Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shadda wadda aka mata paint work mai tasadar orange ce akayi mata kwalliyar light blue,body spary kawai ta fesa ta daura dankwalinta ta debo magungunanta wadanda zata sha da rana ta fito falon,rabi'ah ce da sumayya da anty hauwa,cikin fara'a suka gaisa suka mata sannu da jiki"tace ai na samu sauqi ina momy da iftihal mutuniyata,anty hauwa tace suna gida gurin momyn nace ne ba da wanda zanzo duk har su kausar suna gunta muhammad ma tunda ba nono yake sha ba acan na barshi don suna zamu wuce dqga nan wata maqwafciyata ce ta haihu to kuma da yake haihuwar ta danzo da matsala a gidan su take acqn za suyi taron,tace eh Allah ya qara mata lpy,amin inji anty hauwa
Nan suka shiga hira abinsu minti talatin suka miqe suna shirin tafiya fadila dake ta qoqarin zuba musu abincin tace anty ga abinci don Allah ku tsaya kuci,anty hauwa tace bayan lemo da cake da kika cika mana ciki da shi alhamdulillah wlh,rabi'ah tace nikam anti fa na fasa rakiyar nan gidan sunan kuce da maman hidaya ina mata barka na taho anjima farida ta saukeni a hanya,sumayya tace"dama na sani anti ba rakaki zata yi ba ina ji tana cewa yau ana rana da yawa nasan dama daga nan gidan ba inda zata dara"aishikenan muje mu gaisa da samirah sai.mu wuce,inji anty hauwa,sumayya ta coge😒sannan tace a'ah anty nikam zan jiraki cikin mota ki shiga ki fito tayi saurin yin gaba damma kafa antin ta tsayar da ita,fadila tace "baki kyauta ba sumayya idan kika wuce baki gaidata ba"rabi'ah dake zaune tace wlh anty ko nice ba zan je ba,farida dake ta faman cin abincinta abunta tace qyalesu sister mai daki shi yawan inda yake masa yoyo✋🏻,ai kuwa dai sister farida sai.kaje kayi ta bugu taqi budewa gashi fa kana kallo ta tana kalloka qiri qiri,bayan kuma ta bude sai tayi.bake bake a bakin qofa ta tsare ka da ido tana wani ce maka meye?kamar wanda kazo maula gurinta,duk suka kwashe da diyar yadda rabi'ah ta gwada yadda samiran keyi banda fadila da ta dan murmusa gami da girgiza kai tana mamakin halayya irinta samirah
Biyar da rabi farida ta dauki rabi'ah suka tafi suma sashen sai ya dawo sai ita kadai ta so ta yiwa farida zancan dawowar maman iftihal sai kuma taga mai hakan zai dadeta da shi iyaka ta taya ta jimami sai shawara wadda a yanzu ita ma bawa kanta da kanta take,tunanim data fara yin zurfi a ciki ne yasa barin kanta ya soma ciwo bata yada hakan yayi zurfi ba ta tashi ta jona home theatre dinta ta saka cd plate na karatu ya karade falon

Takwas da mu
mintina na dare nasiru ya turo hancin motar ogan nasa cikin gidan,ya samu parking space ya daidaita tsayuwar motar sanna ya kasheta,a hanzarce ya fito ya budewa aliyu shima ya fito sannan ya miqa masa keys din motar yana fadin gashi sir ya amsa yana cewa debo min files din nan na sit din gaba,ya debosu ya bashi sukayi sallama aliyu ya sallameshi,hankalinsa gaba daya ya yi gaba burinsa kawai ya isa sashen nasa ya watsa ruwa a jikinsa ya samu ya kwanta ya huta,ya soma tafiya idanunsa suka kai kan sashen nata babu wadatar haske kamar bangaren samira dake tarwai da haske harda qarar abin kida ya dauke kai ya shige

