Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ashe yafi wanda yake ma girkin ta?,sai yanzu ya fara ankara da dalilin da yasa yake hasala da yawa idan bata gyara masa part ko bata masa girki ba fiye da yadda yake jin zafi yake hasala fiye da su samira?,sai yanzu ya gane dalilin da yasa yake jin haushi idan ta kammala girki ta bar masa bangarensa kafin ya dawo?,sai yanzu ya fuskanci dalilun da yasa yake qin cin abinci har sai ya tilasta ta ta zauna by his side har sai ya kammala?,ashe sone hakan?,wani irin salon sone wanda bai farga da wane lokaci da kuma yaushe ya shiga zuciyarsa ba sai yanzu?,ba abun mamaki bane don bai taba kamuwa a akaran kansa da *SO* din ba sai a kanta,tamkar ya taso ne ya saba da cusa masa shi ake ta qarfin tuwoKamar ya jawo goben haka yake ji,daren gaba daya ji yayi yayi wani mugun tsawo a gunsa kamar jansa aka dada yi,gani yake kamar gari bazai waye ba,kayanta dake cikin cupboard gana daya ya watsosu ya barbazasu kan gadon ya kwanta akai yana shaqarsu ko zai samu sa'idar zugi da zillo da zuciyarsa ke masa game da ita,saidai inaa....kama da wane bata wane,tamkar wani zautacce haka ya koma idanunsa jazur bashin baccin jiya da yau gabadaya kuma bacci bai ziyarceshi ba sai gab da suba🔅🔅🔅🔅🔅🔅Kiran wayarsa su mr lun ke tayi amma gaa daya layukan switched off,suna baqatarsa sosai don awanni uku kacal ya rage a soma gudanar da bikin,baqi masu zuwa nata tambayarsa,hakan yasa andi da kansa ya taho gidan takanas ba shiriCikin bacci yaji anataba qararrawa da alamun neman izinin shigowa ake,tsaki yaja ya maida kansasaman filon hadi da maida fuskarsa hannun hagu maimakon dama a yadda take dazu bashi da ko niyyar tashi,saidai mai danna qararrawar yaci gaba da matsata kamar babu gobe har sai da mijin nadiya ya fito abdul basid,hakanne ya sashi miqewaa fusace ya zare rigar saman ya cire tie din ya wurgar ya bar 'yar ciki ya fito cikin haushin kaza huce kan damiSuna hada ido da andin yasan cewa babu lafiya fa,don kalli daya zaka yima aliyyun kasan ya koma wani hargitsatstsen aliyyu,cikin tsawa yace "what doyou want?!" Cikin girmamawa yace "sir d time is passing,u have to prepare........." "leave me alone!" Aliyyun ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu cikin wata tsawar,ya ja qofarsa garam ya kulleta ya koma cikiSaman kujera ya koma ya zauna yana nishi,sai a alokacin idanunsa suka sauka kan wayarsa da ya tarwatsa jiya,yasa hannunsa ya tsince ya maida layukan ya sanya batirin ya kunnata,servicena gama hawa massage suka yita shigowa sun kusa hamsin,ko guda baiyi sha'awar budewa ba bare ya karanta,hasalima hankalinsa bai kanta nashi tunanin daban,cikin haka kira ya shigo,bai ko kalli wayar ba bare akai ga batun dagawa,sai da tayi ta katse har sau biyu,cikin jan tsaki ya sanya hannu ya janyo wayar da niyyar kasheta,number din uncle abba ya gani,bau damar kashewa kenan,luguden bugu kawai zuciyarsa ke masa,ya danna ok,ya gama bada amannar cewa fadila taje musu ne,ba qaramin rudewa yayi ba saboda sanin halin abban nasa sarai bashi da sauqi kan wasu lamuranYa kara a kunne jiki a sanyaye,tambayar da abban nasa ya masa ta sake sashi cikin wani halin ha'ula'in"me kake yi haka ne aliyyu?,lafiyarka kuwa qalau?" Cikin rawar murya yace "abba...wallahikuskure ne....kuskure aka samu kuma....."ya dakatar da shi"ya isa bana son jin komai maza ka tashi ka shirya,mr lin ne ya kirani ya gaya min komai har mutum ya aiko maka ka koreshi,damar da ka ka jima kana jira yanzu don ka sameta shine kakeso kayi wasa da ita?,maza ka ahirya kafin lokacin yayi kamar yadda aka tsara"wata boyayyar ajiyar zuciya ya saki ya maida bayansa jikin kujera "to abba inshaAllahu" suka qare wayar yana masa addu'ar samun nasara tare da sanya masa albarkaYa kashe wayar sannan ya zuba mata ido,yana ji a jikinsa da zuciyarsa bai kyautawa abban nasa ba ma,bai san da qanne ido zai kalleshi ba,cikin kasalartasa ya miqe ya shiga toilet ya hada ruqan wankanshi da kanshi don cika umarnin abban nasa,awanni biyu ya dauka ya kammala shiryawa,komai da yakeyi babu walwala a fuskarsa,dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka? Hakanan babu kuzari ko qanqani tattare da shi,shigarsa ta suit yayi saidia wannan ta musamman ce 'yar ubansu,wadda dama an tanadeta ne domin wannan rana,maqudan kudade aka kashe gun siyan nata,kai da kanka idan ka kalleta ba sai angaya maka ta lashi kudi ba zaka baiwa kanka amsa ash ce mai cakude da yarfin baqi rigar ciki kuma da tie dinsa kuma light pink ne,agogo da ya daura da takalmi na qafarsa ma kawai abun kallo ne,sumarsa tayi kyau sosai kamar yasa mata relaxer,sosai aliyyun yayi kyau tamkar balarabe,yaya dama mai kyau yasa abu mai