Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaddararta.
Bata ankara ba taci karo da wata tsohuwa, mayafin da take ta famar gyarawa ya faɗi kasa, kuma ɗaurin ɗankwalin dake kanta ya zame yayi baya, ta ruƙo imran dake barazanar faɗuwa batamabi ta kan gyalen nata ba ta dubi tsohuwar.
“Fan Allah kiyi haƙuri Iya, ban lura da ke bane”
Tsohuwar data tsaya tana mata kallon ƙurilla ta kasa cewa komai, ta tsirawa tawadar Allahn dake goshinta ido, da zirin farin gashin daya Dan leko ta ƙasan ɗankwalin kanta , sai kuma ta kalli wadda take wuyanta, gabanta ya buga, amma sai tayi dauriyar kallon fuskarta.
“A'a babu komai jeki kawai”
“To iya, sannu kinji”
Maryam ta faɗi tana gyara ɗaurin ɗankwalin dake kanta, tareda janyo mayafinta tafita daga wajen.
A hankali tsohuwar ta juya ga teburin da taga yarinyar ta taso, taga wata Karima wadda ta sani a cikinsu, ta kira sunan Kariman, sannan ta yafitota da hannu, Karima ta taso tazo tana gaisheta.
“Wayece waccan wadda ta taso daga teburin ku ?”
Tsohuwar ta tambaya bayan ta amsa gaisuwar Karima
“Iya jakadiya, sunanta Maryam, ƙanwar Fatice matar habib”.
Jakadiya tayi shiru tana nazarin maganar
“Karima a ganinki za tayi shekaru nawa haka ?”
Karima ta tabe baki cikin tunani
“Eh banajin zata wuce ashirin da ɗaya.... zuwa da biyu”
Zuciyar jakadiya ta buga wani tsallen murna, dan da alama watan yin arziƙintane ya kama.
“Inace unguwarsu kuma waye mahaifinta ?”
“Iya jakadiya kode ɗanki zaki nemawa aurenta ne ?, naga sai tambayoyi kike jero min”
Jakadiya tayi mata wani kallo, wanda yake nuna mata cewar da gaske take ba da wasa ba, hakan yasa Karima ta tara yaɗonta gu ɗaya tace.
“Aiko da ɗan naki zaki nemawa aurenta da ya dace da mata, yar garko ce, kusa da kan matoya, sunan babanta Tijjani direba”
Wani murmushi ya subuce daga leben jakadiya, tana ƙara bin hanyar da Maryam tabi da kallo.
An ce komai yanada sila, komai yanada mafari, wannan shine mafarin wasu ƙaddararorin, mafarin faruwar abubuwa da dama, silar gyaruwa wasu abubuwa, silar 6qcin wasunsu.
🌸-SAI KASKA CE-🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
©By Sai Kaska
My wattpad page @Sai_Kaska
*Proud of my first novel*
*TAURARI WRITTER'S ASSOCIATION*
*BABI NA TAKWAS (8)*
Maryam tana fita daga wajen ta samu wani wari can nesa da mutane, kusa da inda ake ajebmotoci, ta zauna a kan wani dakali, tana ta mitar ƙaran kiɗan da yayi yawa a ciki, Imran ta zaunar gefe tareda kunna masa cartoon a waya, sai kuma ta ɗago tanata bin motocin dake parker kusa da inda take da kallo, wato su masu kuɗin nan basu da wata matsala a rayuwa, ta faɗi hakan a ranta.
Tafida ya fito daga cikin wajen taron, sbd ya gaji da mitar da ake masa, ga jikinsa dake ɗaukar zafi, kuma kansa na masa ciwo, alamun baƙin ruhinsa na kusa, yazo ya tsaya kusa da motarsa yana ƙoƙarin shiga ya tsinkayi wata murya a bayansa.
