Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sanin cewa A strong woman will always turn pain into power.
Ta miƙa hannu ta karb'i Arya dake kuka, a lokacin data ƙarasa kusa dasu, ita kuma Rafi'an su Nabila sai zaginta suke sbd tana kuka akan wannan yaron, Inna Ai ta wurgawa Hanam harara tana faɗin.
“Gara ai, gara kizo ki fitar min da shege daga rumfa,daga ke har uwarki babu na kirki, Ai mu Muhammadu ya gama b'ata nan zuri'a, tunda har ya auri mana dangin ano ba”
Hanam ta tsaya daga fita daga cikin rumfar, ta juyo ta kalli tsohuwar, zuwa lokacin kowa yayi shiru yana san ganin yanda za'a kaya, dan dama can a gidan basa san uwar hanam ɗin.
“Iya Ai, ya.....isheki haka, kiyi magana a kaina babu damuwa, amma kada ki ƙara dangantani da waccan matar, ni bani da uwa.....”
“shi kuma ɗanki bashi da uba ko?”
Inna Ai ta yi saurin faɗi, tana katse Hanam ɗin, harda wani miƙewa tsaye tana jijjiga,.
Hanam ta ɗaga kanta sama tana lumshe ido, tare da lasar lips ɗinta, bata so ta yi loosing temper ɗints, amma da alama yau Inna Ai tana so ta tunzurata, ga kukan Aryaan dake hawa mata kai, idonta ta buɗe.
“Lak kras wu laik!!”
(Kayi min shiru!!)
Ɗif, kukan da Aryaan ɗin yake ya ɗauke, sbd gigitaciyar tsawar data daga masa, ita ba ta san damuwa, sai yayi shiru yana kallonta, ta juya ga Inna Ai.
“For the last time zan faɗa miki wannan maganar, babu ruwanki da ɗana, ta ya na sameshi ?, waye ubansa ?, daga ina yazo ?, duka bai shafe ki ba, sbd wannan damuwata ce”
Ta nuna kanta
“Damuwatace ni ɗaya, sbd Arya ɗana ne ni ɗaya, ɗana, ina fatan kin fahimta?”
Tana kaiwa nan taja jakukunanta ta yi b'angaren Baabaa, matar kakanta ɗaya da duk gidan babu me ƙaunarta kamar ita. Dan mahaifiyar Abba ta rasu, kuma kakansu matanza uku yanzu.
Uchenna Franklin ya bar ƙfar gate ɗin gidan, bayan ya gama sauraren duk abinda ya faru, har cikin ransa yake tausayin Hanam, memakon su tambayeta cikin ruwan sanyi ta faɗa musu a ina ta samo yaron sai de kawai su riƙa jifansa da kalmar shege, me yasa ne haka ?, me yasa.....
“Ah-ah, Harisu ashe da kai aka zo ?”
Uche ya yi murmushi yana duban tsohon da suke tare da Abba.
“Ai kasan babu yanda za'a yi a zo ganinka babu ni, sbd nayi kewarka sosai”
“Ƙaryar banza, idan kana kewata ka dawo hakiɗau da zama, ka riƙi fatanya sai na yarda da kayi kewata”
“To ai ni ko ƙauyenmu ma bana zuwa sbd noma, haka kawai da kuruciya ta zan zo nayi ta maka noma kaida matanka da ƴaƴanka kuna ta ci ni kuma na tsofe na rasa me aure na ?”
Tsohon ya yi dariya irin tasu ta manya.
“Sai in baka ɗaya daga cikin jikokina”
Uche yayi dariya
“To ya Maman taka ta ke ?”
“Mamana lafiyarta ƙalau, tana Enugu”
“To idan kunyi waya kace ina gaishe ta”
“zakuwa taji”.
***
*Da misalin 08:00pm*
Hanam ce ke girki a ƙofar rumfar Baabaa, noodles take girkawa akan ƙaramin gas stove ɗin da ta taho da shi.
Hatta da noodles ɗin ma ita ta taho da ita, dan ita ba iya cin abincin gwana goma za ta yi ba, bawai abincin nasu ne ba zata iya ci ba, domin suna da cima me kyau, kawai de tsaftar masu girkin nasu ce bata yarda da ita ba.
