Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

me ma zaice mata ?, yaya zata ɗauki zancen ?, kawai sai ya kalli tsabar idonta ya fafa mata cewar mahaifinta ya rasu?.
Dama haka lamarin Allah yake, a sanda suke ganin kamar wahalhalunsu na rayuwa sun ƙare, a sannan wani yake barin duniya, tafiya irin ta har abada, tafiyar da babu dawowa, tafiyar da kuɗin ka, mulkinka, ƴaƴanka ko ikonka basu isa komai a cikin ta ba. Ayyukanka da kyawawan halayenka sune zasu finsheka.
Allah yasa mu cika da kyau da imani.
*Lagos*
*St. Nicholas Hospital*
*Da 10:15am*
“Khabir ina Tafida ?”
Khabir yaci gaba da kallon Heleen dake tsaye a gabansa, tana masa wannan tamabayar, kansa ya kawar gefe tare da faɗin.
“Sun shiga operation”
Heleen ta gyaɗa kai.
“Ok bari na jira shi”
“Am...He...Heleen, d...dama i...ina....san na fada mi...miki....ne”
Jin yana inda-inda yasa Heleen gyara tsaiwa tana dubansa.
“Menene ?”
Khabir ya haɗiye wani abu sannan yace.
“Dama z...zan faɗa miki c...cewar..dama Tafida ya .....yi au.. ya yi aure”
Kamar yanda aradu ke sauƙa a kan bishiya ko dutse haka Heleen ta ji sauƙar maganar tasa, ta ƙanƙance ido tare da karkatar da kanta gefe tana dubansa, kalaman nasa ɗaya bayan ɗaya suka samu waje suka yi gini a cikin ƙaramar kwakwalwar ta, Tafida yayi aure ?, kalaman suka ƙara rubuta kansu da manyan baƙi a cikin ƙwaƙwalwarta kanta.
Sai ta ware idonta sannan ta tsaida kanta dai-dai, tana murmushi, tare da cije leb'enta na ƙasa.

*Da misalin 05:30pm*
MARYAM POV.
Tafe suke ita da su Zara, yau gaba ɗaya sun zama silent, sun kasa yarda ko ido su haɗa da ita, muguwar kunyarta suke ji kamar me, ita kuma sai jansu take da hira tana nuna musu cewar komai fa ba komai bane, amma sunƙi sakin jikinsu da ita.
Saida suka zo dai-dai block ɗinsa sannan ta tsaya ta kallesu.
“Sai gobe”
Da ƙyar Aisha ta amsa.
“Wai ku me ya same ku ne yau ?, gaba ɗaya kun canja min”
“Haba Maryam, ba dole mu canja miki ba, irin maganganun da muka yi ta yi akan mijinki kuma a gabanki, ai dole ne muji kunyar ki”
Zara ta faɗi cikin sinne kai, Maryam ta yi dariya.
“Wallahi kude kun cika abun dariya, wai kunya ?, to miye a ciki, irinku nawa ne suke irin wannan maganar akan sa, ya kai ayi magana akansa ne, ni ban isa na hana ƴan mata ganinsa ko magana akansa ba....”
Sude basu yarda sun ƙara haɗa ido da ita ba suka mata sallama suka yi gaba.
*** *** ***
Yau babu gajiya sosai a jikinta, dan haka tana shiga gida wanka ta fara yi, sannan ta sauya kaya, tana tsaye a gaban mirror ta ɗauko wannan hair pin ɗin da Fidar Yara ya bata jiya, yace mata na maansa ne, ita ba wani iya gyaran kai ta yi ba, dan haka kawai ta naɗe gashin nata cikin bun, sannan ta saka pin ɗin, me shape ɗin rose flower a gefen bun ɗin, ta ɗaura ɗankwalinta.
Ba ta yi kwalliya ba kamar yanda ta saba, sai kawai ta fito, yau tana hutun sallah dan haka bata ɗau azumi ba, ta shiga kitchen kawai tana shirin dafa abinda zasu ci da daddare.
Wayarta dake maƙale jikin ring light ce ta shiga ruri, dan haka ta dakatar da abinda take ta ɗauki wayar, ganin 'SUNDAR' rubuce a kan screen ɗin yasa ta amsa da murmushi.
“Asslamu Alaikum”
Tayi sallama sanda ta kara wayar a kunnenta.
