Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wayayya mai faran faran da son jama'a duk da ita miskila ce,wunin ranar tayi shine tare da managing director da wasu ma'aikatan tana arranging din ayyukanta ciki harda tsara sabin shirin da suka qirqiro wanda za'a fara gabatar da shi a asabuwar shekara wanda itace mai gabatar da shirin da taimakon fauziyya ta sake fuskantar yadda abubuwa suke duk da dama tasan da wasu lokacin attachment dinta
Kwana biyu tayi tana tsara komai ta mai da kanta busy sosai ta hana kanta sukuni hakan yasa bata da wani lokaci na tunani ,da ta koma gida tayi wanka tayi sallah sai ta samarwa kanta abunci simple ta ci sai kwanciya idan da wuri ta dawo kuma takan yi tilawar alqur'ani tunda dama ta jima da kammala haddarsa tun lokacin da tayi candy,idan ta gama taga tana da wani lokcin sai ta dauki wani aiki da zai taimaketa a office ta yi ko tayi amfani da laptop dinta tayi research na wasu abubuwan masu muhimmanci,a rana ta uku ne da taga komai ya kammala ta nemi hutu na kwana biyu ba wani matsala suka bata tunda dama bata soma gabatar da ayyukan ba cikin shirye shirye dai take,tayi hakanne don a lissafinta ya bata yau itace zata karbi girki ,kuma dama tuni ta shiryawa zuwan ranar
Da wuri ta koma gida ruwa kawai ta watsa ta zura doguwar riga har qasa mai hannun shimi ruwan hoda ta saka,ta taje dogon gashinta ta daureshi da ribbom shima ruwan hodar ne,farin hijabi ta saka wanda iyakacin qirjinta kawai ya rufe,ta wuce locker dinta ta lalubi inda ta adana muqullan da bata amfani da su ta debesu gaba daya ta zira farin silifas na fata ta fito,a falonta ta soma tsayawa ta bude fridge ta dauki lemon chi exotic nectar na pineapple da yayi sanyi sosai ta sha ta maida sauran ta rufe sashen nata,
TO FADILA SAI INA?🤔

🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣5⃣
Kai tsaye sashen Aliyyu ta nufa gabanta na dan faduwa kadan kadan har ta isa qofan,addu'a fal bakinta ta ke sanya muqullan daya bayan daya take gwadasu har ta dace da na qofar,ta tura babbar qofar ta shiga sanyin a.c ne da daddadan turaren aliyyu ne yayi mata maraba,ta dan lumshe ido kadan sannan ta waresu sosai kamar mai neman wani abu,a hankali take bin kowane sashi na falon da kallo tabbas yana buqatar gyara,bata shakka cewa har bedroom dinsa ma na buqatar a kintsashi,ba tare da tsayawa wani dogon nazari ba ta dauko dust bin dake falon ta ajjiye a tsakiyar falon ta zare dan hijabin nata ta jefashi kan kujera ta fara tattare ta fara tattare leda takarda gwangwani da duk wani abu da ya zama datti ne tana jefashi cikin kwandon sharan
Tana tsaka da aikin ne taji ana taba qofar alamar an shigo a tsorace ta dago tana tsammanin aliyu ne sai dai kuma maimakon haka sai taga ashe salima ce tayi tsaye a abayanta tana qare mata kallo ,fadila ta tsani yadda matar me mata naci nkallo haka,dama ita tun da can ta tsani mutum mai azabar kallo,to haka saluma ke mata a duk sanda hanya zata hada su ,abinda ita fadila bata sani ba shine kishine taf cike a zuciyar saliman don so tayi ta samesu gaba daya babu mamora kamar yadda taga samira bata da qira sam,saidai ance gwano baijin warin jikinsa ne ita dinma da tayi dogon nazari da tsinkaye da ta fahimci yadda tata qirar take irin matan nan ne masu azabar tsawo da sirantaka sai wani azababben fari da take da shi irin me gauu din nan to duk da babu laifi tafi samirah amma ko kusa bata kamo qafar fadila ba,tsawonta da azabar sirantaka su suka sata take a miqe kamar number 1 ba wani shape sai tsabar iyayi da yauqi
Ta kau da kai.daga kallon fadilan ta tabe baki sannan tace"oh nayi tsammanin mai gidan ne ya dawo da naga gun a bude" a taqaice fadila ta amsa mata da"A'a" taci gaba da aikinta,sai kawai salima ta bude fridge ta dau maltina hadi da kunna t.v ta nemi gu ta hakimce,sarai ta gano ba abinda yasa saluma zama a gun banda bin qwaqawafin taga me take yi hakan yasa ta sa key ta bude bedroom dinsa ta shige tare da rufe qofar da muqullin ta ciki,salima tabi qofar da kallo cikin takaici don ba haka ta so ba,nan ta zauna tana ci gaba da shan maltinan tana dakon fitowar fadila wadda batasan ma tana jiran ba
Ta qarewa shima bedroom din kallo sannan cikin nutsuwar nan tata ta fare tattare shi shima tana kintsa komai a muhallinsa tanayi tana mamakin kamar babu wasu mata dake kwana a dakin komai a yamutse?towel ne underwear ne comb ne mayuka ne turaruka ne kai tarkace dai wanda da alama a safiyar yau kafin ya fita yayi amfani da su warwatse bisa gadon bedsheet din kansa duk da babu datti amma ya yamutse,kowanne abau ta maidashi inda ya kamata cikin qanqanin lokaci dakin yayi fes komai ya dawo cikin hayyacinsa ta kunna kaskon turaren wuta electric ta zuba irin turaren wutan da take amfani da shi a bangarenta sanna ta wuce toilet
Toilet ne qaton gaske wanda yakai girman ciki da falo na mata da yawa yana dauke da duk wani kayan amfanin toilet na zamani,cikin lokaci qanqani shima ya dau haske komai na cikin sa farine sai da ya dawo daidai tamkar ka zuba abinci a qasan ka ci,sai da komai ya mata yadda take so ya wadatu da sanyayyan qamshi sannan ta bude qofan ta koma falon don ta qarasa aikinsa
Salima ta bar falon saidai ga gwangwani nan da tasha malt cups da qarin ledojin cake da na wasu tarkacen ciye ciyen nata watse a agun da ta tashin,baki ta tabe cikin ranta tana cewa"Allah ya sawwaqe an san yadda za'a bata amma ba'asan yadda za'a gyara ba sai kace ba mata ba,tana wanna zancan zucin tana kammale falin duk da girmansa kuwa,har kitchen bata barshi a baya ba sai da ta gyareshi ,"haba duk kyan abu ai yana buqatar gyara"inji fadila tana riqe da qugunta ta fada bayan ta gama aikin tana qarewa bangaren kallo yadda ya koma tamkar ba shi ba
Aikin ya ja mata lokaci sosai kuma ya gajiyar da ita,tana kimawa bangarenta nan ma dai ba zama din kitchen ta shiga ta kama habarta🤔 cikin tunanin me zata girkawa aliyyu wanda zata iya kammalashi kafin kiran sallar magariba ganin gashi hudu tayi har da rabi,abu mafi muhammancin ma bata san choice din aliyyu ba ,sai ta yanke a ranta bari ta fara gwadashi da tuwo ta gani din ta fuskanci wasu mazan ba sonshi suke ba in yaso idan yayi masa shikenan an wuce gurin
Tuwom shinkafa ta daura miyar danyar kubewa wadda ta dagargaza mata zallar tsokar kaza sanna ta sa tantaqwashi ya wadatu a ciki,misalin qarfe shida komai ya kammala ta soma mulmula tuwon da yayi fari sol cikim farar leda ya tuqu sosai ya hada jikinsa,sababbin warmers masu kyawun tsari ta dauko ta jerashi a ciki,ta gama ta gyara ko ina kamar bata yi aiki a kitchen din ba,ganin tana da ragowar lokaci yasata ta dora farfesun danyan kifi ragon ruwa maimakon zaman jiran dahuwarsa sai ta hada zobo wanda ta markada wadatacciyar abarba ta zuba a ciki ta hada da citta da kanunfari ta dafa,shima ta zubasu a mazubi ta wanke tukwananta,cikin azama ta shiga toilet ta silla wanka
😂😜 na gano su maman sa'ida fa na son jin qwaqwaf an baza👀👂🏻👄 anason aji ya aka kaya ko
To🤔🤔🤔kada dai ku gaji ku biyo safiyya insha Allah don jin kanun labaran
Mrs muhammad dinku ce 07066139278
📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻



