Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tarin kayan abinci akan coffee table, wanda yake da tabbacin nasa ne, yayi murmushi yana juya kai kafin a hankali ya ƙaraso cikin parlon saida ya shiga ya zauna, sannan ya lura da ashe bai rufe kofar ba, dan haka yayi nuniga kofar ya motsa hannunsa nan take kofar ta rufe kanta tareda motsawar hannun nasa.
A lokacin ne kuma ta shigo cikin parlon, bakinta ɗauke da sallama, ya ɗaga kai ya kalleta yana mata murmushin me tsada, wanda ba a ko yaushe yake irinsa ba, dan har hakwaransa na bayyana, itama murmushin take har ta ƙaraso ta zauna a kujera kusa dashi, cike da girmamawa ya gaishe ta, sannan suka ɗan ta6a hira kaɗan, dan ita izzar mulki ta mayar da ita muskila, shi kuma jinin mulki dake yawo a jikinsa yasa baya zantuka barkatai, abici ta fara gabatar masa sannan ta tashi ta bashi waje yaci abinci.
Fulani khadija kenan, matar sarkin hadejia alh Abdullahi abubakar masu (c.o.n) shugaban hukumar sarakunan jahar jigawa, itace matarsa ta farko,bayan ita yanada wasu matan har guda biyu, fulani sadiya itace me bi mata sai kuma fulani usaibatu, fulani khadija sau ɗaya ta ta6a haihuwa, itama kuma bayan sun shafe shekaru samada ashirin ita da me martaba da aure, tukunna ta samu, inda ta haifi ƴarta mace me suna Nadra.
Ita kuma fulani sadiya yaranta huɗu a gidan, habibu shine na farko, kuma shine babba a cikin ƴaƴan me martaba, wanda yake riƙe da sarautar galadima a yanzu, hakan tasa ake kiransa da sunan, ko kuma ace yarima, sai maimun wadda tayi aure suna zaune da mijinta a buja, sai amina da za'ayi aurenta yanzu, sai autansu nabil wanda ya kasance karamine bai wuce 10 yrs ba.
Fulani usaibatu kuwa yaranta biyu, abbas da kuma amra, suke nan iyalan gidan me martaba alh Abdullahi abubakar masu (c.o.n).
Abincin ya buɗe ya ɗan ɗiba kaɗan domin baya jin yunwa, idan kuma yace bazai ci ba fulani bazataji daɗi ba.
Nadra ce tayi sallama tana shigowa cikin parlon, wani uban tsalle ta saki haɗi da ihu yayinda tayi arba da Tafida zaune a parlo yanacin abinci.
Bata san da Labarin zuwan sa ba, yanzu haka tana garden ne taji wasu bayi suna hirar wai Tafida yazo, shine tace bari tazo ta ganewa idonta, kansa tayi da gudu ta rungumeshi, ya aje plate ɗin dake hannunsa shima ya riƙeta yana murmushi me kama da dariya
“hamma yaushe ka zo ?”
ta faɗi tana sakinsa tareda zama a gefensa
“jiya na zo”
Tayi dariya, inda sabo ta saba da wannan halin na Tafida, ya iya mannawa mutum magana, idanta ne sauƙa akan ƴar hadejian dake kwance a gefen fuskarsa, kusa da kunnensa gefen sajensa, ƴar hadejia tsago ukune sirara da haifaffun haidejia kanyi a gefen fuskarsu, kusa da sajensu wajejen kunnensu, hakan tasa aka sanya mata 'yar hadejia
“laa hamma kalli 'yar hadejan ka, ta kusa bacewa, dama nice, allah ba karamin cutar mutane suke ba da suke musu wannaan ƴar hadejan”
Tafida ya kai abincin bakinsa yana murmushi, kowani ɗa dake fadar inhar ya haɗa jini da fadar walau mace ko na miji to sai ka sameshi da wannan zane, kuma bama fada kawai ba har mutanen gari.
Hannunsa ya kai ya tura sumar kansa baya, bawai dan ta sauko masa kan goshi bane, saide dan hakan ta zama ɗabi'arsa a duk lokacin da kansa yake babu hula.
“to ko zamuyi changing face ?”
“aa hamma rabani, ni da irin fuskarka ai duka samarin hadejia dawowa zasuyi suce suna sona, kamar yanda kaima kaf ƴan matan hadejia ke sanka”
maganar tata ta bashi dariya, amma kawai sai yayi murmushi
“au haba ?, ni ɗin suke so kuma ?”
