Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba.....anyway kaji a bakinta,ga magunguna nan ,ba za'a yi birede a gaba na ba,idan kun tafi nurse zata zo ta kulle qofa"tayi haka ne don tasan za'ayi budurin yadda tasan alin da son yara na masifa


A hankali ya duqa gabanta "da gaskene Fadeelah kina da ciki?"cikin jin kunya ta gyada kai,sai ya hade fuska tsam,ciki tsawa tace"don me yasa zaki boyemin kyautar da Allah yayi min?shin ban can can ci in sani bane?"
A Dan tsorace ta kalleshi,sai Kuma taga ya rungumeta "am sorry dear,banji dadi bane da kika boyemin,kunya Daren jita na cutar da ke,da wa ni Abu ya faru daku keda baby na bazan yafewa kaina ba Fadeelah,bazan gaji da roqamiki rahamar Allah ba,bazan gaji da roqarmiki albarkar ubangiji ba,ke din wa ni alkhairi ce a tartare da ni ,bani d halin da zan miki godiya don tayi kadan,bansan da me zan saka miki da shi ba fadeelah,Abu day dai da na sani kin zama mahadin rayuwata Fadeelah,na tabbatar idan babu ke rayuwata bata da amfani"


Ga mamakinta sai taji ya fashe da kuka sosai,tabbas rabo ajali,rabo ne mai zafi ashe tsakaninsa da fadilan,hawayene sosai ke sauka bisa fuskarsa,hakan ya sake nunawa fadila yadda Aliyyu ke tsananin son yara,ita din ke share masa hawaye tana lallashinsa
"Allah shi ya cancanci ka godewa bani ba,ni da kai duka bayinsa ne yadda yaso haka zamu gani"
Baiyi qasa agwiwa ba Kuwa ya kama"alhamdulillah"ba qaqqautawa
"Allah ka yimin dukkan wata ni'ima a rayuwata,Allah ka bani ikon saka maka ta hanyar yi maka da'a da biyayya da bin dukkan wani umarni naka"



Addu'ar d aliyyun y dinga yi kenan gwiwoyinsa kafe a qasa hannayensa a sama,ba fita daga asibitin ba sai da ya yiwa doctor sa'adah albishir din Kujerar umrah,fadilan ma hañata tafiya yayi ya kafe sai dai ya dauketa,sai da tasa masa kukan shagwaba sannan ya bari,roqarsa ta dinga yi cikin mota don Allah kada ya fadawa kowa
Girgiza kai yayi"mummunan labari ake boyewa,ban miki alqawari ba ruhina,na dai yarda bazan fada ba amma Duk wanda ya tambayeni zan fada masa"ba yadda ta ita haka ta qyaleshi,motsi kadan yace"sannu,yaya?"
Tun tana amsawa har ya soma bata dariya,



Marairaice masa tayi kan sai ya kaita gida taga umminta,dole ya kaita ganin tanason sa masa kukan nan nata da ba yaso,tayi Sa'a kuwa ta tadda Farida tazo,wayyo dadi gun Fadila ba'a magana,humaira nata rarrafe abunta,yarinyar ta sake kyau kamanninta da fadilan ya sake fitowa,sai ta sake shiga zuciyarta,Fadila na shirin daukarta ummi tace"Allah yasa ta yarda da ke 'yar nema,wai nan qiwa fa take"sai kuwa ta ba su mamaki don luf tayi abunta jikin Fadilan


Can jimawa saiga 'yan biyun Anty hafiza,tunda cikinta ya tsufa ya Ahmad ke tarkatosu gun ummin lokaci bayan lokàci musamman weekend dob mamansu ta huta, ummi ce ta kalleshi"gayamin kwana nawa za suyi,don bazasu zo tafiya amira rigima ba"yayi murmushi"anjima ma zan dau ke su,idan natashi daga kasuwa,naji tana gobe can gidansu za'a kaisu za suyi taro"



Sai kuwa hussaina tace"abba da hassana kawai zaka tafi ko?ni a gun ummi sanya kwana"ta fadi taba fadawa saman cinyar ummin"kiji mai ka irin wayo wato don kin fita baki ko"inji Muhammad daya dungure mata kai din shi hasana ce mutuniyarsa