[10/16, 12:38 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

WA YASAN GOBE?

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

▶2⃣6⃣

A bakin mudubi ta yada zango ta fara shafe loko da saqo na jikinta da turare dama ta saba da yin hakan kwalliya irin ta zamani mai tsari ta shiryawa fuska fuskarta bata cikata da jagwalgwalo ba ta taje gashinta mai tsaho da sulbi ta daureshi da ribbon ja swiss lace ta saka orange mai adon ja riga da skirt dinkin rafa wanda yayi masifar fito da sharp dinta,ta bata lokaci tana zana dauri a kanta ya zauna gwanin sha'awa fashion ta saka na dutse na sarqa da dan kunne sannan ta cika hannunta da awarwaro irin na india ja mai ashirin da hudu ya ahmad ne ya taho musu da tsarabarsa sati biyu da suka wuce,plate shoe ta saka orange and red ta sake feshe jikinta da turaruka sanna ta kalli kanta a mudubi,masha Allah ta fadi ba tare da tasan ta fadi ba sai murmushi ya subuce mata ita kanta yau ta sake gasgata kyawun da ake fadar tana da shi,kiran sallar magaribar da taji shi ya sata saurin fitowa ta shiga kitchen ta shirya kayan abincin ta kulle sashen nata ta fito tana tunanin qila ma aliyyu har ya dawo,ta cikin balcony din ta ta isa sashen ba alamun ya dawo don haka ta sa key dinta ta bude tana shirin shiga tajiyo alamun tsayuwa mota ta waiwaya sai taga samirah ce ke shirin fitowa daga motar tata wani irin kallo samiran ta watso mata wanda fadila ta gaza gane mai take nufi,dauke kanta tayi abinta ta shige don ba ita bace a gabanta tana mamakin masifaffen yawo irin na samira

Cikin qwarewa ta shirya table din sannan ta sauko cikin falon ta kunna tafkekiyar t.v plasma din dake manne a bango cikin sa'a kuwa malaminta ne ke karatu a saudi qur'an ta dan qaro volume matsakaici ya game falon ta koma gefe ta tada sallarta cikin nutsuwa bayan ta idar ta koma ta zauna tana kallon yadda mahajjata ke dawafi

Mintina biyar da zaman nata taji ana bude get jikinta ya bata Aliyyu ne jikin window taje ya dage labulen tana kallonsa har ya fito daga motar dukkan alamun dake nuna gajiya ga mutum sun bayyana a tare da shi,duk da ya gajin amma a nutsenshi yake kyawunsa na nan saidai fara'a da tasake yiwa fuskarsa qaura hirar da fadila keyi kenan ita da zuciyarta nasiru ne ya kulle motar bayan yafito sanna ya miqa masa kayayyakinsa da muqullan cikin rusunawa kamar ko yaushe aliyu ya karba yana cewa👉kada kowa ya jirani gobe ka sallamesu don bazan fito da wuri ba idan ka sallamesu sai kuci gaba da list din suna yan wadanda suka karbi kayan amma a cire sunan alhaji hamza wannan mun gama da shi✋🏻,nasiru yace ok insha Allahu ya juya yana shirin wucewa yace Allah ya tashe mu lafiya,ameen ya amsa masa

