Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kira Jabeer ɗin ya sanar masa, Jabeer yazo sukayi magana basu wani ja abun da tsawo ba dan dama tun farko an fara maganar bikin.
Sbd haka suka yanke biki sati biyu, Hanam sam ba haka taso ba, ita bata ƙi a barta daga ita sai Arya da Abba ba, amma babu yanda za ta yi, ko kaɗan bata san Abba ya yi fishi ko ransa ya b'aci, tafi so a kullum ta ga yana farin ciki, inde har auren nata shine farin cikinsa to za ta yi auren.
**
“Wai yanzu mom bari za ki yi tayi auren nan?”
Muryar Kamal ta faɗi, yayinda yake zaune a ɗakin mahaifiyar sa, suna facing juna, Mero ta yi wani murmushi wanda za'a iya kira dana makirci.
“Kamal kenan, ai bazan tab'a bari ta yi auren nan ba, bade Jabeer bane ?, to ita da Jabeer sai a lahira idan ana haɗuwa, amma babu ita babu shi, bazan tab'a bari ta auri Jabeer ba”
Kamal ya bushe da dariya harda buga ƙafa.
“To yanzu miye shirinki ?”
“Kaide ka zuba ido ka gani, Allah ya kaimu ranar ɗaurin aure, ba de ita wannan shashashar taƙi yarda mu haɗa kai ba?, ni ɗaya zan yi abuna na gama”
“Wa kenan ?”
“Hajjo mana, wai ita me tsoron Allah”
ta ƙarashe da kwafa.
“Auren yar lele,bari muga to idan za'ayi”
gaba ɗayansu suka saka dariya.

UCHENNA POV.
Zaune yake a ɗakinsa, guitar yake kaɗawa cikin wani kiɗi me taushi da sanyaya ruhi, waƙar daya rubuta yake rerawa tareda ƙidan.
Waƙa na ɗaya daga cikin mafarkansa na rayuwa, kuma tun yana ƙarami yake so ya yi waƙa, dan haka yake rubuta waƙar yana ajewa, idan ya samu free time kamar haka sai yazauna yana rerawa, wata ƙila ya kore ƙunci damuwa da b'acin rai dake cikin zuciyar sa.
Labarin ɗaura auren Hanam a gobe ya dakeshi, hakan yasa yake cikin duwa, dan har yanzu yana santa, kuma dama bai tab'a dena santa ba, ita kaɗai ya so, kuma ya ƙudircewa ransa ita zai ci gaba da so har zuwa lokacin da zai rasata, wata ƙilla Allah baisa ta kasance tasa ba, wata ƙila ba shi da rabon samunta, wata k......
Wayarsa da ta yi ringing ta dakatar da tunani da kuma kiɗan da ya ke lokaci guda.
Uchenna ya juyo ya kalli wayar tasa dake aje a gefensa 'MOM' shine abinda ya fito b'aro, b'aro akan screen ɗin, ya aje guitar ɗin yana murmushi kafin ya kai hannu ya ɗauki wayar.
“Mom”
Ya kira sunanta, kuma yanajin sautin murmushin ta ta cikin wayar, kafin ta amsa
“Na'am Haris, ya kake?”
“Ina lafiya, and you ?”
“ I am fine also”
“How is zakiyya ?”
“she is fine, she went to school”
Yayi murmushi, yana shafa sumar kansa
“Zaki zo bikin ne?”
“Me zai hana Haris?, mutumin nan ya yi maka komai daya kamata ace mahaifin ka ne yayi maka, ya zama dole nazo na taya shi murnar auren ƴarsa”
Ya gyaɗa kansa kamar tana ganinsa.
“Yaushe za ki zo ?”
“Gobe inshallah, i call to inform you dama”
“Ok mom see you tomorrow”
“Take care of yourself, Allah ya maka albarka”
“Emeen”
Daga haka wayar ta ƙare, ya lumshe idonsa yana jingina da jikin gado, yana azabtuwa, Allah ya sani yana azabtuwa sosai.

MARYAM POV.
Tsaye take a jikin lokarta tana shirya kayan data wanke kuma ta goge yau da rana, dan gobe monday, tun shekaran jiya take cikin damuwa, sam bata jin daɗin ranta, gaba ɗaya lamarin Tafida ya dagula mata lissaffi, tarasa wani mataki zata ɗauka akai, kuma gashi bata san kowa yasan halin da yake ciki, dan wannan sirrinsa ne, da tanemi shawarar Anti Fati......