Ummice ta bige masa hannu"ina ruwanka ,baban kawai"ya qyalqyale d dariya ya dauke hassanar sukayi ficewarsu yana yiwa hussainar gwalo,bata damu ba don ta saba da hakan ta fada cinyar ummin tayi kwanciyarta


*Mrs Muhammad ce*👑


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed💞: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺





*PART 3*




2⃣2⃣



Sosai Fadila taji dadin yadda ummin nata keta nan nan d ita cikin kulawa,saidai yadda ummin nata ke binta da ido Duk Indi tayi ke sata jin kunya da rashin sakewa,kiranta ummin tayi lokacin da su ke kitchen su na hada abincin rana ita da farida,gefenta ta nuna mata "zauna a nan bar faridan ta qarasa aikin tunda ita lafiyayyiya ce"kunyar ta sake kamata ,zaman tayi don dama aliyyu ya ja mata kunne da kanta yake tace zataita aiki



Faridan ta fito daga kitchen din tana kallonsu "ya haka sister ina can ina jira?"
"Eh ni nace ta zauna ,jeki qarasa tunda kin fita lafiya"tsalle faridan ta daka kamar yarinya"wallahi ummi sai da nace sister kamar mai ciki ta wani harareni ,ashe na canko gaskiyar lamari"
"Tashi dalla Mara kunya ki bawa mutane guri fitsararriya"inji fadilah dake hararar farida,bata damu ba taci gaba da murnarta



Gab da magariba aliyyu ya iso,ya shigo suka Gaisa da ummi wani kunyarta yakeji sosai,yanata satar Kallon Fadila yana mata alama ta taso su tafi amma tayi qirmisisi kamar bata gane me yake nufi ba,har sai da ya miqe yana yiwa ummin sallama ya fice,ummin ta kalleta "zaman me kikeyi haka,ki tashi mana Ku tafi"
"Haba ummi banga abba ba fa,Kuma ga farida nan ita da ta fini zuwa ma bata tafi ba sai ni"ta fada kamar zata saka kuka
"Nima Motata na gun gyara ne da tuni na wuce,Mubarak ne Zai biyo must tafi"tana qunci tana komai ta fita



Aliyyu sarkin yara,yana jingine jikin motarshi shi da 'yan biyu sunata hirarsu abinsu,shikam dama idan ka ganshi tare da yarda zakayi mamaki,sosai yake sakarmusu hadi da biyewa shirmensu,tahowarta ce ta dauke masa hankali cake daya kan 'yana biyun,tunda ta taho tunda ya lura ranta kamar a bace
"Allah ya taimakeki,wa ya tabamin ke?"y fada yana leqa fuskarta
"Bayan Kaine,ka barni kawai na kwana amma don Allah, yaushe rabona da gida,kunsan five months fa"



Ya harde hannunsa a Qirji ya gyara tsaiwarsa"ba Matsala mana don dai kwana,amma ina fatan kin tanadar mana dakin da zamu kwana diñ ko?"
Murnar da take ta koma ciki,ta zare ido"wai ni da kai Zamu kwana a Daki gudan,a gaban ummin da abba?"
Baice komai ba ya bude mata gaban Motar sannan tace"kinga to ashe babu batun kwana my queen, wlh bazàñ biya ba Fadeelah, daga yau fa sai nayi kwana hudu kafin kwananki ya zagayo,pls ki tausayamin mana Fadeelah baby"



Sai ya kashe mata baki,tabbas aliyyu na qaunarta,bai kamata ta zalunceshi ba,saboda haka babu musu ta shige,cikin jin dadin rashin musu irin nata ya rufe mata qofa,two thousand ya ba wa su hassaña,da guduvsuka shige parlour suna tsalle su na ce wa"uncle ne ya bamu naira biyarr"don basu San kan kudi ba

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Cikin lkc qalilan Fadila ta fuskanci waye ainihin aliyu,very intelligent simple peace and humble man,mutum ne mai kyakkyawar zuciya mai cike da alkhairi,maye ne Kuma gwanin Soyayya,dau tafi idan ya rudata da salon soyayyarshi sai ta rasa a wacce duniya take?,shin duk duniya ma akwai macen da ta ka ita sa'ar miji?
Soyayya yake gwada mata ba ta wasa ba,wadd ita da kañta wani lkc take roqonsa ya rage nuna mata haka