“Barka dai”
Sai kawai ya fasa buɗe motar ya juyo yana kallon ma abociyar murya, wata budurwa ce, matse cikin dikin staright gown, kai da ganin farinta kasan na mai ne, ga wata b'ular hanci tayi, mayafinta riƙe a hannu, baice mata komai ba sai tsaiwarsa da ya gyara yana binta da kallo, kuma ko bata faɗa ba yasan me zaisa tazo ta masa magana.
“Idan bazaka damuba dan Allah lambarka nake so, ina sanka da soyyaya”
Ba itace ta farkon masa irin wannan abunba, mata da yawa sun masa irin haka, sbd yasani a karan kansa ba sai an faɗa ba shi kyakyawa ne, amma kuma bayan wannan kyakyawar fuskar akwai wani duhu, duhun da babu wata ƴa mace da zata iya juyashi zuwa haske, wannan fuskar tasa kawai suka sani, basu san ainahin shi ɗin ba.
Eshaan Auwal Tafida bai san cewa akwai mace ɗaya da zata sauya tarin duhun dake cikin rayuwarsa ba, zuwa haske.
Kafin ya samu damar bata amsa, kunnensa ya jiyo masa wata magana a bayan wasu motoci, da farko tsaki akayi kafin yaji ance.
“Aikin banza, wallahi wasu matan basu da kamun kai.....”
Ko ba'a faɗa masa ba yasan cewa abinda yake faruwa tsakaninsu taji, shi yasa take faɗin hakan, dan haka ya mosta kunnensa na dama, wanda yake kusa da inda maganar take fitowa, tayanda yana iya jiyo bugin zuciyar me maganar, ga kuma wani ƴar ƙara kamar ta cartoon, muryarce taci gaba da cewa.
“In banda rashin kamun kai ma me zaisa kazo kana wani cewa namiji kana san sa da soyyaya?”
Aka kuma jan wani tsakin, a hankali take maganar, dan idan ba me ƙarfin ji irin nasa ba babu me iya jiyowa maganar, kuma bayan ta gama maganar sai ya meda hankali wurin sauraron bugun zuciyarta, a hankali take bugawa, sai yaji sautin yana masa daɗi, kamar wakar da yake yawan saurare.
Yayi nisa wajen sauraren bugun zuciyar tata, har baya iya jin abinda budurwa dake gabansa ke faɗi, gani tayi kamar yayi banza da ita, dan haka tayi tsaki ta bar wurin, tana ta mita a ranta na cewar gaskiyane abinda ake faɗi akan Tafida kan bashi da kirki, shi kuma ganin ta bashi damar shaƙar iska yasa ya shiga cikin motarsa yana ta sauraren wannan bugun zuciyar da baisan mamallakiyarsa ba.
*HAKUƊAU GROUP OF INDUSTIRIES, ABUJA*
*Da misalin karfe 10:00 am*
“Uallabai!, yallabai!, yallabai!!”
A firgice Alhaji Muhammad Hakuɗau ya ɗago yana kallon PA ɗinsa, wanda ke ta ƙwala masa ƙira, sai kuma ya kawar da kansa gefe, PA ya samu kujera ya zauna yana kallon ogan nasa.
“Abba me yake damunka ?”
Ya tambaya a matsayinsa na ɗa a wajensa ba wai shugaba da na ƙasan sa ba, Alhaji Muhammad Hakuɗau yayi ajiyar zuciya yana jingina da kujerar da yake zauna a kai.
“Abba ka manta that we are friends, we do'nt use to hide komai wa junan mu”
Maganar taso ta saka Abban murmushi, sai kawai ya gyara zamansa yana kallon PA ɗin nasa.
“Haris abinda ke damuna da yawa, ba duk kai zai iya ɗauka ba”
“Try me”
Abba yayi murmushi
“Matsalar ƴata ce Hanam”
Haris yayi murmushi shima, dama yasan zance gizo baya wuce na ƙoƙi, shi bai taba ganin ƴar me gidan nasa ba, amma a koda yaushe abban bashida abun faɗi ko abun magana akai sai Hanam, hakan yasa shi san ganinta koda sau ɗaya ne.