kya?,saidai cikin zuciyarsa sam babu nutsuwa ko farinciki ko dayaSuna waje suna jiransa cikin dalleliyar sabuwar baqar mota,sabuwar qira ce don a shekarar aka farahawanta,yana daya daga cikin kutane na farko da suka mallaketa ko a qasar chinan,mutum uku ne suka miqe ya watsa musu harara don yana ganin susuka takurashi zuwa gurin tamkar su suka yi laifin,dayan ya bude masa inda zai zauna yayin da ragowar biyun suka bishi da gaisuwa,baiko kallesu ba sun san ba lafiya son haka basu sake cewa komai ba suka shiga mai tuqi ya tafa motarTafkeken dakin taro ne dake cikin ginin kamfanin*maitama factory*,hall ne da yaci sunan hajiya*maimunatu ibrahim muhammad* mahaifiya gareshikenan,cike yake da al'umma mahalarta taron,sosai aka qawata gun,decoration aka masa mai azabar kyau da tsari,kowanne table kujeru hudu ne suka zagayeshi,kusandukka mahalarta taron sunyi shiga ne ta baqaqen coat kamar masu ashobi,maza ne damata jinsin yarw da qabila daban daban,kowanne zaune gurinsa a nutse cikin tsari suna sauraran bayanai daga bakin mai gabatarwa duk cikin dakon isowar aliyyu,babu wata hayaniya kai sai ka rantse babu mai numfashi cikin hall dinShigowar tasa ya sanya duk wani dake dakin taron miqewa tsaye cikin girmamawa,tafi ya cika hall din raf raf raf,tamkar ya zura da gudu ya bar hall din haka yake ji don tafin nasu wani kuda yake masa akunne,sai da ya hau step din da ka tanadar musu don zama gefan hannun hagunsa mr lin kusa da shi miss sisineo ce hannun damansa kuma ramzan ne kusa da ramzan kuma mukhtar ne,sai da auka kmmla zama sanna kowa ya koma.mazauninsaya zaunaDakin taron ya sake yin shiru,mai gabatarwa ya yi wa aliyyi barka da isowa,sannu a hankali aka ci gaba da gabatar da taron yadda aka tsara daki daki,duk anun nan da kae maganar minti biyu aka ritsa aliyyi da bindiga aka ce ya maimaita saidai a harbeshin don baya gurin *gangar jikinsa* ce kawai zaune,hankalinsa na kan fadila da agogo,duk bayanminti guda sai ya duba lokaci,jawabai masu muhimmanci da ka tsara shi zai gabatar babu ko daya da ya iya yi,sai ya bada uzirin baijin dadi sosai,drinks da kayan ciye ciye da ka cika gaban kowa da shi babu qanda ya iya kalla balle ya tantance yana sha'awarsu ko baya yi bare akai ga batun zai ci ko zai shaAwanni biyu aka dauka sannan aka zo gangara,su mukhtar suka tilastashi kan dole ya karba yayi jawabin godiya ga dimbin al'ummar da suka.tako gari ya gari suka zo masa,yana ture lasifiqar yana komai haka mukhtar ya manna masa ,idanu da sukamasa ca yasa ya sa hannu cikin kasala da rashin sanin a halin da yake ciki ya amsa"Fadeelah!" Abinda ya soma mabata kenan cikin bututun maganar,tsit suka yi fiye da wanda sukai dazun tamkar wanda yayi calling attention nasu,ido kowa kr binsa da shi don dai sun san suna.ya ambata "fadeelah ta soni matuqa cikin rayuwarta.....na zauna da ita cikin boyayyen nuni gairin tawa kalar soyayyar gareta",ya danyi jim sannn ya shaqi numfashi ya dora "fadeelah ta barni a lokacin da ya bayyana gareni na dade nima ina sonta ba tare da nawa sanin ba....ta barni a lokacin da nake da buqatar yi mata mafificiyar soyayyar da ba'a taba gwadawa wata 'ya mace irinta ba......ta barni da wani nauyi mai azabar nauyi cikim zuciyata ba tare da na samu na sauke mun raba tare ba......fadeelah ta zama ruhina da gangar jikina"dora hannun sa yayi saman qirjinsa saitin zuciyarsa "fadeelah ta mallaki nan ba tare da saninta ba,ya dade da zama mallakinta ba tare da sanin ku mu duka biyun ba""Na tsinkayi fushi fusata da rashin fahimta masu tarin yawa qunahe cikin kalamanta,qunshe cikin takardar da ta zamo baqa aguna,cikin saqon dake bayyana bankwana da abinda zuciya ke so,cikin shafin takarda qwaya daya tal saidai sun yimin nauyi fiye da littattafai dari masu shafuka dari dari"ya hade tafukan hannayensa guri guda yana yinsa ya sauya soaai da alamun abinda yake fadi din na taba zciyarsa sosai,da alama zancan daga ainihin zuciyarsa yake fita ba daga harshensaa yakeba "ku yimin alfarmar sani a addu'o'inku....ku yimin alfarmar roqa min Allah ya huci zuciyarta,na gode muku baki daya...."ya fadi yana qoqarin komawa ya zauna,gaba daya suka.miqe suna tafi,yanayin salin ne ya burgesu,fuskarsu da zuciyarsu cike da tausayinsa,abunka da mai jajayen kunnuwa akwai girmama soyayya komai tsufanta,miss sisineo ce tabude 'yar jakarta ta fiddo da bangles na gwal guda biyu danqara danqara ta ajjiye gaban aliyyu tace ga kyautar ta a isar da ita ga fadilaSosai abun burgeshi ta yima fadilansa kyauta duk da yana da arziqin da zai siya mata ninkin wanann amma ayi kyauta wa masoyinka ma abun faranta ranka ne,yasa hannu ya dauke yayi masu kyakkyawar ajiya..........*mrs muhammad ce*👑📘📘📘✍🏻✍🏻✍🏻✍?