Wutar da aka ɗauke ce tasa tunaninta yankewa, tunda tazo garin kusan sati biyu amma bata tab'a ganin wutar gidan y ta yi koda fari ba, balle a ɗauke, abun ya bata mamaki, tsoro ya mamayeta ganin duhun da ɗakin yayi.
Allan ya yi ta da wani bala'in tsoro, tana da tsoro sosai musammanma na duhu, tana tsoron duhu shi yasa ma bata kashe wuta idan zata kwanta, yanzu gashi ita ɗayace a ɗakin bazata iya tuna inda ta aje wayarta bama balle taje ta ɗauko.
Taji kamar ana tab'a balcony ɗun ɗakinta, ta zabura ta yi waje, wajen ma babu haske, ko ina yayi duhu a gidan, dan wajejen karfe 10 ma ne na dara.
Maryam taci gaba da takawa tana bin corridor ɗin a tsorace, ji take kamar ta fasa ihu....., sai kuma gashi ta fasa ihun, saka makon karo dataci da abu kamar mutum, hannunta taji an ruƙo, ta kara rudewa tana fasa ihu, sai kuma taji ance
“Ssssshhhhhh!”
Ta ƙzra ruɗewa tana ƙoƙarin ƙwatar hannunta daga ruƙon da aka mata, tsabar ta kiɗime sam bata gane muryarsa ba.
“Ke !!, Miriam nine ”
Inaa, sam bata ta gane yaren da yake, tsoro ya cika mata ciki, tsalle kawai take da ihu tana haɗawa da kiran sunan Allah.
Tafida yaga abun nata bana ƙare bane, shima yana waya da Fulani yaga wutar ta ɗauke shi yasa ya fito dan ya duba meke faruwa, shine yaci karo da ita.
Tafin hannunsa na hagu wanda be riƙeta dashi ba ya buɗe, nan take wuta ta bayyana tana ci, kuma bata tare da ta tab'a tafin hannunsa ba, maryam ta ƙara fasa ihu tana fadin.
“Wayyo Allah wayyo Maanmu, dan Allah karka ƙonani aljani, kayi haƙuri kaji, dan Allah kayi haƙuri, to wai ni me na maka wa ?”
Tafida yana murmushi ta ya ɗago da hannun setin fuskarsa ta yanda zata samu damar ganin fuskarsa, sai kuma tayi shiru ta tsaya da tirje-tirjen da take, yana murmushi har hakwaransa na bayyana yace
“Main hoon na (nine), nine Eshaan, Tafida”
Ya faɗa mata sunayen har guda biyu duk dan ta gane, babu abinda ya bashi dariya sai ganin yanda fuskarta take sharkaf da hawaye.
“Eshaan ne ?” ta tambaya kamar wata sokuwa, yana murmushin dake barazanar komawa dariya ya gyaɗa mata kai
“Eh nine”
har yanzu wutar na setin fuskarsa, yayinda yake riƙe da hannunta ƙaya
“Ki koma ɗakinki ki zauna, zanje na duba wutar”
A kiɗime ta ƙankame shi daga gefe kamar side hug amma duka hayyaneta biyu kewaye daya shi, ita kanta bata san ta yi hakan ba, dan gaba ɗaya ta tsure ta ƙidime, ta shiga girgiza masa kai tana kuka.
“Ni a'a, bazan koma ɗakin ba, tsoro nake ji Eshaan, i am scared, Eshaan....Eshaan”
Dariya tana so ta kifecewa Tafida ya kai hannunsa ya ciro nata daga jikinsa, ya riƙo hannun nata.
“To muje tare”
Ya faɗi yana jan hannunta, a hankali suke taka stairs ɗin, ya riƙe hannunta da hannunsa ɗaya, ɗayan kuma har yanzu wutar na ci, yana haska musu hanya har suka shiga garden ta kofar dake parlo, kasan cewar makunnar wutar gidan gaba daya a garden ɗin take.
Koda ya buɗe wajen sai yaga layin wutar ne ya sauƙa, dan haka ya meda latin, nan take haske ya gauraye ko ina a gidan, Maryam ta sauƙe wata ajiyar zuciya ta kwanciyar hankali.