“eh mana, akwai wata class mate ɗina ma datake yawan damuna da zancenka, tace Tafida kaza, Tafida kaza, har cewa ta yi idan tazo bikin nan dan Allah na haɗaku ku gaisa, nace mata kanajin hausa ta ƙaryata ni, wai aikai indian ne taya zaka iya hausa”
“kaimin jakata bangarena pls, i am tired of wannan surutan naki”
Nadra ta miƙe tana jan jakar tasa dan ta sani yayan nata baya san surutu dayawa, hakama mumzzy, gashi kuma ita allah yayita da magana.
🌸-SAI KASKA CE-🌸
⭐YADDA ƘADDARA TASO⭐
⭐شاء القدر⭐
©By Sai Kaska
My wattpad page @Sai_Kaska
*proud of my first novel*
*BABI NA HUDU(4)*
Da misalin ƙarfe goma na dare, fulani khadija na zaune a ɗakinta tana karatu, taji wata iriyar razannaniyar ƙara, wadda ko tantama batayi daga ɗakin Tafida ta fito, a ruɗe ta aje littafin hisnul-muslim ɗim da take karantawa, ta fito da sauri.
A hanya taci karo da Nadra, wadda ko tantama batayi itama jin ƙarar ne yasa ta fito, basu cewa juna komai ba, suka ɗunguma zuwa ɗakin nasa dake can nesa da nasu.
Nadra ce ta murɗa handle ɗin kofar kuma har lokacin sunajin gurnanin da yake, da sauri taja kofar ta rufe tana fashewa da kuka, ko fulani bata tambaya ba tasan me tagani, wannan abun ya saba faruwa dashi a wasu lokutan, amma kuma sam bayayin irin wannan abun.
Matsar da ita tayi daga Jikin kofar ta kama kofar ta buɗe, ta ganshi yana murƙususuwa a kasan ɗakin, kwayar idonsa ta koma ja, dogayen fiƙoƙin nan sun fito masa, gaba ɗaya ya hargitsa ɗakin, gurnani yake da fisge-fisge, nan take kwalla ta ciko idonta, tausayin ɗan nata na ƙara rufeta, shi kuma haka ƘADDARA TA SO ya kasance, a yanzu babu temakon da zata iya bashi, domin tana kusantarsa zai iya halakata, dan wannan ba shi bane, shaiɗanin ruhin nan ne, kuma da zarar ya shigeshi, baya gane ɗan uwa, aboki, ƙawa, uwa, uba ko masoyi.
A baya ta ta6a kokarin kusantarsa lokacin da yake cikin irin wannan halin, abinda ya mata har yau bata manta ba, dan saida ya buga mata kai da bango, kuma har yanzu akwai raunin a goshinta.
A duk lokacin da abun ya tashi rikiɗewa yake ya koma dodo, kofar ta janyo hawaye na mata zuba, addu'a ta shiga masa dan ita kaɗaice abun da zata iya masa a yanzu, jiki a sabule ta koma parlo, yayinda Nadra ke biye da ita, suka zauna sukayi jigum-jigum, banda kuka babu abinda Nadra take, duk da ba yau ta saba ganinsa cikin irin wannan halin ba.
Fulani kuwa hawaye kawai take gogewa, gashi yau ba itace keda turaka ba. Dolene ma gobe ta nemi ɗan masani, lokaci yayi da zai faɗa mata yarinyar data dace, ya kamata a kawo karshen wannan abun, ta gaji, bazata iya zama tana ganin ɗan nata cikin wannan halin ba.
MARYAM POV.
Yau islamiyya ta tafi, domin ta ɗan kwana biyu bataje ba, Kuma tun bayan da tayi sauƙa ma ba sosai take zuwa ba, yau ta samu space hakan yasa tace bari taje makarantar.
Kuma bayan sun taso ne tana tafe a hanya ita ɗaya, kamar kullum sanye cikin dogon hijabi, sai taga sanata a gabanta yana mata murmushi.
“hajiya Maryam, barka da yamma”
Ta ɗan kawar da kai gefe sannan tace “yauwwa barka”
Ta amsa ba yabo babu fallasa
“Maryam kinƙi ki bani dama, kullum cikin bayyana miki sirrin zuciyata nake amma kinƙi ki gane, wallahi maryan ina sanki, ki yarda dani”
Ta ɗan juyo ta kalleshi “amma sanata kasande bai kamata ace ka tsareni a titi kana min magana ba ko ?”
