bari na kawo miki gyale ki saka”
Ta faɗi tana shiga dakinta, Maryam ta ta6e baki, tana cigaba da karyawa imran karas ɗin da baya iya cinsa duka.
Jim kaɗan Anti Fati ta fito ta miƙa mata wani baƙin babban gyale, babu yanda zatayi haka ta kar6a ta mike tsaye ta cire hijabin jikinta tana ninkewa, Anti Fati na cewa.
“Maca har mace, diri har diri amma kina boye shi cikin hijabi”
Ita dai Maryam bata ce mata komai ba, ta yafa mayafin.
“muje ?”
Anti Fati ta dafe goshi cike da ta kaicin kanwar tata.
“A kullum ana miki kallon wayyayya amma sam Maryam baki waye ba, dan Allah kalli daurin dankwalin kanki, kalli fuskar ki”
Maryam ta kawar da kai
“Ke idan bakya san kiyi aure to mu muna so, kullum ke cikin boye jiki fuska a koɗe kamar matar takaba ta ina wani zai gani yace yana so, zauna nayi miki kwalliya”.
Maryam bata iya musu ba, dan haka ta zauna.
“Amma dan allah kada kimin da yawa”
Anti Fati ta zauna ta shafa mata hoda, ta bata kwalli ta saka da kanta, ta saka mata lip gloss, sannan ta daura mata dankwalli, kasan cewar atamfar tata me ɗan kyauce bataji jiki ba yasa Anti Fatin bata nemi data sauyata ba.
“Haba dan Allah, kalli kanki kiga”
Maryam ta dauki mudubi tana duban fuskarta, tunda ta taso tayi wayo bata taba kwalliya a fuskarta ba, koda kwalli bata ta6a sakawa ba, amma yau gashi itace harda hoda, kuma ba zatayiwa kanta ƙarya ba, yau tayi kyau.
“Ki gafa yanda Kikayi kyau”
Wannan kalma ta kyau bata taba dosar inda take ba, babu wanda ya ta6a ce mata tanada kyau, dan ba kwalliya take ba, bare ace tayi kyau, karewarta ma Husssain cewa yake da a ace bata da hasken fata da bazata ganu ba.
🌸-SAI KASKA CE-🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐️
⭐️ شاء القدر⭐️
©By Sai Kaska
My wattpad page @Sai_Kaska
*Proud of my first novel*
*BABI NA BAKWAI (7)*
“Meema event center zaka kaimu”
Muryar Anti Fati ta faɗi bayan sun fito daga gidan sun tsaya a bakin titi, sannan suka tsaida me napep.
“Ku shiga muje to”
Anti Fati ta juyo tana kallon Maryam wadda ke tsaye a bayanta sai gyara zaman gyalen dake jikinta take, ita jinta take kamar tsirara, gaba dayanta a takure take dan bata saba ba.
“Muje”
Tana ta jajjan mayafin daga baya ta shiga adaidaitar, ta kar6i Imran daga hannun Anti Fati, sai waige-waige take kamar wadda tayiwa sarki ƙarya.
Da haka suka isa katafaren sabon event center din da aka bude a hadejia kwanannan, tun daga bakin gate Maryam ta tabbatar da ba bikin ƙananun mutane suka zuba, dan tun daga maka makan motocin dake parker a harabar wajen, zuwaga mutanen dake kaikawo a wajen da yanayin suturunsu zaka tabbatar da ba ƙananun mutane bane, Maryam ta kama kanta tana bin Anti Fati a baya.
TAFIDAH POV.
_🎶If this is a dream babe i don't wanna wake up ooh yeeh !_
_This is too sweet to be real babe i don't wanna wake up oooo yeeeh!_
_You give me life you give me vibe ooh, you be my energy i can't deny oh_
_Super man you will be my hero what is love if you not there ?_
A hankali wakar Sweet wadda Rayvanny tareda Guchi suka rera take tashi daga cikin home theater ɗin dake katafaren falon gidan Tafida.