Abinda ke tunzura Zuciya Salima da salima Kenan,sau tari yakanyi wasu abubuwan da gayya wai ko zasu dauki darasi su gyara tsarin ràyuwàrsu,amma a'a maimakon suyi Koyi da ita sai su sake fandarewa,maganganu kala kala marasa kan gado
"Matsafan chaina dai aka bi,idan baka ga haka ai kafin ku tafi ba haka yake miki ba"dariyarta taci sosai,bata kulasu ba kamar yadda ta saba don aji tàyi musu gudà sakasu,Aliyyu ne da yake jinsu yace"Duk wadda zàtayi bin màlamai irin nata yaso ni zañ dinga biyañ kudin,indai irin nata ne"



Iya bakin qoqarinsa yanayi don ya saitasu a hanya amma inaaàa......kamar sake rubuta su akeyi,ya gama haqaqewa ransa tabas babu Wanda ya isa ya shiryar da batacce sai Allah



*Mrs Muhammad ce👑*


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed💞: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺




*PART 3*

2⃣3⃣


Daga hutun sati sai aliyyu ya birkice Fadila bata komawa aiki,bata iya sa'insa da shi ba sai kunya da ta zauna tana rusa masa babu qaqqautawa,shu kuwa Abu guda dake daga masa hankali kenan,zama yayi dirshan yana clarifying mata dalilansa
"Baby bana so ,duk sanda zaki fita baby na akwai mai kalle min ke,duk sanda na tuna hakan sai naji zuciyata na quna,pls my unique ko don babymmu da kike dau ke da shi ki haqura,ki gayamin nawa kike dauka a Wata nayi alqawarin zan miki multiplying nasa"



Ta share qwallar dake shatata Duk da ba daina zubar tayi ba,"banaso ni aikina nake so,ka ganshi fita ko ina sai tare da kai,matanka su da yake kana sonsu fiye da ni ai gashinan babu inda baka barinsu suje,sai ni da nake fita aiki "ta fadi cikin fushi tana zumburo baki,Dariya ta bashi sosai,don ya lura gaba daya cikin nata yasa mata saurin fishi hasala da saurin kuka,kan cinyarsa ya dorata yana gorge mata Hawaye
"Gaba maman biyu,kin manta ke din ta musammance?kin manta aliiyunki bashi da kamar yake?ko kuwa kin manta cewa kace mace ta farko da aliyyun ya mallaka mata komai nasa kamàr yadda kika kasançe mace ta farko da ta mallaka wa haidar din komai nata?,hakanan ta farko da ya fara so da kangin kansa?"



"Kiyimin rai ki raini yarona ba tare da yasha wuya ba,dama tun farko aikinki din nan ba Sonshi nake ba,idan ba zaki manta ba ranàr farko da zaki fara zuwa irin sharudan da na dinga gindaya miki,wlh a lokàciñ zuciyata tàfasa kawai take,bans an sink I da na boye ne yasa ni jin haka ba,banda Ahmad ne ya same ni kai tsaye da maganar da ba zakiyi shi ba,na roqeki kiyimin wan an alfarmar ki haqura"ya Jade hannunsa da nata yana Kallon qwayar idanunta,sai taji bazata ita wofantar da alfarmar da aliyyun ya roqeta ba,saboda haka a take ta rubuta letter din barin aikin ta damqa mishi,



Aliyyu ya cancanci komai a gunta,tsananin kulawa da qaunar d yake nuna mata kadai ta isheta,abinda kullum ke dawwamar da ruhinta cikin farinciki da begensa,godiya ya dinga mata har sai da ta rufe masa baki

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Duk cikinsu babu wadda ta ankara da cikin d fadilan ke duke da shi,ba wa ni shiga sabgarsu take ba bare su ganta,don tuni aliyyu yayi mata maganinsu,iskancinsu na da suka so su dawo da shi,su shigo musu ranar girkinta a cinye abiñci da su,sannan kuma suqi tafiya suyi zamansu,bayan ita ranar nasu girkin da ta shigo ta masa barka d dawowa minti goma ta bar gurin ta koma bangarenta,duk nacinsa bata zama don bazata yi abinda idan ita akaiwa ba zata so ba