Sai ya shiga sosa ƙeya “to kiyi haƙuri zanzo gida na sameki”
Tafiyarta taci gaba dayi, ta barshi tsaye a nan, yana binta da kallo, shide nan duniya baiga wadda yake soba kamar Maryam, komai nata ya masa, nutsuwa, kamala, ilimi, haƙuri ga kuma kirki, ta haɗa komai da namiji yake buƙata a mace.
Tana zuwa gida ta aje jakar islamiyyar a ɗaki tareda hijabin ta fito tsakar gida, maanmu tana ban ɗaki, muhsin ne kawai zaune a tsakar gidan nasu data sha shara ƙaƙal, kamar ka suɗe, yana wasa, ta zauna kusa dashi tana kakka6e kurar dataga a kansa, yayinda shi yake ci gaba da wasan nasa.
“auta me yasa bakaje islamiyya ba yau ?”
“malam shawwal ne yake duka na”
ya bata amsa ba tareda ya bar wasa da motar gorar da hussain ya haɗa masa ba.
“kuma yanzu auta dan malam shawwal na dukanka sai ka dena zuwa?, haƙuri zakayi ka ci gaba da zuwa kaji ?”
“to dukana yake yaya”
“ka de daure kaji ?, ko baka san shiga aljanna ?”
Ta faɗi tana ɗago da kansa ya fuskance ta
“ina so mana”
“da kyau yaran kirki, to sai ka daure ka riƙa xuwa kaji?“ ya gyaɗa mata kai, a lokacin ne kuma maanmu ta fito daga banɗakin.
“maanmu wai su hussain basu kawo komai ba yau?”
“aa sun kawo shinkafa, kuɗin kayan miyane dai babu, amma ai akwai mai da yaji sai muci haka”
Maryam ta miƙe tana faɗin “ina shinkafar take ?, sai na dafa kinga magariba na ƙoƙarin yi”
“duba ɗakina tana kan loka, kuma nayi magana da kawu yace zai turo miki ta account”
Maryam ta shiga ɗakin maanmu tana faɗin
“to a tayani godiya”
Hussain ne yayi sallama, sannan hassan, maanmu tana zama kusa da muhsin ta ɗaga kai ta kallesu tana amsa sallamar, karasowa sukayi suma suka zauna akan tabarmar, hassan ya miƙawa maanmu ledar dake hannunsa yana faɗin
“maanmu gashi kayan miyar ne aka samu, harda nama”
a lokacin ne kuma Maryam ta fito daga ɗakin hannunta riƙe da ledar shinkafar data ɗauko.
“nama?”
muhsin ya faɗi yana washe baki, hassan ya ranƙwanshwshi a ka
“eh nama kuma bazakaci ba”
Ya fashe da kukan shagwaba yana shura ƙafa, maanmu ta janyoshi jikinta
“kasan allah hussain zan sabar maka, ka fita idona akan auta, tam”
ya juya kai yana dariya, hassan ya miƙe ya nufi inda Maryam take
“hassan inji dai ba bashi kuka ci ba”
Maanmu ta faɗi tana duban hassan ɗin, bayan ta buɗe ledar, tsayawa yayi sannan ya jiyo ya fuskanceta
“aa ba bashi muka ci ba, wani mukayiwa gyaran mota kuma bai biya ba sai yau”
“to allah yayi albarka”
Duka suka amsa da ameen, hassan ya ƙarasa wajen Maryam
“wayarki zaki aramin yaya”
“me zakayi da ita?” ta tambaya ba tareda ta dubeshi ba, tana wanke shinkafar data cire a ledar
“kede dan allah ki aramin, abu zanyi”
Ya faɗi yana ƙara ƙasa da murya, ta ɗago ta kalleshi “ammafa ka sauya min screen gard, dan ya faffashe”
“har cover zan sauya miki, kede ki bani”
“yaushe zaka dawo min da ita ?”
“gobe da safe”
“shikenan, dan allah ka biya ta wajen alos ka turomin littafin Sanadin caca, kuma kace masa wanda pinkish lady ta karanta nake so”
“to”
Ta miƙe ta shiga ɗaki ta fito sannan ta miƙa masa wayar.
HANAM POV.
