Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakinsa ya yi sipping na farko, tanaga sanda ƙwayar idonsa ta kawo wani hasken ja, kamar an haska cocila, sai kuma ta ɗauke lokaci guda, Maryam ta fara murna ganin kamar abun yana aiki, shi sam baima ji a jikinsa ba.
A dai-dai lokacin da ruwan sob'on ya sauka a cikin Tafida, a dai-dai lokacin ne cikin Maryam ya wani irin murɗa, wanda hakan yasa ta saki wata ƙarar azaba.
“Ahhhhhhhh!”
Ta kai ƙasa hannunta akan cikinta, ji take kamar ana tsitsinka mata hanji ne, kamar zata amayo da kayan cikinta, azabar da take ji ta wuce misali. Da sauri Tafida ya aje glass cup ɗin hannunsa ya yi inda take durƙushe, ya riƙota.
“Me ya faru ?”
Bata iya amsa shi ba, sbd yanda cikin nata ya ƙara murɗawa fiye da da, tuni idanunta ya kawo ruwa, azabar da take ji yanzu tafi gaban kwatance, bazata iya cewa ga yanda take ji ba sbd yanda cikin nata ke mata, Tafida ya riƘota da kyau ya dawo da ita jikinsa yana faɗin.
“Miriam!, Miriam!, look at me!”
Da ƙyar ta iya ɗaga jajayen idanuwanta ta kalleshi, nan take ya gano abinda ke faruwa, ba a kanta hakan ya fara faruwa ba, ya faru akan Daadi, Neha, Fulani, Mairama harda Me Martaba ma.
“Kin saka wani abu a cikin sob'on ?”
Maryama ta riƙe gaban rigarsa gam, sai gumi take duk da sanyin gari dana acn dake parlon, jikinta sai rawa yake, ji take kamar za'a zare mata ruhinta ne, har wani fis-fisga take.
Da ƙyar ta iya gyaɗa masa kai, ya girgiza kansa cike da tausayawa, ba sai ta faɗa masa ba, yasan inda ke mata ciwo tun da abun shansa ya yi ba shafawa ko shaƙa ba, dan haka ya ɗora hannunsa akan cikinta, ya lumshe idanunsa, sannan ya buɗe Maryam tana ganin yanda ƙwayar idonsa ta yi ja kamar last time.
Sai kuma ta kalli hannunsa dake kan cikinta, wani haske wajen da ya ɗora hannun nasa yake, kuma a hankali a hankali ciwon ke raguwa, ya sani yau shine zai azabtu tunda har ya janye ciwon, kuma ya yarda da gwara ya azabtu da ace yana ganinta ita tana azabtuwa garin ƙoƙarin cetonsa.
Kamar an zare mata ƙaya haka Maryam taji ciwon ya ɗauke, kamar kuma ɗaukewar wutar nepa, sai sauƙe ajiyar zuciya take tunda Maanmu ta kawota duniya batajin ta tab'a cin karo da azaba makamanciyar wannan.
Har yanzu a cikin jikin Tafida take, a hankali ta ɗaga kanta ta kalli fuskarsa, shima ita yake kallo, jikinsa ya ƙara janta sosai ya rungumeta, Maryam taji wani abu na yawo akanta, kamar tana shawagi a sararin samaniya, taji kamar tana a cikin garden ɗin gidan, iskar wajen me daɗi tana shiga hancinta, tajita a wata duniya da ban.
“Miriam why ?, me yasa kika yi hakan ?....”
Muryarsa ta fito cike da damuwa.
“Ni haka nake wifey, you better leave me, na faɗa miki koda guba aka saka min a abu to ba ya cina, saide ya koma jikin wanda ya min abun, haka asiri da addu'a , Fulani ta gwada, Daadi ta gwada, Neha ma ta yi, haka Me Martaba, duk wanda yayi ƙoƙarin bani addu'a to shi zai gamu da ciwo, idan sha na yi, to mutum zeyi ciwon ciki, idan kuma shaƙa na yi wanda ya bani zeyi ciwon kai, idan kuma na shafawa ne a duk inda na shafa a jikina nan ne ze yi ciwo a jikin mutum, wifey ciwo na gaske bana wasa ba, bana so ko wa ya azabtu, bana so wani abu ya sameki a sanadiyya ta Miriam”
Sai kuma ya saketa yana kallonta, har yanzu a galab'aice take, dan ga idanuwanta nan kamar zasu lumshe
“Stay away from me Miriam, i am monster Miriam!”.
