Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata da banbanci da halp vase, duk da hannun rigar dogo ne.
“Kai mata godiya, kace mata nagode sosai”
Ta ƙarashe tana buɗe wani kit na sarƙa da dankunne, ga kuma sarƙar kai a ciki, Maryam ta kama baki, wato de so ake ta koma ba'indiya.
“A'a bazan ɗau wannan nauyin ba, na baki de ki mata godiya”
Ya faɗi yana buɗe wayarsa, Maryam ta gyaɗa masa kai, lambar Neha ɗin ya lalubo, sannan ya miƙo mata, Maryam ta kara a kunnenta.
“ Mera bhai, aap kaise hain? ( yayana, ya kake ?)”
Abinda muryar ba'indiyar ta faɗi kenan, bayan an ɗaga kiran, Maryam ta gane me take cewa, dan irin waɗanan kalaman na indianci tana tsintarsu a kallo, saide bata san da ya zata amsa mata ba, bata saniba ma ko bata jin hausa dan haka tace.
“It's not him, it's his wife”
Sai taji budurwar tana dariya.
“Surukata ya kike ?...”
Mamaki ya ɗan kama Maryam, ko da yake, ai ba abun mamaki bane, tunda yayan nata ma yana jin hausa.
“Lafiya, kema ya kike ?”
Maryam ta tambaya.
“Ina lafiya sosai, kin ɗauka bana jin hausa ko ?”
Maryam na ɗan yaƙe ta gyaɗa mata kai, kamar da aka ce mata Neha ɗin tana ganinta.
“Ina jin hausa sosai, wata ƙilama nafi mijinki iyawa”
“Chup tum, yeh choot bulawu (Ki mana shiru, wannan ai ƙarya ce)”
Maryam ta juya ta kalli Tafida dake wannan batun, wanda yana sauraron abinda suke cewa, duk da wayar ba a speaker take ba, sai Maryam ta sauƙe wayar daga kunneta ta saka a speaker.
“Woh kaun hai ? (waye wanna ɗin?)”
“Au, bama ki gane ni ba kenan”
Ya amsata da hausa, sab'anin ita da ta masa hindi.
“Bhai kaja baya kawai, wannan maganar ba taka bace, ƙarya nayi ?, ai nafika iya hausan”
“Kiyi istingifari yarinya, kinsan de ni hausa ce ta haifeni, ke kuma daga sama kika koya”
Sai faɗan nasu ya bawa Maryam dariya, kamar ba Tafida ba, wannan me kama kan, me ji da aji, me magana cikin ƙasaita, ya koma Yaya wanda yake nishaɗi da kanwarsa.
“Naji duk da daga saman na koya nade fika”
“Ki kiyaye nifa Nik(Neha Imran Khan), ki bar ganin ke soja ce, ni har yanzu ina miki kallon wannan yarinyar wadda na ɗauketa sanda tana jaririya”
“Surukata manta da wannan, idan muka biya shi ba zamu zanta ba”
Maryam na dariya ta cire wayar a speaker, sannan ta mayar kunnenta, hira suka ɗan tab'a kaɗan, kafin Maryam ta mata godiya daga haka wayar ta ƙare.
“Naga itama tana jin hausa sosai”
Tafida na murmushi yace.
“Mijinta ai ɗan nigeria ne, shima bahaushen ne, kuma gata sojar nigeria”
“soja kuma ?”
ya gyaɗa kai yana ɗauko bowl ɗin yoghurt ɗin nan.
“Eh soja ce”
maryam ta gyaɗa kai cikin gamsuwa, ƙwaƙwalwarta na hasko mata wannan hoton nasu da ta gani shida ita, wanda jta ɗin kesanye cikin kayan sojoji.
“Shima mijin nata soja ne”
“Lalle kam”.
“Tare muka taso da ita, duk da ba sosai muke haɗuwa a india ba, amma muna haɗuwa a abuja, dan ina zuwa hutu a gidansu, kuma itama da ta gama secondary a nan india ta koma taci gaba, sosai na shaƙu da ita, kamar wata ƙanwata da muka fito ciki ɗaya haka nake ɗaukarta”
Wayarsa ce ta yi ƙara dan haka ya kai haannu ya ɗauka, a lokack guda yana aje bowl ɗin hannunsa, Khabir ne ke kiransa ya ɗaga da sallama a bakinsa.