“Abba a matsayinka na mahaifin ta, addu'a ya kamata ace kana mata, duk da bansan abinda ya faru da ita ba, kuma ka kasance a kusa da ita domin ƙwarara mata gwuwa, ba kazo ka zauna kana tunani ba”.
“Haris Allah baya barin wani dan wani yaji daɗi”
“Ban gane ba”
“Ina nufin akwai mutuwa, akwai jinya dole wata rana zan zo na rabu da ita, hakan yasa nake san nayi mata aure kowa ma ya huta, amma kuma sam taƙi yarda da auren”.
“A'a abba bai kamata kace haka ba, kamar yanda na faɗa maka kayi mata addu'a just pray for her”
Ya ƙarashe yana murmushi, shima Abban murmushin yayi, Allah ya sani cewa yana matuƙar san Haris, da ace Hanam zata amince da ya saka ya aureta.
Abinda bai sani ba shine, wasu ƙaddarorin suna faruwa kamar yanda muka so.
“To meke faruwa ?”
Sai kuma ya dawo serious, ya miƙa masa file ɗin daya shigo da shi.
“file ne daga office ɗin manager”
Alhaji Muhammad Hakuɗau ya kar6a, ya buɗe file ɗin yana gyaɗa kai.
“Zaka iya tafiya”
“Ok sir”
Ya faɗi yana ƙoƙarin fita, a bakin ƙofa yaci karo da Kamal, babban ɗa a wajen shugaban nasu, wani banzan kallo Kamal ɗin ya watsa masa, dan Allah ya sani cewar ya tsani UCHENNA, dan a kullum mahaifinsu yana fifitashi akansa. Uchenna kam ko kallon Kamal ɗin beyi ba, ya rab'ashi ya wuce.
Ko ina ya wuce sai an kirashi, dan babu wanda bai san shi a kamfanin ba, dan Uchenna akwai raha, barkwanci da kuma haba-haba da mutane.
Office ɗinsa ya shiga ya zauna, tareda ɗora ɗaya akan ɗaya, ya janyo wayarsa ya kira ƙaninsa a waya, suka shiga waya, kuma bai kashe ba saida suka jima suna wayar.
Sai wajejen ƙarfe tara na dare ya tashi daga aiki, ya fito daga cikin ginin kamfanin nasu ya isa parking lot ɗin kamfanin, ya buɗe motarsa ƙirar Honda Accord, ya shiga ya tayar sannan ya wuce gidansa dake Cosgrove Estate Wuse.
Yana shiga cikin kyakywan gidan nasa wuta ya fara kunnawa, sannan ya ya haura sama ya shiga ɗakinsa yayi wanka sannan yayi sallahr isha'i da bai samu yayi ba, ya sauƙo ƙasa ya Shiga kitchen domin ya samawa kansa abinda zaici.
Duk da kyau da tsaftar gidan shi kaɗai yake rayuwa a ciki, babu kowa nasa tare da shi, shi ɗaya yake rayuwarsa.
*Hadejia Emirates*
Mai martaba Abdullahi Abubakar Masu ya tsaya tsirawa matarsa ido, wadda ta gama shaida masa da ta samo yarinyar da ake buƙatar Tafida ya aureta, bawai be yarda da ita bane, saide yana san ya san taya akayi ta samo yarinyar. Suna zaune ne a babban falonsa wanda yake cikin turakarsa, kuma babu me ikon shigowa wajen idan bashi ba ko matansa, sai kuma amintattunsa da suke zuwa su gyara wurin.
“Fulani, taya kika samo yarinyar?” Maganar tasa ta fito cikin ƙasaita kuma a hankali.
“ Bayan abinda ya faru jiya..... Na saka an kiramin Ɗan Masani, kuma ya ƙara faɗamin alamomin yarinyar kamar yanda ya shaida mana a wancan lokacin, kuma na ƙira jakadiya babba mun ƙara tattauna maganar da ita...... Kuma bayan ta dawo daga gidan kamu ne tazo take shaida min da taga yarinyar kuma tayimin bincike akan yarinyar..... Sannan babu alama ɗaya da yarinyar ta rage wadda ake nema”.
