Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din falo tana wanka taji moysi kadan kadan a falonta,da sauri ta kammala tana son taga waye don a bude tabar bangaren nata,kacibus sukayi da shi tsaye yake tsakiyar falon yana sanye da kufta dark coffee wadda tasha aikin sarauta sai hukarsa baqa abinka da fari sai yayi matuqar kyau kyansa da jaskensa ya sake fitowa shigar ta amshe shi sosai fadila ta lumshe idonta tana jin wani abu na zagaya jikinta"ki shirya na kaiki gida ki masu sallama,gobe zamu bi jirgin yamma insha allah zamu wuce china"duk maganar nan da yake idonsa na kan wayarsa dake hannun hagunsa damansa kuma cup ne cike da maltina mai sanyi🍺,ta dan langabe kai kamar bata ji mai yace din ba"ina zamu je?""kaiki zanyi na siyar"ya fada yana ci gaba da danne dannensa ta faki idonsa ta manna masa harar ta zagayeshi ta wuce zuwa bedroom

A sanyaye ta kammala shirinta cikin atamfa dinkin riga da zan8 simple style hakanan fadila take bata fiya son abimda ya cika ado da yawa ko daukan hankalin jama'a ba yadda take bata da hayaniua haka dabi'unta suke saidai idan ta so,ta lullube kanta da wadataccen mayafi kalar kayan,ta jawo locker dintabta debo kudaden da suke ciki ire iren kudaden da aliyyun ke basu ne duk qarashen wata da kuma na cefane acewarsa tunda komai suna da shi a ajjiye hatta magi ba zasu buqata ba ta watsa su cikin jakar sannan ta rataya ta ta fito,yana zaune a mazaunin driver tasan bata isa ta shiga baya ba ko ya shiga zai maidoto ne gaba don haka ta bude gaban ta zauna,yadan kalleta hadi da dauke kai ya daga glassan motar gaba daya samà ya rufe su ruf hadi da kunna a.c,wani irin tuqi yake slowly tamkar baza'aje ba tayi tsammani zaiyi irin tuqin nan nasa mai gudun tsiya,a hankali suke ratsa titi nan har suka qaraso cikin anguwarsu fadila

Muje zuwa masu karatu🚶🏻🚶🏻🚶🏻🚶🏻

Mrs muhammad ce👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:50 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*part 2*

2⃣3⃣&2⃣4⃣

A qofar gidansu yayi parking,bata ce masa komai ba kamar yadda bai tsinka mata ba,ta bude murfin motar ta nufi bakin get din gidan cikin doki ta dan tsaya suka gaisa da malam mai bude masu qofa idan zasu shige da motarsu

Parlour din babu kowa sai qamshin fresher da ya gauraye da na girki ,murmushi fadilan tayi kai tsaye ta nufi kitchen cikin zuciyarta tana cewa"ummi na bakya tsufa kullum gida kamar na budurwa" (haka haj amina take ma'abociyar tsafta ce da gayu,don bata yarda wai don tana da manyan yara harda jikoki ta zauna haka ba,baka raba qafarta da hannunta da jan lalle mai ado irin na yanzun wanda akeyi,hakanan kullum kalolin girkinta daban ne masu dannkaren dadi hakan ne yasa yaranta sukayi gadonta suma,tun aurensu ita da alhj abbas koda wasa bai taba tunanin qaro aure ba donba cewarsa ta isheshi duk dashi qarin aure qaddara ce rubutacciya idan Allah ya qaddaro maka sai kayi

