Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai baka san shi ba, dan haka kada ka ƙara haɗani da wani gunkinka”
Yana ƙarashewa ya janyo hannun Roshni ya figeta zuwa cikin gidan, duka a kan idon Subhu, yanda Roshni ɗin ke kuke ne ya ƙara ɗaga masa hankali.
***
“Gata nan Maa, so take ta jamana abun kunya !”
Imran ya faɗi a sanda ya wurgar da Roshni ƙasa, wadda take ta gursheƙan kuka, Mahaifiyarsu Parvina ta miƙe daga kan kujerar da take ta kamo Roshni ɗin jikinta.
“Me ta yi Yaya ?”
Yayan Roshni ɗin Irfan, wanda yake a matsayin ƙanin Imran ya tambaya.
“Ka tambayeta ta baka amsa, tsabar yarinyar nan bata da mutunci tana so ta zubar mana da kimarmu da ɗan addinin hindu take soyyaya!”
Parvina ta saki Roshni dake gunjin kuka, Roshni ta kalleta tana girgiza mata kai.
“Wai wannan Subhu ɗin?, Guna(Abokinsa na makaranta) yace min babansa ma boka ne a ƙauyen balu thanda, tsafin da yake ne yasa aka koreshi da ga cikin garin, yanzu haka Guna ɗin yace min a cikin wani kogo yake”
Imran ya haɗe hannyensa biyu alamun roƙo.
“Na roƙeki Roshni da kada ki zubar mana da mutunci, ki duba kimar mahaifinmu da ke ƙarƙasbin ƙasa kada ki mana haka”
Roshni ta ja hanci.
“Wallahi Bhai (yaya) zan iya sauya shi, yana sona sosai, idan na ce ya musulunta ze musulunta wallahi”
Imran ya ɗauketa da marin da sai da yasa jini ya fito daga hancinta, shatin yatsunsa suka fito a kumatunta.
“Ke wata iriyar yarinya ce ?, a ina kika bar karatun da ake mana a masallaci ?, baki san cewa Allah baya karb'ar tuban da yake bana gaskiya ba ?, idan har danke zai musulunta to kisani tubansa be karb'u ba, kuma kin tab'a ganin inda ƴan kanhan suka musulunta, a tarihin india kaf akwai wanda ya tab'a faɗa miki cewar akwai musulmi ɗaya ɗan kanhan?!(wato ƙabilar su Subhu ɗin)”.
Roshni ta miƙe tsaye tana share hawaye, Allah yasani cewa tana san Subhu, amma soyyayar da take masa bazata sa ta rabu da ƴan uwanta ba, ƴan uwanta sun gama mata komai a rayuwa, sanda ta taso bata da uba, su suka zame mata uba, a koda yaushe burinsu su faranta mata.
“Roshni, babu ke babu Subhurmanyam da ga yau!”
A karo na farko tun bayan fara maganar Parvina ta sa baki. Roshni ta goge jinin da ya fito daga hancinta, sannan ta yi murmushi.
“Ina san Subhu, amma soyyayar da nake masa bata kai wadda nake muku ba, kunfi shi matsayi a zuciyata, na haƙura da Subhu har abada, ba zan ƙara kula shi ba, ku yafe min”
Ta ƙarashe tana sakin sabon kuka, tare da haɗe hannayenta biyu🙏.
Imran ya share ƴar guntuwar ƙwallar da ta zubo masa sannan ya ja ƙanwar tasa jikinsa ya rungume, Irfan ma ya zo ya kwanta a bayanta, hakama Mahaifiyar tasu da suke kira da Maa.
***
“Roshni!”
Muryar Subhu ta kira sunan Roshni a karo na barktai, amma taƙi kulashi, tun daga bakin gate ɗin makarantar ya hangota amma taƙi ta ko kalleshi.
Se ransa ya raya masa cewar wata ƙila fishi take, se kawai ya dunƙule hannunsa na dama sannan ya buɗe, wasu taurari masu basheƙi suka bayyana, suna tashi a iska tura mata su ya yi setin fuskarta.
Yana ci gaba da binta amma bata ko kalli taurarin ba.
Abun ya bashi tsoro, ba haka suka saba da ita ba, ya saba a duk sanda ze mata magana bata share shi, kuma ko da ta yi fishi da ga zarar ya mata ƴan tsafe-tsafensa da ya koya daga wajen mahaifinsa zata manta da fishin, ama yau ba haka ba ne.
