Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

numfashinta da ƙyar, wanda ke shirin zarcewa maƙogwaranta, sbd wani abu daya ratsa tun daga hannunsa har zuwa fatar kanta, wani abu kamar shock ɗin wutar lantarki.
Abinda ya faɗi bayan hakan shine ya ƙara saka zuciyarta kokwanto a kansa.
“Subhannallh, jikin akwai zafi sosai”.
Anya kuwa taji da kyau ?, kamar subhannal taji yace ?, Anya kuwa ba a baibai take kallon Uchenna ba ?, shin da gaske shi Cristian ne kokuwa ?.
______________
_Helloo!, Hanam na tambaya, someone should answer her please_
_Game da ESHAM(ESHAAN DA MARYAM). Bani da ta cewa_
🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.


⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Gareki na sadaukar da wannan babin Maman Ihsan*

*BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI (27)*

*Cogrove Estate,st 3, house NO 334*
“Malaria ce kawai, amma babu wata damuwa ki tabbatar kinsha waɗanan magungunan, in Allah ya yarda zaki ji sauƙi”
Muryar Dr. Hasina likitan asibitin Cosgrove estate ke korowa Uche da Hanam wannan bayani, bayan Uchenna ya yi amfani da wayar kiran emergency ya kira can asibitin sun turo musu ita.
Hanam dake kwance akan gado rabin jikinta lillib'e da bargo ta gyaɗa mata kai.
“Bani takardar sai inje na siyo mata”
Muryar Uchenna dake tsaye daga baya ta fasi cikin irin wannan kulawar ta ɗazu, riƙe yake da Arya a hannunsa yana kallonsu, Dr. Hasina ta juyo tana masa murmushi.
“Kada ka damu Uche zan siyo sai na aiko maka, ai kai kafi da haka Uche”
Ya ɗanyi murmushi, kirkinsa na saka a masa alfarma a lokauta da dama, dan Uchenna na kowa ne, kowa nasa ne, bashi da abokin faɗa kona gaba, ga haba-haba da kowa, kuma kullum cikin barkwanci ya ke.
“A'a Dr. Ki bari de naje”
“A'a ka zauna da matarka kawai, tana buƙatar ka”
A hankali ya jinjina kai, Dr. ta gama haɗa kayanta sannan tai musu sallama ta fita
“Bari naje na rakata”
ya fice hannunsa riƙe da Aryaan, Hanam tabi bayansa da kallo tunanika iri-iri na yawo akanta, wai meke shirin faruwa ne ?, ya zama dole ta nemi Abba su tattauna.
Jim kaɗan ya dawo, zama ya yi a kusa da ita cike da kulawa irin ta ɗazu yace.
“Me zaki ci ?”
Kai ta girgiza masa a hankali tanaci gaba da kallonsa.
“No you need to eat, how will you take medicine without eating?”
“Baki na nake ji da ɗaci....”
Ta amsa masa a hankali muryarta na fita cikin zafin zazzab'in dake jikinta.
“Duk da haka, ya kamata ace kinci”
Bata san musun, dan haka ta gyaɗa masa kai, dan yawan maganar zai iya saka mata ciwon kai, ita dama can ba me yawan surutu bace, yanayin rayuwane ya sa ta zama me yawan magana.
“Baki da zani na goye shi?"
“Babu zani saide towel”
Kansa ya gyaɗa mata sannan ya shiga bathroom ya ɗauki towel ɗin, bai fito ba saida goyon Arya.
Hanam taji zuciyarta ta motsa, wani abu daga can ƙasan zuciyar tata ya gangara zuwa ƙasa, ƙasa can inda bata san da shi ba.
*Alaro city lekki, lagos, B3 house No. 122*
*Da 10:00am*
TAFIDA POV.
“Me ki ka dafa yau ?”
Muryar Tafida me zurfi ta tambaya, yayinda yake karb'ar wayar da Maryam ke miƙa masa bayan ta fito daga kitchen, yayinda shi yake zaune a parlo bayan ya dawo daga wajen buga cricket.