Dan ta taso a cikin hausawa ne, amma wannan kyankyamin irin na larabawa a jininta yake, ko kaɗan bata san kazanta. Noodles ɗin ta juye a cikin plate sannan ta ɗorawa Arya baby feed ɗinsa.
Data gama ta juye masa a baby bottle ( fida) ɗinsa me kan teddy, sannan ta kashe stove ɗin ta kawar da shi gefe, ta koma ɗakin.
Baabaa ta iske zaune tana lazimi ga Aryaan zaune a kan cinyarta, sai yunƙurin kamo carbin hannunta yake ita kuma Baabaan sai ɗaɗɗaga carbin sama take, sai ta miƙo masa kamar zata bari ya kama, kuma sai ta ɗga shi sama, shi kuma sai ya saba kansa sama sa hannunsa yana son ya kamo carbin.
Tayi musu dariya tana zama, hasken ƙwan lantarkin dake ɗakin ya haska ko ina, dan gidan kwana ake a yini da generator kamar ba kauye ba. System ɗinta ta cire a chargy, ta zauna ta shiga daddanawa tana cin abincin.
“Gashi ki bashi bulumbotin nasa ya sha”
Hanam tayi dariya
“saide na baki ki bashi da kanki”
Baabaa ta miƙa mata hannu, Hanam ta bata baby bottle ɗin.
“Amma fa da zafi”
“Bakya bashi abinci ne ?”
Hanam ta girgiza kai, tana ci gaba da danna system ɗin gabanta.
“Ina bashi, saide bana bashi me yaji”
Baabaa ta gyaɗa kai.
“Hanam ya kamata ace kinyi aure”
Hanam ba ta kalli Baabaa ba, dan wannan sabbabiyar maganace a wajenta, ta yi murmushi me ciwo, tana kai cokalin noodles bakinta.
“Aure ?, Baabaa babu wanda zai aure ni a haka, babu wanda zai aureni da ɗa, kowa kallon shege yakema ɗana, to waye zai auri uwar shege ?”
Tausayinta ya ƙara rufe Baabaa, tun tana ƙarama bata samu wani farin ciki ba, sbd uwarta data tafi ta barta, yanzu ta girma lokacin da ya kamata ace ta yi aure tana gidan mijinta kuma wata ƙaddarar da ban ta sameta.
“Kiyi haƙuri Hanam, Allah yasan da ke, wasu lokutan ɗan adam bai san sanda ƙaddarorinsa zasu ƙare ba, ki yi ta addu'a Allah zai baki wami sabon fata da ban”
Yanzuma murmushin ta yi kuma tana ci gaba da danna system ɗin.
“Baabaa nayi wannan addu'ar a baya, sai Allah ya bani Arya, na ɗauke shi a matsiyin wannan sabon fatan, shi da Abba kaɗai sun isheni”
Muryar ta fito cikin shaida abinda take faɗi gaskiyane, kuma haka ɗin ne bata buƙatar kowa ya shigo rayuwata, kullum cikin godewa Allah take daya azurta ta da Abba da kuma Arya.
“Salamu alaikum”
Sukaji sallama daga bakin ƙofa, Baabaa ta amsa. Uche ya leƙo ɗakin, Hanam tana mamakin yanda yake abu sai kace musulmi, ita dai bata amsashi ba, tanaga yanda suka gaisa da Baabaa kamar da suka saba sosai, abun ya bata mamaki.
“Hanam, Baba ne ke kira”
Uchenna ya faɗi yana duban Hanam, a hankali ta gyaɗa masa kai, shi kuma ya fita.
Ta miƙe ta saka takalmanta, wata farar cardigan dress ce a jikinta, ta san yanzu ba a gida take ba dan haka ta ɗauki wani ƙaramin gyale ta yafa a kanta, sannan ta karb'i arya a hannun Baabaa, ta ɗauki wayarta da ruwan gorarta ta fita.
A tsakar gidan taga gaba ɗaya ƙannenta da yayanta kamal ga abba ga uc3he a gefe, ga Inna Ai dake aiko mata saƙon harara.
Hasken globe ɗin dake wajen ya temaka mata wajen kallon kowa gaba ɗaya, daga gefen kakansu kuma ɗaya matar tasa ce, da kawunnansu suma suna zaune a wajen, duka de gida an taru, Baabaa ce kawai babu, waje ta samu ta zauna a kusa da kakanta tana masa murmushi
“Kai ɗan kauye baka kira Baabaan ba ?” Baba ya faɗi yana duban Uche.