*Da misalin karfe 11:00pm*
Maryam ce kwance akan gadonta, gaba ɗaya tunanin abinda ya faru ɗazu ya hanata bacci, akai-akai take kai hannu tana share hawayen dake zubo mata, yanzu ita bata san me ya kamata tai masa ba, yana buƙatar temako, to amma yaya zatayi ?.....
Wani irin gurnani taji yana fitowa daga ɗakin dake maƙotanta, a firgice ta miƙe zaune,.
Can kuma sai taji ihu, taji abubuwa na fashewa, sai kuma ƙarar Eshaan, daga inda take taji yanda ya bugu da kasa.
Ta rintse idanunta wasu sabbin hawaye na zubo mata, haka bige-bige da Shure shuren yaci gaba, ga gurnani da take ji kamar na zaki.
Gani tayi zaman nata ba zai iyu ba, dan haka ta miƙe taje ta ɗauto alwala ta shiga miƙawa Allah kukan ta, dan tasan shi kaɗai ne zai masa magani.

UCHENNA POV.
_ .“Allah ya tsine maka Uche”. _
_ .”Yesu baze tab'a saka maka albarka ba”._
_ .“Na tsine maka uchenna”. _
A hankali ya kai hannu ya shafa sumar kansa, yayinda kalaman mahaifinsa wanda yake furta masa su a mabanbanta lokuta ke dawo masa cikin tunaninsa.
Zaune yake a cikin motarsa ya jingina da kujera, motar na parker ne a compound ɗin gidansa, ƙofar motar ta inda yake a buɗe take, yayinda iskar da ke kaɗawa take shigowa cikin motar, a lokacin ƙarfe tara saura, kansa ya ɗaga sama yana kallon saman motar tasa.
“Kace bazan tab'ayin albarka ba Baba, gashi nanyi, kace bazan tab'a samun abinda nake so ba, gashi na samu, kace min ni tsinanne ne, Abba kuma kullum cikin sakamin albarka yake, kana gani ko ?, kana ganin yanda nake ci gaba a rayuwata, abba gaba ɗaya abubuwan daka faɗa basu faru ba, wanda Allah yasa ƘADDARA TA SO a kaina sune ke faruwa”
Sai kuma ya ƙarashe da murmushi, miƙewa zaune ya yi yana kallon ƙofar entrance ɗin gidan nasa, wai yanzu Hanam ce ciki, Hanam ce a cikin gidan, kuma a matsayinta na matarsa, me yafi wannan daɗi ?, saide kuma duk da haka yana cikin shakkun yanda zata karb'eshi, bai sani ba, wata ƙila tace bata sansa, ya saketa ta koma gidansu, sai kuma yaji gabansa ya faɗi.
Ya fito daga motar da sauri, ƙofar motar ya rufe sannan ya shiga cikin gidan, babu kowa a parlo dan haka yayi sama, ƙofar ɗaya daga cikin ɗakunan gidan yaga a buɗe kuma yaga ƙwan ɗakin a kunne, hakan ke nuna masa cewar tana ciki.
Ta maza ya yi ya dake, ya shiga taku har zuwa ƙofar ɗakin, a bakin ƙofa ya tsaya yana kallonta, duk da ba fuskarta yake kallo ba, dan ta bashi baya.
Wata baƙar tank top ce a jikinta, sai farin cuffed trouser, gashin kanta paker a bayanta, ƙafarta sanye da crocs farare.
Kayan Arya data taho dashi take shiryawa a cikin wata chest drawer, Gaba ɗaya ta fawwala Allah lamuranta, dan abinda ya faru ɗazu ya bata mamaki, taya Abba zai aura mata Cristian, kuma bama haka ba wai har su Baba goyon bayansa suke, wannan wata iriyar rayuwace?, dan anaso ta yi aure ai ba sai an aura mata Cristian ba, ko jabeer yaƙi aurenta sai ta nemo wani da ban.
A ɗazun bata iya cewa komai ba sai tashi da tayi ta fice daga parlon, kanta na juyawa, ga wani duhu daya mamaye kafofin ganinta.