Maryam ta zauna a ƙarshen kujerar tana amsa masa da.
“Shinkafa da wake”
“Bana cin shinkafa da wake Miriam”
Ta ɗan juyo ta kalleshi, a sannan ne kuma taga abinda bata lura dashi ba ɗazu, gefen fuskarsa ya yi ja da shatin circle, kamar an daki wajen da wani abu.
“Me yasa baka cin shinkafa da wake?”
Ya shafa sumarsa yana ci gaba da danna wayarta sbd yana mata editing vedion da ta yi recording na jiya dana yau, dan bai samu zama ba jiya.
“Haka kawai, dan ban tab'a ci ba, kuma babuma a inda zan ganta bare nace”
Har Maryam za ta yi magana sai kuma ta yi shiru, to a ina kuwa zai ci?, shida yake gidan sarki, sai ta sauya zance da.
“Da wasa nake maka ma, ba ita na yi ba, pancake ne da salad sai fried chicken”
Ya jinjina mata kai kaɗan, yana ƙara godewa Allah da ya sako Maryam a cikin rayuwarsa, kyawawan halayenta sune a kullum suke bata matsugunni me kyau a zuciyarsa.
Bugun zuciyarta ya fara saurare, kafin ransa ya raya masa ya yi abinda zai saka zuciyar tata ta buga da sauri, dan idan zuciyarta na bugawa da sauri sautin yafi masa daɗin saurare.
Karshen kujerar ya kara matsawa sannan ya kwanta, Maryam bata zata ba taji kansa a cinyarta, zuciyarta ta buga da ƙarfi, wani abu ya shiga kaikawo daga zuciyar ta zuwa ƙwaƙwalwarta yana faɗa mata cewar bazata tab'a sabawa da wannan yanayin ba.
Wata busashiyar iska ta haɗiye a maƙogwaronta sannan ta sunkuyar da kanta ta kalleshi, amma kuma shi ba ita yake kallo ba, Wayar dake hannunsa yake kalla yanaci gaba da dannata.
Kafin taga ya ɗago hannunsa ya kamo nata hannun wanda ke ɗauke da guntun jan lallen da ta yi da be koɗe ba. Maryam ta rintse idanunta.
Sakamakon hannunta daya sauka kan lallausa kuma me taushin sumarsa, sai kawai maganar su Aisha ta shiga dawo mata a ƙwaƙwalwarta, ranar da suke faɗin suna so su tab'a sumarsa.
Sumarsa nada laushi da santsi fiye da tata dan shi tasa naturally haka take, ita kuma tata ƴan dabarune akayi ta koma kamar hakan.
Muryarsa ta fito a hankali, cikin wani irin yanayi daya haddasa bugawar zuciyar Maryam sau biyu a lokaci guda.
“Wifey ki sosa min kaina, sumar ta min yawa”
Da ƙyar ta iya lalubo sautin muryar ta, sannan tayi ƙarfin halin furta.
“Ƙaiƙayi take maka ?”
Yanayin yanda muryar tata ta fito, da yanda zuciyarta ta buga saida ya kusa saka shi dariya, amma sai ya dake, dan da gaske yana buƙatar a sosa masa kan nasa, a hankali ya girgiza mata kai, wadda ya haddasa motsawar cinyarta.
“A'a ba ƙaiƙayi take ba, kawai de banajin daɗin yawan sumar dake kan nawa ne”
“To me yasa ba zaka aske ba ?”