Muhammad ta tarar ciki riqe da babban spoon na qarfe yana ta faman juya fried rice,dariyar da fadila ta tuntsure da ita ita ta saka shi juyowa don bai ankara da shigowarta ba sai lokacin,ya saki murmushi yace"anty fadila yaushe kika zo?" Ta kama baki"🤔ina zaka san na shigo ka taqarqare kana ta jagwal gwalawa ummi abinci,wai yaushe ma ka fara shiga kitchen?"ya saki spoon dinnyana share zufa a goshinsa"😊 ni wallahi ma gwara da Allah ya kawomin dauki ,please anty karbi girkin nan,haka yanzu ummi kemin ko ta daina sona ne ma oho?,amma don Allah anty fadila ina ni ina wani kitchen?,wai gwara na iya tunda ku kun tafi saura ni da ita kawai a gidan"dariya fadila ta sake saki ,ta qaraso kan girkin tana gyara wasu abubuwa sai da ta hada komai ta rufe ta rage mata wuta don ta turara sannan ta tambayeshi ya haye saman freezer yayi zamansa"ina ummi" "tana gun Abba yanzu ya dawo daga kasuwa ne amma tunda an fara kiran sallah yanzu zaki gansu"

Yana rufe baki kuwa saiga dariyarsu cikin falo,da hannu Muhammad yayi mata nuni da falon cikin salin gulma,dariya ma ya bata ta miqe da sauri ta isa falon,ita da abban ne kuwa yana tsaye riqe da abun sallah ummin kuma na dauke da hularsa,da murmushi suke kallonta ta durqusa ta gaida su abban na tambayarta yanzu take tafe?,ta gyada kai yace masha Allah ya mai gidan?,tace abba tare muke yana waje,"ashshsha banda abin fadila shima ai gidansu ne amma don sakarci kika barshi a waje "ummi tayi saurin qwalawa Muhammad kira tace ya zo ya shiga da shi,abba yace barshi naje na sameshi in yaso idan mun idar da salla sai mi shigo tare,a shirya mana abinci kafin mu shigo din

Ummin ta dan rusuna tana miqa masa hularsa tace"insha Allah abban Muhammad a dawo lafiya"ya karba yana dora ta a kansa yace "Allah yasa Allah yayi miki albarka" cikin dariya yaran suka taya ta amsawa da amin

Sai da fadila ta taya ummin suka shirya komai kan dining sannan suka tafi yin sallah ummi ta ahige dakinta fadila ma tsohon nata dakin ta bude ta shiga,bin dakin tayi da kallo komai yana nan kamar yadda yake,dan fridge dinta na boye ice cream 'yar kwanar da take ibadunta,inda take boye kanta idan zatayi kukan Aliyyu,sai komai yake dawo mata"Allah sarki" ta fada a fili tana shafa filonta da take cusa kanta a qasansa ,qwalla ta dan taran mata a ido ta sa yatsanta ta dauketa,toilet ta tura ta shiga ta daura alwala ta dawo inda ta saba yin sallarta tayi,bayan ta idar ta duba kan mirror dinta powder ce kawai akai ita ta dauka ta sake gyara fuskarta sannn ta mutstsika turare ya sauka qasan

Muhammad ne kawai zaune kan table din yana buga game a wayarsa ta zauna kusa da shi hadi sa dan dukan kafadarsa,ya dago ya dubeta yana murmushi, "ka shiga aji nawa ne har ummi ta yarda aka baka waya,cikin dariya yace "haba anty nafa zama senior ina s.s one fa,kuma ma yanzu nine babba a gidan nan"dariya ya bata sosai tana cikin darawar ne ummi ta fito,tuni har ta yi wanka ta canza shiga tayi kyau duk da ba make up take yi ba,fadila na shirin tsokanarta tace tayi kyau sallamar abba da ta aliyyu ta karade falon wadda ta yake hirar da suka so farawa

Abban ne a gaba aliyyu na biye da shi har suka qaraso dining space din abba ya fara cewa da aliyyu bismillah kai tsaye taga yaja kujerar dake kusa da ita ya zauna sai tayi duru duru har rudewarta taso ta fito,ji tayi ya take mata qafa ta danji zafi ta dago kai suka hada ido yayi mata alama da ido na ta nutsu,sannan ya duqar da kansa ya gaida ummi cikin girmamawa,ita kuma ta amsa masa cikin kulawa tana tambayarsa mutanen gidan

Fadila ita tayi serving kowa banda ummi don tasan ba zata ci ba,tazo kan aliyyu sai ya rasa mai zata zuba masa idonta na kan warmer tace "mai zaka ci?" "Zuba min duk abinda zaki ci" ya fada abunsa tamkar ba shi yayi maganarba,da sauri ta dago kai ta kalleshi saboda wata kunya da ya bata amma sai taga shi ko ajikinsa,ta saci kallonsu ummi sai taga hirar su ma suke da abba kamar basu san da su agun ba,sai kawai ya zuba masa fried rice da farfesun naman kaza mai yawa tana son qureshi taga zai cin?