“Wannan ai matarka ce, kaje ka kirata da kanka”
“Ja'iri ɗan nema, jeka kira min ita”
Uche na dariya ya shiga sashen Baabaa, Hanam de kam kanta ya kulle, taga kowama na gidan ya saba da shi, to yaushe hakan ta faru ?.
Bayan ɗan wani lokaci sai ga uche ya dawo Baabaa na biye sa shi, hanyar ƙofa ya yi zai fita, Baba ya kirashi yana faɗin.
“Ina za kaje ?”
“Waje zan fita naga ka tara iyalanka ne, ban sani ba ko wasiyya zaka basu”
“Ɗan nema dawo ka zauna, ai kai ma ka zama dan gida”
Arya ya na ta ɗagawa Abba hannu Hanam ta miƙa masa shi tana faɗin.
“Abba gashi yana maka magana”
Abba ya karb'eshi yana dariya.
Nasiha Baba ya musu kamar yanda ya sabba musu idan aka taru irin haka, kuma ya ƙara da magana akan auren Hanam, ita de kawai jinsu take, dan ita tasa a ranta babu wani aure da za ta yi.

MARYAM POV.
*Da misalin 09:00pm*
Tsaye take jikin kitchen island, tana decorating cheesecake, ranta fes, bata da kowace duwa, domin yanzu duk tsoranta akan halin da su Maanmu ke ciki ya kau, tana jin kamar ko wani buri da take da shi ya cika, babu abinda ya rage mata sai godewa Allah.
Yau Sunday babu makaranta kuma babu aiki, tun bayan da Tafida ya ci abincin safe yayi wanka ya shirya cikin kayan wasan cricket yace mata Ya tafi filin cricket, Kuma har yanzu bai dawo ba.
Tunaninta ya katse lokacin da aka turo ƙofar kitchen ɗi, ta ɗago da kanta ta kalli wajen, duk da tasan babu me aikata hakan sai me iko da gidan.
Kamar yanda ta zata shiɗin ne kuwa, ya sauya kaya daga green Jersey da ya fita da ita zuwa wata blue, a gefen Jersey ɗin an rubuta india, hakan ke nuna mata cewar ta india ce, sai wani jeans dake jikin nasa, gashin kansa a jike ya sauƙo kan goshinsa, alamun de wanka ya yi, idonasa manne da wani baƙin glass me duhu, kamar kullum fuskarsa babu fara'a babu akasinta, sai ya fito kamar wani jarumin Bollywood.
Kamar yanda take kallonsa shima ita ɗin yake kallo, bai jima da dawowa daga filin wasanin ba, sbd Khabir da ya kirashi yace masa ansamu hijaba nan, kuma gashi nan a hanya zai kawo masa su, bayan ya fito daga wankan ne ya kalli idonsa a mudubi yaga ƙwayar idonsa tayi ja.
Shi kam ya fara tabbatarwa da maganar su Fulani, da suka ce masa wata ƙila Maryam itace maganin matsalarsa, dan kusan sati biyu kenan rabon da baƙin ruhinsa ya tashi, kuma duk ya danganta hakan ne da shigowar Maryam rayuwarsa.
Baya san ya riƙa tsorata Maryam shi yasa ya saka glass ɗin, Abinda ya saba ya shiga yi, wato sauraron bugun zuciyarta.
A hankali cikin takunsa na kullum ya fara takowa cikin kitchen ɗin, still idonsa a kanta, ita kuma sai ta kawar da idonta a kansa ta ci gaba da jera raspberry ɗin da take jerawa akan cheesecake ɗin data hada.
“Yaushe ka dawo ?”
Muryar ta fito ba tare da ta kalleshi ba, tana ci gaba da abin da take, Tafida yaja kujera ɗaya daga tsallekin inda take tsaye ya zauna sannan ya amsa mata da.
“Ban jima da dawowa ba, saƙo za'a kawomin shi yasa na dawo da wuri”
Ta gyaɗa kanta tana saka raspberry ɗin na ƙarshe.
