Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aljanin jikinsa, wanda yake tare da shi a koda yaushe, idan har aka bashi magani zai sakawa wanda ya bayar ɗin ciwo, koda tsafi za'a masa ba zai tab'a cinsa ba, shi kuma ya hana shi yin karatun addininku, dan yana saka ɗayan baƙin ruhin rauni,ya kuma hana shi komai na karatun addininsa, yake saka masa ciwon kai a duk sanda zai ko ji karatun da ga bakin wani.....”
Ya watsa wani abu me ruwa kamar mai a cikin wutar, sannan ya kalli Maryam.
“Ina so rayuwarsa ta lalace fiye da haka, shi yasa na bashi ƙarfin tsafi, domin duk wanda zai ganshi yana tsafi zai ɗauka cewa boka ne, dan haka zai guje shi.....”
Faɗowar wani abu ce ta katse maganar tasa, a tare suka kalli inda ƙarar ta sauƙa shida Maryam da Manikandan..........
_______________
_A'a, menene kuma ya faɗo ?, kode fidar yara ce ta iso ?, bana ce ba de_
_Ina godiya masoyan asali_
🌸SAI KASKA CE✍️🌸



⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*BABI NA HAMSIN DA HUƊU (54)*

.........A hankali ƙurar da ta turniƙe wurin take bajewa, siffar Tafida ta bayyana a gabansu, tsaye yake ƙyam, ƙwayar idonsa ta rikiɗa zuwa ja.
“Koda yaushe gargaɗinku nake a kan zuwan wannan ranar, amma babu wanda ya kula a cikin ku, yau ce ranar sakamako, za ku girbi abinda kuka shuka”
Muryar Kundali ta karaɗe wurin, a sanda take sauƙowa ƙasa.
Maryam na ɗora idonta a kan Tafida ta miƙe da gudu ta yi inda yake, tana isa kusa da shi suka rungume juna, ƙanƙameshi ta yi da ƙarfi tana sakin kuka, shima ya ƙanƙameta a jikinsa yana shafa kanta, shi ba zaice ya san yanda akayi ba, amma yana wannan maganar, bau ƙara gane kansa ba sai yanzu da ya ganshi a wannan duniyar.
“Ya isa...”
Ta sake shi tana kamo fuskarsa a raunane, hawaye ya shiga share mata ya na girgiza mata kai.
“Ina nan tare da ke, bazan bari wani abu ya sameki ba Miriam....”
Sautin dariyar Subhu da ta karaɗe wurince tasa ya yi shiru, ya tura Maryam bayansa yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya.
Fuskar Subhu ɗin kawai ya gane, dan shine ke shigo masa a mafarki, sai kuma wannan wutar da ke ci a gaban Subhu ɗin, domin irinta ce sak take ci a hannunsa a duk sanda baƙin tuhinsa zai tashi. Har zuwa lokacin Subhu na ƙya-ƙyata dariyarmugunta hara riƙe ciki.
“Zaka kare ta......”
Ya kwatanta yana kwaikwayar muryar Tafidan, sannan ya ƙara bushewa da dariya.
“Kai ne wanda zaka kasheta da kanka yaro”
Maryam ta ƙara riƙe rigar Tafida ta baya gam, tana kallon Subhu ta ƙasan kafaɗun Tafidan.
“Waye kai?!, kuma me kake nema?!”
“Rayuwarka nake so, taka dama ta duk wanda kake so, yanzu ba kai zan kashe ba, matar ka zansa ka fara kashewa”
Cikin ruɗu Tafida ya ɗan jiyo ya kalli Maryam.
“Eshaan shine ya zama sanadiyyar mutuwar Maanka......”
Ta shiga bashi labarin da ya bata wanda shi sam ma be sani ba.
Cike da masifa bala'i da kata'i ya juya ya kalli Subhu, kuma tun kafin ya yi wani yun ƙuri Subhu ya shiga karanto wasu ɗalasuman tsafinsa yana watsa jan gari a cikin wuta.