Sai kuwa ya shayar da ita mamaki don abincinsa yake ci hankli kwance duk da baici da wani yawa ba yafi shan lemo,bayan sun kammala ita ta kwashe kayan ta kaisu kitchen ta hada ta wankesu kamar yadda ta saba tanayiwa ummin tun kafin tayi aure,tana aikin cikin ranta tana gulmar aliyyu bai da kunya

Saman kujera ta tadda su ta parlour ta samu gefan umminta ta rakube,aliyyu ne ya dora kan maganar da sukeyi da abban "sallama mukazo yi muku abba saboda gobe insha Allah zamu wuce china" abban yace "zancan bude kamfanin ne ya taso kenan munyi maganar da abban naku ai wancan watan yake gayamin an dan samu tasgaro ne da tuni cikin wannan watan company n ya fara aiki" aliyyu ya gayada kai yace "eh abba insha Allah wanna karon za'a kammala komai a budeshi daman cike ciken takaddu ne na yarjejeniya tsakani na da gwamnatin qasar ya kawo tsaiko amma yanzun al'a muran saun daidaita

Mrs Muhammad ce 👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

1:41 pm 29/8/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*

2⃣5⃣&2⃣6⃣

Abban ya jinjina kai yana cewa "kasan qasa ce mai tsari da doka ba irin namu qasaahen ba da sai dai muce inna lillahi wa 'inna ilaihi raji'un,Allahbya taimaka ali ya kuma yi jagora yasa a budeshi a sa'a,Allah yayi ma jagora a dukkanin lamuranka"ummi na amsawa da amin yayin da shima yayi qasa da kansa yana cewa "ameen ameen abba na gode Allah ya qara girma" yana shirin miqewa yasa hannu cikin aljihun kuftanshi na riga ya zaro turare yan ubansu designers ya ajjiue wa abban,albarka yasa masa tare suka qarasa miqewa abban zai masa tattaki kasancewar alhj abbas mutum mai sauqin kai ba ruwansa da wai shi mai shekarune babba ne kowa nasa ne

Sai lokacin fadila ta janye idanunta daga kan aliyyu kallonsa tayi sosai don bata taba ganin sa yayi doguwar magana irin haka ba,yanayin yadda yake maganar cike da girmamawa sai ya sake burgeta ta sake lafewa jikin ummin tana saukar da ajiyar zuciya,ummin ta kalleta sanda suka gama ficewa "au sake ma wani rabewa kike ajikina ke da ake jiranki?" Dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki sai kuwa ta saki kuka,ummin ta saki baki tana kallonta "wai wannan wane irin sakarci ne ko wata matsala kike da ita?" Kai fadilan ta girgiza,ance tsakanin d'a da uwa sai Allah hakanan sai tausayin gadilan ya kama ummin don yasan duk mace kimai jin dadinki baki rasa matsala ta zamantakewar aure,a da rance take mata nasiha hadi da lallashi

Ganin hankalin ummin ya tashi sai tace cikin son kawar da hankalin ummi daga tunanin ko tana da wata matsala tunda tasan halin iyaye yanzu sai ta fita shiga damuwa"ummi bana son na barku ne har wata hudu" ta saku ajiyar zuciya tana godewa Allah "idan banda quruciya irin taki fadila ko kina nan din ma basai ki kusa wata biyu ma baki gan mu ba ummm.....kiyi addu'a kinji Allah ya kaiku lpy ya dawo da ku lafiya kawai" tace amin tana share hawayen cikin dakiya