Bata ankara cewa hannunta na cikin na Tafida ba saida suka shiga parlo, aiko tana ganin haka ta yi saurin zame nata daga cikin nasa, ta kalle shi da idonta da har yanzu akwai sauran ƙwallar data taru mata a ciki.
Sai kuma ta ruga da gudu ta haye sama ta faɗa ɗakinta tare da banko ƙofa. A jikin ƙofa ta jingina tana maida numfashi kamar me asthma, hannunta akan kirjinta, idanuwanta a lumshe, sai yanzu duk abinda ta yi yake dawo mata daki-daki, da ace wani ne ya faɗa mata cewar zata iya riƙe Tafida kamar yanda tayi yau to da kuwa ko qur'ani ne zata dafa akan hakan bazata faru ba.
Hannunta na dama daya rike ta ɗago ta kalla, sai kuma ta yi murmushi sannan ta bar jikin ƙofar tana goge hawayen idonta, sannan ta koma taci gaba da saka kayanta a wardrobe.
Tafida ya bi bayanta da kallo yana murmushi har sanda ta shige dakinta, sannan ya tako zuwa saman shima ya shige dakinsa, gaba ɗaya ta haga bashi dariya yau ɗin nan, ga yanda yaji zuciyarta na bugawa a ɗazun, ya saka shi cikin nishadi.
___________________
_To fa, nima fa ina ganin kamar akwai wani a bayan wannan lamarin kamar yanda Hasana sa Husaina suka faɗi, to koma de waye Allah bayyana mana kai, dan mun gaji da ganin fidar yara 😁 cewar maryam yana shan wahala, ko ba haka ba ?__
_Jama'a Hajiya Mero ta ɗauki zafi, ko me ta tana sa ?_
_To kide biyo ni, Dan juga yanda zata kaya_
_Ina me muku godiya 🙏_
🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.


⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Babin yau naki ne Fatima Abdulƙadeer*

*BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA (21)*

UCHENNA POV.
Tsaye yake daga can nesa da masallacin da ake taron ɗaurin auren Hanam, waya yake da mamarsa tana faɗa masa cewar bazata samu damar zuwa ba, sbd ciwon mijinta ya tashi jiya da daddare.
“To mom ba damuwa, kice ina gaida shi, Allah ya bashi lafiya”
“Ameen, ka bashi hakuri please kace masa inshallah zan zo ko bayan bikin ne”
“To”
“Zan kiraka letter”
Daga haka ya sauƙe wayar yana kallon Abba daya taho wajensa da sauri.
“Abba lafiya?”
“Ina fa lafiya Haris, call this number for me”
“Ok”
Ya faɗi yana karb'ar wayar da Abban ke miƙa masa sam, hankalinsa ba akwance yake ba, ya kira Jabeer amma yaƙi ɗagawa, Uchenna ya saka lambar a wayarsa sannan ya aika mata kira.
“Ta shiga ?”
“Eh ta shiga...”
Baima gama rufe bakinsa ba Abba ya warce wayar, saida ta kusa katsewa sannan aka ɗaga.
“Hello jabeer nine....”
Daga can b'an garen Jabeer ya sauke wayar daga kunnesa ya duba screen ɗin, shide lamba ya gani.
“Dan Allah kar ka kashe”
Ya rintse idonsa, dan da shirin kashewar yake.
“Ina kake Jaber ?”
Murya ciki-ciki jabeer ya amsa da
“Ina gida”
“Me yasa zaka min haka Jabeer ?, kasa na tara mutane amma kaƙi zuwa, haba jabeer”
Cike da rashin kunya Jabeer yace.
“Dallah daka tamin malam, ni bance me yasa kamin haka ba sai kai zaka zo ka wani titsiyeni da maganar banza, Da kake so na aure guntuwar yar ka to Allah ya toni asirin ku kaida ita, ashe karuwanci taje tayi a USA shine har ta dawo maka da jika, To Allah yasa matarka mutuniyar arzikice, ta kirani ta faɗa min komai, Dan haka ni bazan auri guntuwar yarka ba, wadda maza suka gama da ita, kada ka ƙara kirana sai anjima”
Dib!!, kiran ya yanke, duka abinda Jabeer ya faɗi a kunnen Uche, saurin kamo hannun Abba ya yi gani yana shirin faɗuwa.