“....Swastikam,namonamaham....fabrishka ... fabrakam...oumm jeje bahim, oum nambakar.....”
Tafida ya ƙame ƙam, kafin duhu ya mamaye jiniyon ganinsa, kamar an kunna inji haka ya juya yakalli Maryam dake tsaye a bayansa.
Maryam ta zabura tana ja da baya, ido waje take kallon Tafidan da ya nufota, suna kaiwa ƙarshen bango ya damƙi wuyanta tare da ɗagata sama. Maryam ta shiga kakari tana kallon jajayen idanuwansa, magana ma ta kasa se bibbige hannunsa da take.
Da Kundali ta ga abun ba na ƙare ba ne, sai ta ɗuko wani botikin ƙarfe me ɗauke da ruwa, ta b'ace b'at, sannan ta zo ta tsaya a kan wutar tsafin gaban Subhu. Ta gwammace mijinta ya mutu, ta gwammace ɗanta ya mutu, dama ita tata ra ƙare, amma ko ba komai ya kamata a ce waɗanan masoyan sun samu rayuwar farin ciki, ba haka ta so ɗanta ya kasance ba, sai de ta yarda da ƙaddara, ta kuma san yanda ƙaddara ke sauya abubuwa da dama, ta so a ce Subhu ya yi karatu me zurfi, ta so ace ya zama wani abun a rayuwarsa, sam bata so a ce ya taso a matsayin boka ba, bata san sana'ar mahaifinsa, amma babu yanda ta iya, haka ƘADDARA TA SO.
Ba tare da wani tunani ba ta ɗaga bukitin sama ta juye ruwan ciki tas a kan wutar.
Subhu ya ga ruwa na zubowa da ga sama yana kashe wutar da ya kunna shekaru talatin da 'yan ka baya, wutar da ya sha zama ya na gadinta, wutar da ya yiwa alƙawari da ba ze yi wanka ba tsawon rayuwarsa, wutar da yake hana idonsa bacci domin kula da ita, yau itace ta mutu murus a kan idonsa.
Wata razannaniyar ƙara ya saki yana miƙewa. Fitar ƙarar tasa ta yi dai-dai da faɗowar Maryam ƙasa, sbd wuyanta da Tafida ya saki.
A hankali tunaninsa ya shiga dawowa cikin kansa, duk irin abinda ya yi wa mutane sanda baƙin rubin nan ya shiga jikinsa ya dawo masa.
“Kin cece shi yanzu, amma fa ki sani Kundali bazan barshi ba!”
Cewar Subhu yana kallon sama, duk da baya ganin Kundali ɗin amma yasan cewa tana jinsa, kuma itace ma ta kashe wutar.
Sauƙowa ya yi da ga kan kujerasa, ya nufo inda Tafida ke tsaye ya dafe kansa, Manikandan ne ya riƙo hannunsa.
“Kada kaje yaro, komai ya ƙare, zaka iya jawa kanka matsala ”
Subhurmanyam ya kwace hannunsa daga riƙon da Manikandan ya masa.
“Bazan haƙura ba, sai na ɗau fansa ta”
Yana faɗin hakan ya juya ya ɗaga sandarsa a setin Tafida, nan take Tafida ya tashi sama, ƙafafuwansa suka rabu da ƙasa, yayin da wani baƙin hayaƙi ya mamaye shi.
Da ƙyar Maryam ta iya miƙewa zaune, hannunta dafe da wuyanta, se faman tari take, idanuwanta sun ƙwalalo waje. Bango ta daddafa sannan ta miƙe.
“Eshaan ka kira sunan Allah!”
Da ƙyar Muryar tata ke fita, dan Allah ne kaɗai yasan irin dauriyar da ta yi wurin furatata, sama take kallo inda gangar jikin Tafida ke yawo a iska.
“Ka kira sunan Allah Eshaan!”