Kamar yanda abba ya faɗi, ita bazata tab'a bijire masa ba, tundade aurenta da Cristian yake so to za ta yi haƙuri ta zauna da shi, amma babu wani abu da zai shiga tsakaninsu, ita matarsa ce shi mijinta ne, kuma suna rayuwa a gida ɗaya, shikenan, bayan hakan kuma bata jin akwai ƙarin wani abu.
Motsin takun dataji a bayanta yasa ta waiga, Uche ta gani yana nufar inda Arya yake zaune yana wasa, taci gaba da binsa da kallo har ya ɗauki Arya ɗin, da ace wani zai faɗa mata cewar za ta iya auren Uche, da ta ƙaryata shi, koda a mafarki bata tab'a kawo hakan ba.
Itafa sam bata tab'a san Uche koda da second ɗaya ba, tana ganinsa a matsayin wani mutum da ban ne, bashi ma da matsayi a wajenta ko kaɗan, kawai ta ɗauki aurensa ne a matsayin YADDA KADDARA TA SO.
“Sannu da zuwa”
“Yauwwa”
Ta amsa masa tana juyawa taci gaba da jera kayan dake hannunta, bayan haka bata ƙara cewa komai da shi ba, har ya gama yi wa Arya wasa bata ko kalleshi ba, shi dan kansa ya aje Aryaan ɗin sannan ya kama hanya zai fita.
“Zanci gaba da aikina, fatan Abba ya faɗa maka”
Ya tsaya cak, sannan ya jiyo ya kalleta, wasu kayan take jerawa a wani basket, ko kaɗan ba shi take kallo ba, amma yasan maganar tasa ce.
“Babu matsala, zaki iya ci gaba”
Yana kaiwa nan ya ƙarasa ficewa. Ƙasa ya sauƙa ya dudduba gidan kamar wani baƙonsa, yana dubawa yaga irin kayan da ya kamata ace ya ƙaro a gidan.

MARYAM POV.
Zaune take a parlo tana jiran fitowar Tafida dan yazo su fita, yau da safe ta ganshi sanda ya fito cin abinci, tana ganinsa tausayinsa ya ƙara kamata dan har ya rame a iyaka jiya kawai, Allah ne kaɗai yasan abinda yake ji a jikinsa.
Takunsa da taji yasa ta ɗaga kanta sama ta kalleshi, sanye yake da wani yadin voil milk color, sai wata baƙar hula a kansa, da baƙaƙen takalma, hannunsa riƙe da wayarsa daya, ɗayan hannun kuma riƙe da key.
Ta miƙe tsaye tana ɗaukar wayarta da jakarta.
“Kin shirya ?”
Ta gyaɗa masa kai idonta a kansa, da hannu ya mata alama da suje, shi yayi gaba ita tabi bayansa, wani yanka taga a bayansa setin wuyansa, hakan yasa ta zaro ido tare da tsayawa da tafiyar da take, a kiɗime ta ƙira sunansa.
“E...Esh...Eshaan”
Shima ɗin ya tsaya da tafiyar da yake, karo na biyu kenan da ta tab'a kiran sunansa, na farko ranar da wuta ta ɗauke a gidan, sai kuma yau, ta iya kiran sunansa kamar ita ta raɗa masa shi, ya juyo yana kallonta with his blue eyes.
“Rauni a wuyanka....”
Gaba ɗaya ta gama tsorata, itafa bata san damuwa, dan raunin yana da girma ga faɗi, kamar da aka saka wuka aka yanka, idonsa ya lumshe, bayan ɗan wani lokaci ya buɗe, sai kuma ya juyo mata bayan nasa.
“Ya haɗe ?”
Ya tambaya ba wai dan bai san ya haɗe ɗin ba, dan de kawai ta gani hankalin ta ya kwanta, dan baya son damuwarta ko kaɗan, baima san da raunin ba shi yasa ya barshi har ta gani, Allah yasa lokacin da yaji shi baƙin ruhin daya shiga jikinsa jiya na nan, dan haka zai iya hadewa.
*
A kai a kai take sharan hawaye, dan gaba ɗaya ta rasa abinyi, bazata iya zama ta zuba ido irin haka na faruwa da shi tana gani ba, she needs to do something.
