Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba da kallonsa tana sanbjin abinda ya saka shi dariyar.
“Wata rana muna cin abinci da Neha, Biryani ce Daadi ta dafa mana, a sanda ina ƙarami ina san cin yaji da yawa, sai na dauƙo yaji na shiga zubawa a iyaka inda zan ɗiba”
Yanzu kam dariya ya yi me ɗan tsayi kafin yaci gaba.
“Sai kawai Neha ta saka kuka, nayi-nayi ta yi shiru amma taƙi, sai kawai ta kama kiran sunan Daadi, Daadi ta fito daga kitchen ta na faɗin 'Me ka mata Eshaan ?’, nide bance komai ba, sai binsu da nake da kallo, kuma inaci gaba da cin abincina, Sai kawai Neha tace ‘Daadi kinga Bhai (brother) ko?!’”
Ya kwatanta maganar cikin kuka, Maryam ta yi dariya shima kuma sai ya yi dariyar yana aje fork ɗin hannunsa, ya tura sumar kansa baya sannan y ɗauki ɗan cup ɗin da cake parfait ɗin nan ke ciki.
“Daadi tace ‘Me Bhai ɗin ya yi ?’ Neha taja hanci sannan ta nuna ni tace ‘Yana cin gun yaji’”
Daya kai karshen sai ya ƙyalƙyale da dariya, Maryam ma ta tabya shi, Idan yana raha da surutu irin haka yana bata mamaki, A koda yaushe yanayin fuskar sa babu fara'a bare annuri, saide kwarjini kawai, kuma ko a fuska bashi da yanayin yawan surutu.
Ya dauki spoon ya gutsiri cake sannan ya kai bakinsa yana taunawa yace.
“Daadi tace ‘Wato shi yake cin yajin amma ke kike jin raɗaɗi?’, Meriuty yajin india yana da zafi sosai, ba duk bakine ke iya ɗaukar yajin ba, amma haka nake iya cinsa a lokacin, ita kuma sai take kuka dan tana ganin kamar ina jin zafin yajin”
Suka kuma yin dariya a tare.
“Yaushe zakubyi final exam ?”
Muryarsa ta tambaya yana tauna cake ɗin bakinsa, Maryam ta ɗago ta kalle shi, shi ba ita yake kallo ba, plate ɗin gabansa yake kallo, wani abu da Maryam ta kula kamar hakan ɗabi'ar sace, sai ya yi maka magana ba tare da ya kalle ka ba.
“Nan da sati ɗaya”
Sai ya jinjina kansa yana ɗagowa ya kalleta.
“Allah ya amsa addu'ata, dan sati saya ne kawai zai rage min a nigeria”
Girar Maryam a haɗe tana faɗin.
“Ina kuma za ka je ?”
“Zamu je dai, bani ba, india zamu je, najima ban je ba, dan nafi shekara ba tare da na je ba, ko auren Neha ban samu naje ba, tun bayan aurenmu Daadi tace min na taho, kuma zuwana a time ɗin ba zai iyu ba, yanzu kuma lokacin da na mata alƙawari ya kusa, ga auren abokina da za'ayi a can, ga gasar world cup na cricket da za'ayi,ga sumar kaina ta isheni, ina buƙatar zuwa india, kuma de kinsa ba zan tafi babu ke ba”.
India ?, kuma wai ita ?, ita Maryam ce zata je india ?, wani iko sai Allah, a ranta ta godewa Allah sannan ta shiga masa kirari, dan Allah abun godiya ne.

HANAM POV.
“Dan Allah mana bannute”
Harees ke maganar cikin sigar magiya, yayin da yake kallon Hanam dake zaune a ɗaki, Hanam ta ɗaga kai ta kalleshi.
“Nifa ba na san zuwa”
Har iyakar gaskiyarta ta faɗi, da gaske take masa cewar ita bata san zuwa wani Black Friday Fair, Kewace ke damunta, tana kewar Abba da kuma Arya, dan haka bata san zuwa ko ina, ko office ba zuwa take ba, dukuwa da yanda take bawa aikinta muhimanci.
Uchenna ya zauna kusa da ita, sannan ya kamo hannayenta duka biyu yana kallon cikin idonta.