Wannan karon maganar tata da ɗan ƙarfi ta fito, amma babu ma alamun Tafin ya jita, sbd wata ƙara da ya saki.
“Ka kira suna abin bautarka yaro!”
Muryar Kundali ta ta ya Maryam wurin faɗin hakan, kuma har yanzu bata bayyana ba, tana da ga sama tana kallon abinda ke faruwa.
“Ka kira sunan Allah Eshaan”
“Yaro ka kira sunan abun abun bautarka”
Kusan a tare suka furta hakan, wasu hawaye masu ɗumi na sauƙowa daga idon Maryam.
“Ka furta sunan Allah Eshaan,nasan kana ji na, Allah shi kaɗai zai iya cetonka”
“La'il....”
Bakinsa ya rufe, sbd yanda Subhu ya ƙara ƙarfin tsafin da yake aika masa.
Amma Tafida be daddara ba, ya ƙara furta.
“Lahau....”
Muryar tasa ta fito dai-dai da kawowar hasken baƙin zaren da ke ɗaure a ƙafarsa ta dama, yana yin shiru kuma sai zaren ya ƙara komawa baƙi.
“Kada ka saduda, say it again!!”
A dai-dai lokacin a cikin kansa tunanin rayuwarsa ta baya ga shiga dawowa masa.
*
Shine zau ne a kan kujera, baƙin zaren da Roshni ta saba ɗaura masa riƙe a hannunsa.
_“Kai Eshaan, baka jin magana ko?!!”_
Muryar Roshni ta faɗi tana zama kusa da shi, tare da karb'ar baƙin zaren hannunsa. Ta ɗago ƙafarsa ta dama sanna ta shiga ɗaura masa zaren.
_“Kana ji na ko?!, kada ka sake cire zaran nan”_
Ta saki ƙafar tasa tana shafa sumar kansa.
_Maa, me yasa kowa yake saka baƙin zare a ƙafar dama?”_
Roshni ta janyo shi jikinta.
_“Kowa ma a india yana ɗaura baƙin zare a ƙafarsa ta dama, 'yan addinin hindu sun ce kariyace da ga abun bautarsu, mu kuma musulmai, muna sakawa ne sbd kariya, domin addi'o'i da ayoyi ne a jiki, kamar yanda ayatul kursi ke bada kariya ga gida muma haka baƙin zaren ke bamu kariya, sbd haka kada ka ƙara cirewa kaji ?”_
Ya gyaɗa mata kai. Roshni ta kai hannunta tana tura sumar kansa baya.
_“Yeh mera bacca hai!(That's my boy!)”_
Ya yi dariya yana kwanciya a jikinta.
_“Tashi kaje ka yi wasa, maza,maza,maza!, hhhhhhhh”_. Ta ƙarashe tana masa cakulkuli.
_“Hhhhhh, Maa, Chor mujeh, (Ki bar ni)hhhhhh!”._
*
Shi da Auwal ne tsaye a ɗakin wani mara lafiya, kullum idan Auwal ɗin ya dawo gida se ya bashi labarin wani yato da suka karb'a a asibitinsu.
Auwal ɗin yace masa yaro ne ƙarami, ya gamu da ciwon Cancer, shi ne yau Auwal ɗin ya ɗauko shi yace su zo su duba yaron.
Hannun Eshaan ɗi sanye cikin na Auwal, yana kallon yaron cike da tausyawa.
_“Appa yana jin ciwo ko?”_
Auwal ya sunkuyo da kansa ya kalle shi.
_“Sosai ma kuwa”_
_“Amma ai ze warke ko?”_
_“Inshaallah”_
_“Idan ma be warke ba idan na zama likita zan masa magani”_
Auwal ya sunkuya ya ɗauke shi a hannunsa, suka ci gaba da kallon yaron.
_“Na sani My Boy, na san cewa idan ka girma zaka temaki kowa, ka saka kowa farin ciki”_.