Tafida dake driving ta juyo ya kalleta, a dai-dai lokacin da yayi parking a inda ya saba sauƙeta idan ya kawota makaranta.
Ya juyo da kyau yana fuskantar ta, hannunsa ya kai ya kamo nata, Maryam ta zabura sbd yanda yatsunsa suka nade nata cikin bazata, bai tab'a riƙe hannunta ba, shi yasa bata tab'a jin abu makamancin wanda take ji a yanzu ba. Tafida ya shiga murza yastunsa akan nata yana kallon ta.
“Miriam look at me”
Da ƙyar Maryam ta iya ɗauke idonta akan hannunta ta fora akansa, sai kuma ta kawar da nata idon, dan nasa sun mata tsauri da yawa, kwarjininsa ba zai bari ta ci gaba da kallonsa haka ba.
“Miriam na faɗa miki tun farko, i am monster, so me yasa kike damun kanki, tun tasowata ni a haka nake, haka na taso naga rayuwata, ban tab'a jin daɗin rayuwata na second ɗaya ba, komai baya min daɗi, sbd inayinsa ne yanda aljanin dake jikina ya sa ni, ba dan raɗin kaina ba, Wifey akwai wahala a rayuwata, i don't wanna hurt you Miriam, i want keep you safe....”
Itade bata ce masa komai ba, har yanzu kallon hanunsa take wanda ke kan nata, kuma kalamansa ɗaya bayan ɗaya iska ke ɗurasu a kunnenta, ta ji kuma ta gane.
“Mirian i am sorry, ban so kika shigo cikin wannan rayuwar da nake ba, da ace an bar ni ni ɗaya da komai sai tafi sauƙi, amma an sakoki ciki kum......”
Kanta da yaga tana girgizawa yasa shi yin shiru, kafin ta ƙarfafi zuciyarta ta ɗago da kanta ta kalleshi.
“Kada ka tab'a tunanin cewa kana cutar da ni, dai-dai dana second ɗaya baka tab' cutar dani ba Sultan (king), you now become my other half, Eshaan, Maryam Tijjani Muhammad can never ever live without you, you become part of my story, you are my savior, my hero, i can even call you my lifeline....”
kuma tana kaiwa karshe ta janye hannunta daga nasa ta ɗauki jakarta ta buɗe ƙofar zata fita, ya yi sauri ya riƙo hannunta.
Kalamanta ne ke yayo a kwanyarsa, har yanzu bai kai ga fahimtarsu ba, yana buƙatar sharhi, wata ƙilama sai ya zauna yavyi nazarin word by word kafin ya fahimta.
Maryam ta saka masa kansa a tukunya, hannunta daya riƙo ya saka mata kuɗin daya saba bata kullum idan ya sauketa a matsayin kuɗin kashewa a makaranta, sannan a hankali ya janye hannunsa itama kuma bata jira komai ba ta fita daga motar.
Kuma ba ta yi nisa da tafiya ba ta hangi su Zara na shigowa, Allah ya temaka basu ganta ta fito daga motar Tafida ba.
Yana tsaye a wajen har ta ƙulewa ganinsa, hular kansa ya cire ya shafa sumarsa data fara taruwa sosai, sannan ya meda hular, ya kasa kama tunanin ɗaya ƙwaƙƙwar wanda ya kamata ace ya yi nazari akai, hular ya mayar kansa sannan ya tada motar yayi reverse ya bar wajen.
_Tir kashi, to nifa wannan abun ya fara kulle min kai, anya kuwa mutum ne yakewa fidar yara wannan abun ?, nide bazance komai ba, aa to_
_Su Uchenna ango, zan zo cin kazar amarya, fatan de za a ajemin tawa_
_Ina miƙowa godoyata sinƙi-sinƙi, Allah ya bar ƙauna masoyan asali🙏_
🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Wannan naki ne Fatima Ahmad Isah*

*BABI NA ASHIRIN DA UKU (23)*
HANAM POV.
Dawowarta kenan daga wajen aiki, tun daga parlon gidan ta fara ganin sauye-sauye, duk da gidan bawai dama bashi da kya bane, yanada kyau kuma sosai, dan ko gidansu saide ya faɗa masa girma ba kyau ba.
