Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duba wasu sabbabin design din dinkuna.
*****
Motarta kirar hybrid take tukawa akan titi, bayan ta tashi daga aiki, yayinda ɗanta sanyin idaniyarta ke zaune a seat ɗin me zaman banza, cikin car seat dinsa.
Jifa-jifa take juyowa tayi masa wasa, a gaba ɗayan rayuwarya bata da wani abu me mihimmanci bayan wannan dan nata da kuma mahaifin ta, su kaɗai tasan tanada su, batajin tana san kanta kamar yanda take sansu.
Yau ta kama ranar zagayowar haihuwarta, bayan mahaifin ta da baya gari babu wanda ya kirata ya tayata murna, kuma dama hakance ta saba faruwa da ita a duk shekara, wattanin baya ita kaɗai ko ita da mahaifinta suka shagalin murnar zagayowar ranar haihuwartata, gashi kuma yau mahaifin nata baya gari, dan haka ta yanke shawarar yin shagalin daga ita sai ɗanta.
Dan haka ta parker motar tata a gaban chedi plaza shopping mall, ta ciro dan nata daga cikin car seat din dayake ciki, ta daukeshi a hannu ta nufi cikin mall ɗin. Bayan dan wani lokaci ta fito daga mall din hannunta rike da leda me dauke da tambarin mall din, wanda aka sako mata dan karamin cake din data siya a ciki ( bento cake), ta dawo ta zaunar da yaron a seat dinsa ita kuma ta zagaya ta shiga driver seat taci gaba da tuki.
A gaban maƙararen gidan nasu ta tsayar da motar ta danna horn cikin salonta, wanda bayan ita da me gidan kansa babu wanda yake irin wannan horn ɗin, hakan tasa me gadin nasu buɗewa gate ɗin cikin sauri, dan ya gane cewa itace, sbd me gidan baya gari.
Shigowa tayi da motar tata, tayi parking a parking lot, ta fito daga motar ta ɗauki yaronta haɗi da jakarsa da kuma tata sai ta ledar cake ɗin data siyo.
A babban parlon gidan nasu ta samu kowa na gidan, tun daga iyayen yaran har yaran, bata ko kalli inda suke ba ta haye tagwayen benin dake parlon domin shiga ɗakinta
“mtswww!, aikin banza, wallahi na tsani ganin yarinyar nan, idan na ganta ji nake kamar na bita na shake mata wuya ita da wannan shegen ɗan nata”
Cak ta tsaya daga tafiyar da take, ta juyo a hankali ta kalli babban yayanta kamal dake wannan batu, a hankali ta aje jakukunan hannunta a kasan tiles ɗin dake saman stairs ɗin, dan har ta kai ƙarahe, sauƙowa ta farayi tana tunkarar cikin parlon
“ya kamal gata nan fa zuwa” ƙanwarsa na'ima ta faɗi tana kallonta, mahaifiyarsu hajiya mero ce ta buga uban tsaki
“sai me kuma idan ta zo ?, ko dukansa za tayi ?”
Gabansa tazo ta tsaya, shima ganin hakan yasa ya miƙe tsaye, harma da kowa na parlon
“kamal kake ko wa ?, kada ka ƙara jifan ɗana da kalmar nan ta shege!, ɗana yanada uwa kuma yanada uba, kuma duka nice, dan haka ɗana ba shege bane, ka riƙa kula da kalamanka, idan har a kaina zasu tsaya ba zan tanka maka ba, amma idan har suka ƙetara layi zuwa kan ɗana" tayi wani murmushi me ciwo
“zan koya maka hankali kaida wannan uwar taka da bata gabana, bana shiga sabgar kowa, dan haka bana buƙatar kowa a tawa sabgar, ɗana ɗanane, babu wani wanda keda iko dashi, ka fita sabgarsa”
“ke !, dan tsabar baki da mutinci akan wannan sheg......”
Bai samu damar karasawa ba, sakamakon marin data sakar masa a kumatumsa na hagu, ya dafe wajen idanunsa waje yana kallonta, bama shi kaɗai ba, kowa dake parlon saida ya kama baki yana kallonsu su duka, cikin mamaki, a da idan sun maga abu bata kula su sam, amma gashi yanzu harda mari
“ke hanam dan baki da hankali shine zaki mari ya kamal ?”