*
Shine tsaye a gaban teburi me ɗauke da cake, wanda aka rubuta 'HAPPY BIRTHDAY ESHAAN', duka danginsa na india dana nigeria sune tsaye a bayansa suna taya shi murna.
*
Shi da Neha ne suke guje-guje a lambun gidan Daadi. Yayin da shi ke riƙe da ball, Neha ɗib kuma na binsa da gudu tana faɗin.
_“Bhai ka bani, ka bani mana!”_
Shi kuma ya ci gaba da gudu yana dariya.
*
Shine zaune a gaban Me martaba da Fulani Kahdija, Chiroma, Turaki da Mairama, ranar da aka ce masa Maansa da Appansa sun rasu, a lokacin da Fulani tace.
_“Ni zan kula da shi, dan Allah a bar min shi....”_
*
Shi da abokansa na jami'a ne suka buga wasan cricet a filin criket na jami'ar su.
Yayin da shi ya daki ball ɗin, ta tashi sama, kuma ta tsallke layin da ake buƙata.
Abokan nasa suka iyo kansa da gudu suna kiran sunansa.
*
Shine tsaye a cikin ɗaliban da suka yi graduation, sanye yake da acadamic gown, hannunsa riƙe da certificate ɗinsa.
*
Shine yake gaisawa da wani babban likita, a ranar da aka karrammashi sakamakon bajinta da ya nuna a aikinsa na likita.
*
Shi da Muktar ne suke zaune a chikin wani restaurant suna hira har da dariya.
*
Shine durƙushe a gaban su Me martaba ranar da suka faɗa masa cewar sun ɗaura masa aure da Maryam.
*
Shi da Maryam ne tsaye a gaban indian gate, yana ta mata bayani a kan tarihin ƙofar, sai ya lura da kamar hankalinta ba ya kansa, dan yaka ya tab'a ta.
_“Miriam!”_
_“Hmm!”_
_“Lafiya?”_
Sai ta girgiza masa kai, hannunta ya kama, sannan ya motsa kunnensa yana sauraron bugun zuciyarta, Maryam ta kalli hannunsa sannan ta kalli nata, ta ɗago ta kalleshi.
_“Ina tare da ke, komai zai yi dai-dai.......”_
*
“Ka faɗi sunan Allah”
Muryarta ta farkar da shi, ba shiri ya buɗe idonsa.
“La haula wala ƙuwata illah billahil aliyul azim!, La'ila ha'illa huwa, wahadahu la sharika lahu, hasbinnalahu la'ilaha'illalah!”
Wani abu sabo, wani abu da ya manta rabonsa da ya furta.
Fitar muryar ta sa ta fito tare da bajewar baƙin hayaƙin da ya mamaye shi, baƙin zaren ƙafarsa ya shiga kawo haske, wani irin farin haske da ya mamaye gaba ɗayan kogon.
Hasken da ya yi tafiya ya isa zuwa ga Manikandan da Subhurmanyam ya ɗaga su sama.
*** *** ***
A hankali Maryam ta shiga ƙifƙifta idonta. Kafin ta buɗe shi gaba ɗaya abubuwan da suka faru suka shiga dawo mata daki-daki.
Kafin ta bi wurin da take da kallo, cikin ɗakinta ne, dai-dai inda Subhu ya ɗauketa, kamar mafarki take, kamar idonta ta ƙifta sannan ta buɗe, haka take ganin faruwar komai.
Kuma kamar yanzu ta shiga ban ɗaki ta fito. Sai dai raɗaɗin da wuyanta yake mata da wanda goshinta ke mata ya tabbatar mata da gaske ne, duk abinda ya faru gaske ne.
A firgice ta miƙe zaune, dubanta ya kai kan Eshaan dake yashe a gefenta, kamar ma ba ya numfashi, kamar ba shi da rai!!.
*
“Baban Ilham dan Allah ka temaka mana, Esh...Eshaan ne ba shi da lafiya, ka kira emergencyn Alaro pls”
Muryar Maryam ta faɗa a sanda Ƙofar gidan su Ilham ta buɗe, Baban Ilham ya bayyana a gabanta.