Yana fitowa daga toilet ya zabi doguwar riga jallabiya fara sol.mai yankakken hannu ya saka ya feshe jikinsa da turarukan baccinsa masu sassanyan qamshi kan sofa ya fada ya miqe qafafunsa sannan ya hardesu ya kansa na kallon sama yasa daya hannun nasa ya shafi cikin sa,yunwa yakeji amma ya rasa inda za shi ya samu abincin da zai gamsar da shi,mutum ne shi.mai tsan tsami ba ko ina yake iya saki jiki ya ci abinscinsu ba sai ya yarda da ingancin tsaftarka hakan ne yasa ya tsani masu aiki hakan yasa tun yana gida ya yi ruwa yayi tsaki ya hana mominsa daukar masu aiki yace meye amfani su sumayya duk da suma bai yarda ko kadan yaci girkinsu sai na mominsa

Ya tashi ya qarasa fridge ya bude ya dauko yoghurt na l&z ya hado da fura ya samu cup ya dama ya sha ,ya sake tashi ya maida cup din kitchen sannan ya qarasa window dinsa yana bude glass din don ya bawa iska daman shigowa duk da iskar a.c da ta mamaye dakin kasancewar mutum ne shi maison natural air,idonsa ya sake fadawa kan bangaren nata duk da yaune ya shigo bashi da niyyar ganin kowa bacci yakeso ya samu isashshe don haka har wayoyinshi ya kashe su gaba daya
Ya saki labulen yana ajiyar zuciya saboda tunawa da yayi haqqine a kansa ya kula da lafiyarta don rabonsa da ita tun jiya da ya batta da magungunan da ya siyo mata ,ya zari keys dinsa ya zura slippers dinsa ya fice

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶1⃣9⃣

Tana kwance a miqe sambal bisa kujera three sitter don tunda tayi sallar isha'i bata tashi ba agun falon tsit yake ba komai sai sanyin na'urar sanyaya daki wanda ta gauraye da qamshin freshner mai dadi idanunta na lumshe ne tamkar mai bacci saidai ba bacci take ba tayi nisa ne a wata duniya mai wuyar fassarawa duk da ciwon da kan yake mata das das das amma hakan bai dameta baqarar bude qofan falon da qamshim mayen turarensa dake rataye da zuciyarta shi ya dawo da ita,ta bude manayan idanunta akansa yayin da shi kuma ke qoqarin tura qofar tayi namijin qoqarin tashi ta zauna kanta na sunkuye a qasa don ba zata iya jurewa kallonsa ba,hannayensa ya goye a bayansa ya qaraso falin yana kallonta da qayatattun idanunsa ya lura kamar ta dan rame duk da ba sanin ainihin kamanninta ya yi ba"ina yini"tace still kanta na qasa,cike da qasaitarsa da izzarsa ya dauke kai ya maida mata gaisuwarta da tambayar jikinta,da sauqi ta fada cikin sassanyar muryarta data sanya yaji wani dan yam ajikinsa

Bata zata ba bata kuma tsammata ba sai jinsa tayi zaune kan kunerar da take kai.kuma dab da ita ya sanya bayan hannunsa a wuyanta da niyyar jin temperatures din jikinta ba komai aransa,sai dai baisan illar da ya sake yiwa fadila ba a zuciya da gangar jikinta ba,kasala mai tsanani tashi guda da kuma wani irin shauqi taji ya saukar mata numfashinta ya tsaya cak na wucin gadi,sam bai kulaa ba yace"still jikinki da ragowar dumi ya kamata ki warke kafin isowar abokiyar zamanku right?ya qare maganar da sigar tambaya,ya.miqe yana cewa babu abinda kike buqata,tamkar ta ce masa"kai nake buqata aliyyu ka qarashe awoyin wannan daren naka tare da ni,maimakon haka sai ta sake gyada masa kai,yace " alright gudnyt"ta bishi da kallo idanunta fal cike da qaunarsa da kewarsa har ya fice daga part din nata ya rufe mata part din,ta koma da baya ta jingina jikinta da kujerar hadi da runtse idanunta hawayen dake maqale a idonta suka gangaro mata wani radadi da zugi zuciyarta ke mata lallai kishi masifa ne