Burinsa ya isa gida yayi wanka ya samu abinda zaici ko da tea ne donshi kam har yau cikin matan gidan babu wadda zai nuna👉�yace girkinta ya masa har gwara salima yakan qoqarta yaci indomie dinta don kore yunwa,yayi mamakin ganin qofar tasa a bude amma sai yayi zaton ko salima ce,ba wani dadi da yaji don ason ransa so yayi ya zauna shi daya ya samu hutu

Saidai yana tura qofan wani daddadan qamshi ya daki hancinsa wanda ya tilasta shi lumshe ido kasancewarsa ma'abocin son qamshi sai ya shiga tunanin inda ya taba jin qamshin amma ya kasa cankowa idanunsa suka sauka a kanta bata anakara da ya shigo bane ko tsorone ya hanata motsi?ya dan tabe bakinsa 😠yana tunanin mai ya kwao ta kuma? Ya qarasa shiga falon yana sallama a nutse ta dago tana amsawa ya dan zubawa fuskarta ido zuciyarsa na son yaba wani abu amma ya rasa meye shi?ita kuwa gabanta ke faduwa cike da fargabar kada ya wulaqanta aniyarta yadda ya saba ganin yaddda ya hade rai kamar ya ga kashi,sai kuma taga ya dauke kansa ya nemi kujera can gefe ya watsar da kayan hannunsa sannan ya zauna har baisan sanda yace wash! ba ya sake lumshe ido yana ci gabada sheqar qamshin da ya ji yayi masa har cikin zuciyarsa ya rasa kuma ta Inda ya samu don dai shi har ya bar falon baiji qamshin ba sai yanzu da ya dawo

📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

▶2⃣7⃣

Sannu da zuwa tace cikin cool voice dinta,ya bude idonsa tana durqushe gabansa riqe da cup da jug na glass baice komai ba yabi hannun nata da kallo dake riqe da cup din tana tsiyaya masa lemon zobon dake ta tsatstsafar sanyi da qamshin abarba ta janyo center ta dora a kai sanna ta balle murfin gorar ruwa na c'bon ta cika masa shima cup da shi ta ajjiye masa duk baice komai ba cikin dari darin kada ya gwasaleta ta miqe ta dauki briefcase dinsa safa takalmi key dinsa da duk ya wurgar din ta yi cikin daki da su

Tana shiga tayi maza ta maida qofar ta jingina jikinta ta dafe qirjinta tanajin yadda yake bugawa da sauri da sauri idanunta a lumshe tana dan murmushi☺, cikin zuciyarta tana cewa wai Allah na! Sai da ta dan nutsu sannan ta ajjiye kayan a inda ta tsara musu kai tsaye ta wuce toilet ta kashe makunnin heater din don har jar danja ta kama alamar ruwan ya tafasa ta hada masa ruwan wankan a bathtub ta saisaita shi ya zamo mai dumi sosai yadda zaiyi saurin saukar da gajiya sannan ta zuba masa turarukan wanka a ciki

A hankali yasa hannu ya dauki cup din zobon yana tunanin meye wannan? Ya kai bakinsa da niyyar dandanawa sai gashi ya shanye har da qari sai da yasha cup uku sannan ya saki ajiyar zuciya saboda yadda dadinsa da sanyinsa ya ratsa shi sai yaji kaso goma na gajiya da qishirwarsa har ma yunwar sun fara sakinsa ya samu relief har a qwaqwalwarsa ya jingina bayansa da makarin kujera

Sai a yanzu ne ya lura da canjin da falon ya samu ko ina tsaf tsaf kamar yadda yake so,tunanin wa ye yayi aikin yake don shi kqm daga samira har salima yasan cewa matane masu azabar ganda da ko ruwan sha sai ya tambaya ake iya tashi a dauko masa,ga ruwan wanka can a toilet ko kana da buqatar yin wanka,ya dago da kansa tuni har tayi hanyar kitchen fadila tayi hakanne don gujewa baqar maganarsa ko da ziyi mata ta maqale a window din kitchen tana leqensa