“Sbd na yiwa Daadi alƙawarin bazan aske sumata ba sai naje india, kuma dama mun saba haka da ita, idan tana so na zo india sai tace tanaso na tabbatar mata da alƙawarina, ni kuma dan na tabbatar mata da zanzo ɗin sai nace mata zan tara sumar kaina, tasan cewa bana so gashi ya min yawa, shiyasa take yarda dana faɗi hakan, idan ina india kullum ita take min susar kai, dan ina so”
Duk da Maryam bata san wacece Daadi ɗin ba, amma kamar ta fahimci cewa kakarsa ce, dan haka taji indiyawa suna faɗawa kakaninsu a film, Da ƙyar ta iya motsa hannunta a cikin tarin sumar kan nasa, hannunta ya nitse a ciki.
Tafidah ya lumshe idonsa sannan ya buɗe, ya yi kewar hakan sosai ba kadan ba. Dalilan da kam ƙara sakawa yaji Maryam har ransu shine tana sakawa yaji kamar yana india.
A hankali take motsa hannun nata a cikin sumarsa.
“Wai ni Miriam da wani suna kike amfani ne ?”
“Maryam Tijjani Muhammad”
Kansa ya girgiza mata wanda yasa cinyarta motsawa yanzuma.
“Ba'a school ba, a page ɗinki, naga kamar babu suna ma”
Kai ta gyaɗa masa tana motsa hannunta a cikin sumarsa.
“Umm, babu suna, na rasa wani suna zan saka ne”
“Ya kamata ki saka suna”
“Me ya kamata na saka, da ina tunain na rubuta 'MARYAM'S KITCHEN'”
“A'a 'DAASO'S KITCHEN' dai”
Sai ta yi dariya yayinda shi kuma ya yi murmushi.
“Seriously ki saka 'MRS TAFIDA'”
Yanzuma dariyar ta yi.
“A'a 'MRS ESHAAN' dai”
“Ummm yafi kam, bari na rutuba miki to”
“To kuma iyaka Mrs Eshaan ɗin za'a rubuta?”
Ya tambaya a sanda hannunsa ya danna edit account.
“ ‘MRS ESHAAN’S KITCHEN”
“ MEK kenan ?”
“Eh”.
Shiru Ya ratsa parlon, kafin Maryam ta tambayi abinda take san tambaya tun ganinta da shi a yanzun.
“Sultan (King), menene wannan a gefen fuskar ka?”.
Tafida ya ɗago da idonsa ya kalleta, tareda lumshe idonsa, sbd yanda ta motsa hannunta a cikin sumar kansa dan ta tab'o har fatar kansa, sai kuma sunan da ta kirashi dashi 'Sultan', idon nasa ya buɗe sannan ya kalleta da kyau.
“Joakim ne ya bugomin ball ɗin cricket”
Ya juya idonsa yaci gaba da kallon wayar yana latsawa.
“Baka saka helmet bane ?”
“Mantawa nayi”
“Ai ko gashi wajen yayi ja, harma ya kumbura....”
Wayarsa da ya baro a ɗakinsa tana cahrgy ce ya ji kamar tana ƙara, dan haka ya motsa kunnensa ya tabbatar da ƙaran wayar yake ji.
Kansa ya ɗaga daga cinyar Maryam sannan ya miƙe, kafin yace mata komai aka ƙwanƙwasa ƙofar gidan, a tare suka kalli ƙofar shi da ita.
“Bari na ɗauko wayata, naji tana ringing”.
“Ok to nima bari na duba waye”
Shi ya yi sama ita kuma ta ƙarasa ta buɗe ƙofar.
“Surprise!”.
Abin da muryaryoyi biyu dake tsaye a ƙofar gidan suka faɗi kenan, zuciyar Maryam ta takarkara ta yi tsalle a kirjinta, ta ji kamar zuciyar tata zata fito daga kirjinta ne.
Zara da Aisha ne, ba wai bata san zuwansu gidan bane, bata so suga Tafida ne, dan har yanzu a cikinsu babu wanda yasan cewa ita matarsa ce, kuma har wa yau basu fasa zantuka akansa ba.
Da ƙyar ta lalubo murmushi ta yab'a akan fuskarta. Sannan ta haɗiye wani guntun yawu, ta ƙarasa bud’e ƙofar tana faɗin.