“Bannute nasan me yasa bakya san zuwa, kewar Abba da ta Arya”
Nan take taji ƙwalla na tarar mata a ido, aƙalla de ta samu wani wanda yake iya fahimtar halin da take ciki, a cikin ranta ta yiwa Abba addu'ar Allah yaji ƙansa.
“Abba addu'a yake buƙata, Arya kuma ai ko ɗazu ma naga kunyi waya, ki aje komai Hanam, idan har muka ci gaba da waiwayar baya, bazamu tab'a ci gaba ba”
Hannu yakai ya share mata ƙwallar da ta zubo mata yana girgiza mata kai
“Abba bashi da magana data wuce, Hanam jarumace, bata kuka, tanada juriya, amma ni banga hakan ba”
Ta yi dariya cikin kuka tana kallonsa.
“Ummuahh, ta shi muje kinji?”
Ya furta 'ummuah' ɗin a kan bakinsa, ya miƙar da ita zai fara janta.
“Wait bari na ɗauki mayafi”
Ta ƙarashe tana cire hannunta daga nasa, wardrobe ɗinta ta buɗe ta ɗauko gyale ta ta yafa a kan Farar abayar dake jikinta.
Sannan ta kama hannunsa suka fita.
Kamar yanda yace zata buɗe ido kuma ta samu nishadi, ta samu ɗin, sai da taga wurin wasan yara ne ta ayyana cewa da ace Arya yana nan da sun kai shi wurin ya yi wasa.
Amma babu komai nan da wani watan zata je Cairo, kuma daga nan zata taho da shi.
Gada ɗaya bata jin daɗin komai, babu Abba babu Arya, duk sai take jin kanta wata iriya, dan ma akwai Harees, yana iyaka bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ba ta shiga damuwa ba.
MARYAM POV.
Yau zasu yi final exam, Ga kuma shirye-shiryen tafiyarsu india da suke, dan yace mata zasu jima a can, kamar yanda Tafida ya saba kawota kullum yau ɗinvma shine ya kawota.
“Ga lunch box ɗin ka”
Ta faɗi tana fitar masa da lunch box ɗin, tare da aje masa shi a kan cinyarsa.
Hannu yasa ya ɗauka, sannan ya mayar dashi kujerar baya.
“Sai kin dawo ?”
Ta gyaɗa masa Kai tana goya jakarta a baya, hannunta ta ji ya riƙo, dan haka ta damke hannun jakarta da ƙarfi, dan ji ta yi kamar ya saka mata shock ɗin wutar lantarki ne.
“Miriam”
Maryam ta lumshe idonta sannan ta buɗe, a hankali ta juyo ta kalleshi, yana kusa da ita, kusa sosai, kuma tana juyowar ya kama fuskar ta tarebda dora tasa a kanta ta.
Har cikin ranta take addu'ar Allah yasa ba abina da ya mata rannan zai sake ba, dan wata ƙila idan ya sake ba lalle ta iya rubuta exam ɗin ba, dan gaba ɗaya zata rasa nutsuwarta ne kamar last time.
Saide addu'arta ta bata karb'u ba, dan Tafida yana ɗora hancinsa kan nata, ya shiga kissing ɗinta, wannan karon ma yabfi na farko.
Bata san yanda yake riƙe kansa ba ne, tun a ranar da ya yi kissing ɗinta yake so ya sake, amma haka ya daure, dan baya so taga gaggawarsa.
A hankali ya ja fuskarsa baya, Maryam ta yi saurin kifa kanta a gefen kafaɗarsa, gwara ta yi hakan, dan wata ƙila hakan zai sa ta gujewa kallon idonsa, dan gaba ɗaya notukan kanta sun kunce, _'yar haddar karatun da ta yi sun tashi sun bi iska, ba lalle ma ta iya tab'uka komai ba yau.
Memakon hakan da ta yi ya sa ta ji sauƙi, sai ji ta yi Tafida ya ƙara riƙeta gam a jikinsa, hakan ya ankarar da ita abun da ta ke, dan haka da sauri ta zame a jikin nasa, ko lunch box ɗinta bata ɗauka ba ta fice.
Har saida ta ƙule masa sannan ya lura da lunch box ɗin nata, ya yi murmushi sannan a hankali ya furta.
“Uwar tsoro!”
Lunch box ɗin ya ɗauka sannan ya fita, dan ya san ajinsu.