Me mai martaba ya sauƙe wani gwauron numfashi
“Na roƙeka ranka ya daɗe....dan Allah ka aura masa yarinyar nan, na gaji da ganin ɗana cikin wannan halin, ina so naga ɗana nima ya warke, na ganshi cikin farin ciki, naga ya tara iyali....”
Sai kuma ta kasa ƙarasawa, sbd kukan daya ci ƙarfinta, me martaba ya rungumeta a jikinsa cikin sigar lallashi
“Amma kinyi bin cike sosai akan yafinyar ?, dan bana so muje mu kawo wadda bata dace ba cikin ahalin mu, garin gyaran gira a rasa ido”.
Fulani taja hanci
“Eh na ƙara sawa an min bincike akanta, yarinyar tanada tarbiyya sosai, kuma daga gareta babu wani aibi, mahaifin ta ne ba mutumin kirki ba”
Me martaba ya gyara riƙon da ya mata a cikin jikinsa sannan ya furta abinda ya zama sannadiyar sauyawar ƙaddarorin Tafida da wannan yarinyar da suke magana akai.
“Yarinyar ce zata zauna da ɗanmu ba mahaifin ta ba, dan haka na ɗauka miki alƙawarin a gobe goben nan za'a ɗaura auren Tafida da wannan yarinya, kamar yanda za'a ɗaura auren Amina da Adam, wannan alƙawari na miki”.
**
A daidai wannan lokaci, a wani ban garen na masarautar Tafida ne yake tafiya cikin nitsuwa izza da ƙasaita, wayoyinsa ne guda biyu riƙe a hannunsa na dama, hannunsa na hagu kuma key ɗin motarsa ne yana tafe yana ɗan kaɗa key ɗin.
Bayace ga dalili ba, amma wannan bugun zuciyar daya saurare ya kawar da abubuwa da yawa a cikin kansa, ya mantar dashi sign ɗin zuwan baƙin ruhinsa, ya mantar dashi komai, sautin ne kawai ke bashi nishaɗi, kamar kaɗawar igiyar teku, yayinda yake tsaye a gab'ar tekun, iskar da tekun ke busowa me ciki da daɗi da ni'ima tana busawa akan fatarsa.
Haka yake jin bugun zuciyar tata, kuma kamar wata waƙa me daɗi daga bakin babban mawaƙinsa, yaso ace ya dawwama yana sauraron bugun zuciyar nan, dan bayan daya shiga motarsa bai fito ba, kuma baiga yarinyar ba.
Kawai de ya zauna yana jin bugun zuciyar tata ne, kuma jifa-jifa yake ji tanayiwa wani ƙaramin yaro magana, alamun ba ita kaɗai bace a wajen, kusan minti goma sha, sannan sai wata murya ta kira sunanta 'MARYAM' a lokacin ne kuma ta tashi ta bar wurin.
Kuma bai dena sauraron bugun zuciyar tata ba har suka fita daga wajen. Sunanta da kuma muryarta dama bugun zuciyar tata baki ɗaya sunyi gaba da zuciyarsa, har cikin ransa yake fatan sake ganinta......
🌸-SAI KASKA CE-🌸.
⭐YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
©-By Sai Kaska
My wattpad page @Sai_Kaska
*Proud of my first novel*
★TAUTARI WRITTER'S ASSOCIATION★

*BABI NA TARA (9)*
.....Idansa ne ya kai kan Galadima wanda yake tafe Dogarai na take masa baya, kallo ɗaya ya masa ya sheƙar, banda shi Galadima ɗin da bai ko kalli Tafidan ba, dan wata iriyar tsanarsa yake kamar idan aka bashi wuƙa yau akace ya kasheshi zai iya, bayasan Tafida ko kaɗan.