“Ku shigo daga ciki”
Har ranta ba haka ta so ba, duk da ta ji daɗin zuwan nasu, sam bata fatan Tafida ya sauƙo yazo ya iskesu, zama suka yi akan kujera suna ta mata murmushi wanda itama take meda musu martani.
“Wai dama Maryam ke a gidan ma da hijiabi kike zama kullum?”
Maryam bata amsa Zara dake wannan batu ba, sai kawai tace.
“Bari na kawo muku abun sha...”
“Ke bar abun shan nan wallahi”
Maryam ta gyaɗa musu kai kaɗan, a lokacin kuma Tafida ya sauƙo daga sama, hannunsa riɗe da ɗan ƙaramin littafi da kuma pen, sai wayarsa data Maryam a ɗayan hannun nasa.
“Wifey ai wayar taki ba data....”
Zuciyar Maryam ta dungura ta ƙara dungurawa, ta rintse idonta gam, a lokacin da take da tabbacin su Zara sunga Tafida, kuma sunji sunan da ya kirata dashi.
Shima sai yanzu yaga cewar ba ita kaɗai bace a falon, su uku ne, abinda yasa wayar tasa bata jima ba shine, me martaba ne ya kirashi, yake sanar masa da cewa Galadima bashi da lafiya, wai wani abu ya sameshi kamar junnu, yanzu haka ma sun Tafi india shida Fulani Sadiya da kuma Galadiman.
Addu'ar samun sauƙi yabyi masa sannan wayar tasu ta ƙare, ya ɗauko wani ƙaramin littafi da pen sbd yanaga kamar sunan nan da suka zab'a be dace ba, ya kamata ace sun ƙirƙiri wani sunan da ban, shine ya sauƙo yanzu. Cikin falon yaci gaba da takaowa yana faɗin.
“Baƙi mukayi ne ?”
Zara da Aisha waɗan da suka daskare a wajen suka kalli juna a tare, Tafida ne fa wannan a gabansu, Tafidan da a koda yaushe suke kwana da tunanin sa, yau shine tsaye a gabansu, kuma sune a cikin gidansa, bama wannan ba, ƙawarsu Maryam da a koda yaushe suke yawan mata hirar Tafida dan suna ganin cewa block ɗinsu ɗaya itace matarsa?, matarsa ta aure, Maryam fa ?.
Gaba ɗaya kuma sai kunyar Maryam ɗin ta kamasu, dan sun tuna yanda suke yawan maganganu akan mijinta, amma me yasa btaa taba faɗa musu ba?.
“Eh ƙawayena ne, wanda muke department ɗa ya”
Kusa da ita ya zauna.
“Sannun ku da zuwa”
Abu ɗaya yake yawo a tunanin su biyun, dama ance musu yana jin hausa, amma basu ɗauka har haka ba, duk da suna ganinsa cikin kayan hausawan, amma basu tabbatar ba sai yau.
“Ki kawo musu abin sha mana Miriam”
Kai ta gyaɗa masa sannan ta miƙe ta nufi kitchen, shima kuma sai ya miƙe yabi bayanta.
Zara da Aisha suka haɗa ido, kuma ba tare da suncewa juna komai ba, suka miƙe da sauri suka bar gidan.
Maryam ta gama jere drinks ɗin data ɗebo a fridge akan tray, sannan ta juyo ta kalli Tafida dake tsaye a bayanta.
“Kin gama ?”
Ta gyaɗa masa kai tana shirin wucewa, saida tazo wucewa ta gabansa taji sauƙar hannunsa akan kafaɗarta ya dafata, zuciyar Maryam tayi rawa kirjinta, ta ɗan ɗaga kai ta kalli fuskarsa, taga yanda yafita tsayi sosai, kamar tana tsaye a gaban wani dogon gini ne.
Tafiya suka fara shida ita a tare kamar wata ƙawarsa.