“Wifey”
Taji ya kira sunanta cikin wata kasallaliyar murya, kamar wanda ya tashi daga bacci, kuma kamar a gajiye yake.
“Ummm”
Ta amsa masa a hankali.
“Kin dawo daga school ?”
“Eh”
“Ya exams ?”
“ Alhamdullilah”
“Me zaki dafa yau da daddare ?”
Maryam ta yi dariya, dama tasan zancen gizo baya wuce na ƙoƙi, zancen abinci zai mata, idan taga yanda yake cin abinci yana bata mamaki sosai.
“Danderun kaza da dambun couscous”
“Yauwwa matar arziƙi, sai me kuma ?”
Ya faɗi hakan da zumuɗi, dan ya tuna sanda ta fara masa danderun kaza, daɗin da abincin ya masa bame faɗuwa ba ne.
“Sai mocktail....”
Ta ɗan dakata sakamakon ƙofa da ta ji ana bugawa.
“Waye ?”
Muryar Tafida ta tambaya daga cikin wayar, dan shima yaji bugun kofar, dan ba a hankali aka buga ƙofar ba, wayar na kare a kaunnen Maryam ta wanke hannunta tana bashi amsa da.
“Ban san ko waye ba, bari naje na duba”
Ta goge hannunta still wayar na kare a kunnenta, kuma shima bai kashe wayar ba.
Maryam ta ɗan ja baya ganin matar dake tsaye a ƙofar gidan, Sanye cikin baƙin leggings, ga wata tank top a jikinta itama baƙa, gashin kanta kalabar attachment ce pink color, ta ɗaureta a tsakiyar kanta, fuskar ta fayau babu kwalliya, sai wani nose ring dake maƙale a tsakiyar hancin nata.
Maryam ta tsorata da irin kallon da matar ke mata, amma sai ta dake, dan zama da Tafida yasa ta rage tsoro, ta kai hannu ta sauƙe wayar dake kare a kunnenta ta riƙe a hannu, kuma har lokacin kiran Tafida na tafiya, bai kashe ba yana sauraron ta.
“Baiwar Allah wacece ke ?”
“Heleen!”
Wani shaftararen yanki na zuciyar Tafida ya yanke ya faɗo ƙasa, kamar yanda ƙasa take shaftarewa a sanda ruwa ya zaizaye ƙasanta. Heleen ?,yaushe ta dawo ?, waye ya faɗa mata cewar ya yi aure ?, dama yasan tasan gidansa, wanna ba abun mamaki bane, matsalar ɗayace yasan cewa Heleen muguwace, zata iya komai domin ta cutar da Maryam.
Ba tare da tunanin komai ba, ya miƙe yana faɗin.
“Hello Miriam!, Daaso ?, Maryam ?, Maryam!”
Amma shiru, baya iya jin komai, saide gashi kiran na tafi, keyn motarsa ya fin cika ya yi waje.
*
“Wa kike nema ?”
“Ke nazo nema.....”
Heleen taƙarashe tana kaiwa Maryam naushi, wanda yasa wayar dake hannunta yin kan sofa, ita kuma ta faɗi a ƙasa, matar ta ƙarasa shigowa cikin gidan, a lokacin da Maryam ta miƙe da gudu ta yi kan stairs, Heleen ta biyo bayanta, ta riga ta yanke cewar bazata bar yarinyar nan da rai ba, tun da har itace zata iya zuwa ta mata shigege a lamura.
Maryam ta shige ɗakinta tare da banko ƙofar, ta saka sakata, tare da fashewa da kuka tana ja da baya, hannu ta kai ta tab'a gefen fuskarta taga jini a hannunta ta ƙara ruɗewa.
Ji ta yi matar na buga ƙofar ɗakin kamar zata b'allata, Maryam ta ƙara curewa a gu guda tana kuka.
“Is better for you to open this door, dan idan har kika bari na buɗeta da kai na, to zamu kwashi ƴan kallo da ke”
Maryam ta ƙara tsurewa, wacece ita ?, me yasa take so ta halakata ?, me ta mata ?, ita da bata tab'a ganinta ba ma.
Tunaninta ya katse a sanda ta ji ƙarar bindiga daga wajen, ta kalli wurin sakatar taga yanda aka harbi wurin, sakatar ta b'alle, kafin ƙofar ta buɗe a hankali, sannan wannan matar mara imani ta bayyana a bayanta, hannunta na dama riƙe da bindiga.