Cikin daren bacci gagararta yayi juyi take kawai akan makeken gadonta cike da sha'awar aliyu tunda take bata taba jin makamanciyar sha'awa arayuwarta irin wannan ba
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Sannu a hankali ta miqa dukkan lamuranta ga Allah cikin ikon sa kuwa ta fara samun sauqinsu saidai fa har yanzu babu sauqi ta bangaren soyayyar Aliyu dake maqare cikin zuciya ,cikin lokacin sam ta daina bari idanunta suga aliyyu duk da tarin zugi da zullo da zuciyar keyi na son ganin nasa amma ta danneta

Cikin lokacin aikinta ya samu freedom da express din duk suka buqaci yin aiki tare da ita,ya ahmad dinne ya kawo.mata da kansa bayan ya sanar da aliyu da kansa ya kuma amince mata da fara aikin nata,tayi murna tayi tsallae tun a gaban ya ahmad din ya sha godiya sosai har da qwallar farinciki saboda yadda take masifar son aikin jarida shikam dariya yayi yace Allah zata godewa,bayan tafiyarsa ta kira farida dake fama da laulayi suka sha murnarsu tare,nan fa ta zauna ta soma tsarawa kanta yadda zata tafi da rayuwar aikinta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Cikin satin Aliyu ya shirya musu fita wadda ta farko ce agun fadila don bata taba fita ba wani gu da sunan unguwa ba bayan shopping da suke zuwa duka qarshen wata za suje ne gaida hajiyarsa

Tun rana fada ke zumudin fitar tana tunanin mai zata kaiwa momin,akwatunan lefenta dake shaqare da kaya wadanda kamar ba'a taba amfani da komai a ciki ba ta bude ta zabi turarurruka designers guda uku ta warewa abba,ta duba akwatinta da ta adana gift da ta samu na biki ta cirarwa momin atamfofi super Holland da England guda biyu,da kanta ta aiki yaron dake musu gyaran flowers ya samo mata kilishi mai kyau da zuma

Tun magariba ta yi wanka ta shirya kanta cikin atamfa dinkin riga da zani kamar light grean da milk sai ratsin baqi dinkin ya mata cas kamar a jikinta aka qirqireshi yari da sarqa ta saka ma dutse masu kalan milk sai farin agogon hannu tq zuba awarwaro mai 24 farare takalmi da jaka milk sai laffaya data nannade jikinta da ita milk ce mai adon baqi ta debi tsarabarta ta dawo falo ta kunna arewa 24 tana kallon shirin matasa at 360,tayi wani masifar kyau ta fito sosai a babarbariyar ta

Ya qarashe karin hular sa yana daidaita ta a kansa shaddace fara qal a jikinsa dinkin tazarce sai walwali take ta sake fidda sirrin kyawunsa mutum ne shi ma'abocin iya ado ta wannan fannin kam ko mace haka ta ganshi,komai nashi fari ya sanya hatta da agogo,ya sanya glass dinsa sanna fesa turarensa ya rufe sashen

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

▶2⃣0⃣

Bangaren samirah ya nufa wanda sai ta kama dole yake shigar sa,ga mamakinsa aai ya taddata sirshan tana zaune abinta zaninta da rigarta daban daban kanta da ta tsefe shi yana tsaitsaye kamar tabarya😜dama ita ba wani tsawon gashi gareta ba sai qarfi da gashin yake da shi,ba abinda falon keyi saiqarnin kifi sardine ta tara gwangwanayen a gabanta ua daurw yadda qarnin ke bugar hancinsa yana tayar masa da zuciya cikin bacin rai yace mata zaman me kikeyi baki shirya ba tun dazun?ta dan yatsina fuska tace qawatace wlh ta kiarani a waya ta kwasheni da jira ya gyara tsaiwarsa cike da qosawa da azababben qarnin kifin yace mata is ok sai ki nemi wanda zaku tafi tare kinsan bana jira yana kaiwa nan ya sanya kai zai fice yana jan tsaki cike da takaici ,ta yi saurin shan gabansa tana cewa haba sweet kayi haquri mana pls ka bani minti uku kaya kawai zan canza,ya kauce ya fice yana cewa wataqila idan kinyi sauri kin tadda ni kafin in ciro mota is ok,ya barta nan baki a sake ta bishi da kallo sai kuma ta zabura tayi cikin daki don ta shirya

