Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma hakan a kayi, ya koma makaranta ya ci gaba da karatu.
Sede matsaltsalun dake faruwa a gida basa saka shi ya yi focussing a kan karatun, sau uku yana maimaita aji, kafin ya samu ya wuce, amma duk da haka abokan karatunsa sun masa nisa a lokacin.
Wata rana da bana matawa Ina zaune a gid naji ihu da kururuwar Rashidat, na fita domin kai mata ɗauki, dan nasan Aja ne ke dukanta, a sanda na shiga gidan na tadda ta yashe a ƙasa Aja na dukanta, Jude da Zakiyya kuma tsaye gefe suna ta kuka.
Na shiga bawa Aja haƙuri amma ko saurare na ma be yi ba, a haka har Uche ya dawo daga school, shi kuma a ranar yaji cewa ba ze iya jurewa ba, dan haka ya ɗauki madoki, ina riƙe shi amma seda ya fisge ya daki Aja da abun a kai.
Aja ya bar kan Rashidat ya dawo kansa, yana dukansa yana tsine masa, Rashidat ma taga bazata iya jirewa ba, dan haka ta ɗauki madokin da Uchenna ya cillar ta daki Aja da shi.
Aja ma yaji ba ze iya jirewa ba a take a wurin ya saki Rashidat. Kar ko so kiga yanda tayi murna ranar, dan ko kwana a gidan ba ta yi ba, a nan gida na ta kwana.
Washe gari da safe ta ɗauki Zakiyya ta yi enugu da ita.
Kuma bayan ta gama idda miji ya fito mata ta yi aurenta. Rayuwar Uche a gidansu ta ci gaba da ta fiya cikin kunci da damuwa, Aja ya ƙwace keken da yake ɗinki da shi, baya ba shi abinci se anan gidan yake zuwa na bashi, gashi shi ba abokai gare shi ba.
Tsangwama babu kalar wanda Aja baya masa, ke hatta da dabbobin da yakw kiwo ɗakin Uche yake ɗaure su, gwarama Jude dan shi baya masa komai, dan yana san yaron sosai, duk da shima musuluci yake.
Rana ɗaya Aja ya bushi iska ya ya kori Uche, babu yanda ban bawa bawan Allahn na haƙuri ba amma yace fir be san zancen ba, hatta da mijina se da ya bashi baki amma yace ba zs haƙura ba. Sai kuma a kazo ana bani labari kan cewa wai Uchenna ya hau kan titi mota ta kaɗe shi.
Wannan shine labarin uche, a washe garin ranar da uche ya hau titin nan mahaifinki yazo har gidan nan ya yi min tambayoyi akan uche da mahaifiyar sa, bayan nan kuma Rashidat take sanarmin da cewa ya samu aiki, yana rayuwarsa cikin kwanciyar hankali”
Ta ƙarashe tana kallon Hanam, wadda idanunta sukayi ja, tana so ta yi kuka amma ta nemeshi ta rasa, Bata san cewa akwai wani wanda ke cikin baƙin ci ba bayan ta.
Zuciyarta ta cika fal da tausayin Uche, lokacin suna makaranta yana cikin wannan halin amma sam baya hana shi dariya, murmushi da raha, amma ita fa?, ita abu ɗaya ta rasa a lokacin, kulawar uwa, amma take ware kanta da kowa, bata shiga cikin mutane, duk dan wannan ciwon dake cikin zuciyar ta.
🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.



⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Na sadaukar da wannan babin gareki Mounira Aboubacar*

*BABI NA TALATIN DA ƊAYA (31)*

*Lagos*
*Da misalin 11:20am*

MARYAM POV.
Tsaye take a cikin kitchen, hannunta cikin wani silver bowl tana mulmula laddu, sai yanzu tunanin abinda ya faɗa mata ɗazu ya dawo mata, dan ɗazu sam bata samu damar yin tunani me kyau ba, sai yanzu kalaman ke dawo mata daki-daki.
