Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dora mata kule kulen samari ba amma yau kamar almara sai gata a wata wawakekiyar qofar jarrabawa,ta saki ajiyar zuciya sanda ta iso bakin get din gidan malam sani ya budw mata qofa ta shige ta tsaida motarta bayan ta daidait parking,a gefabta taga motar farida hakan yasa ta gane sun dawo,ta saki doguwar ajiyar zuciya tafito daga motar ta kulle ta tunkari falon nasu

MRS MUHAMMAD BELLO
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻📝📝📝
07066139278
[10/16, 2:39 PM] ‪+234 706 914 1005‬: 8:39 pm
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma

▶8⃣

Bata nemi kowa ba kai tsaye dakinta ta nufa ta shiga wanka ta hado da alwala ta gabatar fa shafa'i da wutirinta tunda tun a gidan ya ahmad tayi isha,ta dauki kimanin minti goma ta azakar dinta sannan ta ninke sallayar ta sauko qasa ta nufi dakin ummi,ummin ta amsa sallamar bayan ta mata sannu da zuwa ta sanar da ita anty hafiza na gaisheta ummi tace "kinje kenan?"ta gyada kai tace"bayan fitarku ne ummi gidan shiru ba dadi😒shine nace bari kawai na leqa biyu"har ta bude baki zata mata fadan fita ba tare da ta tambayeta ba sai kuma ta tuna fadilan ba gwanar yawo bace banza bata kai zomo🐇kasuwa,ta tabbatar ba'a banza ta fita ba,dama farida ce to tasan hali,sai kawai tace"ina amsawa"fadila tace "ummi bari na wuce na kwanta na gaji"ta dubeta tace"au yau ba zaki jirayi dawowar abban naki ba?"ta gyada kai"um ummi abincinsa na dining area na parlour dinsa ni dai sai da safe"ta miqe ummi tace"Allah ya tashe mu lpy nima wanka zan shiga ki jamin qofar"tana qoqarin fita taji ummi ta kirayeta ta dawo da baya tana amsawa"bayan fitata wa ya kawo kaya a baqar leda suna nan a parlour?",sai a sannan ta tuna da kayan da aliyu ya aiko a kawo mata,ta sunkuyar da kanta😔tace"ummi yaya aliyu ne ya kawo to sai na mantasu a parlour"ummi ta gyada kai tace"yayi miki kyau,fadila ki maida hankalinki fa,gidan kishiyafa zaki,ba ke kadai zaki zauna ba ballantana kice zaki dinga abinda ranki keso......ta danyi jim,jin fadila bata ce komai ba ta Dora"sai kije ki debe tun kafin abbanki ya zo ya gani ranki ya baci"ta qarasa maganar tana shigewa bandaki ,jikinta a salube ta fita,ta isa inda ledar take ta dauke ta tayi sama da ita
Hannu biyu ta tallafe habarta da su ranta a jagule,yaushe su ummi zasu fahimci tsananin da take ciki?,har ga Allah tana son ali yana burgeta a rayuwarta komai nasa yana bata sha'awa,yau da za'a ce aliyu yana sonta a sai ta fi kowa farinciki,to su su ummi suna tsammanin ita ke son kawo cikas,ta share hawayenta ta daga ledar tana zazzage kayan ciki
Bandir ne na 'yan dubu dubu sababbi fil a miqe💶 guda hudu sai chocolate packet hudu manya🍫,sai turare guda hudu designers,sai awarwaraye banguls da zobensu na gold guda biyu💍,sai agogon hannu na azurfa guda biyu shima,komai tsada ne da tsari,cikin zuciyarta take fadin"yadda Aliyu na ke da kyau da tsari haka everything na shi yake,yadda aliyu yake special haka komai daya dangaceshi yake,komai nashi special one ne hakanan abun ban sha'awa ne,ina ma aliyu zai soni?,ina ma Aliyu zai rufeni da da so da qaunarsa da na zamo daya daga cikin mata masu tsananin sa'a a rayuwarsu"hawayen tausayin kanta suka ziraro mata,ta dauki daya daga cikin rapper din kudin tana shinshinawa,ta lumshe idonta don qamshin turarensa kawai ke tashi a jikinsu(haka aliyu yake saboda yadda turare ya zaunar masa a jikinsa duk abi da yayi gogayya da shi sai yayi qamshin turarensa)
Farida ta shigo dakin da sallamarta,fadila ta amsa tana janye mata kayan dan faridan ta samu gun zama,cikin tsokana faridanke tambayarta kayan,tace"duba ki gani ya Aliyu ne ya kawo dazun ki zabi abinda kike so(haka ummi ta koyar da su tun suna qanan idan daya ya samu abu to zai raba tare da dan'uwansa )ta yaba kayan sosai ta dauki turare biyu tace sun isheta,fadila tayi tayi da ita ta qara taqi,ta turo mata kudaden gabanta hadi da yage 'yar paper da taga anyi rubutu a jiki kamar haka"kiyi hidimar biki idan basu isa ba zansa a adado miki"tadan tabe baki ☹cikin ranta tace"nafi buqatarka da su da zaka gane hakan""farida ga kudin hidimar bikinan inji aliyu idan basu kai ba a mishi magana"farida ta dauki kudin tana juyawa tace"har dubu dari hudu😳"fadila tave"hmmm ni da ua ban su nasan mai zanyi ma da su"farida tace"ni da anty hafiza munsan me zamuyi miki da su,ko iya wadannan ma sun isa ya sallameki"ta miqe tana cewa"bari in nunawa ummi,sai da safe sister"ta fita taja mata qofar tana ayyana abubuwan da zasu yiwa fadilan masu amfani
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Duk cikin satittikan da suka biyo baya cikin hidamar shirye shiryen biki suke,ita kam fadila bata da wani zabi na kanta,da zasu yarda ma da sun qyaleta haka don bata da sha'awar yin komai kama daga gyaran jiki zuwa kan duk wasu events da ake yi yayin bikin aure,don duk abinda zatayi wanda za'ayi don shin abun bai dada shi da qasa ba baya gabansa hakan yasa itama ta tsani komai,sai da anty hafiza ta zaunar da ita ta nuna mata duk abinda tayi idanun👀 duniya na kanta,zata tona asirin kanta da kanta ne sannan ta amince da tsare tsaren da suke zuwar mata da su,hatta magunguna tanajin farida na sha da qyar tana mita ita kam nata ido👀karba kawai take ta daddake tunda tana ganin babu wani amfani da zasu yi mata