👉🏼 *PART 3*👈🏼

3⃣&4⃣

Bayan ciye ciye da akayi a gun suka soka fita gun ainihin ginin kamfanin wanda aka zagaye shi da wani yadi mai kyau aka daure bakin qofar shigar da shi,aliyyun ne a gaba a tsaye andi ya miqo masa qaramin almakashi ya amsa ya dora saman yadin ya datse,tafi aka saki sannan suka dunguma gaba daya sukayi ciki,guri guri suka dinga shiga daya bayan daya cikin kamfanin,sosai ginin ya tsaru yayi kyau matuqa da gaske,komai cikin fasali gwanin sha'awa

Ba qaramin qaguwa yayi ba,duk bayan minti daya idanunsa na kan agogo,gani yake kamar yanga lokacin yake masa,binsu kawai yake ba tare da fahimtar abinda suke yi ba,sam hankalinsa bai tare da su,cikin dabara ya zame jikinsa ya koma office dinsa wanda aka tanadar masa ko da zai zo wani lokacin,yasa key ya bude ya shiga sannan ya koma ya kulle ya koma saman kujera ya zube,awoyi uku ya rage jirgin nasu ya tashi,baya tsammanin zai iya zaman jira,ya zaro wayarsa cikin hanzari ya kira jumong da mukhtar