_ “Miriam you make home inside of my heart, i wish that one day you will know what it feels like to make a home inside of someone's heart, eventually i find that one person that understand the melody of my soul, and now you are sing it back with ease, and see, it's beautiful....i find a women that can vulnerable with, while feeling completely safe, you mean everything to me Maryam, you complete me, tum mera aakhoka tara...”_
Tunanta ya datse sanda aka murɗa ƙofar kitchen ɗin, ta yi sauri ta kalli jikinta, babu hijabi a jikinta, daga ita sai ƙaramin mayafin abayar dake jikinta, kuma kafin ta yi wani yun ƙuri har ƙofar ta iyo ciki, wanda yake bayan ƙofar ya sako kai.
Kamar yanda itama take kallonsa shima ita yake kallo, kayan dake jikinsa ɗazu da zai fita sune har yanzu, wata baƙar hoodie ce, sai 3qtr ash color, har yanzu gashin kansa yan kan fuskarsa, bai meda shi baya ba, na bayan ma ya sauko masa kan wuya, kansa sanue da p-cap, amma bai cusata duka a kan nasa ba, ya ɗan dorata ne kaɗan, hakan yasa gashin nasa sauƙowa ta kasanta.
Ba yau ta fara ganinsa cikin kayan ba, dan ta tab'a ganin ya saka kayan, amma yau na daban ne, yanda gashin kan nasa ya sauƙo masa sai ya zama kamar wani yaro ɗan shekaru ashirin, idonta ya kai gefen fuskarsa, har yanzu wannan raunin da ya ji da ball jiya yana nan, amma kumburin ya sace kaɗan.
Duk da idonsa manne yake da baƙin glasses amma tasan cewa ita yake kallo, hannun ƙofar ya saki bayan ya rufeta, ya ƙarasa shigowa ciki, a kan Island ɗin ya aje ledojin hannunsa sannan muryarsa ta fito a hankali, kamar me tsoron kada wani yaji.
“An samu cow tail ɗin”
Maryam ta dakata daga mulmula laddu ɗin da take gaba ɗayi ta kalleshi, a sanda yake zama akan kujerar island ɗin.
“Kai ka siyo dama?”
Ta tambaya ne dan tasan ɗazu da ta faɗa masa cewa tana san cow tail David ya kira a waya ya faɗa masa suna buƙatar cow tail ɗin, kuma yanzu fitar da ya yi cabege yace ze je ya siyo.
Ya kai hannu yana ɗaukar laddu ɗaya daga cikin wanda ta gama mulmulawa ya na kaiwa bakinsa sannan ya girgiza kai.
“Nop, ba ni bane, David ne, na dawo daga siyan cabege ɗin na ganshi shima ya dawo, shine na karb'a”
Taci gaba da abinda take tana gyaɗa masa kai, yaci gaba da kallonta ta cikin glasses ɗin, ba kasafai yake ganinta ba hijabi ba, amma ko yaya ya ganta tana burgeshi, ya kasa kunne yana sabbaben nasa, kafin ransa ya raya masa da ya kamata ya bata abinda ya samo a cikin kayansa yau.
Miƙewa ya yi, kuma a lokacin idonsa ya kai kan takardun dake wajen, wanda da be lura da su ba, yana zagayawa inda take yake faɗin.
“Karatu kike ne ?”
Gabanta na dukan tara-tara ta gyaɗa masa kai, dan Allah ya sani bata iya jurewa abinda yake mata, karatun take sanyi amma ta kasa, abinda ya faru ɗazu ya hanata sukunin yin karatun.
“Mun ku...sa fara... exam ne...”
A ransa yace good, dan lokacin bikin holi ya kusa, baya so lokacin yazo basu yi hutun makaranta ba. Ƙafafunsa suka dakata a setinta, Maryam ta kalleshi ta gefen ido, tana haɗiye wani abu.
So take tace masa dan Allah ya matsa ko zata samu ta shaƙi iska me daɗi, dan wadda take shaka yanzu ta garwaye da ƙamshin turarensa, idan ya matsa ɗin ma wata kila zafin zazzab'in dake jikinta ya sauƙa, zazzabi ?, wata ƙilama a cikin kasusuwanta take jin zafin zazzab'in, babu akan fatarta, dan da ace akwai akan fatarta da yaji zafin, wata ƙilama ya lona masa hannu, dan Allah ne yasan irin zafin da take ji a jikinta.