Knocking taji anayi don haka ta zira hill shoes dinta fari ta rataya jakarta ta dauki ledarta don jikinta ya bata aliyu ne shi dinne kam idonsa na bisa screen din wayarsa yana danne danne bai dube ta ba ya juya taja part din nata ta kulle tabi bayansa tana qare masa kallo"ya gaji da haduwa"ta zanta hakan a ranta,tana jingine da rumfar ajiyar motoce har ya gyara parking qa'idarsa ne indai tare zasu fita baya neman driver duk da dama nasiru ne kawai.ke driving dinsa,wanni dogon hirn ya ja da sauri ta daidaita nutsuwarta ta nufo motar tun kafin ta qaraso taji an bangaji kafadarta da mamaki ta dago don ganin waye samirah tana ta zuba sauri zani a hannu tana gyara daurinsa,duk saurin da take gidan gaba aahe takewa,abun ma sai ya baiwa fadila dariya ta saki murmushi😊

Cikin mintuna da basu gaza talatin ba suka qaraso gidan,harabar gidan tsaf kuma fetal da haske ba kowa sai mai gadi shi da wasu mutum biyu zaune kan benci suna sauraron duniya tumbin giwa suna cin gyada jefi jefi suna taba hira,cikin girmamawa ya gaida aliyu sannan ya gaida su fadila ta amsa masa fuska a sake tunda dama da yar sanayya tsakaninsu ya samirabko kallo bai isheta ba bare tasan yana yi,ya dage masa get din ya wuce ya yafitoshi yayi masa ihsani kamar yadda ya saba shi da wadanda ke zaune a gun suka hau zuba godiya abinsa shi kuma baiso

Samira da aliyu suka jera suka fara yin gaba zuwan falon gidan fadila bin bayansu tayi ,sumayya da rabi'ah ne zaune a falin da hijabai ajikinsu da alamar sallar isha'i suka idar,suka juyo suna amsa sallamar sannan suka miqe tsaye cikin farin ciki suna gaida su hankalinsu na kan fadila itama su take kallo suna gaisawa sabanin samirah da ta riqe qugu tana qarewa falon kallo tana yaba tsaruwa da dukiya da ya lashe kamar wadda aka bawa kwangila sannan daga bisani ta zabi kujerar da tayi.mata ta zauna akai,cikin dakiya irin ta babban wa yake tambayarsu ina momy sumayya tace tana sama ya nufi benan taku biyu uku sukayi kacibus da iftihal na saukowa kamar yadda ta saba ta tsugunna ta gaidashi sanna ta daneshi ya sabeta a kafada yana tambayarta momi

Tare suka sauko shi da momin yana take mata baya iftihal na hannunshi ganin fadila ya sata ta zille ta diro ta nufeta a guje cikin murmushi fadilan ta tareta ta dora ta bisa vinyarya dukkaninsu suna dariya ta gaisheta,duskar momi washe da fara'a take.musu barka da isowa samira dake zaune dare dare bisa kujera kamar tata tave yauwa fadila dama.na qasa ne kan carpet ta duqar da kanta qasa tana murmushi cike da kunyar momin,gaisuwa aukai da samirah kamar qawa da qawa yayin da fadila ma ta kasa hada ido da ita a haka suka gaisa,ganin taqi sakin jiki ya sa momyn tace su rabi'ah su kaisu dakinsu itama zata gun abbansu yanzu ya shigo gidan,hira suke abinsu da fasika yayin da samirah ta zaro wayarta ta hau danne danne tana ganin duk ta girmesu tafi qarfin zama cikinsu ai,ga takaicin yadda aujewa fadila haba haba itq aunqi mata haka cikin ranta take cewa hmm dangin miji kenan tsinannu(kunji fa?)