Tare sukayi knocking ya tashi ya bude musu,kan kujera mukhtar ya qarasa ya zauna yayin da jumong ya rusuna yana jiran jin umarni,"ka shirya mota zan fito yanzu zaka kaini airport" "ok sir" ya fadi hadi da juyawa cikin hanzari ya fice,yayin da mukhtar ke kallonsa yana son tambayarsa me zaya yi a airport?,bai bashi wannan damar ba ya soma masa bayani da kansa ba tare da ya tambayeshi ba "nijeria zan wuce mukhtar nan da awa uku,ina son na bar komai a hannunka kayi handling dinsa,bazan yi sallama da kowa ba its urgent,ka wakilceni please"cikin rashin fahimta yake dubansa "like how aliyyu baqin naka zaka bari ka wuce nijeria?" "Pls mukhtar if u cannot help just tell me directly" yasan halin kayan sa sarai saboda haka ya gyada kai "is ok,is ok I will" ya miqe tsaye ya sake duba passport nashi da ticket dake cikin jakan sa,yaga komai na nan yadda zai buqace shi,ya dauka gami da zaro master card platinum ya ajjiyewa mukhtar din sukayi hand shake "thanks" aliyyun ya fada a gaggauce sannan ya bude qofar ya fice,mukhtar da mamaki ya cika shi yabi aliyyun da kallo galala,gaba daya aliyyun ya fita daga hayyacinsa sam ya fice daga nutsuwarsa

Ta get din baya ya fice don baison kowa ya tsaidashi,don kuwa baiga abinda zai tsaida shi daga tafiya nijeria ayau din nan ba saidai ikon Allah,ko cikin motar ma gani yake jumong baya sauri laqaqai laqaqai kawai yake,gaza haquri yayi har sai da ya soma masa maaifa kan ya qara gudu "sorry sir ida mukayi gudu ya wuce qa'ida camera na kallon mu za'a iya kama mu" sai a lokacin ya tuna ba'a nijeria yake ba dole ya haqura a haka har suka isa airport din,ko jirgin ma gani yake ba sauri yake ba shirme yake(hhhhhh),da suka sauka ko a ethopia aka basu dakunan kwana kan sai gobe zasu qarasa nijeria jinsa yayi kamar a saka shi a kurkuku,masifa kawai yake yana fadin dole ya sayi private jet nashi,dole yana ji yana gani ya haqura har sai washegarin

🔅🔅🔅🔅🔅

Qarfe goma na safe a garin kano tayi masa,tuni nasiru yazo da mota don daukarshi,gidansu yace ya wuce da shi kundila maiduguri road,yana shirin fitowadaga cikin motar saiga sumayya ta fito cikin shirin tafiya school,da sauri ta sauya akalar tafiyar tata ta nufo gurin motar fuskarta qunshe da fara'a"sannu da zuwa ya aliyyu" ta fadi tana leqa cikin motar cikin neman fadila,"yauwa" yace yana sanyo qafarsa waje,ya dubeta cikin dakiyar nan tasa "ke,me kika bani ajiya kikemin leqe leqe cikin mota" sai ta dawo ta tsaya dai dai cikin fara'a "anty fadila nake leqe ko zan gani yaya,surprising din mu kuka so yi shi yasa ko a waya bata gaya mana ba,kwananta biyu ma bata kira mu ba ashe kuna hanya"da sauri ta juya tana shirin komawa ciki tace "bari na fara yi mawa momi albishir"sosai jikinsa ya mutu basu da labarin ma ta dawo to me yake faruwa ne?"maida qafar tasa yayi cikin motar ya rufe ya bawa nasiru umarnin ya kunnata su wuce sani mai nagge(unguwar su fadila)