Zaune take a office ɗinta, tana zane a ipad ɗinta, Secretary ɗinta ta shigo bayan ta nemi izini, ta aje ipad ɗin tana kallonta
“madam an gama haɗa rigar ”
“ok muje na gani”
Ta faɗi tana mikewa, haɗi da gyara botton ɗin suit ɗin jikinta, secretary ɗin ta juya zata fita har suka kusan cin karo da me shigow, ta bashi haƙuri sannan ta fice, hanam ta tsaya tana kallonsa, ya ƙaraso har gabanta ta harɗe hannayenta tana ci gababda kallonsa.
“magana nake san muyi”
“Babu abinda ya rage da zamuyi magana akai jabeer”
“a'a hanam, akwai ya kaamata ki saurareni“
“faɗi ina jinka”
ta faɗi tana gyara tsaiwarta
“ya kamata mu zauna tukunna”
“nop, ka faɗi abinda zaka faɗa anan, inkuma ka manta abinda kazo faɗine zanje nayi aikin dake gabana”
“ Dan allah hanam ki saurareni, a da mun shirya yanda zamu rayu tare, muntsara duk yanda zamuyi rayuwarmu ta aure, amma cikin shekaru biyu komai ya sauya, kika watsar dani, dan allah hanam ki dawo ainahinki, hanam ɗin dana sani a baya”
“ka gama ?, ni zanje nayi aikina” tayi maganar tana duba digital watch ɗin dake hannunta, bai haƙura ba yaci gaba.
“hanam dan Allah ki tuna, munyi alƙawarin zamu rayu tare, zamu haifi yara mu tsufa tare, komai zamuyi tare, zamu haɗa gidanmu, daga ni sai ke sai kuma ƴaƴan da zamu haifa....”
Bata ko tsaya ta ƙarasa jin bayanen nasa ba, ta rabashi ta wuce, ta buɗe kofar ta fita tana faɗin.
“idan ka gama zaka iya fitowa daga office ɗin”
Jabeer ya sandare a wajen tsabar mamaki, hanam ta gama shayar dashi ruwan mamaki, ya rasa gane kanta, ya rasa abinda yake damunta.
Saida taje ta gama na zarin sabuwar rigar da ɗaya daga cikin designer ɗin fashion house ɗin nata ya ɗinka, sannan ta nuna inda bai mata ba da inda take so a gyaggyara, sannan ta fito daga inda akaware domin yin ɗinki kawai a fashion house ɗin.
Ta kamo hanyar dawowa office ɗin, kukan aryaan taji daga cikin ɗakin data ware domin kula dashi, wanda a da ya kasance office ɗin wani ma'aikaci, kofar ta buɗe ta shiga, kuma tun kafin ta buɗe ɗin taga karima naani ɗin nasa ɗauke dashi tana jijjigashi, kasan cewar wajen glasa ne
“me ya faru ?”
Ta tambaya tana karasawa ciki “kuka yake tayi, nayi tunanin yunwace shine na bashi custard amma yaƙi karba”
Karima ta koro bayanin yayinda hanam ke karbarsa daga hannun kariman
“bari na shayar dashi”
Karima ta risina tana kwashe kayan wasan daya barbaza, ita kuma hanam ɗin ta zauna akan armchair ɗin dake wajen, tareda saka mishi mama a bakinsa, ya karba ya fara tsotsa, a lokaci guda yana wasa da perndat ɗin sarkar dake wuyanta, ta kai hannu ta cire hular sanyin dake kansa me kunnuwan teddy bear, ta shiga shafa gashin kansa wannda yake baƙi siɗik, kuma me taushi, sai kuma ta dawo da hannunta ta riƙe dogon hancinsa irin nata sak tana faɗin
“zaka sani duk ranar dana maka yaye”
Sai taga yayi murmushi, still kuma maman na bakinshi, kamar wani wanda yasan me take cewa, itama sai ta masa murmushin.
TAFIDA POV.
Kirari da kuma maganganun hadimai yayinda suke gaisar da me martabane ya ankarar da fulani cewa mai marta ne ya shigo bangaren nata domin su gaisa, dan hakan al'adarsa ce duk safiya yakanbi ɗakunan matansa su gaisa, kasan cewar suna falo na biyu ne yasa ta iya jin maganganun nasu, kafin kuma kofar ta buɗe, a lokacin da hayaniyar ta ragu, wanda hakan ke nuna mata cewar hadiman sun fita falo na farko, mai martaba ya shigo cikin shigarsa ta alfarma, tris yaja ya tsaya yana kallonsa ɗaya bayan ɗaya.