Ta zuge zif din jakarta ta fito da kudaden nan ta dorasu cinyar ummin,ummin ta kalli kudin sannan ta dubeta "wannan fa na meye?" "Naki ne ke da abba" "ina kika samo su fadila?yaushe kwata kwat kika soma aikin? Ina fatan ba roqonsa kike ba dai ko?", ta girgiza kai "a'ah ummi shi yake bamu kullum idan zai fita" ta dauke kudin ta ajjiye a gefe tana cewa "za'a dai juya miki zan bawa abbanki ko yayanki zasu san inda zasu sa miki su" ta langabar da kai tace "don allah ummi to ko dan wani abu 👌🏼 ne ki cira aciki ke da abban ku samin albarka" ta bita da "to naji"

Idonta fal da hawaye zuciyarta a raunane ta fito ,suna tsaye jikin motar aliyun ta qaraso ta tsugunna har qasa idanunta rau rau muryarta na rawa tana yiwa abban sallama "to fadila Allah yayi muku albarka ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya,ki zauna lafiya agidanki bana son fitina kada na ji kada na gani" tuni kukan ya qwace mata "insha Allahu abba"kasa tashi tayi har sai da abban ya daga ta da kansa,aliyyun ya zuba musu ido wani abu yaji ya taba ransa shi ya bude mata motar Abban ya sata ciki da kansa,aliyun ya rufe qofar sukayi sallama da abba ya zagaya ya shiga gun zamansa ya tada motar

Shiru cikin motar sai sautin kukanta danke tashi kadan kadan hadi da sheshsheqa,burki taji yaja bayan ya gangara gefan tati ya kashe motar sannan ya dan kwantar da kujerar da yake kai din ya kwanta rigingine idanunsa alumshe yana sauraran sautin kukan,sai da suka kusan kwashe awa guda ahaka lokacin tuni har kukan nata ya tsagaita,ya miqe a kasalance ya gyara zaman kujerar baice uffan ba ya tada motar suka wuce

Cikin daren bata kwanta ba sai da ta hada duk abinda take da buqata cikin babbar trolly dinta sannan ta kwanta zuciyarta fal da saqe saqe kala kala

⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Cike da kasala take janye da akwatin nata har ta iso bakin motar qirar sienna dake fake a harabar gidan,yadine a jikinta mai sulbi blue 🔷 tayi rolling da red din mayafi🔴🔵,sosai rigar ta bude daga qasa takalminta red ne hill sosai 👠,motar na bude duk suna ciki nasiru na mazaunin driver aliyu na kusa da shi sai salima dake sit din can baya bisa dukkan alamu ga fuskarta nan ta sha kuka,fuskar samira ba yabo ba fallasa tana sit din tsakiya,yayin da fadila ta zauna a sit din farko nasiru ya karbi troly din nata ya sanya a baya

Cikin hanzari nasiru ke ruqin aliyyu ya sake duba gaogonsa yace "nasiru qara sauri zamu iya missing flight" ya sake qarawa motar gudu don bin umarnin ogansa

Ba dadewa suka isa aminu kano international airport nasiru ya ajjiye motar inda aka tanada don ajiyar motoci,dukkaninsu suka fito daidai lokacin da airport din ta karade da sanarwa neman masu tashi a jirgin ethopian airline,hakan ya tabbatar ma da aliyu sun kusa makarar kam,tuni nasiru ya ciro musu jakankunansu,ya dubi samira da salima da fuska take adinke musamman salima da takejin kamar ta dora hannu aka ta zunduma ihu,"sai na dawo" yace kamar mai jira salima ta fashe da kuka ta taho a guje ta fada jikinsa,ya saki dan qaramin murmushi hadi da sa tafin hannunsa yana dan bubbuga bayanta alamar rarrashi,ya miqawa samira daya hannun alamar ta taho,dauke kai tayi tana turo baki zuciyarta babu wani takaici sosai Idan ta tuna da maqudan kudaden daya barwa kowaccensu tasan zasu sha bushasha don ma yayi misu gqrgadi da jan kunnen akan fita"sai ka dawo"tace kawai,ya dan janye salima daga jikinsa sukayi sallama da nasiru,ya wuve fadila ta rufa masa baya saluma ta bita da harara kamar ta fincikota,batasan itama fama take da fargabar bin aliyyun ba