Kamar kullum yauma sanye yake cikin manyan kaya, wata green ɗin shaddace a jikinsa, kansa babu hula, dan yanzu ya tara gashi da yawa, kuma idan ya saka hular bata zama, shi yasa ya dena sakawa.
Ko da ya shiga class ɗin nasu sai yaga babu malami a ciki, ya shiga dube-dube, can ya hangota a karshen benci, ta kifa kanta a kan desk, kamar kuka take kuma kamar me bacci.
Be yi wa kowa magana ba ya shiga cikin ajin, idon 'yan matan ajin kamar ya faɗo ƙasa dan ganin Tafida a ajinsu, shi kuma bai kula kowa ba.
Zara da Aisha ne suka juyar da kansu gefe, basa so su haɗa ido da shi, dan basu sani ba ko Maryam ta faɗa masa abin da suka yi.
“Miriam!”
Kamar a mafarki Maryam ta ji muryarsa tsaye a kanta, kai ina taya za'ayi ma yazo wajen, sai dai kuma tunawa da ta yi a mota ta barashi, bataga tafiyarsa ba, yasa ta ɗago da sauri, shiɗin ne kuwa tsaye a gefen desk ɗinta.
Ya Allahu ya Allah, wai shi be san halin da take ciki bane?, me yasa yake mata haka?, wallahi idan akaci gaba da haka zai iya zautata.... Lunch box ɗin ya miƙa mata sannan yace.
“Kin manta wannan”
Ta yi sauri ta karb'a, tana bin 'yan class ɗin da kallo, gaba ɗaya ido ya dawo kansu, kallonsu ake daga ita har shi, wasu na mamakin alaƙar da ta haɗasu, wannan de baya kama da ita ta ya za'ayi ace yayanta ne, sai dai ko saurayi, kusan irin wannan tunan ne a kan kowa dake ajin.
Maryam ta haɗiye wani abu sannan ta juyo ta kalleshi, yana nan tsaye be tafi ba.
“Kuka ki ke ?”
Da sauri ta girgiza masa kai.
“Me yasa ki ka kifa kanki a kan table ?”
Kode ta faɗa masa cewa abinda yake mata ne yake sata take nitsewa a cikin lake chad ?,a'a ko zata faɗa masa ba'a nan ba, nan ba wajen maganar su ba ne, ita da zai temaka mata ma ya tafi, da sai tafi jin daɗin ranta.
“Babu komai, haddata ce bana so ta....ta zube”
Ita kanta sai da ta sarawa kanta da wannan ƙaryarta ta, zubewar hadda kuma ta nawa ?, ai tun da leb'ensa ya sauƙa cikin nata haddar ta zube, saide ta sake sabon lale.
Ya cije leb'ensa yana kallon ta, dariya ce take san kama shi, amma ba zai yi dariya a nan ba, dariyarsa ta makusantanasa ce kawai, ba wa al'uma duka ba, shi yasan kome take, ba hadda take san riƙewa ba, jinyar gangar jikinta take sbd ya yi kissing ɗinta.
“Ok ki kula, Allah ya temaka, Allah ya bada sa'a”.
Da fatar bakinta kawai ta amsa ameen ɗin, shima kuma yana kaiwa nan ya fice ya bar matan ajin da bin bayansa da kallo, Maryam ta kallesu takaici na san kamata.
Tafida na fita suna dawowa da kallonsu kanta, suka iyo kanta zasu tambayeta amma Zara ta dakatar su ta hanyar faɗin.
“Ba sai kun tambaya ba, mijinta ne ”
Maryam ta kifa kanta a kan desk, sbd kallon da suke mata.

*R NO 147,JJ hospital, byculla, Mumbai, India*
A kan gadon marasa lafiya, Galadima ne kwance, yayin da rabin jikinsa yake a rufe, ya ƙara ramewa ya yi baƙi, kansa ya langwab'e daga gefe, bakinsa sai zubar yawu ya ke, yanzu maganama ba ya iya yi, hannayensa da ƙafafunsa kam sam basa aiki, ko zama baya iyawa sai an zaunar da shi.
Da ga kan wata kujera kuma Fulani Sadiya ce, wadda idan ba kasanta sosai ba a da, to baza ka ce ita bace a yanzu, ta rame ta zama wata iriya, tsabar tashin hankali, ɗan da ta saka buri da rai a kansa, shine yake kwance yau a cikin wannan hali, sai an kwantar sai an tayar.