Sai da ya bata lokaci sosai har fadila tayi zaton bazaiyi wankan bane ta soma dana sanin shishshiginta sanna ta hangoshi yana kwance agogon hannunsa hadi da cire suit dinsa ya riqesu a hannu ya shige dakin tabi bayansa da kallo,ta janye idanunta hadi da lumshesu ta dafe goshinta da tafin hannunta tana cewa a can qasan maqoshinta"wo hoho Aliyyu badai miskilanciba?.... sai kuma ta sake sakin murmushi tana cewa"Allah ka mallakamin Aliyyu"tayi saurin dafe bakinta tama zare ido saboda ta fuskanci maganar zuci ce ta fito fili

Sak yayi ya tsaya yana kallon dakin baccin nasa komai kamar yanzu aka jerashi ko tsinke babu a farin tiles din dake mamaye da dakin ya jinjina kai ya ajjiyr kayan hannunsa a gefan gado ya fara binciken inda ya ajjiye rigar wankansa sai ya bude wardrobe donnya dubata a ciki,canji idanunsa suka masa karo da shi,wardrobe ce ta jikin bango mai hangar komai ya canza bangaren shadda daban yadi daban suit dinsa haka kai hatta socks dinsa da handkerchief an masu nasu tsarin bai san sanda ya saki murmushi ba don tsarin ya burgeshi kasancewarsa dan gayu ya tabbatar babu tsarin rigar wankansa a gun don haka ya haqura ya wuce toilet cikin ransa yace wonderful cikin wani glass dake manne a kwanar bandaki ya hango rigunan a tsare jikin hanger bai bata lokaci ba ya shige cikin ruwan wankan duminsa da qamshinsa suka ratsashi sai yaji kamar kada ya fito,ya shafe kusan minti talatin sannan ya sabe jikinsa ya dauraye ya fito bisa gefan gadon ya zauna ya tsane jikinsa ya nemi farar jallabiya yasa don yafi son sata idan ya dawo daga aiki ya taje kansa ya feshe jikinsa da turare sanna ya bude jakar computer dinsa ya cirota yayi waje da niyuar shiga kitchen ya tafasa ko tea ne ya sha

Ganin ya zauna yana aikinsa ya sanyata debo kayan ta shimfida babbar ledar cin abinci a gabansa baisan me takeyi ba sai da yaji qamshin abinci nata shiga hancinsa sanna ya dago kansa ya dubi gabansa ta jera tuwon a farin kyakkyawan plate miyar na wani dan kwano na tangaran shima fari ne tasha man shanu ta cika wani plate din da farfesun ragon ruwan ta zuba ruwa na sha da na wanke hannu ta tsiyaya masa lemo sanna ta janyo tissue box ta ajjiye masa tace bismillah ya kalleta 😠yace " ce miki akayi da yunwa na zo? Ko an baki labari ina buqatar abincinki kinga malama kwashe abincinki ki ban wuri,

Ba qaramin sosa mata zuciya maganganun suka yi ba bata san sanda hawayen da take boyewa suka silalo mata ba😭karo na farko kenan tun sanda ya fara mata cin kashi,batayi qoqarin maidasu ba ta barsu suka ci gaba da zuba

Cikin zuciyarsa addu'a yake allah yasa kada ta kwashe din don tunda yaji qamshin sha'awar cinsa ta kamashi ai kuwa aadu'arsa bata karbu ba don a zuciye ta soma maida abincin cikin warmers din 
😜😜😜

Kuyi haquri da wanna yau bani da chargy wadatacce

Mrs muhammad na muku fatan alkhairi👏🏻

📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:39 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

WA YASAN GOBE?