“Kaifa baka san zaman lafiya, yanzu sbd Allah jiya fa na dawo, amma shine kake wannan magamar”
Shine abinda ya faɗi bayan ya gama sauraron Khabir ɗin, ya kuma yin shiru yana sauraren nasa.
“Shikenan Allah kai mu goben”
Daga haka ya sauƙe wayarsa, ya kalli Maryam da take kallon tv.
“Gobe da yamma ki shirya, zamu fita”
Kalmar 'fita' ita tafi yiwa Maryam daɗi, dan tun da ta sako ƙafarta a Alaro city bata ƙara fita ba, ko saloon ɗin da suka je a cikin Alaron yake.
Taji dadi sosai, ko ba komai ta samu dalilin da zata saka chickankari ɗinta, dan shi yafi mata kyau fiye da saree ɗin, ta ƙudirce a ranta cewa bazata saka saree ɗin nan ba, to a wani dalili ma?, haka kawai, ita bama ta iya ɗaura shi ba, kuma bazata iya saka shi ba da wannan gajerar blouse ɗin da bata kai cibiya ba.

*Birnin taraiyya, Abuja*
*Da 09:00pm*
Heleen ce tsaye a ƙofar wani tsohon gini, bayan ta kuma yaranta ne guda biyu, gaba ɗaya ranta a b'ace yake dan ita ta yi niyyar komawa lagos jiya, amma ogansu Ya roƙeta da kada ta dawo ta bari su gama aikin tukunna, dan haka ta haƙura, amma ta yi alƙawarin sauƙe bacin ranta akan wanda suka zo farmaka.
Sanye take da baƙar tank top, sai wani baƙin legging, wannan kalbar attachement din ta ɗaureta da ribbom, ƙafarta sanye cikin takalimin timberand boot, hannunta na dama riƙe da bindigarta ƙirar pistola.
“Zamu iya shiga Oga”
Ta gyaɗa masa kai tana saka bullet a cikin bingidar, sannan muryarta Ta fito cike da umarni.
“Muje!”
Itace a kan gaba, su kuma suna bayanta yayinda suma suke riƙe da bindigar. Kan me uwa Da wabi kawai suka shiga yi a cikin wajen, duk wanda su ka yi karo dashi sai sun sammasa alburishi.
Da haka har suka ƙarasa gaban Ogan nasu, wanda yake pointing ɗin Heleen da bindiga, babu ƙwayar tsoro a idonta ta tunkareshi, an jima da wuce lokacin da za ta ji tsoro, sanda zata shiga ƙungiyarsu ta aje tsoronta.
Hannunsa sai karkarwa yake yana nunata da bindigar a lokaci guda kuma yana ja da baya, Heleen bata fasa tunkararsa ba, da haka har saida ta cimmasa.
Kuma tana ƙarasa gabansa bata jira komai ba, ta ɗago da ƙafarta ta daki hannunsa, bindigar ta faɗi can gefe, Ya juyo ta kalleta bayan ya kalli bindigar dake yashe a ƙasa, babu alamun rahama ko imani a idon ta, kallonsa take cikin ido.
Hannunsa Ya ɗaga zai roƙeta kan ta yi haƙuri ta masa afuwa, bata bashi damar magana ba, ta sakar masa naushi a fuska, sannan ta masa wani a ciki, kafin ta riƙe wuyansa da hannunta ɗaya ta ɗaga shi sama.
Ya shiga kakarin mutuwa yana riƙe hannunta dan Ya shaƙu sosai, sakinsa ta yi tana dukansa a ƙafarta. Ya faɗi ƙasa timm!, ta gyara tsaiwarta tana zaro bullet haɗi da lodawa a cikin bindigarta, dan ta ƙarar da wanɗa ta loda ɗazu.
“Me yasa kaci amanar mu ?”
Muryarta ta fito cikin wani irin b'acin rai, kuma bashi take kallo ba, bindigarta data ɗaga sama bayan ta loda bullet take kallo, cikin shaƙaƙƙiyar muryar da taci azaba yake faɗin.
“Na roƙe ki Heleen, kiyi min.....”
Ji kake tass!, ta sakar masa bullet a ka, bindigar tata har hayaƙi take.
“Oga ai bai gama bayani ba kika sheƙe shi”
“Bana buƙatar bayaninsa, shine ya zama katanga tsakanina da ganin Tafida, ba shi kaɗai ba, duk wanda yaso Ya raba tsanani da Tafida irin sakamakonsa kenna”.