Kanwar kamal ɗin rahina wadda suke uwa daya ta faɗi
“na mareshi ɗin, ko akwai me rama masa ?....... Kai kuma”
Ta faɗi tana juyowa kan kamal ɗin dake dafe da kunci yana kallonta da tsananin mamaki
“na faɗa maka cewa ka fita sabgar ɗana, dani kake faɗa ba dashi ba, kuma ɗana ba shege bane, nice ubansa mark my words”
Tana kaiwa nan ta bar wajen a fusace, ta bar kowa da baki a sake yana kallonta, dama sun saba mata cin kashi, babu kalar baƙar maganar da basa faɗa mata, tanayin haƙuri ta shanye, amma yau sun kaita bango.
***
Zaune suke a haɗaɗɗen dakin ɗan nata, wanda bai cika girma sosai ba, saide cike yake da kayan wasa kala-kala, yaron na zaune cikin floor seat, yana wasa da rattle ɗinsa (kacar-kacar), sanye yake cikin onesie (over rall)baka.
Yayinda hanam ke zaune a gefensa cikin Wata linen tunic dress, rigar dama ta zaman gidace, bento cake ɗin nan ta dauko ta buɗeshi daga cikin take away ɗin da aka saka shi 'HAPPY BIRTHDAY' shinr abinda aka rubuta a jikin cake ɗin
“Aryaan, yau mummy take birthday, let's cut the cake”
Ta faɗi tana kallon yaron, kamar wani babba haka take magana dashi, dan hatta dariyarta da mutane suka dena gani cikin wannan shekarar toshi tana masa, karamar wuka ta dauka ta yanka cake ɗin tana wakar happy birthday, cake ɗin ta yanko ta kaiwa yaron baki, yaron ya buɗe ya karba yana ci, itama ta yanko ta saka a nata bakin, tana masa wasa ta dauki tisseu ta goge hannunta sannan tana kallon yaron ta fara cewa
“abu ummuh an nas bi ƙulu innak ibn gair shar'i, bas ummak bita'arif innak shar'i, li'anna hiya yalli wulidtak, wa rabaitak, wa ɗaitak killil hub, ya ibn hayyi duniya yalli nahni fiyya annas ma bihibbul kil, bihibbu nafsun wa bas, bas saddiƙni ana kitir bihibbaka, wa ana ba'arif innaka bta'arif hasshi sah?”
(Baban mamansa mutane suna cewa wai kai shegene, amma mamanka tasan cewa kai ba shege bane, sbd mamanka ita ta haifeka, ta reneka, kuma ta baka kowace iriyar soyyayarta, ɗana wannan duniyar da muke ciki ba kowa ke san wani ba, kansu kawai suke so, amma ka yarda dani dan ni ina sanka sosai kuma nasan kaima kasan hakan ko?)
"Abu ummu ta'al ila huna (baban mamansa zo nan)"
Tayi maganar tana daukansa ta rungume shi a kirjinta tana pecking kansa
“ni bazan taba guduwa na barka ba, kamar yanda tawa mahaifiyar ta gudu ta barni”.
MARYAM POV
Zaune suke gaba dayansu akan babbar tabarma, ita da maanmu da muhsin suna cin jallof ɗin taliya da waken da Maryam ɗin tai musu da daddare, yayinda hussain da hassan suma suke cin nasu daban, hussain sai zabga santi yake, dan idan batun girki ne to Maryam ba daga baya ba
“Kinsan allah yaya, ni ji nake na kamar akawai kifi a ciki ”
Maryam da maanmu suka masa dariya, banda muhsin dake shirgawa cikinsa abinci, da kuma hassan da dama shi can miskili ne
“au dariya na baku ?”
“eh mana, muhsin ɗauko pillow nai masa waigi, dan naga ƙiris ya rage ya faɗi.....”
Sallamar mahaifin suce ta tsayar da hirar, ya shigo cikin gidan yana musu kallon ɗai-ɗaya, wanda hasken fitilar da suka kunna ya bashi damar ganin fuskokinsu, sigarinsi yake busawa kamar kullum, Maryam, hussain da muhsin suka masa sannu da zuwa, yayinda maanmu da hassan ko takansa basu bi ba, kuma kamar yanda ya saba babu wanda ya kula a cikinsu, idan da sabo sun saba, amma kuma kullum basa fasa gaidashi
“ina abincina ?”