Ta tashi Eshaan amma ko motsi baya yi, hatta da numfashinsa ma babu. Hakan yasa ta fito da ga gidan, kanta ko ɗankwali babu.
“Ki nutsu Maryam, ina Eshaan ɗin yake ?”
Ta kasa magana sbd kuka, ta fita hayyacinta baki ɗaya, ta kasa banbance baƙi da fari, ta gaza gane meke shirin faruwa da su, wace iriyar ƙaddara ce haka?. Side ɗin gidan kawai ta nuna masa da hannu.
“Maman Ilham, ki kula da ita, bari naje na duba Eshaan ɗin”
Maman Ilham da ke tsaye a bayansa ta gyaɗa masa kai, a lokacin dare ya yi.
Baban Ilham zai fita Maryan ta bi bayansa da gudu. Maman Ilham na riƙita sai de ina, hankalinta ya yi gaba.
A kan idonta a ka fita da Eshaan ɗin a ambulance, sannan ita ma aka wuce asibitin alaro ɗin da ita, dan goshinta da ke zubar jini har zuwa lokacin.
________________
_To ƙarsheb Subhu ya zo, amma kuma kamar akwai ƙura har yanzu, dab Fidar yara fa baya numfashi, toh!, ku biyo ni de_
_Godiya nake masoya🙏_
🌸SAI KASKA CE✍️🌸.



⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*BABI NA HAMSIN DA BIYAR (55)*

*Alaro city Hospital*
*12:30am*
Maryam ce zaune a kan kujerar dake kusa da gadon marasa lafiya. Ɗazu bayan sun kawo Eshaan asibiti, likitoci suka shiga duba shi.
Yayin da itama aka shiga dubatan, amma hankalinta na kan Eshaan ɗin, shi yasa bayan an gama mata tretment ta bazama ta fito ta tsaya tare da Baban Ilham.
Suna wurin har likitocin suka fito, suka sanar musu cewa doguwar suma ya shiga, amma su sun duba basu ga abinda ya janyo masa doguwar sumar ba.
Sai da Baban Ilham ya tambayeta abinda ya faru da su, amma bata ba shi amsa ba, dan a ganin ta babu wanda zai yarda da abinda zata faɗa.
Shima kuma be ƙara tambayar tata ba ya barta, abinci ma da Maman Ilham ta kawo musu bata ci ba, kuma rabonta da abinci tun daren shekaran jiya, amma bata jin yunwa, batajin wani abu me kama da ita.
Babu abinda ke gabanta sai ganin tashin Tafida, ya kalleta da shuɗayen idanuwasa ko kuma ja idan ya rikiɗe, ya kirata da 'Miriam' ko 'Daaso' ko yace mata 'Wifey'. Amma sam hakan ya gagara, gashi kwance a gabanta tana ganinsa, kamar me bacci, kamar idan ta kira sunansa ze amsa.
A hankali ta kwantar da kanta a kafaɗarsa, sannan ta ƙara riƙe hannunta dake cikin nata.
“Kai jarumi ne, jarumin da ya tsaya a gaban sheɗanu, ya fuskance su, ya yi yaƙi da tsoransa har ya yi galaba a kansu, me yasa yanzu ma bazaka yi yaƙi da wannan tsoron ba?”
Ta tambaya tana ɗago da kanta, ta kalli fuskarsa ta cikin hasken dake ɗakin.
“Me yasa ba zaka yaƙi abinda ya hanaka tashi ba ?”
Muryarta ta kuma amsawa a cikin dubun daren, da kuma shurun ɗakin.
Ƙara kwantar da kanfa ta yi a kafaɗarsa, tana karanto dum addu'ar da Allah yasa ta gifto a ranta.