“Abba ka nutsu, ciwonka kada ka bari ya tashi”
A lokacin Baba da kanin Abba suka ƙaraso wajen suma.
“Kai harisu me yake faruwa wai ?”
“Baba yaron nan yaci amanar mu, yace wai bazai iya auren Hanam ba”
Abba ya faɗi cikin wata iriyar murya dake nuna tsantsar tashin hankalin da yake ciki, tunanika da yawa suna ta yawo a cikin kansa, to yanzu me zaije yace da Hanam, kuma wai tsaya yace matata?, wacece ta kirashi ta kitsa masa ƙarya da gaskiya ?.
Mero, wata murya ta faɗi a cikin kansa. Idanuwansa suka kaɗa sukayi ja, wato Mero duk abinda zai zo ya samu Hanam na farin ciki ita bata so.
Yayi ƙwafa a fili, sannan ya juya ya kalli Uche wanda ke riƙe da shi, sannan ya furta abinda ya zama sanadiyar sauyawar Ƙaddarar mutum uku a lokaci guda. Hanam, Arya, da shi kansa Uchennan.
“Haris, dan Allah inaso ka auri ƙanwarka Hanam”.
second ɗaya.... biyu....uku.

HANAM POV.
Zaune take a ɗakinta ita da ƙawayenta biyu na amana tun na primary, Falaq da Iqra, she can't believe wai yau aurenta ake, abun na bata mamaki.
Sanye take da farin lace ɗinkin doguwar riga kuma kamar kullum fuskarta babu kwalliya, yau sai take jinta a kaɗai ci, dan tun safe Rafi'a ta rabata da Arya.
Hayaniyar mutane a waje da taji ne yasa ta fahimci cewa ƴan ɗaurin aure ne suka dawo, sai taji gabanta ya takarkara ya faɗi, yanzu wai an daura mata aure ?, shikenan yanzu ta zama matar jabeer ?.
Ƙofar ɗakin aka turo Rafi'a ta shigo hannunta riƙe da Arya dake sanye cikin farar shadda wadda su kayi anko shida Abba, Hanam ta kallesu su duka.
“A'a masoyi ina ka shiga ne bamu ganka ba?”
Cewar Iqra tana miƙewa ta ƙarasa inda Rafi'an ke tsaye riƙe da Arya.
“E ba, nima ban ganshi ba”
Cewar falaq, a lokacin kuma Rafi'a tace.
“Anti Hanam kije inji Abba, yana babban parlonsa”
Hanam taji gabanta ya tsananta bugu, kamar wani abu ne da ban ya faru da wanda take tsammani.
*
Ganinsu su uku a parlon yasa gabanta ƙara tsananta bugu, Abbane da Baba da kuma ƙanin Abba wato kawu Audu.
“Zo ki zauna a nan”
Taje ta zauna a kusa da Baba dake wannan batu, tun da ta shigo Abba ke binta da kallo tausayinta na ƙara kama masa zuciya, ta wahala sosai a rayuwarta, kuma yana fatan wannan auren da ya mata ya zama silar samun farin cikinta a rayuwa, yasan abinda yayi daidaine.
Dan yanaganin shine ma abinda da yadace ace ya yi tun-tuni, amma da Allah ya ƙaddara cewar hakance zata kasance gashi ta kasance, kuma yana da tabbacin za ta yi farin ciki a nan gaba.
“Hanam”
Ya kira sunanta, a hankali ta ɗago da kanta ta kalleshi tana amsawa, sai kuma ta ƙara sun kuyar da kan nata ƙasa.
“A yau na ɗauri miki aure da wani ba Jabeer ba, sai a yau na tabbatar da Jabeer sam bai dace da ke ba, ya sakani na tara jama'a shi da wakilansa kawai ake ake jira amma yaƙi zuwa, na kirashi a waya sai yake cemin wai shi ba zai auri sauran ƴata ba, ya faɗi maganganu da yawa, daga karshe yace kada na ƙara kiransa....”
Sai kuma ya yi shiru, Hanam dake jin duniyar ta mata shiru tun a maganarsa ta farko ta ɗago ta kalleshi, idan ba Jabeer aka aura mata ba to waye ?!!.