Hassan ya zaburo zaice, ya basu kuɗin abincin ne ?, hussain ya riƙe hannunsa yana girgiza masa kai, hassan yaji kamar ya saka ihu dan tsabar takaici, hussain ya juya ya kalli Maryam.
“yaya ki zubawa abba abinci”
Maryam ta miƙe ta nufi rumfar da suke girki, maanmu taji wani malolon takaci ya tsaye mata a maƙoshi, kamar yanda ya saba maƙale mata a duk sanda zata kalli tijjani a matsayin mijinta.
Sam bata san ta riƙa sa'insa dashi a gaban ƴanƴansa, dan sam bata san su renashi kamar yanda hassan ya rainashi, shi kullum babu ruwansa da ya suka tashi?, yaya suke?, shin suna cikin halin bukata? ko aa, babu ruwansa da cinsu, shansu, sitirarsu, kula da lafiyarsu, duka bai damuba.
Maryam ta dawo hannunta rike da wani ƙaramin food flask ta tsugunna ta mika masa, a wulaƙance ya kar6a sannan ya juya ya fice daga gidan, da alama yau bazai kwana a gidan ba.
Maanmu taji wata kwallar baƙin ciki na shirin sauko mata, amma sai ta dake, ta hana kanta yin hakan, domin sam ko kaɗan bata san yaranta su karaya, tasan da cewa itace kwarin guwarsu, idan har ita ta gwada rauni, to su yaya zasuyi ?.
“maanmu dan allah”
Maryam ta faɗi a sigar roƙo tana gargiza mata kai, maanmu tayi murmushin takaici, tana kawar da kai
“Maryam kenan, aini na jima da hana hawayena zubowa, idan de har akan tijjani ne, to bazan ƙara kuka ba”
Gaba ɗaya yaran nata sai jikinsu yayi sanyi, sun san halin mahaifinsu sun kuma san irin abinda yake a waje.
***
Maryam ce kwance a ɗakinta, cikin gidan sauro ita da muhsin, shegen tsoronta ya hanata kwana ita ɗaya, Allah ya hallito ta da wani irin bala'in tsoro, yanzu hakama fitsari take ji, kuma gashi tana tsoron fita ita kaɗai, dan tsabar tsoranta ko horro film bata iya kalla, hannu ta kai ta dan daddaki muhsin, ya miƙe zaune cikin magagin bacci
“muje muyi fitsari auta”
“ummmhmmm”
Muhsin ya amsa cikin magagin bacci, net ɗin ta ɗage a hankali, gudun kada ta ɗuro musu sauro, ita ta fara fita sannan shima ta fito dashi, aƙƙalla idan da muhsin ɗin bazataji tsoron sosai ba, lokacin suna kwana da anti fati itace take rakata idan fitar dare ta kamata.
TAFIDAH POV
A hankali ya shiga ƙif-ƙifta idonsa bayan rana ta ratso ta cikin katangar glass ɗin dake ɗakin, miƙewa yayi zaune yanata waige-waige, shi tun bayan daya dawo daga masallaci baisanma bacci ya kwashe shi haka ba.
Miƙewa tsaye yayi yana miƙa, yau monday dan haka dole yaje aiki, gashi kuma yanajin jikinsa babu daɗi, and so weak, dan haka ya nufi kofar toilet ɗin ɗakin, ya buɗe da hannunsa tunma kafin ya ƙarasa jikin kofar, ta hanyar nuni da handle ɗin kofar.
Bayan jimawar wani lokaci sai gashi ya fito, a gurguje ya shirya dan ya kusa makara, wata bluen shadda ya saka ya dora hula dara itama blue, ya saka flat takalma.
Ya sauko ƙasa da sauri, kitchen ya faɗa ba zai iya jira yayi girki da kansa ba, dan haka yayi amfani da ƙarfin dayake dashi ya hada girkin ya saka launch box, dan sam bashi da lokacin da zai zauna yaci.
A gurguje ya shige office ɗinsa bayan yakai asibitin
“Tafida ya akayi ka makara yau ?”