Reception suka wuce suka qarasa departure ta farko suka shiga layin screening,aka kammala da su aka basu boarding pass suka qara gaba,immigration suka sake duba visa dinsu suka buga musu stamp suka shiga dan dakin jiran jirgi,mintina qalilan jirgi yayi ready suka bi layin shiga jirgi tana gabansa yana tsaye a bayanta

Mrs muhammad ce😘

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻






[10/16, 1:51 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*part 2*

2⃣7⃣&2⃣8⃣

25 and 26 ne number din sit din nasu don haka sune maqotan junansu,aliyyu ya daga yar trolly din da aka barsu suka shigo da ita saboda kilo din ba wani mai yawa bane ya sanyata a inda mayafiyan ke ajjiye jakankunan nasu,yan kallo fadila nata kiciniyar sanya tata saboda ta dan yi mata nauyi,sai da ta soma gajiya sannan ya sa hannu ya janyeta ya fada kan kujerarta ya daga trolly din tata ya sanya mata ya koma sit dinsa ya zauna yana gyara zaman suit din jikinsa

Kowa ya zauna a mazauninsu,fadila na bakin window ta zubawa filin airport din ido tana fargabar yadda jirgin zai Lula da su sararin subhana duk da yawansu kasancewar wannan shine shigarta jirgi na farko a arayuwarta

A hankali aka zare matattakalar aka maida qofar jirgin aka rufe bayan sun gama duk wasu yan tsarabe tsarabensu suka bada sanarwar daura belt,fadila ta jawo belt din saidai bata san yadda zata sata ba,tana satar kallon aliyyu ta gefan ido yana daura tasa,ya kammala ya fito sa laptop dinsa ya dora bisa cinyarsa

A hanakali jirgin ya soma qugi hadi da shawagi a doron qasa na kimanin minti goma sha biyar sannan ya yunqura don rabuwa daa doron qasa,fadila ta runtse idonta saboda wani tsoro da ya kamata,ta qanqame belt din dake hannunta wadda ta kasa daurawa jin jirgin na niyyar dawowa qasa ya tarwatse da su😂😂😜😜 lol har naga idon masu karatu aliyyu salim mai tama da fadila zasu mutu😂😂

Ta qanqame belt din dake hannunta jin tana niyyar subucewa daga kan sit din ta,cikin zafin nama aliyyu ya kareta da hannunsa sannan ya amshe belt din ya zagayeta da hannayensa ya daura mata hadi da cewa "silly girl" ya gama ya koma kan danne dannen da yake kan laptop abinsa ba tare da ya sake dubanta ba,a dan sace ta harareshi gami da jan dan siririn tsaki ,ya juyo da sauri don tsakin kunnuwansa sukaji kamar tayin da azama ta dauke kanta ta maida window Allah ya taimaketa basu hada ido ba sai ta waske

Tafiya ce ta awa hudu ta saukesu a *ethopia* don musayar jirgi cikin babban birnin na *ethopia* wato *addis ababa*,ba kwana zasuyi ba amma saida aliyyu ya kama one room apartment cikin hotel din dake kusa da airport din,tamakar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta nemi gefan kujera qwaya daya dake cikin dakin ta zauna a takure,sallar magariba da isha'in da bata yi bane ke damunta amma duk a takure take bare tayi azamar tashi

Tana kallo ya dora jakarsa💼 kan gado ya tube takalminsa 👞 da socks dinsa ya shige toilet,motsin ruwan da ta ji yasa ta raya alwala yakeyi

Kusan minti arba'in ya fito sanye da rigar towel mai budadden qirji👘,kallo daya ta masa ta dauke kai tsigar jikinta na tashi 😣,gashine kwance luf a qirjinsa baqi sidik tamakar wanda ake sawa relaxer kamar yadda na hannayensa da qafafunsa suka kwanta saboda ruwan da suka sha,ta sake runtse ido gabanta na dan faduwa💔 da alamu ma shi ko ajikinsa don goge sumar kansa yake da dan qaramin towel dake riqe a hannunsa