Ga abinci tile a gabansu su duka amma sam basu ko taba ba, fulanice ta ɗago da rinnanen idonta ta kalleshi, hankalinsa ya tashi, amma kwarjininsa da kuma kamewarsa irinta mulki batasa ya nuna hakan ba, ƙarasowa yayi zuwa cikin parlon ya zauna akan kijera kusa datata.
Nadra ta zame daga kasan kujera tana gaisheshi, ya amsata yana ci gaba da binsu da kallo, kuma ko bayan ya amsata ɗin bata mikeba, tana nan durƙushe a wajen kanta a kasa, ya juyaga fulani, tun kafin yace komai yaga ta fashe da kuka.
Yasan cewa Tafida ya dawo, domin tun a jiya Tafidan ya nemi da su haɗu amma kuma yace masa saide da safe, dan hakama ya shigo da kansa dan su gaisa, kuma kukanta ke nuna masa cewar koma miye ya faru to Tafida ne, Fulani bata kuka akan komai sai akan Tafida.
***
“Eshaan jeka ɗauko min waccan ball ɗin”
Muryar Roshni mahaifiyar eshaan a wancan lokacin ta faɗi, wani karamin yaro ɗan shekara huɗu ya ɗago ya kalli kyakywar matar wadda take ba'indiya, ya ɗaga manuniyarsa ya nuna ball ɗin tareda faɗin
“yeh ? (wannan?)” ya tambaya cikin harshen indiyanci, matar na murmushi ta gyaɗa masa kai, ya fita da gudu yayi wajen da ball ɗin take, matar kuma ta biyoshi da gudu itama tana dariya tareda faɗin
“eshaan kabi a hankali, eshaan!!... eshaan!! ...eshaan!!!!”
“maa!, maa!, maaaaaaaa!....”
Yana fisge-fisge yake furta maganar, a razane ya mike zaune, Idanuwansa gaba ɗaya sun firfito waje sai haki yake, duba yakai ga hannunsa na dama, sai yaga wutar nan daya saba gani naci a tafin hannun nasa, idanunsa ya lumshe a hankali sannan ya dunƙule hannun nasa ya buɗe tareda idonsa nan take wutar ta bace, hannunsa yakai jikinsa yana shafawa.
Yaji t-shirt ɗin daya kwanta da ita jiya gaba ɗaya ta jiƙe da gumi, ya kuma lumshe ido, fuskar mahaifiyarsa ta dawo masa tunanin sa, a hankali ya buɗe ya sako kafafunsa ƙasan gadon ya saka slide sandales ɗinsa dake kasan gadon, hasken dake shigowa ɗakin ta windows ɗin dakin sune suke nuna masa cewar gari ya waye.
Idonsa yakai inda ya aje wayarsa jiya daddare, kafin abinda ya sameshi jiya ya faru, yasan cewa dole ya hargutsa abubuwa da yawa a ɗakin, amma kuma gashi an gyara komai tun kafin ya tashi daga bacci, tafin hannunsa ya buɗe sannan ya miƙa hannunsa zuwa ga inda ya aje wayar dake can a kan wata chest drawer, nan take wayar ta tashi daga kan chest drawer ɗin da take a aje ta iso ta sauka akan tafin hannun nasa kamar wani magnet ne ya janyota.
Charger ya janyo ya sakata a chargy bayan ya cire ɗayar a chargy, ya miƙe tsaye ya shiga ban ɗaki yayi wanka haɗi da alwala ya fito yayi sallar asubar data wuceshi, sannan ya miƙe ya koma ban ɗakin yayi brush ya fito ya buɗe jakar dayazo da ita ya fito da wasu riga da wando na farar shadda, yau za'ayi hawan angwance, ya saka kayan sannan yaje ya tsaya a gaban dressing mirror ya shiga gyara gashin kansa kamar yanda ya saba kula dashi a kullum, sannan ya feshi jikinsa da tirare, ya ɗauki hularsa zanna bukar me aikin blue da fari ya saka a kansa sannan ya saka flat shoes blue ya d'auki wayoyinsa sannan ya fito.