Khabir ya faɗi bayan ya biyoshi cikin office ɗin
“kaide bari, wallahi yau banajin daɗine, kaga ko abinci ban samu naci ba”
Tafeedan ya bashi amsa yana saka lap coat ɗinsa
“to allah kyauta, madam tana gaishe ka”
Tafida yayi murmushi “ace nima ina gaisheta”
“yauwwa, HELEEN tazo jiya, tace wai na sanar maka cewa zatayi tafiya, bata da ishasshen lokaci da taje gidan naka ta sameki”
Tafida yayi masa banza, yana jan keyboard din desktop dinsa, khabir yayi murmushi yana jijjiga kai, dama yasan ko ya masa maganar ba zai kula ba, dan yasan Tafidah, ya kuma san waye shi.
Wayarsa ce ta ɗau ringing dan haka ya ɗauke hannunsa daga kan keyboard ɗin, ya kai hannunsa da sauri yana ɗaukan kiran ganin wanda ya kira 'MUMZZY FULANI'.
Da sallama a bakinsa ya ɗaga wayar, yana murmushi, cike da girmamawa yake gaida wadda yake magana da ita a wayar
“Yaushe zaka shigo ne?”
Muryar matar me cike da ƙasaita da kuma kamewa ta fito daga cikin wayar
“yaushe ne wai bikin ?” saida ta ɗanyi jimm, bawai dan ta rasa abinda zatace masa ba, saidan ƙasaita sannan ta bashi amsa
“saura kwana biyar”
“wata ƙila gobe na shigo”
“allah ya kawoka lafiya”
“allah ya ƙara girma”
Daga haka kuma wayar ta ƙare, khabir dake zaune a kujerar dake fuskantar Tafida yace
“ ina zaka je ?”
Yana ci gana da danna desktop ɗin ya furta “hadejia”.
🌸-SAI KASKA CE-🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐شاء القدر⭐
©By Sai Kaska
*proud of my first novel*
*BABI NA UKU (3)*
HANAM POV.
Tsaye take a cikin babban kitchen ɗin gidan nasu, tana haɗawa aryasn elecare, wani nau'in abincin yara, tana bashine sbd mama baya isarsa, kumama yana ƙara girma dan haka take haɗa masa da sauran kayan abinci yara. Sanye take da green cargo pants, sai wata baƙar shirt mara hannu, ta ɗaure gashin kanta da rubber band.
Fitowa tayi daga kitchen ɗin tana fifita abinda ta zuba a cikin wani sabon bowl da taga a kitchen ɗin, a lokacin masu aikin dafa abinci na gidan suna jera abinda suka dafa a kan danning table, waje ta samu tana aje bowl ɗin, yayinda take amsa gaisuwar da masu aikin suke mata.
Dakinta ta koma wanda yake haɗe da ɗakin aryaan ɗin, ta shiga ta sameshi zaune cikin munchkin baby cradle ɗinsa yana jujjuyashi, yayinda yake tsotsar pacifier ɗin dake bakinsa
“aaaah, aryaan ammy”
Ta faɗi tana masa wasa tareda ciroshi daga cikin baby cradle ɗin, ta sabashi a kafaɗa, wayarta dake cikin aljihunta ce ta shiga ringing ta sa hannu ta ɗauko wayar, ganin abbabnta ne yasa tayi murmushi, ta ɗaga kiran ta gaisheshi, baya ha amsa yace
“maman babanta, mamarki ta....” tun kafin ya karasa ta katse shi
“la abba hiya mana immi”
( a'a abba ita ba mahaifiyata bace)
“to matata, shikenan?”
Ta gyaɗa masa kai kamar yana gabanta sannaan shima yaci haba
“ta kawo min kararki, wai kin mari ɗanta”
Ta ɗan gyara riƙon da tayiwa arya a hannunta da babu wayar
“eh hakane”
“to maman babanta me yasa ?”
“abba arya ya kira da shege, ni kuma na gaza jurewa shi yasa na mareshi ”
“to maman babanta a dinga haƙuri dai, kinga shi yayanki ne, ya girmeki, kuma ko ba haka ba shi namiji ne, a dinga ƙoƙarin sarrafa fishi”
“umhm” daga haka kuma suka ɗan tattauna daga bisani sukayi sallama bayan ya faɗa mata cewar gobe zai dawo, ta aje wayar sannan ta fito daga ɗakin zuwa ƙasa.