A haka bacci ya dauki iftihal akan cinyar fadila aliyu ne ya leqo hukarsa a hannu yace ke sumayya ku taho dining"samrah ce ta fara miqewa tana cewa dama yunwa nake ji ta fice,qememe iftihal taqi kwanciya dole iftihal na nishi ta sabota a kafada suka fito su sumayya nata dariyar yadda ta dauki ifrihal din da qyar,momy ce da abba sai aliyu bisa dining din kusa da abban abba na dariya yaceyau ban dawo da wuri ba bare a murqushen tsohon
qashi na shine aka rama akanki ko?

Duk sukayi dariya kowanne ya samu kujera daya ya ja ya zauna banda fadila dake tsaye sabe dà iftihal wani baccin nason daukarta amma ta qi yarda tayi don kada a sauketa

Mrs muhammad ce

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻





🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣1⃣
Momy ta kalli aliyyu tace alii rabata da rigi mammiyar yarinyar nan don idan ba kai ba ba wanda zata yarda ya sauketa,ya miqe ya nufesu yanayin yadda ya tsaya gab da ita yana yunqurin karbar iftihal ya haifar mata da wani yanayi cikin jikinta,ya sa hannu zai dauketa cikin rashin sani hannunsa ya shafi qirjinta wani abu taji ya tsirga mata tun daga kanta har tafin qafafunta hakanan shima yaji tsigar jikinsa ta tashi wani shocking yaji kamar an jashi da wutar lantarki,ya sabata a kafadarsa ta miqe zata soma rigima suna hada ido da shi tayi gum da bakinta🤐 ta mayar da kanta kafadarsa ta kwantar ya sauka da ita cikin falom ya kwantar da ita bisa doguwar kujera ya karanta mata addu'o'in bacci na tsari ya tofa mata sannan ya koma
Ta tsugunna ta gaida uncle abba ya amsa mata cikin kulawa yana cewa lpy lau diya ta,sannan ta ja kujera itama ta zauna,sumayya tayi serving din kowa🍽🍴 sannan akai bismillah aka fara ci,kwata kwata kasa sakewa fadila tayi ta kasa kai koda loma guda bakinta sai juya cokalin kawai take a cikin abincin ,amma ga tarin mamakimta sai taga samira ta saki jiki tana ta kaiwa uwar hanjinta🍜 harda tsiyaya lemo 🍹🍾da ruwa da kanta,tayi sakewar da ko ita da uncle abba yake kamar uba a gareta ba zata iya irinta ba
Abinka da mata momi na ankare da yanayin nutsuwar kowaccensu tana kuma sake godiya ga sarki Allah da ya qaddara fadila ta zamo daya daga cikin family dinsu,afakaice rabi'ah ta qarewa samirah kallo uadda take lodar abincinta ko aliyyu da yake dan gida baiyi haka ba,ki saki jiki mana fadilan ummi kici abincin ki mu fa iyayenki ne ko babu aliyu baki ga yadda yar uwarki ya saki jikinta ba?,cewar ummi,samirah ta amshe cikin tabe baki tace momi kinsan wani akwai qauyanci da rashin wayewa atare da shi"sai kowa yayi dif rabi'ah da takaici ya cikata tace ba rashin wayewa bane kowa dai da irin yanayinsa,ta sake tabe baki tace uhmm,ita kuwa fadila dariya ma ta bata sai daga qarshe ne taga kada suji ba dadi ta kurbi lemon da rabi'ah ta zuba mata
Bayan sun kammala momi tasa rabi'ah da sumayya suka gyare gurin suka kwashe kwanukan,suna shirin wucewa don su basu guri momi tace su dau iftihal su wuce da ita,falon yarage daga fadila aliyu samirah sai momi da uncle abba