🌸-SAI KASKA CE-🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TASO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
©By Sai Kaska
*proud of my first novel*
*BABI NA BIYAR(5)*
Ya dinga wuce falukan dake turakar fulani kafin ya iso falo na biyun karshe, abinda ya gani ya tayar masa da hankali, jiki a sa6ule yayi sallama, fulani dake risgar kuka ta ɗago da kai ta kalli inda yake, hakama me martaba, zuwa lokacin nadra ta bar falon dan bazata iya jurawa ganin mahaifiyar tata na kuka ba.
kansa a kasa ya ƙaraso cikin parlon ya zauna a kasa kusa da kafar mai martaba, yana duƙar da kansa, me martaba kuwa tunda ya shigo yake ta binsa da kallo har ya zauna a kusa da ƙafar tasa, duk da ya jima bai ganshi ba, amma kuma yaga cewar ya rame sosai fuskarnan tasa babu komai sai dogon hanci, gaishe da me martaba yayi me martaba ya amsa a nutse.
“ina kwana ranki ya daɗe” fulani ta share hawaye, cikin dakiya tace
“lafiya Tafida, fatan ka tashi lafiya”
“lafiya kalau”
“ina zakaje naga ka shirya”
“jawan angwancen da za'ayi zanje”
“kaji sauƙin jikin naka ne?”
muryar mai martaba ta tambaya, Tafida ya ƙara ƙasa da kansa.
“eh ranka ya daɗe banajin komai”
“tashi kaje, nayi maka lamuni”
“aa bakaci abinci ba”
“zamuci tareda muktar”
ya faɗi bayan ya miƙe har ya fita daga parlon basu sami damar kallon kwayar idonsa data sauya kala zuwa ja ba, sun glasses ɗin daya saka a aljihun sa ya zaroshi ya saka a idonsa, dan yayi duk yanda zaiyyi amma idon yaƙi komawa yanda yake.
Yana taka ƙafarsa a parlo na farko ya motsa kunnensa ta yanda zai iya jiyo abinda ake tattaunawa a parlo na biyu, muryar me martaba ya tsinkayo yana bawa fulani haƙuri sbd kukan data ci gaba dayi.
Sai ya motsa kunnen nasa yaci gaba da tafiya, ƙarfin ji na ɗaya daga cikin baiwar da allah yayi masa, ga kuma baƙin ruhin dake jikinsa dake ƙara masa.
Daya fita waje ya iske tawagar mai martaba, suna ganinsa suka miƙe sunata zabga ƙirari, murmushin dole ya ƙirƙiro yayi musu yana amsa gaisuwar tasu.
MARYAM POV.
“ke dallah ki tashi muje ”
Muryar Badar ta faɗi yayinda take kallon Maryam ɗin wadda ke zaune tana yankewa auta farce, Maryam ta ɗago ta kalli Badar dake tsaye ta ci uwar kwalliya kamar me shirin shiga hasar sarauniyar kyau.
“wai zuwan dole ne ?, sanin kanki ne ni ba zuwa kallon hawan doki nake ba”
Kuma haka ɗin ne, dan koda wasa Maryam bata zuwa kallon hawan dokuna, sbd tsabar tsoranta, tsoran bingidar da ake harbawa kafin sarki ya ƙaraso dama shi kansa dokin tsoransa take ji.
“Dan allam Maryam ki tashi mu tafi, ni yau so nake sai kinga TAFIDA”
Tafida ?, sunan ya maimaita kansa a cikin kanta, ita sam bata taba ganinsa ba koda sau ɗaya, amma babu budurwa da bazataji zancensa ba a bakinta, hatta da Badar kuwa, itama batada zance sai nasa, dan haka yasa yauma da aliyu yace bazai samu damar zuwaba ranta ya mata fari, dan yau Tafida zai hau hawan angwancen da ake yau, sbd auren ƴar sarki da ake, ko ba komai zata samu ta kalli kyakyawar fuskarsa, wannan ma kaɗai ya isheta.
“Badar waini wannan Tafidahn annabi ne ?, da zaki dage akan sai nawani je na ganshi ?”
“aa fa, ba annabi bane, kinsan allah Maryam dan baki ganshi bane, da zarar kin ɗora ido akansa wallahi zaki fara sansa, ba'indiye ne fa, najima wai anacewa babarsace ba'indiyar, shiyasa ya biyo kamarta”
Maryam taja tsaki a cikin ranta, Badar bazata gane ba, itafa bazata iya wahalar da kan taba tana yankawa kare ciyawa, yau yankawa kare ciyawa mana, inba yankawa kare ciyawa ba me yasa zaka zo ka saka wanda baima san kanayi ba a rai.