Mamakine ya kamasu sanda suka tarar da babu kowa a falon, abun yaso ya bata dariya, dan tasan guduwa suka yi.
“Ah-ah ina kuma baƙin suka shiga?”
Maryam tana riƙe dariya tace.
“Sun tafi”
“Sun tafi ?!”
Ya dawo mata da tambaya, ta gyaɗa masa kai tana cije lebenta na ƙasa dan ta hana dariyar dake neman kufece mata fitowa.
__________________________
_To!, su Aisha dai anji kunya an ofe_
_wai ni meke goin a haɗejia ne ?_
_Ina godiya masoya🙏_
🌸-SAI KASLA CE✍️-🌸.


⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Mrs Nazif wannan naki ne*

*BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS (28)*

*Da misalin 01:00am*
Maryam ta fito daga kitchen, hannunta riƙe da jug me ɗauke da ruwa, so take yau ta yi sallahr dare, bayan ta farka kuma sai ta ji ƙishin ruwa, dan haka ta sauƙo domin ta ɗauki ruwan.
Ji kake taratsa-tsa!, jug ɗin glass ɗin dake riƙe a hannunta ya faɗo a dandaryar tiles ya fashe. Sakamakon abinda ta gani.
Idanuwa waje take kallon Tafida daya shigo cikin gidan, rigar dake jikinsa duka a yage, ga jini na zuba a jikinsa, daga yanayin yanda yake tafiya ta san cewa a galab'aice yake,to ina yaje da wannan daren ?.
Gani ta yi ya faɗi ƙasa yaraf!, duk wani tsoro da take dashi ta ji ya gushe, babu abinda take hangowa sai mutumin daya alkinta rayuwarta tafannuka da dama kwance ba a cikin hayyacinsa ba, kuma yana zubar da jini.
Da gudu ta nufi inda yake, har tana taka kwalbar data fashe a ƙasa amma bata kula ba, kansa taje ta tsugunna, tana kiran sunansa, gaba ɗaya hankalinta ya tashi kuka kawai take tana faman kiran.
“Eshaan!, Eshaan!.....Eshaan!!!”
Hannu ta kai ta riƙe fuskarsa tana jijjiga shi, idonsa taga ya buɗe, duk da hasken fitulun dake falon bashinda yawa saida taga ƙwayar idonsa data koma ja, kallonta yake shima yayinda taga ya buɗe bakinsa yana so ya mata magana, anan tayi arba da dogayen haƙwaran dake bakinsa, hawaye gaba ɗaya ya gama jiƙe mata fuska har yana ɗiga akan tasa fuskar.
“Miriam....s..stay away..f..from..me”
Ya furta maganar a rarrabe, Maryam ta shiga girgiza masa kai tana ci gaba da yin kukanta me sauti.
“Eshaan me ya sameka haka ?”
Bai amsa ta ba sai ƙoƙarin tureta daga jikinsa da ya shiga yi, da ƙyar ya samu ya rabata da jikinsa, ya miƙe zaune tare da jingina da jikin bango, Maryam ta ƙara matsowa kusa da shi, ya shiga ɗaga mata hannu alamun ta dakata, kuma bata dakata ɗin ba saida ta matso kusa da shi.
“Eshaam dan Allah....”
Maryam taga yanayin fuskarsa ya sauya zuwa fishi, bakinsa ya buɗe haɗi da cije haƙwaransa wannan fikar ta sauko masa har kan haƙwaransa na ƙasa, ya kalleta da jajayen idanuwansa.
“Nace ki ƙyale ni ko!”
Ba ƙaramar razana ta yi ba, ƴaƴan hanjinta suka yamutse, ganinsa cikin wannan fusatar, shifa dan ita yake yin haka, baya so ya cutar da ita, ya kamata ace ta fahimce shi.
Amma bata fahimta ɗin ba, ta ƙara riƙe shi tana sakin wani sabon kukan.
“Miriam stay away from, i am a monster Maryam, i am a beast!”