TAFIDA POV.
Ganin ƙofar gidan a buɗe ne yasa shi ƙara razana, a dugun zume ya shigo cikin gidan yana ta bude-dube, ganin jini akan tiles ne ya ƙara har gitsa masa tunani, zuciyarsa ta mara gudu fiye da kima, dubansa ya kai kan wayarta dake yashe a kan sofa.
Kunnensa duka biyu ya motsa, ya jiyo bugun zuciyarta a cikin ɗakinta, amma kuma zuciyar tata a raunane take bugawa, kamar mara kafiya.
A ɗari uku da sittin ya yi saman, ƙofar ɗakin nata ma a buɗe ya ganta dan haka ya kutsa kai, mutuwar tsaye ya yi yana kallonta yashe a ƙasa, hannunta na dama a kan wuyanta, jini na fita daga bakinta da hancinta, numfashinta ma da ƙyar yake fita, ga idanuwanta dake barazanar rufewa, amma tana buɗe su da ƙyar.
Tafida ya ji sauƙar wani abu a kansa kamar ƙaton dutse, kamar da aka saka baƙin ƙyalle aka rufe masa ido haka yake ganin baƙi, ga wani gumi daya shiga tsatsafo masa, ƙafafunsa kuwa kamar da aka mannasu a wajen, nan take ƙwayar idonsa ta rikiɗa zuwa ja dan tsabar tashin hankali, da b'acin rai.
*
Zaune yake a bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da Maryam, gaba ɗaya gaban pink Oxford shirt ɗin dake jikinsa ya b'aci da jini, hannayensa biyu dunƙule a kan bakinsa, jijiyoyin kansa sun fito raɗau-raɗau, ga gashin kansa daya sauƙo masa kan fuska.
Ƙwayar idonsa tana nan a ja bata dawo blue ba. Ba zai iya duba Maryam a halin da yake ciki ba, dan Allah ne kaɗai yasan abinda yake saƙawa da wanda yake kuncewa a ransa.
Shi yasa yana ɗaukota ya kawota st. Nicholas hospital, yanzu haka su Dr. Ola ne a kanta, a ransa yake hasaso irin abinda ze yiwa Heleen, bata san shi bane, shi yasa take masa abinda ta gadama.
A da tana yawan takura masa, ta zo office ɗinsa taje filin cricket ɗinsu, taje gidansa, babu inda yake zuwa da bata bibiyaraa wurin, amma baya kulata, haka zata zo ta ƙaraci haukanta amma fimm!, bazai ce mata ba.
Wato tana ɗaukar shirunsa a matsayin rauni, gani take kamar baisan abinda yake ba, ko da ace Maa da Appa sun tsine masa kafin su mutu babu abi da ze yi da Heleen, karuwa mazinaciya, ƴar daba, me kisa, duk ita kafai, kuma ta yi zaton zai sota a haka ?, ta yiwa kanta ƙarya wallahi......
“Tafida kayi haƙuri pls...”
Muryar khabir ta katse shi, dama shi yake jira, dan haka ya miƙe, bai kalleshi ba, hasalima gefe yake kallo, dan baya so yaga kalar idonsa.
“Heleen ta zo ?”
Khabir ya haɗiye wani abu, jin wata wutar masifa na kamawa a cikin ɗacin muryar tasa.
“Eh tazo, kuma nine na faɗa mata cewar ka yi aure, na faɗa mata hakan ne kawai dan ta rabu da kai, amma ban san cewa zata ci gaba da bibiyarka ban...”
Ya dakata yana kamo hannun Tafida dake shirin barin wajen.
“Ina kuma zaka je ?, ka zaun...”
Ɗif!!, maganar tasa ta ɗauke, ganin yanda Tafidan ke kallonsa, ga yanda ƙwayar idonsa ta koma ja, cikin Khabir ya ɗuri ruwa wata iska ta shiga kai kawo a maƙogwaron sa, ba shiri ya saki hannun Tafidan.
Kuma daga haka Tafida ya juya yaci gaba da tafiya, Khabir yabi bayansa da kallo a razane.
________________
_Inalillahi wa inna ilaihi rajiun, wai me ?, Abba ne ha mutu!?, kai jama'a!_
_Allah sarki Daaso, to Allah ya baki lafiya_
_Nace ba, ran maza fa ya b'aci, akwai kata'i a babin mu na gaba, kude ku tara domin jin yanda zata kaya_.
🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.


⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Na sadaukar da wannan babin zuwa gareki yayata Oum Ahmad*

*BABI NA TALATIN DA UKU (33)*
HANAM POV.
A hankali ta shiga motsa idonta, kafin hasken dake wajen ya shiga idon nata, ƙara meda idon nata ta yi ta rufe, tunanin abinda ya faru har ya kawota asibiti ya dawo mata sabo, Ita de bata san me ya faru ba, kawai Haris yace mata tazo su tafi, shi ne ya ɗauki Arya ita kuma ta bi bayansa.
Gidansu taga ya nufa, kuma tun daga shigarta falon gidan tasan cewa ba lafiya ba, dan taga kowa na gidan yana kuka, kowa ta tambaya lpy ?, sai yaƙi mata magana, Kamal ne kawai ya iya furta mata cewa
_ “Hanam Abba ne ya rasu, ya rasu a hanyarsa ta dawowa Abuja daga Lagos....”_
Suman da ta yi shine ya hanata fahimtar ƙarshen maganara, sai kuma data farfaɗo ba sai yanzu.
Zabura ta yi ta miƙe zaune, tana bin wajen da take da kallo, asibiti ne, tabbas asibitine, bata ma lura da wanda ke zaune a gefen gadonta ba saida ta ji ya riƙo hannunta, ta kai dubanta gareshi, Harees ne, yanayin yanda taga fiskarsa ne kawai ya tabbatar mata da abinda Kamal ya faɗi da gaske ne.
Kanta ta gyaɗa masa alamun da gaske ne?, shima ya ƙara gyaɗa mata nasa kan, ƙris ya rage bata koma ta sume ba, wata ƙilama itama mutuwar za ta yi, Abba ya mutu ?, wai Abba ne ya mutu ?, tunanin ma kansa hargitsa mata lissafi yake, taji iska bata shiga huhunta yanda ya dace, kamar an sakata a cikin kwalba an kulle, babu ta inda iska ke shiga bare ta fita, Mahaifin ta ne fa ya mutu, mahaifin ta da ya zame mata uwa kuma jigon rayuwa.
Sai ta nemi hawaye ma ta rasa, dan da gaske ne abinda aka faɗi, wani tashin hankalin yafi gaban kuka.
“An ƙaraso da gawar tasa, zamu iya tafiya”
Idanuwanta a bushe ta zuro ƙafafunta ƙasa, babu ko takalmi a mafarta, saida Harees ya bata takalmanta ta saka.
*
Yanda taga harabar gidan nasu a cike ne ya ƙara tabbatar mata da abinda aka faɗa mata, kasa shiga cikin gidan ta yi, sai ta tsaya a jikin ƙofar entrance, tana kallon yanda mutane ke ƙara tururuwa a gidan.
Babu yanda uchenna be yi da ita ba kan ta shiga cikin gidan amma ta ƙi, ta kafe makarar da aka aje a compound ɗin gidan da ido.
Kamal ne yazo ya mata magana cikin sanyin murya kamar ba shi ba.
“Hanam, ki shiga cikin gida”
Sai yanzu ta motsa, juyowa da kanta ta yi ta kalleshi, a gaba ɗaya rayuwarta a gidansu, magana irin haka bata tab'a haɗata da Kamal ba, kullum cikin takun saƙa suke, basu tab'a shan inuwa ɗaya ba.
A hankali kammanin fuskarsa ke rikiɗe mata zuwa na Abba, domin dama kaf gidansu babu me kamar Abba sama da shi, komai nasa ya ɗauko, halinsa ne kawai ya kwaso na uwarsa.
Sai yanzu ta ji wata ƙwalla na taruwa mata a ido, kuma a hankali ta sauƙo mata. Ƙafarta ta fara takawa zata shiga cikin gidan, har ta kai ƙofar ta ji ana ƙoƙarin ɗaukar makarar dan fita da ita.
Sai kuma ta juyo da sauri, a dai-dai lokacin wata mota ta shigo cikin gidan, masu makarar suka fita motar kuma ta shigo, Hanam ta ji wani kuka na ƙwace mata, yanzu shikenan zasu rabata da Abba, inde suka ɗauke shi ba zata sake ganinsa ba.