Se kawai ya sha gabanata, Roshni ta dakata tana kallonsa, ji ta yi zuciyarta na shirin karyewa, kamar hawaye za su zubo mata. Gyara zaman mayafin chickankarin da ke kanta ta yi tana kawar da kai.
“Roshin me ya faru ?”
“Subhu stop it......... kada ka ƙara min magana”
Daga haka ta rab'a shi ta ci gaba da tafiya, ƙara biyota ya yi ya sha gabanta.
“Amma me yasa ?, nasan cewa kina so na Roshni....”
“Bana sanka Subhu, bana.........sanka, ka rabu da ni!”
Cikin ƙaraji ta furta maganar har ta ɗauki hankalin waɗan da ke kusa-kusa da su, kamar status haka Subhu ya ƙame, ya na kallon Roshni.
Rab'ashi ta kuma yi ta wuce abunta, Allah ne kaɗai yasan yanda wannan ƙaryar ta tab'a mata zuciya, ita kaɗai tasan abun da take ji, amma tun farko ita ta yaudari kanta da cewar zata canja shi, koma me ya faru da ita, ita ta janyowa kanta, hawaye ta share tana ci gaba da tafiyarta.
A lokacin tana shekarar ƙarshe, kuma har ta gama makarantar Subhu be ƙara kulata ba kamar yanda ta nema, har tama fara mantawa da shi.
Sai dai shi kuma be manta da ita ba, ko da yaushe yana sintiri a unguwarsu.
Har shekaru uku suka shuɗe, amma yana bibiyar ta, a koda yaushe da tunaninta yake kwana yake tashi.
Wata rana yazo unguwarsu da safe zai wuce ta k'ofar gidansu sai ya ga ana decorating gidan, hankalinsa ya tashi a sanda zuciyarsa ta raya masa kode auren Roshni za'ayi?.
Ɗaya da ga cikin masu aikin decorating gidan ne ya fito, Subhu ya dakatar da shi yana tambayarsa.
“Auren wa a ke a gidan nan ?”
Mutumin ya tsaya ya kallashe.
“Ƴar gidance mace, mema sunanta?......... yauwwa Roshni”
Wani ƙaton bom ne ya tashi a zuciyarsa, gangar jikinsa ta shiga rawa, tunaninsa ya ɗauke. Be san sanda ya nufi cikin gidan a fusace ba.
“Roshni!.....Roshni!....Roshni!”
Kawai yake ta faɗi, be ko damu da masu aikin gidan da ke binsa da kallo ba.
“Kai miye kazo kake haɗa mana hayaniya a gida ?”.
Imran ya faɗi a sanda ya fito, bayansa kuma Irfan ne sai mahaifiyar su Parvina.
“Ina Roshni?!”
A hasalle Imran ya ɗauke shi da mari, sannan ya ci kwalarsa ya hankaɗa shi baya.
“Kai waye da zaka zo kana nemanta?, ka fice ka bar mana gida!”
Ran Subhu ya b'aci, ƙwayar idonsa ta rikiɗa zuwa ja, ya miƙe zaune sannan ya ɗa ga hannunsa setin wuyan Imran ya matse, Imran ya dafe wuyan nasa yana jin kamar hannune ya matse shi, Irfan da Maa suka yi kansa suna kiran sunansa sbd azabar da yake ji ko amsawa ma ya kasa.
“Roshni!, ki fito Roshni!....”
Ya ci gaha da kiran Roshni ba tare da ya saki wuyan Imran ba duk da be tab'a shi ba.
Roshni ɗin ce ta fito da ga cikin gidan, sanye take cikin farin chickankari.
Subhu na ganinta ya saki wuyan Imran ya yi gabanta da sauri, Imran ya faɗi ƙasa yana dafe wuya, Parvina da Irfan suka shiga jera masa sannu.
Subhu na kaiwa gaban Roshni ya shiga magana a gaggauce cikin fitar hayyaci.
“Roshni meke faru?!, me...me yasa zaki min...”
Wani Gigittaccen mari da ta ɗauke Subhu ɗin da shi yasa shi yin shiru, wata ƙwalla me ɗumi ce ta silalo da ga idonta, ita gaba ɗaya ma ta manta da labarinsa, ta karb'i sauyin da rayuwa ta zo mata da shi.