Hannu yasa ya juyo da ita gaba ɗaya, kafin ya kalli hannayeta da suke da danƙwan sugar dana condensed milk, sai kuma ya kalli fuskarta, yana jin yanda zuciyarta ke tsere a kirjinta, be san meke damunta ba, amma duk sanda zai riƙeta yana jin yanda bugun zuciyar tata yake sauyawa.
Hannunsa na dama ya kai ya kewaye waist ɗinta tare da janyota gaba ɗaya cikin jikinsa, Maryam ta dunƙule yatsun hannunta tana rintse ido, wai meke damun bawan Allahn nan yau ?, shi fa da kansa yake cewa su nisanci juna, amma kuma shine yake mata haka?, wani ya temaka ya faɗa masa cewar ba zata iya ba, wallahi bazata iya ɗauka ba.
Ba ta yi aune ba taji ya zame mayafin data ɗaura a kanta, hakan yasa ta yi saurin buɗe idonta tana dubansa, gashin kan nata da babu ribbon ya sauƙo a gadon bayanta, har wani na sauƙowa a kafaɗarta, ya kai hannunsa yana kawarwa da gashin, kafin muryarsa ta fito can ƙasan maƙoshi.
“Yana damun ki ne ?”
Yanda kalaman suka fito akan fatar Maryam yasa ta kuma rintse idonta tana kawar da kai, wata ƙila za ta ji sauƙin abinda yake mata idan ta yi hakan.
A lokaci guda sai kuma ya saketa, ya saka hannunsa ɗaya a aljihun 3qtrn jikinsa na baya, ya fito da wani abu a hannun nasa.
Ya kai hannunsa duka biyu ya kamo gashin da suka sauƙo mata a kafaɗa daga ko wani b'an gare, ya kaisu baya, tareda saƙala hair pin ɗin da ya ɗauko a aljihun nasa.
“Haka zaki na masa, na Maa ne, ki kulamin da shi”
Ta gane miye na Maan, yana nufin hair pin ɗin,ta gyaɗa masa kai, tana ƙoƙarin juyawa, hannunta ya riƙo ya fisgota ta dawo jikinsa, yana jin yanda jikinta ke karkarwa, shi bai sani ba, wata ƙila tsoransa take ji, to in ba tsoronsa take ji ba me zaisa zuciyarta take irin wannan gudun ?, kuma har jikinta yana rawa haka?.
Fuskarta ya riƙo da duka hannayensa biyu, tare da kara tasa akan tata, yana kallon fuskarta ta cikin baƙin glashin idonsa, hancinsa a gefen nata, lebensa ma daf da nata.
Maryam taji kamar ya saki fitsari a wajen, kamar ta ƙwalla ƙara wata ƙila ta samu sauƙin abinda ke yawo a kanta, ina wannan mutumin yake so ya kaita ne?, wata ƙila zautata yake shirin yi.
Yana shirin haɗe tazarar dake tsakaninsu wayarsa ta yi ƙara, hakan yasa yaja kansa baya kaɗan yana kallon yanda ta ƙanƙame idonta, sai ya saketa ya ja da baya kafin ya juya ya zagayo inda wayar take ya ɗauka, domin kirane ɗaga india, abokinsa ne wanda suka yi karata ARJIT.
Maryam ta yi sauri ta juya masa baya, tana maida numfashi, kai kace gasar tsere ta shiga, ita a yanda take ji ma bata da maraba da wanda ya yi tseren, dan wani abu take ji yana mata yawo a jiki, wanda ba zata iya tantancewa sunan sa ba.
Ta godewa wannan wanda ya kira wayar yafi a ƙirga, dan ko ba komai ya dakatar da abibda yake shirin tafiya da iskar da take shaƙa.
Tana jinsa yana magana da harshen hindi, idan kaji yanda yake maganar ba zakace yasan wani yare ba wai shi hausa, cike da ƙearewa yake magana da na wayar, kuma a yanda take jin maganar tasa kamar yana cikin nishaɗi, duk da ita ba wani indiyanci take ji ba, sai ƴan kalmomin da ba'a rasa ba.