Ta nufi gate da gudu zata bi masu makarar ta dakatar dasu, ta faɗa musu cewa kada su fita mata da Abbanta, su bar mata shi taci gaba da kallonsa, Haris da Kamal ne suka yi kanta zasu ruƙota.
A sannan ne kuma ƙofar wannan motar data shigo gidan ta buɗe, wata farar balarabiya ta fito daga ciki, koda wutsiyar ido zaka kalleta zaka gano kammaninsu da Hanam, fari kawai zata fi Hanam ɗin, sai kuma shekaru, wasu yara ne guda uku suma suka fito daga cikin motar, wanda suma kana ganinsa kaga 'ya'yanta, dan suna kama da ita, mace ɗaya maza biyu.
“Hanam la shu hazal jnan! (Hanam wannan wani irin hauka ne!...)”
Cak Hanam ta tsaya, hankalin mutanen da suka rage a farfajiyar gidan ya dawo kansu, Kamal ya santa dan haka be yi mamakin ganinta ba, Haris ne ya tsaya yana kallonta, dama sauran ƙannen Kamal ɗin maza wanɗa basu san matar ba.
Hanam ta juyo ta kalli inda matar take, tunda ta taso bata tab'a ganinta ba, hotonta kawai ta sani, amma bata tab'a ganinta ido da ido ba, Matar dake amsa sunan mahaifiyarta, mahaifiya ?, mahaifiyar da bata shayar da ita ba, bata kula da ita ba, bata mata tarbiyya ba, bata bata ɗumin uwa ta sani ba, bata zaune da ita har girmanta ba, yau itace tsaye a gabanta tana mata magana cikin iko da isa harma da gadara.
Sai tashin hankalin da take ciki ya rikiɗa ya koma fishi, ta yi kan matar, Haris ya riƙo hannunta, amma ta fisge, hakan yasa ɗankwalin dake kanta ya faɗo, gashin kanta ya barbaje, wani a bayanta wani a kan fuskarta.
“Min inti ?!”
(wacece ke ?!)
Hanam ta tambaya idonta cikin na matar, wannan hawayen da ta fara ya ƙafe, idonta a bushe take dubanta. Cikin ƙarfin hali matar tace.
“Ana immik...”
(Nice mahaifiyar ki).
“Inti manik immi!”
(Ke ba mahaifiyata bace!)
Hanam ta katseta a tsawace, kuma tana ɗaga mata hannu, ta zaro mata ido tareda nuna matar da dan yatsa.
“Inti....manik...immi”
(Ke....ba....mahaifiyata bace)
ta maimaita mata dalla-dalla. Ji kake tas!, matar ta wanke ta da mari, Hanam ta dafe wajen sannan taci gaba da kallonta.
“Ana immik, iza biddik walala, ana hiya immik!”
(Ni babarki ce, ko kina so ko bakya so, nice mahaifiyar ki!)
Bisa ga mamakin kowa sai Hanam ta shiga yin dariya, zuwa lokacin matan gidan da yaransu dama mutanen ƙauye dana gari da suka zo jana'iza sun fito suma
“Akan me zaki mare ta ?!”
Kamal ya faɗi cikin wata iriyar fusata da yake jin tana tasowa tun daga ƙasan ruhinsa, bai tab'a jin tausayin Hanam ba kamar yau, su sunada iyaye mata a kusa da su, ita kuma bata da kowa sai Abba, Abban da ya mutu a halin yanzu.
Hanam ta ƙarashe dariyar ta kai hannu ta ture Kamal daya zo ya tsaya a gabanta, sannan ta kalleshi.
“Yaya, ka bar min wannan faɗan, nawa ne”
A karo na farko data fara kiransa da yaya, amna ya lura sam bata cikin hayyacinta, a lokacin ma Rashidat ta fito daga cikin gidan, hannunta riƙe da Arya yana kuka. Baabaa ce ta sauƙo wurin tana riƙo mata hannu.
“Hanam zo”
Ta fisge hannun bata ko kalli Baabaan ba.
“Baki shayar da ni ba, baki reneni ba, baki bani kulawar da uwa ke bawa ɗa ba, baki min komai da uwa kewa ɗa ba, shine zaki zo rana tsaka kice ke mahaifiyata ce ?”