*Abuja*
“Mom lafiya kuwa ?”
Mero ta ɗago ta kalli Kamal dake tsaye a gabanta, Kamal kam kawai ƙare mata kallo yake, ta rame ta yi wani baƙi, gaba ɗaya basa gane mata a cikin kwanakin.
Zama ya yi akan kujerar da take, kusa da ita yana ci gaba da kallonta.
“Mom, ki faɗa min, meke damunki wai ?”
Mero ta sauya hannunta na dama da na hagu wajen tare hab'arta, sannan muryarta ta fito cike da damuwa.
“Hanama ce Kamal”
Hanam ?, wai yaushe yarinyar nan zata barsu su huta ne ?, ta bar gidan ma amma bata bari sun huta ba?.
“Mom Ya kamata a ɗauki mataki, dan shima mijin nata Ya takura min a wajen aiki”
“Shi arnen ?”
“A'a Mom, uche musulmine, yana sallah”
Ta tab'e baki, dan ita wannan ba matsalarta bace, Uche ko me kamarsa basa gabanta.
“Yanzu miye abin yi ?”
Ta ɗan juyo ta kalleshi kaɗan.
“Babu Kamal, babu abinda zamu iya”
Girarsa na tattarewa waje guda yake faɗin.
“Ban gane ba, babu ?!”
Itama ta gyaɗa masa kai cike da tabbatarwa.
“Babu, mu barsu da balinsu, kaga akan Hanam ɗin nan aurena ke gil-gilwa, dama an yanke min igiya ɗaya sbd uwarta, sauran biyun ma gasu suna shirin tsinkewa”
“Yanzu me Ya faru ?!”
“Abban ku baya min magana, ya yi fushi da ni, ko nice da girki idan na kai masa abinci baya ci, na kasa gane kan bawan Allahn nan, kaga fa da duk abinda nake mata tun tana ƙarama bai tab'a cewa komai ba, sai de ya ɗanyi b'acin ransa na kwanaki, daga nan komai Ya wuce, amma, banda yanzu”
Kamal Ya sauƙe wani numfashi.
“To wai ni taya ma a ka yi Ya sani ?”
“Jabeer ɗin ne ya faɗa masa mana, kaga fa saida na gargaɗeshi da kada Ya ƙira sunana amma, dan sh**yar sai da ta faɗa”
Ta ƙarashe da ƙwafa, Kamal ya yi shiru bai ƙara cewa komai ba, yana tunani.
_Su Daaso ƴan ƙauye, ba'asab chickankari ba_
_Wayyo Allahna, nifa wallahi Heleen tsoro take bani, irin wannan taku baka_
_Ina godiya a gare ku🙏_
🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.


⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Wannan sadaukarwa ne gare ki Ammy Ummi*

*BABI NA ASHIRIN DA SHIDA (26)*
*Hadejia Emirates*
*Da 09:30pm*

Galadima ne zaune a Parlon ɗakinsa yana ɗaga kwalbar giya yana tittilawa a bakinsa.
Be san wata masiface ta same shi ba, a wattanninan kuma giya yake sha'awar sha, ya kasa gane dalilin da yasa duk asirin da za'ayiwa Tafida baya kamashi, me makon ma ya kama Tafidan sai de shi ya yana aikata abinda akayiwa Tafidan asiri a kai.
Kuma har yau ya kasa faɗawa Fulani cewa asirinta fa baya cin Tafida, shi ya ke ci, sbd yana jin daɗin abun, shi yasa baya so ya faɗa mata bare ta dena.
Kansa ya ji yana masa ciwo kaɗan-kaɗan, sai ya aje kwalbar, a hankali a hankali ciwon yake ƙaruwa, kansa ya dafe sai kuma yaji ƙashin hayansa ya amsa.
Wata iryar ƙara ya saki yana riƙe bayan, sai kuma bakinsa ya gurɗe ya koma gefe, harshensa ya karye, ƙafafuwansa suka malkwaɗe masa, ihun ma ya kasa yi sbd bakinsa daya koma gefe harshensa ya harɗe, hannayensa ne suma suka shanye nan take, ya dawo kamar lagwani.
*
Fulani Sadiya na zauna a parlo tana duba wasu kaya a waya, ta ji ƙarar Galadima, A kiɗime ta mike ta yi b'angaren da ɗakin nasa yake, tafiya take sauri-sauri, gudu-gudu.
