Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah ya sani tun daga ranar da yaron ya riƙe ƙafarsa ya shiga ransa, dan haka da sauri ya aje yadin da measuring tape ɗin duka ya fice da sauri ya faɗa ɗakin.
Ya iske Naani ɗin nasa ta na rarrashinsa shi kuma sai kuka yake, gaba ɗaya ya rikita Naani ɗin nasa.
“Kinga kawo shi”
Ya faɗi yana miƙa mata hannu, miƙa masa shi tayi, shi kuma ya karb'eshi ya fice daga ɗakin.
Office ɗin nasa ya koma da shi, ya shiga rarrashinsa, amma yaƙi shiru, sai kawai Uche ya ɗauki wani zanin atamfa daya yanka ya goyeshi, yana jijjiga shi.
Tunda Aryaan yazo duniya ba'a tab'a masa goyo irin wannan ba, dan Hanam bata goyonsa saide ta sakashi a baby carrier, nan da nan yayi bacci.
Hanam taji kukan Arya hakan yasa itama ta fito domin taga abinda yake faruwa, sai Naani ɗin ta faɗa mata cewar ai wannan na ɗayan office ɗin yazo ya karb'eshi, dan haka Hanam ta fita, ta shiga office ɗin Uche.
Samunsa tayi yana kai kawo da Aryaan ɗin a bayansa, kuma gashi ya goye shi, wani abu ya motsa a kirjinta, wanda rabonsa da ya motsa tun shekaru biyu baya, sai ta kawar da tunanin, dan a ganinta abun ba meyiwuwa bane, ita sai abun ma yaso ya bata dariya, namiji da goyo, kuma ya iya goyon ko dan igbo ne oho.
“Yanzu Uche da atamfar dubbunan kuɗin ka goyi yaro ?”
Ta faɗi tana shigowa ciki, shi sam ma bai kalleta ba.
“Me zai hana idan de boy ze yi shiru, idan yana kuka bazan iya aiki cikin kwanciyar hankali ba”
Hanam taji wanna abun yaci gaba da motsawa, kuma wannan irin wanda tavjine lokacin da ta haifi Arya ɗin.
“Naga ya yi bacci kawo shi, kar ya hanaka aiki”
“Ba dole yayi bacci ba, yaji goyo, nasan yanzu haka ba goyonsa kike ba”
Ya faɗi yana ƙoƙarin since zanin goyon.
“Na miye zan wani zo ina goyonsa, ai baby carrier ɗin shine dai-dai shi”
Ta faɗi a lokacin da ya miƙa mata shi, daga haka kuma ta fice daga wajen, Uchenna yabisu da kallo su duka, yana murmushi ya dawo yaci gaba da aikinsa.

*ALARO CITY, BLOCK 3, HOUSE NO 122*
*Da misalin karfe 06:00pm*
Maryam ce tsaye a cikin kitchen ɗin gidan, meat pie take haɗawa, dan yau da safe Tafida ya faɗa mata cewar an gama komai na makarantar ta dan haka gobe za suje tare a ƙarasa sauran abubuwan.
Yanayin murnar da take ciki sam bame kwatantuwa bane, lokacin da aka ɗaura musu aure kowa faɗi yake cewa tayi sa'a duk bataga sa'ar da tayi ba sai yanzu, a yanda ta fahimta shima sam baisan da auren ba, amma kuma haka ya haƙura ya karb'i auren nasu hannu biyu.
Kuma babu abunda ya rageta da shi, komai yana mata, bata da wani abunyi sai godewa Allah da kuma shi Tafidan, data fusakanci baya san tana gode masa sai ta samo wata hanya ta gode masa da ban, Ta lura da yanada san cin abinci, kuma yana san abincin da take girkawa dan haka sai ta ke gode masa ta hanyar abinci.
Kullum da safe sai ta tsantsara masa girki na gani na faɗa, da yamma ma haka, dama na rana baya ci a gidan, duk girkin da take dashi a wayarta shi take masa, kuma dama ita gwanace wajen girki, kuma ta lura da yana jin daɗin girkin nata.
Sbd zata fara zuwa makaranta yasa yau ta yanke shawarar musi meat pie da cake, sbd koda zata makara da safe wata rana, Sai su samu su rage hanya.