To su kam basu sàn hakanba,don haka da zarar sun wuce minti goman zai janyota jikinsa ya fara yamutsata,to yanzun nan zaka ga kowàcce ta ja qafafunta ta wuce,dariya yakeyi abinsa yace tunda ke kin kasa maganinsu abun ni gashi nayi miki ko?"ita din ma wani lkc dariyar ke ka ma ta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Wata hudu cikin amma idan ka ganshi sai Kayi tsammani yayi wata shida,sosai abun ke basu mamaki su duka,amma babu abinda fadilan ta fasa,mita da qorafi kam tana shansa,don wa su lokutan ma idan ranar girkinta ne idan zai fita gidan anty hauwa yake kaita tace"ga gajiya nan ya kawo kada a barta tayi koma,idan ya dawo sai ya biyo ya dauketa,da ya ajjiyetan sai fa ta faki idonsa ta masa girki ko da mai sauqine don tace ita kam ladan bai isheta ba



Aliyyu tace"shi kam indai lada ne ya isa haka,don kuwa ko iya cikin jikinta ya isheshi,aljanna kuwa indai shi zai dage mata qafa ta shigà to tuntuni tasa a rage take"dariya taci ranar cikin alfahari da jin dadin kalaman yabonsa a gareta

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Ya kaita gidàn Anty hauwa yadda ya saba ita Kuma tace kausar tazo ta rakata gidansu nuratu ayi mata Jan lalle,anty hauwa tace"sannu Fadila da qoqari,ko wuya zaman lallen baya miki?"
Tayi 'yar dariya "wlh Anty bana jin dadin batun hannuna ne haka,Kuma ma ya aliyyu naso"
"A'h tunda ya aliyyu na so sai a bada himma,don na fuskanci kin gama shagwabashi gaba daya,mu nan duka yanzun ganin must yake bamu iya zaman aure ba"ta qarashe maganar cikin tsokana,dariya ta kama Fadila lkcn da take sanya hijabinta "wlh Anty ba haka bane"
"Allah kin gama shagwabashi,idan yaso gidan nan ya dinga min fi'ili kenan"ta sake tuntsirewà da dariya lkcn bilkisu ta shigo tace"Anty kamalu driver yace ya fito da Motar mu fito,tare suka tafi akabar antin a gida


*Mrs Muhammad ce👑*

📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed💞: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺



*part 3*


2⃣4⃣

Har aliyyu yazo daukarta basu dawo ba,nan ya dinga saukewa Anty hauwa kwandon mita ya dinga yi kamar zai ari baki,safe baki kawai Antin tayi tana kallonsa
"To ni meye nawa aliyyu,kwalliya take son yiwa mijinta sai na hana?"
Dariya taso ka nata ganin yadda yaketa safa da marwa kamar Wanda kace an saceta,ga wayarta Kuma na kan Kujerar falo ta manta ta



Minti ashirin Motar su ta shigo,da suri ya qrasa ya bude mata qofar Gaisa miqa mata hannunsa ta Dora nata a kai,Jan lallen kam yayi dau ya haska idanunsa,Zara zaran yatsunta suka sake yin kyau,diba yasa ido ya sakar mata hararar wasa,ta saki murmushi idanunta cikin nashi tana langabar da kai cike da kissa
"Zaki sani tunda kika ke kikayi zaman lalle kika wahalrmin da baby,punishment dinki na yau babu ke ba tafiya da qafafunki"kafin tace komai har ya sunkuceta ita da cikin jikin nata ba tare da jin nauyinsu ba,yasa kunya ce da ita bata son ya dinga daukarta haka cikin mutañe



Cikin mitarsa ya sakata bayan ya kwantar mata da Kujerar,cikin shagwaba ta kalkeshi
"Please my haidar,baby I fa sallama da anty ba"
"Shshhhhh"ya dora yatsansa Dan man uni kan lebansa"ta yafe ba sai kin mata ba,mu tafi gida ki huta baby"ya zagayo side dinshi ya tada motar,ai kam kafin su isa gidà har bacci yayi awon gaba d ita,murmushi ya saki ya Shadda fuskarta da daya hannun nasa yanajin wani sonta na shigarshi



Yana tsaida motar ta farka idanunta fes bisa fuskarshi,sukayiwa Kuma murmushi yadda suka saba a duk yayin da suka kalli juna,ya fice ya zagayo ya bude qofar hadi da daukota cak
"Wayyo my haidar ,don Allah ka saukeni"ta fadi tana wutsil wutsil da qafafunta gami da dan dukan qirjinsa kadan kadan
"Kun manta punishment dinki kenan?"