Zama tayi ta shiga bashi baby feed ɗin tana masa wasa, zuwa lokacin mutanen gidan sun fara fitowa, arya sai ƙyal-ƙyala dariya yake har haƙwaransa biyu na sama da suka fara fitowa na bayyana
“kutumar dumadu”
Hanam ta tsinkayo muryar hajiya mero a bayanta na ƙunduma ashar bata ko juyo ba taci gaba da yiwa ɗanta wasa tana bashi abincin
“ya sa kika damawa shegen ɗanki abu a cikin sabon kwano na ?, ko ke kika siyomin ?”
Nan da nan hanam ta tsuke fuska ta aje bowl ɗin ta juyo ta fuskanci hajiya meron da kyau
“kikace kwanan ki, yau ai ni inajin duk cikin ku babu wadda tazo koda da cokaline gidan nan, ko waccen ku haka aka wanko kafarta ziƙa-ziyau aka kawota, kuma kina zancen naki tunda ya riga ya shigo cikin gidan ubana ya riga ya zama mallakinsa, kuma ma faɗa min sana'ar me kike da kika samu kuɗin siyan bowl ɗin ?..... babu ko ?, nasan ai kiɗin ubana ne, dan baka babu ruwanki da ni”
“lalle hanam wuyanki yayi kauri, yanxu ni kika dubi ƙwayar idona kike faɗa min wannan maganganun?.....naji ni haka ziƙa-ziyau aka kawoni gidan ubanki, me gidan uba, shiyasa naga taki uwar ta gudu ta barki cikin zanin goyo”
A fusace hanam ta miƙe tana kallon cikin idon mero
“mero bari kiji na faɗa miki, ni bani da uwa abba shine uwata kuma shine ubana, waccan matar ba uwata bace, watace can da ban, kuma magana ta ƙarshe kada ki kuskura ki ƙara kiran ɗana da shege, ɗana ba shege bane yanada uba, kuma nice ubansa, fatan kin fahimta ?”
Tana kaiwa nan ta bar wajen bayan ta ɗauki ɗanta.
MARYAM POV.
*Da misalin karfe 7:30am*
Maryam na zuba musu abinci a kwanuka, dan hassan da hussain da muhsin duka sun shirya domin zuwa makaranta.
Abincin ta gama zubawa tazo ta aje musu a gabansu.
“yaya ke yau bazakije makaranta bane ?”
Hassan ya tambaya ganin sam ba tayi shirin zuwa makarantar ba
“aa hassan bazanje ba, registretion mukayi ai”
“oh na gane”
“au ni kin tuna min ma, idan kin gama ki kiramin kawu usman ɗin nayi masa maganar kuɗin” cewar maanmu.
Kawu usman shine babban yayan su maanmu, kuma tun lokacin da tijjani ya tsiri rashin mutunci shine ya dawo yake kula da maanmun da yaran nata, kuma yanzu haka shine yake ɗaukar dauyin karatun Maryam ɗin, dan a yanzu haka ta gama ND 1, zata shiga ND 2, kwana nan suka gama siwes ma.
“to, in anjima zanje gidan su Badar, jiya nace mata zanje amma banje ba....”
bata ko gama rufe bakinta ba saiga sallamar Badar, tana shigowa ta gaida maanmu ta shiga aikawa Maryam sakon harara.
“Badariyya zo muci taliya”
“aa wallahi maanmu, a ƙoshe nake, dade ɗumame ne”
“ke wai yau bazakije makarantar ba ?”
“ban sani ba”
Badar ta faɗi tana kawar da kai
“ke kiyi haƙuri wallahi jiya aiki ne ya riƙeni shiyasa banzo ba”
“hassan kuyi sauri ku gama ku miƙamin yaron nan makarantarsu, kar ya makara su dakar min shi”
“ai da zasu dakeshi ma da ba haka ba” cewar hassan yana wurga masa harara
“wai dan allah me auta ya tare muku ne ?”
“babu wallahi kawai muguntace irin tasu” cewar Maryam.
Bayan sun gama cin abinci su hussain suka fita suda muhsin, su suna ss3 ne a makarantar government day garko, yayinda shi kuma muhsin yake primary 3 a garko islamiyya, duka makarantun nasu basu da nisa da gida.