Ganin ya soma kunce dan zaren da ya taimaka wa rigar ta rufe jikinsa ya sata yin azamar afkawa toilet,ta dade numfashinta na kaiwa da kawowa wani abu na mata yawo a jiki sannan ta iya daura alwalar ta fito,ta cimmasa tuni ya har ya tayar da tasa ta koma gefe ta kalli inda taga ya kalla ta tayar da alama nan ne alqibla har ta kammala tata ta zauna tana lazumi lokaci lokaci tana satar kallonsa har ya sallame

Shirye yake a yanzun cikin jacket masu kalar green da black sabanin dazu da yake sanye da suit baqaqe kullum aliyyu cikin sa kaya yake sabanin wadanda ta sanshi da su,kusan ma zata ce bata taba ganinsa yayi maimaice ba,yana zaune saman qafafunsa ya kammala addu'arsa ya shafa ya miqe tayi saurin yin qasa da kanta don kada su hada ido tana yiwa Allah tasbihi saboda kyawun da taga yayi mata har ya juya ya fice

Fitarsa ba dadewa daya daga cikin ma'aikatan hotel din yayi knocking ya shigo mata da abinci fried spaghetti ce da roosted chicken sai drink da ruwan gora mai sanyi duk da cewa akwai su cikin fridge dake dakin,babu abijda ta iya ci sai lemon da ta sha

Saman kujera ta nade ta janyo wayarta ta kunnata wadda tun shigarsu jirgi ta kashe,babu service da ya hau saboda ya fita daga inda yake da amfani ,ta danna power off ta kashe don bata da wani amfani ta maida kanta ta kwantar a hannun kujerar

A hanzarce ya shigo ya dauki jakarsa 💼 ya juya yana cewa "let's go"ta miqe ita ma ta dauki tata👜 ta bi bayansa

🎊🎊🎊🎊🎊🎊

*_CHINA (SIN)_*

*_guangzhou airport_*

Qarfe hudu ⏰ na yamma da minti ashirin a agogon qasar china qarfe sha daya da minti ashirin agogon Nigeria suka sauka a qasar,iyakar gajiya fadila ta yita,tafiya ce ba kadan ba tamkar ta yada shege zama ne na awanni kimanin goma sha biyar a jirgin wadda bata taba tafiya makamanciyar ta ba

Da qyar take daga qafarta da tayi mata taruwar jini saboda tsabar zama,suka sake bin layin screening immigration suka karbi passport suka kuma duba visa dinsu don tabbatar da cewa sun samu izinin shigowa qasar tasu,bayan sun tabbatar da ingancinta suka buga musu stamp suka wuce

Sauran kadan aliyyun ya bace mata saboda ta lura cike yake da kuzarinsa tafiyarsa yake kamar baiyi wata doguwar tafiya ba bisa dukkan alamu ya saba da irin wannan tafiyar,motar ce mai azqbar kyau da daukan hankali tayi parking gabansu mutum uku ne suka fito dukkaninsu sanye da coart baqaqe baqin space da baqin sau ciki😎,cikin girmamawa suka iso inda aliyyu yake biyu daga ciki suka miqa masa hannu sukayi musabaha,cikin harshen nasara suka fara gaisawa dayan dake gefe ya dauki akwatinansu ya sanya a bayan motar

Bayan ya ruge boot suka dunguna gun motar fadila ta bisu a baya,ita da shi na sit din tsakiya biyun kuma na sit din can bayan driver din kuma ya shiga mazauninsa ya tada motar,hira suke abinsu da aliyyu yayin da hankalin fadila ya kasu biyu,daya ta dora shi ne bisa ga aliyyu yadda yake turanci kai sai ka ranyse
[10/16, 1:52 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*part 2*