Tsarin gidanjen estate ɗin na da kyau sosai, ɗakin data zab'awa Arya ta fara buɗewa da zummar shiga. tris ta tsaya tana kallon yanda aka sauya komai na ɗakin.
Ga uban tarin kayan wasa da aka cika ɗakin dasu, baby cot, baby cradle, da manya-manyan teddies.
Duk yawan kayan wasan sa na ɗakin na da bai kai wannan yawa ba, baki sake ta ƙarasa shiga cikin ɗakin, kafin ta sauƙe Arya daga cikin baby carrier ɗinsa, ta aje baby carrier ɗin, sannan ta ɗauka masa wasu teddies guda biyu.
Kafin ta fita daga ɗakin, ɗakin data zab'awa kanta ta shiga, taga shima an sassauya wasu abubuwan a ciki, ta aje Aryaan ɗin akan gado sannan ta bashi teddies ɗin data ɗebo, ta shiga ban ɗaki ta fito bayan ta ɗaura alwala.
Sallah ta yi sannan ta fita zuwa ƙasa dan ganin abinda zata iya samawa kanta, kitchen ɗin ma da ta shiga taga sauyi sosai, dan yau maƙil yake da kaya.
A ranta tana jinjina ƙoƙari irin na Uchenna, girki ta samu ta ɗanyi me sauƙi sannan ta zauna ta ci.
Sai wajen Bayan magariba Uchenna ya dawo, a lokacin suna zaune a parlo ita da Arya shi yana wasan sa ita kuma tana aiki a laptop, sau ɗaya ta ɗaga kai ta kalleshi tai mishi sannu da zuwa, bayan haka bata ƙara ce dashi komai ba.
Shima kuma bai matsa akan sai an masa maganar ba, dan haka ya yi sama abinsa.
“Nagode, naga kaya”
Sai ya tsaya da tafiyar, kafin kuma yaci gaba yana faɗin.
“Don't mention it”
Da sauri Hanam ta ɗago da kanta ta kalli bayansa, wannan muryar, tabbas ta san muryar itace muryar wannan wanda ya temaketa a hannun ɗan daba nan, kenan shine ?, to ai dama ba taga fuskarsa ba a lokacin. Dan haka zai iya kasancewa shi ɗin ne.
*R120, TRANSCORP HILTON HOTEL, ABUJA*
*Da misalin 12:30am*
Wata baƙar budurwa ta fito daga banɗaki, sanye cikin wando leggings baƙi, sai wata baƙar half vase wadda bata ko rifi cibiyarta ba, ta kawo baƙar leather jacket ta ɗora akan half vase ɗin, gashin kanta kuma kitsan kalbar pink ɗin attachment ne, ya sauƙo har kasan mazaunanta.Hanyar ƙofar fita ta yi za ta fita daga wajen.
“HELEEN ina kuma zakije baki bani kuɗina ba?”
Wani matashi dake kwance a kan gadon dake fakin duƙunƙune cikin bargo ya faɗi, a hankali ta juyo ta kalleshi tana gyara tsaiwarta.
“Kuɗi zan baka ko ?”
“Eh mana, ai ke kika kirani kika ce nazo idan mun gama komai zaki biyani”
Ta bushe da wata mahaukaciyar dariya, sannan ta saka hannunta a bayanta ta ciro bingida ƙirar pistol, tunda yaga haka ya tsorata gaba ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake, setashi ta yi da bindigar sannan tace.
“Ga kuɗinka nan zan baka, a sauƙa lafiya..."
Ta ƙarashe tare da sakin kunamar bindigar, kasan cewar akwai salansa sai ƙaran harbin bai fito ba. Meda bindigar ta yi bayanta ta sofare, tana leƙa fuskarsa.
“Au ya sheƙa, an gode Allah matsala ta kau”
Wani makeken sun glasses ta maƙala a idonta, sannan ta buɗe ƙofar ta fita, yaranta biyu suna tsaye a waje suna jiranta, suna ganinta suka matso kusa da ita tun kafin ta musu magana.
“Na aika shi lahira, kuji da securities”
“To oga”
Tana gama basu umarnin ta yi gaba.