*
“ke tura min sabbabin vedios ɗin”
cewar Maryam yayinda suke zaune a ɗakin Maryam ɗin
“ke aliyu ne zai zo jibi”
cewar Badar, aliyu shine saurayin Badar, kuma a yobe yake da aiki, amma ainahinsa ɗan hadejia ne, aikine ya kaishi can
“to allah kawo shi lafiya”
“girki nake so ki masa”
“Badar, ina rabaki da kiwon killa kina killa ta haihu, ba wai girkin ne bana san miki ba, tsorona duk ranar da kukayi aure yace ki masa girki irin wanda kika saba masa lokacin kina budurwa, kikayi bai kai nawa ba yaya zakiyi ?”
“ke rabu dashi wallahi, ni bazan iya ba, kawai ki masa”
“shikenan, me za'a masa ?”
“kinga last time fried rice aka masa yanzu kawai a masa awara me miya”
“shikenan, amma ki kawo da wuri, dan nima jibi zan raka anti fati gidan auren 'yan uwan mijinta”
“ai shikenan”
Badar ta faɗi tana duba mata sabbabin vedios ɗin girkin data samo mata a tiktok.
TAFIDA POV.
zaune yake a mazaunin me zaman banza, yayinda abokinsa muktar yake tuƙa motar, dan dama shine yaje ya ɗauke shi a airport bayan ya sauƙa a kano, idanunsa sanye da wani sun glasses, ya boye kalar ƙwayar idansa data koma ja tunda safe, duk da muktar yasan halin dayake ciki amma baya san ya ɗagawa kowa hankali.
Ya ɗora hannunsa akan bakinsa yana nazari, nazarin abinda zai iya faruwa a hadejia, yanzu ya shiga cikin wani irin hali da baƙin ruhin dake cikinsa yake tashi akai-akai, a da sai yayi wata da wattani bai tashi ba, amma a kwanakin nan abun ya ta'azzara.
muktar ya d'an kalleshi da gefen ido
“tunanin me kake ?”
a hankali ya sauke hannun daya ɗora akan bakinsa ya juya yana kallon window, sai ya lura da har sun shigo ƙofar garin hadejia ta farko
“babu komai...”
“aa Tafida, akwai wani abun”
hakane, kamar yanda muktar ɗin ya faɗa akwai wani abun, jikinsa ne ke bashi cewar akwai wani abu dazai faru, to amma taya zai faɗa masa cewa jikinsa na bashi cewar wani abu zai iya faruwa.
Bai amsa shi ba, sai hannu dayakai ya cire sun glasses ɗin dake idonsa, a lokacin suka karaso dai-dai round about ɗin na malam zangi, babban round about ɗin hadejia.
Tun daga ganin lambar motar matasa suka gane cewa TAFIDA ya shigo gari, tun bayan daya dawo daga india, aka naɗa shi akan sarautar mahaifin sa ta TAFIDA, yayi hawan doki matasan garin dama ƴan mata suka ganshi, shikenan suka samu abun magana, kaf ƴan matan garin haɗejia babu wadda bata san Tafida ba, samari na matukar sansa, hakan tasa a duk lokacin da za'ayi hawan sallah ko na kilisi dakarun Tafida sunfi na kowa yawa, sbd rabi da kwatan matasan had'ejia suna sansa, Allah ya masa wannan farin jinin, ga kuma tarin ƴan matan da zaka gani a wajen idan har yayi hawa, kowa zaka tambaya zai baka labarin Tafida a haɗejia.
Juyowa yayi ya kalli muktar da jajayen kwayoyin idonsa, muktar ɗin ma ya jiyo ya kalleshi, saida gabansa ya faɗi yayinda yayi arba da kalar idon nasa, duk da ya saba ganinsa da idan kwayar idon nasa ta sauya, amma na yau yafi ja, jan har yayi yawa.
“Tafida kayi addu'a”
yayi murmushi me ciwo yana kawar da kai
“itace abun da ako yaushe nake sanyi, amma kuma daga zarar na shiga irin wannan halin bana iya yinta, bakina nakeji yamin nauyi, hatta da harafi ɗaya na larabci bana iya furtashi”
muktar ya girgiza kai cike da tausayin abokin nasa, wata iriyar rayuwa yake me cike da ban tausayi.
Hannunsa ya mika baya, ba tareda ya ta6a bottle ɗin ruwan dake kan kujerar baya ba, bottle ɗin ta taso da kanta zuwa cikin hannunsa, ya dawo da hannun nasa gaba riƙe da bottle ɗin ya buɗe ya kafa kai yana sha, zuwa yanzu sun shigo cikin kofar garin had'ejia, kuma sun hau titin fada, so yake ya samu yayi yaƙi da sheɗanin ruhin nasa kafin su karasa fada.