Hannunta ta daure ta wanke a sink, sannan ta daurewa zuciyarta ta juyo, tare da mata alkawarin bazama ta kalleshi ba, ta juyo ta dawo inda take a tsaye a da, ta mulmula curin laddu na karshe, sannan ta juyo zata dauƙo plate, sai ta tuna cewa tsayinta baya kaiwa wajen, dan haka ta kuma juyowa ta kalli inda yake, zuciyarta ɗaya, taga shima itan yake kallo, amma yanzu da idonsa yake kallonta, dan ya sauko da glasa ɗin kan hancinsa, yana kallonta ta saman glass ɗin, da ƙyar ta samu ta haɗiye wani abu, kafin tace.
“Side plate zaka ɗan ɗauko min”
Sai yata ya jingina da jikin kujerar da yake kai, ya ɗauki wayarsa da hannun dama, sannan ya yi amfani da hannunsa na hagu ya buɗe cabinet ɗin, ya fito da plates ɗin ya aje mata akan island, duk yana zaune daga inda yake, kuma yana danna wayarsa.
Ta kuma haɗiyewa wani abu, sannan ta ɗauki plates ɗin ta ƙara ɗauraye su, duk da tana da tabbacin a wanke suke, laddu ɗin ta saka masa akan plate ɗaya, ɗayan kuma ta aje shi a gefe, dan dama ɗaya take buƙata, ta gyara wajen tsaf, sannan ta ɗauki ledojin kayan da ya aje mata ɗazu, ta haɗa kan handout ɗinta.
Duka Tafida na zaune a wajen, yana danna wayarsa kamar ba ita yake kallo ba, bayan kuma ita yake kallon, kawai ya waske ne.
Maryam ta buɗe fridge ta ɗauko soymilk ɗin da ta haɗa, ya yi sanyi, ta ɗauko wata jar me starw ta zuba masa sannan tazo ta aje masa a gabansa tare da laddu ɗin.
Zata tafi ya dawo da ita ta hanyar jayo hannunta ya zaunar da ita a kujerar gefensa, zamansa ya gyara yana aje wayar akan island ɗin, a lokaci guda kuma yana kallon abinda ta aje masan.
“Miye wannan ?, ko kunun aya ne ?”
Kan Maryam a kasa ta girgiza shi.
“Ba kunun aya bane, soymilk ne”
“Soymilk ?, ba kin yi awara da waken soyar ba”
A hankali ta dago ta kalleshi, sannan ta amsa masa da.
“Ba duka nayi awarar da shi ba, biyu na raba shi shine na haɗa wannan ɗin”
Ya riƙe jar ɗin a hannunsa, shi bai tab'a shan abun ba, amma yau zai gwada, bakinsa ya kai ya zuƙa sau ɗaya, amma saida ya yiwa abun babban gib'i, dan sosai na cikin jar ɗin ya ragu.
Mabambantan taste ne suka ziyarci harshensa, akwai garɗin madarar dake ciki, ga zaƙin sugar dana condensed milk, ga kwakwa a ciki, ga kuma ɗansanon shi kansa waken soyar ga sanyin abun, abun yana da daɗi, kuma ya burgeshi sosai, bai san cewa haka yake da daɗi ba ai, ƙara kaiwa bakinsa ya yi kan starw ɗin bai sauƙe ba saida yasha fiye da rabi.
Sannan ya aje jar ɗin, yanata santi a ransa shi ɗaya, kafin ya ja plate ɗin laddun, ya fara ci, daga inda yake yanzuma ya buɗe fridge ya dauki ruwa, saida Maryam taga haka sannan ta tuna da bata kawo masa ruwa ba.
“I am sorry Sultan, mantawa na yi ban baka ruwa ba”
“No Wifey, is not a big deal ai, amma pls ki dena cemin Sultan ɗin nan”
Girarta ta haɗe waje guda alamun mamaki ta furta “Me yasa ?”
Kansa tsaye ya amsata da.