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

▶2⃣8⃣

Sai da yaga da gaske take cikin daurarriyar fuska yace kinga malama zuba kada a qarani gaba ace bani da adalci tunda kin kawo kanki" ya fadi kamar wanda da gasken tilastashi akayin,kalmar tunda kun kawo kankin tayi matuqar bada gudun mawa wajan qona mata rai don haka hawayen da suke zuba suka qara gudu😭

Malmala daya ta saka masa da miya ta miqe wata zuciyar na zugata kiyi tafiyarki kawai wata kuma na lallashinta da hanata tafiya tana gaya mata saurin fushi ba nata bane yanzu da sauran lokaci dai,kujerar da ta tashi a kai can ta koma ta zauna tana qoqarin maida kukanta ta canza tasha zuwa mbc boollywood ta tarar suna film din kuch kuch hotahie tsohon film ne amma bata gajiya da kallonsa

Ta kasa hankalinta kusan gida uku kason farko na kan aliyyu ne da taga ya ci gaba da danne dannensa a computer ya shanya abincin,na biyu na kan matan gidan da ta ga har yanzu ba wadda ta leqo da niyyar yi masa barka da dawowa ashe haka suke masa har ita din?,na uku kuma ta dorashi kacokam ne bisa t.v dake gabanta sai ka rantse da Allah ta bata hankalinta ne gaba daya

Ta gefan ido taci gaba da satar kallo da nazarinsa sanda taga ya rufe computer din ya sauko qasa mamakinta zaman da taga yayi zamane irin wanda annabi yake yayin cin abincinsa mamakinta ya sake qaruwa ne sanda taga yayi bismillah ya sa hannunsa ba tare da ya nemi cokali ba

A hankali taci gaba da bi biyarsa da idanunta,yanayin yadda yake cin abincin a nutse yq burgeta tana ankare da shi har sanda ya cinye ta biyu ya soma cin ta uku,ranta yayi mata dadi ganin yadda yake cin abincin bisa dukkan alamu yayi masa dadi

Hankalinsu dukkansu ya kai bakin qofar jina naturo ta,saluma ce ta shigo da yalwar fara'a a fuskata amma sai taja tayi turus ganin fadila a falon,cikin iya tsabar duniyanci da iya waskewa ta gayyato fara'a fuskarta ta dubi sashen aliyyu tace" a'ah dear inacan ina zullumin yau ka jima baka dawo gida ba"ya miqamata hannu sanda ya sa lomar tuwo a abakinsa yana mata nuni alamar ta taho ,ta taho din kuwa ta zauna kusa da shi sai da ya hadiye sannan yace almost one hour da wani abun da dawowata na gajine shi yasa ba wanda na nema"da ido ta nuna masa fadila tana masa nuni da ita ya akai tasan da dawowarsa har ta rigata zuwa?,dauke kai yayi kamar bai fuskanci abinda take nufi ba don ba'a haka shi da shi,itama tasan hali don haka ta bar maganar

Murya a anarke tace dear dama zancan ankon lubabatu ne qawata da nayi maka,kudin nakeso na karba don banason in zama a qarshe saboda baka fiya samun mai kyau ba"ya gyada mata kai yana ci gaba da cin abincinsa,ta tsare shi da ido ganin baice komai ba bayan gyada kan sai tace sake cewa naji kayi shiru baka"ya dago cikin qosawa yace ba munyi maganar ba tuntuni ba kuma ana amsa miki kuma yanzu baki ga abinci nake ci ba" tace cikin son wayancewa ok takai dubanta ga abincin gaban nasa sannan tace" dear yaushe ka fara cin tuwo?"kai tsaye yace "yau"cikin mamaki ta maimaita yau" ya gyada kai yace "yes"sai kuma tace ammafa nima abincin ya burgeni bari muga"ta tsoma hannu a plate din nasa,aliyu ya tsaida cin abincin ya bata fuska ya dago yana dubanta "repeatedly am telling you duk sanda kika soma cin abinci ba tare da kinyi bismillah ba kina cine tare da shaidan ko?" Ta dan dafe kai tace oh sorry na manta bismillah amma fa abincin nan dear yayi sosai a wane restaurant ka siyo" na gida ne ya bata amsa ya dan dubi sashen fadila wadda idan ka kalleta a zahiri zakayi tsammanin kallin film dinta takeyi haiqan sai dai duk tana jinsu tayi kunnan uwar shegu da su,salima ta fuskanci abinda yake nufi don haka ta tsuke bakinta😷tana da na sanin yabawar da tayi wa abincin din bata yi tsammanin fadilan ce tayi ba