Bama wannan bane abun damuwar, da suka zo asinitin saida a ka masa general test, kuma a nan ne a ka asanar musu da cewa yana shaye-shaye. Sai a yanzu ta gane cewa duk abinda takewa Tafida kan ɗanta yake komowa, babu ɗaya dake samunsa duka.
Ta yi kukan baƙinciki dana nadama fiye da ƙirgenta, gashi ta yi magana da boka kan a san yanda za'ayi a warware asirin, amma bokan sai ya tunasar mata da cewa itafa tace kada ayi wanda zai tab'a karyewa, kuma shi ya mata.
Ƙofar shigowa aka turo, me martaba ya shigo, ta ɗaga kai ta kalleshi sannan ta sauƙe, takowa ya yi zuwa kan kujerar da take zaune.
“Ya me jikin ?”
Ya tambaya yana kallon Galadiman da ke kwance a kan gado, Fulani ta kalleshi itama.
“Jiki da godiya”
“Tafida ya kirani, ya faɗa min cewar nan da wani satin zai shigo india, kuma zai zo ya duba shi”
Wata ƙwallace ta kufce mata, ƙwallar nadama da kuma baƙin ciki, duk halin da ɗanta ke ciki itace sila, yanzu shi Tafidan da take komai dominsa shine ma wanda zai zo ya duba shi, bayan ko ga miciji basa yi.
A ranta ta shiga jero istingifarin da ya zame mata jiki akwanakin nan, so take ta nemi yafiyar Allah, wata ƙila ya yafe mata kura-kuran da tavyi, amma tabbas tasan cewa ita me lefi ce gareshi, shin anya ma kuwa zai yafe mata ?.
_________________
_Fulani Sadiya is asking, shin za'a yafe mata ?, kun san shi Allah gafurun rahimun ne, sanan kuma ba'a shiga tsakanin Allahbda bawansa, to a har kullum de, Allah yasa mufi k'arfin zukatan mu, Allah ya tsare mu da aikata da na sani_
_Wai nace ba, kowa fa ya shirya jakarsa tsaf, dan bana naga k'aunar nan india zata kaimu, k'asar masoya ba, to ku ci gaba da zuba ido, dan jin yanda ta fiya india zata kaya, A har kullum, nice ta ku SALMA AHMAD ISAH(Wato SAI KASKA), na gode mukubda goyon baya._
🌸SAI KASKA CE✍️🌸.

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Wannan naki nw Deejamah*

*BABI NA TALATIN DA TARA (39)*


*Hanam fashion house, Gwarinfa, abuja*
HARIS POV.
“Me ya faru ?”
Ya tambaya yana kallon Hanam data kirashi tace yazo. Sai kawai ta girgiza masa kai, sannan ta ɗauko wani ƙaramin envelope ta miƙa masa.
“Kasan SSGF ai ?”
Ya karb'i envelope ɗin yana kallonta sannan ya kalli envelope ɗin.
“Mall ɗin Falaq ?”
Ta jingina da jikin kujera tana gyaɗa masa kai.
“Eh ita, kaje ka kai mata wannan pls”
Har zai ce wani abu, amma sai kawai ya yi shiru, ya miƙe zai fita, ƙofar da aka turo yasa shi dakatawa.
A razane Hanam ta miƙe tsaye, ganin wanda ya shigo, bakinta a buɗe take kallon suɗayen idanunsa, wanda ya kafa mata su yana kallonta, a take wurin ya fara sauyawa a idonta.
Office ɗin ya rikiɗe ya koma mata ƙofar gidanta na USA, yanda yake kallonta a yanzu haka ya kalleta a time ɗin.
Waɗanan shuɗayen idanuwan irin wanda Arya ya gada daga wurinsa. Da ƙyar fatar vakinta ta furta sunan da ta riƙe ta yi haddarsa a cikin kanta.
“Gabriel!!”
*Flash back......*
A shekarun baya Hanam fashion sun samu takardar kwantiragi da ga kamfanin The House of Sofia couture dake New York USA, suna buƙatar da C.E.On Hanam Fashion house da ta zo ta yi aiki dasu na shekaru biyu.
Sun yi yarjejeniya a kan hakan, sannan suka tsara komai. Har zuwa lokacin da Hanam ɗin ta shirya ta tafi can USA ɗin.