Kuma shekaran jiya yace mata taje su gaisa da matar maƙocinsu, kuma taje ɗin dan harma ta ɗan jima a gidan dan matar tana da kirki, duk da ta girme mata a shekaru, dan zata iya fin Anti Fati ma.
So take tayi ta gama soya meat pie ɗin kafin magariba tayi, dan cake kam tuni ta riga ta gama shi, shima meat pie ɗin kaɗan ne ya rage.
Kuma kafin magaribar ta gama soya shi tas, ta juye a wasu containers masu kyau, ta zuba cake biyar meat pie shida a wani ƙaramin kwano me murfi, wanda zata miƙawa Maman Ilham, kamar yanda matar tace mata shine sunan ƴarya ta farko.
Ta zuba gaba ɗaya kayan data b'ata a dish washer, dan bata wani wanke-wanke, komai cikin sauƙi take yinsa, ta goge duk inda ta b'ata, sannan ta ɗebi warmers ɗin data zuba abincin data girki, ta fita daga kitchen ɗin.
Ta jerewa Tafida nasa akan danning table, sannan tayi sama. Sallar magariba ta gabatar, sannan ta ƙara sauƙowa ƙasa ta ɗauki wayarta dake chargy a parlo, ta ɗauki wannan kwanon data zubawa Maman Ilham meat pie ɗin, ta janyo ƙofar parlon ta fito compound ɗin gidan.
Sai da ta kalli parking lot ɗin gidan, motocin Tafida ne guda biyu kawai, dan ya fita da guda ɗaya, ta buɗe ƙaramar ƙofar gare ɗin ta fito.
Bata damu da ta kulle gidan ba, dan a ganinta babu wanda zai iya shiga gidan bare har yayi sata, ta tsaya tana kallon kyakyawar unguwar tasu, yanda take da kyau da daddare, bata tab'a fitowa da daddare ba sai yau, dan last time data fito har ta shiga gidan Maman Ilham ɗin da rana ne, kuma shine fitarta na farko, sai kuma yau a gaba ɗaya zamanta a unguwar wurin kwana shida, saide ta ganta ta saman balcony.
A hankali ta shiga takawa har zuwa ƙofar gidan dake jikin nasu, wanda yake shima sak nasun yake, ita ranar data shiga gidan ma tayi zaton zata ga komai na ciki irin nasu ne, amma sai taga hatta da ginin cikinma irin nasun ne amma banda kayan cikin.
Kanta tsaye ta tura ƙaramar ƙofar ta shiga, dan ta lura da gaba ɗaya gidajen unguwar basubda masu gadi.
Sai da ta ƙwanƙwasa ƙofar parlon gidan, sannan aka buɗe, Ilham ɗin ce ta buɗe mata ana gaisheta, itama Maryam ɗin ta amsa mata da fara'a
“Ilham waye ne ?”
Muryar Maman Ilham ɗin ta tambaya daga cikin parlon, Ilham ɗin ta buɗe kofar gaba ɗaya tana faɗin.
“Anti Maryam ce”
“To ta shigo mana, sai ta tsaya a waje?”
Maryam ta shigo tana murmushi, Maman Ilham ɗince a parlon ita da sauran yaran nata biyu, aliyu da abdul, ta zauna a sanda suma suke gaishe ta, sannan suka gaisa da Maman Ilham ɗin.
“Maman Ilham meat pie ne nayi, shine nace bari na kawo miki a bawa yara”
“A'a to an gode”
Maman Ilham ta faɗi tana karb'ar bowl ɗin
“Gobe zan fara zuwa makaranta”
“Tanan ALARO zaki fara zuwa ?”
“Eh”
Maryam ta amsata kanta a ƙasa kamar yanda ta saba.
“To Allah ya temaka, Allah ya bada sa'a Maryam ”
“Ameen, ni zan koma”
Take miƙe
“Har zaki koma?”
“Eh magariba ta yi, nasan ya kusa dawowa ”
“Hakane kam, Ilham tashi ki rife mana ƙofar”
Ta ƙarashe tana kallon ilham ɗin, lokacin Maryam har ta kai bakin ƙofa.
Tun daga fitar ta daga gidan su Ilham ɗin ta hangi motar Tafida sai kawai ta tsaya a ƙofar gidan har ya ƙaraso, ya buɗe gate ɗin da wayarsa sanna ya shiga da motar.