Shi kuma yaci gaba da kallon duk motsin da take, ya kalli hannunta, a hannunta na dama a yatsarta ta tsakiya akwai zobe, wata ƙila azurfa ce, dan yana kama da azurfar. A tsintsiyar hannunta na hagu kuma akwai wasu jerin abun hannu na ƙananun beads masu sheƙi, sai wal-wali suke a cikin hansken fitilun dake haskawa a kitchen din.
Maryam ta bar jikin island ɗin, ta nufi jikin cabinet ɗin da take aje ƙananun plates, kasan cewar cabinet ɗin a sama suke yasa sai ta yi tattage, kamar wani abun baki sai tsayinta ya kasa kaiwa, ko hannun cabinet ɗin ta kasa tab'owa bare ta buɗe.
“Matsa”
Ta tsinkayo muryarsa a bayanta, kuma cikin umarni, matsawar ta yi ta juyo tana kallonsa, daga inda yake ya ɗaga hannunsa saitin cabinet ɗin, ya motsa hannunsa daidai buɗewar ƙofar, Maryam ta juyo ta kalleshi ta jiya ta kalli cabinet ɗin data buɗe kanta.
“Me ki ke so ki ɗauka ?”
Maryam ta haɗiye wani abu, sannan ta lalubo muryarta tace.
“P...plate”
Saida yayi wani murmushi, sannan ya kuma motsa hannunsa, nan take plate ɗin ya fito daga cikin cabinet ɗin, kuma bai sauƙa a ko ina ba sai akan cabinet ɗin.
Duka a kan idon Maryam, wadda ta yi sumar tsaye, kamar mafarki take, kode tsafi yake ?, kuma ai yace mata he is monster saide kuma babu yanda za'ayi mutum ya zama dodo.
Kamar me tsoron taka ƙasa haka ta tako zuwa jikin island ɗin, hannunta na rawa tunani da yawa na yawo a kanta ta kai hannu ta ɗauki wuƙa.
Duka abinda take Tafida na lura da ita, so yake yayi dariya, amma kumma sai ya dake, yanzu iyaka wannan kawai ta gani ahse idan ta ganshi a wancan halin suman gaske za ta yi.
Da ƙyar Maryam ta samu ta iya yanka cake ɗin, ta ɗora akan ƙaramin plate ɗin da ke aje a gabanta, sannan ta ɗora karamin cokali a kan poate ɗin.
Ta tura plate ɗin gaban Tafida dake zaune a tsallakenta ya kafeta da ido, ya tabbatar da a halin da take ciki yana cewa kett!, zata saka gudu, dan ga yanda bugin zuciyarta ya sauya, tana bugawa da sauri-sauri.
Ya kai hannu yana jan plate ɗin gabansa, ya ɗauki ƙaramin cokalin ya guntsiri cake ɗin ya kai bakinsa, kamar kullum girkin Maryam 100% ne koma ya fi hakan, babu wata makusa. Yana ci yana kallon Maryam da ta masa nutsuwa.
“Ki zauna”
Maryam ta kasa ganewa umarni yake bata ko kuwa, tade kawar da komai dake kanta ta zauna, amma har yanzu ba a nutse take ba.
“Kin manta da abinda nace miki rannan ko?”
Yayi maganar a sigar tambaya, saide be jira amsawarta ba yace.
“Miriam”
Ya kira sunan daya raɗa mata ƙarfi da yaji, Maryam ta yi ƙarfin halin ɗagowa da idonta ta kalleshi, har yanzu idonsa sanye yake da glass, amma sai ya aje cokalin hannunsa ya kai hannu ya cire glass ɗin,
Ƙwayar idonsa da ta yi ja ta bayyana a idon Maryam, gaban Maryam ya shiga bugu fiye da ɗazu, ta zazzaro idanuwanta gaba ɗaya tana kallonsa, tunda Maanmu ta kawota duniya bata tab'a ganin abu makamancin wanda take gani yanzu ba, zata kawar da kanta gefe ya dakatar da ita.
“No dont, keep looking at me”
Babu yanda za ta yi bata iya musu ba, dan haka taci gaba da kallon nasa, saide zuwa yanzu ta fara hawaye, sai taga yayi murmushi.