Sun fara aiki cikin nasara, domin komai na tafiya dai-dai, kuma sunajin daɗin aiki da Hanam ɗin.
Wata ranar monday, wadda Hanam ta kira da baƙar rana. Ranar da ta mata mugun tabo a dayuwarta, ranar da ta zama sanadiyyar shigowar wani haske rayuwarta, ranar da ta zana silar rushewar rayuwarta.
*
Zaune suke ita da abokan aikinta a office ɗinsu, a lokacin kusan 10:00pm, sun gama haɗa kayansa za su fita.
“Guys, me zai hana muje bar yau”
Cewar Camilla
“A'a ni bana shan giya”
Hanam ta faɗi tana buɗe musu ƙofa.
“Ai ba sai kin sha ba, kawai muje mu ɗanyi rawa”
Cewar Tomas, ba haka Hanam taso ba amma taga suna san hakan, dan haka ta furta abinda ya rikito da duniyarta daga sama zuwa ƙasa, kalaman biyu ne, amma fasirinsu ne yasa komai na rayuwarta hargitsewa.
“Ok muje!”.
*3679 st, Queens, New York Doha Bar lounge*
Wurin cike yake da 'yan mata da samari, banda kiɗa me ƙarfi babu abinda ya ke tashi a wajen, wasu na zaune suna shan barasa, wasu kuma na rawa.
Haka su Hanam suka shigo wajen, gaba ɗaya sai wajen ya bata ƙyanƙyami, ita bata tab'a zuwa irin wajen nan ba. Daga can inda babu mutane suka zauna, Camilla ta yi musu oder na giya, tasa a kawowa Hanam ruwa kawai dan shi tace tana buƙata.
“Gabriel kalli can!”
Kyakyawan baturen me blue eyes da farar fata irin tasu ta turawa ya juyo ya kalli inda abokin nasa ya ke nuna masa.
“Wacce da ga ciki ?”
Ya tambaya yana rarraba idanunsa a kan matan biyu dake wurin.
“Balarabiyar mana”
Ya saki wani kasaitaccen murmushi a sanda ya haɗa ido da ita.
“Tana da kyau, bari naje na gwada sa'ata”
Yana miƙewa abokan nasa suka saka ihu suna masa tafi.
Hannunsa riƙe da wine glass wanda ke ɗauke da giya ya ƙarasa wajen da suke zaune.
“Sannun ku de 'yan mata”
Camilla ce tace.
“Gabriel sannu”
Baki washe ta furta hakan, dan duk wanda ke zuwa doha bar yasan Gabriel, musamman 'yan mata da ke matowa a kansa.
“Menene sunanki kyakyawa ?”
Hanam bata ko kalleshi ba, tun ɗazu da suka hada ido ta ji tsanarsa ta daki ƙirjinta, ta tsani mashayi.
“Maganafa nake....”
Ya yi maganar yana shafar damtsenta, Hanam ta miƙe a fusace sannan ta ɗauke shi da mari. Ji kake tsit!, wajen ya yi shiru, sai kiɗan dake tashi kawai, idon kowa ya dawo kansu, wannan wata me sa'arce haka ta mari Gabriel.
Hannunsa kan kunci Gabriel ya miƙe tsaye, wata wutar masifa da bala'ice ke ci a idonsa.
Hanam ta nuna shi da ɗan yatsa cike da kashedi tace.
“Kada ka kuskura ka sake, ni ba irin akuyoyin da kasaba bi bace ka kula da abinda ka ke!”
Kuma tana kaiwa nan ta ɗauki jakarta ta bar wurin.
“Sannu Gabriel”
Abokinsa ya faɗi, yayin da yake miƙo masa handkacief, ya karb'a a fisge yana goge jinin daya fito daga bakinsa, abinka da fatar turawa ba wani ƙwarin arziki gareta ba, ɗan marin da ta masa shine ya fasa masa baki haka.
Hanyar da Hanam ɗin ta bi ya bi da kallo
“Me ya kamata a mata ?”
“Dolene na sameta a yau, sai na ɗanɗana mata kuɗarta, zata san ta yi wasa da Gabriel Vicente”.
*House 1011,188 power street, Brooklyn New York*
*Da misalin 1:30am*
Hanam ce zaune a falon gidan, domin bayan zuwanta garin nan ta kama haya, kuma wajen yana kusa da wurin aikinta, shi yasa ta kama gidan.