To fa masu karatu ga fadila Abbas na shirin shiga gidan Aliyu salim maitama,gidan da aka gargade ta da shigarsa tun kafin ta kai ga shigarsa,shin mene shawararku gareta????
10:34 pm
07066139278
✍🏻✍🏻✍🏻📝📝📝📝



🌺🌺🌺
[10/16, 12:25 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

▶9⃣

Ranar laraba 12 ga watan biyu aka soma da kamu👰🏻,ba dan qaramin kyau amare sukayi ba,kai kaso kazo kaga yadda kamun ya qawatu matuqa da gaske,an zubar da dukiya sosai kasancewar wannan ne bikin ummi na farko kuma na qarshe,tamakar tagwaye haka suka zama komai iri daya suka sanya hatta da awarwaro da zobe
Kasancewar abban su babar bare umminsu bafulatana sai aka raba abun biyu shigar farko sukayi shiga irin ta bare bari cikin wata lafiyayyar lafaya wadda kudinta ya tasamma kimanin dubu ashirin kamu aka musu irin na bare bari sosai sannan daga bisani kuma suka canza shiga irin ta fulani cikin kayan saqi nan ma aka musu kamun fulani,shida na yamma aka tashi bayan sallar magariba kuma masu kidan qwarya suka zauna zuwa goma na dare
Irin cikar da gidan yayi yasa su fadila haqura da zaman gidan su da qawayansu suka koma gidan maman zainab maqociyarsu ce kuma babbar macace don idan batayi sa'ar umminsu ba to zata girmemeta,zainab din yarinyarta ce kusan sa'ar farida ce
Fadila nabin kowa da ido don a yanzu kam jikinta ya qarasa mutuwa murus,bata da kuzari ko qanqani komai cikin dakiya da qarfafa mata gwiwa da anty hafiza ke mata take yinsa,ga wani ciwon kai da ya addabeta,ta riga ta saba ita ko da can bata saba da shiga hayaniya ba ko bikin dangi ne bata kwana sai dai farida ta kwana ita kam komai dare zata dawo gida ne,ko hayaniya tayi mai yawa to yanzu kanta zai fara ciwo ko qirjinta ya dau zafi