“Ba tsafi nake ba Daaso, baƙin ruhi ne a cikin gangar jikina, yana controlling ɗin base on yanda yake so, kuma tun ina ƙaramin yaro na gamu da wannan abun, babu wanda yasan abinda ya haddasar min da wanna abun, su me martaba sunce akwai ɗaya daga cikin our forefathers da ya yi rubutu akan irin wanna abun nawa, kuma sunce wai ta yanda za'a dakatar da hakan shine ta hanyar aura min wata yarinya.... ni ban ma riƙe signs ɗin da sukace yarinyar tana da shi ba, shi yasa suka auramin ke, dan sunce wai kece yarinyar, Maryam a duk lokacin da baƙin ruhi na zai tashi bana ji bana gani, bana banbance masoyi ko maƙiyi, hatta da kaina ma bana ganewa, akwai abinda ban tab'a faɗawa kowa ba, amma zan fada miki.....”
Sai kuma yayi shiru, ganin yanda Maryam ke ta zubar da hawaye, miƙewa ya yi da ga inda yake ya dawo inda ta ke, ya zauna a kujerar dake gefen tata, ya miƙa mata hankin daya ciro daga aljihun wandonsa, Maryam ta karb'a tana share hawayen da suka ƙk tsayawa, kuka take da gasken-gaske, amma mara sauti, tausayinsa ya cika mata zuciya, Tafida ya gyara zamansa yana juyowa ya kalleta da kyau.
“Abinda ke jikina aljanine, kuma yana bani super natural, sannan yana kareni daga cin asiri, a duk sanda za'amin asiri baya cina, saide ya koma kan wanda yamin, kuma turoshi a kayi, idan ina mafarki ina ganin wanda ya turoshi, bansan waye shi ba, kuma bansan me yake nema a wajena ba, amma tabbas nasan shine yake cutar dani, rayuwata bata da wani amfani, dan sam bana iyayiwa ubangijina tasbihi, bana iyayiwa manzona salati, hatta da kalmar larabci ɗaya sometimes gagarata take, kuma kin san wani abun mamaki ?”
Ya faɗi yana kallon Maryam, ita de har yanzu kuka take, amma mara sauti, sai share hawaye take, bata iya ce masa komai ba shima kuma sai yaci gaba..........
________________
_Nace ba, wai a ina su Baba suka san Uchenna Frankline ?_
_Menene Abun mamakin da Ficar Yara yake SO ya rasa mana ?_
_A har kullum, ina me matuƙar godiya a gare ku, ngd sosai da goyon bayanku, me ƙaunar ku ce Salma Ahmad Isah_
_I LOVE YOU WUJIGA-WUJIGA❤😂_
🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: (Salma Ahmad Isah Sai Kaska)
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Na sadaukar da wannan babin gare ki Bilkisu H Muhammad*

*BABI NA ASHIRIN (20)*

.........“A duk sanda zanyi sallah, dana na yi takbiratul ihram sai na ji kamar wani abu ya fita daga jikina, kamar akwai wani gingimemen dutsi a kaina da aka sauƙe min, kamar da a ɗaure nake sai aka sakeni, kamar kuma ina ƙarƙashin sarrafawar wani abune, bana tantance yanayin amma sai naji ni wasai, ina jin cewa nine, nine ni a karan kai na, inayin sallahta a nutse, amma daga zarar na yi sallama, wannan nauyin dake kaina da zai dawo, wannan ɗaurin da a kamin zai dawo, zanji kamar ana sarrafani, kamar bani bane, bani bane akaran kai na, rayuwata akwai wahala WIFEY, shi yasa nake ganin lefin su Fulani da suka sakoki a cikin rayuwata, rayuwata bata da alƙibla, rayuwa nake ba irin ta sauran mutane ba, na banbanta da sauran mutane, sam bana farin ciki, duk dariya ko murmushin da zan yi yakan tsaya akan lebena ne kawai, baya kaiwa har cikin zuciyata, ko kaɗan bana farin ciki, saide kuma inasan naga na saka wasu farin ciki, tunda ni bazan samu ba me zai hana na bawa wasu, amma kuma Maryam shigowarki rayuwata ya sauya wasu abubuwan, a da baƙin ruhina baya kusanta ta sai raina ya b'aci, amma a wattanin nan da muke ciki sai abun yayi ƙamari, ya dawo yana tashi kullum, saide tun daga ranar da aka ɗaura mana aure bai ƙara tashi ba, saide kl nayi wannan....”