Coffee take sha, yayin da take waya da Jabeer (wanda zata aura).
Ƙarar door bell ce ta karaɗe falon, dan haka tace dana cikin wayar.
“Ana ƙwanƙwasa ƙofa babe, ma yi magana daga baya”.
“Ok i love you”
“Me too, bye”.
Daga haka ta sauƙe wayar, mayafinta ta ɗauka ta rufe kanta, sannan ta nufi ƙofar, ta wani ɗan ƙaramin rami ta leƙa dan ganin me danna door bell ɗin, sai taga mutum tsaye, kansa sanye da p-cap ta shagon Joe's pizza, haka ma rigar jikinsa, kansa a sunkuye yake, hakan yasa bata iya ganin fuskarsa ba.
Mamaki ya kamata, itafa ba ta yi order ɗin komai ba, dan haka ta buɗe zata faɗa masa cewar ba ita bace ta yi order ba, may be gidan gaba ne.
Tana buɗewa ƙofar tace
“Ba nan ban....”
Maganar ta maƙale a maƙoshinta sbd kansa da ya ɗago, yana mata wani irin kallo da blue eyes ɗinsa, da ƙyar bakinta ya iya furta sunan da ta ji Camilla ta kirashi da shi ɗazu.
“Gabriel?.........”.

*Present day....*
“Fita min da ga office”
Cikin ƙaraji da fishi ta yi maganar, tana kallon mutumin da ke gabanta. Idonta a bushe, babu ko alamar hawaye.
Bai fasa shigowa ba, shida wata mace biye a bayansa, wadda suke da tabbacin matarsa ce.
“Hanam me ye faruwa ne wai ?”
Haris ya biɗa a ruɗe, sam ya kasa gane abinda ke faruwa.
“Hanam listing to.....”
“I said get the hell out of here!”
Ta faɗi tana nuna masa hanyar da ya shigo.
“Dan Allah ki tsaya ki ji abinda yazo damu...”
Hanam ta kawar da kanta daga barin kallon fuskokinsu, hakan ya bawa matar damar cewa.
“Na san cewa mijina ya miki kuskure, amma dan Allah ki yafe masa, yanzu haka abinda ya miki shine yake bibiyar mu, wattani shida da aurenmu ya yi haɗarin mota, kuma an tabbatar mana da cewa bazai sake haihuwa ba, mu kuma muna matuƙar san haihuwa, haka muka shiga neman duj hanyar da zata sada mu da samun ɗa na kan mu, amma bamu samu ba, daga baya yace dani ya tab'a yin wani kuskure a baya, wata ƙila shine yake bibiyarsa, dan haka muka shiga bincike a kan ki, maƙociyarki ce ta sanar mana cewa ke yar nigeria ce, kuma ta faɗa mana inda kike aiki har take sanar mana da cewa kin haihu ma, munje can inda ki kayi aikin, kuma sune suka bamu address ɗin wannan wajen naki, dan haka muka taso ƙafa da ƙafa dan muzo mu baki haƙuri.....”
“Kun gama ?,......To ku fita!”
“Hanam ya kamata a ca.....”
“Ku fita nace!”
Matar ta kalli mijinta da idanuwanta da suka cika da ƙwalla, kafin idonta ya kai kan wani hoto dake manne a jikin bango, hoton wani ƙaramin yaro ne, yana kama da matar da suke tsaye a gabanta tana musu cin mutincin.
Amma kuma farin fatarsa da kuma ƙwayar idonsa irin ta Gabriel ɗinta ce, sak irin nasa ne. Hakan ke nuna mata cewar wannan shine ɗan da ta haifa, ɗan da ta haifawa Gebriel.
Hannunta na rawa ta ɗaga tana nunawa Gabriel hoton, a lokacin har ƙwallar da ke tare a idonta ta zubo.
Shima kansa ya juya ya kalli wurin, idonsa ya sauƙa a kan hoton, ya juyo ya kalli Hanam sannan ya kalli hoton, shima sai a lokacin ya zubar da hawaye.
“Wannan shine ɗan da ki ka haifa?....”
“Kar ka kuskura ka sake magana a kan ɗana!”
Ta yi maganar tana nuna masa ɗan yatsa, ya girgiza kansa.
“Wannan ba ɗanki ba ne ke kaɗai, ɗan mu....”