Tai mata maganar cikin harshen hausa, dan tasan cewa tana jin hausar, sai kuma Hanam din ta fara hawaye, ta kai hannu ta tura gashin kanta baya.
“Me na miki Masarrat ?, me na miki ?, me yasa kika tafi kika bar ni?”
Ta kira sunanta na ainahi, cikin gunjin kuka, kuma tana murza goshinta, ta ja hanci sannan taci gaba.
“Wancan dake cikin makara, shine ya rene ni, ya bani kulawa, yamin duk abubuwan da ya kamata ace ke kika yi. Bayan kinsa ƙafa kin tsallake ni kin tafi, Abba ya bawa Mero ni, yace ta rene ni, Mero tace ai lokacin da kuka zauna tare kullum cikin mata sharri ki ke, dan haka bazata karb'eni ba, Abba yavyi haƙuri da wannan ya kaiwa Hajjo ni, ita kuma tace ita amarya ce, bazata iya renon ɗa ba. Haka Abba ya aje komai a gefe, ya reneni da kansa, kullum da kansa yake bani madarar yara, ya min wanka, ya sauya min kaya, tun ina jaririya har na tasa Abba bai dena reno na ba, na taso cikin gidan 'yan uba, waɗan da basa sona, kullum cikin hantarata kowa yake, tun ban gane hakan ba har nazo na gane, haka zansa Abba a gaba na tambayeshi shin ni bani da Mama?, sai yace min ina da ita mana, tayi tafiya ne, amma ta kusa dawowa, a koda yaushe haka yake cemin, har na taso na yi hankali, na gane cewa tafiya kika yi kika barni sbd san zuciyar ki, kullum kalaman da Mero ke faɗamin kenan akanki. Na kawar da wannan na rungumi Abba a matsayi uwata da ubana, domin bani da kamarsa”
Ta saki kuka me tsuma rai, data tuna cewar Abba fa ya mutu, ba zata sake ganin sa ba, kowa dake wajen saida jikinsa ya yi sanyi, hatta Mero da Hajjo, dan sun tuna lokacin da Abban yazo yana ta musu magiya akansu temaka su karbi yar tasa cikin tsimman goyo, amma kowacce a cikinsu taki, yayunta mata kuma da suka yi aure suka tuna yanda suka yi ta kyarar ta sanda tana ƙarama, hakama Kamal.
Hanam ta share hawayen dayaƙi tsayawa sannan taci gaba.
“Haka na taso cikin tabon rashin uwa, saide kuma hakan ni baya damuna, dan inada Abba. A sanda na samu ɗana sam banyi ƙokarin yada shi ba, duk kuwa da zan iya hakan, amma banyi ba, sbd me ?”
Ta tambaya tana kallon fuskar Masarrat dake ɗauke da damuwa, duk bata san cewa ta yi nadama ba sai yau, Hanam ta nuna kanta.
“Sbd akwai soyyayar uwa a tare da ni, lokacin da zan haihu babu kowa a tare da ni, ba yaya, ƙanwa ko ɗan uwa, ba uwa bare uba, daga ni sai maƙociyata, naci a zaba sanda zan haihu, har ta kai ma ance bazan sake haihuwa ba, bayan na haihu na ɗora ido akan waccan hallitar, naji duk baƙin cikina na duniya ya yaye, naji cewar zan iya kareshi daga duk wani abu na cutarwa a duniya, naji cewa zan zame masa katanga daga duk wani abu mara daɗi. Sannan a lokacin sai na yi tunanin cewa, idan har uwa zata iya jin wannan azabar kafin ta kawo ɗa duniya, to me zaisa ta tafi ta barshi?, wata ƙila ke baki ji irin azabar da naji ba, shi yasa har kika tafi kika barni, zuciyata ce ta faɗa min bakan”
Zuwa yanzu ta dena gunjin kukan, sai hawaye dake mata zuba, ta kafe Masarrat da manyan idanuwanta, tana jiran amsarta, bata tab'a tonawa wani cikinta kamar haka ba, bata taba faɗar ciwonta ba, koda Abba bata tab'a magana irin wanna da shi ba, ko wani ciwonta a cikinta take riƙe shi, bata barin kowa ya sani ciki kuwa harda ƙawayenta.
“Baki da amsa ko ?, na sani ai Masarrat, bazaki samo amsar ba,inti ananniye ya Masarrat, ma biddik yani li'annu ana bintu la Muhammad mu ?”