Kwance take kan gadon zainab din ta juya ma tarin 'yammatan dake dakin sunata hayaniyarsu baya ta fuskanci fuskar gadon,yawancinsu duk qawayen farida ne sai 'ya'yan 'yan uwa,farida tayi sallama ta shigo dakin ita da aminiyarta ruqayya hannunsu dauke niqi niqi da ledoji na take away wanda aikin mubarak(angon faridan) ne shi yace a tazo suje tayi musu take away,ta zube musu nan hayaniya ta qaru kowacce tana daukar tata,ta iso kan gadon hannunta da ledoji biyu,ta dan taba qafafun fadilan tace"sister tashi"fadila ta miqe daga kwanciyar ta zauna tsakiyar gadon ta tanqwashe qafafunta tana kallon farida,qasa-qasa muryarta tace "yayaa ga abinci ki daure ki ci sai ki sha maganin ciwon kan ko dan idon mutane ida yaso sai ki kwanta ki huta,"tana maganar tana bude ledar da ta shigo da ita din ta tura mata gabanta,ta sake bude dayar ledar tana cewa"ga dinkimmu na dinner din gobe ta can muka biya da mubarak muka maso"ta soma fito da su
Wani dan ubansun material ne mai azabar kyau wanda ko makaho ya shafa yasan cewa ba qananan kudade aka sa aka siyeshi ba,milk ne da ja(milk and red),ita kanta faridan da tunda ma anty hafiza ta bawa ya ahmad da zashi india ya siyo musu bata ganshi ba sai yau da aka karbo dinki faridan ce ke zuzutashi sai yau taganshi yayi bala'in tafiya da ita ,ta jinjina kak tace"an gode miki sister farida"farida tayi dariya tace"ai wannan aikin anty hadiza ne ragowan su earings ma da zamu sa suna gunta"fadila tace"Alla ya saka mata da alkhairi"ta jawo ledar da faridan ta bude mata,gasashshiyar kaza ce🍗 da hanta wadda aka mata gashi mai ruwa ruwa da albasa,shawarma🌮 sai kuma ice cream roba biyu🍧🍧,tayi murmushi ta kalleta kafin tave komai faridan ta rigata magana"ke dai yaya ki ci kawai,kina tsammanin bansan abinda kime boyewa bane a dan qaramin fridge dun gefan gadonki ba wanda ke hanaki maida hankali kici abinci?☺"sai dariya ta kama fadila,lokaci guda kuma tausayin rabuwa da junansu da qaunar 'yar uwarta ya kamata,lallai ne dan uwa rabin jiki,naka nakane qwalla ta ziraro mata ita ma faridan sai ga qwallar,dai dai nan rumasa'u(yar qanwar umminsu ce(ta shigo dakin,ganin haka ta saki dariya"😄a'ah kaga twince sisters wato ku daga fara biki har kun soma gunsheqen kukan rabuwa tun kafin aje ko ina?"yawan hayaniyar da yammatan keyi ya hanasu jin abinda take cewa,farida na dan murmushi ta goge hawayanta,ita kuwa fadila da yake sa'annin juna ne saita harareta"to ina ruwanki 'yar sa ido?"cikin dariya tace"🤗a'ah Allah ya huci xuciyarki bani na kar zomon ba ratayar ma ba'a bani ba ni ummi ce ta turoni tave inzo inga kinci abinci don tasan hali"ta fada tana leqen ledar gaban fadila,fadila ta muwa lanqwashe ledar,tana cewa"kuma duk kwadayin mutum bazaici ba ba?"cikin son zolaya rumasa'u tace"haba aminis ni dake fa bata baci"fadila ta zaro kazar ta nannde mata tace "ungo a banni na hadiyi yawu"tafice tana dariya,farida da tun dazun take ta musu dariya tace"hoo 😂yaya ruma akwai zolaya da abun dariya yanzu fa idan kika bibiya itama bacin zatayi ba baiwa wani zatayi"fadila tayi murmushi tace"ta ji dai
Shi dai gundura kawai"