Samira dake manner da earpiece a kunnanta ta fito daga bangareñta,kamar umarni idanunta suka sauka a Kansu,riqe bakinta tayi a ahankali ta dinga takowa indai su ke idañunta qyar kan cikin fadilan,ashar din da ta lailayo ne yasa suka ankara da ita a gun,da hanzari Fadila taci gaba da mutsu mutsu ko zata samu ya sauketa ko don idon Samira
"Kace tuni ka dirka mata mu ka barmu kara zube saboda tsabar iya cin Amana"ta fada sanda ta tsareshi d ido,girgiza kai yayi lokacin da murmushi ya subuce masa,shikam yana mamàkiñ Samira idan tayi wa ni abuñ



baiko kulata ba ya barta nan a tsayen ya nufi bangarensa don baisan me takeso ya gaya mata ba,qasa qasa Fadila ke cewa"bai kamata ba dear fa,ko nice ba zanji dadi ba"
Baisan lkcn da ya tuntsure da dariya ba"mene bai kamata ba?,cikin naji?,ai bani na baki ba Allah ne ya baki,idan da sun so wataqil da tuni Allah yasa sun Samu tun kafin ke,ko Kuma sahun nata zaki ni?"ya qarashe cikin sigar tsokana

⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Dirshan take zaune saman cinyarsa,ayabarta wadda ita ce abincin yake bare mata,sai zuba shagwabarta wadda take burgeshi take,qaramin wandone a jikinta sai Riga ta vest wadda ta fito d turtsetsen cikinta,Kanta ya sha gyara Wanda Aliyyu ne ya zauna ya gyare abunshi tsaf ya mata parking sonsa



Salima ce ta shi go da sallama ,ragowar sallama ta maqale a maqoshinta,tashin ahankali wanda ba'a sa masa rana shi Salima ta shiga,ciki?ciki a jikin Fadila?yarinyar da ta tsana take adawa da ita fiye da duk Wata halitta dake bayan qasa?,kasa dauke idnunta Sam tayi saga kan cikin,hakanne ya bawa fadila tsoro tuni ta Dora hannun nata saman cikin nata idanunta a lumshe tana ta soma karanto addu'o'in tsari,aliyyu ke Kallon yadda Saliman ke wani numfarfashi kamar maras lafiya,tuni ya soma tambayarta menene ya soma yunqurin Ajjiye Fadila don ya isa gareta



Tuni ta saki handle din ta juya ta five ba tare da tace koma ba,kuka sosai ta rushe da shi,matsananciyar qiyayyar cikin da uwarsa suka lullubeta,wani tsàutsayi ne tuntuni ya hanata sakin jiki ta cika gidan aliyyu da 'ya'ya fiye da kowcce mace da da zaya ajjiye?,take ta ciwa kanta alwashin ko ta halin qaqa ba zata taba lamincewa cikin nan ya taka doron qasa ba,domin tana ganin ita tàfi kowacce mace cancanta ta sake haifawa aliyyu yara ba Wata càn ba,nan shaidan da Zuciya suka ci gaba da tunzurata gamida shirya màta sharri kala kala

*Mrs Muhammad ce👑*

📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed💞: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 3*
2⃣5⃣



Doguwar Riga ce jikinta kamar yadda suka zamo sune shigarta na yau da kullum,sabida cikinta bai bari ta sake cikin ko wani irin kaya idan ba su ba,ita kanta girman cikin na bata mamaki,wayarta ce a hannunta tana tsarawq aliyyu tex na an wuni lpy kamar yadda yake al'adatarta kullum idan ya fita babu fashi koda sunyi Waya koda Kuma ba ranar girkinta bane