*
Zaune take a cikin motarta ƙirar Lamborghini, glass ɗin da ta saka ɗazu ta sauƙo da shi kan hancinta, tana zaune a wajen aka zo aka wuce da gawar yaron da ta kashe ɗazu, taja wani uban tsaki.
“Shi ji yake ya burgeni, yau ni har akwai wani wanda zai burgeni kamar masoyina TAFIDA”
Sai kuma ta yi murmushi tana jingina da jikin kujera.
“Ina kewarka masoyi”
Sai kuma ta zabura ta zauna da kyau, wayarta ta ɗauko ta aikawa ogan kungiyarsu kira, yana ɗagawa ta fara magana cike da gadara, kamar itace ogar bashi ba.
“Na gaji da Abuja, zan dawo lagos”
Daga can bangaren scorpion ya girgiza kai, ya rasa yaushe har ya yi sake fan kada ya girma, ya tuna shekaru bakwai da suka wuce, lokacin da HELEEN tazo gareshi a garin lagos.
Tana uar ƙauyenta fitik, lokacin ko bihim bata sani ba, tace masa wai wanine ya mata fyaɗe kuma ta samu ciki iyayenta suka koreta daga gida, tana so ta samu ƙarfi ta yanda zata rama wulaƙancin da aka mata.
Kuma ya tausaya mata lokacin, dan haka ya yarda ta zauna a dabar tasu, a kowani aiki ita yake ɗorawa har tazo ta shahara a daba, yanzu kuma sam ma bata jin maganarsa yanda taso haka take abunta.
“Tunda kin riga kin yanke hakan kuma miye na wani kirana, ai wannan sanar dani kike ba izini kike nema ba”
Ta sosa kanta kaɗan
“To zan ɗora laku akan aikin, zan dawo jibi, kewar masoyina nake, ina san na ganshi”
Bai ce mata komai ba ya kashe wayar. Ta koma ta ƙara jingina da jikin kujerar tana murmushi domin tinawa da sahibul ƙalbinta da ta yi, ta lumshe ido tana tuno ranar da ta fara ganinsa.
Ranar faɗa sukayi da wata daba, har aka harbeta a hannu, shine su laku suka kaita st. Nicholas hospital.
A nan ta fara ganinsa, domin shine ya ke kula da ita a asibitin.
“ I am coming for you my ESHAAN”.
*
“Kasan Allah sai ka siya mata”
cewar Khabir yana kallon Tafida, yayinda suke tsaye a cikin Admiralty mall lagos, dawowarsu kenan daga asibiti, yau motar Khabir ɗin tana wajen gyara shi yasa Tafidan ya ɗauko shi.
Kuma suna hanya yace su tsaya yau Valentine's day yana so ya siyawa matarsa kyautar da zai bata, da suka shiga ciki ne yace Tafida ma sai ya siya.
“Wai dole ne ?, ai ba dole bane!”
“Dole ne mana, dan Allah ka siya mata, wallahi za taji daɗi”
Ya karkatar da kai gefe yana kallon baskert ɗin da ake ce masa ya siya, sai kuma ya dawo da kansa dai-dai sannan ya gyaɗa shi a hankali.
“Nagode nawan, ni zan biya kuɗin ma”.
Kuma daga haka ya ɗaukar musu basket biyu, sannan suka fita bayan Khabir ɗin ya biya.
Saida Tafida ya kaishi garejin da ya kai motar tasa gyara sannan ya tafi gida, dan an gyarawa Khabir din motar tasa. Ya tarar da go slow a hanya, hakan ya haddasa masa makara wajen dawowa gida.
Tunda ya sako motarsa cikin Alaro city, ya tsinci kansa cikin irin yanayin daya saba, duka damuwa da gajiyar daya baro wajen aiki dasu ya nemesu ya rasa.
Da haka ya isa cikin gidan nasa, parking ya yi sannan ya buɗe motar ya fito, ya zagayo gidan baya ya buɗe, ya tsaya yana kallon basket ɗin dake aje a wajen, kamar me nazarinsa, sai kuma ya kai hannu ya ɗauko shi, yaji shi da nauyi, dan haka sai yasaka karfinsa.