Babban abun haushin ma Tafid shine ya san sirrinsa da babu wanda ya sani kaf duniya, ciki kuwa harda Fulani Sadiya, haka suka zo suka wuce opposite, amma babu wanda yakula wani.
Tafida na shiga turakar Fulani, a parlo na uku ya samu Nadra tana kallo, gaishe da shi tayi sannan ta bishi da ƙorafin ƙin tsayawa ya gaisa da ƙawarta da beyi ba, daga nan tai mishi tayin abinci, kuma bai ƙiba amma sai yace bari yaje yayi wanka.
Bayan yaje yayi wankan ya sauya kaya zuwa farar T-shirt da baƙin jogger pants, ya saka baƙaƙen slide sandales a ƙafarsa, ya riƙo wayarsa ɗaya ya fito.
Yana wannan takun nasa na izza da jan aji, har ya ƙaraso parlo na ukun, dan shi bangarensa na parlo na huɗu, yayinda ɗakunan Fulani da na Nadra yake parlo wajen na shida, kuma akwai wani dogon corridor dake haɗa ɗakunan nasu.
Abincin ta zuba masa, shinkafa ce fara wadda aka dafata da green beans da kuma carrot, sai kuma miyar kifi da daffafen kwai, ta zuba masa pineapple juice ɗin da ke aje a wajen, ya kar'ba yana ci yana ɗan danna wayarsa.
Itama sai ta koma gefe tana kallo, bai tambayeta ina Fulani ba, dan yasan tunda baiganta ba to yau itace keda turaka, ya kai hannu ya tura sumar kansa baya, wadda daga ƙasa wajen fade ɗin ta dan taru, alamar yana bukatar aski, gashi kuma a haɗejia babu me iya askin sumarsa, ko a lagos ɗinma yana manege ne kawai.
Babu inda ake masa aski me kyau, irin wanda yake so kamar a india, idan de yaje shi to dama sumarsa ƙalau zai dawo da ita, kuma cio8 kalar askin da yake SO.
“Canza mana wanna tashar mana”
Nadra ta juyo ta kalleshi kamar zata fasa ihu, dan serice ɗin da take so ake haskawa a mbc bollywood, yau suna hidimar biki bata samu ta kalla ba, shine yanzu take ganin maimaici.
“Ayya mana hamma, ban gani bafa da yamma”
“shikenan ci gaba dakallon ki”
Ya faɗi yana ci gaba da cin abincinsa, dan dama kallon ba damunsa yayi ba, kawaide harufan larabcin ne suka ishi kunnensa.
“Lokaci na ƙurewa kije ki kwanta”
Muryarsa ta fito bayan wani lokaci
“Bari to a gama......”
Wani kallo da ya mata ne yasa ta haɗiye maganar a cikinta, gashi ya kafeta da shuɗayen idonsa, dan haka ƙafarta a likafa ta ɗauki wayarta zata tafi ɗaki, sai ta tsinkayi muryarsa.
“Ki dawo ki kashe kallon”
Tafida bawai a fuskarsa yake da kwarjini ba kawai, hatta da muryarsa kwarjini gareta, da wuya yayi maka magana ka musa masa, dan haka ta dawo ta kashe sannan ta nufi ɗakinta tana masa mu kwana lafiya.
“Sleep tight”
Daga haka shima ya miƙe yabi bayanta, ta wuce parlon ta shiga na gabansa, yayinda shi kuma ya buɗe ɗaya daga cikin ƙofofin dake parlon, wanda shine ɗakinsa.
A bakin gado ya zauna yanajin wani abu na taso masa, jin abun na neman fin ƙarfinsa Yasa ya cilla wayarsa kan gado inda ɗayar ma take, ya dafe kansa yanajin maganganu na yawo a kan nasa kamar kullum, sai yaji gaba ɗaya ɗakin na juya masa.