Cike da mamaki ta dagi tana masa sallamar Salima wadda ta shi go hannunta dauke da wa ni madaidaicin food flask fuskarta qunshe da murmushi,Fadila ta boye mmakin nata ta Hawa Salima tayi gurin zàma,ta sauna din kuwa idonta na akan fadilan
"Sannu uwar hudu"ta fadi cikin salon son nuna tsokana ,sai itama tayi qoqarin dora murmushin kan fuskarta
"Yauwa sannu an wuni lpy?"
"Lpy qalau"ta fada tana tunda flask din gaba fadilah
"Wannan dama na kawo miki,nasa masu ciki akwaiku da kwadayi,Duk da ba'a gaya mana qaruwr da aka samu ba,ai dan aliyyu namu ne mu duka"ta fada kai ka rantse har zuciyarta,murmushin itama ta sake yi,t janyo flask din tana budewa



Fasten dankali ne Wanda ya sha danyen kifi irin marar qayarnan,a zahiri abincin yayi don qamshin curry kawai yake zubawa,kana Kallon abincin kai kasan ba Salima ce tayishi ba don ba zata iya din ba
Amma maimakon ya burge ta sai ma tashin Zuciya da haifar mata,don ita yanzu a duniya babu abinda yake burgeta take biya ci irin ayaba ,komai dadi ko haduwar abinci,saidai ko lemon zobo,koda ta kwata cin ma amai ne ke biyo baka



Ta rufe da sauri tana mata godiya,maimakon taga salimar ta tafi sai taga tana gyara zama harda qoqarin zuba mata
"Gara kici tun da duminsa,nasan hàlin masu ciki yanzu yana kaiwa anjima zai iya fita daga ranki",da sauri fadilan ta dakatar da ita"kada ki zubamin yanzu don banajin yunwa"
Sororo saliman tayi cikin rashin jin dadi har hakan ya bayyana akan fuskarta,tilas ta haqura ta rufe ba don ta so hakan ba,saidai don bata so ta fiya matsantawa har fadilan ta dago wani abu,



Haka ta fice tana jaddadawa mata taci fa,sanda wai sai tana ci tana qoshi,hakanan fadila taji ko bayarwa bata so tayi,saboda haka ta samu baqar leda ta kwafe a ciki ta cilla cikin dustbin



kwana daya biyu salima taji shiru,ba qaramin tashi hankalinta yayi ba,Duk wani shishshigewa da kulawa tayi wa Fadila shi,duk cikin qoqarinta na ganin ta samu yarda gurinta,babu abinda bata dafa ba na kwadayi ta kai mata ba,sai dai kash....abinda bata sani ba babu abinda cikin fadilan ya sani banda ayaba

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Dukkansu sun shirya don zuwa gidañ Momi karbar lefen sumayya da rabi'ah Wanda za'a kawo ranar,mai gidan ne da kanshi zaya kaisu cikin motarshi sabuwa dal da duka dauka shekaran jiya ta iso,yayi haka ne a fakaice don fadila wadda ke sanye cikin doguwar riga ta atamfa exclusive mai adon orange da army green, Duk da turtsetsen cikinta hakan bai hanata yin adonta ba,Kuma tayi kyau abinta,ta fita daban a cikinsu tamkar zahra cikin taurari,hakan ne ya sanya aliyyu ya kasa yiwa idonsa shamaki daga kanta,Duk inda ta motsa idanunsa na biye da ita



Baisan me yake sàurin daya fushi ba,kwanakin gaba daya a fusace take,Abu dan qanqani sai ta hau masifa ko tasa kuka,har doctor ya tambaya tace masa kada ya Samu wa su matañ idan su na da ciki hakan na faruwa da su,musamman idan yaw soma tsufa suka fara gajiya da shi,to ko a yanzuñ ma ya lura kamar 'yan rigimàr na kusa,don ko su Samira da bata kulawa a irin wannan mood din tana jin dai dai take da duk wadda ta tabata a cikinsu



Ya sake kallonta,tayi lullubi har saman kanta da farin mayafi da ya dace da atamfarta,ba kamar lullubin 'yan uwanta ba ita kafada,sai ta sake masa kwarjini,cikin ya mata kyau duk da dan uban girmansa Wanda ke sake sashi jin tausayinta tare da sake mata addu'ar sauka lfy



hannunta harde saman cikinta,tayi kicin kicin da fuska,hada ido sukayi ,ta same qwayar idonta ta wani dauke kanta tamkar bata ganshi ba,dan qaramin murmushin nan nasa ya saki,wani lkçn salon shan qamshinta da miskilancin nan nata na burgeshi,ta iya shariya da dake kai da gangan