Bottle ɗin ya aje a gaban motar, ya dafe kansa da hannuwansa, da muktar yaga haka sai ya shiga tofa masa addu'a duk wadda tazo bakinsa, bayan ɗan wani lokaci ya jiƙe sharkaf da gumi, har ya jiƙa rigar yadin dake jikinsa.
A hankali ya ɗago ya jingina da jikin kujera, yanajinsa ya dawo dai-dai, shed'anin ruhin nasa ya tafi, ƙwayar idansa ta dawo ainihin blue ɗinta.
Da haka suka karasa katafariyar fadar garin hadeji, hadejia ginsau birnin doki, ta ɗan abubakar sarki babba. Inji ja'e haɗejia.
A gate ɗin farko wanda aka tanada domin aje motoci muktar yayi parking, suka fito a tade, muktarb ya ɗauka masa jakar dayazo da ita, gaba ɗaya harabar fadar a cike take fal da jama'a, sbd bikin da za'a gudanar na yar sarki gimbiya amina,isarsa ba jimawa labari ya karaɗe fada akan Tafida ya shigo garin.
Kofa ta biyu suka zo wucewa dogarai da hadimai sai kwasar gaisuwa suke, duk da shi Tafidan baya san hakan sam, shi baya d'aukan kansa daban da kowa, gani yake shi dai-dai yake da kowa, amma haka ƙa'idar take, dan haka babu yanda zaiyyi face ya amsa, su kuma suna gaisheda shine sbd suna sansa, dan yafi yarima ɗan uwansa halin arzik'i.
Daga wannan gate na biyu suka shiga soro na farko a fadar wanda ya kasance soron masu gadi da tsaron fada a da, amma yanzu babu kowa a wajen sai masu wucewa, daga soron farko sai na biyu wanda shi kuma ya kasance soron malamai a zamanin da, wanda shima a yanzu babu kowa, sai kuma soro na uku wanda shi kuma ya kasance na ƙoramai, sai soro na huɗu wanda yake d'auke da wata babbar karaga ta sarkin hadejia, daga kasan kujerar wani lallausan yashine zube, sannan kujera a samansa, a duk lokacin da sarki ya sauko daga sallar jumu'a yakan tsaya a wajen ya zauna ayi fadanci sannan a tashi, daga shi kuma sai soron bayi, wanda kuma a yanzu yake ɗauke da tsofaffun bayi na da, wanda har yanzu akwai sauransu, gaba ɗaya saida Tafida yabisu ya gaisar sunata saka masa albarka sannan ya wuce, daga nan kuma wani tamfatsetsen filine, wanda ya kunshi hanyoyi hud'u, daya wadda zata sadaka da 6angaren matan sarki da kuma turakar sarkin, ɗaya kuma wadda zata kaika ai nahin majallisun sarki, sai kuma wadda zata kaika 6an garen bayi da kuyangu na fadar, Sai ta murin dominan sarki.
Nan ɗin ma a cike yake da jama'a haka suka yanki hanyar da zata sadasu da 6an garen matan sarki, wata uwar doguwar tafiya suka yanka kafin suka iso ainahin inda bangarorin matan sarkin suke guda uku, wanda yafi kowanne girma suka nufa, kowanen gini akwai beni, amma kuma kuma irinsu ɗaya sai na tsakiyarsu daya yafi girma.
Aminttaciyarta suka samu tana fitowa daga ƙofar shiga, ta gaishe su tareda faɗi bari tai musu iso, muktar sai ya tsaya yana faɗin
“na gama nawa aikin, na kawoka gida lafiya, dan haka sai anjima idan ka samu fitowa”
Tafida ya juyo yana kallonsa, sai kuma ya ta6e baki cikin ɗaga kafaɗa, dan muktar ba balo bane, shi ɗan gidane, ya karbi jakar tasa sannan ya saka kai cikin kofar parlon, tuntuni an masa iso wajenta, dan haka ya saka kafarsa cikin parlon kai tsaye daga parlon farko ta wuce na biyu, a nan yayi birki, kamshin turaren wutane ya fara ziyartar hancinsa, kafin a hankali ya fara bin parlon da kallo, baiga kowa ba sai himilin

Please Login or Register in order to submit comment