Amma bai kulle gate ɗin ba dan ya ganta shima, fitowa yayi daga motar ya dawo ƙofar gidan inda take, Kuma tun kafin ya ƙarasa inda take ya fara sabbaben nasa, wato sauraren bugun zuciyarta, wani abu da ya zame masa farilla a kwanakin nan, abun na mugun bashi mamaki, dan yanxu abun ya zame maza jiki.
Idan baya gidan har Allah-Allah yake ya dawo, dan yazo yaci daddaɗan girkinta, ga kuma daddaɗan sautin bugun zuciyarta, wanda yake saka masa nutsuwa a koda yaushe, a da daga asibiti sai gida sai kuma filin wasan cricket, bashi da wani abu na nishadi bayan cricket ɗin.
Amma yanzu an samu sauyi, zuwan Maryam rayuwarsa ya sauya abubuwa da dama, ya koma wani Tafidan da ban da na da, yanzu ya koyi yawan cin abinci, sab'anin da, da ba sosai ya cika cin abincin ba, sbd shi bai cika san cin abincin waje ba, yafi so ya girka da kansa, wani lokacin a makare yake tashi baya samun damar yin girkin.
Da yamma kuma ya dawo a gajiye wataran saide yaci bread kawai ya sha ruwa, amma yanzu a kullum so yake tace masa ga abinci, dan ya samu yaci daddaɗan girkinta, shi yana mamakin yanda kanta yake a waye, ga yanda ta iya girki, har tunani yake ma wata ƙila tayi makarantar koyon girki ne.
Ga kuma yawan sauraren waƙa da yake a da, amma banda yanzu, sam sauraren waƙarma baya gabansa, wannan bugun zuciyar tata, shine ya zame masa kamar waƙar, wani lokacin sai ya raba dare yana saurarensa, koda tana ɗakinta yana iya jiyoshi.
Saide idan tana ƙasa ne, amma middin tana ɗaki to zaiji yanda zuciyarta ke bugawa, kuma har yanzu idan yana tsaye a gabanta zuciyarta na bugawa cikin tsoro.
Sai kuma wani abu dake faruwa da shi, rabon da baƙin ruhinsa ya tashi tun yana haɗejia, kuma hakan ya bashi mamaki, duk da a wasu lokutan idonsa na sauya kala, duk da a da can baƙin ruhin baya tashi sai idan an b'ata masa rai.
Shi kuma abu mawuyacine ke b'ata masa rai, a kwanakin nan ne abun yayi ƙamari, amma kuma yanzu gashi ya tafi, Sannan har cikin ransa yake fatan Allah yasa ya tafi har abada. Sai de kuma shi da kansa yawan cewa yana nan, babu inda ya tafi, Dan akwai wannan super natural ɗin a jikinsa.
Ko kaɗan baya fatan wani abu da zai cutar da Maryam, musamman ma ace daga gareshi ne. Gaskiya Muktar ya faɗa, tabbas yayi dace, dan Maryam ɗayace tamkar da dubu, samun irinta a wannan zamanin sai an tona.
“Sannu da zuwa”
Muryarta ta fito cikin sanyinta, kuma yaji sanda zuciyarya ta buga, ya samu kansa cikin irin yanayin da yake tsintar kansa a duk lokacin da ya saurari bugun zuciyar tata cikin tsoro ko nishadi koma murna.
“Sannu Daaso, gidan Mustapha ki ka je ?”
Daaso ?, shekaran jiya ya fara kiranta da sunan, wata ƙila dan nishaɗi yake kiran sunan, Mustapha kuma ta san sunan mijin Maman Ilham ne, dan haka ya faɗa mata ranar da yace mata taje gidan.
“Eh, nan naje, banma jima ba yanzu na shiga kuma na fito”
Ya ɗan cije lips dinsa kaɗan, sannan ya gyaɗa kansa a hankali.
“Hira ki ma je ku kayi?”
“Ko kaɗan, nayi meat pie ne, shine na kai mata nace a bawa yara”
Yanzu ma kansa ya gyaɗa sannan yace.
“Muje ko?”
A hankali ta fara takawa zuwa cikin gidan, ya tsaya a wajen yana kallonta, sannan ya rufe gate ɗin, ya shigo gidan shima.