“Hanam, na aura miki wanda na aura miki ne dan na isa da ke, nasan da cewa ke me biyyayace ga duk abinda nake so, nasan baki tab'a bijire min ba, kuma nasan cewa wannan karon ma bazaki bijire ba....”
Ya kuma yin shiru yana ci gaba da kallon reaction ɗinta, har yanzu bata ce komai ba kallonsa kawai take, ita buƙatarta taji waye ya aura mata.
“Hanam, ba kowa na aura miki ba face UCHENNA!”.

MARYAM POV.
Tafe suke akan titi, ita da sabbin ƙawayenta ne, Aisha da Zara, hira suke ta yi amma Maryam bata saka musu baki ba, dan hira suke akan wani kyakyawa dake a block3.
Tun da Maryam ta fara zuwa makarantar ta lura da ƴan matan ajinsu basu da aiki se hira akan wani kyakyawa, kuma ita jikinta na bata cewa Tafida ne, kuma tunanin nata baije ko ina ba ta tabbatar da hakan lokacin da Zara tace.
“Wai ke Maryam baki sanshi ba ?, a block3 ɗinku yake fa, sunansa Tafida”
Damm!, gaban Maryam ya faɗi, wani abu me kama da kishi nasan taso mata, ji take kamar ta koma Makarantar ta tara duka ƴan matan ajinsu, musulmai da Cristian, turawan da baƙar fatar duka tabisu da mari ɗaya bayan ɗaya, ciki kuwa harda su Zara dake tareda ita....
“Ya za'ayi tace bata san shi ba, ke babu budurwar da bata san shi ba a Alaro city gaba ɗaya”
Maryam ta juya ta kalli Aisha, sai kuma ta kawar da kai taci gaba da kallon hanya.
“Ke nifa wannan gashin kan nasa kawai nake san tab'awa, daga nesama fa har sheƙi yake, gashi jiya dana ganshi naga gashin nasa ya ƙara tsayi”
Cewar Zara, idonta har wani kyallin murna yake.
“Kede bari Zara, wallahi sumar nan tasa tana burgeni, shi tsiyarsa ɗaya, ba ya yiwa ƴan mata magana sai de maza, kuma mazan ma ba sosai yake musu magana ba, ke nifa ina ganinma jinin sarauta ne”
Maryam tayi shiru, sumarsa ?, itama de taga a kwanakin nan ya fara tara suma, wata ƙila so yake ya tara kamar ta wannan hoton, sai tunanin yaso ya bata dariya, taji itama tana san ta tab'a sumar tasa ta ji, ita zata iya hakan, amma su fa?, kawai de suna karanta wasiƙar jaki ne.
“Hmm aisha sai kingan shi yana magana, damn!, i can't wait to sit on that mouth....”
“Sai goben ku”
Maryan ta faɗi tana jara saurin tafiyarta haɗi da shan kwana ta shige block finsu, dan idan ta tsaya ta ci gaba da jin zantukan da suke zuciyarta kan iya bugawa, ko wata ƙilama ta yanke jiki ta faɗi, ko kuma ta make ɗaya daga cikinsu, tafiyar tata itace mafi a'ala.
“Me yake damunta ?”
Aisha ta tambaya girarta a haɗe waje guda tana duban Zara, Zara ta dage kafaɗa alamun bata sani ba tareda faɗin.
“Ni ya za'ayi na sani, wata ƙila bata da lafiya ne”
“wani irin rashin lafiya kuma ?, bayan ƙalau muke tare da ita yanzu”
Zara ta tab'e baki cikin faɗin
“Allah yasa lafiya, kinsan ita Maryam ba san surutu take ba, wata ƙila damunta mukayi”
Daga haka sukaci gaba da tafiyar su suna ci gaba da hirar da suka fara.
Maryam ta tsaya a ƙofar gate ɗin gidansu, sannan ta saka hannunta a cikin jaka ta zaro remote control ɗin da Tafida ya bata domin ta riƙa amfani da shi wajen buɗe gate din gidan.
Ilham ce ta fito daga gidansu hannunta riƙe da leda, tana ƙwala mata kira, Maryam ta tsaya daga buɗe ƙaramar ƙofar da take shirin yi, ta juyo ta kalli ilham ɗin.