Abba yayi gyaran murya yayi bismillah sannan ya kirawo sunan aliyu ya amsa masa"naam abba"ya dora "aliyyu girma yanzun ya hau kanka duk da a baya kwatan kwacin wannan girman ya taba hawa kanka kuma kayi namiji qoqari wajen riqeshi yadda ya kamata amma bai kai wannan ba,a yanzu dole na sake jaddada maka saboda zama ne da zaka yishi tsakanin iyalinka har su uku wanda ko ni mahaifinka banyi duk da komai tsarin Allah ne
Daga samirah har fadila babu wadda gabanta bai fadi ba har sai da samiran yabdaga kai ta kalli abban,uncle abba yaci gaba "lamarin mata ali sai da haquri kawaici da kuma jajircewa halitta ce su maau wuyar sha'ani amma idan ka duba Allah sai komai ya zo maka da sauqi ,aliyyu ina horarka da kaji tsoron Allah ka tsaida adalci tsakanin matanka duk wadda ka cuta wlh wlh sai allah ya bi mata haqqinta sai kuma ya tambayeka,kuma ko ni ban lamunci rashin adalci ba acikin gidanka ka riqe Allah ka kuma ji tsoronsa
Ya juyo gunsu fadila da kansu ke qasa kowa da abinda ke cikin zuciyarta yace "dukkaninku ina kallonku ne a matsayin 'ya 'yana na na cikina da na haifa nasihar da zan muku itace kuma ku ji tsoron Allah kuyi zamqn aure a matsayin ibada kuyi biyayya ga mijinku.ku kyautata zamantakewar ku domin kuwa shine muqullinku na shiga aljanna ko wuta idan kuka saba masa Allah ya tsare mu,magana ta biyu kuma na dakatar da shi ne daga gaya muku don inason na gaya muku ni da kaina ta hanyar da ta dace,nasan kowacce mace haka Allah ya halicceta da kishi kuma ba zaku so abokiyar zama ba a yanzu amma ba yanda muka iya da hukuncin ubangiji kuma aure rai ne da shi matuqar bai qare ba komai dadewar zamani sai an dawo anci gaba da yinsa to ina mai baku haquri a madadin aliyyu,mahaifiyar khadija(sunan iftihal na gsky haka abba ke kiranta yawancin lokuta)zata dawo dakun aurenta ina fata zaku hada kanku ku zauna lpy,samirah ta dago kanta a gigice tana fiddo da idanu waje😳tace"abba mai kake fada ne?dama da gaske aliyu yake da yafara zancen?" aliyyu ya juyo ya kalleta wani huci ya saki abba ya lura da yadda yanayinsa ya canza ya san yadda fishin aliyyu yake don haka ya danne shi,cikin tausasawa ya kalli samira yace ki kwantar da hankalinki yata insha Allahu ba zaku fuskanci rashin adalci ba daga gun aliyu ni kaina bazan lamunci hakan ba shiru tayi tana muzurai idonta ya kada yayi ja saboda ganin yadda aliyu ke gasa mata hara ra tamkar zai cinyeta danya,itakam fadila gabq daya jikinta ya saki tunaninta daya ta ina zata samu aliyyu bayan ga wasu na farautarshi ? Jin sunyi shiru dukkaninsu abba yace da momi"kina da magana momin yara?" Ta danyi murmushi tace" aikace komai abban yara,saidai nace aliyu kaji tsoron Allah kamar yadda abbanka yace sannan ku kuma Allah yayi muku albarka kuyi haquri kuma kuyi biyayya sai.kuci riba"suka amsa da amin banda samira da ta kasa furta komai sai tafasa da zuciyarta keyi,abban ya sake basu dama akan idan da mai magana ya yi,ba wadaa tace komai sai aliyu da yace"abba da momi na gode muku kuma insha Allah zaku sameni mai amfani da duk nasihar da kuka yimin zan zamo mai adalci da yardar Allah"Allah ya amince suka ce,fadila ta fito da kayan data taho musu da su ta dorawa abba nasa a gabansa sann ta dorawa momi nata