A kwanakin nan ta haɗu da wani baƙin fata ɗan ƙasar nigeria da ke zaune a unguwarsu, kuma ya bayyana mata cewar yana santa, sannan itama ta amince da shi, ta damƙa amanar soyyayarta gare shi, ta watsar da wani Subhu. So take ta gina sabuwar rayuwarta da masoyinta Auwal, wanda a yanzu yake daf da zama mijinta.
“Fita mana da ga gida”
Ta faɗi tana nuna masa hanya, da tsantsar mamaki yake kallonta, yayinda hannunsa na dama ke dafe a kan kuncinsa.
“Baka ji ba ne ?, na ce ka fitar mana daga gida”
Ya kasa magana ya kasa motsawa, ita kuma ganin haka yasa ta kama kwalar rigarsa ta ja shi zuwa waje, a bakin ƙofar gate ta hankaɗashi ya faɗi ƙasa. Juyowa ya yi yana kallonta daga zaunen da yake, kuma har lokacin hannunsa dafe da kuncinsa.
“Kada ka ƙara dawowa rayuwata, na manta da kai, kuma kai ma ina fatan zaka manta da ni”
Daga haka ta juya ta koma cikin gidan nasu, ya ci gaba da kallonta har ta ƙulewa ganinsa.
***
A ranar ya koma garinsu wajen mahaifinsa, wanda ya kasance gawurttacen boka a ƙauyen balu thanda dake can yankin telugu.
Mahaifin Subhu ya kasance babban boka ne me yin baƙin tsafi, a sanda tsafinsa ya gawumurta ne shugaban ƙauyen Balu thanda ya koreshi, dan yana zuwa maƙabartar musulmai yana haƙowa kabari ya yi tsafi da gawawwaki.
Bayan an koreshi sai ya koma cikin dajin kurabi, cikin wani kogo ya ci gaba da harkar tsafe-tsafensa. Mahaifiyar Subhu ta mutu sanda yana ƙarami, sbd soyyayar da Manikandan da matar tasa Kundali su ka yi kafin ta mutu yasa shi fasa binne gawarta ya yi tsafe-tsafensa ya mayar da ita fatalwa, ta zauna cikin wata gangar jiki me haske.
Kasan cewar yin karatun Subhu ɗin burin mahaifiyarsa ne yasa Manikandan ya tura shi kudancin india ya fara karatunsa har ya kai matakin jami'a.
*** *** ***
“Sun nuna maka halinsu ko ?”
Subhu ya ɗago da idonsa yana kallon mahaifin nasa.
“So nake na ɗau fansa”
Manikandan dake zaune a kan wani dutse ya miƙe tsaye ya isa gaban ɗan nasa.
“Kai ɗana ne,zan ɗauka maka fansa”
Subhu ya girgiza kansa.
“A'a, zan ɗauka da kaina, so nake naga bayan Roshni da mijin da zata aura”
“Kai Subhu!”
Muryar Kundali ta faɗi a sanda take sauƙowa ƙasa cikin suffar mace amma kuma haske ne kewaye da ita.
“Ban amince ba, ni bana so ka zama boka, so nake ka yi karatu”
“Ba zan koma rayuwar mutanen gari ba, fansa nake son ɗauka, bazan huta ba se ɗau fansata.....”
_________________
_To ka ji!, ai ni dama na sani, to yanzu shi da yace a kai shi nigeria, me yake shirin yi?_
_A harkullum dai ina miƙa godiya gareku_
🌸SAI KASKA CE✍️🌸.



⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*present day*
*House No.122, B3, Alaro city lekki, Lagos*
*BABI NA HAMSIN DA UKU (53)*
*08:50am*
TAFIDA POV.
A hankali hannayensa suka ƙara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Maryam a karo na barkatai.
So yake ya ganta, dan da asuba da ya farka sam be ganta ba, yau tashi ya yi ya ji shi free, ya ji yanayin nasa kamar yanda yake ji sanda ze yi sallah, babu wannan nauyin da ke danne shi, ya ji yana iya controlling kansa, duk wata jijiya dake jikinsa ta ware, yana abu cikin 'yancinsa.
Yanzun ma bata buɗe ƙofar ba, dan haka kawai ya yi amfani a ƙarfinsa ya buɗe ƙofar, sannan be jira komai ba yasa kai.