Kamar da ga sama ta ji motsawar yatsunsa cikin nata, da sauri ta ɗago da kanta tana kallon fuskarsa, hannun nasa ya ƙara motsawa. Bakin Maryam ya tale da dariya, tana ci gaba a kallonsa.
“Da kyau, nasan zaka iya, Allah zai temakeka...”
Bata ko rufe bakinta ba idonsa ya motsa, kafin a hankali ya shiga buɗe shi, ya sauƙe su tar a kan Maryam.
Ƙoƙarin miƙewa zaune ta ga yana yi, dan haka ta shiga ƙoƙarin taya shi zaman, har ta samu ya jingina da jikin gadon, se jera masa sannu take, yayin da shi kuma ya ci gaba da kallonta, yana ganin yanda take ta fara'a. Zama ta yi a gefen gadon tana kallonsa fuskarta ɗauke da murmushi.
“Kaga ko...”
Hannunta da ya ja ta faɗo jikinsa yasa ta yi shiru, se kawai ta kwantar da kanta a kafaɗarsa tana kewaye shi da hannayenta.
“Allah ya bamu iko Daaso, Allah ya temaka mana”
Ƙara matse hannayenta ta yi tana murmushi. Kafin ya sake ta yana kallon fuskarta, zuwa yanxu ta fara hawaye, dan haka ya motsa hannunsa na dama a setin bedside drawer yana so tisssu yasauƙa a hannsa,amma ko motsawa tissuen be yi ba.
Ya juyo ya kalleta yayin da ita kuma take dariya, hannayenta ta saka ta tallafi fuskarsa.
“Komi ya ƙare Eshaan, babu abinda ya rage, sharrinsu ya bisu, babu baƙin ruhi babu jan ido, babu fiƙa, babu gurnani haka kuma babu super natural, yanzu kai ne, asalinka, gangar jikinka, ka sarrafata yanda kakeso”
Ƙara rungumeta ya yi a jikinsa yana furta.
“Alhamdulillah, Allah na gode maka”.
Ka fin Maryam ta ɗago da kanta tana kallon fuskarsa, still tana kwance a jikinsa, shima sai ya sunkuyo da kansa ya kara fuskarsa kan tata.
A hankali Maryam ta lumshe idonta sannan tabuɗe su cikin nasa.
“Miriam!, I love you to the moon and back....”
A hankali muryarsa ta faɗi, kuma leb'ensa kan na Maryam, kafin Maryam da kanta ta haɗesu wuri guda.....
*Peacock theater, 777 Chick Hearn CT, Los Angless*
Babban ɗakin taron cike yake fal da shaharrarun mawaƙa, makaɗa, 'yan fim da masu bada umarni, duk wani me ruwa da tsaki na harkar entaitament to ya hallara. Sakamakon taron karammawa da ake na Grammy Awards.
Daga kan stage kuma me gabatarwa ne ke jawabi cikin harshen turanci kamar haka.
“......Kamar yanda kowa ya sani, yau ne ake raba lambar yabo ga zaƙaƙuran da suka dace da samun wannan kyauta, a jiya aka gabatar da Grammy award talent cast, a yau kuma zamu karrama waɗanda suka yi nasarar cin wannan karammawa ta Grammg Awards.
Zan kira babban zaƙaƙuri, fasihin mawaƙin da waƙarsa ke zagaya faɗin duniya baki ɗaya, haziƙin da ya lashe lambobin yabo masu dama, irin su First african Grammy nominated artist, highest dubut on billboard hot hundred for an african artist, the accumulator of more than 7 million views on tiktok, waƙarsa ta CONTROL itace on top 10 biggest song globally on Spotify, haka kuma vedion waƙar tasa ta Control ta samu makallata sama da mutum million 57 a cikin wata ɗaya kacal, idan har nace zan ci gaba da lisaffo nasarorin da wannan waƙa da mawaƙinta suka samu zamu cinye lokacin shirin ba tare da na gama ba, leddies and gentlmen wannan nawaƙi ba kowa ba ne faceeeee. Uchenna Haris Franklin!”