“Kada ka ƙara dan ganta ɗana da kai, kai ba ubansa ba ne, Arya ɗana ne ni kaɗai !”
“Arya ?, haka sunansa ?”
Gaba ɗaya kan uchenna ya kulle, ya kasa gane komai, kawai binsu yake da kallo baki buɗe.
Gabriel ya durƙusa guwowinsa ƙasa hannayensa a haɗe yana kuka kamar ƙaramin yaro.
“Na roƙeki Hanam, Sbd uban gijin da ki ke bautawa kada ki min haka, na roƙeki”
“A wacan ranar, nayi maka roƙo irin wannan fiye da yanda za'a iya ƙirgawa, amma baka kula ba, baka amsa ba, saida ka aikata abinda zuciyar ka ke raya maka, yanzu haka nima bazan saurare ka ba, ka fitar min daga office, daga kamfani na, daga garina, daga jasata, daga nahiyata, idan zai iyu ma ka bar min duniyar, inaga kamar zai fi”
Matar Gabriel ta dafa shi itama tana kuka, ta riƙe kafaɗarsa har ya miƙe. Sun juya zasu fita sai Gabriel ya tsaya, ya juyo ya kalleta.
“Idan zai iyu, ki sanarwa da ɗana cewa ni ne mahaifinsa”
Daga haka ya juya suka fice daga wurin.
Uchenna ya juyo ya kalli Hanam wadda idonta yake a bushe babu ko alamar hawaye.
“Ka je kawai, i am okay”
Sai kawai ya gyaɗa kansa, duk rintsi de ai zata komo gida, sai ya tambayeta ya ji meke faruwa. Dan zuwa yanzu ya fara fahimtar inda zancen ya dosa.
*
“Uche manyan gari, ashe ana ganin ku ?”
Muryar Falaƙ ta tambaya, yayin da Uchenna ke zaune a tsallaken teburinta, ya yi murmushi.
“Ana ganin mu mana, kune de ku ka b'uya”
Falaƙ ta yi dariya.
“Ga wannan wai tace na kawo miki”
Falaq ta karb'i 'yar envelope ɗin, ba sai ta buɗe ta ba, dan tun farko sun yi magana, dan haka kawai sai ta miƙe tana faɗin.
“Biyo ni”
Bayanta ya bi suka fita har waje, b'angaren studio ya ga sun nufa a cikin mall ɗin.
Kuma suna shiga Falaq ɗin ta yi magana da me kula da studio ɗin sannan ta kalle shi ta furta abinda ya sauya rayuwarsa tun farko har ƙarshe.
“Ka shirya yin waƙa ?”.

MARYAM POV.
“Zuwa jibi yace zamu tashi, dan Allah ki faɗawa Maanmu”
Maryam ta faɗi, yayin da wayarta ke kare a kunnenta, tana waya da Anti Fati, Muryar Anti Fati ta fito daga cikin wayar.
“To ba damuwa, zan faɗa mata, Allah ya tsare, ya kiyaye hanya, and Maryam dan Allah a kula, kinga mijinki wayyaye ne, gashi ya taso cikin jinsin kyawawa, wallahi Maryam idan bakya kula da shi kina zaune zaki ji anyi wuff da shi”
Maryam ta yi murmushi, a duk sanda za suyi waya da Anti Fati sai ta mata magana irin wannan, dan haka tace.
“Insha Allah, a gaida Ƙauna, da babansa, kuma kicewa Maanmu ina gaida ta”
“Zasu ji, sai anjima”
Ta sauƙe wayar da ga kunnenta, hijabin dake jikinta ta cire, ya rage daga ita sai wata farar high neck top, da wata bluen high waist skirt.
Yau ta tashi da niyyar gyara ko ina na gidan, dan ya faɗa mata cewar idan sunje india zasu jima, dan ko kayan abincima yace wanda tasan zai lalace ta bayar shi.
Cat ears headphones ɗinta ta ɗauko, ta yi connecting da wayarta, sannan ta kunna waƙa.
Da ga ɗakinta ta fara gyaran, inda ta cire curtains ɗinsa duka, ta zubasu a cikin wani basket da ta ɗauko daga store, ta yi moping ko ina da ina, da gogge shi tas, sannan ta ɗauki basket ɗin ta yi waje.
Balcony ta shiga nan ma ta

Please Login or Register in order to submit comment