Maryam ta ɗora hannayenta akan fuskarsa tana gursheƙan kuka, goshin ta jingina akan nasa sannan ta girgiza masa kai, wanda yasa nasa kan shima motsawa.
“A'a Eshaan, i can't, i can't stay away from you”
Idamuwansa ya rintse yana jan numfashi da ƙyar, kanta ta ɗaga daga goshinsa sannan ta miƙe ta riƙe hannunsa tana san ta mikar da shi
“Ka tashi dan Allah”
Da ƙyar ya iya miƙewa, dan babu wani ƙarfi a jikinsa na arziƙi, ita ta kama shi har zuwa ɗakinsa, in da taga komai a hargitse, rabonta da ɗakin nasa tun ranar da ta fara zuwa gidan, dan ba shiga ɗakin nasa take ba, hatta da shara ba masa take ba, shi yake kayarsa da kansa.
A kan gadon ta samu ta aje shi, sannan ta shiga bin jikinsanda kallo, idonta ya ƙara zarewa ganin yanda duka jikin nasa ke da rauni.
Numfashi ma da ƙhar Tafida yake, dan Allah ne kaɗai yasan abinda yake ji yanzu haka, Maryam ta ƙara ruɗewa tana dudduba jikin nasa.
“Me...miye haka a j...jikin ka ?”
Hannun ta dake dudduba jikin nasa ya riƙe sannan a hankali ya furta
”Ki tafi.... kada na cutar... dake, dan Allah Miriam”
Yanzun ma kai ta girgiza masa kukanta na ƙara ƙaruwa, ko a ranar da aka aura mata shi bata shiga tashin hankali irin wanda take ciki ba a yau.
Jikinsa ne taga ya fara girgiza harda wani fisge-fisge yake.
“Eshaah?!.....Eshaan?!...Esh..”
A kiɗime ta faɗi, jin yanda ya matse mata hannunta dake cikin riƙon nasa, idanuwansa taga sunyi sama, kamar wanda ya suma, kuma kamar....., ta kasa ƙarasawa sbd hannunta daya saki, kansa yayi gefe sannan ƙwayar idonsa ta yi sama gaba ɗaya.

HANAM POV.
“Kin tabbatar kin ji sauƙi ?”
Muryar Uchenna ta fito a sanda yake kallonta, Hanam ta gyaɗa masa kai, tsaye suke a parlo yayin da ta fito cikin shirinta na tafiya office, dan yau taji sauƙin jikinta, kwananta uku kenan tana jinya, kuma kulawa babu kalar wadda Uchenna bai bata ba.
Ko office baya fita sbd ita, ga ɗawai niyar kula da Arya kullum shi yake. Dan haka ta saka a zuciyarta cewa zata je ta samu Abba yau, tana so ya faɗa mata waye ainahin Uche, tana san sanin asalinsa.
Shima kan ya gyaɗa mata sannan ya miƙa mata Arya daya gama yiwa wanka ya shirya shi cikin wata hoodie da wandonta black color.
Karb'ar Arya ɗin ta yi tana ci gaba da kallonsa.
“Yau bazaka je aiki ba ?”
Kansa ya gyaɗa mata yana faɗin.
“Nayi magaa da Abba kan bazan samu damar zuwa ba yau, wata ƙila sai gobe”
Ta gyaɗa masa kai a hankali sannan ta juya tana faɗin.
“Sai na dawo”
“A dawo lafiya”.
Office ta fara zuwa, ta tarar da tarin aikin dake jiranta tsawon kwanaki, dan haka bata samu damar tashi ba sai wajejen karfe 05:00pm.
Kuma daga fashion house ɗinta Hakuɗau Group of Industries ta nufa.
*
“Kayi shiru Abba”
Hanam ta faɗi tana duban Abban, sbd ta faɗa masa abinda ya kawota wurinsa amma sai ya yi shiru yana kallonta.