Maryam na ganinsa ta razana, Allah ya sani tana jin bugun ƙofar tasa,amma bazata iya buɗewa ba, ba zata iya buɗewa ta yarda su haɗa ido ba, dan bayan abun da ya faru jiya ji take bama zata ko iya tsayawa a gabansa ba.
Tunaninta ya dakata a sanda ya tsaya a gabanta, kanta a ƙasa tana shaƙar ƙamshin turarensa.
“Me na yi kuma ?”
Bata amsa shi ba kuma bata kalle shi ba. Yana iya jiyo sautin bugun zuciyarta, sai dai ba sosai ba, bazai ce me yasa ba, ammam baya jin sautin sosai kamar da. Sai de kuma sautin yana fita cike da tsoro, tsoron da sam bai ji shi ba jiya, jiyan da yake kuka yana faɗamata ta rabu da shi.
“Ko jikin naki ne?”
Da sauri ta girgiza masa kai tana ja da baya. Amma se ya saka hannunsa ya fincikota ta dawo jikinsa, Maryam ta rintse idonta tana kawar da kanga gefe.
“Wai menene ?”
Tsoro da kunya sun hanata magana, a jiyan kawai wani shakkarsa da kwarjininsa ne suka ƙara cikata. Fuskarsa ya kai cikin wuyanta sannan yace.
“Dan Allah kice wani abu, idan ba ki yi magana ba bazan sakeki ba”
“Ina kwana”
Ta furta da sauri tana tureshi ganin kamar yana shirin yin nisa, sai ta ga ya yi murmushi.
A lokacin ne fa lura da raunikan dake fuskarsa, wanda tana da tabbacin baƙin ruhin da ya tashi jiya ne ya haddasa masa.
A ruɗe ta ƙarsa gabansa tana dudduba fuskar tasa.
“Me...me yasa be haɗe ba?”
Yana kallonta yace.
“Nima na yi ƙoƙarin haɗe su, amma na gaza”
Kafin ya ƙara tallafo fuskarta, kuma be jira komai ba ya haɗe bakinsa da nata.
Ba shiri Maryam ta ƙanƙame rigarsa ta baya, tana jin kamar wani abu na janta zuwa ƙasa duk da yana riƙe da ita.
Jin yanda harshensa ke motsi acikin bakinta ne yasa ta saka gaba ɗaya ƙarfinta tafice da ga hannunsa.
“Na....n...na gama..a..ab.abinci”
Shima juyawa ya yi yana shafa sumarsa, kafin yace.
“Na makara, sai dai ko idan na dawo”
Sai kuma ya juyo ya dawo inada take, a tsorace Maryam ke kallonsa, ji tayi ya ɗora hannayensa biyu a kan waist ɗinta,sannan ya yi pecking kanta.
“Sena dawo”
Da ƙyar ta iya gyaɗa masa kai, kafin ta kwantar da kanta a ƙirjinsa, hannayenta suka kewayo ta bayansa, shima ya ƙara matseta a jikinsa, ya kuma pecking kanta, ya saketa kafin ya juya ya fita.
Kuma yana fita ta daddafa ta koma kan gado ta zauna, yau bama za ta yi aikin gidan ba, abincin ma dan shi ta yi, dan ita baza ta iya ci ba.
Ga jikinta da ta ji ya ɗauki zafi, ga ciwon da gab'ob'inta ke mata, dan haka kawai se tabja hijabinta ta saka, sannan ta kwanta, ta dukunƙuna a bargo, bata jima ba kuwa bacci ya ɗauketa.

*11:30am*
MARYAM POV.
Fitowarta kenan da ga bayi taga wata guguwa na turniƙe ɗakin, ɗakin ya yi duhu duk da bawai dare ne ba, bata iya ganin komai a ɗakin sai iskar da ta ci gaba da kaɗawa a ɗakin kamar zata ɗauketa.
Hannunta ta kai ta kare idonta tana karonto addu'a a ranta, wani jan haske ya ci gaba da mamaye ɗakin, ga guguwar dake ƙara yawa kamar ana ingizo ta.
Can kuma kamar ɗaukewar wutar nepa, ta ji ɗip!, iskar ta tsaya, a hankali ba ta tare da ta fasa karanto addu'o'in ba ta sauƙe hannunta.