Da taimakom farida fadila ta saki jikinta sosai don har ta samu ta shige cikin 'yammatan aka shiga hirar harda ita,hakan ya taimaka mata ta samu sauqin takurar da zuciyarta tayi sosai kafin dare yayi kowa ya kwanta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegari gidan kwalliya anty hafiza ta debesu suka tafi,cikin wasu awoyi aka qalqale wa kowacce fuskarta da kwalliya ta garari dubu ashirin aka ajiyewa matar,itakam anty hafiza tsayawa tayi tana kallon sarautar Allah kyansu ya qara bayyana qarara,daga baya ta kasa ahiru sai da tace"ashe haka kuje da kyau yammatan ummi musamman fadila ashe hasken fata kawai za'a nuna miki?"dariya dukansu sukayi har da ita mai kwalliyar wadsa itama tinda tayi musu take kallo fuskarsu tace"dama ai ba fari ne kyau ba don wani choculet din yafi fari kyau nesa ba kusa ba"
sai bayan idar da sallar magariba aka kammala kwashe yammatan zuwa royal tropicana,amare sun gama shirinsu kayan kam sun amshi jikinsu don tamkar saboda su aka halicci yadin da shi kansa dinkin,kiran mubarak ya shigo wayar farida yana sanar mata isowarshi qofar gidan,ta kashe wayar fuskarta na bayyanar da damuwa ta kalli anty hafiza da ta luea tun dazun ta kasa zama sai kaiwa da komowa taketana kiraye kirayen waya ta fuskanci akwai abinda suke boye mata,farida tace"anty ya za'ayi gashi har mubarak ya iso?"hafiza vikin damuwa ta kalli fadika tace"fadila kibi motarsu farida kawai kije"ba abinda tace mata kawai tabi bayan farida suka fice,ko ba'a gaya mta ba itafin ai ba yarinya bace qarama ta sani koda wasa aliyu ba zuwa zaya yi ba,ko da yazo ma tana fargabar kada ya yi mata wani abun da zata kunyata a idon duniya,shi yasa tun usuli ta so su shiryawa farida dinner din ita kadai abunta,mubarak ke driving motar da kansa don haka suna fitowa da kansa ya bude mata kujera mai zaman banza ta kusa da shi ta shiga ya rufe sannan ya koma ya shiga nasa gun,ita kuwa tana baya ita kadai,tunani ya cika zuciyarta tana sha'awar soyayyar farida da mubarak dinta,yana matuqar nuna mata qauna da kukawa ko da a gaban waye,tunda aka fqra hidimar bikinannan kusan tare suke jigilar shi da ita,duk da tana da moyar ta amma ba ruwansa da wannan,
da yake basu fito da wuri basun dan bata lokaci gun jira jiran da fadila ta samasa jiran gawon shanu don tasan ba komai bane face jiran tsammanin zuwan Aliyu ya dauketa ita damata ahekara da sanin ba zuwa zaiyi ba,a farfajiyar farko kafin ka shiga tafkeken hall din mubarak yayi parking,saiga anty hauwa anty hafiza da tuni ta iso sumayya rabi'ah da 'yan biyu,fuskar anty hawa da alamun bacin rai ta kalli su mubarak"kama hannunta ku shiga su fadila zasu shigo daga baya"yace "to"ya kama hannun farida su sumayya suka take musu baya su da wasu yammata cikin anko codelace milk dake tsaye bakin qofar ahiga hall din,cikin son kauda ahitun da gun yayi antu hauwa tace"gsky hafiza mun tsinci dami a kala fa,irin wannan tsaleliyar budurwa haka?"duk sai da ta basu daroya,anty hauwa ta budewa fadila motarta gun kujera mai zaman banza tace zauan fadila,wayarta ta zarota shiga kira"muna qofar hall inda ka shanya mu muna jira"ta fada cikin fusata sannan ta kashe wayar,sundebi kusan minti ashirin suna zaman jiran har fadila ta qosa sosai tayi kamar ta nemi alfarmarsu akan su qyaleta ta koma gida tana ahirin yin hakan waau jerin gwanon baqaqen motoci motoci suka danno kai cikin harabar gurin,anty hafiza ta sake feshe fadila da turare sannan duk da qamshin da take zubawa fuskarta fes take kamar yanxu aka gama kwalliyar sai alamun damuwa da suka bayyana a fuskar anty hafiza ta