Abba ya gyara zamansa yana bawa Arya pen dan yayi wasa da shi, yana kallon Hanam.
“Maman babanta Abban ki ya tab'a zab'a miki abinda zai cutar da ke ?”
Ta girgiza masa kai.
“Good, to ki tabbatar da auren Haris ma haka ne”
“Harees ?, waye Harees”
Taja 'ree' ɗin, sbd arabic ascent ɗin dake bakinta, bama iyaka wannan ne take kiransa a haka ba, sunaye da dama ita bata furta su kamar yanda bahaushe ke yi, tana furta su yanda larabawa ke yi.
“Uchenna”
Abba ya b'ata amsa hankalinsa kwance, idanuwa waje kuma cikin tsantsar mamaki take kallon Abba, Harees ?, wai uchenna ne Haress.
“Nasan yanzu duk abinda zan faɗa miki ba lalle ki yarda ba, ga wannan adireshin da lambar wayar, kije ki samu matar zata baki ko wani bayani akan Uchenna Haris Franklin”
Hanam ta kai hannu ta karb'i takardar da Abba ke miƙo mata, ita ta ma rasa takamemen tunani ɗaya da zata yi a kanta.
Takardar ta shiga dubawa tana karanta adresa ɗin 'SULE JA, RAFIN CINNAKA'.

TAFIDA POV.
Fuskar wannan matar ce, take kallonsa, fuskarta ɗauke da murmushi, gudu yake yayinda yake bin ball ɗin nan a baya, ita ma tana biyoshi tana kiran sunansa, daga can wata ƙofa kuma a bayan gidan, wani mutum ya fito, hannunsa riƙe da mug yana faɗin.
“Roshni!, Eshaan!”
A tare suka tsaya da gudun su duka, suka kalli kyakyawan baƙin mutumin, wanda kana ganinsa kasan ɗan africa ne, murmushi ya sakar musu, yayinda su kuma suke kallonsa da blue eyes ɗinsu su duka.
“Guje-guje ko ?, ki dena sai kunje kun faɗi?”
Yaron ya juyo ya kalli babarsa wadda take kallon babansa da murmushi.
“Ball ce zamu ɗauko”
Cikin gurb'attaciyar hausa ta faɗi zancen.
Daga nan kuma sai wata ƙara ta cika wajen, ƙarar Roshni tana kiran sunan Eshaan, yayinda shi kuma baya ganin komai sai duhu, daga can kuma sai muryar mahaifin sa yana kiran sunansa.
“Eshaan!, Eshaan!...Eshaan!!”
Yadda ƙarar kiran sunan ta cika masa kunne yasa ya toshe kunnesa ya durƙushe a wurin.
Sai kuma ya shiga fisge-fisge kamar zai karya gadon da yake kwance a kai.
Maryam dake share ɗakin ta yi saurin sakin broom ɗin ta ƙaraso wurin gadon, ta zauna a kusa da shi tana riƙe hannunsa na hagu.
Bai fasa fisge-fishen ba, kum idanuwansa a rufe suke, ya rintse su gam-gam, gashin kansa ya musu rumfa.
Maryam tana hawaye tana tofa masa duk addu'ar da tazo bakinta.
“Maa!, Baba!, Appa!, Maa!...Maaaa!”
Sai kuma ya buɗe idonsa gaba ɗaya, a sa'ilin daya buɗe idon, wuta ta kama a hannunsa na dama, ya ci gaba da ware ido yana kallon inda yake, hannunsa na dama yake san ya kai kansa sbd ya riƙe kan nasa dan ciwon da yake masa.
Yana ɗagowa hannun yaga wuta na ci, hannun ya dunƙele tare da rufe idonsa, wutar ta b'ace, hakan ya bashi damar ɗqora hannun a kansa.
Hannunsa na hagu yaji kamar an riƙe, ya yi sauri ya miƙe zaune. Idonsa ya ɗora a kanta yaga yanda idonta ya yi ja sosai, alamu dai taci kuka, daki-daki abinda ya faru jiya ya shiga dawo masa a ka.