Sai kawai ya rintse idonsa yana san yayi addu'a kamar kullum, saide ya kasa kamar Kullum ɗin, da wani irin sauri ya buɗe idonsa, tuni ya sauya kala zuwa ja, wata iriyar ƙara ya saki, wanda ta saka bakinsa buɗewa.
A hankali wannan doguwar fiƙar take sauƙowa daga haƙwaransa na sama, ya fita a hayyacinsa, sam baya ƙarƙashin ikon kansa, ya dawo under control ɗin baƙin ruhin nan, miƙewa yayi da sauri, Nan take ƙafafuwansa suka rabu da ƙasa yayi sama, sai kuma aka bugashi da bangon gabar, aka dawo da shi na yamma, kansa duka ya fashe sai zubar jini, wani irin ƙara da kururuwa yake, gaba ɗaya ya sauya ya zama dodo.
Nadra dake zaune a ɗaki ta fashi da kuka, ta tashi ta kulle ɗakinta, gudun kada ya shigo ya illa tata.
Yau abun nasa yayi ƙamari, dan glass ɗin balcony ɗin ɗakin ya fasa ya fita cikin wani irin tsalle wanda yafi ƙarfin ace normal mutum yayi shi, ya ɗale saman rufin turakar Fulani khadija, ya saki wata iriyar ƙara, kamar wani zakin da yayi nasara akan wata dabbar daya farauta, kuma haka sautin ƙarar tasa yake fita, kamar na kura ko zaki kuma kamar na gwagwan biri, yana yi yana yakushin jikinsa.
Fulani sadiya dake maƙale a jikin tagar ɗakinta ta saki wani miskilin murmushi, ta tako ta juyo zuwa cikin ɗakin nata tana kallon Galadima.
“Shi ɗin ne ko ?”
Muryar galadima ta tambaya
“Shi ne, da waye dodo a masarautarnan idan ba shi ba ?”
Tayi maganar a sigar tambaya, amma kuma ba tambayar bace, dan daga ita har Dan nata sun san cewa Tafidan ne
“Ai bazan taba barin Tafida ya zauna lafiya ba, sai naga bayan Tafida da duk abinda yake taƙama dashi”
Ta ƙarashe da wani bussashen murmushi a fuskarta.
“Ɗaxuma na ganshi, sai wani faɗi yake yana taƙama kamar wani ubansa shi ne sarki”
Fulani tayi wani kasaittacen murmushi
“Ko ubansa Tafida bai isa ba, bare shi karan ƙaɗa miya”
“hakane mama, nasan zaki iya”
“dole ne gobe na aika jakadiya taje ta amsomin wannan laƙanin, dan ba a bori da sanyin jiki”
“shi yasa a kaf duniya bani da wata kamar ki”
Fulani tayi dariya cike da nishaɗi.
MARYAM POV.
Tunda suka baro event center ɗin kai tsaye gidan Anti Fati suka wuce, ta ɗauki hijabinta ta mayar, har wata ajiyar zuciya tayi ta nutsuwa bayan da hijabin ya rufe jikinta ruf.
Anti Fati tace mata ta zauna taci abincin dare amma sai taƙi, tace yau dambu sukayi a gida dan haka shi za taje taci, Anti Fati tayi ƙorafi akan me yasa bata kawo mata dambun ba, dan inde Maryam ce tayi abinci to baya kwantai a gidansu, kamar wani abune a cikin hannunta idande tayi girki to babu makawa zaiyyi daɗi.
Da zata tafi Anti Fati ta bata kuɗi da wasu kayan abinci wanda ta tambayi mijinta akan zata bawa Maryam ta kaiwa Maanmu idan tazo, kuma ya amince hardama ƙara mata da kuɗi.
Ta rakota har bakin titi ta hau adaidaita, Imran sai kuka yake akan sai ya bita, dan wata ƙauna Allah ya saka a tsakanin ita dashi, wasu lokutan ma Anti Fati ɗin kance da ace Maryam tayi aure to da cewa zatayi Imran ɗanta ne, yaron yana bala'in kama da ita.