Da haka har ta iso ƙofar parlonsa hannu ta kai ta buɗe ƙofar, abinda ta fara arba dashi shine, Galadima ne yashe a ƙasa, kansa a langwab'e a gefe, bakinsa ya goce, yawu na zuba ta gefen bakin nasa, hannayensa a shanye, ga ƙafafunsa sun malkwaɗe kamar wani alkaki.
Wata razananniyar ƙara ta saki haɗi da salati hannunta a ka, sai kuma ta yanke jiki ta fadi.
(Ta mance cewa Allah ne me komai da kowa sai yanzu dan taga ɗan da cikin wani hali ta ambato sunansa,hmmm Allah ya fishemu).

MARYAM POV.
Ta juya a gaban mirror yafi sau goma, chickankari(pakistan) ɗin da ta saka ya bala'in mata kyau, gashi ya karb'i jikinta kamar da aka gwada da ita, waje ta samu ta zauna akan stool ɗin gaban dressing mirror, tana bin kayan kwalliyar da suke kai da kallo.
Tunda tazo lagos kusan wata biyu bata tab'a yin kwalliya ba ko sau ɗaya, duk da ko sanda tana Haɗejia ma ba yi take ba, saukaƙƙaƙiyar kwaliya ta yi a fuskarta, gashin kanta da take ganinsa kamar ba nata ba sbd laushin da ya yi ta saka masa ribbom kawai ta fakeshi a baya.
Ɗan gashin dake gaba-gaban bashi da laushin da zai kwanta kamar na bayan, dan haka ta saka gell, ta kawo sea green ɗin mayafin ta ɗora a kanta, sannan ta ɗauki sea green ta kalmi da jaka a cikin na kayan aurenta ta saka takalmin ta riƙe jakar a hannunta.
Zata iya kirga lokutan da ta tab'a saka gyale a ratuwarta, bata cika saka gyalen ba amma yau ta saka, sbd tsabar daɗin da take ji zata fita daga Alaro city, ko ba komai zata ga gari, kuma ita tun da Allah ya yi fa da san fita.
Ta fesa turare me sanyi sannan ta ɗauki wayarta ta saka a cikin jakar ta fito.

TAFIDAH POV.
Zaune yake akan kujerar parlon gidansa, Maryam yake jira dan shi ya jima da shiryawa.
Sanye yake da farar plane hoodie, sai farin chinos trouser hatta da canvas ɗin dake ƙafarsa farine, ya kawo denim jacket baƙa ya ɗora akan hoodie ɗin wadda kalarta ta haɗu da gashin kansa, wanda ya ƙara tsayi sbd rashin aski, amma kuma kamar kullum a cikin tsari me kyau sai sheƙi yake.
Taku yaji daga kan stairs hakan ke nuna masa cewar Maryam ta gama shiryawa, a hankali ya ɗago da kansa ya kalleta.
Tunda yake bazaice bai tab'a ganin mace wadda ta yi kyau kamarta ba, ya gani ya ga wanda sukafita ma, amma kuma nata kyan na da ban ne, yau ta masa kyau fiye da kullum, kuma babu abinda ya ƙara mata kyau a idonsa irin kayan al'adarsa da ta saka, ya ƙara mata kyau sosai, masam cewarsa mutum me san al'adu.
Maryam ɗin ma kallonsa take, ba zatace bata tab'a ganinsa da ƙananun kaya ba, dan yana sakawa idan yana gida, amma idan zai fita ne bata tab'a gani ba, bata tab'a ganin ya saka ƙananun kaya ba idan zai fita, sai de idan filin cricket zaije, kuma shima jersey yake sakawa da wandonta.
Shi baya buƙatar ace ya yi kyau, kullum cikin kyansa yake, sai de ya ƙara wani abun. Miƙewa ya yi sannan yace.
“Shall we ?”
Ya ƙarashe yana miƙa mata hannu, Maryam ta sunkuyar da kanta ƙasa tana murmushi kunya na kamata, ko rannan ma da ya yi hugging ɗinta Allah kaɗai yasan yanda ta ji kunyarsa. Tana jin sautin murmushinsa.
Kafin ta ji yana takowa inda take, kuma beyi tunanin komai ba ya kai hannunsa ya kama nata wanda bata riƙe jakar da shi ba.
Maryam ta ji abinda ta saba ji a duk sanda zai riketa, na ratsawa tun daga kanta har kafafunta.