“Sbd Sultan sarki ne, ni kuma ba sarki bane, ki nemo wani sunan da ban de”
“Amma kuma Sultan ɗin ya dace da kai”
Ya kai hannu ya cire p -cap ɗin kansa sannan ya kawar da sumarsa zuwa sama,
“Nop, bana so, ni duk wata harka ta sarauta bana so, dokine kawai abinda nake so a tsarin sarauti, shi yasa nake hawa duk shekara ko kuma duk biki idan ya taso, amma ni bana san rayuwa mara ƴanci, idana kanada sarauta baka da ƴanci, misali, idan kai mutumin gari ne zaka iya zuwa ka ci awara a kan hanya, sarki fa ?, babu shi babu wannan damar, ni kuma ina san irin wannan rayuwar, shi yasa nafi san rayuwar india fiye da ta nigeria, dan india muna yawan zuwa muci street food. So you better find another name”
Maryam taci gaba da kallonsa, duk da shi ba ita yake kallo ba, wasu lokutan yana bata mamaki yanda yake hira sosai, bata tab'a Ɗauka cewar yanada magana haka ba, sai idan suna hira,wai awara?, wata ƙila ma shine a ransa, dan ita ta yi jiya.
“Kinga, idan ke baki da idea ne sai na baki, kamar mi vida, mon prince, my boo, babe, pannah, yaar, jaan, piya, mehboob, my life line da dai sauransu”
Ya ƙarashe yana juyowa haɗi da tura sumar sa baya, Maryam ta girgiza kai
“Ai wanna basu dace da kai ba, wadan da suka dace da kai sai de kamar my little inflatable tube man, jack skeleton, hekter floor lamp.....”
Sai kuma ta yi shiru tana shirin bushewa da dariya, ganin yanda Tafida ke kallonta ido waje.
“Nasan ni dogo ne, amma ai ban kai waɗanan abubuwan ba, tab! wa ya ga tube man!”
Maryam ta kwashe da dariya tana kawar da kai, shima murmushi ya mata, sannan yace.
“Gaakiya waɗanan basu yi ba, ki nemo wani de”
Ta shanye dariyat tana gyara zama.
“Kaga kuwa a tictok na gani, sun ce idan ka faɗawa dogon saurayinka ze so sunayen, amma ga wani.....”
“Banda na shirme fa!”
Ya katseta tun kan ta faɗi abinda ke bakinta.
“Ba na shirme bane, hermoso ? (handsome) ”
ya gyaɗa mata kai.
“Wato Spanish aka koma kenan ?”
Tana murmushi ta gyaɗa masa kai.
“Ya yi, amma dade kin sauya min”
“Ok, ok, ok, ammm!, sundar ?(handsome)”
“Gwara-gwara dai, dan kinsan ni ina kishin yare na, na hindin yafi daɗi”
Ta gyaɗa masa kai kawai tana jan takardunta, tunda yanzu ta ɗan sake ya kamata ace ta yi ɗanyi karatun.

HANAM POV.
Jiki a sab'ule ta shigo cikin gidan, gaba ɗaya ta rasa wani tunani ya kamata ace ta yi, haƙiƙa ta cutar da Uchenna tsawon zamansu, amma shi a kullum burinsa ya ga ya faranta mata ita da ɗanta, kaico!, kaiconta da ta zama me san kai da yawa, tana zarginsa kan abida bai aikata ba, to waima ina tunaninta ya tafi ne, me yasa har take zaton cewa Abba zai iya kawo wani abu na cutarwa a rayuwarta.....
Tunaninta ya katse sanda ta iske Uchenna da Arya auna wasa a falo, sai dariya suke ƙyalƙyalawa, zuciyarta ta matse gu guda, wani abu ya shiga mata kaikawo a zuciya.
“Uche...uchenna zaka ce....”
Uchenna ke taya Arya gwalantu, yana koya masa sunansa.
“Arya kace papi!....”
Daga yaron har Uchenna suka juyo suka kalleta, ganin yanayinta kamar mara lafiya yasa Uchena miƙewa da sauri, yayin da ya aje Arya akan sofa, a ruɗe ya ƙarasa gabanta yana tab'a goshinta wai ko zaiji zafi, amma sai yaji babu zafin face sanyi.