2⃣9⃣&3⃣0⃣

Yayin da hankalin fadila ya rabu gida,daya ta dorashi ne kan yadda aliyyu ke turanci kai ka rantse da Allah cikakken buture ne gaba da baya,babu tuntuben harshe ko kuskure ko qanqani,daya kuma ya tafine kan kyawu tsari gami da tsaftar garin ,garine mai azabar kyau da tsari,yanayin gine ginensu sun burgeta matuqa da gaske,saidai abu na farko da ya daga mata hankali dan banzan sanyin da suka tarar ana danawa a garin🌫,taji daya daga cikin yan chinan na sanar da aliyyu yanzu ma aka shiga cikinsa wanda irin wannan sanyin a Nigeria shine wucewar jaurarmu

A hankali motar taci gaba da kutsawa cikin cikin kyakkyawan shimfidedan titin har suka shigo cikin wata kyakkyawar unguwa mai tsafta da tsari wanda tafiyar fadila tsakanin airport da inda suke yanzun ta fuskanci haka unguwanninsu suke,basu yi wani nisa a layukan da suke wucewa ba suka sa signal suka gangara wani layi,sun kusa kaiwa qarshen layin driver ya faka qofar wani dan kyakkyawan gida dake yanyame da shukoki daga gaban gidan kuma grass carfet ne to kusan ko wanne gida dake layin haka yake left to right

Driver din ne ya fito ya bude musu qofa sannan ya bude boot din ya fitar da kayansu,Aliyyu ya ciro keys daga aljihun cikin rigar suit dinsa ya miqa masa ya sa hannu ya karba ya nufi gidan ya bude,ya shigar da kayan sannan daga bisani shima ya shiga

Tun fadila na tsaye har ta gaza jure tsaiwar ta maida bayanta ta jingina jikin wata 'yar bishiya dake dashe a gun,shi kam tsaye suke qyam jikin motar shida lukas da andi suna ci gaba da hirar kasuwancinsu cikin harshen nasara,jifa jifa tana tsintar wani abu wani abun kuma ya kuce mata idan tunani ya rinjayeta,tsayuwar awa guda cif sannan ya fito ya qarasa shigar da ragowar kayan da bai dauka ba ya kaisu ciki,ya dawo cikin girmamawa ya ya miqawa aliyyu maqullan ya karba yana tambayarsa "have you finished?" Ya gyada kai gami da cewa "yes sir everything is ready"ya girgiza kai yana cewa "well done"ya juya gunsu andi da lukas ya basu hannu sukayi musabaha gami da sallama ya juya ya nufi cikin gidan su kuma suka shige motar driver ya jasu suka bar gun a kasalance ta rufa masa baya zuwa cikin gidan

Falone wanda ba za'a kirashi qato can ba hakanan ba zaka kirashi da qarami ba,saidai yadda ya tsaru dole ya qayatar da kai ta yadda zaka iya fin sha'awarsa ma fiye da wani qaton,kujeru ne set guda yan madaidaita masu azabar kyau sai labulaye na alfarma da suka kewaye falon ta yadda baka iya bambance ina qofa take center carfet center table da wasu yan qanana dake maqale tsakanin kujera da kujera tafkekiyar plasma TV da home theater dining area mai dauke da dining table mai kujeru hudu komai na falon fari ne tas sai wasu abubuwan masu sirkin baqi kadan,qofofine hudu cikim falon daya kitchen ne sai store sai public toilet sai bedroom,komai tsaf yake kuma qal qal ta tsammaci hakan dama idan tayi la'akari da dan karen son tsafta irin na aliyyu

Fadila ta zabi daya faga cikin kujerun tayi saurin zama saboda yadda take jin gajiya na nuqurqusarta har cikin qashi ji take tamkar ba zata iya daga koda yatsanta ba,tana nan takure kan kujerar tana satar kallonsa,gaba daya sanyin garin ya soma takura ta tun yanzun,ga bashin sallah dake damunta tunaninta daya ta ina zata soma iya taba ruwa da wannan azababben sanyin?

Key yasa

Please Login or Register in order to submit comment