A sanda ya ambato suna gaba ɗaya hole ɗin aka saka tafi, kowa dube-dube yake dan ganin ta inda wannan ɗan baiwa ze fito, da ga seat ɗin gaba ya miƙe yana murmushi.
Sanye yake cikin baƙar suit, haka ya shiga taku har zuwa kan stage ɗin, sai da suka gaisa da wanda ze gabatar masa da award ɗin, sannan ya damƙa masa. A lokacin wurin ya kacame da ƙarar tafin jama'a, ga 'yan jarida da ke akkin ɗaujar hoto.Microphone aka miƙa masa dan yin jawabi.
A sanda Haris ya karb'i microphone ɗin, a lokacin wata ƙwalla me ɗumi ta sauƙo da ga idonsa na b'angaren hagu, Abba ya tuna, yau gashi ana lisaffo sunansa cikin masu nasara, amma baya raye, baya duniyar bare ya ga irin nasarar da ya samu.
A hankali dubansa ya kai kan ahalinsa dake zaune a kusa da kujerar da ya tashi, Rashidat, Zakiyya, Jude, Aja da ya koma yahaya, Hanam, Arya, Masarrat, Salwa, Al-amin, Khalil, Abu Tayyab, da Kamal wanda yazame masa babban aboki ayanzu.
Ji ya yi ya gama samun komai,baya buƙatar komai, gaba ɗayan ahalinsa na tare da shi, a shekaran jiya Rashidat ta yafewa Yahaya, komai ya cika, Abba ne kawai babu.
Hannunsa na dama ya kai ya share ƙwallar,sannan ya kai microphone ɗin bakinsa.
“Ina me matuƙar godiya ga ƙungiyar Grammy, sannan ina me godiya ga SSGF Record leble, da ma ita kanga C.E.O ɗin, wata Falaƙ, ina me godiya ga masoyana na duniya baki ɗaya, zan yi amfani da wannan damar wajen sadaukar da wannan lambar yabo ga matata da ɗana”
Wurin ya ƙara ruɗewa da tafe-tafe harda masu fito, Hanam ce ta miƙe, tare da riƙo hannun Arya dake tafiya kan ƙafafunsa, sanye yake da Baƙar suit irin ta jikin Uchenna, yayin da ita kuma take sanye da wata baƙar doguwar riga ɗinkin Empire.
Uchenna nabinsu da kallo har suka hawo kan stage ɗin, tsugunnawa yayi ya ɗauki Arya a hannunsa, sannan ya riƙo hannun Hanam dake ta jifansa da murmushi.
“Nagode Bannute,kinsauya rayuwata ta inda ban yi zato ba, nagode”.
Hanam ta ci gaba da kallonsa fuskarta ɗauke da murmushi, sai a yanzu ne labarinta ya cika, ƙaddarar ta tazo ƙarshe, ƙaddara da ta mata zab'i mafi kyau arayuwarta.
Abba ya tafi, amma bai tafi ba saida ya bar mata kyawawa abubuwan da zasu ci gaba da faranta mata rai har bayan rayuwarta.
Uchenna ya ƙara kai microphone ɗin saitin bakinsa.
“I love you Hanam, and na sadaukar da wannan Award ɗin da na samu gareki”
Ya ƙarashe yana miƙa mata award ɗin, Hanam naci gana da murmushin da ke fitowa tun daga ƙasan ruhinta ta karb'i award ɗin, sannan ta rungumi Harees daga gefe, masu ɗaukar hoto suka ci gaba da sakar musu shi kamar ba gobe.

*House No.122, B3, Alaro city lekki, Lagos*
*08:00am*
Maryam ta fito daga ironing room, hannunta na dama riƙe da kayan data ɗebo a ciki.