Tunda ya miƙe Hanam ke binsa da kallo har ya tsaya a gabanata haka. Duk abinda ta saurara akansa ya dawo mata, a lokacin kuma Arya ya saka kuka, Uchena ya juya da sauri ya je inda yake yana ɗaukansa tare da faɗin.
“Me ya sameka aboki......?”
Maganar ta maƙale, sbd wani hannu daya zagayo daga baya ya naɗe cikinsa, ya tsaya cak, numfashi yana neman ɗauke masa, sbd kan Hanam daya ji a gadan bayansa, ga wata iska da take fitarwa daga bakinta yayinda take kuka, ga yanda ta maƙalƙale shi, ga kukan Arya.
Gaba ɗaya sai yanayin ya taro ya masa yawa, uwa na kuka ɗa ma na kuka, ya rasa me zeyi, a hankali ya shiga jijjiga Arya, still hannun Hanam na kewaye da shi kuma tana kuka, saida Arya ya yi shiru sannan ya aje shi akan sofa ya bashi teddyn da suke wasa da shi ɗazu.
Saida ya haɗiye wani abu da ƙyar kafin ya kai hannunsa ya b'anb'are na Hanam, tareda janyota gaba yana fuskantar ta, kuka take shab'e-shab'e, kuma tana kallonsa, hannunsa na karkarwa ya ɗago da shi yana share mata hawayen cikin fadin.
“Meke faruwa ?”
Hanam ta girgiza kai, sannan ta ƙara kankame shi, wannan karon kanta ya sauƙa a kirjinsa, ya kuma lumshe ido, wani ɗan ƙaramin yaƙi yana aukuwa a zuciyarsa, yana jin kamar ya saka ƙara, dan ya kasa jure yanayin.
Sake ɗago da ita ya yi yana ƙara share mata hawayen, kafin yaja hannunta ya zaunar da ita akan kujera shima ya zauna yana fuskantar ta. Se da ya juya ya kalli Arya dake zaune akan ɗayar kujerar, wasan sa kawai yake, kafin ya juyo ya kalleta.
“Ki dena kuka, idan kema kina kuka to Arya ma ze yi kuka”
Ta share hawayenta, tana ci gaba da kallonsa, Uchenna ya kalli hannunta dake cikin masa, combination ɗin fari da baƙi, dan kuwa shi baƙi ne, gashi ita kuma fara ce, farar ma fat kamar ba'indiya. A hnakli ya ɗago ya kalleta.
“Ki nutsu ki faɗa min abinda ke damunki”
Hanam ta gyaɗa kai sannan tace.
“Dan Allah Harees ka yi haƙuri, ina me baka haƙuri, ka yafe min....”
Tunda yaji ta kirashi da Haris yasan cewa yanzu tasan komai a kansa, komai yana nufin harda rayuwar da ya yi a baya, kuma yasan ko Abba be faɗa mata ba, wata rana anti Hajiya maƙociyarsu zata faɗa mata, kansa ya kawar gefe yana sakin hannun ta, amma ita sai ta yi sauri ta kama nasa hannun, tana zamewa ƙasa.
“Dan Allah ka yafemin Harees, ka yafe min”
Uchenna ya girguza mata kai yana kamo kafaɗunta, tareda mayar da ita ya zaunar a inda ta zame hannunta ya ƙara riƙewa yana so ya kwantar mata da hankali, inama zata tema ke shi ta dena kukan, dan bata san yanda yake jin kukan nata ba.
“Ba kimin komai ba Hanam, babu abinda kika min”
Hanam ta share hawaye tana ci gaba da kallonsa.
“A ina kuka haɗu da Abba?.....”.
_________________
_E gaskiya ko ni ina san naji ina suka haɗu da Abba_
_Allah Sarki Fidar Yara, shi kwata-kwata ma mulkin baya gabansa, amma Fulani Sadoya na can tana aikin banza_
_To ina godiya my people_.
🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.


⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Wannan babin baki ne Halima Yusuf Musa*

*BABI NA TALATIN DA BIYU (32)*

Hanam tail yiwa Uchenna tambayar dake cikin ranta tun ɗazu, sai taga ya yi murmushi, kafin muryar sa ta fito.