rada mata"be free and comfortable you have to invite happiness in you face even its not true, zaku shiga cikin mutane ke zaki bawa kanki confidences na zaki zaki zama amarya kamar farida da mubarak right?"fadila ta gyada kai tana qoqarin daidaita yanayin din fuskarta,ta maida turaren cikin hamarta tana cewa sai kun shigo "ta wuce ciki,daganan tana hango anty gauwa yadda ta nufesu tana wurwurga hannu da alama masifa take nasa shì kuwa ya yi kicin kicin ya hade ransa sanye yake cikin wata dakakkiyar shàdda milk colour yar ubansu komai na aliyu classic ne yayi wani shegyan kayu dinkin babbar riga da yar ciki ne da wando sai takaminsa half cover na kamfanin mister,daga bisani tafa tana nuno masa ita da hannu itama ta juya tayi shigewarta
Duk takunsa daya shike qaŕa bugun da zuciyarta keyi ta dauke idanunta ta ditasu kacokam kan sitiyarin motar kunnanta na jiyo mata takun tahowarsa gun hancinta na shaqo mata daddadan turarensa,sau biyu taji yayi knocking glass din motar bata da zabi illa ta fuskanceshi sabida haka ta dago razanannun idamunta ta saukesu cukin nasa idanunta da nashi suka hadu gu guda👀,zuciyarsa taďan kai ta jawo kadan duk da yaga kyaunda tayi amma sau yaga batakai kyan da samira ta masa ba,cikin halun ko in kula yace mata"les go"fuska a tsuke ya juya😠,ta bude murfin motar tana qoqarin fitowa ta gurde ta tafi luu zata fadi saboda yadda jikinta ke rawa,yasa sangalalun hannunsa na hagu ya tare ta sannan ya miqar da ita tsaye ya saki tsaki yayi gaba,ta yi qoqarin daidaita natsuwarta sannan ta bishi suka jera
Shigarsu mawaqin ya sauya kidan zuwa wani take na musamman aka bisu kuma da abin qyalli ana fesa musu🎊 ga gayyar yan rakiya a bayansu da suka sasu a tsakiya,suna zama aka maida waqar da shahararren mawaqin nan yayi musu nura m inuwa(anyi aure biki na'ya'yan girma 'ya'yan alhaji abbas bashir sunyi aure)aka dan cashe kadan sannan m.c ya amshi abun magana🎙ya soma zugasu kamar yadda aka sani sunawa amare da angwàye,lokacin mubarak da aliyu suka gaisa cikin mutunta juna,mc bai qyalesu haka ba har sai da ya samo musu kyautar mota daga gun Aliyu mubarak ya bada dubu dari hajiya shatu yayr alh salim maitama ta basu wata qaramar motaŕ dangin mubarak kuma suka qara musu da dubu hamsin,tunda suka samu abinda suje si suka bude fa bakin gangat zamar da bikin qayatacce a idon duniya,biki kam ya qawayat ta kuma nishadantar musamman farida da angonta,don da aka kira amare da angwaye su shigatsu sukayi filin rawa suka taka sosai itakam ita da aliýu sun tsaya ne kurum suna facing juna ita kanta na qasa ma aka musu ana cikin yi aliyun yaja hannuta suka koma sit din su umarni ma yabi da tafiyarsa zaiyi ya barta ita kàdai tsaye a filin sai akan kujerunsu aka qarasa musu liqin,wayrsa ta dauki wani daddadan ringin,ya daga yar kyakkyawar wayar a kunnensa sannan u
yace"oh baby I already told you sai na fara zuwa gun daya dinner din ko idan kuma nabar nan din can zan taho tunda na da wuri zaku tashi ba......ok take care"ya kashe wayar yaja dan siririn tsaki
Farida da mubarak ne suka soma yanka nasu cake din sannan dan gaa kadan nasu fadila mai hawa shidda ne milk sannan red milk sannan red haka haka har step shida🎂,bayan su farida sun koma aka kirasu gabanta na ta duka,suka tsaya gaban cake din maimakon ua fara daukar wuqar saboda tsorata ita tà fàra daùka akasa tagi mc yace yau zamuga sabon salon soyayya uwargida zata fara ci da mai gida wata wuta tayi tsiri saman cake din lokacin da tasa yar qaramar wuqar tana yanko cake din hakan ya sake sa jikinta rawa tadan tsorata