“Ina yini Anti Maryam”
Ilham ta gaisheta yayinda ta ƙaraso kusa da ita, Maryam ta ƙaƙalo murmushi tana amsawa, ilham ta miƙa mata ledar hannunta tareda faɗin.
“Wai gashi inji Mamanmu, tace na kawo miki wai mamarta ce ta aiko mata daga kano”
Maryam tasa hannu ta karb'a, a lokacin da itama tata mamar ta faɗo mata a rai.
“To ki ce nagode”
“To”
Ilham ta faɗi bayan ta juya. Maryam ta ƙarasa buɗe ƙofar ta shiga.
A parlo ta aje jakarta ta makaranta, ta shiga kitchen ta aje ledar da Ilham ta bata, sannan ta shiga fito da kayan dake ciki.
Kub'ewa ce da kuka, kanwa, sob'o harda jan lalle, Maryam ta yi murmushi, tana hango yanda za ta yi amfani da kayan, dan dama tana buƙatar irinsu, kuma bata san inda zata samu ba.
Maman Ilham kamar da ta buɗe zuciyarta ta gani, aiko idan an jima za taje tai mata godiya kafa da ƙafa.
Ma'aji tai wa kowanne, sannan ta ɗauki lallen ta fita a ranta take faɗin, yau kuwa tuwo za ta yi, dan dama tayi missing ɗinsa, lalle kuma sai jibi za ta yi, jakarta ta ɗauka a inda ta aje sannan tayi sama.
Ta shiga ɗakinta ta aje jakar a inda ta saba, sannan ta aje lallen a cikin bed side drawer, ta cire hijabin jikinta ta shiga ban ɗaki, bayan fan wani lokaci ta fito, yau azumi take, dan haka ba abinci zata ci ba, koda safema iyaka na Tafida kawai ta girka, yanzun ma bazata tsiri yin tuwan ba sai anjima.
Balcony ɗin corridor ɗin nan ta tafi ta zauna akan lilon dake wajen, tana jin daɗin iskar garin, dan ba'a jima da ɗsukewar yayyafi ba.
Sai kusan shida ta tashi daga wajen, ta nufi kitchen bayan ta dauko wayarta da ring light din naan, ta jona Ring light ɗin, sannan ta saka wayarta a ciki, ta shiga daukan vedio tana recording girkin da take, ita bata iya editin ba, sai idan Tafida ya dawo yake mata sannan tayi posting.

TAFIDA POV.
_🎶You...._
_you got the keys to my heart, my baby never let me down_
_My baby never lets me down, my baby never_
_You...._
_You deserve a crown, my baby never lets me down_
_My baby never lets me down, my baby never_
_Baby you're my dealer, you my energy _
_I will give you my love, i will give you all of me.....🎶_
Sassanyar waƙar my baby, wanda Ayra Star da Bien suka rera ce ke tashi a cikin motar tasa, a kwanakin nan yana cikin nishaɗi sosai, kuma ba sai an tamabayi daliliba, Maryam ce sila.
A da shi kaɗai yake rayuwarsa, yanzu kuma ya samu abokiyar rayuwa, jinsa yake enough, baya buƙatar ƙari, ji yake ya gama samun komai na duniya, bashi da wani wayo lokacin da iyayensa suka rasu suka barshi, ya taso a wajen Fulani, saide sam babu wata shaƙuwa a tsakaninsa da ita, me martaba kuwa yakan kwana uku ma bai saka shi a idonsa ba a lokacin.
Bayan ya gama secondary kuma ya koma india, a can ne ya samu kulawa, soyyaya da ƙaunar ƴan uwa, duk a da ɗinma yakanje indian ziyara, amma zai iya cewa gidansa a india yake, domin farin cikinsa gaba ɗaya yana can.
Tinaninsa ya katse, a sanda ya ƙaraso ƙofar gidansa, gidan da a yanzu ya fi masa haske fiye da da, a duk sanda zai tako ƙafarsa cikin gidan sam baya san fita, yana so yaci gaba da zama da Maryam, koda babu wani kusanci tsakaninsu, sautin bugun zuciyarta ma kaɗai ya isheshi kasancewa cikin farin ciki.
Yasan i yanzu tana kitchen, dan haka yana shiga sama ya yi, ya yi wanka ya sauya kaya zuwa ash hoodie da baƙin chinos trouser, ya sauƙo ƙasa cikin farin ciki da ɗaukin ganinta.