Duk da ranta babu dadi amma ta ji dadin yadda suka nuna jin dadinsu suka sa mata albarka,aliyyu kansa can qasan zuciyarsa yaji dadin hakan don shi mutum ne mai dake qaunar wanda ke kyatatawa iyayensa,haushi ya sake cika samira tayi dana sanin zuwan ta gidan yafi sau cikin carbi bata son taga wani yana yabo ko son fadila kwata kwata
Cikin mota ma kowa da irin zaren da yakr saqawa zuciyarsa shikam ya dake abinsa kamar bashi ya sanar da mata har biyu zai qara musu abokiyar zama ba tuqinsa kawai yake a nutse,fadila tata saqar na yadda zata juyo da hankalin aliyu take bata so kuma bazata so ace kishiyoyi har biyu su fuskanci raahin qauna da jituwa dake gudana tsakaninta da shi ba,samira kuwa wani mahaukacin kishi ne ke taso mata zuciyarta namata saqa da baqin zare,tana shirya mata irin mummunan matakin da ya kamata ta dauka abu guda ke taka mata burki idan ta tuno yadda aliyyu ya birkice mata da yanayin da ya sameta a daren farkonsu tasan har yanzu dafin na sukar zuciyarsa somin kuwa duk wani tanadin soyayya da sukayi wa juna tn daga ranar ya rushe,duk kuma waa qauna tata dake zuciyarsa wadda ta rage tuni ta rushe
Cikin satin komai ya fara kankama abubuwa suka cedewa baiwar Allah fadila ga zirga zirgar shirye shiryen fara zuwa aikinta ga kuma lamarin na dake mintsinin zuciyarta duk da shiryr shiryenta ya tafi da kaso.mafi tsoka daga damuwar dake cin xuciyarta,tuni tayi waya gidan an ma motocinta service daya tsohuwar tata ce tun ta gida aka sake mata fenti da wasu abubuwa sai ta tashi ta dawo sabuwa dal don tana qaunar motar bata son rabuwa da ita yanzu sai kuma wadda aliyyu ya sa musu a lefe wadda ta sam ira tuni ta dade da cin uban tata ta mora qawaye su ara suma su mora
Kira ta dinga samu daga su anty hauwa anty hafiza har da farida kowannan su nasiha ce da jan hankali ne nasa har farida ta so karayar mata da zuciya saidai tayi qoqari matuqa wajen nuna dakiya da mai da komai ba komai ba
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
▶2⃣1⃣
Samira kuwa abun nata sai ya zamto tamkar mai qaramin ciwon hauka kamar a kanta aka fara kishiya kasancewar ta samu gudun mawar zuga daga qawaye da yan uwa kala daban daban duk da wasu ba don Allah suke bata basuna baqinciki da rufin asirin kawai da take ciki ne(qalubale a garemu mata sai azo ayita baki shawara akan za'a miki kishiya ko wani harkar wani ahaka kamar mai sonki amma da zaki ga cikin zuciyarsa game da ke tsoronsa ma zaki koma ji,sanin haqiqanin mutum sai Allah,sai ki auna da hankali da Allah ya baki a matsayinki na mutum mai tunani)sai ta sake zama kamar zararriya ita kadai ma abangarenta sai ka jiyota tana bala'i tana zunduma ashariya(wa'iya zu billah)cikin satin baqi ta dinga yi kala daban daban kowanne da tasa guzuri da salon hudubar waccan ta shiga waccar ta fita
Tun Aliyu na zuba mata ido idan tana salon rashin mutuncinta da haukanta har sai da ya zamto idan tazo sai dai ta gajibda bugun sashen nasa ta juya da haukanta ta koma inda ta fito,tuni fadila tabgama tsarawa kanta yadda zata tafiyar da rayuwar aurenta ta gama tanadar komai,tana hango cewar itama fa maca ce tana da duk wani abu da da duk wata ya mave maiji da kanta ke taqamar tana da shi,tana da duk wasu qualities da ake buqatar mace da su kafin ta amsa sunan ta na mace,to me yayi saura banda itama

Please Login or Register in order to submit comment