duk da ta saba gani ammada yake a rude take sai hakan ya sake duburburtata,tayi qasa da idonta sanda ta kai cake din bakinsa ,ya kuwa basar ya sa bakinsa ya karba cikin mugunta ya hada da hannayenta ya datse mata sutaji zafi sosai amma kasancewar tasan da gayya yayi sai ta basar kamar baþa ji zafin ba,bai damu da qanqantar bakinta ba ya yanko qaton cake da tasan yafi qarfin bakinta ya danna mata duk da haka itama tayì namijin qoqarin lalubo yatsunsa ta ganyara masa cizo maimakon ya cire hannun nasa sai kawai ya birkitota ya mannata da jikinsa ya maqure ta sosai duk a zuwan rungumeta ya yi ya sanya bakinta cikin nasa yana tsotse butter din da ta bata dan qaramin bakinta,duk gurin ya dau sowa da tafi masu hotuna📸 da video🎥 suka yo ca suna aikinsu saidai fafila ita tasan azabar da take ji domin tsotsar mugunta ce su kuwa a tsammaninsu tsantsar soyayya ce,ta tabbatar lebunanta idan basu tsage ba to daf suke da au tsage din,kunya da takaici suka dabibayeta cikìn dinbin jama'a saboda rashin kunya irinta aliyu ya mata irin wannan abun?ya saketa sannan ya jata zuwa gun zamanta ya zaunar da ita ya dan ranqwafa mata yace"matuqar idan nayi miki abu kikace sai kin rama u wil b suffer"yana gama gaya mata ya juyà yabi ta cikin mitanen ya bar halla din sai jiyowa tayi ta cikin macros phone mc na sanarwa cewa ango yace a masa afuwa kayansa sun bavi zaije gida ya canza yana kuma yiwa kowa fatan alkhairi godiya da kuma ban gajiya amarya kùma tadan daure taje zasu tafi,kasa tashi tayi kuka kurum take na takaici da kunyasam Aliyu bashi da kunya ya rasa tame zai rama saita irin wannan hanyar?idan su sunsan abinda ke zuciyoyinsu ai ragowar jama'a basu sani ba ko?,harsai da text din anty hafiza ya shigo mata kamar haka sannanta iya tashi"malama kukan ya isa haka ki taahi ki bishi yana wahan hall din yana jiranji isan kùna so kike ki tona abnda muka binne to bismillah"ta miqe tana kare fuskarta da purse👛ta fice
Wannan saurayin da ta saba ganinsu ko yaushe da aliyu shi ya fito ya bude mata gidan baya ta shiga sai da ta zauna ta lura da aliyu ahima zaune gefanta bai ko kaeta ba yavi gaba da abinda yake bako motsin mutum cikin motar sai qarar fitar ac har suka qaraso ni'ima guest place,motocin sukayi parking na ciki suka firfito suka tsaya jiran fitowar Aliyu tuni drivan ya fice aliyu ya zube wayoyinsa bayan ya kashesu yà fice shima a motar ya kulleta tare da sa security
Wucewarsu cikin hayaniya ta tawagar ango yasanya gun komawa tsit kamar yadda yake ,tun tanajin tsoro har ta dake tana ta addu'o'i,a hankali abinda ke wakana agun ke isowa kunnuwanta ta hanyar lasifiqan da suke amfani da shi,sunan samira da ta ji hade da na Aliyu shi ya tabbatà mata gun bikinsu ne,wani kishi mai zafi ya shaqeta,ta jingina sosai da makarin kujerar tana ambatar sunan Allah tà lumshe idanunta tana ci gaba da sauraren abinda ke wakana cikin gun dinner din,gajiya tsoro kishi da takaici suka mata taron dagi, tun bata gaji ba har ta sare da zaman gashi ba damar fita bare tayi tafiyarta yabi ya kulle matar,zaman jira na kìmanin awa uku tayi a motar sannan ta fara hango tawagar aliyu