A bakin ƙofar gidansu ta iske Sanata, tana ganinsa ta haɗe rai ta ƙarasa ƙofar gidan, shi kuma tunda ya hangota yake washe baki, dama ya aika yaro ance bata nan, shi ne ya tsaya yana jiran dawowarta, dan yasan bazata wuce magariba ba zata dawo.
Ciki-ciki ta gaisheshi, ya amsa mata da fara'a.
“Rannan kinga ban zo ba ko ?”
Taƙi tace komai ta kawar da kanta gefe
“Maryam ya kamata ace kin faɗa min wani abun ko hankalina zai kwanta, ki faɗamin ra'ayinki a kaina dan Allah”
Maryam tayi ajiyar zuciya
“Sanata inaso kayi haƙuri, a gaskiya yanzu banjin zan iya aure ko kuma sarmunta, kayi haƙuri burina shine na gama karatuna, so dan Allah kayi haƙuri ”
Sanata baiji komai a ransa ba, dan tayi masa magana ne cikin lallashi da kuma nutsuwa irin tata.
“Shikenan Maryam, babu komai zan jiraki har zuwa lokacin da Allah zai sa ki fara tunanin aure”
“nagode daka fahimceni”
“kada ki damu Maryam, ni a koda yaushe me fahimtar ki ne, na barki lafiya”
Maryam ta gyaɗa masa kai, yayinda yake barin ƙofar gidan nasu, Allah ya sani bawai san Santane batayi ba, ita kawai yanzu bata da niyyar yin auren ne, burinta shine ta gama karatu, ta nemi aiki sannan ta ɗauki nauyin mahaifiyarta da kuma ƙannenta, amma ba dan baka ba babu abinda zai hana taso Sanata, domin bashida wani aibu.
Ta ayyana hakan a rantane ba tareda ta san ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta a gobe ba, kaddarar da zata sauya rayuwarta har ƙarshe.
Da sallama a bakinta tashiga gidan, kuma tun daga soro take jin hayaniya da yawa, hakan ke nuna mata cewar baƙi sukayi, ta saka kai cikin gidan tana bin mutanen gidan dake zaune akan tabarma a tsakar gidan da kallo, Maanmu ce itada Muhsin, Hassan, Hussain sai wani Abbalele, ɗan ƙanwar Maanmu wanda yake sa'an su Hassan, kuma dama yana zuwa gidan jifa-jifa.
Ta ƙaraso tana amsa gaisuwar da Abbalelen ke mata, ledojin dake hannunta ta aje a gaban Maanmu tana faɗin
“Maanmu gashi wai injin ya habib” Maanmu ta buɗe tana ta saka masa albarka
“aa yaya kwalliya kikayi ne?”
Maryam taja ta tsaya tayi tunanin da tayi alwala kwalliyar ta koɗe, ashe bata fita ba, banza tayi da Hussain dake mata tambayar ta shiga ɗaki ta saka wata doguwar rigar atamfa mara nauyi ta fito tayi alwala.
Dan zuwa lokacin an fara ƙiran sallar isha ta koma ɗakinta tayi sallah, tana zaune akan sallaya aka ɗauke nefa, bata ko gamayin addu'o'in data saba ba, ta fito daga ɗakin a guje, Allah ya sani tana da bala'in jin tsoro, musamman ma na duhu.
“Ke Maryam lafiya?”
Maanmu ta faɗi tana kunna fitilar dake aje a gefenta, kamar da tasan za'a ɗauke wuta, ta fito waje da ita, sannan ta aje ta a gefenta.
“Babu komai”
Muryarta ta fito cikin ƙoƙarin seta kanta
“Bari naje gidan Iya” (Wato kakar Badar).
Ta faɗi tana saka takalmanta
“Kada ki daɗe fa! ”
“To”
Ta amsa lokacin da ta kai ƙofa
“Tsorata fa tayi”
Hussain ya faɗi yana dariya ƙasa-ƙasa
“Nasani ai, ban san yushe Maryam zata dena jin tsoro ba, ita tsoron nata yayi yawa”.