Gabanta ya yi wata mummunar faɗuwa, sbd wani mutum da ta gani a gabanta, gashin kansa ya taru da yawa an ɗaure shi da wasu zarririka, fatar jikinsa ta yi baƙiƙirin alamun dauɗa, ga wasu fararen layuka huɗu da aka ja daga gaban goshinsa, an ɗisa ja a tsakiyarsu.
Babu riga a jikinsa sai wani baƙin yadi da ya faffarke ɗaure a ƙugunsa, ƙafafunsa babu takalmi, ga wata sarƙa ta ƙwarangwal rataye a wuyansa, hannunsa na dama riƙe da wata sanda.
Ba suffarsa bace kawai abun tsoron, hatta da kallon da yake mata ma abun tsoro ne. Bayansa ta kalla inda taga wani wawaken rami a wurin, wanda yake nuna cikin wani kogo.
Waye shi? daga ina ya zo ?, me ya ke buƙata a wurinta?.
“Kin gama yawo Maryam ”
Mamaki ya kama Maryam, sunanta ya kira, kuma maganar cikin harshen turanci ya yi, to amma ba wannan ba, cewa ya yi wai ta gama yawo.......

TAFIDA POV.
Ba zai iya kwatanta yanayin da yake ciki ba yau, rabonsa da jin kansa a yanayi irin wannan tun yana ƙarami, a sanda iyayensa suka rasu.
Jinsa yake cikin nishaɗi, kome ze yi yanayi ne bisa ikon kansa, wannan nauyin dake kansa babu shi, wannan igiyoyin da yake jin suna ɗaure shi sun kunce.
Koma waye ya ganshi yau ya san cewa yana cikin farin ciki. Sai Allah-Allah yake dan lokacin tashi a aiki ya yi, saboda ya koma yaje ya ga abarsan, matarsa, farin cikinsa, jigon rayuwarsa a yanzu. Da wannan tunanin har lokacin tashin ya yi, ya haɗa nasa ya nasa ya kamo hanyar gida.
A kai-a kai yake murmushi har ya kawo Alaro city.
Sai dai me ?, yana zuwa ƙofar shiga gidan nasa ya ji gabansa ya faɗi, baya ce ga dalili ba, amma haka kawai se ya samu kansa da jin tsoron shiga gidan, kamar kada ya shiga, dan abinda ze gani a gidan ze iya cutar da shi.
Sai de zuciyarsa dake cike da ɗaukin ganin Maryam ta bashi ƙwarin guwar shiga cikin gidan, hannunsa ya kai ya buɗe ƙofar shiga falon.
Kamar mara lafiya haka ya shiga taku a cikin gidan, i yanzu yasan tana kitchen, dan haka kai tsaye ya nufi can, ammam babu ita bare me kamarta. Haka ya haɗiye wani abu da ba zai ce menene ba, ya fita ta ƙofar baya ya duba garden, nan ɗin ma bata nan.
Ya hau saman gidan, still nan dinma be ganta ba. Se abun ya soma bashi tsoro, dan da alama ma gidan kamar ba'a gyara shi ba yau, dan haka da gudu ya sauƙo ƙasa ya nifi ɗakinta. Sai dr yana saka ƙafarsa a ɗakin ya shiga jin wata murya a kansa na magana.
_“Idan har kana so ka ceceta dole kazo, kazo!, ka zo!, ka zo nan matsoraci...” _
Kansa ya dafe da duka hannayensa biyu, be san sanda ya durƙushe aƙasa ba. Nan take ƙwayar idonsa ta rikiɗa zuwa ja, wannan fiƙoƙin suka sauƙo masa, ya ɗago da kansa cikin fusata yana kallon balcony, kamar da a kace masa me maganar yana wurin.
“Hmmm, ni ba matsoraci ba ne,zan iya ceto ta, ina kake so nazo, faɗamini inda zan zo”
Har wani huci yake wurin furta hakan, jikinsa na karkarwa.
_“Kurabi forest” _
Wannan muryar ta faɗi a cikin kan nasa.
Tafida ya ɗaga hannunsa sama yadunƙule shi tare da buga ƙasa.
“Gani nan zuwa”
_ “To taho mana skarai”_........

*Kurabi forest, Balu Thanda Village, Telangana state, South india*

MARYAM POV.
Zaune take a cikin wasu ƙaraguna da suka kewayeta, a taƙaice de zata iya kiran wurin da kurkuku. Kuka take a hankali sannan tana karanto addu'a.