“nifa danma bansan username ɗinsa bane a social media, da na ɗauko hotunansa da yawa na aje a wayata”
“dama kin kama hanyarki kintafi, dan wallahi ni ba zuwa zanba, kinga yanzu inayin abincin rana zan tafi shagari gidan anti fati”
“ke ki jirani na dawo sai mu tafi, kinsan gidanta kusa da gidan Tafida ne, idan allah yasa nayi sa'a sai kiga mun haɗu”
ta faɗi idonta na haskawa da ƙyallin murna.
Yanxu tsakin kam a fili tayi, ta rasa meke damun kan Badar,to ita yau bazatabi ma ta ƙofar gidan nasa ba.
HANAM POV.
*Da misalin ƙarfe 10 na dare*
Hanam ce take taku zuwa inda ta aje motarta, bayan ta fito daga wani shopping mall, gabanta ne yayi mummunar faɗuwa sbd wani mutum data gani a gabanta hannunsa riƙe da wuƙa yana nunata da wuƙar, aryaan ta ƙanƙame wanda ke cikin baby carrier ɗinsa yana bacci.
“give me the baby”
“what!!!!”
Ta faɗi a kiɗime cikin ƙaraji
“yes i say give me the bab....”
Dukan da wani yazo ya sakar masa a baki wanda daga ita har shi basu ga tahowarsa bace tasa shi ya haɗiye maganar dake bakinsa, daga nan kuma ya shiga dukansa tako ta ina, zuwa lokacin Aryaan ya farka sai kuma yasaka kuka, Hanam ta ruɗe tana kallonsu, daga me dukan har wanda ake dukan babu wanda Hanam ta samu damar ganin fuskarsa.
“Dan allah Kayi haƙuri wallahi wani ne waishi kamal ya bani dubu ashirin yacena karbo masa yaron”
Kalmar 'kamal' daya ambata ita ta bawa Hanam Mugun mamaki, ashe tsanar da 'yan uwan nata suka mata ta kai haka ?, yanzu ita me ta musu a rayuwa haka ?, ta juri abubuwa da yawa marasa daɗi a rayuwarta amma hakan bai isheta ba sai ƴan uwan nata sun ƙara mata da wani, me yasa ?, me yasa hakan ke faruwa da ita?.
“Oga pls”
Muryar wanda ake dukan nasa ta ƙara fitowa, kafin wanda yake dukan ya sake shi, da gudu wanda ake dukan ya miƙe ya falfala.
Kuma har yanzu Hanam bata samu damar ganin fuskar kowane ɗayansu ba, sbd shi ɗayan fusakarsa a rufe take da mask, ga kuma duhun dare kuma parking lot din babu haske sosai, shi kuma wanda yake dukan ya bata baya, ba tareda ya juyo ba yaci gaba da tafiyarsa.
“I can't thank you enough”
Ya tsaya amma bai juyo ba sai kuma yace
“ dont mention it”
Ya ci gaba da tafiyarsa.
***
A fusace Hanam ta shigo cikin parlon gidan nasu, Aryaan goye a bayanta cikin baby carrier ɗinsa wadda zuwa yanzu ta juyata baya.
Kamal na zaune a kan 2 seete yana duba wayarsa jifa-jifa sbd yana jiran shigowar saƙon ɗan ta'addan daya saka ya ƙwato masa yaron Hanam, dan tun bayan data mareshi ya saka a ransa cewa ba zai barta ba, sai ya ɗau fansar abinda tai masa, ya kuma ƙudurta a ransa cewar sai ya rabata da shegen ɗan nata domin shine farin cikinta.
Kamar da akace ya ɗago kansa ya kalleta tana tahowa zuwa cikin parlon a fusace, da sauri ya miƙe sbd irin kallon da take masa, Mero da kishiyarta Hajjo da kuma sauran yaransu duka suka miƙe.
Tana ƙarasawa gaban Kamal batayi wata-wata ba ta ɗauke shi da mari, ya ɗora hannunsa akan kuncinsa na dama inda marin ya sauƙa, kuma bata barshi ya gama jin raɗaɗin zafin marin nata ba ta kuma sakar masa wani marin, a dai-dai lokacin kuma abba daya dawo ɗazu da rana ya sauƙo daga sama, kuma a

Please Login or Register in order to submit comment