Ya ƙarashe yana nuna mata ƙwayar idonsa.
“Kuma kece kaɗai kike sakani naji cewa bani kaɗai ba ne, ina da wani, duk da ina da ƴan uwa amma kullum cikin kaɗaice nake jina, abubuwa sunmin yawa akai na, banajin daɗi jikina kullum, ko kaɗan wanna ba rayuwata ba ce”
Sai yaji wani nauyi dake zuciyar sa ya sauƙa, kamar wani dutse aka ɗora akan kirjin sa kuma aka sauƙe haka yake ji, yaji shi free domin ya amayar da abinda ke damunsa tsawon shekaru, bai tab'a zama ya bajewa wani ciwonsa haka ba, ko Neha da yafi kusancin da ita fiye da kowa bai tab'a magana da ita irin haka ba, bai tab'a ba, amma kuma kullum abun na ci masa zuciya, har yana barazanar hanashi numfashi, kuma duk abinda ya faɗa mata haka ɗin ne, baya jinsa daidai, baya farin ciki, yanajin kamar rayuwar tasa ba tasa bace, kamar ana sarrafashi ne, yanzu haka sai da yayi kokawa da wani abu sannan ya iya amayar da wannan maganganun.
“Ke kalleni nan”
Maryam na goge hawaye ta kalleshi, har idonta ya sauya kala zuwa ja, matsowa kusa da ita yayi ya kai ɗan yatsansa ya goge mata hawayen, a tarihin zamansu karo na farko daya fara tab'a jikinta kenan.
“Ki dena kuka is not good for you”
Maryama ta gyaɗa masa kai, wayarsa dake tsallaken island ɗin ta shiga playin waƙar Teri meri khani, hakan ke nuna wa Tafida cewa kira ne ya shigo, dan haka ya miƙe, ya dafa kan maryam sannan ya ɗauki wayar tasa da glasses ɗinsa ya fita.
Bayan Maryam ta iya ƙarfafa kanta ta dena kukan ta ɗauki sauran cake ɗin da bai ƙarasa ci ba, dama wanda ta haɗa ɗin duka ta saka a fridge, ta tattare duk abinda ta bata ta saka a cikin dishwasher na cikin dishwasher ɗin kuma wanda ta wanke ta ɗebesu ta sakasu a inda ta saba ajewa.
Batajin ko cake ɗinma zata iya ci, dan haka ta fita daga kitchen ɗin, fitowar tata ta yi dai-dai da shigowar Tafida daga Ƙofar waje.
Ido suka haɗa sai ta ganshi da baƙin glass har yanzu, taji tausayinsa ya ƙara kamata, hannunsa ta kalla taga ledoji har biyu, bata ce masa ƙala ba ta yi hanyar hawa sama.
“Wifey tsaya mana”
Maryam ta tsaya da tafiyar da take, a hankali ta ɗaga kanta sama tana so ta hana hawayen dake san zubowa sauƙa. Sai da ta tattabar da bazasu sauƙo ba sannan ta juyo, a lakocin Tafida har ya zauna akan kujera, da hannu ya yafito ta, dan haka ta dawo cikin parlon.
Gefensa ya nuna mata alamun ta zauna, sai ta zauna ɗin tana kama hijabin jikinta, yayin da shi kuma yake fitowa da wani kwali daga cikin leda.
“Desktop led ring light ne, tunda zaki fara food blogging”
Ya faɗi a lokacin da yake ciro kwalin, Maryam kawai kallonsa take, tana mamakin yanda yake iya b'oye abunda ke ƙarƙashin ransa.
Shi da kansa ya haɗa ring light ɗin, ya jona da wuta hasken ring light ɗin ya haske fuskar Maryam dan a setinta ya ajeshi, Maryam ta kai hannu ta tare fuskarta.
“Ha kawo ko ?”
“umm”
Ta amsa shi da ƙyar, sai kuma ya zare shi daga socket ɗin, sannan ya dawo ya zauna a inda ya tashi.
“Kinga yanda yake working ko ?”
Maryam ta gyaɗa masa kai, sai kuma ya janyo ɗayar ledar, ita kuma bai buɗe ta ba ya miƙa mata kawai.
“Kije ki, a ina zan aje miki ring light ɗin ?”