Har cikin gidan malam ya bude musu suka shiga,ya fito ya ningina jikin motar bakinshi fal addu'a,yana tunanin yadda zai shiga gidan ne,sai ga muhammad ya fito daga inda suke ajiyar motocinsu hannunsa dauke da qaton almakashi irin na yankan shuka,nasiru ne ya qwala masa kira,da sauri ya juya ganinsu yasa shi nufo gurin yana fara'ar ganin aliyyun,"sannu da zuwa yaya"muhammad ya gaida shi ya amsa masa "kai da anty ne yaushe kuka dawo amma bata gayama ummi zaku dawo ba"ya fadi yana washe baki da son jin amsar inda yayarsa take,innalillahi wa inna ilaihi raji'un"aliyu ke fada cikin wani irin hali,muhammad ya juya yana fadin "bari nakira abba bai fita ba"aliyu na shirin hana shi saiga abban ya fito ummi na riqe da jakarsa

Sosai abban ya nuna jin dadin ganin aliyun,yasa muhammad ya bude sitting room suka shiga,maganar da abban ya qara fadi ita ta sake tabbatarwa da aliyyu fadilan bata zo gidan ba"ina mai kukan tafiya yanzu dai ai kuka ya qare ko tunda gashinan anje lafiya an dawo lpy"aliyun ya sunkuyar da kai wata fargaba na shigarsa "tana lafiya abba" abinda ya iya fada kenan,to shima abban bai takura masa da wata doguwar hira ba ya sallameshi shima ya fice kasuwa

Gidansa kawai yasa nasirun ya kai shi don bai san kuma me ya rage masa ba,tunaninsa ya tsaya cak,a harabar gidan ma'aikata ne kowa na masa barka da dawowa,baijin ma me suke fada hannu kawai yake daga musu,ya sallami nasiru ya fito daga cikin motar yana shirin shigewa ciki aka sake dage gate din gidan,tsayawa yayi hadi da juyowa don hajin wanda aka bude mawar,motar samirah ce wadda ta sake cin ubanta,su hudu ne cikin motar,wata dabance ke driving din samirah na gefanta sai wasu su biyun a baya,dariya suke ta sheqawa sam basu ma kula da wani aliyyu ba har suka yo parking,har ta fito tana sheqa dariyarta kamar wadda aka yiwa albishir din ba zata mutu ba,cak ta tsaya tana kallonsa kamar yadda shima ya zuba mata ido,suma qawayen dariyarce ta tsaya cak,sun san halinsa sarai baya da kyau,sum sum daya bayan daya suka fice daga gidan,kai kawai ya gayada ba tare da yace mata komai ko ya sake kallonta ba ya shiga bangaransa

Yafi mintin talatin a zaune kafin ya miqe yaje yayi wanka,kafin ya kammala shiryawa anyi kiran sallar azahar,duk wani motsi da zaiyi tana manne cikin ransa,duk wani tunaninsa na ina zai sameta?ina zai ganta?ina kuma yanzu zaije nemanta?,cikin yadin tissue fari tas ya shirya,yayi kyau sosai duk da kana kallonsa zaka karanci bai cikin walwala duk da kusan hakan yanayin fuskarsa yake amma wannan karon ya ninka yadda yake da,ficewa yayi kansa tsaye ba tare da ya nemi kowa ba da kansa ya ja motar ya bar gidan

Sai da ya fara tsayawa a masallacin bakin layinsu ya bada faralin sallar azahar dinsa sannan ya wuce,kai tsaye yahaya gusau ya wuce gidan farida,ya dan jima a tsaye a qofar gidan baiga gilmawar kowa ba har yana shirin komawa sai ga dahiru almajirin faridan,da sauri dahirun ya qara so inda aliyyun ke tsaye don ya ganeshi,cikin girmamawa ya gaida aliyyun,ya amsa masa yana tambayarsa matar gidan na ciki?,ya amsa masa da "eh alhaji ko a kira maka ita za'ayi?" "A'ah tambayarka dai nake so nayi"aliyu ya fda yana gyara tsaiwarsa "to..Allah yasa na sani" "tayi wata baquwa tsakanin jiya da shekaran jiya da yau?" "Kai gaskiya a'ah,don suma jiya suka dawo daga lagos ita da mai gidan"ya fada masa cikin bashi tabbaci

Idanunsa ya rufe yana jin wani abu sannan ya bude,ya saki qaramar ajiyr zuciya sannan ya ciro kudi ya bama dahirun ,cikin murna ya amshe yana zuba godiya,bai bi ta kan godiyarsa ba ya shige motar ya tasheta ya bar layin