A tare suka fita kuma hannunsa na cikin nata, har suka shiga cikin mota.
Maryam tana ta kallon unguwar tasu yadda ta mata kyau a cikin yammacin, wasu ma'aikata ne sun dawo daga aiki, wasu ƴan kasuwa, wasu school kowa de yana harkarsa.
Lokacin da suka fita daga babban gate ɗin Alaro city har wata ajiyar zuciya ta sauƙe, taci gaba da kallon gari har suka yi wata doguwar tafiya kamar masu barin gari, amma ba garin suke bari cikin garin ma suke shiga. Tana ganin ana ta kiran wayarsa amma bai kula ba.
Ƙofar wani waje taga sun shiga, wanda a symbol ɗin sa aka rubuta 'LANDMARK BEACH'.
Hakan ke nuna mata cewa wajen beach ne, a parking lot ya yi parking sannan suka fito a tare, shi da kansa ya zagayo inda take yana ƙoƙarin kama hannunta ta janye, ganin wajen akwai mutan.
“Me ya faru ?”
Muryarsa me zurfi ta tambaya.
“Akwai mutane a wajen”
Ya ɗan juyo ya kalleta kaɗan.
“Ko goyonki zanyi anan babu me kallon mu bare ya mana magana”
Maryam ta kawar da kanta gefe, kunya na ƙara kamata, ya yi murmushi yana sauraron bugun zuciyarta.
“Muje to”
Ya faɗi yana nuna mata hanya, suka shiga tafiya a tare, duk inda suka ratsa sai an kallesu, kuma Maryam tasan kallom ba nata bane, na Tafida ne, dan yawanci ƴan mata ne suke kallonsa.
Taji wani abu na maƙale mata a maƙoshi, ta daure ta haɗiye har suka shiga wani restaurant da a samansa aka rubuta 'SHIRO LAGOS'.
Babu kai kawon mutane sosai a wajen, saida taga sun zagaya baya wurin taga a wajen ma babu kowa sai wasu mata da maza dake zaune a kan wasu dogayen sofa.
Mutanen dake zaune a wajen basu haura shida ba, mata uku maza uku, suma mutanen suna ganinsu suka miƙe.
“ Finally de yau munga Mrs Tafida”
Taji wani ya faɗi a lokacin da suke ƙarasawa wurin, kuma tanada tabbacin bahaushene, duk da ba kayan hausawan ke a jiknsa ba.
“Ai kuwa tunda ba'a gayyace mu biki ba”
Matar dake tare da shi ta furta tana murmushi, hannu taga Tafida ya bawa mazan suna gaisawa, ita kuma ta gaisa da matan dan taga ɗaya ce kawai ba bahaushiya ba.
A kujera ɗaya suka zauna ita da Tafida duk da kujerar nada tsayi sosai.
“Tafida matarka ta yi kyau, amma de yace kinyi kyau ko ?”
Wata daga cikin matan itama ta faɗi, tana zaune a kusa da wani wanda da alama mijinta ne.
A hankali Maryam ta juya ta kalli Tafida, kamar shine zai bata amsar, sai kuma ta girgiza mata kai.
“This is not fair wallahi, ya za'ayi ta yi kyau haka baka faɗa mata ba”
Maryam ta sunkuyar da kai.
“Ai babe rabu da wannan, bai iya soyyaya ba kwata-kwata bari zan saka shi a makaranta yaje a koya masa”
Gaba daya suka yi dariya harda shi Tafidan
“Yanzu de dan Allah ka faɗa mata ta yi kyau”
Tafida ya dan juya ya kalli Maryam.
“Miriam”
Ta juyo tana kallonsa.
“You look gorgeous, and you look very attractive and cute, you look very pretty to the extant that i can't take my eyes off you, wifey you have looks to die for, i think you are stunning, you are so adorable wifey”
Duk abinda ya faɗi a bakinsa ya fito ne daga ƙasan zuciyarsa, da gaske yake furta hakan har cikin ransa.
Maryam ta sunkuyar da kai sbd kunya, bata sani ba wata ƙila ya faɗi abinda ya faɗi sbd an nemi da ya faɗa, ko kuma ya faɗi hakan ne kawai dan yana san faɗar, amma ba dan ta kai matsayin ba, ita bata kai haka ba sam.
“Babe kace bai iya ba, wannan kalamai haka, ai ko kai sede ya koya maka”
suka yi dariya.
“Dr. Eshaan ai ya kamata a gabatar da mu ko ?”