Maryam ta karb'i ledar tana miƙewa, bata amsa shi ba, sai kama ring light ɗin da ta yi ta aje shi a kusa da TV stand sannan tayi sama.
A kan gadonta ta zazzage ledar daya bata, hijabaine kusan kala goma, Maryam ta zauna a bakin gadon tana kallon hijaban hawaye na cika mata ido, ya kamata ace tayi wani abu akan rayuwar bawan Allahn nan.
Bai kamata ace ta barshi cikin wannan halin ba, ya zama dole ta temaka masa, kamar yanda ya temaki rayuwarta, sam bai kamata ta zuba ido tana ganinsa haka ba, she need to do something.

*Hadejia Emirates*
*Sashen bayi*
*Da ƙarfe 05:30pm*

“Ke?, wai ina kika je ne ?”
Cewar Hasana tana duban Husainarta, Husainar ta zauna tana sharce gumi.
“Kede bari, wannan mara rabonce tasani binne mata wani asirin da suka ƙara yi akan Tafida”
Ido waje Hasana take kallon yar uwar tata.
“Ke inji de baki binne ba ?”
Husaina ta girgiza kai.
“Na binne mana, me zai hanani binnewa”
“To amma Hassana me yasa ?”
“Sbd inaso na nunawa Fulani Sadiya cewa mugunta sayin faƙo ce, idan baka iya ba ka b'ata jikinka, ita har yanzu Allah bai sa ta gane cewa abinda take ba daidai bane, ta yi, ta yiwa bawan Allahn nan asiri amma bai ci shi ba taƙi ta haƙuri”
Hasana ta yi ƙasa da murya tana faɗin
“Ai wannan addiƙu mina diƙu inna hu ɗiɗif ce”
Suka saka dariya suna tafawa
“Har yanzufa bata lura da cewa duk asirin da ta masa kan ɗanta ya ke dawowa ba, kinga na neman mata data saka aka masa kan ɗanta ya dawo, ta saka a masa na shayeye shima ya dawo kan ɗanta, yanzu haka Allah ne kaɗai yasan name ta sa aka masa wannan karon”
“Allah sarki bawan Allah Tafida,yana can yana fama da kansa ita kuma tana nan tana shirin ƙara masa wani zafin”
Husaina ta dan daki cinyar Hasana tana faɗin.
“Me dallah nace miki asirin baya cinsa, wata ƙilama daya tafi bakinsa ƙofar garin hafejia yake dawowa”
Suka ɗan dara kaɗan kafin hasana tace.
“Kome ya tsare mata?, oho ”
“Wata ƙila dan tanaga yafi ɗanta halin arziƙi ne, sbd kinga shi bashi da wani hali na kushe, amma ɗanta fa ?, yafi kowa lalacewa, wata ƙila tana ganin kamar idan sarki ya sauƙa shi za'a ɗora, ita kuma da ɗanta su tashi a tutar babu, shi yasa take wannan abubuwan”
Hassana ta tab'e baki.
“Ammafa Husaina lamarin Tafida abun a duba ne, bisaga dukkan alamu akwai wani a bayan lamarinsa”
Husaina ta gyaɗa kai tana nazari.
“Ƙila hakane, to amma ke a ganinki waye ?”
“Yaya zan yi nasani, Allah shi ya barwa kansa sani”
Husaina ta aje kofin ruwan data sha tana faɗin
“Koma de waye muna fatan Allah kub'utar da shi daga sharrinsa, dan Tafida mutumin kirki ne”
“Ameen ƴar uwata”.

HANAM POV.

Saida sukayi sati ɗaya a hakuɗau sannan suka dawo abuja, Hanam saida tayi nadamar zuwanta hakuɗau wannan karon, dan basu tahoba saida Naba yace kada ta haura watan nan ba tareda ta nemi mijin aure ba.
Ta rasa yanda za ta yi ita bata da wanda take so, Jabeer ne kawai ta tab'a soyyaya da shi, bata da wata mafita dan Abba ma haka yasata agaba da nasa faɗan, ta laluba ta lalubo bata da wani tsayyaye sai Jabeer ɗin, shi kuma har yanzu yana santa.
Dan haka kawai ta cewa Abba ta amince da auren Jabeer ɗin, Abba yayi murna sosai kuma a ranar data faɗa masa cewa ta amince ɗin

Please Login or Register in order to submit comment