Mrs muhammad bello ce
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:29 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶🔟

Tamakar ya manta akwai wata halitta da ke cikin motar ya shigo abinsa driver yaja motar suka bar gun,ganin haka yasa tayi kamar ta tuna masa su sauketa a gida fa sai taga ai ya ma raina wayonta duk inda zai kaita ya kaita,ganin sunyi hanyar gida yasa ta sake tabbatarwa yana sane kenan

A daidai qofar gidansu driver yayi parking yana tsayawa tasa hannu ta bude motar tayi ficewarta ba tare da tace masa kanzil ba haka shima baice komai din ba dama kuma tasan ba cewar zaiyi ba bata kuma dada ta da qasa ba maganarsa,ahankali take tafiya saboda kasala da bacci ga takaici da ya rufeta ya dan bita da kallo yana mamakin haqurin da tayi bata ce masa komai ba ua juya ya bawa nasiru umarnin ya ja motar su wuce

Kai tsaye gidansu zainab ta tafi don kwanciya kawai take buqatar yi a halin yanzu,dakin da aka basu ta tura ta shiga wasunsu yammatan sunyi bacci wadanda suka rage kuma kowacce na maqe da waya tana tadi kamar yadda farida tabi sahu itama ganin shigowar fadilan ne ya sata katse wayar ta dubeta tace"ya naga kin jima sosai haka"sai kuma ta danyi murmushi😊 tace"um mace da mijinta meye nawa?",tabe baki fadilan tayi☹ta jawo jakar kayanta ta dauki towel ta kwabe mayan jikinta tadaura ganin haka yasa farida ta gane tambayarta bata da amsa kenan,ta sake dariya bayan taga shigewarta toilet tace"ya fadila tawa......miskili kafi mahaukaci ban haushi

Washegari ummi tayi mother's day,cikakkiyar shigar hausawa sukayi ranar don hatta mayafi na atamfa sukayi,kwatsam sai ga momin Aliyyun a gun da mutanenta sunzo wai za ta yi wa fadila nata kamun,gun yayi armashi sosai don kidan qwarya akayi zalla bayan lecture ga amare wadda aka shafe fiye da awa ana musu inda daga baya kuma gun ya karade da waqoqin da irin nasu mamman shata sani sabulu dan qwairo dan indo audu wazirin dan duna da sauransu suma iyaye aka tuno musu da da tunda dama ranar ta iyaye ce,

Washegarin ranar sukayi kuma wuni a gida,wata Washegarin kuma ta zamto ranar daurin aure,daurin auren da ya tara jama'a na ban mamaki garin ranar unguwar ba masaka tsinke,jama'a ne tako ina na nan qasar dama maqwaftan qasashe har da na qetare
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Misalin takwas na daren ranar daurin auren fadila da farida na durqushe gaban umminsu sanye cikin atamfa super England lemon grean ce da pink sai adon fari dinkin riga da zani an nannade masu jikinsu da wata danyar lafaya fara tas mai dige digen pink a jiki,dan kunne da sarqa sai banguls duk na azurfa ne ,babu abinda ke tashi jikinsu sai wani rantsatstsan qamshin turaren humra yar gasken ta bare barin usuli
Da fari ummi kasa magana tayi saboda tausayi da qaunar yaran nata sai jimamin rabuwa da zatayi da su,daga baya ta daurw ta musu yar tunatarwa saboda ita damacan koda yaushe mai dora yayanta ce kan tarbiyyar zaman gidan aure ce,ta kammala nasihar tata da addu'a da fatan alkhairi a garesu,umma A'i yayar ummi ta leqo tana

Please Login or Register in order to submit comment