Bai sameta a parlo ba dan haka yayi saman shima, wanka kawai yayi dan yayi Sallah a hanya, ya saka wasu jogger set farare, ya rufe kansa da hular hoodie ɗin kayan, ya sauƙo ƙasa, cike da farin cikin zai ci girkin Maryam.
Kuma kamar yanda ya zata ɗin ne, ta aje masa komai akan danning, ruwan shansa da abincinsa yaga yau harda juice a wani jug na glass.
Bai san sanda murmushi ya sub'uce masa ba, to shi kuwa miye ba zeyiwa wannan innocent soul ɗin ba ?.
Kujera ya ja ya zauna, sannan ya buɗe plate ɗin da ta aje, ya buɗe warmer ɗin farko, wadda yake da tabbacin miyace a ciki, kamshin spices ne suka fara shiga hancinsa, kafin yayi arba da cabege sauce, kalar cabejin daya hadu da attaruhu da tattase sune sukafi ɗaukar hankalinsa.
Harda haɗiyar yawunsa, sannan ya aje murfin a gefe, ya janyo ɗayar ya buɗe ita kuma farar shinkafa ce a ciki, wadda ta dafata da carrots da kuma green beans.
duka ya juye shinkafar a plate ɗin, sannan ya zuba miyar, ya hauci yana ta lumshe ido, da ace yana da yawan magana da wata ƙila santi zeyi, dan abincin nata ya kai a masa santi.
Yana ci yana haɗawa da strawberry juice ɗin da ta aje masa, har ya cinye tas, dan dama bata tab'a zuba masa abinci ya rage ba. Tashi yayi ya shiga kitchen ɗin, ya buɗe dish washer sannan ya jere mata kayan a ciki.
Har ya juya zai fita kamshin wani abu ya bigi hancinsa, ya waiga ya waiga sai hango wasu containers guda biyu kusa da stove, beyi tunanin komai ba ya nufi wajen.
Ta farko ya buɗe yaci karo da meat pie, hannu yakai ya ɗauki guda ɗaya ya kai bakinsa, ya cinye shi tas, sai kuma ya rufe mata.
Ya buɗe ɗayar ita kuma cup cakes ne a ciki shikam guda biyu ya ɗiba ya cinye shi duka, a ransa yake faɗin, Maryam na so ta maida shi acici. (kujini da ɗan raini😁).
Rufewa yayi ya maida mata ya aje sannan ya fito, a parlo ya zauna, ya kunna wata tashar da ake nuna wasan cricket, ya kishingiɗa yana kallo, harda ture hular hoodie ɗin, ya shiga shafa sumarsa data fara taruwa, sbd alƙawarin da yayiwa Daadi, hatta wajen fade ɗin ma ya tara gashi.
Ko me ya tuna sai ya miƙe tsaye ya nufi ɗakinsa ya ɗauko wani abu ya dawo ƙasan, yana daga inda yake ya ƙwala kiran Maryam.
Maryam na zaune a ɗaki tana sauraren ƙira'a qur'ani, taji kamar Tafida na kiranta, kasan cewar kunne ɗaya ta saka.
Sai ta cire ear piece ɗin, ta shiga ƙoƙarin danna pause amma sam wayar taƙi bata haɗin kai, haka take mata kwana biyu, ta ɗan ja gajeren tsaki, sai ta tsayar ta jikin ear piece ɗin, ta miƙe hannunta riƙe da wayar ta saka hijjabinta ta fita.
A parlo ta sameshi, sai ta zauna a ƙasa.
“No seat here”
Maryam ta kalli inda yake nuna mata, gefen kujerar da yake zaune a kai ne, kasan cewar kujerar nada tsayi ita kuma sai ta zauna a can ƙarshen kujerar.
Kanta a ƙasa kamar kullum idan tana gabasa, gyaran murya yayi, bayan ya gama saurarar abinda ya saba.
“Kamar yanda na faɗa miki, an gama komai da kamai na makarantar ki, so gobe zamuje tare zamu ƙarasa abinda ya rage...... Nasan zaki buƙaci wani abun na amfanin makaranta, so ni bansan me kike so ba, dan haka na yanke shawarar kawai na baki kuɗin ki siyi kome kike so, dan akwai super market nan kusa da block ɗin mu, zaki iya zuwa ki siyi abunda kike da buƙata”
Ya ƙarashe yana mika mata kuɗin da Maryam bata san adadinsu ba, hannunta cikin hijabinta ta karb'a, kuma hannu biyu
“Nagode sosai, Allah ji ƙan mahaifa”
Bai amsa a fili ba sai yaci gaba da cewa
“Kina da waya ne ?”