Tris ta ja ta tsaya,sakamakon shigowar Tafida. Yau monday, kuma ɗazu yace mata ya tafi aiki, ke nan dawowa ya yi ?, Eh mana, ya dawo tunda kina ganinsa a gabanki, cewar wata murya a cikin kanta. Kayan hannun nata ta aje a kan sofa, dai-dai da ƙarasowar Tafida cikin falon.
Hannayenta ta ɗaga ta saƙalo su ta wuyansa, tana kallonsa, ya yinda shi kuma ya kewaye waist ɗinta, bayan ya aje ledar da yashigo da ita.
“Mantuwa ka yi ?”
Sai ya girgiza mata kai yana jingina goshinsa akan nata.
“Ba mantuwa na yi ba, kewarki ce ta isheni, sai kuma wasu kayan jarirai da na gani a hanya, shind na siyo”
Sai da ta ɗan ja da kanta baya ta kalleshi, dudu ma muntunsa nawa da fita?, kuma ita tun suka gano cewa tana da ciki ya fara siyan kayan yara, cikin da baima kai wata ɗaya ba.
“Yaya babyn mu?”
Se ta turo baki gaba tana ture shi tare da juya masa baya, Hannuna ta ji ya kewayo cikinta ta gaba yana janta jikinsa, kansa a kafaɗarta.
“Ina san babyn nan!”
Ƙara ture shi ta yi,amma sai ya sake kamata.
“Laifi na yi dan nace ina san ɗana ?”
Sai ta yi dariya. Ya tsira mata ido yana kallonta, zai iya rantsewa kan Maryam itace silar sauyawar rayuwarsa, tun bayan da ta shigo rayuwar tasa komai ya sauya, duk wani hali da yake ciki ya kau.
Farin ciki yake a ko da yaushe, duk da rayuwar ɗan adam ba'a rabata da ƙalubale, amma rayuwarsu ta hau hanya, a koda yaushe yana cikin ibadarsa, istingfari kuwa baya rabo da bakinsa, dan gani yake kamar shekarun da ya shafe a cikin sab'o ya yi su.
Babu wani super natural a jikinsa, shi ne,ai na hin shi. Ga kuma ƙaruwar ɗa da suke shirin samu. Jan Maryam ya kuma yi sannan ya furta.
“I love you”
A hankali, Maryam ta kwantar da kanta a ƙirjinsa.
“I love you too”
A yanzu bata da buƙatar komai, komai nata ya zama dai-dai, bata da wata buƙata se godewa Allah da take, dan zaman lafiya take da mijinta, ga 'yan uwanta da a koda yaushe suke kiranta ko ta kirasu su mata fatan alkairi.
Sosai Tafida ke kula da ita da buƙatunta, baya tsallke koda abu ɗaya da zata buƙata. Barin ma da aka samu cikin nan, hatta da aikin gidan hanata yi yake.
“Zo mu kalli kayan dana siyo”
Ya faɗi yana ɗagota, ta re da jan hannunta ya zaunar a kan kujera, zama ya yi a gefenta yana nuna mata kayan, ita kuwa dariya kawai take masa.
“Kinga wannan kalar zata masa kyau, dan nasan kamata zai iyo, kinsan sanda ina yaro bana jin magana, shi yasa na siyo masa wannan, tana da kauri, koda ana sanyi k8n hanashi fita, tofa ina me tabbatar miki da sai ya fita, idan wannan na jikinsa sanyi ba zai kama mana shi ba”
Dariya Maryan ta ci gaba da yi, tana ɗora hannunta a kan cikin nata.
Bata ankara ba sai jin sauƙar kan Tafida ta yi a kan cinyarta, yana kallin cikin idonta, yayinda itama take raba nata cikin nasa.
“Miriam Nagode da komai, musammanma wannab kyautar”
Ya ƙarashe yana ɗora nasa hannun a kan cikin nata, ita ma nata hannun ta ɗora a kab nasa tana ci gaba da kallonsa.
_“Allah alhamdulillah ” _
Kusan a tare suka

Please Login or Register in order to submit comment