Salima na ta zubawa aliyyu surutu jefi jefi yakan tanka mata har suka kusan tashi da abincin gaba daya har farfesun kifin,suka gama aliyyu ya koma kan computer dinsa ya ci gaba da lissafe lissafensa na kayyayakin dake cikin store da wadanda za'a zuba sababbi da kuma wadanda ya saba rabawa yan kasuwan

Har kusan tara na dare salima na zaune taqi tafiya,cikin haka saiga samira itama ta shigo yanayin samira ne yasa sauran kadan farida ta tuntsure da dariya duk da quncin da zuciyarta ke ciki,nikam safiyya kasa daurewa nayi sai da na dara😂😂 har sai da maman walid ta rufemin baki don kada su ganni

Zanin shadda ne a jikinta rigar atamfa dankwalin material,har abada ba zaka ga kwalliyar samirah cikin gidanta ba idan har kana son ganin kece ado tofa saidai idan fita zatayi cikin qawaye takan ce kada a raina min wayo ina gidan nera dole na dinga keta shiga da kowacce mace zata kiyayi kanta tasan tana tare da matar Aliyyu salim maitama(kunji wata toshewar basira fa)

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻

03:15 pm

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

WA YASAN GOBE?

▶2⃣9⃣

Salam! Samirah tace cikin daga murya tana tafiya tana wani budewa babu wanda ta kalla direct ta wuce gun maigidan hannunta dauke da zungureriyar farar takarda,ya dan bar abinda yake kana ya dubeta yana masawa,ta qaraso inda yake ta zauna hannun damansa yayin da salima ke hannun hagunsa takardar ta miqa masa ya amsa kafin ya duba yace" kada ki sake min irin wannan sallamar da kikamun yanzu don ba sallama bace take note,ok?"ta gyada kai tana buntsuro baki,ya bude takardar yana dubawa,ya qare dubawar sannan ya dago kai yana kallon fuskar samiran idanunsa da alamun neman qarin bayani,ta dan yatsine fuska sannan tace"eh abu uwan amfani ne da suka qare nake da buqatarsu" ya dan gayara zamansa ya jingina da makarin kujerar ya sanya idanunsa sosai cikin nata,sai ta kasa kallonsa ta dan soma rikicewa tana son janye idonta ta kasa tasan shi tamkar maye yake wajen naqaltar mutum tasan yanzun nan ba qaramin aikinsa bane ya harbo jirginta,da zarar aliyyu yayi ma irin wannan kallon yake gamawa da kai,sai da yayi shiru na muntina sannan yace"ina zaton yau ko sati biyu ba'ayi ba na karbi list na dukkan abunda baku da shi na kawo.....ya akqi naki ya riga na kowa qarewa bayan ko sati biyun ma ba'a cika ba?"

Ganin tayi shiru ta kasa bashi amsa yasa ya maida kallinsa ga salima wadda tayi kasaqe tana sauraronsu zuciyarya cike da farinciki tana mai addu'ar Allah yasa a ci mata mutunci"nawa ne kudin naki ankon"tawani yi fari da ido sannan tace😊 atamfa dubu arba'in ne lace dubu sittin aai gudun mawar da zan bata dubu dari"(kunji tsabar rashin hankali irin na wasu matan mutumin da duk qarshen wata yake fita da su suyi siyayyarsu idan akwai abinda sai anshiga kasuwa ake samu zai sa su su rubuta ya bayar a akawo musu haka nan kayan abinci da na ciye ciye zaisa a sabunta miki koda basu qare ba kuwa ruwanki ne kisan yadda zakiyi da

Please Login or Register in order to submit comment