Tun bayan da mutumin nan yace ta gama yawo bata sake fahimtar komai ba, bata ma san ina kanta ya shiga ba, kawai ta farka ne taganta kulle cikin ƙarafunan wurin.
A halin da take ciki bata jin akwai wani abu da zata iya, babu abinda take ganin ze iya cetonta se ayar Allah, dan haka ta shiga karantota cikin ranta.
Tun ɗazu take ganin wulƙawar wani haske, daga ta ɗanyi karatu sai ta ga ya wunlga, idan ta yi shiru se ta ga ya tsaya.
Dakatawa ta yi da karatun dan tanasan sanin mene hasken. A hankali a hankali suffar wata mata ke bayyana a gabanta cikin suffar haske, kallo ɗaya zaka mata kasan cewa ba'indiyace, dan hatta kayan jikinta ma sari ne.
Kallon Maryam take da tausayawa, har ta iso jikin ƙarfen da Maryam ke kulle ciki.
Ita bata jin hausa, kuma tana da tabbacin Maryam ɗin ma ba jin telugu take ba, dan baka ta yi amfani da tsafinta ta sauya harashe zuwa hausa.
“Magana nake so na miki, amma wannan abun da kike faɗa ya kasa bari na na tsaya, jin sauƙarsa nake kamar ruwan zafi a jikina”
Maryam ta haɗiye yawu ta kuma haɗiyewa, ance wai na zaune be ga gari ba, kuma wai idan da ranka kasha kallo, yaude duk mugun tsoranta se gata a gaban aljanu, dan wannan ba mutun ba ce.
“Ki yi haƙuri kin ji, na san duk yanda a kayi mijinki na nan zuwa, kuma da yardar abun bauta ƙarfin jikinsa se ya yi nasara a kan mijina da ɗana”
Maryam ta kasa cewa komai kawai tana kallon matar, to me take nufi da mijinta nan nan zuwa ?, Tafida ne zai zo ?, kode ƙarya kawai take mata ?, to ta ina ma zai zo ɗin?, ya san inda take ne ?.
Matar ta buɗe tafukan hannunta, nan take wani kwando ya bayyana, wanda yake cike da kayan marmari, a hankali ta tura shi zuwa cikin ƙarfen da Maryam ta ke ciki, kwandon ya sauƙa a gaban Maryam.
“Sunana Kundali, ni ce babar Subhu, ban sani ba ko zaki iya cin wannan, ban san menene abincin garin ku ba, kuma ina da yaƙinin balalle ke ki iya cin abincin mutanen mu ba”
Subhu?, waye Subhu ɗin?, kovde shine wanda ya kawota nan ?, to wai ma ita a ina take ?, me yasa ma shi Subhu ɗin zai kawota nan?, anya ma kuwa zata iya yarda da wannan matar dake gabanta ?.
“Kinga yarinya, ni uwace, ba zan tab'a iya cutar da ke ba, za ki iya yarda da ni....”
“Mama miye haka ?!”
Muryar Subhu ta faɗi a bayansu cikin harshen telugu, Kundali ta ta shi sama tana faɗin.
“Se a zo a aje yafinyar mutane ba a bata abinci ba, shi yasa na kawo mata”
Be ko kula ta ba, ya nufi inda Maryam take, ƙofar wurin ya buɗe sannan ya shiga, ya damƙo kanta da ko ɗankwali babu ya shiga janta zuwa waje.
Tsabar wani wari da hamami da ke tashi a jikinsa Maryam ta ji kamar za ta yi amai.
Janta yaci gaba da yi har zuwa tsakiyar kogon nasu,sannan ya yasar da ita a wurin, ta faɗi har tana fasa goshinta.
Cikin jin raɗaɗi da azaba ta miƙe zaune hannunta na dama dafe da goshinta, ta shiga ƙarewa kogon kallo, akwai haske sosai a wurin, kuma bawai hasken rana ba ne ko na ƙwan lantarki, hasken kaskon wuta ne da ke maƙale a ko wata kusurwa ta kogon.
“What do you want ?”
Ta tambaya da turanci, dan a ganinta ba hausa yake ji ba ba bare ta masa,turancin ma tana mamakin ya akayi ya iya.
Subhu da ke haɗa wani gari ya juyo ya kalleta.