“Hakane, Miriam wannan shine Dr. Khabir, wannan kuma Dr. Abubakar, sai Dr. Ola gaba ɗayansu abokan aikina ne, muna aiki tare a St. Nicholas Hospital. Waɗanan kuma matansu ne, Hajara, Fatima da Comport”
Dukansu Maryam saida ta sake gaisawa dasu. Dr. Ola ne ya fara jawabi.
“Kamar de yanda na sanarwa da kowanmen ku, mun haɗa wanna zamane domin mu samu wani abinyi a wannan watan, kullum muna cikin aiki, bamu da abinyi sai shi, ba kuma ma hutawa sai weekend, wani lokacin ma a weekend ɗin bama hutawa, dan haka yau muka shirya wannan fita dan musamu mu miƙe ƙafa mu kuma ƙara sanin juna”.
Yayi jawabin ne a cikin harshen turanci, Dr.Abubakar ne ya yiwa waiter magana, waitern ne ya kawo abinci kala-kala da suka yi oder aka zube musu shi akan dogon teburin dake aje a gabansu.
*
Maryam ce tsaye a jikin balcony ɗin dake wajen cin abincin, daddaɗar iskar dake busowa daga tekun dake tsallaken balcony ɗin take shaƙa, tana kallon yanda ruwan ke kai komo, ga fitilun wajen da suka fara haske sbd ƙuratowar magariba, ga mutane na wucewa akai-akai.
Ko a mafarki bata tab'a zaton rayuwarta zata sauya kamar haka ba, bata tab'a zaton zata wayi gari ta tsinci kanta a cikin irin wannan rayuwar ba, iskar wajen dake kaɗawa ce ke tuno mata da rayuwarta ta baya da kuma waddama take ciki a yanzu.
“Maryamu Daaso!”
Ta juya a hankali ta kalleshi, duk da tasan shiɗin ne, domin koda a bacci za'a tasheta ta ji muryar sa zata gane muryar tasa, shi ɗin ne tsaye a bayanta, hannunsa sanye cikin aljihun chinos trouser ɗin dake jikinsa, ga wani dan gajeren murmushi dake playing akan lebensa.
Kamar wani jarumin film ɗin india wanda director ɗin yasa shi yayi irin tsaiwar, itama ɗan guntun murmushin tai masa tana juyawa taci gaba da kallon tekun, sakamakon takowa da yake zuwa gareta.
“Bakyajin sanyi ?”
Muryarsa me cike da kamewa da aji ta tambaya, yayinda ya ƙarasa kusa da ita ya tsaya, shima yana kallon wajen.
“Babu sanyi, view ɗin akwai kyau”
Kansa ya gyada mata a hankali, kuma ba tare da ya kalleta ba.
“Ko inama a lagos yana da kyau wifey, akwai wajaje masu kyau sosai, ki bari wata rana zamu zaga gari”.
Tayi murmushi me sauti tana sauƙe kanta ƙasa sannan ta ɗago.
“Muje magariba ta kusa”
Ta gyaɗa masa kai a hankali, sannan suka juya a tare.

UCHENNA POV.
“Ya matarka take ?”
Muryar mahaifiyar sa ta tambaya daga cikin wayarsa, ya yi murmushi yana shafa sumar kansa me karfi irin ta sauran Africans.
Yana zaunene a balcony ɗin ƙofar entrance ɗin gidansa.
Matarsa?, abunma ya bashi dariya, matar da babu wani abu na kusanci irin na mata da miji da ya shiga tsakaninsa da ita, ba wata hira suke ta arziki ba, maganarsu biyuce a rana, daga gaisuwa sai sannu da zuwa, sai kuma yanzu da ta fara girki idan ta gama zabtace masa yazo ya ɗauki nasa, bai san me yasa take haka ba, amma ya san cewa Hanam bata sansa, kuma baisan dalili ba.
“Tana lafiya”
“Ka gaidamin da ita”
“Inshallah zataji”
Daga haka wayar tasu ta ƙare, miƙewa ya yi ya koma cikin gidan, yanzuma bata parlo, sam yau be ji motsinta ba, sau ɗaya ya ji kukan Arya a ɗakinta.
Rashin ganin nata ya ɗarsa masa shakku a zuciyarsa, Hanam ba irin wannan matan bane, tana bawa aikinta muhimanci, koda wasa bata fashin zuwa wajen aiki, sai de idan wani uzurine me ƙarfi ya taso mata, duk yanda akayi ba lafiya ba.