A hankali ta gyaɗa masa kai, tana fito da wayar tata daga hijabi ta nuna masa, saida Tafida ya kusa yin dariya, amma yasan idan yayi zata ji babu daɗi, amma wayar tata ta bashi dariya, like for real matar Tafifa da wannan wayar.
“Daaso wanna ai ba waya bace”
Dama tasan za'a rina, taya za'ayi Tafida ya kalli wayarta da kima, yana riƙe waya biyu, kuma duk da ba sanin kuɗin wayoyin ta yi ba tasan masu tsadane.
Barinma iPhone ɗinsa, dan wayar ta burgeta ita kanta, musamman ma gefen wayar wani abune aka kewaye wayar dashi kamar gold
“Karb'i wannan, akwai numbers ɗima akai, idan na shirya zan karb'e su”
Ya miƙa mata Samsung ɗinsa, ƙirar S22 ultra, Maryam ta kalli wayar, sai kuma a hankali ta ɗago ta kalleshi, shima ɗin ita yake kallo, kafin ta kai hannunta ta karb'i wayar, za tai masa godiya ya katseta da faɗin.
“No Miriam, you don't need to be”
Miriam ?, ita kuma haka za ta yi ta samun sauyin sunaye ?.
Ranar haka ta kusan raba dare tana ta shige da fice a cikin wayar, ita wayar tamafi burgeta akan kuɗin da bata ma samu TA ƙirga ba.
Duk da shima kuɗin ta ji daɗinsa, domin bata tab:a riƙe kudi kamar haka ba, ƙololuwar yawan kuɗin da take riƙewa a hannunta shine na registration ɗinta.
Amma ita wayar tafi yin gaba da ita, kuma taga babu sim a kai, saide wasu numbers da basu da yawa, kuma a ciki akwai ta Daadi, Neha, Chaacu Imran (Wato kawu Imran), Chaacu Irfan (Kawu Irfan).
Choti Gulzar (Sieger Gulzar), Ramesh, Arjit, Mahesh, da dai sauranau, yawancin number ɗin na india ne, hakan ke nuna mata cewar da yan uwansa na india Yake waya.
Sai kuma gallery data duba, tarin hotunansa ne birjit, abun har ya bata mamaki, ganin namiji da yawan hoto, ita da take mace ma bata da wasu hotuna na azo a gani, amma nasa kam sai baki take kamawa dan mamaki.
Kuma ciki taga na wadda take kyautata zaton itace Neha da kayan sojoji an musi shi da ita, abun mamakin shine kayan sojijin nigeria ne a jikinta, kuma gata ba india, hotuna dai sai wanda ya manta baiyi ba.
A ciki ma taga wani nasa wanda ya tara gashi a kansa har yayi parking ɗinsa, harda dariyarta, dan style ɗin hoton ya bata dariya.
“Eshaan Tafiida”
Ta furta muryarta ɗauke da wani irin nishadi da bata san daga ina yake fitowa ba, a cikin daren gaba ɗaya ta ɗebe kayan wayarta ta maida kan wayar, amma bata tab'a masa hotonsa ba ko ƙwara ɗaya, dan wata ƙila ya buƙaci kayansa, amma taji daɗin samun wayar sosai ba kaɗan ba.

HANAM POV.
Cikin sati ɗayan da Uchenna Franklin yayi a ƙarƙashinta sun ƙara samun kusanci, duk da bata fatan ya haura harkar kasuwanci kawai, dan ita dan shi tasa aka kawo shi, bayan nan kuma bata fatan wata alaƙa daban, sbd kamar yanda ta faɗa masa ne a wancan lokacin sunada banbanci sosai.
Kuma cikin sati ɗayan ya gama mata aikin da zai mata, sannan taji daɗin aiki dashi sosai ba kadan ba, dan ya iya ɗinki sosai, kuma bayan sun gama aiki saida ta sake masa tayin karb'ar kuɗi kamar tun sanda suka fara aikin amma yaƙi, kamar de da farkon.
Yace ita ƙanwarsa ce, ba zai karb'i kuɗinta ba, yayi mata ne matsayinta na ƙanwarsa.