Har la'asar aliyyu salim na bulayi bisa titunan kano,shiga wancan fita wancan,ko manshi da yake qonawa bai damu ba,ya rasa inda zai zauna bare yayi tunanin mafita,gaba daya feeling kansa yake a matsayin guilty,cikin rudanin inda ta tafi yake,ina ta boye kanta haka?,duk da yana ji daga can cikin wani sashe na zuciyarsa na gaya masa she is safe and she is in safety place

Sai da ya soma ganin gurare daban daban na ta alwalar sallar la'asar sannan ya samu ya kashe motar a bakin wani masallaci ,ya daura alwalar ya bi jam'i,sai bayan da ua idar ne yaji cikinsa na qugi sannan ya tuna rabonsa da abinci har ya mance,ya miqe ya koma cikin motar tasa ba tare da yabi ta kan yunwar dake sakadarshi ba,sai da akayi sallar magariba yana bilayin yawon titina sannan ya gano cewa wannan fa ba mafita bace,tunanin matsalar itace zata samar masa mafita da gano masa inda fadilan ta boye,ya juya akalar motarsa ya nufi gidansu dake kundila. .......

*mrs muhammad ce*👑

📘📘📘📚📚✍🏻✍🏻


[10/16, 2:09 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


👉🏼 *PART 3* 👈🏼


5⃣&6⃣

Yana shiga ya tadda rabi'ah kan dining area ita da iftihal momy na kitchen,da alamu su din ma zaman na cin abinci ne,da gudu iftihal ta gangaro tana ihu "yeyyyyyy daddyyyy"kamar yadda ta saba ta duqa ta gaidashi,ya amsa mata maimakon ya dauketa ya shilla sama yadda suka saba wannan karon sai taga kawai ya shafa saman kanta yayi hanyar kitchen din,ta tabe baki kamar zata saki kuka

Tana kiciniyar rufe warmer taji an rufe freezer,ta dago kai da sauri aliyyun na tsaye yana daddakar ruwan mai azabar sanyi,sai da ya shanye robar guda momin na kallonsa ta zuba mai ido,ganinsa take a wani birkice duk da jikinsa fes yake kuma ya yi kyau da 'yar cika(sakamakon kulawar da ya dinga samu a china)amma abunka da mahaifiya kallo daya tayi masa t gano akwai damuwa a ransa

Yana qare shanyewar suka hada ido da momin,sai ya kautar da kai ya sanya robar cikin dust bin yana cewa "momi barka da dare ina wuni"bata dai daina kallon nasa ba tace "lafiya lau Ali kun dawo lafiya?" "Lafiya qalau ha fada yana jan kujerar plastic dake kitchen din zai zauna "mun sameku lafiya?" Ya sake tambayar momin yana dauke kai don baya son irin kallon nan na momi,nan da nan take naqaltar mutum,itama sai ta dauke kan tana ci gaba da rufe warmer din tace"lafiya lau,tun safe sumayya tace min gaka,shiru shiru baka shigo ba ko da aka leqo kuma ba kai a gun"ta qarashe maganar idanunta a kansa kamar tana son jin amsa kenan

Ya basar da zancan ta hanyar cewa"rabu da wannan shirmammiyar yarinyar momi,makaramta fa zata tafi amma don gulma ta koma,gida muka qarasa kawai"ta dire warmer din tana cewa"ina 'yata fadila" gabansa sai da ya buga "lafiya"kawai ya iya furtawa tare da miqewa don kada ta sunkuto masa wata tambayar da zai gagara kubutar da kansa,ta waiwayo tana cewa "a'ah ina zuwa kuma?" "Zan wuce gida ne momi" "baku gaisa da abban naka ba,yana gida fa,kuma ma na zaci tare zamuyi dinner ko?" Abinda momi bata sank ba bazai iya jiran abban nasa ba don gani yake kallo daya zai masa ya karanto abinda ke faruwa,karo na farko da aliyyun yayi ma momin qarya a rayuwarsa