Ƙofar parlon ya tura sannan ya shiga abinda idonsa ya fara gane masa shine, Maryam ta taka kan coffee table ɗin dake tsakiyar parlon tana aikin goge saman tv stand, ba wannan ne yasa yake kallonta ba, yau babu hijabi a jikinta, tun ranar da suka zo garin lagos bai ƙara ganinta da hijabi ba sai yau, wata baƙar dolman dress ce a jikinta rigar bata sauƙar mata har ƙasa ba iya karta singalinta, sai farar hula a kanta,bil haƙƙi da gaskiya take aikinta, da alama ma bata san ya shigo ba.
Ear piece ne a kunnenta, tana sauraren littafin Fulani wanda abokiyar hira ta karanata, ko kaɗan bata gajiya da sauraron littafin, bayan ta gama girkin darenta ne taga har lokacin dawowar Eshaan bai dawo ba.
Dan haka ta dawo parlo ta zauna tana kallo, tana jiran lokacin shan ruwa ya yi dan yau azumi take
Sai taga kamar saman Tv stand ɗin ya yi ƙura, sai ta shiga store ta ɗauko wata duster da take goge-goge da ita a gidan, taje ta tsaya a wajen zata goge, bisa ga mamakinta sai taga tsayinta bai kai ba, dan haka ta sauke vase ɗin dake kan coffee table ɗin parlon ta janyoshi zuwa wajen, kasan cewar ba glass bane shine ta taka shi take goge wajen.
“Miriam!”
Ya kira sunanta da ɗan ƙarfi, ganin bata ji ƙiran da ya mata da farko ba, Razana ta yi wadda ta haddasa mata zamewa daga kan coffee table ɗin, ta riga ta gama saddaƙarwa cewa ta faɗo kasa, wata ƙilama ƙashin bayanta ya karye, ko kuma ta gurɗe, gabanta banda matsanincin bugu ba abinda yake, kamar zuciyarta zata fito fili dan tsoro.
Saide kuma abinda take zaton bai faruba, jinta kamar tana yawo a iska yasa ta buɗe idonta a hankali kamar me tsoron ganin wani abu, sai ta ganta ita ba a ƙasa ba ita ba a sama ba.
Ta kai dubanta bakin ƙofa, taga Tafida ya ɗaga hannayensa duka biyu a saitin inda take, hakan ke nuna mata cewar shine ya riƙeta, kuma har yanzu abinda take ji a kunnenta na playing, hannu ta kai ta cire air piece ɗin.
A lokacin kuma tafeedah ya ƙaraso dai-dai inda take, kuma har yanzu hannayen nasa na a setin inda take, yana ƙsrasawa kusa da ita beyi wani tunanin ba ya riƙota dukanta.
Maryam ta riƙe gaban rigarsa gam, sbd abinda take ji akanta, a riƙe take a hannunsa amma ji take kamar zata faɗi, kamar bai riƙeta dai-dai ba, tana ji kamar gravity ne ke janta zuwa ƙasa, itafa bazata iya jurewa wannan kusancin nasu ba, kusan ta yi yawa.
A hankali Tafida ya sauƙe ta kan ƙafafunta, hannunsa kan waist ɗinta, ita kuma hannunta duka biyu akan gaban rigarsa, a dai-dai inda ya ɗora hannunsa yake jin abu kamar beads haka.
Sai ya yi saurin janye hannun nasa itama kuma Maryam ta ɗauke nata hannun daga jikinsa.
“Are you okay ?”
“hmmm”
Ta amsa a hankali, hannunta ɗaya ya kamo ya jata ya zaunar akan kujera, shima ya zauna a gefenta yana kallonta.
Tunani yake yanda za tayi idan ya faɗa mata abinda ke ransa, yana da tabbacin bazata so hakan ba.
Kawar da ko wani tunani ya yi, ya kai hannunsa setin inda ƙaton basket ɗin nan yake, basket ɗin ya taso ya sauƙa gabansa, yakai hannu ya ɗauka.
Sai kuma ya kafa inda-inda, yama rasa me zaice mata, to wai yace mata me ?, shifa ko a da ba budurwa gareshi ba, sau ɗaya ya tab'a yin budurwa, lokacin yana india, kuma bayan ita bai kuma ba.
Itama ɗin rai ta b'ata masa har baƙin ruhinsa ya shiga jikinsa taga abinda yake, tun daga ranar ta guje shi.
Ganin yanda

Please Login or Register in order to submit comment