An ce komai yayi farko yanada karshe, gashi har yau Uchenna zai bar fashion house ɗin, ya shigo office ɗinta tana bawa Arya custard dan yau Naani ɗinsa bata zo ba, ta miƙe da Arya ɗin a hannunts, tana masa murmushin da ma'aikatan wurin suka faɗa masa shi kaɗai takewa irinsa, amma su dai kam basa samunsa.
“Har ka gama ?”
Ta yi maganar tana kallon jakar hannunsa
“Eh wallahi na gama haɗa komai, zan kuma koma bakin aiki na”
“To Mr. Uchenna, Nagode, nagode sosai, thanks a ton”
“ you got it......my friend baƙo zai yi halinsa”
Ya faɗi yana ƙoƙarin karb'ar Arya daga hannunta ta sakar masa shi, ya karb'eshi.
“Muje na taka maka to”
Haka ta raka shi har parking lot, inda ya aje motarsa, ya bata Aryaan sannan yayi musu sallama ya tafi.
*Ma farin komai kenan😉*
_________________________
_Ah-Ah, su Daaso an shiga next level_
_Na fada ?, aa nayi shiru dai_
_Ina me mika muku dubbin godiyata, Allah ya temaki ko wannen ku🙏_
🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Babin yau sadaukarwa ne gareki Maman Eman*

*BABI NA GOMA SHA BAKWAI (17)*

HANAM POV.
Hanam ce kwance akan gadonta, daga gefenta kuma Arya ne zaune yana wasa, waya ce kare a kunnenta, tayi shiru tana sauraron matar dake iƙirarin cewa itace mahaifiyarta.
Wai mahaifiyarta?, matar da tun da tasa ƙafa ta bar nigeria kusan shekara ashirin da biyar bata ƙara waiwayowa ba.
Taje ta can ta haɗa wani sabon iyalin, ta manta da ƴarta dake nan cikin wani hali, hatta da date of birth ɗin yarta tata ta manta, tana da jika amma bata sani ba.
Da ta ga hotonsa akan dpn Hanam ɗin ta tambayeta waye ?, Hanam ɗin tace mata ɗanta ne, kuma bata ƙara cewa komai ba, bata tambayeta ba shin aure tayi ?, tsintar yaron tayi ? ko kuwa.
Babu ɗaya data tambaya daga ciki. kuma sai tayi shekara bata kirata ba, itama kuma Hanam ɗin bata kiran nata sai de idan ita tayi niyya ta kira. Dan ta tica ta faɗawa kanta cewar bata dariya mahaifiya.
“Izan shu an shaglik ?”
(To yaya aikin ki ?)
Muryar matar wadda daga muryarta zaka tabbatar dacewa balarabiya ce, ta fito daga cikin wayar, sai da Hanam ta wani jujjuya idonta sannan tace.
“Kullu tamam..... kaif waladik?”
(Lafiya ƙalau, ya yaranki ?)
“kullun mnah, am ya sallumu alaiki”
(dukansu lafiya, sun cema suna gaisheki) Muryarta ta fito da fara'a, taji daɗi an tambayi yaya lafiyar yaranta, Hanam ta miƙe zaune tana cire wani zare a kan Aryan
“Biya'ar funi shi ?”
(sun sanni ne ?)
Saida tayi dariya sannan ta amsata
“Hinin biya'arfuki kitir”
(sun sanki sosai ma kuwa)
Hanam ta gyaɗa kai.
“Ibni bi hajati, salam”
(Ɗana yana buƙa tata, sai anjima)
“Oh ana asfe, kifu ibnik ?”
(Ohbyi haƙuri na manta, yaya ɗan naki yake?)
Ta manta ?, wai ta manta, taya za'ayi uwa ta manta da cewar yarta tanada ɗana?, ko da yake ba wani abun mamaki bane, hakan zata iya faruwa, tunda uwar ɗan ma manta ta ake, ai ba lefi dan an manta ɗan.
“Huwa mih, bitasil ma'ak ba'adain”
(Yana lafiya, zan kiraki daga baya)
Kuma bata jira cewar ta ba ta kashe kiran, kuma bawai dan Aryaan ɗin na bukatarta bane, wayarce ta isheta, komawa tayi ta kwanta tana kallon Aryaan, yana juyowa ya kalleta suka hada ido, his blue eyes ya tuno mata da shi.