Daga can kan wata kujera ta zaman mutum uku kuma shine kwance, idonsa a lumshe yana bin wakar a hankali, yayi nisa a abunda yake, har Muktar ya buɗe ƙofar bema sani ba, dan hankalinsa gaba daya yana kan sauraron waƙar, saida muktar din ya ɗan daki ƙafarsa sannan ya bude idonsa, har yanzu kalar idon nasa tana nan yanda ya tashi da ita tun safe, ja har yanzu bata sauya kala ba.
Miƙewa yayi ya zauna, yayinda Muktar ya ƙarasa ya kashe waƙar, ya dawo kusa dashi ya zauna.
“Ba hakane ya kamata ba, kamata yayi ace ka kunna karatu ba waka ba, kallifa idonka har yanzu bai sauya ba”
Tafida ya yi murmushi me ciwo, ba sai ya faɗa masa ba cewa a duk lokacin dayaji karatu ji yake kamar ruhinsa zai fita tareda baƙin ruhin nan ba, shima da kansa ya san da hakan, sai kawai ya juya ga wayarsa ya dauki ɗaya daga ciki ya shiga dannawa.
“Abincine Madam ta turo maka”
Wani murmushi ya su6ucewa Tafida, a gaba ɗaya cikin abokansa babu wanda bashi da aure harda yara, amma shi banda shi, dan koda wasa bashida tsarin yin aure a yanzu.
“Ina lil me ?” (yana nufin me sunansa dan gidan Muktar ɗin)
ya faɗi yana aje wayar dake hannunsa
“Yana nan, zasuje gidan kamun ai, wata ƙila ku hadu”
Muktar ya bashi amsa yana zuba masa abincin, shi sai yanzuma da yaga abinci sannan ya tuna ashe baici abincin ba tun safe, dan yana fita daga fada gidansa ya wuto aka fito masa da dokunansa sbd hawan angwancen, ya shirya suka tafi hawan kuma basu dawo ba sai dazu, shine yayi sallah ya kwanta yana hutawa har Muktar ɗin yazo ya sameshi a haka.
“Zakaje wajen kamun ne ?”
“Shi ya zama dole, su Mairama zasu zo fa, kuma da mahaifiyar Amina ne bama shiri ba wai da ita ba”
Tafida ya faɗi yana kaiwa abincin bakinsa, kuma daga haka babu wanda yaƙara cewa komai a cikinsu har ya gama cin abincin, ya tashi ya shiga dakinsa ya shirya sannan ya fito, cikin wata baƙar shadda wadda tayiwa farar fatarsa kyau, sai sheki take cikin hasken fitulin parlon, hannunsa rike da hular da zai saka, ya tako har cikin parlon sai baza kamshi yake.
Muktar ya miƙe yana kallonsa hannunsa na dama yakai ya tura gashinsa baya, wani abu daya zame masa al'ada, sannan ya saka hular a kansa
“Idanka ya dawo daidai”
Muktar ya faɗi ganin ƙwayar idon nasa ta dawo dai-dai, ma'ana ta dawo ainahin kalarta wato blue. Tafida yayi murmushi kawai, sannan ya buɗe tafin hannunsa ya mika shi saitin inda wayarsa take, nan take wayar ta taso ta sauko a kan hannunsa, wannan ba wani sabon abu bane a wajen Muktar, dan tun suna yara yasan wannan side ɗin na Tafidah.
“Muje ko ?”
Muktar ya gyada kai suka fita, saida suka fara zuwa asibitinsa wadda ya buɗeta a hadejia wato CROWN HOSPITAL, kuma Muktar ne yake kula da ita, bayan sun gama abinda zasuyi suka wuce meema event center.
Tunda ya isa wajen ƴan uwansa suka masa caa, kowa da nasa kalar ƙorafin, wannan yazo ya tafi wancan yazo, masu ƙorafi akan baya xuwa gidansu su sukafi yawa, shide nasa bada haƙuri ne kawai.