“Ranar da Babana ya koreni na bar gida, naje na hau kan titin kaduna road, ina so na mutu, a lokacin gani nake kamar mutuwar sai tafi min sauƙi, domin ni kaɗaine a cikin duhu, rayuwata bata da wani amfani, duka buruka na sun bi iska, burina shine na yi karatu na zama wani abun a gobe, na rasa wannan, burina na biyu kuma shine waƙa, ina matuƙar san na yi waƙa tun ina ƙarami, amma shima ya rushe, sai naga to ai bani da amfani a duniyar, dan haka na tsaya ƙyam a tsakiyar titi, na lumshe ido ina jiran fitar raina.
Wata mota ta nufoni gadan-gadan, amma kuma tana zuwa saitina ta taka birki, saide duk da haka saida suka ɗan bige ni, kin san waye a motar ?....”
Ya ƙarashe yana kallonta, Hanam ta ƙara matse hannunta cikin nasa tare da faɗin.
“Abba ne?”
Shima kan nasa ya gyaɗa.
“Ƙwarai Abba ne, shi ya kaini asibiti, na yi kwana ɗaya a can, kafin ya tambaye ni iyaye na, nace masa bani da kowa sai de maƙociyar mu, yace na nasa kwatance dan yaje ya sanar mata, na masa kwatancen gidan Anti Hajiya, shi da kansa yaje ya sameta, Anti Hajiya ita ta bashi duka labarina, kuma daga haka Abba yace zai riƙe ni, zai ɗauki nauyina, na faɗa masa me nake so, karatu nake san yi ko aiki, nace da shi ni aiki nake so, ba b'ata lokaci Abba ya bani matsayin PAn sa, kuma shi da kansa ya saimin wannan gidan tun a wancan lokacin, Abban ki mutumin kirki ne, ba kamar nawa mahaifin ba, babana baya sona, ya tsaneni, kullum yana cikin tsine min, ya dake ni ya daki mom ɗina, mts rayuwa a gidanmu babu daɗi...”
Ya ƙarashe yana jingina da jikin kujera, duk abinda ya faru da shi a baya yana dawo masa sabo, saide har yanzu Hanam hawaye take, ya ɗan karkato da kansa yana kallonta. Da ido ya mata alamar miye ?, sai yaga ta girgiza kai kawai tana haɗiye sauran hawayen.
Zamansa ya kuma gyarawa ya daurewa kansa ya kai hannu ya riƙo fuskarta sannan yace.
“Ki manta da baya, duk wasu abubuwa marasa daɗi da suke faruwa da mu manta su muke, idan kuma mukace zamu ci gaba da tunasu, to bazamu tab'a ci gaba ba a rayuwa, so smile”
Ta yi wani ɗan guntun murmushi, tana ƙarewa fuskarsa kallo, bata tab'a ganin fuskar tasa a kusa haka ba, yau har wani abu taga a goshinsa me kama da tabon sallah, Allah kenan, me fitar da me kyau daga cikin mara kyau, sannan ya fitar da mara da kyau a cikin me kyau.
Ya janye hannunsa daga kan fuskar ta, dan wannan kallon da take masa zai iya sakawa ya rasa nutsuwarsa, ya juya gefe yana faɗin.
“Abba ya kira ki ?”
Ta girgiza masa kai.
“Ai yace ma yau zai dawo”
Ya gyaɗa mata kai, kuma kafin ya sake cewa wani abu, wayarsa ta yi ringing, hannu ya kai ya ɗauka tare da kara wayar a kunnensa.
A wani irin Hanzarce ya mike tsaye, bayanin da ake masa a wayar ya kasa shiga ƙwaƙwalwar sa sam, wayar hannun nasa ya sauƙe ba tare da yace komai ba, ɗaya bayan ɗaya yake lalubo ma'anar kalaman da na wayar ta faɗa masa.
Hanam ta mike tsaye tana dubansa.
“Harees meke faruwa ?”
Idanuwansa da suka rine nan take ya ɗago ya zuba mata su, ta ya zata fahimce shi?, ta ina zai fara?,

Please Login or Register in order to submit comment