Ta kawar da kanta gefe, a lokacin da shima yaron yaci gaba da buga motar wasan dake hannunsa, kuma jiyowa tayi taci gaba da kallonsa, wani abu na mata yawo a ka, tunanin shekarun baya suka su shiga dawo mata, waɗanan shuɗayen idanuwansu.
Ƙofar ɗakin aka ƙwanƙwasa, dan haka ta miƙe zaune, Abba ne ya buɗe ƙofar ya leƙo da kansa.
Kuma tasan babu me mata hakan sai shi, sai kuma Rafi'a ƴar gidan Hajjo, dan Allah ya haɗa jinin yarinyar da Aryaan, tana shigowa ɗakin idan Hanam ɗin tana gida, kuma itama bata hanata ɗaukarsa.
“Abba”
Ta kira sunansa bacin ya shigo ɗakin
“Na'am, Bannute (Babu girl) ”
Ya faɗi yana kallon su ita da Arya, bayan ya tsaya kusa da su.
“Ki shirya jibine tafiya hakuɗau”
“Ai kuwa gwara da ka tuna min, dan na manta, tare da sauran yaran gidan zamuje ?”
“Eh mana, ba ƴan uwanki bane ?”
“Nima bance komai ba fa, zan tafi da motata ne ”
“To shikenan..... Kai ƙatoto bakayi bacci ba ?”
Ya ƙrashe yanawa Arya wasa, Hanam ta yi dariya, irin wadda take a duk lokacin da ɗaya daga cikin su yake tare da ita.
“Wasa ya ke, kace Abba sai ka fara bacci zanyi”
“Idan ya yi magana ai guduwa zanyi“
Yayi maganar yana ɗaukansa, gaba ɗaya suka saka dariya.

TAFIDA POV.
Ƙofar ɗakin Maryam ya dosa, kuma tun kafin ya ƙwanƙwasa ya tsinkayi muryarta tana karuntun ƙur'an, yaji wani dummm, idonsa yayi duhu, kamar ana so za'a zare masa ruhinsa ne, yaji kamar wani abu ne zai fita daga jikin nasa.
*
Yayinda a can cikin wani rami, wata wani baƙin hayaƙi ya shiga yawo a cikin kwalbar, yana girgiza kwalbar.
*
Gara ya buɗe ƙofar ya dakatar da ita daga karatun kafin ransa ya fita gaba ɗaya, irin wannan yanayin yake shiga a duk lokacin da zeyi sallah, daga ya tada kabbarar harama zaiji wani yifff, kamar abu ya faɗo daga jikin nasa.
Sai kuma yayi sallahr cikin nutsuwa, yanajinsa sakayau, yana jin tabbas wannan shine, shine yake controling kansa ba wani ke controling ɗinsa ba, Sannan daga yace assalamu alakum na sallamar da sallah, wannan abun zai faɗo masa a ka.
Sai yaji kamar wani dutsene ya danne shi, kamar an ɗora masa wani abu akan nasa, kamar wani ke controling ɗinsa. Kuma a kullum a cikin irin wannan yanayin yake, sai de idan sallah zaiyi.
Ya kawarda ko wani tunani dake kansa ya buɗe ƙofar kansa tsaye, shi tunda ta zo gidan bai ƙara shiga ɗakin ba sai yau, bai ganta a cikin ɗakin ba, kuma dama ba daga nan yake jin sautin ta ke fitowa ba.
Yau cike da farin ciki Maryam ta tashi, dama ita bata saba baccin safe ba, dan haka tana tashi ta shiga yin aikace-aikacen ta data saba, ta gyara ko ina.
Sannan tayi girki me sauƙi, taci nata ta aje masa nasa akan danning kamar yanda ta saba, taga launch box har guda biyu a kayan kitchen ɗin, dan haka ta zuba musu cake da meat pie ɗin da ta yi.
Kuɗin daya bata kuma ta saka a cikin waya daga cikin jakukunan da fulani ta bata, sbd idan ta dawo daga makaranta zata tsaya a super market ɗin ta yi siyyaya, yau zata huta da zaman kaɗaici, wata ƙila ma sanda zata dawo gida shima ya dawo, dan haka kaɗaici ya ƙare.
Bayan da ta gama duk abinda za ta

Please Login or Register in order to submit comment