Hannu ya kai ya murɗa handle ɗin ƙofar, tsaye ya ganta a jikin cabinet tana ɗaukan plate.
Tafida ya kasa kunne yana sauraron bugun zuciyar ta, yana jin abinda ya saba ji a kullum idan yana hakan.
A lokacin kuma ta jiyo ta kalli ƙofar dan taji lokacin daya turo ƙofar, tana ganinsa zantukan su Zara suka dawo mata, sai ta yi saurin kawar da kanta taci gaba da abinda take.
“Sannu da zuwa”
Muryarta ta faɗi sanda ya ƙaraso cikin kitchen ɗin.
“Yauwwa”
“Na gama recording”
Ya gyaɗa kansa sannan ya ƙarasa zuwa jikin socket din data jona ring light ɗin ya cire, ya ɗauke ring light ɗin da wayar ya fita.
A kan danning ta jera masa abincin nasa kamar kullum, bayan ta gama, tana kallonsa a parlon yana daddana wayarta, da alama editing ɗin yake.
“Na gama abinci”
Tafida ya jiyo ya kalleta, sai kuma aje wayar akan sofa ya taso ya ƙaraso zuwa danning ɗin, zama yayi akan kujera yana kallonta, ita kuma ta shiga buɗe warmers ɗin tana ƙoƙarin zuba masa abincin, ƙamshin miyar ya daki hancinsa.
“Tuwo kika yi ?”
Muryar sa ta fito a lokacin da yake kallonta, itama ba tare da ta kalleshi ba tana saka tuwan semolina ɗin da tayi a plate tace.
“Eh, da miyar kuka”
“A ina kika samu kuka ?”
“Maman ilham ta aiko min ɗazu”
ya gyada kansa a hankali, rabonsa da tuwo ya manta ko a hadejia baya samu yaci shi.
________________
_wani abu yana konewa a nan😁, shin kunaga Hanam zata amince da auren Uchenna, itafa kallon Cristian take masa har yanzu, amma de ban sani ba ko har yanzu yana ruwa_
_bari de nayi nan, kuyi comment ra'ayin ku pls, ngd sosai_
🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*This one's for you 'Yar Hajiya*

*BABI NA ASHIRIN DA BIYU (22)*

Lokacin da akayi sallar magariba Maryam na zaune a parlo ta aje kayan shan ruwanta a gabanta, tuwan ɗazu ne sai sob'on da ta yi, tana addu'a Tafida ya sauƙo daga sama da alama masallaci zaije, ya tsaya yana kallonta da mamaki.
“Wifey wai azumi kika yi ?”
Maryama ta shafa addu'ar wadda rabinta gaba ɗaya akan samun sauƙin Tafida ne, ta kalleshi, sannan ta gyaɗa masa kai.
“Ban sani ba ai”
Sai kawai ta yi murmushi tana shan sob'on da ta yi
“Zanje masallaci”
“A dawo lafiya”
Ya janyo ƙofar parlon yana faɗin
“Allah ya sa”.
Sanda ya dawo daga masallacin tana zaune a parlon still, dan bayan ta ɗan ci tuwon kaɗan ta tashi taje ta yi sallah, shine ta dawo ta zauna tana duba vedios ɗin data fara ɗorawa a tiktok, dan tafi bashi ƙarfi fiye da inster.
Sannu da zuwa ta masa sannan ta miƙe ta shiga kitchen ta ɗauko masa nasa sob'on, yau tana so taga abinda zai faru, addu'o'i kala-kala da surorin kur'ani ta tofa a cikin ruwan sobon. Yau tana so taga ko hakan zai zama mafitar matsalar da Tafidan ke ciki.
Miƙo masa sob'on ta yi ya karb'a yana sauya Chanel daga MBC Bollywood zuwa channel ɗin da suke haske wasan cricket.
Maryam ta zauna a ranta tana faɗin, sauran maza iskansu na ball ne, amma shi cricket yake so, sai kuma ta tsaya ta meda hankalinta kansa tana so taga yanda abun zai kasance, a ranta kuma fal fatane na Allah yasa shawarar da zuciyarta ta bata ta yi aiki.
A kan idonta ya kai

Please Login or Register in order to submit comment