A wata kujera dake kusa da ta Mairama wadda take ƙanwa a wajen mahaifinsa ya zauna.
Itama saida tayi nata ƙorafin, kuma kamar sauran itama dai haƙurin ya bata. Daga nan ya shiga hira da yaranta ƴan mata dake wajen, Mairama kam kallonsa kawai take cike da tausayawa, dan abinda ya faru jiyama Fulani ta kirata ta sanar mata.
“Hamma ga ƙawar tawa”
Muryar Nadra ta faɗi daga bayansu, a hankali ya juya yana kallonsu, bama shi kaɗai ba harda mairama da yaranta, girarsa ta haɗe waje guda alamun rashin fahimta, yana kallon ƙawar tata wadda take ta washe baki, murna fal ranta yau taga Tafida kusa da kusa.
“Ƙawata da na faɗa maka jiya”
Nadra ta faɗi ganin kamar hamman nata ya manta da zancen da sukayi jiya, kuma hakaɗin ne ya manta ɗin, dan shi ba komai yake sakawa a ƙwaƙwalwarsa ba, a daidai lokacin ne kuma Muktar da matarsa da kuma ɗansa suka ƙaraso wajen, dan da tare suke kuma bayan zuwan matar tasa ya fita yace zaije ya shigo dasu.
Nan take Tafida ya manta da Nadra da kuma ƙawarta, ya miƙe yanawa me sunan nasa murmushi, yaron ɗan kimanin shekaru uku ya kar6a a hannun Muktar, yana gaisawa da matar Muktar ɗin.
“ Lil me ykk”
Yaron me tsantsar kama da ubansa ya kalli Tafidah
“Lafiya”
“wai ni da me kuke kiransa ne ?”
Muryar Mairama dake bayansu ta tambaya.
“Tafida”
Muktar ya bats amsa
“Gaskiya kun cuce shi, menene wani Tafidah?, da Eshaan ɗinsa ma kuke kiransa dashi”
Cewar Mairama, tana dubansu.
“Wallahi ranki ya daɗe baban ne yake kiransa da haka, kuma sunan sai yabi bakin mutane”.
“Ai kema da lefinki, sunan da uwa take kiran ɗa dashi ai shine suna”.
“Yanzu ranki ya daɗe menene aibun Tafida ?, nagade sunan ɗan uwanki ne”
“sunan ɗan uwan nawa, amma kuma ai shi yarone ƙarami, sunan ya masa girma”.
Sai maganar ta bawa Tafida dariya, shi tun yanada shekara uku suke kiransa da Tafidan, amma bai musu girma ba a lokacin, sai yanzu.
*
Maryam ta kalli Anti Fati dake ta faman hira itada dangin mijinta, zaune suke a kan wasu kujerun dake wajen, ta juya tana kallon amarya da angon da basu jima da shigowa ba, ita kwalliyar amaryace tafi birgeta, itama ta tsara abubuwa da yawa wanda za tayi idan bikin ta ya zo.
Abinda bata sani ba shine, wasu kaddararorin basa zuwama ɗan adam kamar yanda ya so, suna zuwane kamar yanda suka so.
Ita duk sai tajima wajen ya isheta, yanayin kallon da samari ke mata, ga kidan wajen dake hawa mata kai, dan haka ta ɗauki Imran ta miƙe daga wajen, ta ɗan taba kafaɗar Anti Fati.
“zamu ɗan fita waje”
Ta faɗi bayan Anti Fatin ta juyo ta kalleta
“Ina xakuje ?”
“Waje zamu fita”
“To kada kuyi nisa”
“Umhm”
Maryam ta amsa ranta fari tas, dan zata fita waje ta huta da kallon da samari ke binta dashi, gaba ɗaya a takure take, gyalen nan kwata kwata bata jin daɗinsa, tana tafiya tana gyara gyalen.Alokacin ne kuma abun ya faru, matakin farko na sauya

Please Login or Register in order to submit comment