“Fansa, fansa nake san ɗauka!”
Maryam ta ci gaba da kallonsa tana mamakin ƙazantarsa, dan ko wace gab'a ta jikinsa kukan dauɗa take, ga wasu uban faratu da ya tara, ga gemunsa da ya taru ya cukurkuɗe dan rashin gyara.
“A kan wa zaka ɗauki fansar ?”
“A kan Eshaan dama duk wanda ya rab'i Roshni”
Sunan Eshaan ta ji ya kira, haɗi da suna mahaifiyar Eshaan ɗin, wato Roshni, amma miye haɗinsa da su?.
“Me Eshaan ya maka ?“
Ta tambaya a dake, dan yanzu bata ji akwai wani abu da zata gani ya bata tsoro kuma.
Sai Subhu ya zauna a kan wata kujera, sannan ya kira sunan babansa.
Maryam bama ta lura da akwai wani mutum a kogon ba bayan su, sai ta ga ɗan dattijon ya miƙe hannunsa riƙe da wani kwano ya nufi Subhu ɗin.
“Roshni ta lalata rayuwata, na sota kamar raina,amma da ga bisani sai tace bata sona, ba zata iya rayuwa da ni ba, tace na fita sabgarta, ta yi min korar wulaƙanci, ni kuma raina ya b'aci, dan baka na dawo garinmu wurin babana, ya koya min tsafi na tsawon shekaru bakwai, a lokacin Roshni ta yi aure harda ɗa. Ni kuma a lokacin zuciyata banda tafarfasar ɗaukar fansa babu abinda take, dan haka na shirya kasheta ita da mijin nata dama ɗan nata.....”
Se ya yi shiru yana watsa wannan farin garin a cikin wutar gabansa, Maryam data fara fahimtar inda labarin ya dosa ta ƙure shi da ido.
“A lokacin tacje garin su mijinta, suna tafiya ita da shi a cikin mota, ina da ga nan na aika baƙaƙen aljannu suka kifar da motar tasu, har suka mutu, mutuwa irin wadda babu wanda zai ma iya gane kamaninsu. Game da ɗanta kuma na so na halaka shi shi ma, amma kuma Babana ya sanarmin da cewa ba zan iya kasheshi ba. Dan haka na ya ke shawarar lalata rayuwarsa, na yanke shawarar bashi mutuwa ba tare da an binne shi ba, na yanke shawarar saka shi a halin da kowa nasa zai guje shi....”
Ya kuma yin shiru yana watsa wani jan gari yanzu kuma. Sannan yaci gaba.
“Kinsan shekaru nawa na ɗauka kafin na aiwatar da hakan ?”
Maryam da take jin kamar ta tashi ta shaƙe masa wuya ta ci gaba da kallonsa ba tare da ko tari ba ta masa ba, ashe dama duk tsawon shekarun nan shi ne yake azabtar mata da miji ?, shi ne yake aikata duk abinda yake damun mijinta ?.
“Shekara ɗaya na ɗauka ina aiki a kansa, na yanko maƙogwaron zaki, na ciro zuciyar kura, na haɗo da haƙwaran damisa, na shekara ina haɗe su gu ɗaya dan su bani abinda nake so, kafin na samu suka zama baƙin ruhi, kin san menene sunan tsafin ?, baƙin tsafin Diggam, na saka laƙanin a jikin wani baƙin aljani, sannan na binne sauran a cikin wancan ramin....”
Maryam ta kalli ramin da yake nuna nata.
“Wannan baƙin aljanin da na saka masa wannan laƙanin na tura shi jikin Eshaan ɗan gidan masoyiyata ta da...”
Sai ya yi murmushi.
“Na mayar da shi wata hallitar da ban, na banbanta shi da jinsin mutane, na nisanta shi da zama cikin 'yan uwansa. Bayan wasu satika kuma se 'yan uwansa suka fara masa magani, baƙin ruhin da na tura jikinsa ya fara rauni...”
Yanzu kam dariya ya yi yana ɗaga kansa sama. Har yanzu Maryam kallonsa take, mamaki take shin dama akwai ɗan adam irin wannan ?, bata tab'a ji ba ko a mafarki, ko a labarai bata tab'a jin ƙiyyaya irin wannan ba.
“Ni kuma da na tashi se na tura wani

Please Login or Register in order to submit comment