"Zani gida ne momi za muyi magana da mukhtar,na baroshi ne da mutane a can wadanda ban sallamesu ba na taho" to da yake ma qaryar bata karbeshi ba sai ya jada harda subul da baka ba tare da ya ankara ba "ya zaka dawo bayan baka sallami baqi ba ali?,wai meke damunka ne haka?,a kunnena fa abbanka ya tursasaka zuwa bikin bude kamfani,yanzu kuma ka taho ka bar jama'a acan,baqonka annabinka fa ali"yayi saurin dosar qofar fita yana cewa"momi ai ba matsala mukhtar zaiyi komai kamar ina nan,sai da safe momi idan abban ya sauko ki gaida shi ina hanya goben"baki sake ta bishi da kallo tana ayyanawa tabbas akwai abinda ke damun yaron nan,gashi da shegen zurfin ciki kamar mace,idan kaji cikinsa to ya ciyoshi ne,ta dan daga murya tana cewa"ka gaida mutan gidan" "zasu ji momi" ya fadi yana barin falon cikin sauri don kada suci karo da iftihal ta tsaida shi

Har ya koma ya bude sashensa ya shiga yayi wanka ba wadda ya gani,shi yama fi son haka din ma,yasa koda sunzo babu abinda.zai samu sai qarin tension,shi kuma yanzu abinda ke damunsa yasha kansa fiye da komai,sai da dibi kusan awa daya da wani abu sai ga salima,fuskarsa ta zubawa ido tana murmushi saboda sosai aliyyu ya canza,ya qara ja sumarsa ta sake baqi sidik,gargasar jikinsa kamar an dada mata baqi laushi da yawa,ya sake kyau,badon fadila da ta hargitsa masa lissafinsa ba da abun yafi haka,hakanan shima ya sakar muta fuska don ya zama dole haqqinsu ne don bazaya yiwu haqqin wani ya danne na wani ba,kuma matsalarsa yasan ba tasu bace indai ta wannan bangaren ne

Da sauri ta qaraso ta zube ajikinsa tana fadin "oyoyo welcome my dear"yadan karata ajikinsa yace "thank you ya muka sameku?" "We are fine but I miss you" yadan saki fara'a "ok,to ai yanzu gani mai zan samu?" Ta tabe baki sannan tace "ba komai tunda ai ba yau kace zaka dawo ba ganinka kawai mukayi tsakar rana,ni ta window ma na hageka ka fice" "ni din ma haka dawowar ta zo min" cikin son bin qwaqwafi tace "ko fadilan ce ta takura sai andawo?" "Eh"kawai yace mata cikin som kashe maganar don tamkar allura ce akan qurji idan aka tada masa da zancan fadila, "but ban gata ba kuma ma bangaren ta akle yake" "eh"ya kuma cewa dai bai buqatar taci gaba da yin maganar

Shiru ya dan ratsa dakin kanta na jingine a kafadarsa,kishin fadilan duk ya cikata gani take kamar wani gun ya kuma kaita don ta huta,samira ta danno kai harda sallamarta kamar gaske kai a sunkuye,duk da haka saboda tsabar neman bala'i sai da ta gasawa salima hara ra,ai kuwa itama bata yi qasa agwiwa ba ta rama don ba qaramin adashen tsiya suka dinga shukawa ba sanda baya nan,kullum sai an raba gari a gidan saidai idan garin Allah bai waye ba,amma kwana suke su wuni suna abu guda kamar karnuka,suna hada ido da aliyyu ya bata tasa hararar tayi saurin sadda kai qasa,gefansa ta zauna cikin tausasa murya tace masa "sannu da zuwa an dawo lafiya?" "Lafiya"yace mata a taqaice,duk sai taji ta muzanta,tafi kowa sanin laifinta,gargadi mai zafi babu irin wanda bai musu ba kafin ya tafi kan fice fice,duk da yau ma tsautsayine amma ta kwan biyu bata saci fita din ba,wannan ne satar fitarta ta hudu salima tayi biyu tana tsammanin tayi na qarshe tunda ya kusa dawowa qasar bata san yau ya dawo ba

Shiru ya gauraye falon kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,aliyyu yafi kowa nisan kiwo cikin duniyar tunani,"dear ya kamata muje ku kwanta ko?"salima ta fada tana kashe masa idanu,da sauri samira ta dago "kamar yaya?"cikin

Please Login or Register in order to submit comment