Shawara ya yanke akan zaije ya duba yaga ko lafiya, ɗakin nata ya nufa, saida ya isa ƙofar ɗakin, ya ɗora hannunsa akan handle ɗin, sai kuma ya samu kansa da kasa buɗe ƙofar.
Tunda tazo gidan bai tab'a shiga ɗakinta ba, tun ranar da aka sauya kayan gidan bai ƙara shiga ba.
Sai da ya furzar da wani numfashi sannan ya murɗa handle ɗin, ya tura ƙofar gaba tare da bugawar zuciyarsa, dan baisan me zai tarar ba, ɗakin ya shiga ƙarewa kallo.
Baiga kowa a ciki ba sai Arya dake zaune akan gado yana wasa da teddy, ƙaran zubar ruwan da yaji a banɗaki yasa ya fahimci cewa tana banɗakin.
Ƙarasawa ya yi jikin gadon, ya kai hannu ya ɗauki Arya dake ɗaga masa hannu alamun ya daukeshi, zuwa yanzu ya fara ƙiwa amma kuma shi baya masa, wasu lokutan har idan ya karb'eshi baya yarda ya koma wajen Hanam.
Shi kansa ƙaunarsa da yaron na bashi mamaki, wasa ya shiga masa yana faɗin.
“Yau ina kashiga ban gan ka ba ?.....”
Ƙaran buɗe ƙofar banɗakince ta dakatar da maganar tasa, ya juya idonsa zuwa ga ƙofar bandakin, ya kalleta.
Sai da zuciyarsa ta dungura fiye da ƙirgensa a lokacin da ya ɗora idonsa akanta, wata pleated maxi dress ce me gajeren hannu jikinta, gashin kanta nannaɗe cikin bun, wanda ta ɗora claw clips a samanta.
Ba shigar jikintace ta haddasa dungurawar zuciyarsa ba, abinda yake gani a fuskarta shine ya haddasa masa bugawar zuciya sau biyu a lokaci guda.
Wani irin yanayi ne ɗauke a fuskar tata, irin yanayin da yake gani a fuskar mom ɗinsa a duk lokacin da babansa ya daketa, irin yanayin da yake gani a fuskar mahaifiyar tasa idan bata da lafiya.
Idanuwanta sun faɗa ciki, kuma sunyi ja, haka kuma yanayin fuskar tata a raunane yake, fuskar tata fayau.
Kallonsa take kamar yanda shima yake kallon nata, a hankali ta fara takowa zuwa wajen da yake. Tun safe ta tashi da zazzab'i, yau ta ɗaura niyyar samun Abba akan batun Uche, dan tun rannan baya gari, ya yi tafiya.
Jiya ya kirata yake faɗa mata ya dawo dan haka zata iya zuwa ta ganshi, kuma tace masa zata zo ta ganshi yau, sai kuma Allah beyi ba, ta tashi da zazzab'in.
Ta saba a duk lokacin da take jinya babu me damuwa da halin da take ciki sai Abba, idan kuma baya gari ko baya gidan saide taci ciwonta ita kaɗai ta cinye, ta saba da hakan tun ba yau ba, dan haka a nan ɗin ma da babu wanda ya leƙota bata damu ba duk da tasan Uche ɗin yana gidan, kuma ba ta yi mamakin ganinsa a ɗakinta ba.
Arya ya aje akan gado yana ci gaba da kallonta, ta ƙaraso har gabansa ta tsaya tana kallonsa da idanunwanta dake nuna cewar bata da lafiya ƙarara. A hankali ya yi yaƙi da abinda yake ji a zuciyarsa yace.
“Baki da lafiya ne ?”
Muryar tasa ta fito cike da kulawa, kulawa irin wadda bata samunta daga wajen kowa sai Abba, Abbanta ne kawai ke mata magana cikin irin wannan kulawar, idanuwanta ta ɗan juya kaɗan, sannan tace.
“Zazzab'ine kawai”
Kansa ya girgiza mata a hankali yanaci gaba da kallonta, a hankali ya ɗago da hannun sa ya yi abinda daga ita harshi ba su yi zato ba, shi da kansa da ya yi abun saida ya bashi mamaki.
Da hannun nasa ya tashi sauƙa, bai sauƙa a ko ina ba sai akan goshinta, Hanam ta riƙe

Please Login or Register in order to submit comment