Ya dubi salima wadda ita ke dà girki,ba yadda ya iya a zahiri zaifi son ace Fadilar ce kuwa da shi,ya danna madanni ya bude gidan gaban da a dazu yake a rufe yace da Saliman"shigo nan"



sai ta tsinci kanta da jiñ wani bacin rai,suka Kuma hada ido,batasan sanda ta danna masa harara ba gami dà Jan dan qaramin tsaki a ciki,ta shige sit din can baya na qarshe tana kumburi


*Mr s Muhammad ce*👑


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed💞: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*PART 3*

2⃣6⃣


Jinta take kamar ta fashe,ita kanta tana mamakin yadda yake saurin fusata a yanzu,Duk da ta sani akwai tsananin kishin aliyyu dake dawainiya da ita,tabbas ba kuwa ce maca ce ce zata San Wayne ainihin aliyyun ba ta kada kishinsa,musamman ma ita da kunsan tafi kuwa saninsa zahiri da badininsa



Salima nata rawar kai ta shige gaban,Aliyyu ya tada Motar yana qoqarin gyara madubin motar ta yadda zai samu sukunin gano fuskarta sai dai sam taqi yarda da hakan don tuni ta kautar da fuskarta,dole ya haqura ya soma tuqin hankalinda na rabe gida biyu



Duk yadda salima yaso ta janye hankalinsa suyi hira mai tsawo da dadi ko don ta cusa musu haushi abun ya faskara,dole daga qarshe itama ta haqura ta ja bakinta tayi shiru
Ko da suka shi go harabar gidan tamkar dama Allah Allah take su iso tuni ta rigasu ficewa tamkar bata jin nauyin jikinta,ya biya da ido don ba haka yaso ba



Yaso ne ya datseta a cikin Motar ya mannata da jikinsa ya dan rage mata temper,don a matakin da take ciki tana buqàtar wannan,salima dake lure da shi takaici ya cikata,ta sake qullatar Fadila,ta Kuma sake lasar takobin hana abun dake cikinta tayuwa kota halin qaqa



Ya dauke idanunsa lokacin da ta bace wa gàninsa,bai bai ta kan yadda suke kàllonsa kamar zasu cinyeshi danye ba ya jaw wayarsa dake gefensa ya latsa number din Anty hauwa ya kira,bugu uku ta daga
"Hello mummyn kausar,ga ajiyata nan as usual, pls abata kulawa ta musamman Anty na"dariya ta saka
"Ho,aliyyyuuuu.......to naji,mene tukuicina?"
"IPhone 7 da kike son siya ki bar kudinki ni Zan Waya miki"ta sake dariya"lallai Ashe abun na yine,to ba Matsala,kada ka damu dan qanina"
"Thanks Anty",ya fadi yana kashe wayar



"Amma fisabilillahi tuni yaushe bace maka ina son iPhone 7 din nañ ,kowa cikin qawayena ita suke riqewa ammavkaqi siya mini,sai ganshi rana tsaka kace zata siyawa Waya",Kallon da yayi mata ya sanyata yin dañasañin yin furucin,tuni kafin yace wani Abu ta balle murfin Motar ta fice tana qunquni cikin ranta Wanda ta bata isa ta yishi a fili ba,don ba qaramin wuya ta ci ba lokaciñ da ya amshe mata key din mota da wayarta bakamin ya dawo matà da su



Ya maida idonsa kan salima,tayi qoqarin hadiye bacin ranta don son cimma qudirinta kan fadila cikin ruwan sanyi ba tare da an gano komai ba,ta bude motar itama ta fice ranta na mata wata iriyar suya,tanajin zata iya koda kawar da fadilah ne don ta shigar mata hanci da qudundune da yawa,tasa ta rasa fili da gurbin da ada take jin tana da shi a zuçiyàrsa



Cikin falon ma kowa sannu yake mata,ciki wata bakwai amma sai ka dauka da ka

Please Login or Register in order to submit comment