Yana zaune a work table ɗinsa yana aiki, ya fara jin jikinsan ya ɗau zafi, kansa na sarawa, hakan ya sanar da shi zuwan aljaninsa, kuma tun daga farkon zuwan nasa ya san cewa yau ba da sauƙi ya zo ba, duk da yana cikin wani hali bai manta da Miriam ba, dan haka ya fita ta balcony ɗin ɗakinsa, ya shiga tsalle ta kan rufin gidagen mutane har ya fice daga Alaro city.
Ya shiga cikin wani daji, anan baƙin aljanin ya tashi, kuma kamar yanda ya zata babu sauƙi a lamarin, haka ya yi ta duka da ya kushin jikinsa har na wani zuwa wani lokaci.
Kafin ya dawo hayyacinsa shine ya kamo hanyar gida. Kuma yana dawowar ya isketa a falo.
Kansa ya dafe yana ture sumar da ta sauƙo masa kan ido, ta yanda zai samu damar kallon fuskarta da kyau.
Har yanzu kukan take ba ta dena ba, kuka take sosai, wanda yake fita tun daga ƙasan ruhunta.
“Ka bani tsoro sosai, nayi tunain ka....”
Sai kuma ta kasa ƙarasa maganar, ta shiga share fuska.
“Kullum haka nake Wifey, idan baƙin ruhina zai tashi irin wannan yanayin nake shiga”
Hannu ya ƙara kaiwa ya tura sumar kansa baya tare da furzar da iska, sai a sannan ya kalli jikinsa, gaba ɗaya ta bi duk inda yaji rauni ta saka masa plaster, wanda yake da tabbacin a first aid kit ɗinsa ta samo. Hannu ya kai ya shiga cire plasterr.
“Me ya faru ?”
kansa ya girgiza mata sannan ya ci gaba da cire plasterr har sai da ya cire su duka, sannan ya hade raunin yana faɗa mata cewar.
“Wannan ba rauni na bane, na baƙin ruhi ne”
Ita de bata ce masa komai ba, sai yanzu ma ta lura da ashe fa bashi da riga, kuma itace ma ta cire masa rigar jiya da ta kiɗime ta yi tunain ya mutu.
Saurin miƙewa ta yi daga kan gadon ta koma ta ɗauki broom ɗinan ta ci gaba da shara tana share hawaye, gabanta sai bugun tara-tara yake. Da ƙyar ta iya daurewa tace.
“Kaje ka yi wanka da alwala, gari ya waye”
Tunda ta tashi daga wajen yake kallonta, bai ce mata komai ba sai dubansa daya kai ga balcony, yaga kamar ma rana na shirin fitowa, Dan haka ya miƙe a hankali ya shiga banɗaki.
Maryam ta saki numfashin da ta riƙe sanda yazo giftawa ta kusan ta, kafin ya fito ta gama sharar, ta fita domin ta kawo masa abinci sannan ta ɗauko duster dan ta goge kurar da taga kayan ɗakin sun yi.
Ko da ya fito bai ganta ba sai ya ɗauko jallbiya a wardrobe ɗinsa ya saka ya tada salla.
Sanda ta dawo har ya idar ya koma banɗaki yana wanke bakinsa, abincin ta aje masa akan table sannan ta shiga goge kayan ɗakin, har tazo kan hotunan dake maƙale a bango.
Sai da ta zo kan nasa shida iyayensa sanda yana ƙarami ta tsaya, so take ta tantace dawa yafi kama a cikin iyayen nasa, last time da ta ga hoton bata gama ƙarewa Tafidan kallo bane, amma yanzu data gama karance kammaninsa sai ta rasa gane da wa yafi kama a cikin iyayen nasa.
Farinsa de irin na mahaifiyar sa ne, duk da ta fishi haske, kalar idonsa ma

Please Login or Register in order to submit comment