*
“Ke wallahi kallo yayi kyau, da kika ƙi zuwa in faɗa miki anyi ba ke, Tafida yayi hawa kuma na ganshi dan ma ya rufe idonsa da sun glasses shi yasa ban samu damar ganin his beautifull blue eyes ba”
Maryam taja tsaki, tana mitar ita ko fidar yarane ma ina ruwanta ballan tana wani can waishi Tafida.
“Baki ce komai ba”
Badar ta faɗi tana ta'bata ganin tayi shiru
“Me kike so nace ?”
“say something mana”
Sai ta girgiza kai “I have nothing to say”
“Ai shikenan”
“Ke mu ki kunna mana vedion mana”
“Wallahi kuwa harda yanda ake biryani na ɗauko”
cewar Badar tana buɗe wayarta kirar sumsung.
🌸-SAI KASKA CE-🌸.



⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐️
⭐️ شاء القدر⭐️
©-By Sai Kaska
My wattpad page@Sai_Kaska
*proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*BABI NA GOMA (10)
*washe gari, juma'a*
*Titin barikin sarki, hadejia emirates*
* Da misalin 10:00am*
Ga duk wanda yasan bayan tsohuwar perison, dai-dai kan titin bariki yasan cewa wajen zaman ƴan cacane, mutane masu shekaru harda waɗan da suka fara furfura ne ke zaune a wajen ana kalander, ga kuma masu buga karta, sai hayaniya suke ga warin sigari na tashi a wajen dan ɗaiɗaikune basa busa hayaƙin a wajen, cikin masu busa hayaƙin harda Tijjani direba.
“Tijjani bani kuɗina!”
a hankali Tijjani ya ɗago da kansa ya kalli Wasila, ƴar da batako kai sa'ar yarsa ta biyu a haife ba, amma kalli yanda take wani ƙifi-ƙifi da ido dan tsabar rashin kunya, kuma babu wani baba gatsal ta kira sunansa.
“Haba ƴar Wasil-Wasil, kinsan idan na sam.....”
“Wallahi baka isa ba, kuɗina zaka bani yanzu”
Ta katseshi tun kafin ya ƙarasa maganar, Tijjani ya miƙe ya shiga bata haƙuri, harde ya samu ya kashe bakinta da nera ɗari ta haƙuri ta koma rumfar da take saida abincinta tana aiko masa harara.
Kafin ya zauna wata mota tazo tayi parking a daidai inda suka, gaba ɗayan su suka bi motar da kallo, dogarai suka ga sun fito daga motar har su Uku, gaba ɗaya kowa ya miƙe yana kwasar gaisuwa, dan da gani babu tambaya kasan cewa daga fada suke
“Waye Tijjani anan?”
Wani dogari ya tambaya cikin wata garjejiyar murya, cikin Tijjani ya tsure ƴan hanjinsa suka kaɗa, kadafa ace sarki yayiwa laifi.
“Gashi nan”
Muryar Lautai ta fito yana nuna shi, abokin cin mushen nasa, Tijjani yayi tsilli-tsilli da ido yana binsu da kallo.
“Zaka biyomu muje fada, sarki yana nemanka”
Cikin Tijjani ya ƙara kadawa, har ɗan wani guntun fitsari na suɓuce masa, shiko me zaisa sarki ya nemeshi ?.
“Ko bakaji bane!, ance kada mu maka dole, dan haka salin alin ka biyomu”
“Lautai bari naje na dawo”
Tijjani ya faɗi yana kallon su Lautai, suka gyaɗa masa kai, haka Tijjani ya nufi motar, suka buɗe masa gidan baya ya shiga, ɗaya dogarin ma ya shiga ya zauna, ɗaya ya zauna a mazaunin

Please Login or Register in order to submit comment