(kina da san kai Masarrat, bakya sona sbd ni 'yar Muhammad ce ko ?)
Ta girgiza kanta sannan taci gaba.
“Wata ƙila ba haka bane, au li'annu ana Hanam, Hanam yalli inti wulad tiyya, wa rahti wa taraktiya lahala, ma bihimmik amurah, am tattasili fiyya kil sini mu ?”
(ko kuma sbd nice Hanam, nice Hanam ɗin da kika haifa, sannan kika gudu kika barta, ba ki damu da lamuranta ba, kina kiranta duk bayan shekara ɗaya ko ?)
Sai kuma ta yi dariya.
“Inti bi hayatik marah tikun umm ya Masarrat, inti mara wa bas, manik um”
(A rayuwarki ba zaki tab'a zama uwa ba Masarrat, sbd ke macace kawai, ba uwa ba)
“Inti min bit kuni ?, la hatta rah tawa a'if idam umna, wa tikalli ha tabki bi hadolul kalam yalli andik!”
(wayece ke wai ? da har zaki tsaya a gaban Babarmu kina sakata kuka da waɗanan kalamana naki)
Hanam ta tsirawa yaron ido na 'yan wasu sakkani, Ta tab'a ganin hotonsa sau ɗaya akan dpn Masarrat ɗin, kuma ta tab'a faɗa mata cewa shine ɗanta na fari a auren da ta sake.
“Eh ba'arif ina hiyya umuk, wa ana ma andi ayyi haƙ annah, ilit wa rah irja'a id kalami, ya walad ummuk ananniyya, hai mara mabta'arif ma'ana kalmat um...”
(Eh nasan cewa mahaifiyar ka ce, kuma ni bani da wata dangantaka da ita, na faɗa kuma zan maimaita, yaro babarka me san kai ce, wannan matar bata san ma'anar kalmar uwa....)
Maganar ta maƙale a maƙoshinta sbd marin da Haris ya sakar mata, abun ya yi yawa, duk da tarin lefin da ta mata aƙalla ita mahaifiyartace, be kamat ace tana mata irin wannan rashin kunyar ba, ta dafe kuncinta tana meda gashin kanta baya, ta ɗago da idanuwanta ta kalle shi.
Sai kuma ta fashe da kuka ta kifa kanta a ƙirjinsa tana ci gaba da rera kukanta, Uchenna ya rintse idanunsa, Hanam ta nuna Masarrat cikin kuka tace masa.
“Harees ana ma biddi shufa la hai mara (Harees bana san ganin matar nan), kace mata ta tafi, ta tafi, ta tafi?!!...”
sai kuma maganar ta ɗauke dip!, sakamakon jikinta da ya saki, ta ƙara suma, Uchenna ya riƙeta da kyau, sbd kar ta faɗi.
Shi da kansa ya ɗauketa ya sakata a motarsa ,Sannan ya juya ga Masarrat.
“Nahnu asifin ya ammi, hiya galɗane, wa am uɗlub minnik samah, samihiya”
(Muna masu baki haƙuri ammi, ta yi kuskure, kuma ina nema mata yafiyar ki).
Ya ƙarashe hannayensa a haɗe🙏, alamilun roƙo, duk da halin alhinin da kowa ke ciki saida ya yi mamaki ciki kuwa harda Rashidat, domin bata tab'a sanin cewa ɗan nata ya iya larabci ba.
Masarrat ta share hawayenta tana kallonsa, bata tab'a nadamar abinda ta aikata ba sai yau, yau ɗin da 'yar data haifa a cikinta ta tsaya a gabanta tana faɗa mata cewar bata cancanci zama uwa ba, ita bata dace da zama uwa ba, haka tace, amma yanzu kuma ga wani da batama san waye shi ba yana bata haƙuri, harda kiranta da sunan uwa.
“La taƙal'a ya ibni, mani za'alane a badan, samahta”
(Kada ka damu yarona, raina bai b'aci ba, na yafemata).
Sai ya gyaɗa mata kai yana takawa ys soma barin wurin.
“Min bit kun ?”
(waye kai ?)
Ba tare da ya juyo ba ya amsa ta da.
“Ana bi kun zauja (Ni mijinta ne)”
Su Mero da 'ya'yanta sai kukan nadama suke, Hakama Hajjo, duk da ita

Please Login or Register in order to submit comment